Showing 9001 words to 12000 words out of 130520 words
Chapter 4 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
Malaysia ce, daya kuwa India ce. Yayin
da Umaimah ta ke sheme akan gado ana mata
karin ruwa, idanuwanta a rufe alama dai baccci ta
ke yi.
Ya karaso jikin gadon ya gaishe su, sannan ya
gabatar da kansa cewar shi makocinta ne,
sannan suka saki ransu don da sun yi masa
kallon rashin fahimta. Ya tambayesu yaya me
jikim? Suka yi ta koro masa bayanin abubuwan
da suka faru da ita a jiya, cewar ciwon cikin ya
tsananta, amma yau da safe ta sami sauki sosai,
har ta sami bacci.
A cikin bayanansu ya gane cewar ma,aikatan
makarantarta ne, sai ya ji hankalinsa ya kwanta
tun
da ga masu kula da ita Allah Ya kawo. Ya je
kanta ya tsaya ya yi ta tofa mata addu,o,i na
neman sauki, afuwa, rangwame daga Rabbul-
Samawati.
Ya ce da su, ''Idan ta tashi a ce Abdul-Sabur
yana yi mata sannu.
Ya yi musu sallama ya tafi sai yanzu yaji
hankalinsa ya kwanta, da ya ga jikin da sauki. Da
yammacin ranar Dr. Faduwa zata tafi unguwa ta
biyo ta gidansa ta iske shi a zaune a falo ya yi
tagumi. Kallo daya ta yi masa ta san bayajin
dadin rayuwarsa. Ta sami kujera ta zauna ta
gaishe shi, sannan ta tambaye shi. Shin yana da
labarin halin da marar lafiyar nan ta ke?
Ya amsa mata da, ''eh ta sami sauki sosai, na je
na duba ta ma dazu.
Sai ta yi kasake tana kallonsa, da alama tana so
ta ji yadda suka karke.
Ta tambaya da sauri ''Ta ganka? Kun gaisa?
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''gaskiya bata
ma san na je ba, saboda tana bacci. Dr. Faduwa
ta yi ajiyar zuciya ta ce, ''Barkanka, na
taya ka murna da ba ka sameta idon ta biyu ba.
Ya yi mamaki dajin kalamanta, sai ya tambaya,
''Me yasa kika ce haka?''
Ta tabe baki ta ce, ''Da ba zata amsa maka ba,
saboda yadda nasan tsanar da ta yi mana. Ya
kyalkyale da dariya, ya ce, ''Kai Faduwa, ai abun
bai kai haka ba. Ni dai uzirin da nake bata shine,
na san tana da wani dalilinta na daban, aka
bibiya laifin wasu ne ya shafemu. Ina yi mata
addu'a Allah Ya sa ta gane.
Faduwa ta ce, ''Ai ba don kai ba yarinyar nan ko
zata mutu ba zanje kanta ba. Kai ne dai da naci
ka
kasa rabuwa da ita, na rasa dalili. Koda yake na
fahimce ka, kana son yarinyar nan sosai, kuma
har cikin zuciyarka.
Abdul-Sabur ya gyra zama ya zazzare ido don
mamaki, sai ya girgiza kai. Ya ce, ''Babu ko daya,
da za ki yarda da ni yi miki rantsuwa, wallahi
babu maganar so a tsakanina da wannan
yarinyar. Haba Faduwa kamar ba ki san
halina ba, shekararmu biyu da ke agidan nan, ya
kamata ki fahimce ni ki kuma fahimci irin macen
da
take burge ni. Na daya, kin sanni da son macen
da ta mallaki hankalinta, ta san rayuwar duniya
sosai, ba *yan matan nan da suke rawar kai ba,
wai su *yan boko. Umaimah yarinya ce karama
ba sa,ar soyayyata ba ce.
Na biyu halayenta kwata-kwata ba su yi min ba
don ba ta da tarbiyya, fitsararriya ce, ba ta burge
ni ba don ina son mace mai kunya da sanin
darajar na gaba da ita.
