Showing 39001 words to 42000 words out of 130520 words
Chapter 14 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
mai
zafi ta ce, ''Ashe ita ma sonsa ta ke. Yadda ta ke
zuga ni haka a can bangaren ta ke ta binsa tana
min kazafi kala-kala, har da cewa, an zubar min
da ciki a birni.
Har sai da ya ji babu abin da zai yi da ni sannan
ta yi kokarin cusa kanta wajensa, ba shi da zabi
don babu yadda zai yi, amma zancen so ni ce
kadai macen da yake so a duniya. In ba rashin
wayewa ba me yasa ba zai kira ni ya zaunar da
ni ya tambaye ni ba, ko ya aiko mahaifansa su
bincika?
Ni kuma da yarinta sai nayi ta boyewa Yafindona
ko ta tambaye ni idan taga ina damuwa sai in ki
fada.
Shekara ba ta dawo ba aka zo min da labarin
anyi auren Matawata da Ilahna. Suma ne kawai
ban yi ba, amma na gigice, sai da Nasiba ta rike
ni dan da faduwa zan yi. Kuka muke ta yi ni da
Nasiba tun Yaya Abdul-Basi yana ba mu hakuri,
har ya ji haushi ya kwakkwayemu, ya ce, ni da
nake karatu ina ni ina
maganar saurayi a kauye, almajiri dan Ruga? Ina
ma auren zai yiwu?
Ni da zuciyata ne kadai muka san halin da muke
ciki, wannan bakauyen almajirin ya fi min samarin
Birni sai dubu, don shine farin cikina. Duk
tsananin bacin ran da nake ciki idan na ga Ilah
sai na ji sanyi,
don zai lallashe ni ya ba ni labaru masu dadi.
Wannan shi ne cin amana da musgunawar da
MAKWABTANA suka fara yi min a rayuwa....
Umaimah ta sa gefen hannunta ta sharce hawaye
mai radadi.
''Yi shiru daina kuka. Inji Abdul-Sabur da Faduwa,
Su ma tausayinta ya rufe su.
Ta ce, ''Ban koma garinmu ba, har sai da na
shiga aji hudu na sakandire shi ma ba zuwan
dadi ba ne, kawai Yaya Abdul-Basi ya ce mu zo
gida ana nemanmu, ashe Yafindonmu ce ta rasu.
''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Inji Faduwa da
Abdul-Sabur, yayin da kuka ya barkewa
Umaimah.
Ta dade tana yi kafin su lallashe ta, ta ci gaba da
labarin. Ta girgiza kai ta ce.
''Da aka yi sadakan bakwai dole muka shirya
zamu koma Kaduna, saboda watan haihuwar
Nasiba ne,
ta samu ciki da kyar ya zauna mata.
Ilah ya zo ya yi min gaisuwa a tsaitsaye, amma
Matawata ga ni ga-ta, a jikin zanar gidan su Ilah
ta ki yi min magana. Ciki ne ma da ita a lokacin,
har wata rangwada ta ke yi tana shafa cikin. Wai
har na
zama abar zolaya a wajen Matawata duk amincin
da ke tsakanina da ita.
Zuciyata sai ta yi ta tafasa idan na jiyo masoyina
Ilah da aminiyata Matawata suna hira a gidansu.
Tunda a gidan iyayensa aka ba su daki, mu kuma
katangar gidan mu daya don haka ana jiyo
hirarrakin da ake yi a tsakanin gidajen biyu.
Muka koma Kaduna muka yi jugum-jugum cikin
damuwa, mu dukkanmu. Bayan sati uku dai-dai
da rasuwar Yafindo sai haihuwa ta tasowa Nasiba
aka kaita asibiti. Allahu Akbar haihuwar ta zo da
matsala, likitoci suka yi iya kokarinsu wajen ceto
uwar da *yar abu ya ci tura..
Sai kuka ya hana Umaimah ta ci gaba da
magana.
Faduwa ta zabura ta ce, 'Ba dai ta rasu ba?
