Showing 48001 words to 51000 words out of 130520 words

Chapter 17 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8023

yunwa ba ni da kudin siya, duk *yan
mota suna ta ciye-ciye.
Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, abu bai yi dadi
ba.
Daman shi aure a karkashin bishiyar dabino ake
daura shi, a raba shi a karkashin bishiyar aduwa,
ko darbejiya. Ma'ana bishiyar dabino zaki,
bishiyar aduwa kaya, ko darbejiya daci. Allah Ya
kyauta, Ya kare mu daga sakin aure, ai ni bana
son na ji anyi sakin aure. Bana burin na auri
macen da zan iya saki da bakina sai dai mutuwa
ta raba mu.
Faduwa ta ce, ''Ai ko ba ka fada ba kai ai mai
laushi ne, macen da ta aure ka sai dai ta nemo
rigima da
kanta, amma kai ba ka da matsala.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta ci gaba
da cewa, ''Ilah da almajirinsa da Sabitu kanina
sai suka zuba min ido suna yi min kallon rashin
fahimta da suka ga na fito daga mota jikina sanyi
kalau, ido ya yi min jawur alamar kuka da na sha.
Sun san ba lafiya ba, kuma ba su taba ganin na
zo ni kadai ba
babu Abdul-Basi, kuma a motar haya.
Direba ya sauko min da akwatina, yara suka
kinkima suka kai min ciki. Na sunkuyar da kai na
shige cikin gida.
A zaure na ga Baffa jin sunana da ya yi yasa ya
tashi zaune.
Kira ya ke, ''Ina Bilal zo nan ja'iri.
Sai na girgiza kai na ce, ''Baffa ni kadai na zo, na
baro shi a Kaduna.
Ya ce, ''Af ke da Basi'un ne?
Na sunkuyar da kai ina shirin fasa kuka, sai na
daure na ce, ''Shi ma bai zo ba.
Sai ya yi jigum can ya nisa ya ce, ''Zuwan lafiya
kuwa kika yi ko ce miki aka yi na mutu ne? Na
fara kuka, na ce, ''A'a babu wanda ya ce ka
mutu.
A nan ya fara fuskantar wani abu ba lafiya ba, shi
ma ba ya so yara su ji ko matansa, sai ya yi
sauri.
Ya ce, ''Je ki ciki ki huta kin sha hanya.
Na shiga na gaishe da su Nene sun yi carko-
carko a tsakar gida suna jiran labari marar dadi.
Na shige dakin Yafindo wanda ya zama dakin
Sabitu.
Na yi sallah na jira abincin dare, tuwon dawa ne
miyar kuka lami shatab a haka na cuccusa
saboda
yunwa. Sabitu ya shigo ya zauna kusa da ni ya
gaishe ni ya shiga tambayata. Cikin rada na ba
shi labari, amma na ce kada ya fadawa kowa sai
ya dafe kai ya yi shiru da alama hankalinshi ya
tashi matuka.
Ya ce da ni, ''Ai ko kada ki fadawa Baffa, kada
jininsa ya hau. Ki shirya ki je Gombe ki sanarwa
iyayensa za su mayar da auren tunda *yan
mutumci ne.
Na ce, ''Ai ba ni da kudin mota''
Ya ce, ''Zan ba ki idan kin tashi tafiya.
Da safe Baffa ya tambaye ni lafiya? Sai na shirga
masa karya na ce, umara ya tafi ya ce na dawo
gidansu Gombe na zauna, ni kuma na ce gara na
zo gida.
Ya ce, ''Ban da abinki me ye abin zuwa nan ki
zauna Allah Ya rufa miki asiri kina zaman birni,
me yasa za ki waiwayi baya?
Na ce, ''Ai zan dinga zuwa Gombe ina dawowa''
Sai ya yi addu'a Allah Ya dawo da shi lafiya, na
ce, ''Amin.
