Showing 123001 words to 126000 words out of 130520 words

Chapter 42 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8018

ya so sai
Sabitu ya raka su Dugge su kai.
Ya ce su jira shi a bakin banki zai fito daga Hotel
din daya sauka ya zo ya same su. Bai dade ba ya
bayyana a gabansu wannan karon ba a irin motar
da ya zo da ita ada ba ce, wannan ta fi kyau da
tsada.
Umaimah a gidan gaba Sabitu a zaune a baya,
bayan sun gaisa sai ya shaida mata zai kai ta
gidan su Aisha Bingyal ta zauna sai Aisha ta
rarraka ta su fara rabon kati. Ya zaro wasu
lafiyayyun Katina kala-kala ya mika mata masu
yawan gaske. Ta yi caraf ta karba ta fara
karantawa ta ji idanuwanta sun dauki karkarwa
saboda tsabar gani take kamar almara.
Wasu na daurin aure ne, wasu na yini, wasu
kuma na Dinner party ne da za'ayi a hadadden
Hotel din nan na Emerald Royal Hild. Yin ranar
juma'a a Dugge, daurin aure ranar asabar a gidan
Dagacin Dugge, daga nan sai a dunguma a taho
Gombe dan yin dinner duk a ranar din. Lahadi
kuma kai amarya kuma daga Gombe zuwa Abuja.
Allah Ya ba su ikon halarta, a iso lafiya amin.
Sabitu ba'a iya karatu ba sai dai ya karba ya
jujjuya katinan sai da Umaimah ta karanto masa,
sannan ya hau murna. Su dukka ukun murna
suke suna kyakyata dariya har suka isa kofar
gidan su Aisha,
sun kuwa ci sa'a suka ci karo da ita tana
dawowa itama daga wajen aiki zata shiga da
motarta cikin
gidan data ga su Umaimah bakin get sai ta fasa
shiga ta fito daga motarta ta iske su a cikin
motarsu,
suka gaisa.
Abdul-Sabur ya shaida mata ya kawo mata
matarsa ta rike masa ita zuwa kwana biyu, kada
ta bari ko kuda ya taba ta.
Aisha ta yi dariya ta ce "Ba matsala ranka ya
dade na rike amana.
Suka yi sallama su Abdul-Sabur suka tafi yayin
da Umaimah da kawarta suka shiga cikin gida.
Bayan sun shiga bangaren Mama Umaimah ta
gaisheta sai suka wuce bangaren Aisha anan aka
baje labari da katunan biki, Aisha ta sha mamaki
a lokacin da Umaimah ta fito da katunan biki ta
nuna mata sai ta za ci gezau idanuwanta suke yi
mata.
Ta taya Umaimah murna sosai, bayan da suka
huta su ka ci abinci suka yi sallar azahar sai su
ka bazama suka shiga gari suka fara rabon
katuna na biki.
Duk bayan *yan mintuna Abdul-Sabur sai ya kira
ya ji lafiyar sahibarsa Umaimah, tabbas
mafarkinta ya zama gaskiya abunda taga Sagir
yana yiwa Faduwa ya burge ta ita ma yau gashi
Allah Ya nuna mata ana yi mata irinsa.
Ya tabbatar mata da cewar baki sun iso har zai
kai su Hotel su ci abinci Sabitu ya hana ya ce an
yi musu dafe-dafe a can.
Abdul-Sabur ya tuhumi Umaimah da laifin akan
me yasa ta wahalar da kanta ta dafa musu
abinci, alhali so yayi su je a koshe suna mikawa
su juyo.
Umaimah ta ce kada ya zarge ta dan ta girmama
bakinta abunda ake yi kenan a ko'ina dan me
yasa su zasu ki yi. Ya yi godiya itama ta yi masa
suka kashe waya.
Babu abinda Aisha ke yi sai kallon Umaimah tana
sha'awar kyautar da Allah Ya yi mata tana fata
da buri itama ta sami miji kwatankwacin na
Umaimah.
Masha Allah Tabarakallah.
