Showing 60001 words to 63000 words out of 130520 words
Chapter 21 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
faranti
dauke da katan kek da wukar yankawa ta zo ta
ajiye a gaban Abdul-Sabur. Ya yi murmushi ya
ce, ''Ke ni fa ba wani kek da zan yanka.
Faduwa ta yi dariya ta ce ''Sai ka yanka yanzu
kuwa.
Umaimah ta mike ta nufi kicin yayin da Abdul-
Sabur ya ce, ''Au kema kicin din zaki shigar musu
irin na Yayarki?
Umaimah ta yi dariya ta kada kai ta tafi ba tare
data ba shi amsa ba. Sai Faduwa ce ta amsa
masa ta ce
''Kada fa ka takurawa kanwata ka bar mu yau
mu wataya muna murna da zagayowar haihuwar
dan
uwanmu.
Ya ce ''Allah Ya huci zuciyarku ban hana ku
watayawa ba ai.
Faduwa ta ciro kyamarar daukar hoto ta ce, ''Bari
Umaimah ta zo sai mu fara daukar hoto, kuma ka
yanka kek dinka. Yayana me zai hana mu bi
yarinyar nan a hankali har ta saki jiki damu
sannan mu bayyana mata manufarmu?
Abdul-Sabur ya zabura ya dubi Faduwa a gigice
ya tamabaya, ''Wacce manufa muke da ita a
game da ita?
Ta yi dariya ta gyara zama sannan ta kanne ido
ta ce ''Ah maganar ka da ita mana, ni fa da
gaske nake na maka sha'awarta. Kai ka fi
cancanta ka auri yarinyar nan dan ina tausayawa
rayuwarta, ta sha wahala gata marainiya. Na
yarda dakai, zaka iya rike ta amana.
Sai ya sulale ya mimmike a zaune akan kujerar
da yake zaune, ya daga kai sama saboda tsabar
tashin hankali, dimuwa, mamaki da firgici. Ya ji
ko ya tsansa ba zai iya dagawa ba saboda
sanyin jiki.
Ya hau tambayr kansa da kansa.
Wai shin me yake faruwa da ni ne a yau? Yau me
yake shirin fado min cikin rayuwata ne haka? Me
yasa Umaimah ta yi min sha,awar in auri Faduwa
itama Faduwa ta yi min sha'awar ta yi min
sha'awar in auri Umaimah?
Shin mafarki nake yi ne ko idanuwana biyu? Anya
kuwa ba hade min kai suka yi ba suke shirin su
waina ni ba?
Kai haba ya ma za'ayi a ce sun hada baki,
yaushe suka san juna ma? Ya zanyi kuma
menene ya kamata in yi?
KARKSHEN LITTAFI NA 2..
_________(3)_____
Umaimah ta fito dauke da *yan gwangwanayen
fulawar roba a hannayenta ta zo ta jera akan
tebur,
yadda teburin zai sake kayatuwa. Faduwa ta
shiga tarwatun kiran jama'ar da suke zazzaune
suna cin
abinci, wai su zo su taya su yanka kek din
birhday.
Masu hali irin nata na rawar kai da son wasa
suka ta so yuya guda har da wasu daga cikin
ma'aikata,
ana tafi ana fadin. ''Happy birhday Abdul'' kamar
yadda suka ji Faduwa tana fada suma ita suke ta
fada.
Takaici ya hana Abdul-Sabur sakat ya ji dama
bai zo wajen nan ba, a dole aka kewaye shi ana
kirga daya har zuwa goma sannan ya yanka kek,
aka hau tafawa kamar wani yaro karami. Sai
Faduwa ta shiga daddatsa kek kowa yana caka
da colali yana ci. Hotuna iri-iri Faduwa ta dinga
yiwa Abdul-Sabur da Umaimah a kusa da shi,
babu abinda Umaimah take sai murmushi dan
tabbas ta shaki farin ciki a wannan fita. Bayan
nan sai Faduwa ta yiwa jama'a godiya game da
yi musu tayin su zauna su ci abinci tare da su,
da yake kusan kowa an riga an kawo masa nasa
abincin kan teburinsa sai suka ki zama suka
koma in da suka fito suka zauna suka ci gaba da
cin abincinsu.
