Showing 120001 words to 123000 words out of 130520 words
Chapter 41 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
kwakwaf sun
watse. Ya bude gaban mota ya shiga ya zauna
ya dubi Abdul-Sabur Ya ce "Yayana kada fa ka
damu, idan ka ga aure
anyi shi babu rigima babu kananan surutu ma bai
cika karko ba.
Abdul-Sabur ya girgiza kai ya yi ajiyar zuciya ya
ce "Sabitu gobe zan bar Gombe zan koma
garinmu.
Lafiya?
Me yasa?
Ka fasa aurenta ne saboda Abdul-sabur?
Sabitu ya tambaya a gigice.
Abdul-Sabur ya ce "Haba Sabitu ko raina aka ce
zan rasa ai bazan fasa auren ta ba. Ina jin baka
da labarin irin yaki da wahalar dana sha wajen
nemo Umaimah.
Sabitu ya ce "Kada ka damu Umaimah ta fahimce
ka, mu je kuyi sallama.
Abdul-Sabur ya kunna mota suka nufi kofar gidan
su Umaimah, a zaune a zaure suka hangota ta
tare
da Baffa daga dukkan alamu nasiha yake yi mata,
kanta a sunkuye a kasa tana hawaye. Karar
tsayuwar motar ne yasa suka dago suka kalle su.
Sabitu ya bude ya fito yayin da Abdul-Sabur ya ci
gaba da zama a cikin mota ya kura mata ido
yana kallo cike da damuwa da tausayawar da
yake yi mata. Sabitu da Baffa suka dade suna yi
mata magiya sannan ta yarda ta fito bayan
Sabitu ya shiga cikin dakinta ya dauko mata
gyale da
takalminta. Tafiya take yi cikin sanda har ta
karaso gare shi kanta a sunkuye a kasa, ya sha
magiya
akan ta shigo cikin mota ta zauna zai yi mata
wata magana amma ta ki yarda ta shiga ta
zauna, sai da
yayi ta rokarta kamar zai yi kuka ta tuna ashe ta
daina gudun maganar abunda *yan garinsu zasu
fadi alhali kanta take takurawa kuma duk da haka
bata fita. Sai ta zagayo ta shiga ta zauna, bayan
ta zauna sai Abdul-Sabur ya dubeta ya sunkuyar
da kai kasa ya yi shiru zuwa wasu lokuta masu
tsawo,
sannan ya dago ya dube ta ya ambaci sunanta
har sau uku. Magana yake cikin sassanyar murya
mai cike da damuwa. Ya ce "Ni mutum ne mai
kaifi daya marar boye-boye, ina iya jurewa in yi
hakuri da abunda nake so in har abun nan ba zai
zame min kwanciyar hankali ba, abunda nake nufi
anan shine a lokacin da zan
bar Malaysia na hadu da wani abu mai suna
tsananin kaunar Umaimah ya zo ya hade min da
Faduwa tana tsananin kaunata ni kuma ina
tsananin tausayinta da ganin mutuncinta.
Ba wai na rasa yadda zan yi da ku ba ne ya sa
na gudu na bar ku ba ku dukka, a'a kamar yadda
na fada miki dazu ni mutum ne mai son tacewa
da rairayewa in ga abunda zan yi ya zame min
farin ciki.
Maganar *yar gidan Uncle Hamza dana fada
muku gaskiya ne, na je Ingila na hadu da ita da
mamarta da wanta wato babban dan Uncle
Hamza, a lokacin Uncle Hamza baya kasar. Mun
zauna da su munyi magana tabbas sun nuna min
su dukka suna son abun amma ni na sani ba dan
Allah su ke sona ba, shi kansa Uncle Hamza na
kula bai fahimce su ba.
Manufarsu ta aure ni ta kwashe dukiyata dan
suna cewa a jikin mahaifinsu na samu, in ya so
bayan sun kwashe sai a rabu koma su kashe ni
magana ta wuce.
