Showing 27001 words to 30000 words out of 130520 words
Chapter 10 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
koma in ce Kakanmu
don shine auta a dakin su Ummana Fuse. Ya fi
shekara ashirin a England, ya auri baturiya ya
haifi yaransa Turawa
guda uku, Babban namijin ne zaiyi sa'ana sauran
kuma dukka mata, sai a lokacin ya fara kawo su
kasarsa.
Da Uncle Hamza ya zo gidan Ummana Fuse ya
ganmu sai ya tambaye ta mu su waye? Sai ta
zauna ta bashi tarihinmu kakaf.
Sai ya tausaya mana daman ya ji labarin rasuwar
Babanmu ta waya. Ya tambaya yanzu me muke
yi karatu ko aiki? Ummana Fuse ta fada masa
cewar ni ina tsare kanti, Khausar tana siyarwa
wata abinci a
kasuwa.
Ya tambaye ni nawa ake biyanmu, na koro masa
bayanin cewa babu abin da muke samu banda
abinci, sai ya girgiza kai. Ya ce, ''A'a wannan ba
sana'a ba ce, gara mu koma makaranta.
Kamar yadda na fada muku a baya ana nunawa
Hausawa, Musulmai kabilanci. Ba a bari suyi
karatu, idan sun kutsa sunyi karatun ma babu
aikin gwamnati.
Ya ce kafin ya tafi zai samo min makarantar
sakandire ta kudi na karasa karatuna, tunda har
na
kai aji na hudu a can, kuma ya fuskanci ina da
kokari, ina magana da Turanci sosai.
Ita kuma Khausar tunda ba ta yi nisa a karatu ba
zai samar mata makarantar koyon sana,a ta koyo
ta dinga yi. Sai Ummana Fuse ta ce a saka ta a
makarantar koyon rinin kamfala, amma babu
makarantar anan kusa sai a Abrkan ake yi. Sai
dai idan ta koma gidan kanwarta Umma Aisha da
ta ke unguwar Dukuma ya fi kusa da Abekan.
Shikenan sai aka tsayar da wannan shawara kafin
ya koma England sai da ya tabbatar na fara zuwa
makaranta, Khausar ta khaura gidan Ummna
Aisha da ke Dakuma da zama, tana zuwa Abekan
koyon kamfala.
Ya yi mana alkawarin zai dinga aiko mana da
kudin makaranta (school fees), da kudin motar
zuwa da dawowa har mu gama. Abu daya ne ba
mu ji dadi ba, shi ne da aka raba mu ni da
Khausar domin tunda muke a rayuwarmu ba mu
taba rabuwa ba.
Ta yi ta kuka kullum ana ba ta hakuri haka ni ma
idan na shiga bacci, sai na yi ta kuka ni kadai
don
tausayinta, bata da kowa sai ni na rage mata,
haka ni ma ita ta rage min. Koda yake muna
ganin kakarmu mai tausayinmu muna jin dadi, sai
kadan daga cikin dangi masu kula mu kamar su
Uncle Hamza da ya zo ya taimake mu. Duk
wanda ya taimaki wani Allah Zai taimake shi...''
Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Ya ya aka yi
kuma?
Abdul-Sabur ya yi dan murmushi, ya ce, ''Suna
kiran motar hayarsu Bus da suna Toro-toro,
kullum sai na hau toro-toro na tafi makaranta
idan an taso na hau na dawo gida. Na ga
bambanci tsakanin karatun Kano da na Accra, a
Kano na fi *yan ajinmu kokari, tunda na shiga
makaranta daga firamare har zuwa sakandire ni
ne monita dan kokarina,
amma a Accra ni nake zuwa na karshe a ajinmu
har ana tunanin a mayar da ni ajin baya. Allah Ya
taikama Malamin ajinmu ya ce a kyale ni ya ga
alamar ina da kwazo da saurin koyo, watakila
idan na dage na saba da *yan ajin zan yi kokari.