Suma su Faduwa suka zauna suka fara cin jifgin
abincin da yake jere akan teburin gabansu, daga
gani abincin nan ya fi karfin hanjinsu saboda
yawa gashi kaloli daban-daban.
Duk wanda ya shigo kafin ya zauna sai Faduwa
ta kirashi tebur dinsu, ta yi masa ta yi in akwai
abinda ya ke so a ciki ya zauna ya ci ba sai ya
saya ba sun saya da yawa saboda bikin birhday
da suke yi.
Abinci kadan Abdul-Sabur ya ci sai ya daina ci
yana daga zaune ya dubi Faduwa, ya juya ya
dubi
Umaimah, sai ya yi sauri ya sunkuyar da kai,
yayin da kwalla ta cika masa ido yana tausayin
kansu su dukka ukun. Kasancewarsu gaba
dayansu marayu ne, kuma baki a kasar da babu
danginsu. Haka su
dukka ukun bagware ne, ba su da mai kula da su,
kowannensu shi kadai a cikin gidansa kamar
maye. Ya fi tausayin matan ma akan kansa,
rayuwar mace a gurgunce ta ke muddin ta kai
munzalin aure, kuma ba ta yi ba.
Sai zuciyarsa ta shiga saka masa hanyoyi daban-
daban da zai bi don magance wadannan
matsalolin
da suka addabe su.
Faduwa ta dubi Umaimah ita ma ta dubeta, gaba
daya suka tsurawa Abdul-Sabur idanu, tabbas
sun ga ya sauya yanayinsa, ya shiga halin tunani
a dai-dai lokacin da suke hayaniyarsu su kadai.
Babu
wacce ta tambaye shi me yasa saboda kowacce
ta san dalilinsa na yin haka, sai dai dalilin
kowacce daban, ya sha ban-bam da na dayar.
Faduwa tasan tayi masa maganar ya auri
Umaimah ta san maganar ce ta ke yi masa zillo a
zuciyarsa, ita ma Umaimah ta san maganar data
yi masa kan ya auri Faduwa ita ce ta toshe masa
a kahon zuci. Abin da ba su sani ba shi ne, farin
ciki maganarsu ta saka masa a rai, ko kuwa
damuwa, ya amince ko kuwa bai amince ba?
Shawarar da yayanke shine ya auri Faduwa
Umaima kuma ya aurawa Dan Aunty..lolx..
Ehemm. Ko ya kukagani en uwa.?
MAKWABTAKA 26
Kallon da suke yi masa shiyasa ya hanzarta
farfadowa daga duniyar tunani ya karkato
hankalinsa gare su, ya biye musu aka yi ta
hayaniya da ciye-ciye. Karfe tara na dare suka
baro 'KL plaza, kai tsaye suka wuce da motar
wajen ajiye motocin da yake cikin gidansu. Yayin
da suka firfito kowannensu
cikin fara'a suke yiwa juna sallama da fatan Allah
Ya tashe su lafiya.
Faduwa da Umaimah suka nufi bangarensu, yayin
da Abdul-Sabur ya nufi na sa bangaren. A cikin
lift Faduwa da Umaimah hirarsu kawai suke yi
cikin harshensu, wato Hausa. Wasa da dariya
gami da
dimbin nishadi ne ya tabbata a zukatansu.
Kaunar juna, gami da rashin jin dadin rabuwa
suke ji a cikin kalbinsu.
Faduwa ce ta ba Umaimah hannu suka gaisa
gami da rungume ta, ta sumbaci gefen kumatunta
irin gaisuwarsu ta Larabawa, a lokacin da aka zo
hawa na goma sha takwas wato gidanta. Lokacin
rabuwarsu ta zo kenan amma fa a yau. Kalmar
karshe da ta fadawa Umaimah ita ce 'Bissalam.
Ta fice daga cikin lift yayin da kofar lift ta rufe
kanta,
umaimah da sauran jama'a suka karayin sama, a
hawa na goma sha tara Umaimah ta fice ta nufi
gidanta fuskarta cike da annuri, har waka take
rerawa a hankali cikin harshenta na fulatanci.
Wakar nan da suke yi a dandali ita da kawarta
Matawata,
wacce suke kiran junansu kawata,
masoyiyata kuma makwabciyata.