Na gama sauraron dadin bakinsu sai nima na
shirya musu nawa sharuddan da gangan dan na
san ba za su iya bi ba. Abunda na fada musu
kuwa shine duk matar da zan aura sai ta kasance
cikakkiyar musulma mai shiga irin ta musulunci,
sannan dole ta tsaya a matsayinta na mace bata
da cikakkiyar *yancin da zata dinga fita tana
yawo gari-gari ko kasa-kasa tana yin abunda ta
ga dama.
Sannan ina da damar zabar mata kasar da zata
zauna, kasar nan da zan zaba dole ta kasance
kuwa kasar Musulunci ce kamar Nigeria ko
Indonesia ko Malaysia na cire Ingila ma a ciki.
Daga nan taro ya watse muka tashi baram-
baram ta ce ta fasa ba zata iya ba, daman na
san ba zata iya ba yarinyar da take yawo da dan
siket ko dan wando
iya cinya tana shaye-shaye ina zata iya kulle da
saka hijabi.
Daman ita da uwarta suka kintsa maganarsu
suka sami Uncle Hamza suka kintsa masa da
kanta ta koma ta ce ta fasa, ya same ni ya sanar
min har da bani hakuri kada in ga ya yi magana
ya canja. Na ce masa ba komai.
Umaimah ta gyara zama daga dukkan alamu ta
fara jin dadin sauraron labarinsa.
Ya ci gaba da cewa "Dana gama da wannan
matsalar sai na wuce Cairo daman ina da lambar
wayar wasu daga cikin *yan uwan Faduwa maza,
na sami daya daga cikin kannenta da suka hada
kakanni daya mai suna Habib. Ya zo har Hotel
din dana sauka muka zauna daman tun a waya
na shaida masa ni aminin Faduwa ne daga
Malaysia
tare muke karatu a can. Na fara da tambayarsa
labarin Sagir tsohon saurayinta, ya bani labarinsa
kakaf da halin da yake ciki. Ya ce min bayan ya
rabu da Faduwa sai ya shiga wani hali na
damuwa har ya fara shaye-shaye har sai da aka
dakatar da shi a wajen aiki, da kyar mahaifiyarsa
ta lallashe shi ya auri wata *yar uwarta amma
zaman bai yiwu ba suka rabu ya sake auren wata
suka rabu.
Na ce ko zai bani lambarsa?
Habib ya ce ba shi da lambarsa sai dai ya san
gidansa kuma yasan ofishinsa. Sai na ce ya kai ni
wajen aikin na sa, da farko da aka yi
min iso cikin ofishinsa da ya ji an ce daga
Malaysia kuma abokin Faduwa ne sai ya fara
harara ta yana tunanin mijinta ne amma dana yi
masa bayanin abunda yake tafe da ni sai ya yi
kamar zai kwanta min saboda rawar jiki da
girmamawa.
Abunda na ce masa shine Faduwa ta bani
labarinka kakaf amma bata taba zaton ma zan zo
Cairo ba balle in neme shi ba, ni naga ya dace in
zo in gan shi mu gaisa. Ya nuna min yana cikin
damuwa da tashin hankali a rayuwarsa tunda ya
rabu da Faduwa haka yake, yanzu nemanta yake
kamar ruwa a jallo
mahaifiyarsa ma ta yarje masa ya neme ta ya
aure ta, ta yafe masa. Ni na masa alkawari zan
hada shi
da Faduwa na shirya masa lokacin daya kamata
ya je ya sameta a Malaysia. Na san za kiyi
mamaki idan na ce tare da shi muka je Malaysia
ranar Graduation dinta na hango ku a tsaye a
bakin Hotel din, sanda Sagir ya je ya durkusa a
gabanku. Ina labe a lungu ina gano ku ban fito ba
dan kada ku ganni kuma na fadawa Sagir kada ya
bari ku sani. Na ji dadi da Faduwa ta yarda aka
yi aure duk muna waya da Sagir har sai bayan
data haihu naje Cairo kwatsam Faduwa ta ganni
a gidanta. Na ji dadi da aka
sakawa yarinyar sunan ki kuma nayi mata godiya
na basu abun arziki bana kadan ba saboda
albarkacin sunanki.
