Showing 21001 words to 24000 words out of 130520 words

Chapter 8 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8028

she shine alakalin daya raba
gadon. Aka daukomin takardun da aka yi rabon
gadon.
Ga sunayen magada nan, amma babu sunana,
sannan ga dumbin dukiyar da ya bari, shagunan
kasuwa, filaye da tireloli, amma babu nawa duk
an
rabe musu. Wanda da ace an raba da ni da na yi
sallama da talauci. Baffa Adamu ya dube ni
fuskarsa cike da nadama.
Ya ce da ni, ''Faduwa ina tsoron ranar da zan
mutu Allah Ya tuhume ni da laifin ban fada miki
gaskiya ba. Saboda ni dai banci gadon ki ba ko
sisi. Allah ba zai tuhume ni da wannan ba, amma
zai tuhume ni
da nasan komai na boye miki. Na yi ta kuka na ci
gaba da yi musu bayanin halin da nake ciki a can
Egypt ba ni da komai, ba ni da kowa.
Alkali ya ce, ''Shawara biyu zan ba ki, ki zabi
wacce ta fi miki sauki. Ta farko ko kiyi hakuri ki
bar wa Allah cutar da akayi miki, ko kuma ki
nemo kudi ki dauki lauyoyi su tsaya miki ki karbi
hakkinki.
Amma ki sani za a iya shekara goma ana ta
shari'ar nan ba tare da ta kare ba.
Allah ya raba mu da son zucia.
MAKWABTAKA 13
Na tashi na fice don takaici, Baffa l Adamu ya
dawo dani gida babu abin da yake sai ba ni
hakuri yana
neman gafarata. Yana sake ba ne labarin mugun
hali irin na matan babana cewar, karfi da yaji
suka hana mahaifina maganarmu, don da koda
yaushe yana maganar zaije ya dauko Faduwa ta
dawo
wajensa ko ya je ya ganki, ya ba ki wani abu
daga cikin dukiyoyinsa, wanda zan ci gaba da
karatu. Sai
su ce bazai je ba ni me yasa ban taba zuwa ba?
Kuma duk *ya*yan da yake da su sama da ashirin
ba su ishe shi ba sai ya je neman wata.
Dole ya hakura ya janye wannan zance na zuwa
Egypt don ba yadda zai yi.
Na ce da shi, ''Don kansu, kowa ya yi na gari zai
gani. Nawa rayuwar duniyar ta ke ne?
Washegari da sassafe na hada kayana na ce,
tafiya Abuja zan yi, daman ta Abuja na zo. Baffa
Adamu ya hada ni da babban dansa ya kai ni har
Abuja gidan *yarsa Ummul Kursim na zauna na
gama kwanakina don daman wata guda ne
booking din tikitina, na komawa Egypt.
Gidan Ummulkursi ne tamkar aljannar duniya tana
auren Sanata, komai gashinan a wadace kamar
ba a Nigeria nake ba. Ta zazzagaya da ni garin
Abuja na ga gidaje, sai a lokacin nasan ashe
Nigeria tana da kyau da arziki haka. Sai a lokacin
na ji zuciyata ta fara warwarewa daga kuncin da
nake ciki, ta ba ni
hakuri bisa abubuwan da *yan uwana suka yi
min. Ta yi min alkawari idan har zan iya zama a
kasar nan ita kuwa zata yi wa mijinta magana ya
samar min aiki a asibiti mai kyau inda za a biyani
da kyau,
na kama gidan haya nayi zamana har Allah Ya
fito min da miji.
Na yi sha,awar shawarar nan da ta ba ni, amma
na ce mata zan koma Cairo tukunna na sanarwa
dangina, na kuma yi musu sallama.
Kafin na tahi sai da ta kai ni Kaduna wajen daya
*yar uwar tamu, ita take auren Manajan wani
babban banki, kudi kam ba,a magana. Muka
dungumo muka je Kano wajen Hajiya Lami itama
kakarmu daya, ita ma ta kafu a gidan, mijinta
hamshakin dan kasuwa ne, su dukka sun yi min
kyautar kudi da kaya.