Sai ga Umaimah a gidan Lamijo kwatsam ta
gansu a falonta tabbas ta firgita a fili take a
bayyane sai da
kowa ya gane ta, sai jikinta ya dau rawa
musamman kafin ta ji dalilin zuwansu. Jikinta
sanyi kalau ta tare su tana yake daga gani bai kai
zuci ba.
Bayan data basu izini suka zauna sai suka gaisa
ba tare da bata lokaci ba Umaimah ta mika mata
katunan nan kowanne sai da ta bata daya. Na
daurin aure ta ce ta bawa Baban Hanif, Yini da
Dinner kuma nata ne. Sai Lamijo ta kasa dago
ido ta kalli Umaimah dan kunya.
Ta tambaya "Waye mijin, dan Malaysia ne ko
Abdul-Basi ne ya koma Abdul-Sabur?
Aisha ta yi caraf ta ce "Eh a Malaysia suka hadu
amma Bakanone sai dai mazaunin Ingila ne
amma a Abuja zata zauna, gashi saurayi babu
ruwanta da kishiyoyi.
Bakar magana Aisha ta fada mata, suka mike
suka ce zasu tafi sauri suke yi, har tana kokarin
cewa mai aikinta ta kawo musu lemo suka ce ta
bar shi. Ta rako su har bakin get ta yi arba da
tsaleliyar motar Aisha amma Umaimah ce take
tukawa a zaton ta ma ta Umaimah ce, har da
cewa Umaimah ta bata lambar wayarta dan idan
suka tashi zuwa Dugge biki su kira su ji,
Umaimah ta bata itama ta karbi ta ta.
Gidan mahaifiyar Lamijo suka wuce Umma, itama
dai haka ta kasa hada ido da Umaimah saboda
nauyi da kunyar wulakancin da suka yi mata a
baya.
Umma ta tambaya "Mijin dan ina ne?
Aisha ta bata irin amsar da ta bawa Lamijo dazu.
Suka fito daga gidan sai suka shiga gidan
Makwabciyar Umma wato Salma wacce ta yiwa
Umaimah kazafi, itama ta yi mamaki da ganin
Umaimah a gidanta, bayan sun
bata katin Dinner guda biyu ita da mijinta sai
suka juya zasu tafi.
Sai Umaimah ta ji Salma ta dafa
kafadarta tana juyowa sai taga hawaye yana
surnanowa daga idanuwan Salma.
Umaimah da Aisha suka kidime suna tambayarta
lafiya take kuka?
Sai ta sake fashewa da kuka.
Ta ce "Na zalunci kaina Umaimah da gangan na
yi miki kazafi, saboda kawai ina so ki daina
shigowa gidana na ga kin fini kyau da tsari ina
tsoron kada ki burge mijina ya ji yana sonki.
Gashi yanzu kin yi ilimi, kin yi kudi, kin sami mijin
da yafi nawa. Ki yi hakuri Umaimah ki yafe min.
Umaima ta yi murmushin karfin hali hawaye
zazzafa ya surnano mata, ta sa hannu ta goge
wa Salma hawayen fuskarta.
Ta ce "Ki daina kuka na yafe miki daman tuntuni
shiyasa kika ganni a gidanki ban kullace ki ba ko
kadan, Allah Ubangiji ya yafe mana.
Salma ta yi musu alkawarin za su je ita da
mijinta in Allah Ya yarda.
Suka ci gaba da rabon katuna har sai da dare
yayi sosai suka koma gida akan gobe zasu
karasa rabon. Suna shiga gida Abdul-Sabur ya
kira ya tambayi in da suke, ta ce sun dawo gida.
Ya tabbatar mata masu lefe sun kai sun dawo har
ya kai su masaukin su a Hotel din da yake ya
kama musu dakuna da yawa suna can sun
kwanta.
Ya ce yana so ta shirya gobe da safe su wuce ita
da Aisha su zo su gaisa suma dan suma su
ganta musamman Khausar. Umaimah ta ce "To,
babu matsala za mu zo goben in Allah Ya kaimu.