Turancin su daban da namu, domin su suna
kwaikwayon irin na turawa ne sosai ba kamar
anan Nigeria ba da kowa yake yin yadda ya ke
so.
Hausawa suna turanci kamar da Hausa suke
magana, Yarbawa suna yi kamar da Yarbanci,
haka Igbo da sauran kabilu (broken English).
Idan ka ji dan Ghana yana Turanci sai ka rantse a
Turai ya girma, saboda kowacce kalma suna furta
ta dai-dai da yadda Turawan suke furtawa.
Tabbas yadda Malamin ajinmu ya fada haka ne,
rashin sabo, fargaba da gane turancinsu ne ya sa
na zama koma-baya a ajinmu ba wai rashin
kokarin ba ne. Amma da shekara ta zagayo sai
warware
gaba daya na rikide, ni da *yan ajin ake damawa.
Da muka gama aji hudu muka wuce aji na biyar
nan ne na gagari maza, ba ma matan ajin ba. Mu
uku ne muke gumurzu akan karbar na daya. Idan
na tashi daga makaranta da yamma sai na tafi
'Zarbarma Land' sunan unguwar ke nan, akasarin
*yan unguwar Zabarmawa ne, ma'ana daga kasar
Niger suke. Suna sana'ar canjin kudi, wasu na
siyar
da albasa, leda da fina-finan Hausa ko pure
water.
Ko na je unguwar Zango nan kuma *yan Nigeria
ne, a nan ne za ku ga masu bara kutare, makafi
da guragu. Nan na ke samun abin yi irin su dako,
ko jiran shago ko tallata kaya a cikin kasuwa na
je na
zazzagaya na yi ciniki na kawo a sallame ni da
dan kudi kalilan na ci abinci, na rago sauran na
ba wa
kakata ko na boye na ci abinci a makaranta idan
an fito break....
Faduwa ta girgiza kai alamar tausayi, ta ce, Allah
Sarki, ina kanwarka Khausar, a wanne hali ta ke
ciki a can unguwa mai nisa Dukuma?''
Abdul-Sabur ya yi murmushin karfin hali ya ce,
''Tana can tunda ta je sai da ta shekara ba ta zo
unguwarmu ba, ni ne dai duk sanda na bushi iska
nake zuwa na ganta, haka kakarmu tana kokarin
zuwa. Idan ta samo kwancen atamfofi sai ta
zuba a
leda ta je ta kai mata.
Rayuwar Khausar abin tausayi ce a can, gida ne
da yake cike da *yan mata, *ya*ya da jikoki na
Ummana Aisha. Wasu *yan makaranta, wasu
babu karatun, wasu ustazai wasu kuwa *yan
iska. *Yan mata sunfi goma don haka sai
rigingimu da
tsegungumi, sun tsani Khausar, sharrace-sharrece
kala-kala idan an rasa wani abu ace ita ta dauka
ayi ta zaginta ana dungureta. Sai daga baya aga
abin ko a kama wacce ta sace a cikinsu Haka
kowacce ta ke ciyar da kanta, don haka dole
Khausar ta fita nema. Kudin motar zuwa da
dawowa Abekan ba ya da matsala Uncle Hamza
ya turowa Ummana Aisha tana ba ta, sai na siyen
abinci ne da na zirga-zirga don daga makarantar
wani lokaci suna hawa toro-toro su je wasu
unguwannin koyon aiki kamar unguwar Nima,
Guinea kwanakir ko Mamubi. Suna yini acan tun
daga safe har marece.
Ina iyakacin kokarina wajen kawo mata agaji da
*yan kudade, biredi ko fanke da zata dinga yaga
tana ci a duk lokacin da ta ji alamar yunwa zata
yi mata illa.
Rayuwa kenan, komai mai wucewa ne, dadi ko
wahala....
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ne, babu
abin da yake dauwamamme a duniya.
