Showing 108001 words to 111000 words out of 130520 words
Chapter 37 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
Sabitu haka kawai kamar wata me
aljanu ta tashi ta zuba kaya a jaka ta ce zata
tafi, saboda kawai wadannan masu son nata sun
ce zasu zo da
daddare. Sabitu ya yi ajiyar zuciya saboda ya
sami saukin fargabar da ya shiga, dan har ya fara
tunanin ko
waya aka yi mata gida ba lapia ba.
Ya girgiza kai cike da takaici ya ce "Haba Adda
Umaimah, me yasa ki ke haka ne?
Meye abun tafiya kamar wata wacce za'a kama
ki dole a ce za'a aurar ki, abubuwan da muka zo
yi duk bamu yi ba.
Ta yi sauri ta katse shi ta ce, ''Ni wallahi yanzu
zan tafi sai dai kai ka kara kwana. Abunda na zo
yi na yi
tunda na san takamaimiyar ranar da zan dawo
dan tafiya bautar kasa, sai zuwa gidan su
Babangida shi kuma na hakura daman ina
fargabar zuwa kasancewar karshen sati ne (week
end) ina ga Abdul-Basi yana gari. Daman niyyata
mu bari sai ranar litinin da safe in zamu wuce mu
biya, sannan
ina tunanin yadda za mu yi arangama da
mahaifiyarsa saboda guduna ta ke yi ko a waya
bata so mu hadu saboda kunyar abunda tayi min.
Alhajinsa kuwa bana so mu hadu dan kada ya yi
min magiya in auri dansa ni kuma ba zan iya ba
gashi ina ganin mutuncinsa sosai. Dan haka gara
kawai mu hakura da zuwa gidan, abubuwan dana
siyo musu mu koma da su gida ko in bawa Aisha
takai musu idan ta kai mu tasha tana dawowa da
yake duk hanya daya ce, sai in nuna mata gidan.
Rai a bace Sabitu ya tashi ya debo kayansa ya
karbi jaka a hannun Umaimah ya zuba a ciki ya
fito suka tafi, babu mai walwala a cikin su ukun.
Dan haka gum! Suka yi babu mai yin hira har
suka isa tasha
daidai inda motocin Dukku suke lodi manya da
kanana, Aisha ta ja ta tsaya Umaimah ta juyo ta
dubeta, ta yi dan murmushi.
Ta ce "Yi hakuri kawata, ki yafe min na san na yi
miki ba daidai ba amma ba yin kaina ba ne.
Aisha ta girgiza kai ta ce "Kin ga kamar na damu
ne?
Ba damuwa na yi ba, na fahimce ki kuma zan
taya ki da addu'a duk mai kaunarki zai yi miki
fatan ki sami abunda kikeso.
Umaimah ta gyada kai ta ce "Na gode da kika
fahimce ni, ga sakon su Baban gida idan ba zaki
damu ba ki mika musu idan kika zo giftawa ta
gidan, ai na nuna miki gidan bakin titi zaki gane
ko.
Aisha ta ce "Kawo sakon sai in kai musu ba
damuwa.
Umaimah ta juya bayan mota ta dubi Sabitu ta
ce "Ciro ledar nan ka bata.
Ya mikawa Aisha leda cike da alawowi, biskit da
wasu kananan turarruka na yara masu kamshi
guda hudu.
Aisha ta dunkulo kudi masu yawa ta mikawa
Sabitu shi da Umaimah suka tirje, wai ba za'a
karba ba. Sai da Aisha ta matsa sannan
Umaimah ta ce ya karba. Suka yi mata godiya
suka fito daga mota suka nufi motocin hayar da
suke
lodi, suka zabi karama (Golf) mai kyau suka
shiga. Mutane uku ne ya kamata su zauna a
kujerun baya, Umaimah ta ce a barsu su biyu
zata biya kudin mutum dayan dan kada a matse
su.
Hmmm kudi masu gidan rana Umaimah Bello
Allah Ya yarda, har yanzu dalolin data rago suna
nan dankar tana canjawa a hankali.
