Showing 33001 words to 36000 words out of 130520 words

Chapter 12 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8030

yi mata bayanin
abincin da ta ke dafawa da yadda ake yi.
Tabbas Umaimah ta karu don ba ta taba sanin
irin wannan launin girkin ba, don ba irin namu ba
ne na Hausawa.
Suka karasa yi tare suka zo suka jere akan dinnin
table, kamshi ne ke tashi tururu.
Da suka gama shiryawa sai suka gayyaci Dan
Aunty zuwa kan tebur. Lolx..
Kowa ya maida yawun sa ni kadai aka gayyata
banda gayyar sodi.
Gani ga...
Alhamdulillahi. En uwa ina godia a gareku na
nuna kulawa da soyayya da kuka taimaka mana
da Addu'oi daga bakunan ku masu Albarka.
Alhamdulillahi.
Masu jiki da sauki sosai dan daya yayan nawa an
sallame shi saura kanin namu.
Allah yasaka muku da Alkhair. Ina mai kara godia
a gare ku baki daya.
Allah yabar xumunci.
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 17
Da suka gama shiryawa sai suka gayyaci Abdul-
Sabur zuwa kan tebur.
Tun kafin ya karaso ya hango abincin gwanin ban
sha'awa, kai ka ce a hadadden hotel suke.
Gwanin sha'awa idan ka kalla, haka kamshinsa
abin so ne balle ka kai baki ka ji dandanonsa.
Cokula (forks da spoons) da faranti (plates) aka
ajiyewa kowannensu a gabansa, ga kufuna da
robobin lemuna (juice) kala-kala, shinkafa da
kaza
suna manyan farantai.
Faduwa ta shiga daddatsa dankwaleliyar kazar
nan gashasshiya gunduwa-gunduwa. Kowa ya
shiga zuba dai-dai cikinsa da kansa. Yayin da
sanyin A.C ya fara ratsa hudojin jikinsu, sanyin
lemon ya dinga kwaranya a cikin hanjin jikinsu.
Sannan dadin abincin ya daki harshensu zuwa
tumbinsu. Nan da nan kowannansu ya tsinci
kansa yana cikin farin
ciki da annashuwa a fuskokinsu. Abdul-Sabur ya
hadiye lomar abincin da yake tauna a bakinsa, ya
kora da lemo mai sanyi (apple juice) ya dubi
Umaimah ya yi murmushi.
Ya ce ''Muna sauraronki Umaimah, layi ya zo
kanki''.
Faduwa ma ta kura mata ido kallo ko kyaftawa
ba ta yi, daga dukkan alamu ita ma ta kagu ta ji
abinda Umaimah zata fada.
Cikin jin kunya Umaimah ta yi murmushi, ta
sunkuyar da kai kasa. Can ta dago ta dube su
daya bayan daya, sai ta yi fari da ido.
Ta ce, ''Yau dai kun rantse sai kunji labarina ko?
To babu damuwa ku bude kunnuwanku da kyau
ku ji tarihina mai taken MAKWABTAKA''.
Ai kuwa sai taga suna gyara zama, gami da sake
miko hankalinsu gaba daya a kanta.
LABARIN UMAIMAH.
''Sunana Umaimah Muhammad Bello, muna kiran
mahaifinmu da suna Baffa, mahaifiyata kuwa
sunanta Mariya ita ma muna kiranta da Yafindo.
Iyayena dukka biyun fulani ne, sun fito daga riga
daya, sunan rigarmu Dugge a karkashin karamar
hukumar Dukku jahar Gombe, a kasar Nigeria.
Mahaifiyata ita ce mace ta uku a wajen Baffa
Bello,
ta same shi yana da mata biyu, Nene da Inna,
kusan su dukkansu sun haife ta ma. Sai dai ba
su taba haihuwa ba a gidan, sai a kanta ya fara
samun haihuwa. Aka haifi Yayata mai suna
Nasiba. Nasiba
ta girme min da shekaru biyar, sannan aka haife
ni, bayan shekaru biyu aka haifi kanina Sabitu.