Ya ce, ''Khausa ta rame saboda kewa ta, ga
tsangwama da rashin wadataccen abinci. Sai na
bata shawara ta dinga zuwa kasuwa tana rini
ranar asabar da lahadi sai ta dan adana kudin da
ta samo ta dinga cin abinci a makaranta.
Da kai na na kai ta wata karamar kasuwa da ake
kira Malata, anfi siyar da gwanjo a kasuwar, anan
na samar mata aiki a shagon wata mata mai
suna Mrs. Ibrahim don bana so na kai ta shagon
maza saboda lalata.
Ghana ba kamar Nigeria ba ne, inda ADDINI da
AL'ADA suka saka kunyaa idon mutane, sukan
rike mace a bainal nasi ba komai ba ne. Don haka
zinace-zinace ya yi yawa, saboda arna sun fi
yawa.
Da farko Mrs. Ibrahim ta ki yarda ta dauke ta aiki
data ji an ce sai asabar da lahadi kadai zata
dinga
zuwa, ta fi son wacce zata dinga zuwa kullum.
Na dinga rokar ta har da durkusawa a kasa ina
zubar da hawaye ina cewa ta taimaka mana mu
marayu ne kuma baki ne a kasar dan bamu da
inda zamu je mu sami wani aikin in ba a wajenta
ba. Nan danan ta ji zuciyarta ta karaya sai ta
tausaya mana ta amince.
Sai na ji hankalina ya kwanta dan naga hankalin
Kausar ya kwanta, ta kuwa ci sa'a ta hadu da
uwar daki mai kyauta da tausayi. Tana bata lada
fiye da kudin aikin yadda ta dauke ta. Allahu
Akbar!
Rayuwa kenan Allah Yana bayan wanda Ya
dogara da Shi.
Shekara biyu ne daman ake yi a makarantar
koyar kamfala, Allah cikin ikonSa Khausar ta
kammala, aka bata satifiket dan haka Ummana
Fuse ta daukota, ta dawo da ita gidanta sai farin
ciki ya kama mu. A waya na shaidawa Uncle
Hamza cewar Khausar ta kammala makaranta
tana neman jari za ta dinga yin rinin a gida.
Ummana Fuse ta karbi waya ta sake yi masa
bayani ta roke shi daya sake jurewa ya ci gaba
da taimakon mu, dan mu marayu ne Allah zai
taimakesa shima.
Ya ce babu matsala, Khausar ta rubuta abubuwan
da take bukata da yawan kudaden dan ya turo
mata da kudin. Akwai wani bangare a gidanmu
tsohon waje ne, bangarensa na gado ya ce ya
bata aro ta dauka sai ta dinga yin rinin a ciki.
Daya turo mata da kudin sai muka dauko masana
suka tona mata ramukan, muka je kasuwa muka
hado duk abubuwan da ake bukata a wajen rinin.
Ni da Ummana Fuse sai muke dan taya ta duk da
bamu san yadda ake yi ba amma muna taya ta
da miko wannan, zubo wancan kamo wadancan.
Idan tayi rina ta buga kamfalu kamar turmi goma
ko ashirin sai ta kai kasuwa ta sararwa masu
shagunan da suke sayar da atamfofi, shaddoji da
kamfalu. Khausar ta zamo ita take bani kudin
abinci idan zan tafi makaranta a lokacin ina ajin
karshe ina shirin fita. Muka zamo ba'a sauke
tukunya a gidan Ummana Fuse abincin safe, rana
da na dare duk muna dafawa saboda cinikin
kamfalar da Khausar take samu.
Hankali a kwance nake ta karatu yadda ya
kamata dan haka na ci jarabawa sosai fiye da
tunanin mutane. Daga cikin darussa guda tara da
muke yi na ci A1 shida, B1 biyu C1, kuma
sciences na yi. Koda na fadawa Uncle Hamza
abunda na ci a jarabawa sai ya yi farin ciki ya
kuma yi min alkawari zai nemar min makaranta a
jami'a mai kyau a Ingila sai in karanci Medicine
ko Engineering.
