Showing 63001 words to 66000 words out of 130520 words
Chapter 22 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
ba ya bukatar wani bayaninta. Ta bude gidan
baya ta zauna, ya ja mota suka fara tafiya.
MAKWABTAKA 27
Daga dukkan alamu dalibai da malamai a yau sun
cika da mamaki da suka ga Umaimah tana
magana
da wasu bil'adama har ma da shiga motarsu. Sai
kowa ya yi ta kallon Abdul-Sabur da Faduwa
suna ta yi musu jinjina bisa namijin kokarin da
suka yi har Umaimah ta aminta da su.
Musamman kawayenta *yan Nigeria kuma *yan
garinsu suka
yi tsuru-tsuru suna kallonta suna kallon mutanen
da suke cikin mota, da alama dai sun san ba *yan
uwanta ba ne, amma kuma ga shi ta saba da su.
Abdul-Sabur ya dubi Umaimah, ya ce, ''Karfe
nawa za ki tashi in zo in dauke ki?
Ta girgiza kai, ta ce, ''Kar ka damu, zan dawo da
kaina, ai ba dadewa zan yi ba yau.
Faduwa ta ce, ''To mu zauna ki shiga ki yi lecture
ki fito mu ma sai ki raka mu tamu makarantar da
yamma sai mu dawo tare.
Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce, ''Haba
Aunty Faduwa, ya za'a yi ku zauna ku jira ni
kamar wata Sarki?
Ku je makarantarku. Kada ku jira ni, ni ai ba ni da
nisa, na gode Allah Ya saka muku da alkhairi.
Faduwa da Abdul-Sabur ma suka yi mata fatan
alkhairi, ya ja motarsa suka tafi, yayin da
Umaimah ta juya ta dubi dumbin idanuwan da
suke kallonta.
Ta shiga karanto kula'uzai a zuciyarta don kada
baki ya kamata. Tabbas an saka mata ido a
makarantar nan hakan ya samo asali ne ta
sanadiyyar rashin kula su da ta ke yi, kuma
jama'a da dama suna son shiga harkarta.
*************************
Umaimah ba ta baro gidanta ba sai bayan da ta
idar da sallar magruba. Ta ci sa'a kuwa tana
shigowa
gidan Faduwa ko zama ba ta yi ba, Abdul-Sabur
ma ya shigo, Umaimah ta dube su ta yi
murmushi. Ta ce, ''Ku yi min afuwa na makara
ban zo da yamma ba kamar yadda na yi
alkawarin zan zo, na yi bacci
ne ban tashi ba sai bayan la'asar sosai, shine ya
sa na bari sai da na yi sallar magruba sannan na
shigo.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce ''Ba damuwa,
tunda yamma na zo muke ta jiranki ga shi na
samu na je masallaci na yi sallah nima, na dawo
a dai dai ke ma kin zo.
Ta yi tsuru-tsuru tana jiran abin da zai ce mata,
ta ji shiru bai yi magana ba, Faduwa ce kawai ke
ta zuba kamar bushasshiyar kanya. Labarinta ta
ke ta ba su tun tana firamare yadda ta yi kin ji.
Suka sha dariyarsu har da kyakyatawa.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya
ambaci sunan, sai ta ji wani abu ya tsargo daga
kirjinta don fargaba. Cikin lallausar murya ta
amsa masa gami da tsura masa ido tana son ta ji
abin da yake shirin fada. ''Kina da lambar wayar
*yan gidanku?
Ya tambaye ta.
Nan da nan ta cika da mamakin irin wannan
tambaya da ta fito daga bakinsa.
Sai ta rasa amsar da zata ba shi. Ya lura da
hakan sai ya yi murmushi ya mika hannu kan
teburin da ya ke gabansu ya dauko wani dan
madaidaicin kwali ya hau budewa. Ya zaro wata
tsaleliyar waya kirar
Nokia E5 ya mika mata, ya sake zaro layin waya
ya mika mata, ta karba a sanyaye kuma cike da
mamaki, tambaya ce a cike da bakinta ta gagara
furtawa.
