Showing 30001 words to 33000 words out of 130520 words
Chapter 11 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
sun daina samun kudin cuta. Da akwai yadda
zasu yi da sun kawar da ni daga doron kasa.
Ganin wannan riba mai yawa da Uncle Hamza ya
yi sai ya sake yarjewa da ni ya fi so na kasance
tare da dukiyarsa. Ya sa na zo muka zauna muka
tattauna abin da za a yi kowa ya ji dadi tsakanin
ni da shi. Ya ce, kada na damu da sai na yi aiki,
duk tafiya daya idan aka saro kaya sai a bari a
siyar sannan a raba gida hudu.
Shi kashi biyu, ma'aikatan kashi daya, ni kashi
daya. Na yi murna da jin haka, don kudin da zan
dinga samu ya fi albashina na watanni shida ma.
Na amince na yi godiya muka ci gaba da yin
haka.
Sai a lokacin da na karbi ribata ta farko na shirya
na taho Accra ganin gida, shekaruna shidda
rabona da gida. Na ga Ummana Fuse ta kara
tsufa yayin da Khausar ta yamutse saboda
wahala, ba ta jin dadin auren,
azzalumin miji ta samu yana yi mata wayo tana
nemowa yana karbewa.
Duk sun yi mamaki da ganina, na girma na yi
kyau,
na yi fari kal, ga wata kasumba da na tara. Ina
isowa na tari sabuwar motar da na auno tun ban
zoba na turo, a ita na ke yawo gidan *yan uwa da
abokai. Sai kallo na ake ana sha'awar ni'imar da
Allah Ya yi min a rayuwa, mahassada suna ta
surutai, babu abin da ba su ce ba. Sane nake yi,
damfara, yankan aljihu da dai sauransu haka suke
cewa. Ban damu ba, don ko sauraron su bana yi.
Uncle Hamza ya yi bakin jini a wajen dangi
makusantansa, wadanda suka fini kusanci da shi.
Wai har ya dauko bare ya saka shi a harkar arziki
su bai dauki *ya*yansu ba. Nan fa kowacce ta
fara
buga masa waya tana balokoko da magiya ita ma
ya turo ya kai danta England.
Dogon turanci yake musu, bayanai ne kawai da
lallashi, a cikin bayanan nasa kuwa ba zai yiwu
ba ne kawai su yi hakuri.
Kaina da kafata na yi ta taimakon dangi
mabukata, suna ta godiya, masu kushewa suna
karba sai dai
idan na tafi su zaga. Na canja fasalin gidan
kakata, na canjawa Kanwata ita ma duk
abubuwan da ta ke da bukata. Na kara mata jari,
na kuma bata hakuri gami da yi mata nasihohi
akan ta yi hakuri ta ci gaba da biyayyar aure. Na
kira mijinta muka gaisa, na yi masa kyauta mai
tsoka, sannan na yi masa wa'azi cikin siyasa
akan ya sani mace kiwo ce Allah Ya ba shi, Allah
zai tambaye shi yadda ya yi da ababan kiwon
nan da aka ba shi a ranar tsayuwa. Ya fahimci
abin da nake nufi, shi ne ya rage sosai zaluncin
da yake yi mata,
daman dai ba su taba haihuwa ba, saukinta
kenan.
Na koma England harka ta sake budewa, na
samu Uncle Hamza yana samu, ina murna yana
murna
haka muka yi da bawan Allah nan har tsawon
shekaru biyar. A lokacin ne hassadar iyalansa ta
fito baro-baro *ya*yansa suka zo har ofishina
suka cakume ni suka fito da ni, wai na bar musu
dukiyar mahaifinsu ya tsufa yanzu zasu ci gaba
da kula da ita.
Babu yadda zai yi a gabansa na harhada na fice
yana hawaye, ina hawaye. Ya san kawai rusa shi
zasu yi, tunda duk *yan shaye-shaye ne su da
uwarsu.