Ya ce "Su Khausar suna ta godiya sun ce an yi
musu dafe-dafe, kuma an karbe su hannu bibbiyu.
Umaimah taji dadi da jin haka dan haka sai ta
godewa Allah da suka fita kunya.
Washe gari su Umaimah suka tashi da wuri suka
shirya suka caba ado kai ka ce gidan biki zasu je,
su ka nufi Hotel din data fada musu, a hanya
Umaimah ta tsaya a wani kanti ta sayi alewowi
cikin
leda masu tsada ta tafi musu da shi. Suna isa
bakin get din Hotel ta kira shi a waya, ya sauko
ya shiga da su ciki.
*Yan uwan Abdul-Sabur sun sha mamaki da suka
ga zukekiyar amaryarsu Umaimah, dan basu zaci
zasu ganta hadaddiya kuma wayyiya haka ba.
Har da sun fara *yan gulmammaki suna cewa shi
kuwa Abdul-Sabur me yayi masa zafi ya shigo
Rugar nan neman aure ya tsallake duk matan
duniyar nan?
Duk da Khausar ta san Umaimah amma bata zaci
a Ruga take ba kuma sai ta ga Umaimah ta sake
yin kyau fiye da yadda ta ganta a Malaysia.
Ta gasgata lallai dole Yayanta ya makale ya nace
anan dan tana da kyau ga hankali.
Bayan su Umaimah sun gaisa da su suka dade
suna hira, abokan wasansa suka dinga yiwa
Umaimah
tsiya, ashe da gaske ne dangin mahaifiyarsa
Fulani ne kawai masu jin fillanci dan haka sai
suka sha
yarawa da Umaimah.
Da suka fito zasu tafi Umaimah ta basu alewowin
nan cikin leda ta ce su kaiwa yara, suna godiya
har suka shiga hadaddun motocin da suka zo
suka tafi,
Khausar ta karbi lambar Umaimah itama ta karbi
ta ta.
Umaimah da Aisha suka yiwa Abdul-Sabur
sallama suka ce zasu tafi su ci gaba da rabon
kati yayin da Abdul-Sabur da Sabitu suma suka
nausa gari yawo kamar yadda suka saba.
A yau dai Umaimah ta karade duk inda take so ta
kai kati kowa ta bashi daga cikin maza da matan
da suka yi karatu a Malaysia babu wanda basu je
gidansu ba. Kowa yayi alkawari zai je komai da
komai da za'ayi har da rakiyar amarya Abuja.
A ranar ne kuma da daddare Aisha da Sabitu
suka raka ango da amarya gidan daukar hoto,
hotuna masu yawan gaske aka yi musu kala-kala
aka wanke da yawa. Ya dibi wasu Umaimah ta
dauki wasu dan su rabawa masu bukatar da zasu
buga musu wani abu, duk da ba sai ya jira wani
ya buga masa memo da kalandu ba shi zaisa a
buga kuma masu inganci.
Bayan sun dawo gida ne Sabitu ya samu lungu ya
labe yadda Abdul-Sabur ba zai jiyo shi ba, ya kira
Umaimah a waya ya fara kyasa mata kayan da
aka zuba mata a lefe, kaya masu yawan gaske da
tsananin kyau da tsada. Akwatu na dukan
akwatuna har guda takwas, bayan manyan
gwalagwalai har seti uku.
Mamaki gami da farin ciki ya lullube ta, ta yiwa
Allah godiya ta yiwa Abdul-Sabur godiya.
Washe gari da safe Umaimah da kawarta Aisha
su ka shirya, Abdul-Sabur ma suka shiraya suka
kama
hanyar zuwa Dugge dan su ga kayan lefe kuma
Aisha ta taya ta zabar wadanda zata kai
dinkunan
fitar biki.
Masha Allah!