Da muka koma Abuja a ranar da zan tafi Sanata
ya yi min yayyafin dallar, har sai da na tsorata
don yawa. Allah Mai jinkan bawanSa, Ya hana ni
a can Ya bude min anan.
Na yi kukan farin ciki, gami da godiya mai dumbin
yawa. Duk da haka Ummul Kursim ba ta barni
haka ba sai da ta ba ni shaddoji da leshina
dinkakku ta ce na dinga sakawa a can, ta kara
bani daloli da
yawa. Lallai ba dukka aka taru aka zama daya
ba, wani mai kirki, wani bashi da kirki, wani mai
kyauta wani marowaci. Wani mai tausayi, wani
kuwa mugu ne,
haka mutanen suke ciki. Suka kaini filin jirgi suka
saka ni a jirgi na taho Cairo.
Da na ba wa dangina labari sai suka yi takaici,
suka tayani da addu ar Allah Ya saka min.
Shawarar Ummul Kursim kuwa tuni suka yi facali
da ita, suka ce bazan koma Nigeria ba, gara na
hakura na yi
zamana a cikinsu.
To ba ni da zabi saboda na sallama rayuwar ma
gaba daya ba ta min dadi. Ina zaune ina canja
dalolina a hankali ina ci, talauci ya daina
nukurkusata.
Na dade ina cikin rufin asiri ina kashe dalolin nan,
amma da suka dauko karewa sai hankalina ya
tashi na tabbatar zan koma gidan jiya na
kashewa zai gagare ni, don haka na koma neman
aiki. A asibitin da na yi aiki na fara zuwa na roke
su, su mayar da ni sai suka ki. Babu ta kan
babban da ban bi ina roko, durkuso har kasa
kuka da hawaye suka cemin sun cike gurbina da
wata, ba su da inda za
su saka ni.
Na bazama gari duk wani asibiti da kuka sani a
Cairo sai da na mika takarduna na neman aiki,
kai har ma wasu asibitoci na wasu jihohin sai da
na tuttuta wasu na je da kaina, wasu na aika ta
internate ko na ba wa wani sako ya kai min.
Amma babu wanda ya kira ni interview, don haka
babu aiki. Ina cikin hali na rashi da wahala da
fargabar neman aiki, sai dai a *yan uwana wanda
ya dubi Allah ya ba ni dan kudi, wasu sai na roka
ko su ba ni ko su hana. Babu irin wulakancin da
bana gani, ga shi ba ni da saurayi ko daya balle
so na ya sa ya tallafe ni ya kwantarmin da
hankali. Ana cikin wannan hali sai na hadu da
Gaddafi, a makarantar lafiya ajinmu daya a
jami,a. Ban yi
mamakin ganinsa ba, don shima likita ne, amma
tunda muka gama karatu ban san inda yake ba.
Yana ganina ya rungume ni cikin farin ciki muka
gaisa. Hakika na ga sauyi a fatarsa da kayan da
yake
sanye a jikinsa, domin tsadaddu ne, kudi ya
zauna masa matuka.
Ya tambaye ni ''ina maigida? Ina yara? Ya kuma
wajen aiki?
Sai ya ga alamar damuwa nan da nan a fuskata,
jikina ya yi sanyi don na rasa amsar da zan ba
shi.
''Faduwa lapia kika sauya nan da nan?
Ya tambaye ni yana kallona cikin yanayin
tuhuma.
Cikin hawaye na amsa masa dukkan tambayar da
ya yi min, amsar ita ce babu. Ba ni da uwa, ba
uba babu dan uwa, babu aiki balle *ya*ya.
'Subhanallah! Subhanallah!! Kalmar da yake
ambato ke nan.
Ya ja hannuna zuwa ga kyakkyawar motarsa
muka zauna, ya roki na share hawayena na yi
masa bayanin matsalolina.
Tunda na fara magana ya fara girgiza kai don
tausayina. Hawaye ya kasa tsayawa a idona, har
na sa shima yana zubarwa.