Rayuwa ce ta kauye daga kiwo, sai noma, surfe
da casa, shi kenan sana'armu. A gidan kasa
dakin
yumbu da rufin ciyawa, sai katangar zana, ba mu
da komai bayan wannan. Yaren Fulatanci kadai
na tashi na ji ana yi a gidanmu, don yaren Hausa
ma
sai daga baya na koya a birni.
Muna zuwa makarantar allo kadai ita ma
makarantar da fulatanci muke karatun, bayan
Fatiha babu wani abun da malaman suka iya. Ita
kadai na san na koya, duk sauran karatu rawawu
fulani ne shirme ne kawai, don haka ilimi ya yi
mana karanci a Dugge.
Babu abin da *yan mata da yara kanana suke yi
mata da maza sai wake a dandali da yamma. Ko
kuma a yi wasan shadi idan bukunkuna sun taso,
mu taru muna kallo, shi ne babban nishadin *yan
kauyen.
Abdul-Sabur da Faduwa har lumshe ido suke yi
saboda zazzakar muryar Umaimah da daddadan
labarinta. Har yanzu harshenta bai warware daga
illar lauyewar da Fulatanci ya yi masa ba. Kana
jin Hausar ka ji ta Fulani, amma sai hakan ya
sake
dadada yaren suka ji tamkar ba yaren da suka
iya ba ne. Hausa ta fi dadi a bakin Umaimah fiye
da a
bakunansu. Don Abdul-Sabur Hausar *yan Ghana
ce fal a bakinsa, yayin da Faduwa kuwa ta
larabawa ce wasu kalaman dai sai dai ta soka da
Larabci.
Umaimah Bello ta yi murmushi, yayin da fararen
hakoranta suka sake haskaka, sai kyawunta ya
sake bayyana. Ta ci gaba da cewa. ''Ba kamar ni
ma ina son wasan gada, raye-raye da wake-
wake, da son kallon shadi da garaya. Idan aka zo
dandali kika fito kina waka kawayenki sai su yi
miki amshi su wake miki saurayinki. Da yake tun
muna *yan shekaru biyar-shida kowacce za a
lakaba mata saurayin dandali, wasu su zarce har
su girma ya kai su ga yin aure, wasu kuwa na
yarinta ne su zubar da samartakan a dandali.
Sunan saurayina Isma'il, ana kiransa da Ilah
makwabcinmu ne, katangar gidanmu daya, daga
hannun dama.
Ilah ya girme min sosai, sa'an yayata ne Nasiba
tare aka yi goyonsu, babu wanda ta hadamu
samartaka a dandali, shi ne daman ya ke
matukar sona tun ina goye a baya. Duk da ni ban
san so ba amma na tashi na budi ido da shi yana
yawan kyautatamun a rayuwata.
Kullum sai ya siyo min rake, mangwaro, ko ya
tatsomin nono da madara kullum ne wannan,
saboda mahaifiyarsa tallar nono ta ke yi kasuwa-
kasuwa. Mahaifinsa na da garkunan shanu guda
biyu suna kiwo. Ilah shi ne karami a gidan, kuma
su dukkan yayyansa maza ne guda hudu ba su
da *ya mace ko daya a gidan, kuma mahaifiyarsu
ita kadai ce mata a gidan, ba ta da kishiya. Muna
kallonsu a matsayin masu arzikin Rugarmu.
MAKWABTANMU daga hannun hagu kuwa gidan
Baffa Modibbo ne, suna da *ya Zahra'u.
Zahra'u kawata ce sosai, tare aka yi goyonmu
ma,
kamar yadda muka tashi muka tarar da Innarta
da Yafindona suna kawance mu ma sai muka
jone.
Kowa yasan tauraruwar nan da ta fi sauran
taurari haske, wato 'ZAHRA' da ake cewa matar
wata ce saboda a koda yaushe tana kusa da
wata. To itama kawata Zahra'u ana kiranta da
'Matawata', babu ma wanda yake kiranta da
Zahra'u a garin, kowa da Matawata ya san ta.
Ni da Matawata koda yaushe muna tare kanmu
daya, farinmu daya, yanayin jikinmu daya, har ma
ake cewa mun juye kamarmu daya kamar wasu
tagwaye.