Faduwa ta ce, ''Wayarki ce yayanmu ya siyo
mana iri daya, nima kinga tawa can a caji.
Umaimah ta dubi Abdul-Sabur da sauri shi ma ya
dube ta, sai ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan
murmushi.
Ta ce, ''Na gode Yayanmu, amma ka yi hakuri
bana so in saka ka asara in karbi wayar in ajiye
ta don ba zan yi amfani da ita ba.
Abdul-Sabur ya tsuke fuska, ya ce, ''Ni dai na
baki, idan kin so za ki iya jefarwa a bola.
Daga dukkan alamu Umaimah ba ta ji dadin
wannan kalmar da ta fito daga bakin Abdul-Sabur
ba, nan da nan sai ta ji hawayen takaici ya fara
kwaranya daga idanuwanta.
Faduwa ta zabura ta je ta rike ta tana mai
lallashinta tana ba ta hakuri.
Ta juyo ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka sa ta
kuka fa saboda kalmar da ka fada mata. Kasan
fa ita *yar a lallaba ce.
Ya yi ajiyar zuciya ya daga gira, ya ci gaba da
kallon talabijin bai ce da su komai ba.
Umaimah ta hasala ta ajiye wayar akan tebur ta
zabura ta mike tsaye zata fice, Faduwa ta rike ta
tana ba ta baki. Cikin kuka Umaimah ta ke
magana, ta ce, ''Anti ki kyale ni in tafi gida, shi ya
fi min sauki. Ni bana son waya, bana bukatar in
rike waya a rayuwata.
Faduwa ta ce, 'Duk da haka tunda ya siyo miki
sai ki karba ki yi godiya, bai kamata a gabansa ki
ce ba kya so ba. Yana da dalilinsa da yasa ya ce
ki rike waya. Ki dauka ki sakata a caji ta kwana,
sannan ki saka layinki in an kira ki dauka daman
ba a ce sai kin kira kowa ba.
Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''Ba zan tafi da ita
ba da gaske nake, bana so in rike waya.
A fusace ta warci mukulllin gidanta ta fice,
Faduwa zata bi ta Abdul-Sabur ya dakatar da ita
da hannu
alamar ta tsaya kada ta bi ta. Faduwa ta dawo ta
zauna a sanyaye.
Ta ce, ''Haba Abdul kai da kasan lallabata ake yi
ya zaka yi mata gatse-gatse alhali kasan halinta
baudaddiyar yarinya ce. Ya yi murmushi, ya ce,
''Ina sane na yi mata haka, akwai dalili.
Faduwa ta gyara zama ta tambaya, ''Me ye
dalilin?
Ya yi murmushi ya ce, ''Za ki ji nan gaba.
Faduwa ta ce, ''Koma dai maye dalilinka ka jawo
mana yanzu, tunda ranta ya baci sai mun yi
rabin shekara muna bin kanta kafin ta fara kula
mu. Ai ka fi kowa sanin wahalar da muka sha
kafin ma ta fara amsa gaisuwarmu. Mun samu ta
fara karkatowa kuma ka dagula mana
lamuranmu. Yanzu ga shi
soyayyar da nake shiri ginawa a tsakaninku ka
rusa min.
Ya harare ta, ya ce, ''Waye zai yi soyayyar da
karamar yarinyar da har yanzu ba ta mallaki
hankalin kanta ba? Ni ai ba haka nake ba.
Faduwa ta bude baki don mamaki tana duban
Abdul-Sabur, ta ce, ''Yau kuma da bakinka kake
fadar haka?
Nasan kana sonta. Wai me yake faruwa ne a
tsakaninku, ta yi maka laifi ne?
Abdul-Sabur ya yunkura ya mike ya ce, ''Ki saka
mata wayar a caji ta kwana da safe ki saka mata
layi ki kai mata.
Faduwa ta amsa masa da ''to'' cike da ladabi.
Ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba, ya nufi
gidansa. Da alama dai babu walwala a tattare da
shi yau.