'Faduwa kwantar da hankalinki, zan taimaka iya
karfina. Kalmar da ya fara fada min kenan har
tasa
na tsagaita da kukan.
Ya fara ba ni labarin yadda rayuwa ta yi masa
kyau. Ya ce, da muka gama karatu sai ya tafi
Malaysia karatu akan likita ya karanci kwarewa
akan fannin tiyata ya zama Sugical Doctor
Consultant.
Yana gama karatu sai ya sami aiki a wani
babban asibiti anan cikin babban birnin Kaula
Lumpur ana
biyansa albashi mai kyau. An bashi gida mai
kyawun gaske, ana cirewa a albashinsa har ya
zama nasa. Ya dawo gida ya yi aure ya tafi da
matarsa suna zaune a can lafiya kalau cikin so da
kaunar juna yanzu yaransu guda biyu mace da
namiji su ma har sunyi nisa a makaranta.
Ya ce washe gari zai koma Malaysia, zai karbi
lambata da photocopy din takardu da E-mail
address dina ya tafi da su, zai fadamin halin da
ake ciki game da neman aiki.
Wai amma na je na fara tuntubar dangina sun
yarda sannan zai zo ya karbi takardun a ranar da
daddare, saboda washegari zai wuce. Na ce, kada
ma ya damu, babu abin da dangina za su ce ko
su yarda ko kada su yarda ni dai zan tafi saboda
yanzu da na rasa babu wanda ya dauki nauyina,
babu wanda ya ke tayani yawon neman
aiki, don haka yanzu na gane zan bi duk wata
hanya wacce rayuwa zata yi min dadi idan dai ba
hanyar sabon Ubangiji ba ce.
Na ba shi adireshin gidanmu da lambar wayata,
na ce don Allah da daddare ya zo ya karba zan
hada
masa su. Ya ce, ba don ma bai gama harhada
takardun da ya zo nema ba da mun tafi ya ga
gidan
a lokacin, na ce masa, ba komai ya zo da
daddaren. Sai na fasa shiga neman aikin na koma
gida na shiga tsara takarduna, yadda suna gani
zasu dauke ni. Na dukufa ina addu,a ina kuka, ina
rokon Allah Ya tabbatar min da tafiyar nan, kuma
Ya sa alkhairi a cikinta.
Har karfe goma na dare banga Gaddafi ba, na yi
ta kiran wayarsa bai amsa ba, sai na shiga zargin
karya ya zukala min, nan da nan murna ta koma
ciki.
Sai na ji wayata tana ruri, ina dubawa na ga
sunansa ne, a guje na amsa.
Ya ce, 'Ga ni a kofar gidanki, ki fito. Na ce, ya
shigo babu damuwa. Bayan ya shigo falona na
dinga jere masa abinci da lemo da na yini ina
shirya masa, don ya ji dadi ni ma ya taimake ni.
Ya ji dadi da ganin abincin nan saboda yunwar da
ta ke addabarsa yini guda bai ci abinci ba, yana
ta
yawon harhado kan takardunsa. Ya ci ya sha ya
mike kafa muka yi ta hira muna kallo talabijin har
karfe daya saura, sai da ya fara gyangyadi ya
tashi ya yi haramar tafiya bayan na zuba masa
takardun da duk ya bukata a ambulan na bashi.
Ya kara ba ni hakuri a bisa bakar rayuwar da
nake ciki. Ya ba ni tabbacin zai taimake ni insha
Allahu.
Allah Sarki, abokina kudi mai yawa ya bani da
lambobin wayarsa ta gida da ta ofis na can
Malaysia. Na yi masa godiaya ya tafi, yana isa
Malaysia ya kira ya fada min ya isa bayan
kwanaki biyu ya sake shaida min cewar ya fara
nema min aiki.
Abu kamar wasa an shafe watanni uku babu aiki,
hankalina ya yi matukar tashi, na dameshi da
waya safe da rana, ina rokonsa ya taimake ni.