Duk da ban fada ba matan Babana dai suna ta
zarge-zarge anya kuwa ba karya na ke yi ba,
aurena ne ya mutu irin wannan katuwar akwati
dana ciko da kaya?
Matawata ma yara suke fadamin ta kirasu tana
tambayarsu ko sakina aka yi, na dawo gida? Sai
suka ce mata, a'a mijina ne ya tafi Makka na
dawo gida,
Ta ce, ''Allah Ya sa a sake ta ma.
Ilah ma ya tambayi Sabitu anya kuwa lafiya ya ga
na zo a jejjeme? Sabitu ya ce, ''Lafiya kalau mijin
ne ya yi tafiya shi ne ta zo Gombe daga nan ta
karaso gida.
Bayan kwana biyu na shirya na dauki kayana kala
biyu a *yar jakata na kira Sabitu ya ba ni
isasshen kudin motar Gombe zuwa da dawowa.
Na kama hanya. Na isa da rana na iske Hajiyar
Abdul-Basi, ta kalle ni ta watsar, don ba haka ta
saba yi min ba, sai na tsorata na zube na gaishe
ta. Idan na yi mata
Fulatanci sai ta amsamin da Hausa, sai na rasa
wannan dalili. Na fara yi mata bayani sai ta katse
ni,
ta ce, ta ji duk abubuwan da na shuka, ai ba a
kaina aka fara yin kishiya ba da zan dagawa
danta hankali don zai yi aure.
Na shiga yi mata bayani dalla-dalla sai ta dinga
amsawa a shelake, ban yi mamaki ba don irin
dinkakkun kayan Senegal wanda Zulayha ta ke
siyarwa ta kawo mata, saboda a lokacin ma
irinsu ne a jikinta. Don haka Zulayha ta fi ni kirki,
don ta fi ni kudi tunda ni bana dinko mata kaya
na kawo.
Daman mahaifinsa ne ke son mu ita ta fi son ya
auri *yar mai kudi, *yan birni don dai rabon
Babangida
da Bilal ne, babu yadda ta iya.
Sai na fashe mata da kuka na durkushe a gaban
matar nan ko rarrashina ba ta yi ba, na yi ta yi
har na gaji na daina.
Na tambaye ta ina Alhaji, sai ta ce da ni, ''Me za
ki yi masa?
Na ce ''Zan fada masa cewar Yaya Abdul-Basi ya
sake ni''.
Sai ta ce, ''Wa yace miki bai sani ba? Shi zai
hana a sake ki ko shi yake zaune da ku?
Zulayha ta kira ni a waya a dai-dai lokacin da
kika gama min zagi, wai
kin kwace Babangida ke za ki rike tunda dan
yayarki ne. Ban da munafunci nima da na hana ki
rike shi yanzu na dauka na ba ta saboda na ga
gidan maiko ko?
To duk na ji zagin da kika yi min. Abdul-Basi ma
ya bugo ya tabbatar min kin yi har kin shiga
gidan kin kwaso *ya*yan kina masa rashin kunya
don kin koshi, kinsha jar miya, kin taka matsayin
da ba ki isa ki taka ba, saboda samun guri.
Sannan kika yada sirrinmu a makwabta har ofis
ake gulmarsa, to me zai yi da ke dan ba son kai
da
rashin kunya irin ta mutanen kauye ba?
Hannu na dora aka ina salati ina kuka, ina kuma
rantse-rantsen ban fadi haka ba, sharri ne kawai
aka kulla min.
Da Halamu Littafin nan ya fara isan ku. In
bakwaso kuyi magana sai a canxa wani.
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 21
sai ganin fitowar Ja'afar nagani.
Ya fito a fusace ya daka min tsawa, ya ce, ''Ke
Umaimah ki rufe mana baki, kin ishe mu da kuka
tun dazu.
Sai na nutsu na rufe bakina na hau makyarkyata
kada ya yi min duka, don gidansu na tako na zo.
Hajiyarsu ta ce, ''Yauwa gara ka fada mata,
kukanta ba zai amfane ta da komai ba, domin
mun gano
bakin munafunci da kwantingwilarta.