Abun tambaya a nan shine Faduwa ce ta maye
gurbin Matawata, ko kuwa Abdul-Sabur ne?
Asuba ta gari Fadu-maimah-sabur!!!
Shigar kowannensu gida ba tare da bata lokaci ba
ya yi wanka da kuma sallar isha'i, bayan saka
rigunan baccinsu, sai suka haye gado yayin da
kowannensu ya shiga tunanin dan uwansa suna
masu tunano abubuwan da suka faru da su a
dazun nan. Haduwarsu ta zame musu tamkar a
mafarki, suna mamakin yadda haka ta kasance.
Matsananciyar shakuwa da kaunar juna nan da
nan ta wanzu a ransu. Bacci mai dadi ya kwashe
su a lokaci daya, saboda sun gaji ya hadu da
mafarkai kusan iri daya, abubuwan da suka faru
dazun suke
maimaita gani a mafarki.
Umaimah ta yi firgigit ta bude ido tana mai
murmushi a fuskarta sai ta ga ashe fa a mafarki
ne,
Abdul-Sabur ta yi mafarki yana yi mata magana.
Ya ce da ita, ''Umaimah kinga abin da nake fada
miki ko?
Annabi (S.A.W) ya yi gaskiya da ya ce, ''dukkan
musulmi dan uwan musulmi ne''
Ta yi firgigit ta tashi zaune ta dafe kirji gami da
jinjina kai tana mai gasgata wannan maganar da
ta ji a mafarki. Sai ta yi cimak ta sauko daga kan
gado ta je jikin tagar dakinta ta daga labule ta
leka gidan
Abdul-Sabur. A tsaye ta gan shi a jikin tagarsa
aka yi katari yana
kallonta, sai ta sake firgita ta saki labulen tagar
da sauri tana ambaton.
''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Anya wannan mutum ne?
Ta dade a tsaye a tsakar daki ta rike baki tana
mamaki, can ta suri filo ta fito falo kan doguwar
kujera ta zauna, bacci ya gagare ta, don haka ta
tashi ta shiga kicin ta tsaya, ta dade a tsaye
sannan ta tuna kishirwa ta ke ji, kasancewar an
ci maiko dazu. Ta bude firij ta dauko robar ruwa
ta tsiyaya a
kofi ta kurba. Sai ta jiyo magana a waje kan
baranda kamar muryar Abdul-Sabur. Cikin sanda
ta bude kofar da zata kai barandar waje, tana
budewa sai ga Abdul-Sabur muraran shi ma
atsaye akan barandarsa ta kicin yana mai
dubanta yana murmushi. Ya na magana amma a
waya cikin wani
yare wanda ba nata ba. Dan haka ba ta gane me
yake cewa ba, sai ta yi sauri ta tura kofar ta rufe
ta gaggauta kashe fitulun gidan gaba daya tana
mai tottofa addo'o'i a kowacce kusurwa ta cikin
gidan.
Ta shige daki ta haye kan gado can cikin lungu ta
kudundune a cikin bargo tana ta makyarkyata
saboda tsoron daya kamata. Tana tunanin anya
kuwa Abdul-Sabur mutum ne, ko kuwa aljani ne
yake shigarsa don ya tsorata ta?
Da kyar ta yi bacci bayan da ta daina jiyo
maganarsa da kuma motsin shige da fitar da
yake yi a cikin gidansa. Ko bayan da ta yi baccin
ma mafarkinsa ta ci gaba da yi har yanzu dai
nasihohin yake yi mata a mafarki,
wannan karon kuma babin mace ta yiwa mijinta
biyayya yake bayani.
TIkon Allah, wannan shi ake kira boyayyen
al'amari,
ko mene ne ma'anar hakan? Allah Shi Ya barwa
kanSa sani.
Asuba ta gari Fadumaimasabur.
***************
Dif Umaimah ta bace kwana biyar ma ba su sake
ganinta ba, haka ba sa jin motsinta a gidan, a
makaranta ta ke yini idan ta taso sai ta wuce
Bukit bing tang ta ci abinci a restaurant bayan ta
zazzagaya malls sannan ta dawo gida da daddare
ta kwanta, ko fitila ba ta kunnawa balle a san
tana ciki. Amma koda yaushe MAKWABTAnta
suna cikin ranta, kuma ba ta da mummunan zato
a kansu,
saboda ta saba da zaman kadaici, shi yasa ba ta
damu ta neme su ba.