Har matarsa ta fara kishi da ni, tana cewa wai na
rabu da mijinta kada na sake kiransa. Duk
bayanin da bayanin da ya yi mata cewar ni
kawarsa ce, karatu muka yi tare, amma ba ta
yarda ba, kasan mata da kishi. Ban damu ba duk
yana daya daga jarrabawa daga Allah.
Daga karshe Gaddafi ya fitomin da sakamakon
karshe cewar ba zan iya samun aiki a Malaysia
ba, sai dai idan zan dawo karatu. Sai dai in zabi
bangare daya na karanta har tsawon shekaru biyu
ina gamawa sai su ba ni aiki ba tare da wani
Cuku-cuku ba.
Na ce masa duk wannan ba matsala ba ce, amma
ina zan sami kudin da zan dawo Malaysia na yi
karatu? Ina zan sami kudin abinci da na hayar
gida?
Gaddafi ya ce min, duk ba matsala ba ce, zai fada
min hanyar da zan bi na sami tallafi daga
Gamnatin tarayya. Ya turomin forms ta internate
duk na cike na yi ta kaiwa. Kafin lokaci ya yi
Gamnati ta yarda zata ba ni tallafin karatu har
sai na gama. Kudin makaranta, abinci, kudin
hayar gida duk sun biya min wadataccen kudi.
Sai da komai ya kankama na shapawa dangina
labari, kadanne suka yarjemin, duk ba su bani
goyon baya ba. Na nuna musu ba neman
shawararsu nake yi ba ina dai yi musu sallama ne
tafiya kamar da kasa inji mai ciwon ido.
Gaddafi ya taimaka min na sami gida, muka je
makaranta ya ya taimaka min nayi registration
ina karantar bangaren mata (Gynea). Sai na tsinci
kaina cikin sabuwar rayuwa a Malaysia tare da
sababbin mutane ba wadanda na sani a da ba.
Na yi kokarin na zubar da bakin cikin da yake
damuna a baya, na nemo farin ciki na sakawa
zuciyata ba don komai ba, sai don kawai na
taimaki kaina duniya da lahira. Na yi hakuri, nayi
tawakalli na yarda Allah Yana sane da ni, duk
yadda Ya tsaro min rayuwata dole haka za a yi.
Na yarda da kaddara, yanzu ina shekara ta biyu a
karatuna, ina gamawa ina da kujerar aikina a
Subang Jaya Hospital idan har na ci jarabawata,
wacce ba na fargabar zan fadi.
Umaimah da Abdul-Sabur sun buga tagumi suna
kallon Faduwa. Tausayinta ya cika musu zuciya,
baiwar Allah sai murmushi ta ke don tawakkali.
Nan da nan sabon tunani ya kutso zuciyar
Umaimah ta tabbatar ashe ba ita kadai ce ta ke
da matsala ba a rayuwa. Sai ta ji Faduwa ta
burgeta ta da mayar da komai ba komai ba ta ci
gaba da rayuwarta cikin kawaye da abokai tana
walwala tamkar ba ta da matsalar rayuwa. Amma
ita sam ta kasa yin hakan.
''ina ma zuciyata ta sami juriya da tawakkali irin
na Faduwa? Umaimah ke fada a zuciyarta.
Faduwa ce ta katse tunaninta data ambaci
sunanta. Ta ce ''Umaimah, kalle ni nan ki gani.
Kinga alamar
damuwa ko fushi a fuskata? To haka kowa ya ke
dannewa ya manta da komai. Shekaruna talatin
da takwas a duniya amma banyi auren fari ba,
nan da *yan shekaru zan shiga layin tsofaffi
wadanda
haihuwa zata dauke musu kuma ban haifi ko
daya ba. Har yanzu Allah Bai kawo min miji ba,
ga shi ina son aure. Ya ya na iya, sai in daina
dariya ko kuma sai na tsani mutanen da babu
ruwansu, su suka
doramin? Allah ne Yake jarraba ni ya ga yaya
zanyi idan Ya doramin masifa. Insha Allah Zai
yaye min ko
ban samuba a duniya Zai yaye min a lahira. Na
yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau.