Ya karaso ya zauna ya dade kansa a sunkuye a
kasa kamar mai tunani, sai can ya dago ya dube
mu, ya girgiza kai don takaici. Ya ce, ''Har yanzu
daman ana zama na zalunci da jahilci, gami da
makirci a duniya?
Haba wannan abu da me ya yi kama?
Hajiya ta ce, ''Fada mata dai ta ji, an gano ta
yanzu,
da dai an dauka mai tarbiyya ce, ashe kallon kitse
ake yiwa rogo. An dai ji kunya wai kura da satar
tsumma.
Ya ce, ''Ke dai za a fadawa Hajiya ba Umaimah
ba.
Kin yi kuskure da kika ba wa danki damar auren
karuwa, ya rabu da matarsa ta arziki.
Sai dadi ya sa na yi ajiyar zuciya. Ta kuwa fusata
da jin batunsa, ta hau zaginsa. Tana cewa, ''Au
dama da ni kake, da ka ke cewa ana zalunci,
jahilci da makirci?
Ya girgiza kai, ya ce, ''Ya ya zan ce miki haka?
Da azzalumar karuwar nan nake da shi yaya
Abdul-Basin da suka sami yarinya karama
marainiya suna wahalarwa.
Ta daka masa tsawa, ta ce, ''Ku tashi daga
gabana bana son ganinku.
Muka mike sadaf-sadaf muka fice, yayin da muke
ta jiyo bambamin fadanta. Da muka fito waje sai
na ce da shi, ''Ina Alhaji? Ya ce, ''Ya tafi umarar
maulid shi da Sarki''.
Na ce, ''Ja'afar ya ya zan yi? Ka taya ni fada
masa idan ya yi waya, halin da nake ciki''.
Ya ce, ''Ki yi shuru, ki daina kuka, ki bari Alhaji
ya dawo a tsanake zan same shi na fada masa,
zancen bana waya ba ne. Saura kwana uku ya
dawo sai na zo mu yi maganar, yanzu dai bari na
kai ki tasha ki koma.
Na ce, ''To Allah Ya kaimu.
Ya dauko mukullin motarsa ya fito da motar, na
bude gidan baya na takure yana ta ba ni baki,
yaro mai hankalin manya duk da ya girme ni ma.
Ya fara wucewa da ni wajen cin abinci
(restaurant) ya siya min shinkafa da miya da kaji,
ina ji ina gani kamshin tururu amma na kasa ci.
Yana rokona da kyar na ci rabi muka fito muka
tafi.
Harya kama hanyar tasha zai saka ni a motar
garinmu, sai na ce ya kai ni gidan kawata Lamijo
dake unguwar Checheniya, tare muka yi firamare
a Kaduna, ta dawo Gombe tai sakandire daman
*yan Gombe ne aiki ya kaisu Kaduna a lokacin.
Ta yi aure a nan cikin garin Gombe, ta auri wani
hamshakin mai kudi da mulki. Duk zuwan da
muke yi ni da Abdul-Basi sai ya kai ni gidan na
yini, ita ma idan ta je Kaduna da yake da yayarta
da ta yi aure, sai ta zo gidana ta yiyi ko ta
kwana.
Da farko Ja'afar ya ki amincewa ya kai ni, sai da
na yi masa bayanin cewar, so nake na jira Alhaji
a
gidan ba sai na sha wahalar komawa da dawowa
ba. Ya ce ''Kina ganin za ki zauna a gidan har
kwana uku ba matsala?
Na ce, ''Ba matsala tana da wadataccen dakuna a
gidanta.
Ya amince ya kai ni har cikin get din gidan, ta
hango ni ta wundo ta fito da gudu ta tare ni da
murna, muka yi sallama da Ja'afar. Ya ce, zai
kira ni idan Alhaji ya dawo, sai ya zo ya dauke ni
muje wajensa.
