Showing 75001 words to 78000 words out of 130520 words
Chapter 26 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
zata iya yi
masa musu ba. Ta kula yana yi musu komai
saboda Allah, don Allah Ya halicce shi mutum mai
tausayi, kulawa da kuma son kyautatawa kowa
bata ga wata alama ba bayan haka.
Bayan ta tsallaka gada sai ta tsaya a inda ya
umarce ta da jira shi, ba jimawa sai ta ga ya
bayyana a kusa
da ita cikin tsaleliyar motar nan ttasa. Ya tsaya a
gefenta ta bude ta shiga gidan gaba ta zauna. Ta
dube shi ta yi murmushi, shi ma ya yi mata
murmushi.
Ya ce, ''Kina so ki bata ne a kasar mutane? Ke da
kike kamar kifin rijiya, babu inda kika sani daga
gida sai makaranta idan kin yi nisa ne ma kike
zuwa Bukit bing tang.
Sai ta yi dariya, ta ce, ''Ka kai ni tashar da zan
hau motar Mantin sai in hau in je da kaina ba sai
ka wahalar da kanka ba.
Ya ci gaba da kallon titi yana tuki, yayi dan
murmushi, ya ce, ''Kada ki damu, ba zan kai ki
inda za a ganmu tare ba. Sai in kai ki
makarantarsu tunda a hostel suke gidajen dalibai
ba nisa da cikin
makarantar sai su zo su dauke ki ni kuma sai in
tafi kafin su karaso.
Ta ji sanyi a ranta, sai ta gyara zama ta saki
jikinta.
Ya isa bakin wani banki ya sami waje ya tsaya,
ya juya ya dube ta, ya ce.
''Ki min hakuri mintina kadan zan shiga banki na
fito.
Ta gyada kai, ta yi murmushi ta ce, ''Ba damuwa
sai ka fito.
Ya fice da sauri ya bar mata A.c da CD a kunne
tana ji. Ta bude gidan da yake ajiyer CDs ta shiga
duddubawa can ta hango wakar da ta ke nema ta
saka don wakar rannan ta yi mata dadi wato ta
'Akuri Afomsa.
Ya dan dade amma ba da yawa ba ya fito, bayan
ya yi mata sallama sannan ya shigo motar ya
zauna. Ta dukar da kai ta yi masa sannu da
zuwa. Ya yi murmushi ya amsa, sannan ya fara
tuki. Sai bayan
da suka yi nisa ya kula ta canja wakar ba ta da
ba ce da yake ji.
Wato wakar Rihanna' mai taken 'Te amo' sai ya
ji
ana Yaren 'Asanti' maimakon 'Turanci' ya kurawa
rediyon ido ya juya ya dube ta, ita ma ta tsaya
tana kallonsa tana sauraron abin da zai ce mata,
don
daga dukkan alamu ta ga yana shirin yin magana.
Sai ya fasa maganar ya ci gaba da duban
gabansa.
Ta ji ta fara zargin kanta ko ya fi son waccan
wakar ta canja masa? Nan da nan ta dauko
wancan CD na farko ta mika hannu ta danna
wajen fitarwa, sai ya sa hannu ya
tare ya hana CD fitowa ya sake tura shi ciki, ya
ce gaba da yi.
Ta kalle shi, sai ta sunkuyar da kanta kasa ta
ajiye CD da yake hannunta suka ci gaba da tafiya
ba tare da wani ya sake magana a cikinsu ba. Sai
sanyin AC mai hade da kamshin daddadan turaren
mota,
gami da sautin kida da zazzakar muryar da yake
rera wakarne kadai yake tashi.
Nan da nan sai suka ga tafiyar ta yi musu sauri,
kan ka ce kwabo suka isa Mantin suka gangara
zuwa cikin Legenda makarantar su Hanif. Ya
sami waje ya tsaya sannan ya juyo ya dube ta.
Ya ce, ''Yaushe Hanif din zai tafi Najeriyar?