Faduwa ta kamu da mamakin halin fushi da
Abdul-Sabur ya shiga yau wanda ba ta taba gani
ba. Alhali tunda safe suke tare ba ta ga bacin rai
tattare da shi ba, sai yanzu.
Ta aiwatar da abin da ya umarce ta da ta yi. Gari
na wayewa karfe takwas na safe a kofar gidan
Umaimah ta yi mata. Ta danna kararrawa.
Umaimah ta yi mamaki da jin ana danna mata
kofa, amma
mamakin ba shi da yawa tasan dayan biyun, idan
ba Faduwa ba ce, Abdul-Sabur ne, kuma zancen
dai
na waya ne. Daman idanunta biyu tana zaune a
falo tana kallon wani film baccin safe ta gagari
idanunta na daren ma kadan ta yi, ta rasa
dalilinta na shiga wannan damuwa, saboda sun
sami dan sabani da Abdul-Sabur.
Ta tashi da sauri ta je ta bude kofar, tabbas
tunaninta ya zama gaskiya, Faduwa ta gani tsaye
a
bakin kofarta fuskarta cike da murmushi. Ita ma
ta yi mata murmushi gami da yi mata izini ta
shigo.
Suka shiga suka zauna Faduwa ta zaro waya ta
mika mata Umaimah ta langwabar da kai gefe
tana shirin bude shafin wani sabon kukan. Cikin
shesshekar kuka ta ce, ''Bana son na rike waya a
rayuwata shi ne kadai dalilina na kin hada waya.
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Umaimah, kada ki
zama mace mai yawan taurin kai, ma'ana mai
gardama, kasancewarki mace wacce zata yi aure
ta zauna a karkashin wani bai dace ace haka
halinki yake ba. Maza ba sa son mace mai
gardama, musamman Yayana Abdul-Sabur
mutum ne mai
saukin kai, ba ya shiri da mai gardama. Tunda ya
siyo ya baki ya kamata ki karba ki yi godiya.
Yanzu
ma shi ya aiko ni ya ce na kawo miki, ki karba ki
rike ba dadi mayar da hannun kyauta baya.
Umaimah ta mika hannu a hankali ta karba ta
ajiye a gefenta a sanyaye, sannan Faduwa ta ji
dadi a ranta. Faduwa ta zaro wayarta ta kira
lambar
Umaimah nan da nan ta hau ruri. Umaimah ta
tsurawa wayar ido da kallo.
Faduwa ta ce, ''Ita ce lambata, ki yi saving
Umaimah ta gyada kai ba tare da ta ce komai ba.
Faduwa ta mike ta nufi hanyar fita yayin da
Umaimah ta ke yi mata rakiya har bakin kofa.
Faduwa ba ta daina yi mata nasihohi ba, akan ta
cire damuwa, ba a kanta aka fara samun
matsalar rayuwa ba, haka ba a kanta za a kare
ba. Don haka ta saki jikinta ta yi walwalarta ta
saba da sababbin mutanen da ba su santa a baya
ba.
Bayan Faduwa ta tafi Umaimah ta dawo ta zauna
a kusa da wayar ta buga tagumi tana tunani da
sake-
saken yadda zata salwantar da wannan waya
kada ma ta jawo mata matsala da tone-tone.
Don ita ta buya a duniyar da babu wanda ya
santa, ba ta so a tono ta.
Wayarta ce ta hau ruri abinka da rashin sabo, sai
ta daka tsalle ta mike tsaye, ta tsorata tana shirin
ta
zura da gudu. Sannan hankalinta ya kawo kan
wayar ta tuna ashe waya ta yi sam ta manta. Ta
dawo ta zauna tana ajiyar zuciya, yayin da ta
jawo wayar tana ta kallo har ta katse ba ta amsa
ba. Daga
dukkan alamu ta gane lambar irin ta dazu ce, ta
Faduwa ce. Ba ta gama kallon lambar ba aka
sake
kira, ta amsa a sanyaye ta yi mata sallama.
