Showing 42001 words to 45000 words out of 130520 words
Chapter 15 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
na daf da gama sakandire, sai mace ita
ce a sakandire aji uku. Ta rabu da baban yaran
tun suna kanana ta zo ta kama haya ta ke
kasuwanci, ta ke kula da *ya*yanta.
Ba laifi matar tana da kirki da yawan fara'a da
jan mutane a jikinta, bakinta rai-rai-rai saboda
iya magana, don haka gidanta kullum a cike da
mutane yake, mata da maza, kawayenta da
kawayen *ya*yanta, *yan uwanta da *yan uwan
tsohon mijinta zuwa suke yi tana maraba da
kowa.
Ta ja ni a jiki sosai muka saba tun lokacin
Nasiba,
shakuwarmu ta fi yawa a lokacin da na dawo ni
kadai, ba ni da abokiyar shawara sai ita. Gidaje
hudun kuwa da suke gefenmu, gidan wasu kabilu
ne ba musulmai ba ne, wa da kani, daya sama
daya a kasa da matansu, ko na ce dadironsu,
wadannan ba ma harka da su. Sai dayan ginin
Hajiya Bishra a kasa, mijinta ya mutu ya bar ta
da yara,
amma fa duk ta aurar da *ya*yanta. *Yan mata
biyu ne suka rage mata sa'annina ne, Nana da
Wahida,
suna neman gurbin karatu a Kaduna Polytechnic.
Sai saman su wata amarya ce ba su dade da
tarewa ba, mai suna Bara'atu ta riga ni aure har
ta haifi
*yan biyu. Ita ma kawance muke yi na hakika
kamar yadda mai gidanta Kamal da maigidana
suke yi saboda su dukka banki daya suke aiki.
Duk wani sirrina, na gidanmu can Dugge dama
tsakani na da mijjina da kawata Bara'atu nake
tattaunawa saboda na yarda da ita.
Mijina sai ya yi ta jiyo maganarsa ya rasa daga
inda magana ta ke fitowa. Ban tashi ganewa ba
har sai da abu ya kwabe, a lokacin da bazan iya
gyarawa ba...
Kamar yaya? Abdul-Sabur ya tambaye ta cike da
rashin fahimta.
Cikin jimami Umaimah ta ce, ''Matsalata da
Bara'atu ke nan, sai ni da Zulaiha Senegal.
Auntyna nake kiranta koda yaushe sai na dauki
kayan abinci kamar idan zanyi wainar shinkafa ko
alala, to ban iya sosai ba, ita take koya min. Ko
ta shigo da kanta har gidana ta koya min, ta
koya min yadda zanyi
magana da miji, da yadda ake tafiya da kissa
gami da kisisina. Na dauke ta tamkar *yar uwata
Nasiba, saboda yadda ta ke nuna min, sai na zaci
tana sona.
Abdul-Basi ya fara min fada akan na dinga ja da
baya da Makwabtana, dan ya ga na bawa
Makwabta gaskiya fiye da shi mijina.
Ni kuwa a wajena dole ne na shiga makwabta
saboda zaman gidan ya yi min yawa ni kadai, ga
yawan dauke wuta haka ga mijina baya dawowa
sai karfe takwas ko tara na dare tun karfe bakwai
na safe. Idan ma na zauna ni kadai tunani ne ya
ke addabata na yi ta kuka. Da jimamin rashin
mahaifiyata ko *yar uwata zan ji ko kuma da
takaicin cin amanar da Matawata ta yi min ta
raba ni da wanda nake so?
Makwabta nake shiga in sha hira, suma su shigo
min, amma a ce a raba wannan karfaffan zumunci
ba zai yiwu ba. Don haka ban ji maganar Abdul-
Basi ba, na ci gaba da huldata da su.
Muna nan a haka na samu ciki, na haifi dana
santalele, mai kama da mahaifinsa, aka saka
masa suna Bilal.
Abdul-Sabur da Faduwa suka bude baki don
tsananin mamaki. Tambayarta suke yi, ''Au ashe
kin
taba haihuwa?
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Ina da dana
yana can a gidansu.
Abdul-Sabur ya ce ''Ke kuwa me ya raba ki da
mijinki da danki kika taho kika bar su?
Umaimah ta ce ''Kaddara ce wacce ta riga fata,
kaddara ta sanadin amincewa MAKWABTAKA da
na yo. Kafin na yaye Bilal sai na sami wani cikin,
ni dai tun daga wannan lokacin na rasa kan
mijina, sai na ga kamar ya daina sona, ya tsane
ni. Ya daina shiga harkata, kullum sai ya dawo
gida a koshe ya ce ya ci abinci a waje. Ashe ni ce
ban sani ba Zulayha Senegal ta kwace min mijina,
tun baya biye ta har ya fara.