Su Umaimah sun sha mamaki da suka ga jifgin
kayan nan, kai kace kanti za'a bude, duk yadda
za'a baka labari ba zaka taba gane yadda lefen
yake ba har sai ka gani da idanuwanka. Gaba
daya garin Dugge da Rugagen da suke
MAKWABTAKA da su sai da labarin lefen
Umaimah ya karade, dan basu taba cin karo da
lefe makamancin wannan ba. Aka sha bata
labarin halin da Matawata ta shiga a lokacin da
ta ji labarin yadda lefen yake, aka ce sai data fadi
kasa dan bacin rai da tsananin bakin ciki.
Yaya ta iya da ikon Allah ai sai kallo. Allah ba Ya
son masu hassada da bakin ciki, Allah Ya hana
yin hassada. Allah Ya raba mu da aikata ta amin.
A ranar suka juyo Gombe bayan sun ciko akwati
guda da kayan da ta zaba zata diddinka. Bayan
kudin da suka sako akan lefe a matsayin kudin
dinki, Abdul-Sabur ya hana ta biya kudin gaba
daya shiya biya mata kudin dinkuna, dinkuna
kuwa masu tsada da kyau. Haka ya yiwa Aisha
yayyafin Naira ya ce itama ta yi dinkunan da zata
fito tayi kyau a matsayinta na babbar kawar
amaryarsa.
A Gombe ya bar Umaimah a gidan su Aisha,
Sabitu kuma a Hotel, amma a bisa sharadin
direban gidan su Aisha ne zai mayar da su Dugge
idan an gama dinkunan, dan bai yarda ta hau
motar haya ba.
Allah Sarki kauna!
Bayan jiran dinki ma har da jiran gyaran jiki ne
ya tsayar da Umaimah, mata masu yin dilka da
alewa ne su ka sha suntirin zuwa har gida suka
kalkale ta tatas kai kace fatar dan jarari ce. Har
da Aisha aka shirya tafiya Dugge a lokaci da biki
ya rage saura kwanaki takwas. Da ta yini a
Dugge sai ta koma Gombe a bisa sharadin zata
dawo idan biki ya rage saura kwanaki biyu, idan
ta zo ba zata koma gida ba har sai an kai
amarya Abuja.
Jama'ar gari suna ta kaffa-kaffa da Umaimah
kowa yana mata ladabi idan aka ga abunda bata
So da gudu ake kaucewa wanda take so ne ake yi
mata
tun kan ta ce balle kuma ta ce ayi, ai babu bata
lokaci ake yi. Labarin auren Umaimah ake ta yi a
kowacce kusurwa ka zo giftawa ba a Rugarsu
kadai ba har da rugagen da suka yi
MAKWABTAKA kowa ya kagu ya zo wajen bikin
nan ko da ba'a gayyace shi ba, dan ganewa
idanuwansa kuma su cika tumbinsu.
Washe gari Umaimah ta shiga rabon goro da
alewa dan su a nan babu ruwansu da kati, babu
gidan da bata shiga ta kai ba a garin ita da *yar
rakiyarta *yan mata har ma da matan aure burjik
ana ta take mata baya ana mata fadanci. Gida na
karshe data shiga shine gidan su Matawata, ba
Mawata kadai ba duk mai rai da yake gidan nan
babba da yaro sai da jikinsa ya yi sanyi da suka
ga Umaimah. Ta yi
musu sallama, sannan ta duka ta gaishe da
Mahaifan Matawata, ta basu daurin goro da
alewa har leda uku.
Ta ce daya na Matawata sauran biyun na uwar
da uban. Sai Matawata ta sunkuyar da kanta
kasa bata iya dagowa ta hada ido da ita ba.
Innar Matawata ta rushe da kuka ta nuna
Matawata da yatsa ta cewa Umaimah "Kin ga
yadda kawarki Matawata ta zama ko?
Saboda tashin hankali ta fita hayyacinta ta zama
tamkar tababbiya.
Tunda ta auri Ilah bata taba samun kwanciyar
hankali ba muma namu bai kwanta ba, na san
hakkinki ne yake biye da ita.
Umaimah idan baki yafe mata ba, a haka zata
dauwama.
Sai kuma rana ita yau xaku jini da ci gaban
shirin..
Marbass Dan Aunty.