Bayan ta hada min goma ta arziki muka fara hira,
sai na fara kuka ina ba ta labarin matsalata.
Tabbas ta tausaya min, ta ba ni goyon baya na
zauna a gidanta har Alhaji ya dawo, sannan ta yi
min addu'a Allah Ya sa na koma dakina.
Da daddare dan mijinta ya shigo wani matashi
yaro, a shekarar ya gama sakandire, sunansa
Hanif. Da
takardunsa a hannu ya zo neman Babansa...
Faduwa ta ce, ''Dan mijinta kamar ya ya?
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ke fa Hausa ba
ta ishe ki ba. Ana nufin mijin yana da wata matar
da kuma gidajensu daban-daban. Kuma girkin
amaryar ne shi ne dansa ya zo nemansa. Ko ba
haka kike nufi ba Umaimah?
Ta yi murmushi, ta ce, ''Haka nake nufi kuwa.
Alh. Rabi'u Damuna sunan mijin kawata, matansa
biyu ne, ita ce ta uku, kowacce kuma gidanta
daban, saboda mai kudi ne.
Ina zaune Lamijo da Hanif suna hirar tafiya
karatu Malaysia tun bana fahimta har na fara
fahimta, tun ban damu ba har na tsoma baki ina
jero musu tambayoyi.
Ya ce, ai ba Babansa ba ne zai biya ba, gwamnati
ce ta yi alkawarin duk *yan asalin garin wanda ya
gama sakandire ya keda credit tara za a biya
masa. Sai na ga ai ni ma na cancanci shiga cikin
wadanda ake neman nan. Sai na fara fadawa
kawata to ko nima na dauko takarduna, mijinta
ya taimakamin? Ta ce, a,a ya ya za'a yi haka
alhali ga shawarar da aka yi
za a zartar?
Sai Hanif ya shiga ba ni kwarin gwiwa yana
murna ya sami *yar uwa, ya ce, sai mu tafi tare.
Ya tafi akan zan hada takarduna da nasa a ba wa
babansa ya nemar mana tallafi daga gwamnati
(schoolership),
tunda ana damawa da shi a gwamnati, shi ma
kusa ne.
Lamido ta shiga yimin nasiha gara auren shi ne
mutuncina da na je kasar waje karatu ace na
zama
*ya iska. Na gyara zama na sake bude mata
cikina ta ji duk halin da nake ciki a Kaduna,
Gombe da can
Dugge garinmu. Na tabbatar mata Abdul-Basi ba
ya sona, ba zai mayar da ni ba, ko na koma
Zulayha ba zata bar ni mu zauna lafiya ba. Ga
mahaifiyarsa ta tarko tsana ko ita ba zata bari ya
mayar da ni ba.
Idan na zauna a garinmu gori da wuya ne za su
gallabe ni. Sai ta yi saranda ta yi amanna na bar
kasar. Amma ta shawarce ni na jira zuwa kwana
ukun surukina ya dawo a ji abin da zai ce.
Na dukufa ina ta addu'ar neman zabin Allah mafi
alkhairi tsakanin zuwana karatu Malaysia da
komawata gidan mijina. Na yi ta yin wannan
addu'ar istihara da Manzon Allah (S.W.A) ya ce
mu dinga yi zamu ji abin da ya fi alkhairi ya fi
kwanciya a ran mai yinta..
Faduwa ta ce, ''Ya ya addu'ar ta ke?
Umaimah ta ce, ''Sallah raka'a biyu ce a karanta
Fatiha da kowacce surah, sannan a karanta
wannan addu'ar:- Allahumma inni astihiruka bi
ilmika, wa astakdiruka bi kudaratika, wa as'aluka
min fadlukal azim,
fa'innaka takdiru wala akdaru, wa ta'alamu wala
a'alam, wa anta allamul guyub,
Allahumma in kunta ta'amu an hazal amru kairan
li fi dini, wa ma'ashiyi, wa akibati amri au kala
ajili amri, wa'ajilihi, fakdurhuli, wa yassarhuli,
summa barakli fihi, wa in kunta ta'alamul
annahazal amra, sharranlifi dini wa ma'a shiyi,
wa akibati amri, au kala fi ajili amri,
wa'ajilihi, fasrifhu anna wasrifni anhu, wa kudirli
kaira haisu kana summa Ardinibihi.''