Sai a lokacin Sagir ya fayyace mata komai ta sha
dariya da mamaki. Faduwa ta sanar da ni duk
abubuwan da suka faru bayan
tafiyata, cewar kina sona har ki ka kasa sauraron
Abdul-Basi. Na ce kada ta fada miki komai har
sai
na gama bincikena, a wajenta na sami lambar
wayar ki ta Nigeria.
Umaimah ta tsura masa ido tana kallonsa tana
sauraron hirarsa tamkar almara dan ita bata taba
ganin mutum mai daukar matsalar wani ta zamo
tasa ba irinsa.
Ya ci gaba da cewa "A lokacin da na gama da
Sagir,
Abdul-Basi ma muna waya da shi saboda ina da
lambar wayarsa na tambaye shi ra'ayinsa akan
ki, ya shaida min bashi da mata yanzu kuma ya
kasa kara auren kowacce sai ke yake so.
Amma na fuskanci yana da girman kai yawanci
duk hanyoyin dana fada masa ya bi yaki bi.
Misali na fada masa ya tura miki sako na bada
hakuri gami da daddadan kalamai yadda zaki
huce amma ya ki, ya ce min idan kin dawo zaku
hadu yasan idan yayi magana da su Baffa zasu
tilasta miki ki koma gidansa.
Da nazo Nigeria muka hadu a Kaduna mun zauna
na nuna masa mace bata son ji da kai dole su
mata a bi su da tattausan lafazi da kyautatawa,
har a lokacin na bashi labarin zaman da muka yi
da ke da yadda na yi ta bin kanki har ki ka yarda
ki ka saba damu.
Daga karshe na fayyace masa gaskiya na ce ina
sonki kina sona amma na buya bana so ki san
ma ina sonki dan na fi so ya aure ki ko dan
saboda *ya*yanku. Sai a lokacin ya amince zai je
graduation dinku idan kun hadu acan zaku
daidaita.
Bayan ya tafi nima naje Malaysia na labe na ga
duk yadda ku ke yiwa juna babu maganar
daidaituwa dan haka saina fito fili na bayyana
kika ganni bayan na shaidawa dangina gaba daya
labarinki cewar ke zan aura.
Ni da Sabitu mun boye miki maganar kai kudin
aure da aka yi saboda muna so mu baki mamaki
ki ji kwatsam! Ta sama
dan ki gigice dan dadi to mu shigo da farin ciki
Matawata ta batawa kowa rai na je na sami
Dagaci
na ce a shiga tsakaninku ina fitowa zan tafi kuma
Abdul-Basi ya tare ni yana nemana da bala'i. To
kin ji abubuwan da suke faruwa Umaimah bana
boye miki komai.
Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta yi murmushi gami
da yin fari da ido ta ce "Tabbas nayi mamaki
sannan
na yi farin ciki a lokacin dana ji yadda maganar
ta ke. Amma fa kayi kasada, to da ace a rashinka
na hakura na yarda na amsawa Abdul-Basi yaya
zaka yi alhali na ji a baya kayi magana kan cewa
tsananin so kake yiwa Umaimah.
Su dukka suka kwashe da dariya ya jinjina kai.
Ya ce "Allah ne kadai Ya san yadda zai yi da ni
amma tabbas na san zan shiga damuwa amma
na yarda da kaddara me dadi da marar dadi.
Gashi na girma idan ban yi aure yanzu ba ban
san sanda zan yi ba kuma nasan halina game da
soyayya ba na iya samun wacce zan ji ina sonta
daman daga kan
ki na fara jin son da yanzu na rasa ki kwanciya
zan yi in ce su Khausar su yi min auren dole
kawai tunda sun dame ni da maganar aure.