Umaimah ta gyada kai cikin kuka mai tsanani. Ta
ce, ''Yayata Nasiba ta rasu ita da *yar cikin
dukka.
Sai Faduwa ta rungume ta ita ma kukan ta ke
taya ta don tausayi. Abdul-Sabur ya yi ta girgiza
kai
kalmar ''Sorry-sorry. Kadai ya ke ambato.
Umaimah ta matse hawaye ta gyara zama ta ci
gaba da cewa, ''Na yi kuka, har yau ina kan yin
kuka amma ba zasu dawo ba, sun tafi, sun tafi
kenan. Na damu matuka, amma sai Yaya Abdul-
Basi ya fi ni damuwa, har na fi shi tawakkali, shi
har sai da aka yi ta rike shi don ya rike makara
ya ki ya saki, da za a saka ta a kushewarta. Ta
sha addu'a kuwa a wajensa, ya ce, ''Nasiba, ke
ce matar da na taba so, nake so, kuma zan
dauwama ina so a duniya. Ki sani GANGAR
JIKINMU ce kawai zata rabu, amma ruhin mu
yana tare..''
Hawaye ya yi ta kwaranyowa daga idanuwan su
dukka ukun. Har zuwa lokaci mai tsawo
kowannensu yana matsar hawaye, sannan
Umaimah ta ci gaba da magana.
''Aka kai Babangida Gombe wajen kakarsa wato
Hajiyan Abdul-Basi, ni kuma da kayana kacokan
aka dawo da ni Dugge, sai kunci ya karu. Na
dawo gidanmu dakin Yafindo bata duniya, sannan
babu kawata abokiyar hirata Matawata, babu
masoyina mai saka ni farin ciki, wato, Ilah.
Allah Ya sa Sabitu ya zo a lokacin, da shi kadai
nake hira na dan ji dadi, don shi kadai ya rage
min a
duniya, daga shi sai Baffana. Baffa kuwa ya
tsufa, ciwo-ciwo kala-kala. Kishiyoyin Yafindo
Inna da Nene suka saka ni a gaba suna ta yi min
habaici wai karya ta kare dan birni ya dawo
kauye.
Kullum sai su yi ta zafuta ta da dungure kai, dole
sai na fito daga daki na taya su surfe da girki. Na
ga
tashin hankali don na manta yadda ake surfe da
cin gabza. Yaya na iya, dole na yi ta cusawa
cikina duk abin da na samu, don kada yunwa ta
kashe ni.
Matawata ta haihu, yawanci ma a gidanmu aka yi
girke-girke da taron *yan suna, sai na yi mamaki
da na ji sunan jaririyar, wai MARIYA, sunan
Yafindona ne don dai nasan danginsa kakaf da
nata babu Mariya. Ba su gayyace ni ba suna haka
tashin hankali ya hana ni fitowa daga daki, sai
kuka nake yi yadda ku ka san na tsaga kasa na
shige ta rufe ni na huta don tashin hankali.
Hakika na ji haushin cin amanar da aka yi min,
na shiga zargin ni ce ban sani ba watakila tuntuni
ma suna son junansu. Kamshin suyar naman rago
da dan Akuya har cikin
dakina, amma ko hanji ba a san min ba, raina ya
yi ta biyawa. Babban tashin hankalina ma shi ne
gulmata da aka dasa kungiya-kungiya ana ta yi,
wai na ki auren bakauye na koma birni, ga shi na
rasa dan birni na dawo kauyen,
Ilah ya yi aurensa yanzu bakin ciki zai kashe ni
na ma kasa fitowa cikin jama'a. Su Nene ne
masu kara zuga magulmatan, koma dai mene ne
na fauwalawa Allah komai, Shi ne mai sakayya.
Ba'a yi watanni shida ba kuwa Allah Mai komai
da kowa sai da Ya yi min sakayya a bisa
abubuwan da duk aka yi min...
Faduwa ta dafa kirji tare da yin ajiyar zuciya, ta
ce, ''Me ya faru da su?