Na uku, musulma ce amma ba ta da ilimin
aiwatar da addinin don ba ta bin abin da Allah ya
ce, ba ta
kyautatawa makwabtanta ba, bata bayar da
hakkin MAKWABTAKA. Inajin tausayinta ne kawai
kasancewarta mace,
kuma yarinya karama a kasar da babu iyayenta,
ba dangi ba kawayenta. Ina so na nusantar da ita
tasan hakkin makwabci akan makwabcinsa, ko
don gaba ma tasan yadda zata zauna da
makwabtanta ko bayan ta yi aure. Na dauketa
kamar karamar kanwata mai neman shawarata.
Yanzu da na biye mata shirmen nan da ta ke na
babu ruwanta da mu, da ta yaya za,a yi a san
tana
cikin gidan nan a kwance babu lafiya? Ai ko
mutuwa ta yi ba za,a sani ba, sai dai idan ta
mutun
ta kwana uku ta rube wari ya ishi jama,ar gidan a
balla kofa a ganta. Ina amfanin irin wannan
alhalin
mu dukka musulmai ne?
Faduwa, ina tausayin mace, musamman wacce ba
ta gaban iyayenta, ko hannun mijinta. Duk inda
na ga matashiyar mace sai na ji ina sonta,
saboda ina da kanwa wacce na fi sonta a duniya
fiye da kowa da kuma komai da na mallaka.
Dr. Faduwa ta yi murmushi, ta ce. ''Nasan da
haka Abdul amma fa yarinyar can ba *yar mutunci
ba ce.
Duk inda ka kai ga nuna mata hanyar Allah ba
zata saurare ka ba.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Wanda yake
abu saboda Allah baya cewa ya gaji kuma baya
fushi ya ce ya daina. Ina yi mata addu'ar Allah
Ya ganar da ita, yanzu a matsayinki na likita idan
kika duba
yarinyar nan (psychologycally) za ki ga tana da
matsala a rayuwarta. Zai yiwu an guma mata
wani
abu ne na takaici ta yi hijira ta dawo nan, amma
ya za,ayi ace mace ita kadai ko kawa ba ta yi,
balle saurayi ko miji, kuma ko wayar hannu ba ta
da ita (handset). Wannan fa abin dubawa ne
Faduwa.
Dr. Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Na lura tana
cikin damuwa, amma duk damuwarta ai ba ta fi ni
ba,
amma na ke daurewa na ke shiga jama,a na ke
gaisawa da kowa lafiya.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ka ji ta, wai
ba ta kai ki ba ni me yiwuwa duk na fi ku
damuwa,
amma nake daurewa. Kowanne mutum da kika
gani a duniyar nan yana da tasa matsalar, kuma
tasa kadai ya sani, sai ya yi ta ganin kamar ya fi
kowa matsala.
Dr. Faduwa ta ce, ''Haka ne, Allah Ya yaye mana.
Zo ka raka ni 'KL Sentral zan je na ga wata
kawata ta haihu.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri
wallahi bazan iya zuwa ba. Bana jin dadi saboda
bana iya cin abinci, ba na bacci kwana biyu ke
nan.
Dr. Faduwa ta mike tsaye ta yi dariya, ta ce,
''Lallai kai kafi kowa ma tausayi, akan ciwon
yarinyar ne
ka kasa bacci da cin abinci? Ai kuwa gara ma ka
cire ciwon nan a ranka, kaci gaba da harkokinka
idan dai wannan ce ina nan da kai tana warkewa
zata ce ba ta san mu ba.
Abdul ya yi dariya ya ce, ''Ke ma na ga alama kin
kasa fahimta ta, amma ina fatan ki fahimce ni
nan
gana.
Faduwa ta fice ba tare da ta sake cewa komai ba,
ta bar Abdul-Sabur a nan a zaune yana tunani.