Tabbas Dr. Faduwa ta koya mata dubara.
Tunda suka zauna Sabitu ya lura Umaimah kukan
zuci take yi hawaye yana cika mata ido sai ta yi
sauri ta sharce ta shiga damuwa da tunani mai
tsanani. Ya tausaya mata matuka dan bashi da
maganin ciwon da yake damunta daya je ya
nemo mata ko a ina maganin yake.
Ya fada cikin rada "Adda Umaimah, ki daina kuka
maganin damuwarki ita ce addu'a. Ki yawaita
karanta wannan addu'a sau uku yayin da kika
tsinci kanki cikin musiba da bacin rai. Allah zai
yaye miki cikin gaggawa. "Walahaula wala
kuwwata illa billahil aliyyil azim.
Nan da nan Umaimah ta cafki addu'ar tana sake
maimaitawa, cikin ikon Allah basu yi mintina
talatin ba sai ya fuskanci ta fara warwarewa
daga dinbun damuwar da take ciki.
Ya gyara zama ya ce da ita "Me zai hana ki zaba
daya daga cikin wadannan sababbin mutanen ki
aura idan ma ba zaki koma gidan Abdul-Basi ba.
Saboda zamanki a haka babu aure ba zai yiwu ba
kin ga mu ba a birni muke ba in da aka waye, ga
arziki da wadata. Yanzu kamar a gidan su kawar
nan taki Aisha babu wanda zai damu da sai ta yi
aure da wuri saboda ga dakuna ma sun yi masa
yawa har neman wanda zai taya su zama suke,
amma a Ruga kowa zai so ki matsa dan dakuna
sun yi kadan. Da-san-samu ne ma kiyi aure kafin
ki gama bautar kasa sai kiyi a gidan mijinki. Dan
yanzu ko ba a Abuja zaki bautar kasa, a cikin
Gombe za kiyi kuma bazai yiwu ace kullum ki je
Dugge washe gari ki dawo Gombe ba.
Ki zabi wanda Baban Hanif ya zabar miki tunda
na san ba zai zabar miki wanda ya san ba na
gari ba ne, dan
ki dadada masa.
Umaimah ta tsurawa Malam Sabitu ido tana
kallonsa yayin da take jin maganarsa tamkar
dabaibayi yake yi mata tabbas ta san shawara
mai kayau yake bata kuma abinda zai yiwu shi
za'ayi amma lallai ta sami
tawaya a rayuwarta dan zata kasance ta rasa
walwala har abada, dan ta san ba zata taba son
namijin da zata aura ba in dai ba Abdul-Sabur ba
ne.
Ta gyada kai alamar ta gamsu da shawararsa
daga nan babu wanda ya sake yin magana a
cikinsu har suka isa Dukku. Kafin su hau motar
Rigarsu sai da suka shiga kasuwa dan siyo kayan
abinci kamar yadda yanzu ita ta dauki nauyin
ciyar da gaba daya gidan, kuma abinci mai kyau
ga kifi da nama.
Tuwon dawa ko na gero sai dai su Nene suna so
su ci amarmace su auno su surfa su ci, amma
shinkafa
ta dafawa, fara ta yin tuwo, makaroni, taliya, kifin
gwangwani da kayan shayi duk Umaimah ta jifge
a dakin Baffa. Ba ta ma kai dakinta ba kada ace
kanta ta siyowa.
Da suka gama sayayyar kayan abincin sai suka
loda a motar da zata kaisu gida su kadai da
kayansu har kofar gida. Bayan an lode kaya a
dakin Baffa sai ya dinga kwararowa Umaimah
fatan alkhairi da fatan ta gama da duniya lafiya,
hawayen dadi ne ya sirnano daga idanuwan
Umaimah ta durkusa a gabansa ta shaida masa
cewar tafiyarsu bautar kasa saura sati biyu. Ya yi
mata addu'ar
fatan alkhairi ta je a sa'a ta dawo gida a sa'a.
Shima nasihohin da Sabitu ya yi ma ta shima
irinsu ya yi
ma ta cewar ta daure ta fitar da miji ta yi aure
zai fi musu kwanciyar hankali su dukka.