Ta ce, ''Cikin satin nan ne.
Ya ce, ''Me yasa ke ba zaki bishi ba, ku je ki ga
*yan gida, kin fi so ki ba shi sako? Ta sunkuyar
da kanta kasa da alama ba shi da amsar wannan
tambaya.
Ya ce ''Me da me kike so ki aikawa *yan gidan?
Ta shafa jakarta, ta ce, ''Wata ambulan ce na
rubuta wasika doguwa zuwa ga Baffa da Sabitu,
ina shaida musu ina nan lafiya su kwantar da
hankalinsu. Idan na gama karatu zan zo na gan
su. Sannan na ce su taimaka su je Gombe gidan
iyayen Abdul-Basi
su duba Babangida da Bilal. Sannan na siyo musu
wayoyi guda biyu daya ta Sabitu daya ta Baffa,
don
ina kyautata zaton an kai musu service din waya
garin ko kusa da garin. Sannan na dauki kudi na
je na canja Riggit ya zama Dallar dubu biyu, zan
ba shi idan ya je Najeriya ya canja ya zama naira
dubu dari uku da ashirin da wani abu, ya kaiwa
su Baffa da Sabitu su yi jari, sai kuma hotunana
dana dauka a nan kasar guda goma na wanke na
hada musu don su ganni ina cikin koshin lafiya.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kin yi dai-dai,
gaskiya kinyi tunani, ya yi kyau hakan da kika yi.
Na ji dadi da kika yi wannan tunanin, kuma
daman haka ya kama ta ki yi gara su ji motsinki
akan shirun nan da kika yi kamar ba kya raye.
Yanzu za su ji dadi, kuma hankalinsu zai kwanta.
Sun san bakya tare da Abdul-Basi kuwa?
Ta yi shiru kamar mai tunani, can ta dago a
hankali ta dube shi, ta ce, ''Ina kyautata zaton
sun sani,
saboda daman Sabitu ya sani ban boye masa
komai ba, ban sani ba ko dalili zai sa ya fada
musu.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Zancen
gaskiya sun san ba kwa tare, saboda Abdul-Basi
har garinku ya je nemanki, kuma ya yi musu
bayanin cewar kina cikin wadanda ku ka tafi
karatu Malaysia, shima kuma daga baya ya
bincika a gari
ya ji labari, kaninsa ne ya kai shi gidan Lamijo
nemanki ta ce ba ta san inda kike ba yanzu, sai
Baban Hanif ya fada musu gaskiyar magana. Alh.
Nasir dinma ya fada min haka Abdul-Basi ma ya
fada min, don haka kada ki boyewa Baffa komai
ki sanar da shi ba ki da aure, amma kina kama
kanki, kina tsare mutuncin kanki ya taya ki
addu'a.
Hawaye ya cika mata ido taf! Ta sharce da gefen
gyalenta ta ce, ''Yanzu Lamijo ta ji labarin
tahowata alhalin tana zargina da mijinta?
Abdul-Sabur ya ce, ''Ah! To meye dan ta ji ai ta fi
kowa sanin zaki taho daman kuma me ye abun
mamaki don ta ji kina nan? Mijinta kuwa ai ba da
shi kika taho ba, kin bar mata abinta a can. Kuma
babu
wanda ya fada mata makudan kudin da Alh. Nasir
yake baki ke da Hanif, ko nima ya so ya boye
min,
sai da ya ga dai na sani sannan ya sake fada
min, ya ce kuma bayan Hanif da ke da Alh. Sani
da ya fara
aikowa ya baku bai taba fadawa kowa ba. Kuma
ya gargadi Hanif kada ya fadawa kowa hatta
mahaifiyarsa, saboda yana da *ya*ya da yawa,
duk uwarsu daban abun zai iya zama rigima idan
wata
mata ta ji ita bai bawa danta ba.
Umaimah ta yi ajiyar zuciya ta sake goge
hawayen idonta da alama ta ji sanyi a ranta. Ya
dube ta ya yi murmushi, ya ce, ''Babu matsala.