Ranar juma'a bayan masallci tana cikin
tunaninsu,
sai kuwa ta ji bugun kofa gami da jiyo
muryoyinsu, babu tantama tasan su ne sai ta
rasa dalilin jin farin ciki a cikin zuciyarta. Da sauri
ta bude musu kofa bayan ta zumbula dogon
hijab.
Yadda ta ke murna da ganinsu har sun fita
murna, saboda dariyar da ta ga suna bangalawa.
Ta yi musu iso zuwa cikin falonta suka shigo
suka zauna akan doguwar kujera su biyu a jere.
Ta zauna a kujerar da ta ke fuskantarsu cike da
ladabi ta duka ta gaishe su, sannan ta koma ta
gyara zama ta dube
su ta yi dariya, ta furta kalmar da gaba dayansu
suka dimauce, aka hau kallon-kallo.
Cewa ta yi, ''Kun ba ni sha'awa da na ganku a
tare, Allah Ya tabbatar da alkhairi, mafarkina ya
zamo gaskiya.
Musamman Faduwa ta fi Abdul-Sabur rashin
fahimtar abin da Umaimah ta ke nufi, ga rashin
wadatacciyar Hausa, ga rashin sanin ainihin kan
maganar, saboda ba ta san maganar da
Umaimah ta fadawa Abdul-Sabur ba a kanta. Ita
ma kuma yanzun nan ta sake furtawa Abdul-
Sabur sabuwar maganarsa da Umaimah shi ne
ma dalilin da yasa ta taso shi a gaba don su zo
su ganta duk da ita ma
tana tsoron furatawa Umaimah wannan batu.
Tana gudun kada ta ki amincewa kuma ta shiga
gudunsu, don tasan halinta. Duk da Abdul-Sabur
bai bata goyon baya ba akan aniyarta ta hada shi
da soyayya da Umaimah ba,
har ya kan yi fushin gan-gan idan tayi masa
maganar, amma ta san nokewa yake yana so
yana kaiwa kasuwa. Shi ma kuma ya kasa fada
mata abin da yake zuciyar Umaimah na yunkurin
hada aure da ta ke yi.
Faduwa ce ta takurawa Umaimah da tambayoyi
akan ta yi mata FASHIN-BAKI akan maganar da
ta yi dazun. Hausa cikin Hausa Umaimah ta sake
rikita mata kwakwalwa, sai Faduwa ta dawo
turanci dan
ta ji Hausar ta gagare ta, duk da haka Umaimah
ta goce ba ta bari ta fahimci abin da ta ke nufi
ba.
Abdul-Sabur ya gane, dariya kawai yake kyakyata
musu daga karshe dai ya kawar da hirar ya shigo
musu da wata hirar wacce ta shafi kowannensu,
wato hirar makaranta da shirin fara jarabawa.
Umaimah ta mike cikin nutsuwa ta ke tafiya ta
nufi kicin dinta, ba jimawa ta fito hannayenta
dauke da kwalin lemo da kuma kofuna guda uku,
ta kawo tsakiyar kujeru (center table) ta shiga
tsaiyaya
musu, ta durkusa ta mikawa kowannensu sannan
ta sake tashi ta shiga kicin.
Faduwa ta dubi Abdul-Sabur ta yi murmushi,
magana ta ke yi masa cikin rada.
Ta ce ''Ka ga abin da nake fada maka ko?
Yarinyar nan ta dace da rayuwarka, nutsattsiya
ce ga ladabi.
Sai ya harareta ta kawai ya sunkuyar da kai, sai
ta kyalkyale da dariya.
Umaimah ce ta fito dauke da farantin tangaran
da 'cake' da biskit a cikinsa ta kawo ta ajiye a
gabansu,
ta koma ta zauna suka ci gaba da hira da kallon
talabijin.
Faduwa ta kurbi lemo, ta gyara zama ta ce,
''Umaimah ba ruwanki da neman MAKWABTANki
ko za ki shekara ba ki gansu ba ko?