Umaimah ta yi nata takaitaccen murmushin, ta
ce,
''Uhum, Allah ba azzalumin bawanSa ba ne. Ashe
tunda Ilah ya auri Matawata ba ya jin dadin
zama da ita, bayan rashin son da yake yi mata ta
cika makirci da hada husuma. Ta hada shi da
*yan uwansa saboda fada da take yi da matansu,
ta raba shi da abokansa ta dawo tana hada
iyayensa fada.
Kullum ba ta shiri da surukarta rashin kunya ta
ke yi mata sosai, shi kuma Baffansa yana bin
bayan Matawata don haka sai a yi ta rigima, Ilah
mai hakuri ne yana zaune ba ya magana duk abin
da
zata yi ba ya iya tsawatar mata. Mahaifiyarsa
har kuka ta ke tana cewa, ta yi asarar haihuwa,
idan
har danta zai auro macen da zata yi mata rashin
kunya a gabansa ya kasa magana. Allah kada Ka
tsayar da ni ranar shaida, an ce bokaye ta ke bi
ta shanye shi, ba ya ganin laifinta sam! Amma
Allah Ya fi ta, sai kuwa aka kama ta da laifin
kwartanci ita da tsohon saurayinta lawwali.
Gari gaba daya sun shaida, har aka rakota gida
da waka ana ga kwartuwa.
A take Ilah ya yi mata saki uku, ina daga dakina
nake jiyo komai. Ban fito ba ma balle ace
tsegumi sai na ji a raina ban ji dadin wannan
bakin al'amarin ba. Domin dukkan
musulmi dan uwan musulmi ne, Allah Ya rufa
mana asiri, Ya sa mu gama da duniya lafiya, Ya
sa mu fi
karfin zuciyarmu.
Abdul-Sabur da Faduwa suka amsa da ''Amin''.
Umaimah ta kurbi ruwan sanyi ta dago da ido ta
dube su, ta yi murmushi don ta ga sun kammala
hankalinsu kacokam a kanta, ita suke kallo.
Ta ci gaba da cewa, ''Ai ba'a yi wata ba sai na ji
an ce ga Ilah can da Baffana a wajen Baffana
suna maganata a aure, Ilah har yana kuka yana
bada hakuri.
Na ji zuciyata ta fusata na kudiri niyyar duk
wanda ya kira ni akan maganar sai na fadi ba
dadi, kuma
ba zan yarda ba, don a lokacin ko ganinsa bana
son yi. Ina cikin tunani ne na ji Baffana ya
kwallamin kira,
na saka hijabina na fito na same su a zaure. Na
durkushe a gefe na gaishe su, sai Baffana ya fara
bayanin.
Ya ce, ''Ga Ilah ya dawo daman makircin
Matawata ne ya raba ku. Na girgiza kai na ce,
''Baffa ka yi min afuwa ka bar maganar nan, don
maganar nan ba mai yiwuwa ba ce. Na hakura da
Ilah tuntuni, ya je ya auri wata.
Wato sai da ya rasa Matawata zai tuno da ni? Ai
ba a 6ari a kwashe dukka.
Nan fa Baffana, Ilah da Baffansa suka hau dogon
fillanci, ni wata kalmar hakurin ma sai a ranar na
taba jinta a fullanci. Suka yi ta magiya Ilah yana
sake fada min duk abubuwan da ya faru tun
farko.
Wai ashe sanda na aike ta wajensa sakon da ta
fada masa daban ne ba wanda na fada mata ba
ne, cewa
ta yi na ce na fi karfinsa yanzu, ya cire ma
maganar aure a tsakaninmu. Sai ya ce tace min
ya gode tunda wulakancin da zan yi masa kenan.
Sai ni kuma ta dawo ta ce min, ya ce, me zai yi
da ni na je birni na zama *yar iska ragowar
maza? Sai a lokacin ya fadi duk abubuwan da ta
fada masa a kaina, ni ma na fada muka gane
Matawata ce munafuka, sai zuciyata ta yi sanyi
na amince zan aure shi. Muka watse daga zauren
kowannenmu
cike da farin ciki.