Uncle Hamza ya koma gida ya zauna ya zuba
musu ido sai abin da suka kawo masa yake
karba, sai lokacin ya ga illar auren Ahlul-kitabi,
nasara asarar duniya.
Oho, sunyi ta banza don ni duk ribata da ake ba
ni suna boye a banki, kuma na riga na san hanya
nasan mutanen kamfanin su ma sun san ni.
Da jarin na je na kawo kayan na canja gari na
bude shagona a can. A hankali aka gane ni, nima
na sami masu siya. A hankali na sami ma'aikata
da teloli.
Amma kafin na fara sai da na je na shawarci
Uncle Hamza ya ce ya ba ni izini na yi, ya yi min
fatan alkhairi.
Sai a lokacin na sami nutsuwa nake zuwa Accra
akai-kai, wani zuwa dana yi na iske auren
Khausar dai ya ki yiwuwa, sai da suka rabu ta
dawo gida suka zauna da Ummana Fuse. Na ma
fi jin dadi da aka yi haka, ga shi ba haihuwa suke
yi ba, sai rigima kullum, har dukanta yake yi. Na
ba ta shawara ta koma makaranta ta yi yaki da
jahilci, ta kudi ce ana koyar da kowanne darasi
da Turanci tsabarsa kuma ka sami kwali mai
daraja kamar kowacce sakandire. Ta yarda ta
shiga ta fara daga aji daya na sakandire, don ta
iya aikin firamare.
Ina can dai a Ingila, na sami labarin daga
Khausar cewar ta yi hutun makaranta, sai na yi
musu biza ita da Ummana Fuse, na turo musu
kudi suka sayi tikiti suka zo suka same ni a
Ingila.
Wata guda suka shafe tare da ni ina ta yawatawa
da su, duk wani wajen shakatawa sai da na
kaisu.
Kwanakin su biyu a gidan Uncle Hamza, sannan
suka dawo gidana. To a wannan zuwanne
abokina Shamsu dan Nigeria garinsu Minna, Niger
State banufe ne. Ya ga Khausar kanwata ya ce
yana sonta, shima tare muka yi karatu yana aiki a
Abuja, amma yana zuwa Ingila akai-akai. Sai na
ce, a,a ba zai yuwuba, shi da ya ke saurayi bai yi
auren fari ba, ita kuwa bazawara ce duk da ma
ba ta taba haihuwa ba. Ya girme ni nesa ba kusa
ba, ba yaro ba ne, don alokacin ya yi shekara
arba'in. Ita kuwa ba ta wuce talatin ba.
Ya ce, shi dai yana sonta, zai aureta kuma. Sai
na ga ita ma ta karkata da sonsa. Ban hana ta
ba, na fi kowa farin ciki idan har za a yi auren
saboda nasan Shamsu na san halinsa, yana da
kirki ga rikom
addini. Uwa-uba dan Nigeria ne a can zai zauna
da ita, wanda shi ne ra'ayina daman tuntuni.
Da ta ji na ce Nigeria zamu wuce daga nan ni da
su Khausar, sai ya yi murna don kawai za'ayi ta,
ta kare, ma,ana idan ya biyo mu Nigeria sai ya
kai ta iyayensa su ganta a tsayar da maganar
aure ko ma a daura kawai tunda gani ga Ummana
Fuse, ga dangin mu a can. Mun riga shi iso
Nigeria san nan ya biyo mu daga baya. A waya
ya sanar da ni ya iso Mina, na ba shi adireshin
inda zai same mu. A gwarzo muka sauka, sun
sha mamaki da ganinmu,
don sun zata ma ba ma raye. Tun sanda Baba
Mukhtar ya kai mu ya dawo babu wanda yasan
halin da muke ciki. Sai muka zama tamkar taurari
abin haskawa a kauyen nan. Aka dinga tururuwar
zuwa ganin mu ana kawo mana abinci kala-kala.
Kannena Hassana da Usaina su na fi damuwa da
na gani, Alhamdulillah suna cikin rayuwar rufin
asiri kasancewar mahaifinsu tsayayye ne me
neman na kansa ne. Na siya musu kayan sakawa
da kayan kwalliya kai ka ce lefe ne suma aka
hada musu.