Allah Ya dora min tsananin sonta kamar yadda
nake son Sabitu da Nasiba, komai a bani a gida
ko a waje sai na boye na rago mata, haka ita ma
ta ke yi. Tun iyayenmu suna dungure mu su yi
mana fada
har suka fara kashi da mu. Don haka a gidansu
ina da kasona, haka itama a gidanmu idan dai
Yafindo
ce ta yi rabo zata raba da Matawata. Dan haka
hasken Zahra ya haskakamin fuskata zuwa
zuciyata ita ce kadai wacce na fi so a cikin
kawayena na Dugge da kewaye. Ita ma tana da
saurayi a dandali mai suna Lawwali, kusan
sa'anmu ne ko ya girmemu da kadan.
Muna ta ji dadin rayuwarmu a haka, don mu ba
mu san akwai wani jin dadin rayuwa ba a duniya
wanda ya wuce haka.
Duk ranar asabar kasuwar garinmu ta ke ci, mu
dunkule *yan nairorinmu nu je mu yi siyayya
kamar Aya, Rogo, Gyada, Magarya, Kurna, Kuli-
kuli, mu yi kallon Garaya da Shadi ko kalankuwa
mu dawo gida. A kasuwar muke haduwa da
fulanin wasu garuruwan kusa da garinmu kamar
*yan Konare, Nzagala da Shuwe. Mu ma ranar
kasuwarsu muna zuwa mu saya mu sayar.
Idan muka je rafi dauko ruwa sai mu shiga mu yi
ta wanka har sai an turo babba ya koro mu, don
ba zamu kawo ruwan da wuri ba, idan tukunya ce
ta tuwo aka dora har sai an sauke saboda ba mu
kawo ruwan girkin ba.
Daman ba mu tashi mun ga ruwan famfo ba balle
wutar lantarki, fitilar kwai ce mai lagwani da
kalanzir, ko aci-bal-bal fitilar kwalba a zuba
kalanzir da tsumma a kyasta ashana ya dinga ci
a hankali.....
Faduwa ta zazzare ido, ta ce, ''Kuna iya rayuwa
babu firij ba fanka?''
Umaimah ta yi dariya, ta ce, ''Ba mu san shi ba
balle mu saba da su.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Wannan ita ce
rayuwar *yan Africa ziryan. Ci gaba da labarinki
Umaimah don ina jin dadin sauraronki.
Da ace Turawa za su ga garinku da sunyi fim da
*yan garin don su irin wannan rayuwar suka fi so.
Umaimah ta yi murmushin takaici tare da ciza
lebenta, ta ce gaba da cewa.
''Muna da Sarkinmu, wato Dagacin garinmu da
*yan fadarsa irin su mahaifina dattijan gari, shi
ne mai
fada a ji, su ne masu yin shari'a idan rigimar
gado ta taso, ko rigima akan shanu, ko rigimar
manoma da makiyaya da rigingimun cikin gida
tsakanin kishiya da kishiya ko mata da mijinta,
duk dai wata rigima.
Ana tsoron hukuma don haka kowa yake ta
kiyayewa ana zaune lafiya sumul babu tashin
hankali.
Cikin gidanmu rigimar da sauki, saboda
mahaifinmu a tsaye yake akan iyalansa dai-dai
karfinsa yana ba wa kowacce mata hakkinta.
Daman dai bai wuce ranar girkinki ba ya bude
rumbu ya auno miki dawa ko Gero kwarya daya,
sai ya dora miki da *yar Murtala (naira Ashirin)
kudin cefane. A ciki zaki sayi abin kadi ki yi tuwo
da miyar kuka ko kubewa ba nama, sai dai ki
watsa wake a ciki idan da hali.
Daman wannan a aje yake, ke zaki zuba a turmi
ki surfa, ki bakace ki dake har sai ya zama gari.
Daga
baya ne ma injin tahuna na surfe da nika ya
shigo garinmu mata suka huta da dakan hannu
ko nikan
dutse. Idan mun gaji da cin tuwo sai a matso
nono a sha da fura, ko kuma a yi mana dawa da
wake, dambu, fate-fate, ko gero da wake. Ko
kuma wasa-wasa. Shinkafa kuwa daman sai
ranar sallah kowanne gida ake yin tuwonta, ita
din ma dai *yar Hausa.