Farin ciki ya lullubemu, Ummana Fuse ta ce nayi
shuru da bakina kada na fadawa *yan uba da
sauran *yan uwa masu hassada sai dai kawai
suji tafiya. Na ja bakina na yi shuru inajin *yan
hassada
kuwa suna ta surutai wai mu ne tsintacciyar
mage an ci jarabawa an rasa kudin shiga jami'a.
Da aka
fada maka Hamza zai iya biya maka kudin jami'a
ne? Wanan me shegiyar rowar? Ummana Fuse ta
ce in yi musu shuru kada in ce komai.
Allah cikin ikonSa shekara na zagayowa Uncle
Hamza ya yi waya ya ce in hada takarduna in kai
gidan abokinsa zai kai masa Ingila, ina rawar jiki
na hada na kaiwa abokin.
Bayan tafiyar abokinsa da watanni uku sai ya
turo min da komai na tafiya kamar tikiti da biza
aka tabbatar min na sami shiga jami'ar
Cambridge da take cikin Ingila.
Na yi sallama da kakata da kanwata ina kuka
suna kuka, makiya suka sha takaici a lokacin da
na zaga dangi ina mai musu sallama tafiya ta
tabbata. Na tafi Ingila karatu cikin kwanciyar
hankali, sai dai matsalolin da ba'a rasa ba daga
matarsa da *ya*yansa ba sa so na, saboda
tsabar ba su saba ganin bako a gidansu bakar
fata ba, da kuma yahudancin da yake cikin ransu.
Ko kudi ko kaya
zai ba ni, sai dai da dubara kuma a boye, saboda
matar sai ta hana shi baro-baro a gabana. Kun
san Nasara bai iya boye-boye ba da gulma, gar
da gar suke abubuwansu.
Ban damu ba saboda na saba da irin wadannan
tsangame-tsangwame a baya. Karatuna na saka
a gaba don shi zau fishshe ni. Da zaman ya
gagara ma sai na shawarci Uncle Hamza nace ina
so na koma zama a cikin makaranta a rukunin
gidajen dalibai da yake cikin makaranta. Ina so
mu zauna
gida daya da abokina Usman shima dan Accra ne.
Uncle Hamza ya yarda ya biyamin duk abin da na
bukata na kudin haya, kayan abinci da dai
sauransu.
Lokacin wayar hannu ba ta wadata ba sosai a
Accra, sai dai na kira wani gida a kusa da gidan
su Ummana Fuse na ce a kira su, bayan mintuna
ashirin sai na sake kira mu yi magana da su.
Kullum
suna cemin ba su da wata matsala kasancewar
aikin rinin kamfala ya karbi Khausar, an fara
saninta ana ta kawo mata aiki, suna samun na
cefane. Amma duk da haka idan na sami mai
tafiya ko kuma transfer ta banki sai na kundige
rabin kudin da Uncle Hamza ya ke ba ni na tura
musu,
don su sake jin dadin rayuwarsu. Kasancewar
akwai ayyukan yi a England da na gane gari, sai
na dinga fita ina yin ayyuka irin na awannin nan a
biya ni.
Kamar ba da abinci a hotel, goge-goge da share-
share a ofisoshi, duk ranar da ba ni da darasi.
Alhamdulillahi na samu kudi mai yawa a wannan
harkar, saboda na iya aikin karfi, kuma ba ni da
girman kai. Sabanin abokaina *ya*yan masu hali,
wadanda iyayensu ne suke turo su karatu sun
kuma jifgo musu dukiya mai yawa saboda gata,
kada ma *yan Nigeria su ji labari sun fi kowa irin
wannan wadaka da kudi.
Ina turawa su Khausar kudi masu yawa da kayan
sakawa daga English wears har atamfofin super
Hollanda yayin da mahassada suka shiga aikinsu
na hassada da yada labarun karya.