A ranar da Ja'afar ya ce Alhaji zai dawo na ji
shiru bai neme ni a waya ba. Sai na kira shi bai
dauka ba.
Na ce, to ko shigowar dare ya yi, bari na bari sai
gobe na sake kira.
Washegari har yamma Ja'afar bai kira ni ba, na
kira bai dauka ba. Hankalinmu ya tashi ni da
kawata babu abin da ba mu saka a ranmu ba. Na
tabbatar mata sai dai idan Hajiyarsa ce ta hana
shi fadawa
Alhaji shi yasa bai dauki wayata ba.
Sai Lamijo ta kira da layinta ya dauka da ta fara
yi masa maganata sai ya katse wayar, da muka
sake kira sai muka jita a kashe murus. Na yi ta
kuka Lamijo na ba ni hakuri, ta shawarce ni na je
na debo takarduna ta yi min alkawari zata tsaya
min har sai na sami tafiya, domin mijinta yana
ji da ita. Sai abin da ta ce kasancewar ba ta
haihu ba har yanzu da ita ake cin amarcin, kasa-
kasa da ita yake zuwa. Ta bani kudin mota na
garzaya Dugge takarduna kadai na kwaso na ajiye
wadancan kayan na dauko wasu kala uku, na
kunso a jaka. Na sake
barkawa Baffa karya, amma Sabitu na fada masa
komai.
Da farko ya tsorata ya ce, kada na je kasar
Turawa su kashe ni. Na yi dariya kawai, na san
rashin wayewa yake damunsa. Na jaddada masa
insha Allah ba matsala zan je lafiya na dawo
lafiya, sai ya yi min addu'a Allah Ya ba ni sa'a.
Na dawo Gombe a ranar, na kawowa Lamijo
takarduna, daman ta gama fadawa mijinta ya san
da zancen. Da ya duba sai ya gyada kai ya ce, na
cancanta a ba ni tallafi in je karatu dan na cinye
jarabawata dukka. Sannan ya ce na yi photocopy
na ba shi na ajiye original a wajena.
Ta sake ba ni tabbaci na je na kwantar da
hankalina komai zai dai-daita nan da watanni
biyu zuwa uku komai zai kammala, za'a yi
tafiyar.
Sai a lokacin hankalina ya tashi yadda zan zauna
har tsawon watanni uku a garinmu, wai! Abin da
kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Dama
ya lafiyar Kura bare kuma ta yi hauka?
Ni kam na san tawa ta kare, asirin da bana son
ya tonu ne a kauyenmu shi zai tonu.
Da muka kebe da Lamijo na shaida mata ni fa
bana so na zauna da yawa a garinmu, don ban ce
musu
aurena ya mutu ba, ta ce, to na zo mu zauna a
gidanta mana.
Na ce, a'a ba zai yiwu ba, sai dai ta samo min
aikin wanke-wanke da shara na yi, don na sami
gidan
zama har lokacin tafiya ya yi. Ta girgiza kai ta
ce, ''Allah Ya sauwake na barki ki yi wanke-
wanke da shara.
A karshe dai muka tsayar da shawarar na zauna
da mahaifiyarta, daman ba ta da karamar yarinya
a gabanta, Lamijo ce *yar autarta tare suke
zama,
gashi ta yi aure ta bar ta ita kadai.
Umma mahaifiyar Lamijo ba ta ki ni ba da muka
je,
sai ta amince na zauna tare da ita, unguwar
Herwagana gidan ya ke. Ai kuwa ba ta yi da-na-
sanin zuwana ba, na zame mata abar alfahari,
bacci ne kadai bana yi mata, amma ko tsinke
bana barinta ta dauke.