Na
gode sosai, sai na dawo.
Ta yunkura zata bude kofar mota ta fice sai ta ji
ya ambaci sunanta, sai ta waiwayo da sauri ta
dube
shi.
Ya zaro kudi daga aljihunsa Dallar dari biyar ce
ya mika mata, ya ce.
''Ga shi ki hadawa su Baffa na canjo musu yanzu,
na zaci ba za ki hada musu da kudi ba, sai ki rike
nawa idan kuma kina ganin dukka za ki aika
musu ya yi dai-dai.
Za ta ki karba ya bata rai, kuma ya ja mata
kunne ba ya so duk abin da ya yi niyyar yi mata
ta ce ya bar shi. Tayi godiya ta karba.
Ya ce, ''Yaushe za ki dawo gida?
Ta ce, ''Gobe ko jibi
Ya ce, ''Magana daya za ki fada don zan dawo in
dauke ki a dai-dai nan wajen inda na ajiye ki?
Ta yi shiru can ta ce, ''Jibi zan dawo.
Ya ce, ''To ba damuwa, kuma ga waya ma zamu
yi,
ki gaida su Hanif. Akwai wanda nake so na gani
a cikin garinnan, amma sauri nake yi idan na
dawo
jibin zan gan shi. Zan je na dauko Faduwa a
Putra jaya mun yi da ita karfe goma sha biyu za
ta gama.
Umaimah ta yi murmushi gami da lumshe ido, ta
ce,
''To shi ke nan, ka gaida gida.
Ta bude kofar mota ta fice, yana daga mata
hannu tana daga masa. Ya ja mota a guje ya fice
daga
farfajiyar makarantar. Ta dade a tsaye tana
mamakin irin wannan kirki da kulawa na Abdul-
Sabur. Ta ji dadi data ji yayi zancen Faduwa don
daga dukkan alamu ya yarda da shawararta, ya
amince zai so Faduwa kuma ya aure ta.
''Amma fa na taya Faduwa murna da samun miji
kamili. Ina fatan ni ma Allah Ya ba ni miji na gari
mai
halinsa. Inji Umaimah ta fada a zuciyarta. Yayin
da ta ke kokarin zakulo wayarta daga aljihun
jakarta
zata bugawa Hanif ta shaida masa ta iso
makarantarsu ya zo ya dauke ta.
Tun da Umaimah ta tafi Legenda ba ta kira Abdul
ba, shima bai kirata ba har ta cika kwanaki
biyunta da la'asar tana shirin kiransa sai ta ji ya
kira ta. Ya shaida mata ya shigo garin, amma ya
wuce gidan abokinsa da zai gani don haka ta
shirya bayan sallar magruba zai zo ya dauke ta.
Ya tambaye ta inda zai same ta a gidan su Hanif
ko a makaranta
inda ya ajiye ta?
Ta ce, zata fito ta jira shi a inda ya aje ta. Suka
yi sallama suka kashe waya.
Yana idar da sallar magruba kuwa ya zo ya tsaya
a inda suka yi ya dauke ta, ya iske ba ta karaso
ba,
don haka ya yi zaton ko tana kan hanya don haka
bai damu da ya dame ta da kira ba. Ya shefe fiye
da
awa babu ita babu kiranta. Da ya ji shirun yayi
yawa sai ya kira ta, tana ta ruri ba ta amsa ba. A
masallacin Makarantar ya yi sallar
isha'i ya dawo cikin mota ya ci gaba da jira bata
zo ba sai ya sake kiranta. Tun wayar tana shiga
har ya ji an kashe ta mudik. Sai ya shiga mamaki
marar misaltuwa, gami da fargaba ko ba lafiya.
Yana nan a wajen har karfe goma sha dayan
dare.
Ya yanke shawarar neman gidan Hanif ya je ya
gani ko lafiya? Sai ya fasa zuwa saboda ya
fuskanci ba ta
so a dinga ganinta da namiji. Ya zama ba shi da
wata shawara ko dubara kuma. Ya shiga tunani
anya kuwa mai ilimi da wayewa zata yi haka?