Dare, Safe, da yamma Ilah yana wajena, koda
yaushe sai ya zo zance, hade da hidimomin da ya
saba yi min tuntuni. Kamar: atamfa ce, mangoro,
rake, kaji da dai sauransu.
Ita ma Matawata tana jiyo hirarmu da shewarmu
daga zaurensu, don gidanmu ne a tsakiyar nasu.
Bakin ciki ya rufe ta, ta rasa inda zata saka
kanta.
Rannan har da fitowa tana zage-zage tamkar
mahaukaciya, yara kuwa suka hau yi mata wakar
kwartuwa. Idan aka yi sata ko kwartanci a kauye
ka shiga uku, gara ma ka bar garin zai fiye maka
sauki.
Muna ta shirye-shiryen aurenmu Ilah ya siyo
siminti ya ce zai sumulce bangon dakina sannan
ya yi dabe a kasa, saboda na saba da gidajen
birni. Muka shiryawa kanmu rayuwar jin dadi ta
aure, irin tamu ta talakawa dai, har yake cewa
yana so ya koma Kaltingo da zama wani Alhaji da
ya zauna a gidansa ya ce zai bude shago ya
dinga jire masa.
Muna tunanin nan da wata uku a yi aurenmu.
Allah Mai yadda Ya so da bawanSa, ashe dai Ilah
ba mijina ba ne har abada.
Faduwa da Abdul-Sabur suka zabura suka ce,
''Shi ma ya rasu?
Umaimah ta matse hawaye ta ce, ''Ilah bai rasu
ba,
har yanzu yana nan a raye, koda yake yanzu ban
san halin da suke ciki ba. ''To me ya faru? Abdul-
Sabur ya tambaya cike da zumudi.
Ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa, da alama dai
tana jin ciwon tuna abubuwan da suka faru da ita
ne a baya. Faduwa ta shafa kafadarta tana
jijjigawa, kamar me lallashin jariri. Kalmar,
''Ma'alesh, ma'alesh''. Ta ke ta ambatowa,
ma'ana 'yi hakuri'.
Umaimah ta dago da jajayan idanuwanta ta dube
su, ta ce, ''Kun san me ya faru? Baban Abdul-
Basi
ne ya dawo wajen Dagacin garinmu aka kira
Baffana aka yi shawara, wai na maye gurbin
Yayata marigayiya. Ma'ana na auri Yaya Abdul-
Basi, babu wanda bai amince ba a cikinsu.
Kwatsam ni da Ilah muna zaune wannan bakin
labarin ya zo mana muka gigice nan da nan sai
kuka ya barke mana.
Mun yi tunanin guduwa ma dai muka fasa, Ilah ya
yi min nasiha ya ba ni hakuri, na yi iya kokarina a
fasa auren nan aka fi karfina.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ba kya
ganin auren Abdul-Basi ya fi miki Ilah, tunda
Abdul-Basin
kin san shi, kin san halinsa, yana da kirki?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba maganar kirki
muke ba kadai, maganar so da shakuwa shi ne
aure.
Faduwa ta ce, ''Haka so yake ba ruwansa da kudi
ko birni''.
Umaimah ta ce, ''Son da nake yi wa Yaya Abdul-
Basi na *yan uwantaka ne ba na aure ba, Ilah
kuwa shi ne farin cikina, shi ne abinda nake
tunawa na ji dadi a zuciyata. Daga dukkan alamu
Yaya Abdul-Basi ma ba ya son hadin nan, an fi
karfinsa ne, babu yadda zai yi.
Amma shi ma ya kasa cire Nasiba a ransa.
Aka tarka ta mu aka yi auren aka dawo da ni
gidan nan dai na Nasiba, ba a dawo da Babangida
ba
wajena, saboda Abdul-Basi ya mayar da ni
makarantar boko, aji biyar. Yana kai ni da safe na
dawo a motar haya idan an ta shi, sai dare yake
dawowa.