Nama kuwa sai a layya wasu gidajen kalilan ne
suke iya yanka Akuya ko Bunsuru. Shanu da
Raguna kuwa na kiwo ne ba na ci ba, ban ki ba
dai idan Sa ya kasa dole ne a yanka a kai
kasuwa a siyar a cika a sayo wani, a ci kadan
daga cikin naman. Don haka dukkanmu muke
tafiya a kemare saboda babu abincin da zai gina
mana jiki.
Duk wannan labarin da nake baku dukka
shekaruna ba su wuce takwas ba a lokacin.
Bikin nadin sarauta ya tashi a Gombe, aka
gayyaci Dagatan kauyukan da jama'arsu don su
je taya murna hade da duk wani dan wasa da
za,a nishandantar da bikin. Dagacinmu ya
zazzabi *yan matan garinsa wadanda suka kware
da iya wakoki da rawar Fulani za a kai su wajen
taron.
Nasiba yayata tana daya daga cikin *yanmatan
da aka zaba zuwa birni. Ita ce ma zabiyar da
zata bada
waka,, sauran su yi mata amshi, saboda Allah Ya
yi mata kyau da zazzakar murya. Fara ce sol
tamkar Balarabiya ga kyawun kirar jiki, don haka
samarin kauyen suke ta shan dambe a kanta
saboda kowa
yana so.
Mu kanana ne ba a zabe mu ba, don kada muje
mu bata a cikin taro. *Yan mata goma sha biyu
aka zaba, *yan samari biyar sune masu kada
musu ganga da garaya da kuma yi musu goge.
Abin gwanin ban sha'awa aka koyar da su duk
irin rawa da wakokin da zasu yi a wajen.
Ranar taron aka ba su sababbin atamfofi suka
saka iri daya aka zuba su a mota suka tafi, yayin
da
sha'awarsu ta lullube duk wanda ba a tafi da su
ba. Na sawa a raina zan dage da iya rawa da
rera waka
kafin na girma don ni ma a tafi da ni nan gaba.
Ilah saurayina ya ci sa'a an tafi da shi, ya yi min
alkawari zai siyo min *yar tsana da kifi a birni.
Suka kyalkyale da dariya su dukka ukun.
Faduwa ta ce, ''Gaskiya ina jin dadin labarin nan
naki, kamar tatsuniya. Mahaifiyata ce ta ke ba ni
shigen irin wannan labarin da ina yarinya a
matsayin tatsuniya ashe dai irin hakan na
faruwa?
Umaimah ta nisa ta dago ta dube su daya bayan
daya ta yi murmushi, ta tauna naman da yake
cike da bakinta ta hadiye. Ta ce, ''Kamar yadda
yake faruwa yau Umaimah ta na zama a irin
wannan muhalli ba?
Gaba daya suka sake yin dariya, sannan
Umaimah ta ci gaba da cewa.
''Ba *yan garinmu kadai ba duk Kauyukan da suke
karkashin karamar hukumar Dukku suma an
gayyace su kamar: *yan garin Birni, Gombe Abba,
Konare, Nzagala, Zange da dai sauransu a cikin
garin Dukku suka taru a unguwar Se'ngo, daga
nan aka debe su zuwa cikin garin Gombe kofar
fada.
A ranar yini muka yi a karkashin bishiyoyi mu ka
ki shiga gida muna jiran dawowarsu. Tun daga
safe
har zuwa bayan magruba ba mu shiga gida ba
sai da suka dawo. Muna ganin dogayen bus guda
biyu
muka rugo da gudu muna murna. Dagacinmu da
jama'arsa ne suka firfito daga daya bus din, yayin
da su Nasiba suka fito daga dayar. Su dukka
fuskokinsu cike da annuri hannayensu cike da
ledoji da alama sun samo kyaututtuka.
Nan fa aka hau murna da ife-ife. Wajen Ilah na
ruga na ce, ''Ina alkawarinmu?''
Ya miko min *yar tsana da kifina, sai na hau
tsalle ni da kawata Matawata. Yayin da bakin ciki
ya rufe sauran kawayenmu wadanda ba su da
*yar tsana kuma suna tunanin bazan basu aro ba,
ba ma wasa tare da su.