Suka kyalkyale da dariya su dukka.
Umaimah ta ce "Allah Ya rufa mana asiri, Ya
zaba mana abunda ya fi alkhairi.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce "Allah ma Ya
zaba mana addu'ar da zamu yi nan gaba ita ce
Allah Ya bamu zaman lafiya da *ya*ya masu
tarin yawa da albarka..
Sai Umaimah ta ji ta tamkar a mafarki yau Allah
Ya cika mata burinta a rayuwa ta sami wanda
take so zata aura daga dukkan alamu mijinta ya
fi na kowacce mace a duniya haka take ji a
zuciyarta.
Abdul-Sabur ya ci gaba da cewa "Zan koma Kano
yau, jibi zan tafi Ingila sai in turowa Khausar
kayan lefenki Abuja zai in wuce Ghana in sanarwa
da dangina cewar zan yi aure sai kuma in dauko
Ummana Fuse mu taho Gwarzo sai a hada da su
Khausar da sauran mata, nan da sati biyu a kawo
lefe. Sai mu hadu dake da Sabitu a Gombe a
ranar amma ku je da shirin yin kwanaki uku
yadda zaki ji dadin rabon katin biki dan zan taho
miki da su.
Umaimah ta rike baki dan mamaki ta ce "Abun ya
zo ashe, yaya na ga kamar kana gaggawa?
Amma daurin aure kadai za'yi ko ban da tariya?
Abdul-Sabur ya ce "Daurin aure da biki dukka
meye kuma tariya?
Ta yi dariya ta ce "Haba dai ai ni ban shirya ba.
Ya harare ta ya ce, "Wanne shiri kike tunani za
kiyi alhali gani a raye, ai idan ina nan ko ba ni za
ki aura ba kin san kin daina wahala ko tunanin
yadda za kiyi. Na san bai wuce kiyi maganar
gado da katifa ba wanda bana bukatar wannan.
Na zaci ma zaki tambaye ni a inda zamu zauna
tun da ni Allah Ya halicce ni rayuwata a kasashe
daban-daban.
Umaimah ta yi murmushi ta ce "Tambayar nan
tana raina sai dai na daure na danne ta dan kada
kaga gaggawata. To a ina zamu zauna?
Abdul-Sabur yayi murmushi ya ce "A ina kike so
mu zauna?
Ta sa gyale ta rufe fuskarta alamar jin dadi da
kuma kunya. Ta ce "Wallahi ban sani ba na baka
zabi.
Ya ce "To shikenan tunda kin bani zabi zan zaba
mana, na fi son mu zauna a Nigeria a garin
Abuja,
ina da gida a Gwarumfa sama da kasa ga
bangare daban in da nake so in saka Ummana
Fuse ku zauna tare amma kowa da bangarensa
ga Khausar ma a Abuja baku da nisa. Idan Sallah
ko biki ya taso a dangina sai mu zo Gwarzo ko
Kano mu bude gidanmu mu shiga duk ina da
gidaje. Sai mu dinga zuwa Ghana da Ingila ziyara
lokaci-lokaci, babu abinda zai ragu a
kasuwancina ina da yara masu kular min daman
ba ni nake zama ba, sai dai idan kaya sun kare ni
nake tafiya Indonesia, China, America in auno. Kin
ga sai in bude ofishina a Abuja in baki matsayin
Manajata sai mu fara turo kaya zuwa Nigeria, a
bude babban shago na san zai karbu, Sabitu ma
sai a samar masa abunyi ya yi aurensa.
Hawayen dadi ya rufowa Umaimah ta sharce
hawaye ta ce "Abdul-Sabur ina jin dadin
maganarka tamkar a mafarki ban san kalmar da
zan yi maka godiya ba idan kayi min wata
kyautar,
lallai Allah Ya amsamin addu'ata ya hada ni da
miji na gari. Na so in tura Sabitu makaranta ya
samo ilimin zamani dan na san ko kasuwanci zai
yi sai da ilimin saboda lissafi shi kuwa bai iya ba
a boko.