Bayan kwanaki hudu, sannan aka sallamo
Umaimah daga asibiti, sai da matan nan biyu
suka raka ta har cikin falonta. Bayan sun roke ta
ta dawo gidansu ta zauna har jikinta ya yi kwari
saboda ba dadi zaman ita kadai ta ki amincewa,
ta ce su barta zata iya zama ita kadai. Suka ba
ta magunguna suka fita suka tafi a motar da
suka zo. Fitarsu da kamar mintina goma,
Umaimah na zaune har yanzu akan kujera tana
tunanin tashi ta rufe kofa sannan ta shiga ta yi
wanka, sai taji ana danna kararrawa a bakin
kofar gidanta. Ta yi mamaki marar misaltuwa, ta
taso da sauri ta daga labule don kofar a bude ta
ke.
Abdul-Sabur ta gani cikin kyakykyawar shigarsa
ta wando baki (jeans) da riga fara (Shirt).
Kamshin nan nasa na turaren (Dolce Gabbana)
shi ne ya daki
hancinta, kamshin nan ba karamin tuno mata
baya ya yi ba. Ta yi mamak da jin yau ya ambaci
sunanta
'Umaimah' maimakon 'Maye' da yake kiranta a
baya.
Sai ta ji saukin tsanar da tayi masa a baya. Ba ta
amsa masa ba, ta ci gaba da sauraron abin da
zai ce
don ta matsu ya fada ya wuce, ba ta kaunar ya
dade a bakin kofarta.
Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Ya ya jikinki? Ina
fatan kin sami sauki sosai? Allah Ya baki lafiya.
Ta saki labulen ta labe ba tare da ta amsa masa
ba.
Ya ci gaba da jiran amsar da zata ba shi, ya ji ta
yi shuru. Sai ya gyara tsayuwa. Ya ce, ''Umaima,
ba na binki da wata manufa illa alkhairi. Manzon
Allah (S.A.W) ya ce, kada ka
kwana ka koshi makocinka ya kwanta da yunwa.
Haka ka dubashi idan bashi da lafiya. Idan har
makwabci bai amince da makwabcinsa ba yana
gudun zai cuce shi ta hanyar fada masa bakar
magana, zagi ko duka, ko kuma neman halaka
shi, to wannan makwabci ba shi da rabo a lahira.
A kwai kissar wata mata da ta rasu bayan kuma
an shaide ta da yawan sallah, azumi, kyauta
sadaka.
Amma aka ganta a wuta. Da Annabi (S.A.W) Ya
binciki abubuwan da ta aikata a rayuwarta ta
duniya sai aka shaide ta ta cika komai banda abu
daya, shine ba ta kyautatawa makwabtanta. Tana
musguna musu, ba ta zauna lafiya da su ba,
wannan dalili shi kadai ne ya kaita wuta
(Wa'iyazubillah).
Don haka ya ke kanwata Umaimah ki yi hakuri ki
zauna da MAKWABTANKI lafiya, ki ba ni ba ko
don nan gaba. Na barki lafiya, duba ki na zo yi
ina fatan Allah Ya baki lafiya, bissalam.
Ya juya ya tafi gidansa.
Sai ya wuce ya bar ta a nane da jikin labule ta
kasa motsawa, daga dukkan alamu wa'azin fa ya
shige ta, dan ta tsorata, tabbas ta san gaskiya ya
fada mata tsagwaronta. Amma ba ta jin zata iya
aiwatar
da nasihohinsa, saboda dalilinta da yawa akan
cuta da musgunawar da MAKWABTANTA suka
dade suna yi mata a doron kasa.
Ta girgiza kai ta fada a bayyane, ''Zam iya
amincewa da kowa a duniya, amma ban da
makwabtana, saboda sun zalunce ni.''
UHM to ai da sauki tunda ni ba makwabci bane,
da fatan zaki aminta dani Umaimah...
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 8
Ta jawo kofarta a fusace ta datse, yayin da ta
hau faman huci, ranta ya duguzuma ya baci. Ta
tabbatar
muddin ba ta bi nasihar Abdul-Sabur ba tana
cikin halaka. Duk abin da ya fada gaskiya ya fada
mata, amma kuma ya tuno mata da kasurgumin
bacin ran da ya faru da ita a baya tsakaninta da
MAKWABTA.