Ledojin Nasiba sun fi na kowa yawa, da muka
shiga gida ta zazzage sai kowa ya shiga mamaki,
har da mahaifina, da yake yana gida bai bi
tawagar Dagaci ba.
''Waye ya ba ki duk wadannan kayan?
Baffa ne ya tambayi Nasiba.
Ta ce, ''Wasu daga cikin kayan a can aka rabawa
kowannen mu, wadannan kuwa ni kadai wani
mutum ya ba ni. Amma ka tambayi mai martaba
ya san mutumin da ya bani kayan, na ga sun
kebe suna magana.
Baffa ya jinjina kai ya bude ya sake bubbudewa,
atamfofi ne manya guda biyu, leshina masu tsada
guda biyu, shaddoji guda uku turare da kudi mai
yawa. Yayin da ka ga kishi da hassada a wajen
Nene da Inna, kishiyoyin Yafindo. Suka fara cewa,
kada a karbi kayan nan a mayarwa Dagaci ya
ajiye ya mayar musu, saboda ba a san ko dan
yankan
kai bane, ko dan iska ne ya yi asirin da zata yi ta
binsa.
Surutai dai barkatai na rashin ilimi da hassada
muraran. Baffa ya zugu matuka, ya dura kaya a
jaka ya tafi fada. Yafindo ba ta ce musu komai
ba,
don so suke ta ce a'a a yi fada, sun hade kai
suna ta musguna mata, to ita kuma sai Allah Ya
yi ta mace
ce mai kawaici, sam ba ta nuna damuwarta akan
irin wannan lamarin, wai a zartar da hukunci a
kan nata ta nuna ta damu? A'a ba ta da haka.
Mu ma ba mu tsira ba, sun tsane mu, daga zagi
sai dunguri,
komai muka yi ba dai-dai ba.
Dagaci yana ganin Baffanmu sai ya ce, ''Yauwa
daman yanzu zan aika a kira ka. Nasiba ta yi miji
a birni, yaro dan boko mai ilimin addini da na
zamani. Kyakkyawan bafullatani dan asalin, dan
sarauta, ya ganta a wajen taro ya dasa, har ya
fadawa
mahaifinsa shi ne suka sa aka kira ni aka
tambayi mahaifinta, na ce bai zo ba. Aka ce na
isar da wannan sako nasu cewar suna neman iri
a wajen ka na neman auren yarinyar nan.
Ba ka kusa sai na ga idan na zartar da hukunci
akan yarinyar nan ba zaka ce komai ba, don haka
na amsa musu da cewar, babu damuwa an ba su
ita.
Mahaifina ya yi murna, ya duka ya yi godiya, ya
ce duk abin da Dagaci ya zartar shi ne dai-dai.
Gaba daya magana ya bari a hannunsa har a
gama Hada-Hadar auren. Ya bar wadannan kaya
gaba daya a hannun Dagaci.
Baffa ya dawo gida ya sanar mana da yadda
suka yi, sai gida ya hargitse mu da mahaifiyarmu
muka dau koke-koke, musamman Nasiba ihu ta
ke ta yi, har da yada zani wai ba ta so,
saurayinta Kamilu ta fi so. Baffa ma ya dinga
kuka yana bamu hakuri, ya ce, babu yadda zai yi
ne yana jin nauyin Dagaci.
Yayin da kishiyoyin Yafindo suka hau shewa da
habaice-habaice wai kuda wajen kwadayi ya kan
mutu, da aka ga kaya an bude ana murna, ashe
za'a je a siyarwa da mai kudi *ya.
Wa ya sani ma ko dan yankan kai ne ana yin
auren ya kashe ta ya gudu ba a san asalinsa ba.
Idan suka fadi haka, sai Yafindo ta sake tsorata
ta rusa kuka, nima ina yi Nasiba tana yi, kaninmu
Sabitu yana yi. Gida ya hargitse har makwabta
suka shigo suna tambaya ko lafiya? Aka fara
yamudidi da maganar a cikin garin, maganar ba
ta bugu ba sosai sai asabar din da angon ya zo
da iyayensa maza, a cikin wata dankareriyar mota
baka.