Ummana Fuse ta yi mamaki da ganin yadda
dangin mahaifiyarmu ke da yawa kuma akwai
masu rufin asiri. Har ta bude baki ta yar musu da
magana, ta ce, ''ashe kuna son su amma ku ka
tankada keyarsu Ghana?
Sai kuka yi wuki-wuki, mu ma kunya ta rufe mu,
ni da Khausar. Da Shamsuddin ya ta shi zuwa,
sai ya taho tare da danginsa maza hade da kudin
aurensu, har sadaki.
Sai muka karba aka tsayar da maganar aure.
Bayan wata guda har ya hada lefe mata suka
kawo, aka daura uare gami da *yar kwarya-
kwaryar liyafa.
Muka rakata har katafaren gidanta na Mina.
Bayan danginsa sun gan mu sai muka dungumo
Accra tare da su ango da amarya nan ma aka
gabatar da angon Khausar da dangin Babanmu.
Na sha zagi dai ba adadi saboda na kai Nigeria
dangin uwata sun daura mata aure. Ban damu da
surutansu ba saboda na san ni da kakata ne
kadai muka raine ta babu wanda ya san cinta da
shanta a cikinsu.
Khausar ta yiwa Accra sallama ta biyo mijinta
mai sonta zuwa Abuja, a nan suke da zama din-
din-din.
Yanzu haka *ya*yansu uku, haihuwarta biyu na
farkon tagwayene, mace da namiji Habiba da
Abdul-Sabur, sai na biyu mace ce aka saka mata
sunan Ummana Fuse, wato Usaina.
Nima a Gwarzo na sayi fili na yi mana katafaren
gini inda idan muka je mu dinga sauka a unguwar
iyayen Mahaifiyata.
A Kano kuma a kusa da dangin Malam Barau na
yi gini don a nan na saba duk da ya rasu ina
taimakawa iyalansa a koda yaushe.
WANNAN SHI NE LABARINA.
Umaimah da Faduwa har lumshe ido suke yi
saboda dadin labarin da Abdul-Sabur yake ba su
sun fi jin dadin labarin da aka zo gurin ci gaban
rayuwarsa sai suka ji tamkar almara saboda
komai yana tafiya yadda ya kamata.
Umaimah ta yi murmushi ta dubi Abdul-Sabur ta
ce,
'To a ina ka yi karatun kur'ani, ka sami ilimin
addini haka?
Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce, 'Duk inda na je
kuma ko me nake yi ina samun makarantar
islamiyya na shiga. Kinga da farko daman na
fada muku da girmana na shiga makarantar boko
kinga tun tashina a makarantar allo nake, anan
na koyi baki na iya rubutu a allo na da kaina. Sai
da nayi nisa sosai muka tashi daga Kano muka
koma Gwarzo a can ma na shiga allo ko sanda na
shiga sakandire ta kwana idan anyi hutu ina ci
gaba da zuwa.
Da muka dawo Ghana Ummana Fuse ta saka mu
a islamiyya a nan na koyi Fikhu da Hadisai. Da na
dawo Ingila duk ranar asabar da lahadi muna
zuwa gidan wani Balarabe mutumin Syria ne yana
koyar da mu Kur'ani da Hadidai. Da na fara zuwa
Indonesia sarinn kaya ina zuwa wajen malamai
daban-daban ina neman ilimi, ina samun karuwa
da tasu baiwar. Na yi saukar kur'ani mai tsarki
fiye da sau goma, yanzu haka na haddace shi ina
sake maimaitawa.
Umaimah da Faduwa suka jinjina kai, Faduwa ta
ce kaji dadi, ni ma dai na yi sauka tun ina yarinya
kafin na gama sakandire, daga baya boko ya
hana ni ci gaba. Amma ina da burin ci gaba da
karatun addini a kasar nan idan na nutsu na ga
akwai makarantun matan aure na islamiyya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yana da kyau a nemi ilimin
gaskiya. Ke fa Umaimah ba kya sha'awar shiga
islamiyya?