MAKWABTAKA 53
Tunda ta auri Ilah bata taba samun kwanciyar
hankali ba muma namu bai kwanta ba, na san
hakkinki ne yake biye da ita.
Umaimah idan baki yafe mata ba, a haka zata
dauwama.
Umaimah ta dafa kafadar Inna ta ce "Ki daina
fadin haka Inna, ni fata na ma ace Ilah ya huce
su koma su rike *ya*yansu. Babu abinda ta yi
min, idan ma ta yi min na yafe mata ko ba komai
ni makwabciyar ta ce, ina kare hakkin
MAKWABTAKA. Ina girmama duk wani
makwabcina ina kare hakkinsa domin makwabci
yana da hakki akan makwabcinsa.
Matawata ta dago a hankali ta dubi Umaimah ta
mayar da kai kasa ta sunkuyar.
Umaimah da tawagarta suka fice yayin da kowa
ya dinga yaba hakuri da afuwa irin ta Umaimah.
Allah Ya kyauta!
Da daddare Umaimah tana zaune a kan abun
sallarta a dakinta tana jero addu'o'in godiya ga
Allah da Ya bata miji na gari, bayan ta idar da
sallar isha'i. Sai ta ji yara sun shigo suna cewa
ana sallama da Umaimah a kofar gida.
Sai abun ya bata matukar mamaki ta fito tsakar
gida a gigice ta na tambayarsu "Waye yake nema
na?
Suka ce "Ilah ne.
Ta dan yi kasake kamar ba zata je ba sai su
Nene suka dinga yi mata magiya suka ce ta je.
Ta fita a zaure ta hango shi a rabe a tsugune a
lungu, itama ta zo ta durkusa duk sun juyawa
juna baya. A haka suka gaisa sannan ta ci gaba
da sauraron abunda zai fada mata.
Ilah ya yi ajiyar zuciya ya ce "Umaimah, na zo ne
dan in yi miki murna in kuma yi miki fatan
alkhairi bisa wannan abun arziki daya same mu
gaba daya, dan abunda ya yi ki shi ya yi ni. Ina
jin ki tamkar *yar uwata ta jini ba zan manta da
ke ba har abada kuma ba zan sami kamar ki ba,
ni na san da haka. Ba wai ina dawo da maganar
data wuce a baya ba amma kaddara ce ta gifto
mana ta raba mu wanda komai rubutacce ne a
wajen Mahaliccinmu. Kin yi hakuri, kin jure da duk
abubuwan da aka dinga yi miki a kaina daga
karshe Allah Ya dinga saka miki da wadanda
suka fini alkhairi. Allah bai rubuto ki daga cikin
wahalallu
ba irinmu shiyasa ma ya raba ki da ni.
Daga karshe ina baki shawara da ki bi mijinki sau
da kafa wannan daman halinki ne biyayyar aure.
Allah Ya baku zaman lafiya.
Sai ya surnano da hawaye mai zafi.
Umaimah ta sharce hawaye itama ta ce "Ba
komai Hamma Ilah, nima ba zan daina ganin
girmanka ba haka ba zan yanke zumunci da ku
ba, ba zan iya daina maka kaunar nan ta *yan
uwantaka ba har abada.
Ina rokar ka da ka zama mai tausayi da
rangwame a bisa zamanka da Matawata. Allah
Ya
jarrabe ka da mace mai wuyar sha'ani idan akwai
rabon ci gaba da zama kada ka ki mayar da ita
zan ci gaba da taya ta addu'a Allah Ya shirye ta.
Ilah ya girgiza kai ya ce "Ki taya ni da addu'a
Allah Ya daidaita ni da Furera kawar Aliya ita
nake shirin
aure har magana ta yi nisa, gara Furera ita
yarinya ce karama zata fiye min alkhairi amma ba
zan iya ci
gaba da zama da Matawata ba. Tunda muka yi
aure bamu taba yin sati guda ba, ba tare da mun
bata ba, na gaji.