Faduwa ce ke magana cikin walwala, ta ce,
''Yauwa, ita ce lambar tawa na kira in shaida miki
na iso gida lafiya. Kuma ga cajar wayarki a
gidana duk sanda
kike son caji ki zo ki dauka.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''To na gode
Antina,
Allah huta gajiya, Allah Ya bar zumunci.
Suka kashe wayar a tare. Umaimah ta hau
gunguni tana magana ita kadai,
''kawai ta takura min da kira, shiyasa ma suka
hada min wayar dan su hanani sukuni.
*****************
Tunda Umaimah ta ajiye wayar a daki a karkashin
filo fiye da kwanaki uku ba ta sake waiwayarta
ba. Babu irin kiran da Faduwa ba ta yi mata ba
shiru babu amsa, haka idan ta fice zuwa
makaranta tunda safe har yamma likis ba ta
dawowa gida.
Shin darasi ne yake hana ta ta shi da wuri ko
kuwa saboda wayar da aka hada mata ne, ta
zame mata
tamkar dodo a gidan shi yasa take guduwa? Oho!
Abdul-Sabur ya lura da hakan cewar ba ta
dawowa da wuri, tunda aka bata waya don haka
bai taba garajen kiranta ba ma kada ta zaci
manufar hada
wayar ke nan.
Yana tsaye akan barandar gidansa tun daga can
kololuwar nesa ya hango tana dawowa daga
makaranta a yammacin wannan rana. Yana daga
sama ya zuba mata ido yana kallo, tafiya ta ke
kanta a sunkuye a kasa, ba ta kallon kowa, sai
ya shiga mamaki irin wannan hali nata na ko in
kula da mutane.
Kafin ta hau sama sai ya yi saurin barin barandar
don kada ma su hadu. Ya lura a kufele ta ke da
shi
saboda ya yi mata mummunan laifi da ya fitar da
kudinsa ya sai mata waya, kuma ya tilasta mata
ta
karba dole.
Tana shiga dakinta wayarta ta dau ruri karkashin
filo, da farko sai ta razana har da dafe kirji taji
kara a karkashin filonta. Can ta tuna ashe waya
ce, ta mika hannu da sauri ta dauka, ta ga Dr.
Faduwa ce.
Kafin ta amsa waya ta katse, missed call 49 ta
gani duk na Dr. Faduwa har cajin waya ya kusa
karewa.
Sai ta yi tagumi tana tunani, ita kanta ta san ba
ta kyautatawa Faduwa ba, nauyi da kunyarta
suka addabe ta. Faduwa mai kaunarta ce, bai
kamata ta dinga share ta ba tabbas.
Faduwa ce ta ke kira har yanzu, kunya ya hana
ta dauka, don haka ta yanke hukuncin tashi ta
tafi gidan Faduwa a wannan lokaci, wannan ita ce
hanya kadai da Faduwa zata goge wannan abin
da ta saka a rai cewar wulakanci ne ya hana ta
daukar waya.
Ta ci sa'a ta iske Faduwa a gida, tana ganin
Umaimah sai ta yi farin ciki gami da ja mata
kunne ta murde a hankali.
Ta ce, ''Kin cika taurin kunne Umaima, kin jefar
da wayar ko?
Umaimah ta yi murmushi ta fito da wayar daga
aljihun wandonta (jeans) ta nuna mata.
Ta ce, ''Ban yar ba, a gida nake manta ta idan
zanje makaranta.
Faduwa ta kwashe da dariya, ta ce, ''Au wayar ta
ki ma kike mantawa a gida? Lallai a gaishe ki,
tsabar wayar ba ta gabanki ke nan. Anya
Umaimah rayuwa zata yiwu a haka? Ya kamata
ki sauya ra'ayinki. Nawa kike a shekaru, rayuwar
ma yanzu kika fara da har zaki zama haka.
Umaimah ta zauna a sanyaye ta yi ajiyar zuciya,
ta yi tagumi tana duban Faduwa, ita dai ba ta
gajiya da yi mata nasiha. Ta karbi wayar ta
dudduba sai ta kyalkyale ta yi dariya.