Ashe tunda magruba ya ke dawowa sai ya shige
gidanta a can zai ci abinci, ya yi kallo, ni kuwa
ina
cikin duhu idan babu wuta ina jiransa ya dawo ya
tayar min da janareto don ba zan iya tayar da shi
ba, ya yi min tauri. Ban san wainar da ake
toyawa ba MAKWABTA duk
sun sani babu wacce ta fada min, sai dai suna
gefe suna tausayamin, idan suka ganni a gidanta,
ko
suka ganta a gidana. Ni ma dai na ga a lokacin
ta fiye bugun cikina ta ji irin zaman da nake yi da
mijina, ban boye mata ba na fada mata irin canjin
da na ga ni daga wajensa, sai ta yi murmushin
mugunta.
Ta-kai-ta-kawo sai in zo in ganta a kicin dina
tana min barbaden magani a cikin kwanukan
abincina.
Rannan kuma na kama ta ta budamin gas cooker
wajen da ake ajiye silinda ta jefa min wani abu,
ashe laya ce. Matattakalata duk ruwan rubutu ne
idan na fito nake gani, sai na yi ta mamaki,
amma
kuma ko kusa zuciyata ba ta taba yi miin zargin
tana bi na da sharri ba. Kuma ban daina kula ta
ba.
Wata ranar asabar da safe cikina ya tsufa ina son
na je na nemo mai aiki a unguwar Dosa, wata
Hajiya Balaraba babar kawata ce ta ke samowa,
ta yi min waya ta ce an kawo masu aiki da yawa
na zo na
dauka.
Kasancewar watan haihuwata ne gani da karamin
da bai fi shekara daya da rabi ba, ba ya tafiya ma
a
lokacin sosai, ga shi daf da watan azumi za,a
fara aiki zai yi min yawa dole na sami
mataimakiya.
Na dade da fada masa zan nemi mai aiki, ya
kuma yarda, sai na sanar masa a safiyar ya zo
ya kai ni na dauko mai aikin. Ya daka min tsawa
ya ce, ba zai kai ni ba.
Na shiga yi masa bayani cikin ladabi duk da haka
ya ce, ba zai je ba sai dai ni na je. Na ce ya ba ni
kudin tasi drop na je na dawo, ya ce ba zai bayar
ba.
Na duba jakata na ga kudin dari biyu ne kawai,
ba zasu ishe ni daukar tasi zuwa da dawowa ba.
Sai na kuduri niyyar hawan acaba na yi sauri na
je na dawo, in yaso Haj. Balaraba sai ta ba ni na
dawowar. Na ce to ya rike min dana na je yanzu
na dawo. Abin mamaki sai ya daka min tsawa.
Ya ce, ''dauki danki ki tafi da shi, ba zan rike ba
nima ina da wajen zuwa. Kuma ki tafi da
makullanki
don bazan jire miki gida ba. Na dauki dana na tafi
jikina a sanyaye ina ta hawaye ina jin bakin cikin
wulakancin da ya tarki yi min, da kyar nake tafiya
ga ciki ga goyo, nauyi jikit.
Na fara jin alamun nakuda dan lokacin haihuwar
ya cika. Na wuce gidan Zulayha Senegal na iske
ta tana ta caba ado sai na ga ta yi min kallon
banza. Na gaishe ta, na shaida mata na kawo
mata Bilal ta rike min zan je unguwar Dosa yanzu
zan dawo, zan dauko mai aiki....
Ban rufe bakina ba ta ce, ''dauki danki ki tafi da
shi, nima unguwa zan je.
Na fice a sanyaye na nufi titi na tare dan acaba
na hau. Banda kuka babu abin da nake yi. A
gaban mai babur aka saka Bilal duk da ya yi
kankanta a zaunar da shi a nan babu yadda zan
yi, tsinin cikina
bazai bari na zaunar da shi a gaba na ba, haka
ba zan iya yin goyo ba.
A lokacin ana taron siyasa a garin, kowanne titi a
garin Kaduna motoci ne (go slow). Don haka sai
muyi mintuna talatin akan titi daya kafin mu
matsa gaba.
Kwatsam ina kan babur a cikin rana ni da dana,
da mai acaba mun galabaita. Juyawar nan da zan
yi,
sai na ga galleliyar motar Zulayha a gefena, koda
na sake wurga ido itace a gefe namiji ne yake
tukawa.