Bai taba kusanta ta ba, wata da watanni ina
dakina yana dakinsa. Ina tunanin Ilahna yana
tunanin
Nasibarsa. Ya fada min baro-baro cewar shi fa
Nasiba yake so har yanzu, da zata dawo su
zauna da ya fi masa. Ni ma na fada masa da zai
sake ni na koma wajen Ilahna na zauna da ya fi
min zama a gidansa.
Bai damu ba nima ban damu ba da maganar da
muka fadawa juna saboda kowa gaskiyar abin da
yake ransa ya fada ke nan.
Ba ya damuwa da girkina, balle kwalliyata, haka
ni ma ba na damuwa da na yi masa komai.
'Zo na kai ki makaranta, ungo kudin makaranta,
karbi kudin cefane. Shikenan maganar da ta ke
hadamu. Hakan ya fiye min dadi a rai ni kuwa.
Daga baya ya fara warewa yake yawan shiga
harka ta, yawan jana da hira da kai ni unguwanni
wuraren shakatawa. Ya mayar da ni islamiyya,
ranar asabar da lahadi yake kai ni ya dauko ni, ya
dawo da yi min home work da dai sauran kulawa.
Ni ce nake ta baudewa don ban fitar da ran
komawa wajen masoyina ba Ilah. Da ya dau hutu
ya kai ni gidansu Gombe, muka ga Babangida, ya
girma yana zuwa makaranta. Daga nan na roke
shi
ya karasa da ni Dugge, kai tsaye ya ce 'a'a idan
dai su Baffa ne zai je ya gano su ba sai na je ba'
wai shi
nan da tsiya kishi yake, ya san Ilah nake so na je
na gani.
Na yi ta kuka da ihu har sai da surukata ta ce, ya
tashi ya kai ni garinmu na kwana biyu sannan ya
koma ya dawo da ni. Ya dinga harbamin harara
da ya ga ina murna a mota saboda tsananin
kishi.
Ai kuwa mun kai musu goma ta arziki, kayan
abinci, ya diddika da atamfofi, gidanmu da gidan
Dagaci. Da aka gama gaggaisawa sai Abdul-Basi
ya tafi ya barni. Kudi mai yawa na kunso na
kawowa
tsohona a dunkule a boye na ba shi, ya yi ta
mamaki yana tambaya ta ina na samo kudin nan?
Na shaida masa kudin makaranta ne da ragowar
kudin cefane nake tarawa. Ya yi godiya ya shi
min albarka ya yiwa mahaifiyata da yayata
addu'a Allah Ya sada su da rahama.
Na gyara zama na tambaye shi Ilah, sai na ga ya
girgiza kai ya tabe baki, ya ce, 'Ilah sai addu'a
Allah
Ya hadashi da jarababbiyar mata!. Ina jin haka
gabana ya yanke ya fadi, na ce, 'Lafiya?
Baffana ya yi shiru can ya dago ya dube ni, ya ga
yadda na dimauce. Ya ce, 'Ki rike mijinki, ki rabu
da
Ilah ba mijin da zaki yi tunanin za ki aura ba ne.
Sai na sulale kamar zan kwanta na sume don
fargaba. Baffa ya ce, ''Yarinyar nan Matawata
auren kisan wuta ta yi na sati uku ta fito ta yi
idda ta dawo wajen Ilah, yanzu haka suna tare
tana gidan na ji ance ma wani cikin ne da ita.
Don haka ki je ki kama mijinki ki manta da Ilah a
rayuwarki.
Na matse hawaye na ce, ''Idan Allah Ya so Baffa
na hakura da Ilah a rayuwata.
Na koma daki a sanyaye sai na ji dama Yaya
Abdul-Basi bai tafi ba na bishi mu koma, don
bana son
garin ko kadan.
Matawata ta ji labari na zo, washegari da sassafe
ta shigo gidan ta same ni har kofar dakina ta
zazzage min habaici iri-iri. Wai Ilah nata ne duk
naci da sihirce-sihircena dole na hakura na bar
mata shi.
Ban rama ba ta yi ta gaji ta tafi.