Ta ce, ''Ban da ni babu wanda yake yi miki
waya?
Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Babu wanda ya
taba kirana. Faduwa ta ce, ''Abdul-Sabur bai taba
kiranki ba? Ai yana da lambarki tunda shi ya siyo
mana sim card din.
Kafin Faduwa ta rufe bakinta sai taji kaurin
abincin data dora yana shirin kamawa nan da nan
ta arta
da gudu zuwa kicin. Shigarta kicin ke da wuya sai
Abdul-Sabur ya yi sallama gami da daga labulen
kofar falon ya shigo cikin nutsuwa. Nan da nan
Umaimah ta daga kai da sauri ta dubi mai
shigowa,
sannan ta amsa sallamar ita ma cikin nutsuwa.
Sai ta yi sauri ta sunkuyar da kanta kasa don
kunya da nauyin abin da ta yi masa. Kan ka ce
kwabo ta sulalo daga kan kujera ta gaishe shi
cikin harshen Hausa.
Ya fada cike da fara'a ''ta shi ki zauna ba sai kin
sauko daga kan kujera ba in za ki gaishe ni.
Ina Faduwa?
Ta nuna kicin da yatsanta ta fada cikin
girmamawa, ''Tana kicin yanzu ta shiga.
Ya kwallawa Faduwa kira ta fito da sauri tana
mai maraba da zuwan MAKWABCINTA kuma
abokinta.
Su dukka ukun a zaune suke akan kujeru, Faduwa
ce ke ta labari, tunda Umaimah ta sunkuyar da
kanta kasa ta tattakure ba ta sake dagowa ta
dube su ba.
Wayar Umaimah akan tebur (center table) ta fara
ruri, ma'ana tana nunawa caji ya kusa karewa
wato (battery low), su dukka ukun suka kalli
junansu.
Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Ga cajarki can a
wajen soket, ki saka wayar a caji ga ta nan har
zata mutu kamar a kasarmu Nigeria inda ake
rashin wuta har caji ya kare waya ta mutu.
Daga Abdul-Sabur har Umaimah babu wanda ya
yi magana. Umaimah ta mike a sanyaye ta dauki
wayar, ta je ta saka ta a caji, daga nan ta dubi
kofar fita, ta juyo a hankali ta dube su ta yi dan
murmushi, ta yi musu sallama ta ce zata tafi
gida.
Faduwa ta zabura ta ce, ''Me yasa zaki tafi gida
alhali muna zaune muna hira har an dora mana
abinci ya kusa dahuwa.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Alhamdulillah ai
a koshe nake, ban dade da cin abinci ba. Faduwa
ta yatsune fuska ta ce, 'Ko ba zaki ci abinci ba, ai
sai ki zauna ayi hira in kin je gidan ma ke kadai
ce me za ki yi?
MAKWABTAKA 28
Umaimah ta kara kutsa kai kofar fita, ta ce, ''Ai
ina da ayyukan yi ne a gidan, kuma ina so na yi
karatu.
Faduwa ta juya ta dubi Abdul-Sabur ta ce, ''Ka
taya ni rokonta ta ki zama. Ya dubi Faduwa ya
juya ya dubi Umaimah sai ya juya ya ci gaba da
kallon talabijin bai ce da su
komai ba.
Faduwa ta yi ajiyar zuciya ta tabe baki, ta mike
tsaye kafin ta daga kai har Umaimah ta bace
daga bakin kofar, ba ita babu ko inuwarta.
Faduwa ta wawuro wayar Umaimah da cajar da
sauri ta biyo ta waje tana kwalla kiran sunanta.
Umaimah da Faduwa sun dade a tsaye a bakin lift
suna magana, Faduwa tana nuna rashin kyautawa
da Umaimah ta ke yi wajen rashin sakin jiki su
saba har yanzu. Ita kuma Umaimah tana amfani
da wasu hujjojinta wajen kare kanta. Daga karshe
ta karbi wayarta suka yi sallama ta tafi gidanta.