Umaimah ta yi masa addu'ar alkhairi shima yayi
mata suka yi sallama kowa ya juya ya tafi. Tana
shiga gida sai gashi ya aiko yaro dauke da wani
littafi karami, yaron ya mika mata. Ya ce "In ji
Ilah gudunmawarsa ce.
Sai ta karba cike da tausayi, da sauri ta bude ta
fara karantawa, ta ga addu'oi na zaman lafiya da
kara
soyayya tsakaninta da mijinta da kuma addu'oin
tsari daga makiya, ya zauna ya rubuta mata da
larabci. A tsakiyar littafin kuma kudi ne har Naira
dubu uku. Sai tausayinsa ya kamata ta san yafi
wata guda yana tara wadannan kudi. Ta kuduri
niyyar taimaka masa nan gaba fiye da tunaninsa.
Biki yana ta karatowa ya rage saura kwana uku
aka tashi Umaimah da sassafe tana bacci wai ta
zo ga sako daga Kano. Bata gama fuskantar ma
me ake nufi har sai data fito kofar gida, taga
katuwar mota a cike da kayan abinci da abun sha
har ma da katuwar Saniya da raguna biyu, ga
katon jannareto dan a kunna ayi biki a cikin
haske, ga katon firij
dan asha ruwa da lemo mai sanyi, ga babbar
rediyo mai safiku dan *yan biki suji sauti, manya-
manyan kwalaye har guda uku a cike da kalandu
da memo mai dauke da hotunan amarya da ango
dan arabawa mahalatta bikin duk daga Abdul-
Sabur.
Sai ta ji ta rasa kalma daya da zata furta ta
godiya sai ta koma cikin gida da sauri ta kira
Baffa da Sabitu suka fito cike da murna, aka hada
da kartan gari aka dinga sauke buhunhunan
abinci da za'a ci a biki, bayan nan sai ga
makudan kudi sun biyo baya su kuma na cefane
bayan Kwando-kwandon
kayan miya da aka hado. Tabbas wadata ce duk
ta kawo haka bayan so da kaunar da yake yi
mata,
*yan Dugge suna kallon harkar arziki wanda basu
taba ganin irin ta ba.
Bayan an bawa direbobin abinci sun ci sai aka ba
su tukuicin kudi mai yawa wanda babu wanda bai
yi dariya a cikinsu ba, suna godiya su Umaimah
suna godiya suka tafi. Ta rubuta doguwar wasika
ta basu su kaiwa Abdul-Sabur, kalamai masu
taushi da tausasa zuciya ta rubuta masa tana
nuna godiya a bisa hidimomin da yake yi mata.
***
BIKI! BIDIRI!! BIREDE!!!
Rana bata karta sai dai uwar *ya ta ji kunya,
saura kwana daya a fara biki sai ga garin Dugge
ya fara samun manyan baki ba daga kasar nan
ba ma har daga wata kasa. Aisha Bingyal da
Faduwa ne suka
iso tare ranar alhamis. Zo ka ga tsalle da murna
a wajen Umaimah, da gudu ta rugu ta dane
Faduwa,
ta dauki takwararta *yar jaririyar Faduwa wato
Umaimat.
Umaimah Sagir ta fara tambayar Faduwa ta ce
yana Kano tare da Abdul-Sabur sai gobe zasu
taho Gombe. *Yan Dugge kuwa sai aka bi layi ana
kallon Faduwa ana nuna ta suna fadin ga
balarabiya. Dan basu taba ganin irinta ba a garin.
Gidan su Umaimah ne guda daya tak mai hasken
lantarki a garin sai dai sun samwa makwabtansu
na hagu da dama hasken saboda sanin hakkin
MAKWABTAKA. Ku san dukka *yan mata da
samarin garin sun hallara a kofar gidan da
daddare, babu abinda yake tashi sai kidan
kalangu, samari suna ta shadi amarya tana yi
musu liki.
Faduwa kuwa ta sami abin kallo tana yi tana
mamakin yadda suke tikar junansu da sanda.
Fargaba daya Umaimah ta dinga yi yadda
Faduwa da *yarta zasu iya bacci a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login