Fatansa dai ace tana nan lafiya, kuma cikin
koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Ya shiga tunanin ko kara kwana ta ke so ta yi, ko
kuwa motar haya ta hau ta koma gida?
Sai wata dabara ta fado masa ya yanke shawarar
ya kira Faduwa ya tambaya ko Umaimah tana
gida. Yana kiran Faduwa bugu daya wayar ta
shiga, ta dauka. Ya tambaye ta tana ina? Sai ta
yi mamaki da tambayar da ya yi mata alhali da
yamma nan ma
sun hadu tana gida.
Ta tambaye shi, ''Lafiya?
Ya ce, ''Idan kina gida ki duba min gidan
Umaimah tana nan?
Faduwa dai ba ta daina ambaton lafiya ba.
Ya ce, ''Lafiya mana, ko kinji alamar rashin lafiya
a tare da ni?
Ta yi dariya ta ce, ''Ai tambayoyin ne na ji ba irin
wadanda ka saba yi min ba ne. Ya ce, ''Dubo min
ita za ki yi kawai ki fada min ko ta dawo daga
Mantin?
Faduwa ta ce, ''To kashe wayar bari na gani, zan
kira ka.
Ta kira wayar Umaimah a kashe, don haka dole
ta katse baccinta ta tashi ta dauki mayafi ta hau
sama gidanta. Ta danna kararrawa sau daya
kacal sai ga Umaimah a bakin kofa, ta bude kofar
da sauri tana
kokarin cewa Faduwa ta shigo ta zauna.
Faduwa ta ce, ''Bacci na ke ji zuwa na yi in duba
in ga ko kin dawo? Na ji wayarki a kashe kuma.
Bayanin Faduwa ya ba ta mamaki, tabbas ta san
akwai dalili. Sai ta yi kasake abunka da marar
gaskiya, can ta dago ta dubi Faduwa ta ce, ''Ina
Abdul-Sabur?
Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Shi ya taso ni ya
ce in duba ko kin dawo gida lafiya. Wai me yake
faruwa ne?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Babu komai.
Kamar yadda na fada miki shi ma na fada masa
yau zan dawo, to kuma waya ta a kashe ban yi
caji ba shiyasa ban fada masa na dawo ba.
Faduwa ta ce, ''Kiyi caji ki kunna ki fada masa
kin dawo. Umaimah ta ce, ''Yana gidansa ne?
Faduwa ta ce, ''Ina ma na san inda yake, a waya
dai ya kirani yanzu. Bari na kira na fada masa kin
dawo. Rufe gidan ki kwanta, ni ma zan je in
kwanta.
Ta juya ta tafi, ta danno lambar Abdul-Sabur
tana tafe tana magana da shi yayin da Umaimah
ta sankare a tsaye saboda tasan ba ta kyauta
masa ba.
''Yanzu ina mafita?
Ya ya zan yi in wanke kaina daga wannan rashin
ladabin da na tafka?
Umaimah ta ke wasu-wasi a zuciyarta.
Abdul-Sabur bai shigo gidansa ba sai karfe daya
da rabi na dare, yayin da Umaimah ke tsaye a
dakinta tana kai kawo, ta kasa sukuni har sai da
ta ji motsinsa a cikin gidansa. Tana hango
hasken fitilun da ya kukkunna yana ya kai kawo a
cikin gidansa.
Bai kwanta ba sai karfe biyu da kwata sannan ita
ma ta samu ta kwanta, hakarkarinta. Da kyar ta
yi bacci tana sake-saken yadda zata tunkare shi
da bayanin da zai gamsu da ita, kuma da
idanuwan da zata kalle shi. Tabbas ta tabbatar
ba ta kyauta masa ba.
***************
Washe gari da misalin karfe goma sha daya da
minti goma sha daya Abdul-Sabur ya ji wayarsa
ta dauki
ruri. Yana zaune a falonsa yana kallon labaran
CNN.