Tabbas ta shiga tsaka mai wuya, domin duka
maneman nata babu wanda ta gani da
idanuwanta a cikin su, babu wanda ta zauna da
shi ta ga yadda halinsa yake balle ta rufe ido ta
zabi daya. Sai ta dukufa ba dare ba rana tana ta
addu'a Allah Ya kawo mata mafita mafi alkhairi a
rayuwarta. Allah Ya bata miji na gari mai sonta
su zauna lafiya. Ta ji a ranta ina ma bata dawo
daga Malaysia ba data yi
zamanta acan ko ma dai bata hadu da Abdul-
Sabur ba tana ganin gidansa daya zauna zata fi
jin dan
sanyi. Idan ta fara tuno irin zaman da suka yi da
Abdul-Sabur a baya sai tayi ta kuka ita kadai, ta
yi
nadamar wulakancin da ta yi masa a baya, ta
jinjinawa hakuri da juriyar da ya yi ya ci gaba da
bin
ta, ta yaba matuka da kyautatawar da yayi mata
a baya da yadda ya jajirce har sai da ya nemo
mata gaba daya danginta da kawayenta ta daina
zama ita kadai. Ya cusa mata ra'ayin kaunar
makwabta
wanda a baya ta kudiri niyyar cusgunawa duk
wani makwabcinta.
Allahu Akbar! Ta duba ta hanga, ta ga babu
namijin da zata samu wanda zai yi mata so da
kulawar da Abdul-Sabur ya yi mata. Sai dai ta yi
aure saboda kawai dan ta raya sunna, ta bi miji
dan Allah ne Ya ce mace ta bi amma ba dan
hankalinta zai kwanta ba.
**
Ranar da sati biyu ta cika ranar lahadi da sassafe
Umaimah ta tashi ta yi wanka daman ta shirya
kayanta a karamar akwati tun jiya. Bayan ta yiwa
Dagaci, danginta da Makwabtanta sallama ta ce
Gwamna yana nemansu a Gombe. Ba ta shaida
musu daga Gombe ma Abuja zasu wuce ba duk
da haka sai da ta ji gulmammaki ana ta yada
zance wai kullum tana hanyar birni, kanta ya
waye bata iya zaman Ruga. Shiyasa ta fi so duk
in da zata je ta tafi da muharraminta Sabitu tana
samun saukin zargin
idan aka ga sun tafi su biyu akan a ga ita kadai
ta ci kwalliya ta tafi birni. Dan ita ko kayan da
take
sakawa a tsakar gida ma masu kyaune da tsada
balle ace na kwalliyarta data ware.
SAI MUN HADU ZUWA GOBE INSHA ALLAH.
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 47
Wani cancadeden leshi Umaimah ta saka baki
mai fulawa koriya, aka dinka mata riga da siket
da dan kwali, ta hada da takalmi mai tsini da
gyale kore da bakar jaka. Sai kamshin turare da
mayukan data shafa ya daki hancin *yan gida da
makwabta daga fitowarta daga daki.
Takaici ya kama Matawata a lokacin da ta jiyo
muryar Umaimah da kaninta suna yiwa *yan
gidansu sallama zasu tafi birni sai bayan sati uku
zasu dawo. Matawata ta tabe baki ta harari
maigidanta Ilah
wanda yake zaune akan abun sallarsa yana
lazinzumi.
Ta ce ga *yar iskan birni can Umaimah za'a tafi
birni yin sana'ar.
A fusace Ilah ya juyo ya dube ta duba irin na
tsana da fusata.
Ya ce " Ba lallai ba ne dan mace ta yi karatu, ta
waye, Allah Ya daukaka ta ganin Gwamna baya yi
mata wahala sai a ce ta zama *yar iska. Wata
macen a Ruga take zaune ba kudi, ba wayewa, ba
illimin arabi babu na boko, da aurenta ma sai ta
yi kwartanci a kama ta da mijin da ba nata ba.
Baki da labari jahilci babban ciwo ne?