Abdul-Sabur ya ce "Wannan ai mai sauki ne mun
yi magana da shi ya nuna min cewar yana so ya
je Madina ya karo ilimin kur'ani amma kafin ya
tafi za'a iya samo masa malamin da zai koya
masa
karatu da rubutu na boko a shekara daya ko biyu
zai iya koya idan ya so sai ya tafi jami'ar Makka
ko Madina ya yi digiri dinsa. Ko yaya kika gani?
Umaimah ta gyada kai ta ce "Haka ya yi daidai
ranka ya dade, sai dai in sake neman wata
alfarmar dan Allah.
Abdul-Sabur ya gyada kai ya ce "Fadi duk abinda
kike so Umaimah kina tare da mijinki, a shirye
nake na zama bawa a gare ki.
Ta ce "Ina matukar jin tausayin Ilah, ci gaba da
zamansa a kusa da Matawata ba karamin ciwon
zuciya zai jawo masa ba, ga talauci da yara. Ka
taimaka ka hada shi da Sabitu dukka abunda ka
yiwa Sabitu ka yi masa dan shima tare suka je
yawon almajiranci.
Mu yi masa aure idan ya tashi yi a hada su da
matansu su tafi Madina suyi karatu bayan sun yi
yaki da jahilci sun koyi karatun boko.
Abdul-Sabur ya ce "Kin yi dai dai haka ya nuna
min kina bada hakkin MAKWABTAKA. Na ji
ra'ayinki akan su Sabitu, Baffa da matansa fa,
yaya za'ayi da su?
Ko kina so su ci gaba da dawwama a Ruga har
karshen rayuwarsu?
Umaimah ta girgiza kai ta ce "Abun sai yayi
maka yawa, Baffa yana nan a inda yake bana jin
zai yarda ya baro Rugar nan daya saba. Sai dai
mu dinga kawo masa duk wani taimako yana
daga nan.
Abdul-Sabur ya ce a'a dole Baffa ya dawo birni
ya zauna idan ma ba zai yi nisa ba ya tsaya a
cikin garin Gombe. Babu yadda za'ayi muna birni
muna shan wutar lantarki, ga Ac, ga wayar
sadarwa, su suna cikin duhu. Dole a hankali in
gina gidaje a jere har guda hudu masu dauke da
dakuna uku, daya Baffa da matansa, daya Sabitu
da matarsa daya Ilah da matarsa idan yayi wani
auren amma ba Matawata ba, daya kuma
Umaimah da Abdul-Sabur idan sun zo su dinga
sauka a ciki.
HMM___ wayyo ni Matawata ta, kowa ya tsaneta
haka kawai, mace kyakkyawa da ita. Amma ba
komai zan turata Malaysia ita ma, ko ya kuka ce?
Kuna tare da ni a ko yaushe.
A.A Hada Hada
MAKWABTAKA 52
daya kuma Umaimah da Abdul-Sabur idan sun zo
su dinga sauka a ciki.
Umaimah ta rushe da kukan dadi ta ce "Na ji
dadi da Allah Ya halicce ni Ya raya ni, Ya kaini
Malaysia na hadu da kai, babu abinda zance
maka sai Allah Ya biya ka Ya jikan mahaifanka.
Abdul-Sabur ya ce "Amin na gode. Amma kin san
halina tun ada bana son in yi kyauta a yi ta
godiya balle har a barke min da kuka bana jin
dafin haka.
Ki dauka duk abinda nayi miki aikinane daman,
kuma dole in yi. Kamar yadda dole in rike iyayena
dole in rike su Baffa, haka kamar yadda ya zama
dole in kula da kaina ya zama dole in kula da ke
da duk wani naki.
Mu yi fatan Allah Ya raya mu Ya bamu tsawon
kwana masu amfani.