Sai ta kyalkyale da dariya saboda yadda ta ga
sun tsura mata ido suna kallonta kai kace
talabijin suka saka a gaba.
Su dukka suka yi murmushi, gami da jan doguwar
ajjiyar zuciya. Abdul-Sabur ya ce, ''Ni har na rasa
ma abin da zance da ke, saboda tsabagen
tausayi. Sannu Faduwa, sannu da kokarin hakuri
gami da juriya.
Allah Ya jikan nahaifanki da dan uwanki, ke kuma
Allah Ya warware miki. Wallahi ni dai ina ganinki
amma ban taba tunanin a cikin wannan halin ki
ke cika ba, don ba mu taba zama munyi yi hira
irin hakaba.
Na ga dai alamar dai ba ki da miji, sai na yi
tunanin ko mutuwa ya yi ko rabuwa kuka yi
yaranki na can kasarku.
Faduwa ta girgiza kai ta ce, ''Babu ko daya, haka
nake ni kadai, ba ni da kowa.
Umaimah ta ce, ''Allah Sarki, Allah Ya jikansu, mu
kuma Ya kyautata namu zuwan.
Faduwa ta share hawaye ta ce, ''Ameen, na
gode.''
Su dukka sun kasa cin sandwich din, ruwan
shayin ne suka kukkurba suka ajiye, don tashin
hankalin abubuwan da suke fitowa daga bakin
Faduwa.
Suka dunguma zuwa kan kujerun da suke falon,
suka fara kallon wani film da ake yi a MBC Action
mai suna NIKITA
Faduwa ta dubi Umaimah ta yi murmushi, ta ce,
''Umamah, zan so naji tarihinki. Kina karamarki
me yasa kika shiga damuwa haka? Naga
shekarunki ba suyi nisan da zaki damu ba don ba
ki yi aure ba.
Meye matsalarki?
Yayin da Abdul-Sabur ya ware ido da kunnuwa
yana kallo, yana kuma saurarenta don ya kagu ya
ji ko ita wace ce. Sai kunya ta rufe Umaimah, ta
yi murmushi ta sunkuyar da kai gami da sosa
goshi. Ba ta san ta inda zata fara amsa wannan
tambayoyi da Faduwa ta jero mata ba, tana da
nauyi amsawa sosai.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce, ''Mu da ke
mun zama *yan uwa masu kaunar juna da
tausayawa. Kamar faduwa yaune na farajin
labarinta, na ji na sake shakuwa da ita, kuma
zanyi tattalinta wajen
kula da walwalarta da taimakonta da shawarwari.
To haka musulmai ya kamata su kasance
musamman na MAKWABTA.
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Haka ya ke, ka ba
ni labarinka tukunna sai in bada nawa.
Abdul-Sabur da Faduwa suka kwashe da dariya
ya ce, ''Labarina kike so ki ji kafin ki bani naki?
To ki
gyara zama ki karkade kunnenki kisha labari. Ni
da Faduwa za,a sami wanda rayuwarsa ta fi abin
tausayi. Faduwa da Umaimah suka gyara zama
suka zuba masa na mujiya suna kallo, suka baza
na zomo suna saurarensa, dan sun kagu ya fara
fada.
LABARIN ABDUL-SABUR
Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, sunan mahaifina
Abdul-Rashid, Mahifiyata kuwa Habiba. Mahaifina
mutumin kasar Ghana ne a cikin garin Accra, duk
da asalinsa Bakano ne mahaifansa zama ya kai
su Accra aka haife shi a can. Mahaifiyata
kuwa mutumiyar Kano ce, wani gari da ake kira
Gwarzo.