Sun yi luf a cikin AC babu ruwansu da kura, zafi,
balle hayakin *yan acaba, dariya suke yi suna
hira
da shewa, har da tafawa da hannu. Ko da na dubi
mai tukawar sai na ga Abdul-Basi ne.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Na dinga fada a
bayyane, yayin da dan acaban ya gigice, ya fara
tambayata ko lafiya?
Na barke da kuka, yayin da jikina ya dau
karkarwa cewa nake, ''Ga miji na can da
MAKWABCIYATA suna cin amanata.
Zulayha ce ta fara ganina, muka hada ido, sai ta
zunguro Abdul-Basi ta nuna ni ga mu nan a kusa
da su, muna daf da su. Sai jikinsu ya yi sanyi
suka kasa hada ido da ni.
Mun jima kafin a bada hannu, su ka ja da gudu
suka tafi suka bar mu a baya muna gurgurwa. Na
ga masifa a ranar, na ji kamar na hadiyi zuciya
na mutu. Dan acaban ya yi ta yimin nasiha yana
bani hakuri, suna gabana ina hango motarsu,
hanyar kawo suka yi da alama garin ma zasu
bari gaba daya.
Gudu muke yi kawai a hanya, to ni dai ban san
me ya faru ba, sai na ji mu gijif! Mun watse a titi,
mun yi karo da wani babur din mun fadi. Na fadi
a kan cikin nawa, yayin da dana Bilal aka cilla shi
a gefen titi ya fadi. Ya kurje a fuska da kafafuwa,
ni ma fuskata, gwiwoyin hannu da kafafuwana
duk jini.
Dan acabar ya karye, ya yin da daya mai acabar
ya suma. Nan dai na mike tsaye wuri-wuri ban
damu da ciwon da yake jikina ba, dana kawai na
ke nema. A can gefe aka tsinto min shi, jini gaje-
gaje na rushe da kuka na rungumeshi....
Umaimah ta fashe da kuka, yayin da tausayinta
ya lullube zuciyoyin wadanda ta ke ba wa labarin.
Faduwa ta ce, ''Sannu *yar uwata, ashe kin sha
wuya ke ma?
Umaimah ta nisa ta sa toilet paper ta share
hawaye, ta ci gaba da cewa.
''Alhamdu lillah a kowanne hali nake, sai aka fasa
tafiyar unguwar Dosa, aka kawo motar asibiti
(ambulance) aka zuba mu a ciki, an sace min
jakata, waya ta na hango akan titi har wani ya
dauke na karbi abuna. Wayar Abdul-Basi nake ta
yiwa flashing don ba ni da kudi a wayar, amma
ya ki kira na.
Na yi flashin fiye da sau goma ina so na sanar
masa mun yi hatsari, muna asibiti ya ki kira na,
da na dame shi ma ya kashe wayarsa.
Su Bara'atu na yiwa flashing suka kira ni na
sanar musu halin da nake ciki, na fada musu
sunan asibitin.
Suka gigice ba jimawa kuwa sai gata da Haj.
Bishra sun zo, ni dai ta dana nake yi, ban damu
da kaina
ba. Babu dinki a raunin sai dai aka wanke
ciwukan aka saka mana auduga da iodine. Mun
sha zafi, aka
ba mu allurai da magunguna duk kyauta. Sai aka
zo maganar dan cikina suka ce ya bugu, amma
na
koma asibitin da nake awo na ga likita ya yi sauri
a fitar da jaririn.
Bara'atu da Haj. Bishra na sa su tsayar mana da
me tasi, muka hau muka kama hanyar gida. Fadi
suke,
''Umaimah ma tafi gida kuwa ba asibitin da kike
awo ba zamu je? Saboda maganar dan cikin nan
naki. Ki kira mai gidan ki fada masa halin da kike
ciki mana.
Sai suka ga na barke da kuka, suka gigice ainun,
suna tambaya ta, da kyar na iya fada musu abin
da idanuwana suka hango min, wato Zulayhat
Senegal
da mijina Abdul-Basi a mota suna tafe suna hira
da shewa. Sai na ga sun hada ido sun sunkuyar
da kai kasa,
da alama dai sun san komai, don na ga ba su yi
mamaki ba.
Bara'atu ta fara magana, sai Aunty Bishra ta
dinga zungurarta, wai ta yi shiru. Na ce, ''Au
daman har da abin da zaku iya boyemin? Me
kuwa za ku boye min bayan na gani da idona?
Sai Bara'atu ta gyara zama ta dinga ba ni labarin
abubuwan da suke faruwa wanda ban san da su
ba. Tun ina fahimtarta har na gigice na fita daga
hayyacina, na dora hannu aka na mimmike a cikin
tasi kamar wacce zata sume. Ga ciwo a fuskata,
ga kuka ina yi, ga dana yana nasa kukan saboda
azabar ciwo...