Faduwa ma ta dawo gida, ta iske Abdul-Sabur a
zaune a inda ta bar shi.
Babu yadda Faduwa ba ta yi da Abdul-Sabur ba
akan ya ce wani abu game da al'amarin
Umaimah, ya ki magana. Faduwa ta shiga zulumi
akan wannan sauyin al'amari da yake gudana
tsakanin
Abdul da Umaimah Bello.
Ta fara tambayar kanta, ''Shin Abdul-Sabur ya yi
fushi ne da Umaimah ko kuwa da ni yake fushi ni
da na kawo maganar so ya ji ya tsani daga ni
har Umaimah?
Don Faduwa ta fuskanci baya son maganar
soyayya ballantana maganar aure a rayuwarsa.
Ko kuwa wata *yar aljana ce ta aure shi ya ke
gudun bil'adama?
Allah Shi Ya barwa kansa sani. Ta bi Abdul-
Sabur da kallo a lokacin da ya yi cimak ya mike
har ya fice da alama babu walwala a fuskarsa,
babu annuri sam a tare da shi.
Faduwa ta yi tagumi tana tunani, Umaimah ta
dagulawa yayanta lissafi,
ya fara shiga halin da bata saba ganinshi a ciki
ba. Ita dai a da wasa da dariya suke yi a koda
yaushe
baya fushi. Ta jiyo kauri a kicin, abincinta ya fara
konewa, ta zabura da gudu ta shiga kicin tana
magana ita kadai a lokacin da ta ke kashe wutar.
Ta ce, ''Uhm, ina can ina tunani abincina zai kone
a banza saboda son hada soyayyar da ba mai
yiwuwa ba. Allah Ya yi mana jagora Ya zaba
mana abin da ya fi alkhairi. ***************
********
Abdul-Sabur ne ya fito daga get din gidansu cikin
tsaleliyar motarsa da sanyin safiyar laraba da
alama dai sauri yake zai tafi makaranta. Dai-dai
lokacin Umaimah ma ta fito kamar ta ci da kai
don sauri. Ita
ma rataye da jakar na'ura mai kwakwalwa a
kafada (laptop).
Tana hada ido da shi sai ta yi turus da alama ta
dan razana, taso a ce akwai lungu da zata shige
ta buya
da ta labe idan ya tafi sai ta fito. Ya gangara
gefe ya tsaya yana jiranta ta karaso tana tafe
tana sanda
dole dai ta iso gare shi dai-dai saitin tagar da
yake zaune. Sai yayi sauri ya sauke gilashi ya
leko da kai ya dube ta ya yi murmushi, sannan ya
ambaci sunanta.
Ta yi dan murmushi ta duka ta gaishe shi.
Ya ce, ''Ina za ki je ne?
Ta ce, ''Makaranta, ina da jarabawa. Ya gyada
kai, ya ce, ''Af ku ma kun fara jarabawar, ni ma
jarabawar zan yi. Ki shigo in fara sauke ki sai na
wuce.
Ta girgiza kai, ta ce, ''A'a ka tafi kawai zan
karasa ai da sauran awa daya kafin mu shiga har
zan karasa
ma ba a fara ba, kada ka makara. Ya girgiza kai
gami da yunkurawa ya bude mata kofar gaba ya
ce, ''Ki shigo in kai ki ba damuwa ai.
Nauyi, kunya da fargaba ne suka rufto mata a
cikin zuciyarta. Nauyinsa ta ke ji, saboda ba su
saba ba,
ba ta san wacce irin hirar zata yi masa ba, ga shi
daga ita sai shi yau babu Faduwa sarkin hira.
Kunyarsa ta ke ji saboda abubuwan da ta yi
masa a baya da kuma rashin kyautawar da ta yi
masa akan
tsaleliyar wayar da ya fitar da zunzurutun kudinsa
ya saya mata ta ce bata so.
Sannan fargaba ta ke kada jama'ar makarantarsu
su ganta da shi kamar