Umaimah ta yi sauri ta dubi Abdul-Sabur, yayin
da ya yi saurin kawar da kansa gefe tamkar bai
san abin da suke cewa ba. Kunyarsa ta ke ji
saboda nasihohin da ya dade yana yi mata akan
ta sauya wannan mugun halin na kin mutane. Ta
yi saurin sauya hira, amma sai Faduwa ta sake
jeho mata wata tambayar.
Ta ce, ''Ba kya neman mutane a waya ko ba ki
zo inda muke ba, sai mu dinga gaisawa a waya,
koda
yake ko lambobinmu ma ba ki karba ba.
Wannan karon ma Umaimah Abdul-Sabur ta sake
kallo, yayin da yaki yarda su hada idanu, ya ci
gaba da matsa remote yana sauya tasha a
talabijin.
Faduwa ta ce, ''Ba ni lambarki, ga tawa.
Ta dauko wayarta tana jiran Umaimah ta karanto
mata lambobin. Takaicin tonar asirin da Faduwa
ke kokarin yi mata ta toshe zuciyarta, ba ta so
aka yi
wannan hira agaban Abdul-Sabur ba, saboda
kada ya zaci ba ta sauya ra'ayinta ba har yanzu.
Cikin sanyin murya ta ke ba wa Faduwa amsa ''Ai
ba ni da waya.
Don firgita Faduwa har da dafe kirji, ta dauki
dogon salati kai ka ce mutuwa aka yi.
Ta ce ''Kamar ya ya baki da waya? Ta bata ne
ko ba ki taba yin waya ba daman can a
rayuwarki?
Umaimah ta yi dan murmushin karfin hali, ta ce
''Ban taba yin waya ba daman can a rayuwata.
Kallo daya Abdul-Sabur ya yi musu ya juyar da
kansa ya ci gaba da kallon talabijin.
Faduwa ta zungure shi, ta ce ''Aboki, ka ji ikon
Allah, wai Umaimah ba ta da waya, a rayuwarta
ma bata yi waya ba, ko ta zaci a ruga take har
yanzu?
Su dukka ukun suka kyalkyale da dariya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Matsalata da ke ke nan, kin
cika kwakwazo, meye abun mamaki don bata da
waya?
Kowa fa da ra'ayinsa.
Faduwa ta ce, ''Da mamaki mana yadda duniyar
nan ta ci gaba, almajirai a cikin kauye ma rike
waya suke yi balle ita da ta ke birni. Birnin ma
irin Malaysia, a Malaysia ma a babban birnin
Kaula
Lumfur, kuma a jami'a. Haba Umaimah me yasa
haka, ya ya kike da *yan gidanku, samarinki, da
kawayenki?
Abdul-Sabur ya tsurawa Umaimah ido yana jira
ya ji amsar da zata bayar, sai ta ki magama ta
sunkuyar da kanta kasa, murmushi kadai ta ke yi.
Faduwa dai ba ta daina mamaki ba, haka ba ta
daina yi mata tsiya ba, har sai da Abdul-Sabur ya
mike tsaye ya ce zai tafi masallaci, ya ji ana
kiran sallar la'asar.
Faduwa ta tashi ta bi shi suka fice.
Umaimah ta raka su har kofar bakin lift suka
yiwa juna godiya, sallama, gami da fatan alkhairi
suka
shige lift suka tafi, ita kuma ta p dawo gida tana
maijin sanyi a ranta, kasancewar a halin yanzu
tana samun baki a gidanta, ta sami wadanda
suka san da ita suka damu da lafiyarta, wadanda
zata yi hira da su har su saka ta dariya.
Bayan kwanaki biyu da zuwan su Faduwa
gidanta,
ranar lahadi da yamma Umaimah ta shirya ta
rufo gidanta ta shiga gidan Faduwa don ta gaishe
ta. Faduwa ta yi matukar mamaki gami da farin
cikin ganinta. Ta mike da sauri ta rungume
Umaimah ta kamo hannunta ta zaunar da ita
akan kujera. Sai a
lokacin Umaimah ta dubi mata biyu da suke
zaune a kan sauran kujerun. Ashe baki gare ta,
daya
inyamura, daya *yar Malaysia. Uhum! Faduwa
mai mutane, kawayenta kala-kala daga kowacce
kusurwa ta duniya tana da kawaye mata da
maza.