Ta dade a zaune a falo tana tunanin yadda aka yi
MAKWABTANTA suka san ba ta da lafiya, sai ta
shiga mamakin yadda ma aka shigo gidan akasan
bata da lafiya alhali kofarta a kulle. Ta tashi a
hankali ta shiga dakin, ta tsaya tana kallon inda
ta kwanta, ta shiga dauki ba dadi da
kwakwalwarta tana kokarin tuno abubuwan da
suka faru da ita kafin ta fara ciwon ciki.
Abin da zata iya tunawa shi ne, ta saka rigar
bacci ta kwanta akan gado, yayin da ta fara jin
ciwon ciki mai tsanani ya turnike ta. Tun tana
juyi harta fado kasa abin da zata iya tunawa
kenan.
Ta tsuguna kasa a hankali ta dauko rigarta a
tsakar daki ta dudduba, sai ta shiga dogon
tunanin yadda
aka yi aka sauya mata rigar jikinta. To yaya ma
aka yi aka san bata da lafiya? Shine abin da yake
damunta. Tabbas ishara ce Allah Ya nuna mata,
saboda mutum dadi ne da shi. Duk in da ka kai
da kin mutane ka kwanta kai ka dai a cikin gida
ka
mutu dole mutane za su bude su dauke gawar,
su bunneka, don haka dole mutum ya yi
mu'amala da mutane. Ta dade a zaune tana
tunani, har da koke-koke, dom ita ma ba haka ta
so ta kasance tare da jama,aba, dole ce ta saka
ta ko ta fito da niyyar gaisawa da jama,a tana
ganinsu sai ranta ya baci ta fasa.
Ta jima a zaune a gefen gado tana kuka, sannan
ta tashi ta shiga wanka. Bayan ta yi wanka ta yi
sallah,
sannan ta lallaba ta shiga kicin don dafa abin da
zata ci, saboda yunwar da ta ke addabarta.
Ciwo ne yake samun mutum a lokaci guda, sauki
kuwa sai a hankali. Babu ciwon cikin dai a yanzu
amma ba ta jin karfin jikinta da dadin bakinta.
Tana kuma shan magungunanta, don haka gaba
daya satin Umaimah ta kasance a gida ba ta fita
makaranta ba. Sai da ta tabbatar ta warware
sosai,
sannan ta shirya ta fito zuwa makaranta, ranar
litinin da safe da misalin karfe tara kenan.
A cikin lift Umaima ta hadu da Dr.Faduwa, mai
hali ba ya fasa halinsa, ba ta yarda ta hada ido
da Dr.Faduwa ba, balle ta yi mata sallama.
Kasancewar su takwas ne a cikin lift din, sai ta
sami lungu ta labe daga bayan Faduwa har suka
iso kasa inda kowa ya firfito.
Jefa kafarsu ke da wuya akan baranda suka yi
kicibus da Abdul-Sabur daga dukkan alamu
Faduwa yake jira. Daga yadda ya ga Umaimah ta
zabura ya san ta yi mamakin ganinsa dai-dai
wannan lokacin, kuma a wannan waje.
''Zo ki wuce''. Inji Abdul-Sabur ya ce da
Umaimah gami da matsawa ya bata hanya. Ta
sunkuyar da kanta kasa ta wuce abinta ba tare
da ta gaishe shi ba kamar yadda ya ke sa ran
samun gaisuwarta ko don wa,azin da yayi mata.
Faduwa ta dube shi ta juya ta dubi Umaimah, ta
girgiza kai ta ce da shi.
''Ka ga abin da nake fada maka ko? Ai mai hali
ba ya fasa halinsa.
Tafiya suke zuwa get din fita, yayin da Umaimah
ke gabansu, sauri kawai ta ke yi, don kada ma ta
jera
da su. Amma duk da haka takan jiwo wasu
abubuwan da suke fada a kanta.
Faduwa fada ta ke yi da karfi kan rashin tarbiyyar
Umaimah, yayin da Abdul-Sabur yake nemar
mata uziri cewar, akwai dalilinta na yin haka kada
tayi saurin yanke mata hukunci.
Umaimah ta tabe baki ta ce a ranta, ''Koma dai
me zaku ce matsalarku ce, ku ta shafa dan ba
kwa gabana, da zaku rabu da ni, da na fi jin dadi.