Kasuwanci tsakanin Accra zuwa Lagos, zuwa
Kano shine sana,ar da mahaifina yake yi, shi da
*yan uwansa da abokansa a dalilin haka ne ya zo
Kano harya hadu da Mahaifiyata. Aka yi rufa-rufa
aka
hada baki da tsohon da ya ke yi musu masauki a
Kano mai suna Malam Barau, ya ce shi ne
mahaifinsa, aka ba shi auren mahaifiyata Habibah
ba tare da danginta sun san gaskiyar magana ba.
Bayan anyi biki suka zauna a unguwar kofar
Nassarawa kusa da gidan Sarki, gida daya suke
zaune da Malam Barau.
Don haka Mahaifiyata ta zaci Malam Barau shi ne
surukinta, wanda ya haifi mijinta, ko kuma yaya
ga mahaifinsa uwa daya uba daya.
Suna zaune zama na girmama juna da martaba
juna, har Allah Ya albarkace su da samun
haihuwa,
aka haifi ni Abdul-Sabur sunana, Malam Barau ya
zaba ya saka min, banci sunan kowa ba.
Shekaruna hudu a duniya aka haifi kanwata aka
saka mata suna Khausar. Ni da Khausar muka
taso cikin kuncin rayuwa, shi kan shi gidan
Malam Barau din dan karami ne, matansa biyu da
*ya*ya kwatsam. A cikin gidan aka yanki daki
daya kacal aka zagaye mana babu kicin sai dai
muyi a kofar daki, ban daki kuwa sai dai mu
dauki buta mu zagaya gidan Malam Barau mu bi
dogon layin shiga bandaki.
Babu maganar makarantar boko ma a nan a zube
muke tare da yaran unguwa, sai dai muna zuwa
makarantar allo safe da yamma.
Mahaifina matafiyi ne, bai cika zama a gida ba
saboda yanayin kasuwancinsa tsakanin kano da
Lagos, zuwa Accra bai daina ba, kuma ya fi
dadewa Accra ashe can ne garinsu, can ya fi
sabawa a can
ya fi zama. Mu sai ya shafe watanni shida baizo
ba.
Kayan abinci ya kare babu kudi, sai mu yi ta
fama, bara ce kawai ba ma yi. Allah Sarki uwa,
Mahaifiyarmu Umma Habiba muke kiranta ta sha
wahala da mu. Saboda tsabar surfe da daka har
zannuwanta yayyagewa suke yi, ba
ma a maganar hannayenta duk sunyi kanta, don
kawai ta ba mu abinci muci.
Allah sarki rayuwa kowa da kalar tasa jarabawan.
Allah ya yayewa kowa kunci na rayuwar sa yasa
mu haye jarabawar rayuwar dunia.
Aameen.
MAKWABTAKA 14
Babu irin sana'ar da ba ta yi ba, har da irin
sana'ar nan da mata suke yi a kasuwar rimi ta
siyar da tsofaffin kayan sakawa. Ba zan manta ba
aka ba ta dillancin wasu kaya atamfofi da leshina
akan ta je ta siyar za a bata lada ashe kayan
sata ne, sai mai kaya ta kama kayanta a wajen
siyarwa da aka bi
diddigi aka gane mahaifiyata ce ta siyar, aka taho
da *yan sanda aka kama ta har gida.
Kwanan Ummana Habiba biyar a daure a ofishin
*yan sanda, hankalina ya yi matukar tashi. Daga
lokacin na kuduri niyyar neman sana'ar yi
kowacce iri ce, idan dai halak ce, don na hana
mahaifiyata irin wannan wahala.
Malam Barau ne ya dinga kai kawo da kyar aka
fito da ita da sharadin sai ta biya mutane
kudinsu, ita kuwa ba ita ba ce ta kashe kudi, lada
aka bata wanda bai kai ya kawo ba. Data yiwa
matar data sato kayan ta bata talla maganar
cewar ta kawo wadannan kudi su mayar, sai ta
ce ita tuni ta kashe kudi.
Tsohuwar fankar mu, tsohon gadon mu mai rumfa
na karfe su muka fitar muka siyar muka biya
bashi muka koma bacci akan tsofaffin tabarmi da
tsummokaan kayanmu., don ko tsohuwar katifa
bamu da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login