Umaimah ta daga musu hannu ta gaishe su,
gaisuwar dai ta hello da hi ce, don ba ta ga
alamar musulunci a tattare da su balle ta yi musu
sallama. Suka amsa mata cikin fara'a su ma
yayin da Faduwa ta gabatarwa kawayenta
Umaimah, sannan ta gabatar da su ga Umaimah.
Sun jima suna hira
bayan sun ci, sun sha, Umaimah ta yi musu
sallama kasancewar magruba ta kusa. Su ma
lambar wayar Umaimah suke tambaya. Faduwa
ta yi sauri ta ce, ''Ina da ita, zan baku anjima.
Saboda ta ga Umaimah ta rasa amsar da zata ba
su.
Bayan tafiyar Umaimah sun dade suna yiwa
Faduwa zancenta cewar, tana da kirki ga hankali.
Sannan ta ba su sha'awa yarinya kyakkyawar
gaske kamar ba *yar Africa ba.
Faduwa ta yi musu alkawarin zata kawo musu
Umaimah har gidajensu
wata rana.
Misalin karfe goma na safiyar wata litinin
Umaimah ta bude barandar kiicin dinta don
shanya hankicin da ta gama goge-gogen gidanta.
A tsaye ta iske Abdul-Sabur shi ma akan
barandarsa yana shan iska, sun kwana biyu ba su
hadu ba ko akan hanya. Ta dan razana da
ganinsa, ta yi kamar zata koma ciki, sai ta daure,
ta dake, kasancewar ta daure kanta da dankwali
duk da riga da wandon
bacci ne a jikinta, amma dogaye ne ba kanana
ba. Suna hada ido sai suka yiwa juna murmushi,
ta duka ta gaishe shi.
''Umaimah daman kina nan?
Kwana biyu kin buya.
Abdul ya tambaye ta.
Cikin kadabi ta ba shi amsa. ''Ina nan, lafiya
kalau.
Ta ci gaba da shanya, ya gyara tsayuwa ya ce,
''Ba a ganinki sosai, ko makaranta ce? Koda yake
masu
ganinki suna ganinki, Faduwa ta ce kusan kullum
sai kun hadu, idan ba ta je gidanki ba, ke kina
zuwa. Har ma kun je unguwa jiya tare.
Umaimah ta yi murmushi, ta gyada kai ta ce,
''Haka ne. Ya gyada kai, ya ce ''Yana da kyau,
kuma na ji dadi
da samun wannan canjin. Ki ci gaba da yin
hakan,
saboda zaman kadaici ba dadi.
Ta yi dariya ta ce, ''Insha Allah zan ci gaba da
yin haka.
Ya ce, ''To na gode idan ba zaki damu ba da
yamma mu hadu a gidan Faduwa ina son magana
da ke.
Sai ta ji zuciyarta ta harba nan da nan ta ji
hankalinta ya tashi, ta shiga mamakin dalilin
neman ta da yake yi.
Mamaki cike a fuskarta a bayyane ta dube shi
cikin sanyayyiyar murya ta tambaye shi, ''Lafiya?
Ya yi murmushi ya gyada kai, ya ce, ''Kar ki
damu, ba wata matsala ba ce face alkhairi.
Ta gyada kai a sanyaye ta ce, ''Allah Ya kaimu
yammar.
Ta juta ta shiga gida.
Ta dade a zaune akan kujera tana sake-sake a
zuciyarta tana ayyano mata abubuwa daban-
daban da ya sa yake nemanta anjima a gidan
Faduwa. Ko dai maganar nan da ta yi masa za'a
tayar, wacce ta yi masa na ya auri Faduwa, yake
so
ta maimata a gaban Faduwa? Idan dai haka ne ai
ta kwana gidan sauki, sai ta maimaita ba wani
abu ba ne, alkhairi ta ke so ta hada.
Daga karshe ta mike cimak ta je ta yi wanka, ta
shirya ta fito zuwa makaranta tana da darasi da
karfe goma sha biyu. Dai-dai get din gidansu ta
ci karo da Abdul-Sabur da Faduwa a cikin
tsaleliyar
motarsa za su fita da alama makaranta za su
tafi. Sai da suka rage gilashin motar ta hango su,
sannan ta gane su ne, suka yi mata izini ta shigo
su tafi. Zata yi gardama Abdul ya ce ta shigo su
tafi