Faduwa ta ce, ''Me suka fada miki?
Umaimah ta goge hawaye, ta ce, ''Labarin
dawowar da yake yi da wuri ya shige gidanta ya
ci abinci, ko ya dauketa suje restaurant su ci. Da
yadda ta ke zuwa ofis dinsa daga dukkan alamu
kuma suna neman juna. Yanzu haka wannan fitar
da suka yi garin su Zulay zasu je Zariya maganar
aurensu, ni ban sani ba,,,,,
Abdul-Sabur ya ce ''Allah Sarki, da kin yi hakuri
kin zauna da ita. Me ye kishiya? Ko wacce ta
zauna da halinta.
Umaimah ta tabe baki ta ce, ''Ban ki zama da ita
ba ita ta fitar da ni dole, Ya zan yi tunda an kore
ni?
Faduwa ta ce, ''Ya aka yi da cikin a ranar?
Umaimah ta sake goge hawaye, ta ce, ''Ba muje
asibitin ba, gida na je na kwanta ni da dana,
MAKWABTA suna jinyarmu. Su Abdul-Basi ba su
dawo ba sai karfe goma sha daya na dare. Ya
shigo yana bata rai don kada ma na yi masa
maganar dazu. Sai ya tsorata da yaga ciwon
jikinmu, ya shiga karkarwa. Ban iya yi masa
magana ba sai Bara'atu
ce ta ba shi labari. Ya fito da makulli ya kinkimi
Bilal ya ce, ta kamo ni mu je asibiti a sake
bincikarmu musamman ma dan cikin.
Haushinsa kawai na ke ji, muka duru a mota har
da Bara'atu muka je. Muna isa saiga Zulayha ita
ma ta
biyo mu a motarta, ban san wanda ya fada mata
ba ma. A gigice ta hau kissa da kisisina, wai ita
tausayi. Likita yayi scanning a cikina ya ce,
''Baby ta mutu a ciki, za su ba ni gado zuwa
gobe a yi tiyata.
Cikin dare nakuda ta taso da kaina na haifi *ya ta
fara jawur mai kyan gaske, amma ba ta da rai.
Kwanana uku a asibiti a kwance, abin takaici
Zulayha ce a kaina ita ya barwa kudin komai,
tunda shi yana ofis sai dare yake zuwa su tafi
gida tare,
sun daina boyemin komai ma a gabana ake hirar
soyayya, wasa da dariya. Abincinta nake ci, haka
dana a hannunta yake kacokan ita ke kula da shi.
Na yi kuka, na sha takaici, ba yadda zan yi sai
kallo da ido.
Bara'atu na sake dora min da wasu bayanan ma
da ban sani ba, ashe an dade ana cin amanata.
Su ma MAKWABTAn abin da suke takaici
ta girme shi, ya fi ta kyau, ya fi ta ilimi ba ajinsa
ba ce. Me zai yi da tsohuwar *yar duniya? Kanta
har da farar fufura, shi da yake da mata kamar ni
fara, yarinya mai kyau da ilimi?
Amsar ita ce ta fini iya duniyanci, bariki zalla,
wayo, iya tattali da rashin kunya, sai kuma asirai
da ta dogara da shi, ta haka ya fara sonta.
Aka sallamo ni na dawo gida zan karbi dana sai
ta hana ni, wai na bari sai na gama jego tukun
na ita
zata kular min da shi. Tsabar kissa ce da son jan
ra'ayin Abdul-Basi ba don Allah ba ne, na hakura
na bar sa. Ta goya shi ta sauke, ta yi masa
rawa, ta kai shi kantina siyayya kala-kala.
Uban kuma sai ya yi ta jin dadi.
Wata asabar suka shirya a motarta shi da ita
suka tafi Gombe wajen mahaifansa, zai gabatar
da ita a matsayin amaryar da zai aura. Kudin
cefane kawai ya wurgo min kan cinyata, ya ce mu
mun tafi
Gombe sai goben za mu dawo.
Na san da ita za su tafi, na daure ban tambaye
shi ba balle na yi korafi, ya samu damar yi min
rashin
mutunci. Ya kada kai ya fice da jakar kayansa.
Na tafi wundo da gudu ina lekensa, na ga ya
shige gidanta fiye da mintuna ashirin, sannan
suka fito a tare, ashe shaddar jikinsu iri daya ce.
Ita ta dinko musu daga Senegal sun yi kyau, sai
kamshi suke yi.