Wai sai dai idan ba karatu na je ba, damfara nake
ina turo musu da kaya da kudi haka. Idan su
Khausar suka fada min sai na yi dariya na ce su
rabu da su, kuma su toshe kunnuwansu ko sun ji
su ki ji.
Abinka da Babba sai Ummana Fuse ta shiga yimin
nasihohi tana cewa, kada na yarda na biyewa
abokan banza na fada harkar banza. Kada na
sake na yi sata ko damfara dan na turo musu da
kudi, su rinin kamfalar nan ma ya ishe su, su ci
abinci.
Na yi mata rantsuwa bana banayin wannan
harkar inda ina yi da Uncle Hamza ya sani
tuntuni, kuma da zai sanar da ita koma ya koro
ni gida. Kuma can kasa ce mai tsaro kana yi za,a
kama ka, na'urorin daukar hotuna a ko'ina.
Khausar daman a bayana ta ke, tasan halina don
haka ba ta damu da sharci-fadin mutane ba, ita
ce
mai hana Ummana Fuse zato.
A waya suke fara fada min cewar, Khausar ta
sami saurayi yana so ya aure ta, sunansa Isah. A
Accra yake zaune yana sana'ar siyar da gwanjo,
amma dan asalin garin Kita ne dan Yaren Aibe.
Umaimah ta ce ''duk kasar Ghana ne? Ya ce ''Ai
garin Kita nan ne ma asalin Ghana dan dai yanzu
garin duk babu mutane sosai ruwa ya cinye su,
saboda suna da katon teku wanda ya ke fita har
kasashen turawa.
Akwai gidajen tarihi da suke wajen idan ku ka je
zaku ga jinin bayin da turawa suka kashe, idan
bayin suka yi gardama ko rashin lafiya, ko idan
suka yiwa mace baiwa ciki sai su harbe ta anan
dan basa son su haihu da su. Ban bawa Khausar
goyon baya ba, don ban cika son auren Accra ba,
dama zata sami dan Kano mana ta aura ta dawo
gida don ni har yanzu ban fitar da ran zan kaura
gida ba, don tarbiyar Ghana ba ta yi min ba, ga
su da nuna kabilanci.
Da na ji maganar aure tana kara kankama sai na
fito baro-baro na fada musu ra'ayina cewar, bana
so a yi auren nan, na fi so ta auri Bakano. Haba
sai Ummana na Fuse ta hauni da fada, ta zage ni
tas har
da koke-koke a waya, wai dama har yanzu ba na
kaunarsu, su dangin mahaifina, na fi son dangin
mahaifiyata duk wahalar nan da ta yi da mu
dama niyyarmu mu gudu mu bar ta wata rana?
Kun san tsoho da rikicewa, yanzu ya lauya maka
magna.
Hankalina ya tashi na shiga lallashi ina gyara
lafazina.
Da kyar dai ma samu ta huce da ni, don da ta
daina zuwa ta dauki wayar ma idan na bugo sai
dai Khausar ta zo.
Daga baya ma na hada musu wayar a gidan (land
line) suka huta zirga-zirgar daukar waya gidan
mutane kullum....
''Ya yi dariya.
Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai, ta ce
''Kai!
Me yasa ba ka so kamwarka ta yi aure alhali ta
yi shekara ashirin koma fiye da haka tunda ba
karatu take yi ba ai gara auren.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya yi dariya, ya ce
''Haka ne, na gode da wannan tambaya taki. Ina
da dalilaina masu yawa. Kinga macen Ghana dole
ta fita nema don idan ma baki da sana'a ko aiki
babu mai auranki. Na tabbata yaron da yake son
Khausar ya zo wajenta ne a dalilin ya ga tana da
sana'a, tana samun kudi, kuma ga ni Yayanta a
turai, ina turo musu da dukiya. Da ace ba ta da
komai ba ma zai zo ba.
Haka idan an yi auren raba dai-dai za a dinga yi
ta yi wani aikin ciyarwar, ya yi wani shima. A
lokacin ne ma zata fi zagewa tana yin rini tun
karfi don takai masa wadataccen kudi.