Abunka da Ruga ba a saba ganin mota mai kyau
ba, sai aka hau guje-guje, wasu suka haye
bishiya, wasu suka labe a bayan Zana, wai ga
yan yankan kai nan.....''
Suka kyalkyale da dariya su dukka. Ba kamar
Faduwa ma har da hawaye ta ke yi dan dariya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Ikon Allah ashe da gaske
ana irin wannan rayuwa a kasarmu. Yaya aka yi
kuma da suka zo?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mu dai muna daga
gaba-gaba muna kallon *yan birni. Sunan
saurayin da yake son auren Nasiba Abdul-Basi,
ya hadu karshe inji samari. Dan Fulani, dogo,
kyakkyawan gaske dan boko. A lokacin yana hada
digiri dinsa a jami'ar Ahmadu Bello (A.B.U Zaria)
bai gama ba.
Mahaifinsa ma mai arziki ne da sarauta a Gombe,
tare da shi suka zo da *yan uwan mahaifin. Aka
yiwa Nasiba kwalliya da daya daga cikin leshinan
da ya bata aka sa kawayenta biyu suka rako ta
fada ta gaishe su. Duk da hawayen da yake zuba
daga idanuwanta, amma ta yi kyau. Abdul-Basi
kallonta kawai yake yi, na so da kauna.
Mahaifina yana kusa da Dagaci aka gama
magana sun nema kuma aka yi musu alkawari an
ba su. Sai
suka yi musu yayyafin naira, wacce sai da su
kansu su Dagaci suka tsorata suka tafi suka bar
*yan gari da yamadidi da zance.
Watan Nasiba ya kama a garinmu, duk lungu da
sako hirar kawai ake yi, yayin da Nasiba ta kaura
daki ta dunkule a lungu ta bude shafin kuka.
Hakuri kadai iyayenmu suke ba ta, da fatan
alkhairi a cikin wannan lamari mai ban mamaki....
Faduwa ta kurbi lemo ta dubi Umaimah, ta ce
''Yaya ta kasance kuma?
Umaimah ta ce, ''A takaice dai an yi auren amma
ba yadda iyayensa suka so a yi da wurwuri ba.
Abdul-Basi mai ilimi ne, ya ce su bari a shekara
tukunna shi da ita su gama fahimtar juna, kada a
yi tana koke-koke tana jin tsoronsa, shi ma a
sannan ya kammala karatunsa.
Da motar haya yake zuwa garinmu, dan acaba ya
shiga da shi har kofar gidanmu. Ya shigo
zaurenmu
ya zauna akan tabarmar kaba a kira masa ita. Ta
kudundune a lungu ta ki magana, sai dai ya yi
hira da kawayenta. Inda ya burgeni sai ya daina
cusa mata kudi sai dai ya yi mata kyaututtuka
kadan-kadan ya fi so ya sami soyayyarta ba don
kudinsa ba.
Haka yake zuwa dandali ya zauna idan ana gada
yana sauraron dadadar wakokinmu na gargajiya.
Ranar kasuwa ma sai dai kawai mu gan shi
tsakiyarmu idan muna Hada-Hadar cin
kasuwarmu.
Ni ce *yar gaban goshinsa daman na cika rawar
kai, sai na yi tsalle na dane shi, ya ba ni kudi na
siyo mana gyafa, magarya, kantu, mu shimfida
tabarma mu zauna mu ci. Ita kuwa Nasiba ko
tana walwala da ta gan shi sai ta bata rai, ta hau
murgude-murguden baki,
kawayenta suna ta shakiyanci suna sake tura ta.
Sai su yi ta ce mata, ''Ka ga amarya, dan ta ga
angonta har wani fari ta ke yi da ido.
Shi ma ya shiga a yi ta zolayarta, dole ta yi
dariya. Wasa-wasa har ta saki jiki da shi suke
hirarsu rangadadai. Kafin ayi auren sai da ya sa
su Baffa suka je gidansu suka gani, Nasiba ma da
ni da kawayenta mun taba zuwa gidansu muka
gaishe da mahaifiyarsa.
Gida ne mai get na bulo da bulo a cikin garin
Gombe. Hajiyarsa ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login