Ta yi murmushi, ta ce, ''Ina da niyya idan Allah
Ya so zan shiga nima.
''Kin yi nisa ne a kur'ani? Abdul-Sabur ya
tambaye ta cike da zumudi.
Ta yi dariya ta gyada kai ta ce, ''Alhamdulillah, ni
ma dai na sauke kur'ani tun ina matashiyam
bayan na girma na ci gaba da karatun har na fara
hadda. Abdul-sabur ya ji dadi da jin haka, da ya
zaci Umaimah jahila ce da yaga yadda take danne
hakkin MAKWABTAKA.
Ya yi murmushi ya ce, ''Alhamdulillah, mu dukka
mu godewa Allah da Ya ba mu ilimin saninSa.
Allah Ya ba mu ikon yin amfani da shi. Su dukka
suka ce ''Amin.
Faduwa ta gyara zama ta ce, ''Abdul-Sabur ba ka
gama labarinka ba. Ban ji ka yi maganar matarka
da *ya*yanka ba. *Yar ina ka aura, Ghana,
Najeria. Ingila ko *yar Indonesia?
Abdul-Sabur ya kwashe da dariya, ya ce, ''Kai
Faduwa ta yaya za ki jero min wadannan kasashe
Ingila da Indonesia daga zuwa ci-rani sai na hau
yin aure? Ai ba zan yi wannan kuskuren ba, na
auren matar da ta ke wata kasa wacce ba kasata
ba. Ashe zan maimaita kuskuren da iyayena suka
tafka, suka haife mu muka shiga garari a duniya
ba tare da mun san dangin da zamu bi ba, duk a
rarrabe?.
Faduwa ta ce, ''Yar Accra ko Kano ka aura?
Ya sake yin dariya ya girgiza kai, ya ce,, ''Babu
ko daya wallahi.
Faduwa ta harare shi, ta ce, ''Ban fahimce ka ba
kana nufin ba ka taba yin aure ba ne? Ko dai kun
rabu ko ta mutu?
Umaimah ta dube shi ita ma cike da rashin yarda
ta ce, ''Me kake so ka ce mana, ba ka da mata?
Matar da na ganka tare fa a Saudia kuna dawafi
ka dafa ta?
Faduwa ta gyada kai, ta ce, ''Af har ma kin taba
ganinsu ko?
Da har zai boye mana. Ai na san kana da mata,
tunda baka dadewa sai ka je gida ka gan ta
sannan ka dawo. *Ya*yanka nawa?
Har yanzu Abdul-Sabur dariya yake yi musu ya
kasa amsa jerin tambayoyin da suke jeho masa.
Can ya yi ajitar zuciya ya gyara zama ya dube
su, ya ce, ''Babu maganar boye-boye a
tsakaninmu, ku kannena ne tamkar na jinina mun
zama daya. Ban yi aure ba har yanzu balle na
sami *ya*ya, ga shi
kuwa wannan shekarar zan cika shekaru arba'in a
duniya.
Na zama tuzuru nima kamar Faduwa. Su dukka
ukun suka kyalkyale da dariya.
Faduwa ta ce, ''Kai ai namiji ne, kai zaka nemi
aure kuma duk irin wacce ka nema zata so ka
saboda
kana da kudi, kyau da ilimi. Watakila dai zabe
kake yi har yanzu kana ruwan ido.
Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya ya ce, ''Haka
ne, amma dai yadda kike tunani ba haka nake ba.
Ni dai kawai ba ni da ra'ayin auren ne saboda a
tsorace nake da matan, kuma mata suna sona su
yi
ta bibiyata ina zukewa. Tunda nake a rayuwata
ma sau daya na taba yin budurwa wacce na ji ina
sonta
har na taka gidansu da sunan hira, sunanta
Aminat a Ingila muka hadu, asalinta *yar Bauci
ce. Ta so ni sosai, ta so na aure ta na ki saboda
wasu dalilaina.