Ai mai ilimi yana gudun ya sabawa Allah.
Tabbas Matawata ta san dukka wannan mugayen
halaye ita ya suffanta kuma da ita yake. Yana
rufe bakinsa sai ta yi kukan kura ta shake shi
yana zaune. Dakyar ya yunkura ya tashi zaune,
dambe ya barke. Ya dake ta, ya sake daka san
ransa daman ta ishe shi da rashin mutunci kala-
kala tunda Umaimah ta dawo, yayin da ta dinga
ihu tana
yago fuskarsa da farata. Unguwa gaba daya ta
cika da ihun Matawata, kasancewar sassafe ne
ita kadai ake jiyowa. Hankalin kowa ya tashi
musamman sirikan Matawata da iyayenta da
kuma *ya*yanta da suka dinga tayata da ihun
suma.
Sai hankalin Umaimah ya fi na kowa tashi
musamman data ji akanta aka barke da danbe.
Ta ji kwata-kwata ta washi zaman garin nan, ta
kudiri niyyar idan ta tafi yanzu ba zata dawo ba
har sai ta gama bautar kasarta na tsawon
shekara guda kuma Abuja zata zaba tayi zamanta
acan duk abunda mutane zasu ce su ce.
Kwatsam! Umaimah ta jiyo muryar Ilah ya
furtawa Matawata saki daya, ai da saki uku ma
zai yi aka dafe bakinsa manya suka hana shi.
Bakin Matawata baya shiru bata daina kiran
sunan Umaimah ba tana dirka mata zagi ba, tana
fada tana sake maimaitawa Umaimah karuwa, shi
kuma bai daina bi yana tafka mata duka ba
muddin bata
daina zagar masa abar kaunarsa ba. Babu wanda
bai fito rabiya ba, mata da mazan unguwa harsu
Baffa, Sabitu da su Nene amma
Matawata bata ji nauyinsu ta daina dankarawa
Umaimah zagi ba. Kofar gida ya cika dankar sai
hayaniya ake yi babu wanda yabi bayan
Matawata har iyayenta laifinta ita suka bawa
laifi.
Umaimah ta rushe da kuka ta koma daki ta
zauna ta kudundine a lungu ta rasa me yake yi
mata dadi.
Baffa yana kuka ya shigo dakin Umaimah bayan
da rigima ta lafa, dan an tura Ilah gidansa yayin
da Matawata ma aka turata gidansu.
Ya dubi Umaimah ya ce "Tashi ku tafi kada ki
damu Allah Yana bayan mai gaskiya, shaidar
duniya ita ce ta kiyama, duk wajen nan babu
wanda baiyi miki shaidar arziki ba kowa yasan ita
ce watsattsiya
tunda mijinta ma ya fada kwartuwa ce, ke meye
abin damuwa. Ki daure dai kiyi aure sai ki cire
kage da zargi a zuciyar makiya.
Umaimah ta gyada kai ta ce "Amin Baffa insha
Allahu zanyi aure.
Sabitu ya dora akwatinan kayansu aka, Baffa ya
raka su har kofar gari, suka yi sallama, su dukka
ukun kuka suke yi.
A cikin mota ma Umaimah bata daina kwararar
da hawayen bakin ciki da damuwa ba yayin da
Sabitu bai fasa kwararo mata nasihohi da wa'azi
ba har sai da zuciyarta ta yi sanyi kafin su isa
birni. Sabitu ya ishe ta da Magiya akan ta daure
ta shafa hoda da kwalli a fuskarta dan kada
jama'a su gane ta yi kuka kasancewar
idanuwanta duk sun kumbura sun yi jajawur.
Kafin su sauka daga mota Umaimah ta goge
fuskarta ta shafa hoda da kwalli kamar yanda
dan'uwanta ya bata shawara, suka fito daga
tasha
zuwa bakin titi inda zasu hau tasi zuwa gidan
Gwamnati.
Karfe tara da rabi a kofar gidan gwamna ta yi
musu, yayin da suka iske taro yayi taro kowa ya
hallara,
ga dogayen motoci da zasu kwashe su zuwa
Abuja.