Ta kara daga kafa tana sauri, ta haye saman
bene a
inda zata haye gada zuwa makarantarta. Daga
nan ba ta waiwayo su ba, bata san inda suka
bulle ba kuma. Tana kyautata zaton tasi suka
tsayar suka shiga.
****************************************
Zangon karatu na karshen 2nd semester ya zo
karshe, har an fara jarabawa a wasu makarantun,
yayin da makarantar su Umaimah har sun yi nisa
da farawa.
Ta yi karatu cikin dare, ta yi da safe, ta yi da
maraice, yayin da ta ji kwakwalwarta ta yi kamar
zata buga don takura. Harta daina fahimtar abin
da ta ke karantawa don haka sai ta harhada ta
rufe. Ta
fito baranda ta tsaya tana kallon titi, motoci da
mutanen da suke giftawa. Iska mai sanyi ta
yamma
ce ta ke fifitawa, ta sake gyra tsayuwarta tana
kallonsu, sai ta ji ta fara washewa daga damuwa
da gajiyar karatu.
Sallama ta ji an yi mata babu bata lokaci ta kalli
inda muryar ta fito, ko ba a fada mata ba ta san
Abdul-
Sabur ne dan daga saitin gidansa muryar ta fito.
Ta dube shi ta ga yana tsaye a barandarsa yana
yi
mata murmushi. Ya yi matukar mamaki da ya ji
ta amsa da ''Wa'alaikassalam.
''Ya ya karatu? Ya yi karfin halin tambayarta.
Wannan karon dai bashi da amsa, don haka ya ja
fatar bakin ya kame, bai sake yi mata magana ba.
A
zatonsa zata koma cikin gida kamar yadda ta
saba idan ta ganshi, sai ya ga ba ta tafi ba,
amma ba ta sake daga ta dube shi ba. Ya dade a
tsaye yana kallonta, sai ya koma ciki ya rabu da
ita. Sai da ta ji ana kiran sallar magaruba ta
koma cikin gida daga nan bai sake ganinta ba, sai
da yammar washegari tana dawowa daga
makaranta da alama dai jarabawa ta je ta zana
ta dawo.
****************************************
A lokacin da gaba daya makarantun jami'o'in
suka gama jarabawa suka yi hutu, dalibai suka
fara yayewa, yayin da Umaimah ta ji a ranta,
daman zata iya tafiya kasarta hutu itama don ta
gaji da zaman kadaici, sai dai kash! Ba zata iya
tafiya ba don ba ta so a san tana raye.
Jifa-jifa ta ke hango Faduwa da Abdul-Sabur da
alama su ma wannan hutun ba zasu tafi gida ba.
Suna nan, don haka sai ta dan ji sanyi a ranata,
ta ji ashe ba ita kadai ba ce wacce zata zauna.
Duk da ba ta tunanin za su dauke mata kewar
komai.
Idan taji kamar zuciyarta zata fashe don tunani,
sai ta shirya ta fita wuraren shan iska, inda zata
ga
jama'a daban-daban da abubuwa masu ban
sha,awa.
Malaysia kasa ce wacce babu abinda suka saka a
gaba irin shakatawa musamman daga yamma
zuwa dare. Idan ka shiga cikin KL inda tulin malls
suke babu abin da zaka dinga jiyowa sai sautin
kida. A gefen tituna kuwa jama,a ne da'ira-da'ira
sun zage abubuwan kallo kamar masu wasa da
maciji, masu kada giraya (giter), masu rufa ido.
Kida kuwa duk kusurwar da ka zo giftawa da irin
sautinsa, kasancewar baki musamman Turawa
suna shigowa sosai don shakatawa.
A yau Umaimah yawon nata ne ya motsa don ba
ta san takamaimai inda zata nufa ba, zaman
gidan ne
ya ishe ta niyyarta tunda yamma idan ta fita sai
dayan dare zata shigo gida. Don kwanaki biyu ta
yi
tana bacci ta gaji da kwanciya. Da ta je sayan
tikitin jirgin kasa sai ta tamabayesu, ina ne tasha
ta karshe
idan aka tafi daga nan? Matar mai sayr da tikiti
ta zayyano mata cewar.