Yana dubawa sai ya ga Umaimah ce don haka
sai ya gyara zama don ya ji abin da zata fada
masa,
sannan ya danna wayar gami da yi mata sallama.
Shima maganin sa. Yabi ya takura mata sosai.
SAI GOBE INSHA ALLAH.
MAKWABTAKA 33
Ya ji tana magana da kyar yayin da muryarta ke
karkarwa. Bayan ta gaishe shi, sai ta fara da ba
shi
hakuri, sannan ta dora da bayanai barkatai..
Da ya hada dogayen bayananta a waje daya ya
dunkule ya fuskanci tana magana ne akan da ta
tashi tahowa Hanif da kawayenta ne suka cika
mota guda suka ce za su kawo ta har gida, ita
kuma ta kasa fada musu akwai wanda ya ke
jiranta. Sanda yake kiranta a waya tana tare da
su a mota ba zata iya amsa masa ba a gabansu,
don haka ta kashe wayar.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Kada ki
damu Umaimah na fahimce ki sosai, kuma na yi
miki uziri.
Hakan da kika yi kin yi dai-dai da ba ki bari wani
ya zarge ki ba balle aje Gombe ana yadawa
nasan halin mutanenmu. Ki shirya da yamma ke
da Faduwa za mu fita mu dan kewaya gari.
Farin ciki ya rufe ta da Allah Ya sa ya fahimce ta.
Nan da nan ta amsa masa da, ''To, Allah Ya
kaimu anjimar, na gode.
Karfe biyar saura kwata a motar Abdul-Sabur
suka hallara shi yake tukawa, Faduwa na gefensa
a gidan gaba yayin da Umaimah ta ke zaune a
kujerar baya. Babu abin da yake tashi a motar sai
sautin kida wakar larabawa ce Faduwa ta saka ta
'Nancy' mai taken 'Yatabtab.
Tana daga zaune ta ke rawa tana bin wakar.
Abdul-Sabur ya kashe, ta sake kunnawa idan ya
rage sai ta sake karawa, Umaimah na zaune ba
ta da aiki sai dariya da kyalkyalawa.
Waje-waje na shakatawa suka dinga zuwa kama
daga wajen cin abincim shan ice-cream, gidan
zoo
da kuma malls inda ya ce kowacce ta dauki abin
da ta ke so ko nawa ne zai biya, su ka jidi kaya
kuwa. Ba su shigo gidajensu ba sai karfe daya na
dare daman sun riga da sun yi sallolinsu a
masallacin 'BB
Plaza' don haka kowannensu wanka ya yi ya
kwanta.
Washe gari da ya yamma sai ga Faduwa a gidan
Umaimah dauke da wasu takardu a hannunta,
tana shigowa ko zama bata yi ba sai ta mika
mata.
Ta ce, ''Ga form, ki cike inji Abdul-Sabur na
makarantar koyon tukin mota ne, kullum da safe
ko da yamma ake zuwa. Ke da ba ki taba iya
tukin mota ba watanni uku zaki yi. Kina gamawa
in kin ci jarabawa za'a baki 'driving liences'. Ni
kuma da yake tsohuwar direba ce wata daya
kacal zan yi a ba ni nima nawa idan na ci
jarabawa.
Umaimah ta cika da mamaki ta ce, ''Me yasa zan
shiga Makarantar koyon tuki alhali ba ni da mota,
kuma ba inda nake zuwa Makarantarmu ga ta a
kusa da ni? Faduwa ta ce, ''Haka dai ya ga ya
dace mu shiga kasancewar dogon hutu ne, idan
ma kika zauna a
gidan me zaki yi kuma shi tuki ai yana da amfani
idan ka iya din, saboda ko a kasarku nan gaba
zai
amfane ki sai ki dinga tukinki ba sai kinyi ta
neman direba ba. Umaimah ta ce, ''Haka ne, na
gode. Ta karbi forms din ta cike ta mikawa
Faduwa.