Bayan anyi musu *yan muhimman jawabai
takaitattu sai aka basu umarni su je su shiga
motoci akai su Abuja.
Ana fitowa sai ta ci karo da Baban Hanif a kusa
da shi wani mutum ne dogo baki suna tsaitsaye a
kusa da dogayen bus, ta durkusa ta gaishe su
cikin ladabi. Bayan sun gaisa sai Baban Hanif ya
juya ya dubi abokinsa ya yi murmushi.
Ya ce "Ranka ya dade, gata ma ashe ta iso.
Sai yanzu Umaimah ta gane shine Alh. Nura dan
haka sai ta sadu da mummunar faduwar gaba,
Alh Nura ya yi dariya.
Ya ce "Na gane ta ai, na santa tun a Malaysia ita
ce dai bata waye da ni ba.
Umaimah ya kokari, za'a tafi bautar kasa ko?
To Allah Ya yi jagora.
Ta duka ta ce "Amin na gode.
Sabitu ma ya duka ya gaishe su, sai Baban Hanif
ya tambayi Umaimah "Shima wannan acan ku ka
yi karatun amma ban taba ganin shi ba?
Umaimah ta girgiza kai ta ce, "Bada shi muka je
ba,
kanina ne sunansa Sabitu.
Su dukka suka hada baki "Malam Sabitu ya gari?
Dadi ya rufe Sabitu ya ga manyan mutane suna
gaishe shi, sai ya duka ya ce "Gari lafiya kalau.
Aisha Bingyal ce ta taho a gigice tana neman
Umaimah can ta hangota, ta karaso inda suke
bata kula da wadanda Umaimah take tare ba ta
jawo hannunta. Ta ce "Zo muje tun dazu
Bilyaminu ya zo ya ce in nemo ki.
Umaimah ta ji tamkar ta nutse a kasa dan kunya,
ta fisge hannunta daga hannun Aisha ta fada a
sanyaye.
"Ki bari mu gama gaisawa da Baban Hanif.
Sannan Aisha ta lura da wadanda suke tare nan
da nan ta zube a kasa ta kwashi gaisuwa.
Alh. Nura ya yi gyaran murya ya ce "Zaku tafi
ko?
Gara ku yi sauri ku kama hanya kada ku yi
yamma dan ku samu ku fara 'registration' yau
kuma za ku
yi kwanan 'camp' Umaimah ta durkusa ta yi
musu sallama cike da ladabi Aisha ma haka suka
juya suka fara tafiya Sabitu yana biye da su a
baya sai Alh Nura ya kira
shi zuwa wajen motarsa bandir din kudi ya
zakulo ya mikawa Sabitu *yan dari biya-biyar
sababbi naira dubu hamsin kenan ya ce ya kaiwa
Umaimah shi kuma ya zaro bandir din *yan dari-
dari dubu goma kenan ya ce na sa ne.
Farin ciki ya rufe Sabitu yana ta godiya har suka
rabu. Umaimah ta sami jikin daya daga cikin
dogayen motocin nan ta tsaya ta ki bin Aisha
wajen Bilyaminu duk da magiyar da Aisha take yi
mata bata amince ba. Sai dai Aisha ce ta je ta
kira shi ya iso ga Umaimah ta kirkiro murmushi
ta duka ta gaishe shi sai ta birge shi data
durkusa masa ya tabbatar yarinya ce mai hankali
ba irin *yan matan zamanin nan ba ne masu
rawar kai. Ya shiga yi mata bayanai barkatai
wadanda bata cika gane me yake cewa ba duk da
yaren fulatanci yake magana.
Ta kagu ya gama ya matsa ko zata sami saukin
nauyin da kwakwalwarta ke faman yi mata.