Umaimah ta goge hawaye ta ce "Amin.
Ya ce "Yauwa, ko ke fa, goge hawayenki ki daina
kuka. Yanzu zan tafi ki taya ni da addu'a in je
lafiya in dawo lafiya in same ku lafiya. Sai nan da
sati biyun in mun hadu a Gombe, ki sanarwa
Baffa *yan uwana mata za su zo kawo lefe nan
da sati biyu.
Umaimah ta ce "Zan fada masa daga na shiga
gida yanzu, Allah Ya kawo su lafiya. Ina yi maka
fatan ka
je lafiya ka dawo lafiya.
Ta bude kofar mota ta fita ba tare da zuciyoyinsu
suna so ba, basa so su rabu da junansu sai dole.
Ji yake tamkar ya hadiye ta dan so da kauna
haka itama take ji a ranta tamkar su dauwama
suna tare suna hira.
Ya tafi yana daga mata hannu tana daga masa
itama har ya bace. Ta shiga gida da sauri ta iske
Baffa da Sabitu a dakin Baffa sai ta daka tsalle ta
shiga tsakiyarsu ta zauna tana ta dariya da
shesshekar jin dadi ta rasa daga inda zata fara
zano musu irin wadan nan abubuwan alkhairi, sun
kagu su ji sun tattara hankulansu gaba daya gare
ta suna ta jero mata tambayoyi.
Ta gyara zama ta fara zayyano musu abubuwan
alkahairi sanka-sanka daga Abdul-Sabur zuwa
gare su sai Sabitu ya sulale ya kwanta
wai shi dadi ne ya sumar da shi, yayin da Baffa
yake faman daga hannu sama yana ta hamdala
ga
mahaliccinsa.
Umaimah ta sami sukuni a zamanta na Dugge,
Matawata ta tsorata bata kara jiyo habaicinta ba
balle zagi, haka su Nene da mutanen gari kowa
girmanta yake gani, tun kafin ta ce ayi abu ake yi
balle kuma ta ce ayi din.
***
_____
Tun bayan tafiyar Abdul-Sabur Umaimah bata
kwanta ba aka hau gyaran gida ana ta yi masa
kwaskwarima yadda *yan kawo lefe da *yan biki
zasu sami dan wajen zama mai kyau. Ta hada ku
san kudinta kakaf wajen sumulce bangon gidan
da tsakar gidan aka cire duk inda zana take aka
dora bulo din kasa aka sumulce da zumunti, aka
buga runfunan kwano yadda za'a zazzauna a
sami inuwa, bayan data katange bandaki da bulo
da simunti aka saka kyaure.
Tabarmi manya-manya masu yawa ta aika
Sabitu ya siyo mata a birni.
Sannan ta zauna ta rubuta yawan abinciccikan da
za'a shiryawa baki, ana gobe zasu zo *yan matan
garim irin su Aliya da take kama kafa da
Umaimah suka zo suka taya ta soye-soye, bata
bari su Nene sun saka mata hannu ba dan ta san
basu iya girkin zamani ba. Haka a ranar da za'a
kawo lefe ma
tunda asuba su Umaimah suka tashi aka dora
abinci kala-kala kamar Fried rice, cincin, miet pie,
kek, sakwara da dai sauransu. Aka siyo mata
kankara da kuloli aka saka lemuna iri-iri. Sai da
ta
shirya komai sannan ta yi wanka ta shirya
kayanta kala uku ita da Sabitu suka nufi Gombe
da misalin
karfe goma sha daya da rabi suka isa. Kai tsaye
ofishinsu da take bautar kasa ta fara zuwa, ta
saka hannu aka tabbatar mata an kara mata
hutun sati biyu Abdul-Sabur ya nemar mata
wannan alfarma.
Tana fitowa ta kira shi a waya ya tabbatar mata
a Gombe ya kwana amma su Khausar sun taho
sun
kusa karasowa Gombe da kayan lefe in