Bayan zuwana da sati biyu na ga ya dace na je
gida na sanarwa Sabitu kada ya ji shiru ban dawo
ba ya dauka Turawa sun sace ni ya fito da
maganar.
Na shirya na tafi Dugge, na zaunar da shi na ba
shi labarin halin da ake ciki. Ya ji dadi da ganina,
don gaskiya har ya tashi hankalinsa.
Baffa kuwa karya dai na sake shimfida masa, na
ce Abdul-Basi ya dawo zan koma Kaduna, kuma
ina
tunanin zamu kaura wata kasar nan da *yan
watanni, zan zo na yi masa sallama idan dai
tafiyar ta tabbata.
Ya ce, 'To Allah Ya kaiku lafiya.
Na zabgawa *yan gida karya na kwashi kayana
dukka na nufi birni na ci gaba da zama da
Umman Lamijo.
Tafiya kamar zata yiwu kamar ba zata yiwu ba,
sai da aka zarce watanni hudu ma, abinka da
gwamnati kuma sai masu hanya. Na takaice
muku ma dai sai tafiya ta fara shiriricewa kamar
an fasa.
Hankalina ya tashi na gigice, ga shi an ce lokacin
karatu ya karato, idan ba mu je akan lokaci ba
sai dai mu bari sai wata shekarar. Na sankare a
kwance ina kuka, ina tunanin yadda zan koma
garinmu na ci gaba da rayuwa. Na rame kai ka
ce
ban taba cin lomar tuwo bakina ba, rama da
koke-koke ma sai sanda MAKWABTANA a nan
Gombe suka sake banka min wata kullalliyar.
'kamar ya ya, a nan Gomben kika yi MAKWABTA
har suka kulla miki kullalliya?
Abdul-Sabur ne ya tambaye ta cike da takaici.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali, sannan ta
zubo da hawaye ta yi sauri ta sa hannunta ta
goge,
ta ci gaba da cewa.
'Ina zaune da Ummar Lamijo lafiya cikin jin dadin
juna ba tsangwama ta lura dai ina cikin damuwa
don idan na zauna sai ta ga na yi tagumi. Cikin
dare idan ta farka sai ta gan ni a zaune,
kwanciya ta gagara sai shesshekar kuka.
Ta dinga yi min nasihohi, ta ce na yi tawakkali na
yi hakuri komai mai wucewa ne. Ta yi ta
shawarta ta na dinga shiga gidan Salame
makwabciyarsu ita ma dai duk sa'armu ce, kawar
Lamijo ce sosai kafin ta yi aure, kullum tana
shiga tana hira, sai na cewa Ummar Lamijo a'a
zan dinga zama a gida ni kadai.
Ita kuwa Salame tun farkon zuwana ta ke ta
nacin na dinga shigowa gidanta idan ta shigo
gidan. Ko ta yi ta aiko *ya*yanta wai na zo zata
yi min wata magana, hankalina ya tashi na suri
gyale a gigice na je, sai na iske daman ba komai
zata fada min ba,
hira kawai ta ke so mu yi. Sai na dan zauna
mata kadan sannan na tashi na shigo gida.
Kamar da hantsi idan mijinta ya tafi aiki yaranta
suka tafi makaranta, Umma ta shiga daki baccin
hantsin da ta saba, da yake ta manyanta tana
shan magungunan ciwuka kala-kala. Sai na dauki
gyalena na shiga gidan Salame mu yi ta hira,
hirar ma ta Lamijo ce kawai don babu wani
wanda muka sani tare, bayan Lamijo. Sai na ga
tana ta bugun cikina tana so ta ji ni budurwa ce
ko bazawara, ni *yar uwarsu ce ko kawa ce, na
kauro Gombe gaba
daya da zama ko zan koma garinmu?
Bana ba ta amsa sosai, don haka ba ta san
komai nawa ba, idan taga kamar bana so sai ta
canza hira,
mu koma hirar makaranta.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login