Sabitu ya kara so inda Umaimah take dan ya
dade yana nemanta sai ya yi kasake yana kallon
Bilyaminu tabbas yasan dole Umaimah ta shiga
rigima, dan gaba daya masu sonta manyan
mutane ne babu wanda ya zo da maganar wasa
duk aurenta suke so suyi. Sabitu ya gaishe shi
sannan
ya gabatar masa da kansa duk da ba'a tambaye
shi ba. Sai Alh. Bilyaminu ya saki jiki ya sake
gaisawa da Sabitu. Ya dauko naira dubu ashirin
daga aljihunsa ya mikawa Umaimah sai taki
karba, sai ya mikawa Sabitu ya ce ya rike mata,
ya bawa Sabitu dubu biyar, ya mikawa Aisha
Naira dubu goma.
Suka yi masa godiya ya yi musu fatan Allah ya
kiyaye hanya. Ya ce Umaimah ta daure ta kunna
wayarta zai kira ya ji idan sun isa lafiya, sanna
ya juya ya tafi.
Aisha Bingyal ma ta tafi tayiwa Babanta sallama
dan shi ya kawo ta.
Umaimah da Sabitu ne suka kebe a gefe suna
maganar sirri, ya dauko himilin kudin Alh Nura ya
bata da wanda ya bashi sannan ya dauko kudin
da Alh Bilyaminu ya bayar, da ya hada kudinta
dukka Naira dubu saba'in ne, nasa kuma dubu
goma sha biyar. Umaimah ta saka gefen gyalenta
ta matse hawaye.
Ta ce "Sabitu yaya zanyi da raina? Ina zan kai
wadannan mutane?
Gashi kowa ka karbar masa kudinsa. Sabitu ya
shiga damuwa sosai sai ya hau bata hauri yana
bata shawara cewar komai ta fawwalawa Allah,
Shi zai zabar mata abinda ya fi alkhairi.
Umaimah ta gyada kai yayin da hawaye ya ki
tsayawa daga idanuwanta.
Ta ce "Yaya kake ganin zamu yi tafiyar nan?
Ba yadda za'ayi mu tafi Abuja tare, ko ka bi ni
Abuja ba yadda za'ayi mu zauna waje daya tunda
mu sojoji ne zasu tsaremu a NYSC Camp ba zasu
bari ka shiga ba sannan baka san Abuja ba balle
in ce ka zauna a cikin gari ka jira ni. Kunyar
Aisha nake balle in ce ka zauna a gidansu har mu
je mu dawo sannan kuma bana so ka koma
Dugge su ga an yi sati uku ban dawo ba Sabitu
ya ce "Sai in kama hayar daki anan garin in
zauna har ku dawo tun da ga kudi mun samu da
yawa.
Umaimah ta ce "Kana ganin babu matsala ba
zaka takura ba, ka san garin nan ba zaka bata
ba?
Ya yi dariya ya ce "Adda Umaimah, mu ne fa
garin nan, na san garin nan tun ina yawon
almajiranci.
Ta karbi Naira dubu ashirin ta saka a jakarta. Ta
ce ya rike sauran ya kama daki ya dinga cin
abinci amma ya yi hankali da kudin kada ya
kashe dukka.
Farin ciki ya lullube zuciyar Sabitu ya fada a
bayyane "Na godewa Allah da Ya yi mu ni da ke a
ciki daya, ke alkhairi ce a tare da ni shiyasa Allah
Ya bar min ke. Rayuwata ba irin ta da ba ce, ta
canza yanzu, Ada sai an rage jagwalgwalallan
tuwo sannan a bani yanzu kuwa ki gani dubu
sittin da biyar a hannuna.
Sai ya surnano da wani zazzafan hawaye yayin
dana Umaimah ta fi nasa fitowa.
Ta ce "Idan muka yi sati ukun za'a tura mu
wuraren da zamu shekara muna aiki naji ana
cewa matan za'a dawo da mu cikin Gombe, maza
ne zasu zauna suyi aiki a Abuja. Ka ga zamana a
garin Gombe ma ni kadai matsala ne dan haka
nake so idan na dawo zamu kama gida a garin
nan sai ka auro Aliya Budurwar da kake so ka
dawo birni, sai ku bani daki daya mu zauna tare
har in gama bautar kasar idan ka sami cikakkiyar
sana'a kaga