Wasika doguwa da ajami Ilah ya aiko ,in da
daddare yana mai ba ni hakuri da yi min fatan
alkhairi, ya kuma roke ni da na taya shi da
addu'a, rayuwarsa tana cikin kunci don bai yi
sa'ar abokiyar zama ta gari ba.
Ban gama karantawa ba ma na yayyaga na zubar
a shara. Ban yarda na hadu da shi ba har na yi
mako a garin, sannan Yaya Abdul-Basi ya zo ya
dauke ni muka tafi. Tun a hanya ya ga alamu ina
cikin damuwa, da ya dame ni da tambaya sai na
rushe da kuka. Na
shaida masa Ilah ya sake mayar da Matawata a
dakinsa. Wani dogon tsaki na ji ya ja, sannan ya
watso min wata hargitsattsiyar harara.
Ya ce, 'Idan bai mayar da ita ba ke zai saka a
dakin?
Wallahi Umaimah ki rufawa kanki asiri, ki sani fa
kina kona kanki ne, da auren wani a kanki amma
kike tunanin wani katon banza, har kina kishi
akan ya maida tsohuwar matarsa. To ina
ruwanki?
Ya shiga yi min nasihohi masu ratsa jiki ya ce,
gara ni da shi dukka mu yi wa kanmu fada mu
manta da Nasiba da Ilah mu fuskanci sabuwar
rayuwa, Allah ne kadai Ya san dalilin da Ya raba
mu da wadanda muka fi so, Ya hada junanmu.
Marbass Dan Aunty..
MAKWABTAKA 19
Tun lokacin na yiwa kaina fada, na nutsu na fara
kokarin cusawa raina zama da Abdul-Basi a
matsayin miji na, shi ma haka. Sai bayan ma da
na
gama sakandire sannan muka budewa kanmu
sabuwar rayuwar jin dadi da son juna.
Abdul-Basi ya dawo yana sona tamkar Nasiba,
don na juye ta sak! Da na yi kiba, ni ma na cire
Ilah a
raina, na daukeshi a matsayin munafiki na barshi
da Matawata can su karata da bakin
munafincinsu...
Abdul-Sabur ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya aka yi
kika zo nan kasar kika baro masoyinki Abdul-Basi
a can?
Sai ta yi murmushi karfin hali, ta ce, ''Kai ma tun
da ka ganni a nan kasar alhali ina da aure a can
kasan
sai dai idan da wata matsala ne. Kuma ai da
sauran kuka wai anci gumba an hana maye, me
aka yi a hawa bishiyar bare a tsinko reshenta?
Sai Abdul-Sabur da Faduwa suka hada idanu.
Sannan Faduwa ta dafe kirji, ta ce, ''Me ya hada
ku?
Umaimah ta tabe baki ta ce, ''MAKWABTANA ne
suka hada mu,
MAKWABTAKA! ''Kamar yaya? Abdul-Sabur ya
tambaya cike da fargaba.
Umaimah ta yi shuru kanta a sunkuye a kasa,
kamar me tunani. Can ta dago ta dube su,
idanuwanta a cike da kwallah.
Ta ce, 'Na kasance mai saurin yarda da
amincewa mutane, na saba da Makwabtana da
*ya*yansu tun lokacin marigayiya don haka nake
jinsu tamkar dangina.
Kamar yadda na fada a baya gidaje takwas ne a
farfajiyar, sama da kasa guda hudu. Mu muna
sama
kasanmu kuma wata mata ce mai suna Hajiya
Ladidi, *yan garin Minna ne aiki ya kawo mijinta
Kaduna, suna yaren Nufe da *ya*yanta hudu ta
girme ni harta kusan haifata ma.
Sai gidaje biyu da suke fuskantar namu wata
beyarabiya ce amma musulmace mai suna
Zulaiha Senegal. Tana zuwa Senegal tana dinko
kayan mata da maza shaddoji da yadiddika tana
siyarwa *yan siyasa da matan masu kudi. Tana ji
da gayu da rawar kai tana abu kamar wata
budurwa alhali ta
ajiye karatan *ya*ya guda uku. Samari maza
guda biyu har daya ya gama sakandire ya shiga
jami'a,
daya ya