Yayin da Faduwa ta ce, ''Ai tashi zaki yi mu je
koyontukin yau za'a fara, ga Abdul din can ma a
mota
yana jiranmu.
Umaimah ta dafe kirji ta zabura ta ce, ''Wai!
Tukin yau zan fara? Gaskiya Anti Faduwa tsoron
mota nake ji.
Faduwa ta kyalkyale da dariya, ta ce ''Ke *yar
kauye ce har yanzu. Meye abun tsoro kuma a
tukin mota?
Ki zo mu je kada mu bata masa lokaci.
Daman Umaimah a shirye ta ke tsaf, don haka
gyalenta kadai ta jawo da wayarta ta rufo gidan
suka sauko, suna shiga motar Umaimah ta
gaishe shi sannan ta yi masa godiya bisa kulawar
da yake yi musu.
Faduwa ta fara ba shi labarin yadda suka yi da
umaimah a sama da ta ce ita tsoron tukin mota
ta
ke yi. Suka sha kyalkyala dariya su dukka ukun.
Abdul-Sabur ya shiga yi mata bayani akan ta
kwantar da hankalinta ba wuya, shi tuki nutsuwa
ya ke so da kuma cire tsoro.
''Na samar muku makarantar da ba ta da nisa ko
bana nan sai ku dinga takawa da kafa ko ku hau
tasi, Riggit uku ma zai kai ku. Inji Abdul. Su
dukka suka amsa masa da godiya gami da fatan
alkhairi.
Ashe dai makarantar koyon tuki makaranta ce
sosai, har da ajujuwa da takardun rubutu da
karatu. A koya musu a rubuce sannan a fita ayi
gwaji a zahiri.
A ranar Abdul-Sabur ya jira su a mota har suka
gama suka fito daga ajujuwansu suka dawo gida
tare. Amma sun yi shawara su dinga zuwa da
safe ba da yamma ba, karfe tara zuwa karfe
goma sha
biyu na rana.
Don haka kullum Umaimah ce ta ke saukowa, sai
ta bi ta gidan Faduwa sannan su dunguma su tafi
a motar haya, ko a kafa ko kuma Abdul Sabur ya
kai su, ko ya dauko su idan ya ga fitarsu.
Ku san kullum da yamma ka'ida ne sai sun fita
wuraren shakatawa iri-iri, don haka kowannensu
ya daina girki abinci kala-kala suke ci a waje,
kuma har su tafi da wasu gida.
Gaskiya Umaimah ta ji dadin hutun nan, ba ta
taba jin dadin Malaysia irin wannan karon ba, har
kiba ta fara yi babu kashin nan rankwal-rankwal
na rama. Babu sauran
hawaye a idanunta, kullum suna tare su uku,
wasa da dariya kadai ne a tsakaninsu. Sai ta ji ta
saba da
su sosai ta cire jin kunya, nauyi da tsanar
ganinsu da take ji ada da.
Sai ga ta gidanta ba ya rabo da mutane ku san
kullum sai ta yi baki *yan makarantarsu, kuma
*yan garinsu suma suna zuwa. Su Aisha Bingyal
sukan yi kungiya su ziyarce ta, ita ma da su
Abdul-Sabur suna biyawa ta gidajensu.
A wannan sabuwar makarantar ma ta koyon tuki
sai ga ta ta yi kawaye mata wasu sa'anninta,
wasu kuma sun girmeta sosai, su ma har gidanta
suke ziyartarta.
Wasu kuwa kawayen Faduwa ne idan suka zo
gidan Faduwa sai ta shigo da su gidan Umaimah.
A hadu a yi ta hira ana ciye-ciye ana shewa. Idan
dare ya yi kuma sai ta yi zaman kiran wayar *yan
gida Nigeria, garin Gombe wato *ya*yanta,
Babangida da Bilal. Wannan dole ne kullum da
daddare sai sun yi waya, kuma