Ina saka ran za su miko min dana kafin su wuce,
sai na ga har da shi da kayansa suka shige mota,
an yi masa kwalliya shi ma. Na manta rabon da
na ga dariyar Abdul-Basi amma tunda suka shiga
mota suka fara hira da dariya, har da
kyakyatawa.
Na sake bin daya wundon da gudu don na ga
fatarsu daga get, to ko na gani ma ba komai zai
kara min ba banda tsabagen takaici da kunar
zuci. Suna tafiya na sulale na zauna na dora
hannu aka na surnano da wasu zazzafan hawaye
mai radadin fita.
Kafin hawayen ya diro kasa sai na ga Haj. Bishra
a tsaye a gabana, na yi sauri na goge hawayena
ina
kokarin wayancewa. Sai ta ce, ''Kada ma ki bata
hawayenki *yata, ki kwantar da hankalinki, ki
saka musu ido kawai,
komai ya yi farko zai yi karshe. Da yarinta jikinki
shi yasa kike amincewa kowa alhali ana cutar da
ke.
Ba Zulayha kadai ba, duk wasu da kike mu'amala
da su a gidan nan sai kin yi taka-tsan-tsan,
kuma kin rufe bakinki, kin boye sirrinki.
Ba ta fada min ba dai baro-baro saboda gudun
haddasa husuma a matsayinta na babba, amma
tabbas na san akwai wata magana a kasa. Sai ta
tashe ni tsaye ta zaunar da ni akan kujera ta ci
gaba
da yi min nasihohi masu kwantar da hankali, sai
na ji dan sanyi a raina. Na yi mata godiya ta tafi
na kasa cin abinci, shi ya sa ban dafa ba. Daga
lemo da biskit sai ruwa na yi ta sha, a lokacin ina
da kiba
tunda na yi wannan ramar har yau ban mayar da
jikina ba.
Da na tuna da son da Alhaji surukina ya ke yi
min, sai ban damu ba nasan da kyar zai amince
ya bar Abdul-Basi ya yi wannan auren.
Mahaifiyarsa ce dai na ke zaton zata amince, don
duk abin da *ya*yanta suke so shi ta ke so, ba ta
hana su. Na dukufa ina ta addu'a ina kuka akan
Allah Ya dawo da hankalin mijina kaina, don na
ga ba ya sona yanzu.
Bara'atu kawata, makwabciyata ta shigo gidan da
yamma da sababbin gulma, ita ba kwantar min
da hankali ta zo ta yi ba, irin na Haj. Bishra, sai
ma tayar min da hankali ta sake yi. Mijinta ne
yake sanar
mata da komai, duk hirar da suke yi da Abdul-
Basi akan Zulayha. Wai shi Zulayha ta fiye masa
ni, gara ya auri babba mai hankali wacce ta san
tattalin miji ba irina ba, raino kadai yake yi. Ni ma
na saki baki
na yi ta fada mata irin wulakancin da yake yi min,
Allah Sarki! Kuruciya dangin hauka.
Ba su dawo ba sai washegari lahadi, da daddare
ya dawo gida bai yi min bayanin komai ba ya
shige dakinsa ya kwanta kamar yadda ya saba,
ya raba daki da ni yanzu. Da sassafe ya fice
wajen aiki ko kudin cefane bai bani ba, ina sallah
na ji fitarsa.
Misalin karfe goma da rabi na safe na ci kuka na
gaji, na fito barandar waje na tsaya ina mai kallon
gidan Zulayha, sai kawai na yi ido hudu da
Babangida dan gidan Yayata a zaune akan kujera,
dana Bilal akan cinyarsa. Yana ganina ya zabura
ya ce, ''Aunty Umaimah''. Bilal ma ya hau tsalle
da
murna da ganina.
Na yi matukar razana da ganin Babangida, na
dafe kirji na ce, ''Lah yaushe ka zo?
Ya ce, ''Ni da Abba muka zo jiya, ai na dawo
Kano gaba daya za'a saka ni a makaranta a nan.
Anti Zulayha ta ce min ba kya nan ni daman a
wajenki zan zauna''
Sai ya mike da sauri ya ajiye Bilal yana shirin ya
zagayo wajena. Sai na ce, ''Ka taho da Bilal shi
ma.
Ya dauko shi suka taho, a falo na jiyo muryarta
ta ce, ya koma ya zauna babu inda za su je. Sai
na ji
shiru ba su zagayo ba. Na fusata ainun na kwalla
kiran sunansa, amma kiri-kiri matar nan ta hana
shi amsawa. Ban dauki gyalena ba sai na fita na
shiga gidan haka nan. Na iske su a zaune a
gabanta sun