Yanzu ta yi aurenta har ta hayayyafa a garin
Manchester gidanta ya ke.
Yanzu dai a takaice Allah ne bai kawo lokacin yin
auren ba, da zarar ya zo sai ku ga Allah Ya hada
ni da matar, sai mu yi aure mu hayayyafa. Ko ba
haka bane *yan mata? Umaimah wannan matar
da kika ganni tare da ita a Saudia ba wata ba ce,
kanwata ce Khausar. Tana son zuwa Umra duk
shekara
mijinta kuma ba shi da lokaci koda yaushe to da
naje Najeriya a cikin hutu sai ta ce na yi mata
namijin biza mu je muyi umarar kwana biyar, shi
ne kika gan mu tare. Ita ma haka ta tutsiye ni da
tamabaya wai ina na sanki, ko dai ke budurwata
ce. Sai na fada mata ke makwabciyata ca a
Malaysia,
da farko ta ki yarda amma da nayi mata
rantsuwa sai ta yarda daga baya, don dai ta san
bana yin budurwa.
Su dukka ukun suka yi dariya a lokaci guda.
Abdul-Sabur ya dubi Faduwa ya juya ya dubi
Umaimah, ya ce, ''To *yanmata kunji tarihin
Abdul-
Sabur daga farko har tsakiya, Allah ne kadai Ya
san karshen abin da zai faru. Idan akwai mai
tambaya ta tambaye ni akan abin da ba ta gane
ba, ko wanda na manta ban fada ba.
Suka yi dariya, Umaimah ta girgiza kai, ta ce,
''Babu tambaya, ni dai a nawa bangaren. Allah Ya
jikan wadanda suka rasu, mu kuma Allah Ya
kyautata namu zuwan. Abdul-Sabur ya yi
murmushi, ya ce, ''Amin, na gode kanwata.
Faduwa ta ce, ''Allah Sarki Abdul abokina, dan
uwana, maraya kuma tuzuru. Allah Ya jikan
iyayenmu, Ya bamu abokan zama na gari.
Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya ya ce,
''Faduwa kin cika abin dariya, koda yake addu'a
ce mai kyau. Amin Ya Rabbu''.
Abdul-Sabur ya juya ya dubi Umaimah wacce ta
yunkura tana shirin tashi ta tafi.
Ya ce, ''Kin ji tarihinmu, yanzu kin san mu, kin
san asalinmu. Ko zamu iya saninki ke ma?.
Ta mike tsaye gaba daya tana murmushi, ta ce,
''Eh, za ku san ni, amma sai nan gaba. Yanzu zan
tafi gida, ina da *yan aikace-aikacen da zan yi. Ai
muna tare, komai daren dadewa tunda kun hana
ni tashi
daga gidan nan, za ku san ni.
Faduwa ta jawo hannun Umaimah ta zaunar da
ita,
ta ce, ''Babu inda zaki je, yau a nan zamu yini
har la'asar. Sai kin bamu tarihinki kamar yadda
kika ji namu.''
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce ''A,a kada ki
takuta mata Faduwa, ki bari a hankali wata rana
sai ta bamu.
Faduwa ta ce, ''Wannan yarinyar, lallai ba ka san
halinta ba, yanzu idan ta shige gida ba zamu
kara ganinta ba, ko mun buga ba zata bude ba''.
Suka tuntsire da dariya su dukka, Umamah ta ce,
''Ai da ne, yanzu ba haka ba ne, za ku ganni
mana.
Faduwa ta ce, ''Ni dai ban yarda ba, yanzu nake
so a bani labari na ji. Umaimah ta ce, ''To zan
bayar, amma ki bari na je gida na yi sallar walha
tukunna, sai na dawo. Kina
ganin har goma da rabi ta yi''.
Faduwa ta ce, ''To muje na kai ki ban daki sai ki
yi sallar a nan, ni fa har yanzu tsoronki nake''.