Na biyu, tarbiyar yaran da zata haifa ba zata yi
kyau ba, saboda al'adunsu kamar babu musulunci
a ciki.
Na uku, bana so na tafi na bar ta ita kadai a
kasar, na santa da mako, tuni zata gigice ta rame
da koke-koke don ba ni da ra'ayin sake zama a
Accra kuma,
idan bana turai to ina Nigeria, Abuja da Kano.''
Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Ashe ba ka auri
*yar Ghana ba?''
Ya tuntsire da dariya, ya girgiza kai, ya ce, ''Ban
auri *yar Ghana ba. Ina can suka fadamin an
saka rana,
don haka suna bukatar kudi masu yawa saboda
shagalin bikin da ake a can ya baci. Bidi'a ce
zallah.
Umaimah ta ce, ''Ai daman ko a Nigeria al'adar
auren Hausawa gidan mata suna shan wuya,
bayan
kayan daki da gara. Abdul-Sabur ya girgiza kai,
ya ce, can mata ba sa
kai kayan gara, duk miji ne zai yi. A inda suke
kashe kudi a wajen shagalin biki ne sai a fi sati
mata suna daukar girki ba na wasa ba, kuma mai
dadi da nama cusu-cusu. A biki dole ne ka yanka
sa ko shanu, rago ko raguna, bayan kaji. Saboda
bikin ne mata suke hada kungiya
(meeting) suna taro duk karshen wata suna tara
kudi ana ajiyewa don idan biki ya kama wata a
cikin kudin da aka tara za a siya mata abubuwa
don ta rage nauyi.
Suna fara aiki ranar juma'a da daddare a yi
kunshi nan ma taro ne za a yi mata tuli a kan
kujeru a kofar gida, abinci kala-kala, iyayen
amarya dole su sayiwa *yarsu leshi mai tsadar
gaske ta saka a wannan rana. Washe gari asabar
sai a yi Ashadi shima amarya sai ta canza kaya
tsadaddu kamar kala uku ko biyar. Duk sai da na
kundige wadannan kudade na aiko musu suka
sha shagalinsu, na bita da addu'ar fatan fatan
alkhairi.
Da na kammala karatun degree dina da kaina na
biya na wuce na yi masters dina. A lokacin na
mallaki gidan haya babba ni kadai, da motar
hawa.
Sai dai naje ofishin Uncle Hamza na gaishe shi a
can dan kiyayyara tayi tsamari tsakanina da
iyalansa har babban dansa ya ja min kunne kada
in sake zuwa gidansu, idan ya sake ganina sai ya
harbe ni.
Don haka sai na fadawa Uncle Hamza sai dai na
dinga ganinsa a ofis ko kan titi.
To yawanci ma sai ya zo ya same ni a makaranta
ko a gidana mu yo maganar da zamuyi, don so
yake idan na gama karatu ya gutsuro wasu daga
cikin dukiyarsa ya
fara aikena Indonesia da Swizerland ina saro
masa shaddoji, leshina na mata da huluna
sana'arsa ke nan.
Amma ya lura *ya*yansa da matarsa suna
kacaccala masa dukiya sai ya je kasuwa ya tarar
sun je sun karbe ciniki bada izininsa ba.
Haka kuwa akayi, ina gama karatu ya hadani da
wani Ishaya babban yaronsa dan Nigeria ne shi
ma, muka je kasashe uku ya nunamin wuraren sa
suke saro kaya.
MAKWABTAKA 16
Zuwana cikin shagon sai na ruguza cutar da suke
yi masa wajen lissafin bogi, na saka musu ido
don ba su isa su yi min wayo ba, na fi su ilimi.
Sabanin Uncle Hamza wanda bai yi makaranta
ba. Bakin jini na yi sosai a wajen ma'aikatan dan
suna ganin ba karamin tauye musu rayuwa nayi
ba,