''Yanzu jirgi zai zo daga KL Centaral, ya shigo ta
'Tunsamban Than' ya zo nan 'Maharjalela', sai
ku tafi 'Hangtuah', sai 'Imbi' sannan 'Bukit bin
tang,
Umaimah ta ce, ''Idan ya wuce Bukit bin tang, sai
ya tafi ina?
Matar ta ce, ''Zai tafi 'Raja Chuland', 'Bukit
nenas' 'Dang Wangi', 'Medantuanku', 'Chow kit'
sai ya tsaya a 'Titi Wangsa' sannan ya juyo...''
Umaimah ta yi murmushi, saboda ta ji yawon da
akalla zata kai sha biyun dare a hanya. Sai ta
tambaya nawa ne kudinta daga Maharjalela zuwa
Titi wangsa?
Matar ta ce, ''Riggit goma sha uku''. Ta zaro ta
biya ta wuce, zuciyarta cike da annuri.
Ana ta turmutsitsin shiga jirgi mutumin da ke
gabanta ya yi sa'ar samun kujera ya zauna. Ita
kuwa a tsaye ta ke ta rike karfe. Bayan ya zauna
ya juto ya dubi mutanen da suke tsaye a kansa.
Abdul-Sabur ne sai yayi ido hudu da Umaimah
itama sai yanzu taga fuskarsa, sai ya yi zuruf ya
mike tsaye kai ka ce bawa ne ya ga ubangidansa.
Yayin da ita kuma take kokarin kawar da kai gefe
har da matsawa da da hanya ma cikin mutane
zata
kutsa ta bace masa.
Cikin harshen Turanci yake magana, don haka duk
jama'a na jin abin da yake fada kuma sun zuba
musu ido.
Ya ce, ''Zo ki zauna, ki zauna ga kujera.
Umaimah zo ki zauna.
Har sau uku, don babu yadda zata yi ido ya yi
mata yawa ta lallabo ta zauna cikin sanda kanta
a sunkuye a kasa. Ranta a bace don bata so
hadu da wanda ta sani a yammacin nan, saboda
ta fito da niyyar yawatawa ta ga gari, gari ya
ganta. Ba ta son wani mahaluki ya dame ta
kuma.
Jirgi dai sai tafiya yake yana tsayawa a tasoshisa
daban-daban, ya sauke wasu ya kwashi wasu.
Sai ta ga Abdul-Sabur ba shi da niyyar sauka ta
dago ta dube shi, shima ya dube ta sai ya yi
mata murmushi,
Ya ce, ''Ai ba'a zo Bukit bin tang ba na san a nan
za ki sauka, ni ma haka can zan je.
Ta tabe baki ta sunkuyar da kai kasa cikin rashin
kulawa da zancensa. Ba jimawa aka sanar, 'Bukit
bin tang', ya juyo ya kalle ta, sai ta rataya
jakarta ta yunkura ta tashi, ta bi bayansa su da
dandazon jama,a. Yayin da ta tabbatar ya wuce
gaba, sai ta
noke ta ki fita ta kutsa lungu cikin mutane ta
sami kujera ta yi zamanta a wani bangaren. Ba ta
dago da kanta ba sai da ta tabbatar an rufe jirgi
yadda bazai iya dawowa ba. Ai kuwa ta hango
shi yana ta waiwaye-waiwaye yana nemanta, har
ya so ya ba
ta tausayi, amma kuma taji sakayau kamar an
cire mata kaya da ya sauka.
MAKWABTAKA 9
Duk ta karaci yawonta da bata lokacinta a karfe
goma ta hawo jirgi ta juyo gida. Da suka zo
tashar
'Bukit bin tang' sai suka sauke fasinjoji suka dibi
wasu. Kwatsam sai ta ga Abdul-Sabur ya nufo ta
kai tsaye,
idanuwansa a kanta suke.
A ranta ta ce, ''Ga mayen nan, kamar aljani, duk
inda