Umaimah ta yi murmushi kawai ba ta ce komai
ba, tana biye da ita har katafaren dakinta a inda
kayataccen ban dakinta yake ciki. Gidajen iri daya
ne har kayan ciki, yadda na Umaimah yake haka
sak na Faduwa ma.
Gida ne mai dauke da dakuna biyu babban daki
da bandakinsa a ciki, sai wani karamin daki,
bandakin kuma a waje (coridor). Kowanne daki da
gado, madubi da durowar kaya da labulaye na
alfarma kalar kore (lemon green),
sai katafaren falo mai dauke da dinning area duk
an zuba kujeru da dinnin table da labulaye koraye.
Kicin ma babu abin da ba'a saka ba, kama daga
injin wanki, gas cooker, firij da duk wani abun da
ake bukata a kiicin kamar tukwane, farantai,
cokula. Kofuna da dai sauransu. Duk kasan gidan
tiles ne launin kore da fari, haka kofofin gidan
farare ne sun kayata.
Faduwa sarkin kwalliya, ta kayata bandakinta da
kyalkyali, komai ruwan hoda ne (pinc color).
Umaimah ta yi sha'awar bandakin nan tas-tas
kamar mutum ya kwanta ya yi bacci. Da ta idar
da
alwallar sai ta fito ta iske Faduwa har ta yi mata
shimfida da sallaya da tsaftataccen hijabi.
Umaimah
ta yi godiya yayin da ta shiga saka hijabi ta fara
haramar yin sallah. Faduwa ta fito daga daki ta
iske Abdul-Sabur ya fito daga daya bandakin ya
dauro alwala shi ma. Ta yi sauri ta shimfida
masa abin sallah a falo ya tayar da ikama.
Faduwa ta yi murmushi ta ce, ''Wato ku dukka
sallar walha ku ke yi ashe, ni kadai ce bana yi?
Gaskiya da sake, na daina yarda kuyi min wayo,
ni ma zan yi wa kaina fada na fara yi.
Tana gama magana ita kadai, har ta shiga kicin a
inda ta bude firij ta dauko dankwaleliyar kaza a
gidan kankara ta shiga wankewa, ta bankare ta
ta zuba mata kayan hadi, yayin da ta turmutsa ta
a cikin oven don gasawa.
Kan ka ce kwabo kamshi mai dadi ya gauraye
gidan, ta fara tururi. Yayin da ta dora shinkafa
fara amma fa irin dahuwarsu ta *yan Egypt. Farar
shinkafa ce ake dafawa kafin ta dahu sai a saka
gishiri, maggi, koren wake (green beans da
peans), karas sannan a yayyafa dan man kuli. Ba
sai an yi
miya ba, sai a ci hade da gashasshiyar kaza.
Kafin su idar su hallara a falo har Faduwa ta fara
jera musu abubuwa akan dinnin table. Kamar
ruwa, lemon (juice) ayaba, lemo, abarba, kayan
shayi da dai saauransu. ''Abincin mai zamu ci
kuma yanzu bayan mun yi karin kumallo?
Umaimah ta tambayi Faduwa a lokacin da ta ke
duban ta tana dariya.
Faduwa ta yi dariya ta ce, ''Abincin hantsi zaku
ci.
Na ga duk ba mu ci abincin ba dazu saboda
tashin hankalin labarina, duk muna kuka, ruwan
shayi kadai muka kukkurba.
Abdul-Sabur ya yi murmushi, ya ce, ''Ruwan
shayi ma ai abinci ne, ni ba don ku bama da ba
zan karya ba, don ni bana yin karin kumallo ma
kwata-kwata.
Ai shi yasa kike ta sake dunkulewa kina yin kiba
kin cika ci. Suka kwashe da dariya su dukka,
Faduwa ta ce ''Au tsiya kakemin a gaban
kanwata? To zan rama''.
Umaimah ta ce, ''Mu je kicin din na taya ki aiki,
ko nima na koyi irin abincinku na Larabawa. Na ji
kamshi sai fitowa yake yi.
Faduwa ta wuce gaba, Umaimah na biye da ita
har kicin a inda Faduwa ta shiga