Showing 36001 words to 39000 words out of 130520 words

Chapter 13 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8016

yi murna da ganinmu, ta yi
mana kyauta ta girma. Ita ma tana son Nasiba
sosai, ta roke ta data auri danta su zauna lafiya
dan babu abinda ta fi so a duniya wanda ya wuce
abunda *ya*yanta su
ke so musamman ma Abdul-Basi, tafi sonsa
gashi ba dan fari ba kuma ba auta ba. Aka zo
muka sha biki a kauyenmu, irin wanda ba a
taba yin irinsa ba. A lokacin an tura shi bautar
kasa a Kaduna, a can aka wuce da amaryar.
Muka je muka ga gida kamar ba a kasar nan ba,
kuma gidan bene ne. Shi ma benen ba mu taba
hawa ba,
ya zama abin kwatance a wajenmu. Amarya tana
son angonta kamar yadda yake matukar sonta,
suka yi zamansu lafiya a can Kaduna.
Sai da ya dade bai kawo ta ba, amma sanda ya
kawo ta sai suka ganta da ciki. A lokacin duka-
duka shekarunta ba su wu ce goma sha hudu ba
a duniya.
****************************
Ni da saurayina Ilah muna ta ci gaba da shakuwa
don a lokacin ba zancen soyayya ba ne. Ta kai ta
kawo duk garin an san shakuwarmu. Ko kiwo ni
nake rako shi ni da kawata Matawata. Wata rana
wasu baki manyan Alarammomi suka zo garinmu
gidan Dagaci suka yi wa'azi suka bada shawara
akan ya kamata a tura yara makarantar allo.
Wato yawon almajiranci don a sami Malamai a
garin, su ma nan gaba su koyar da na bayanmu.
Sun yi gaskiya don gaskiya kam babu ilimi a
garin, haka muke kara zube yara da manyanmu.
'Dirga da dirge' haka ne karatun da ake koya
mana ba Fikhu, ba Tauhid, ba Hadis. Sallah kuwa
duk yadda muka ga dama muke ta dungurawa.
Da Dagaci ya yi yekuwa (sanarwa) aka hada
dattawan gari ya sanar da shawarar wadannan
malamai sai iyayen yara da yawa suka ki yarda,
kalilan ne suka amince.
Mahaifin Ilah ne yayarda zai tura yaransa biyu
kananan wato Ilah da yayansa Sule. Mahaifina ya
yarda zai tura dansa kwaya daya dan karami
Sabitu kanina. Sai wasu kalilan da iyayensu suka
amince. Muka yi ta kuka da zasu tafi yawon
almajirancin nan da tabarma da akwatunan su
aka. Ni abin ma
ya yimin yawa, ga saurayina zai tafi ga dan
karamin kanina da nake so zai tafi ya bar ni. Har
kofar gari
na dinga bin su da gudu ina kuka, Matawata ta
ruko ni, ita ma da Ilah kukan suke yi. Ina ji ina
gani suka tafi suka barni, garin Kaltingo aka kai
Ilah karatu, yayin da Sabitu aka kai shi Numan.
Sauran yara aka kai wasu Mubi, Jalingo da
Adamawa da dai sauransu.
Na dawo bana jin dadin garin a sanadiyyar rashin
Ilah, babu mai siya min Rake, Kifi Mangwaro, in
ci. Babu mai taya ni hira, saboda haka kullum ni
da Matawata ba mu da hira sai tasa, tana
matukar tausayamin, musamman idan ta ga na
zauna ina ta kuka.
Har waka na yi masa da YARENMU na Fulatanci
ina bayyana yadda na yi rashinsa a tare da ni....
Tana zuwa nan ta kyalkyale da dariya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Gaskiya sai kin rera mana
mun ji, don nima din da kika gan ni ina jin
Fulatanci kadan-kadan.
Faduwa ma ta yi dariya ta ce, ''Ki rera mana ko
kadan ne mu ji.
Umaima ta sake tuntsurewa da dariya, ta ce,
''Yau dai kun saka ni a lungu bayan labari har
waka zaku sani na yi? To bari na rera muku
kadan ku ji.
''Baba warnanu
Inna warnanu
Udilli uwartai Sayinde in gartatai
Wure in imirintima
Mi huidi a warti''
Ma'ana
''Baba ka zo
Inna ki zo Ya tafi bai dawo ba
Yaushe zaka dawo?
Ka zo ina jiranka
Na yi mafarki ka dawo.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Allah Sarki
sabo,
dan na san a lokacin ba ki san soyayya ba, don
shekarunki ba su wuce tara ba a duniya zuwa
goma.
Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Haka ne, ban kai
shekaru goma ba a lokacin. Babu yadda
iyayenmu
ba su yi ba a kawo Nasiba gida ta haihu, Abdul-
Basi ya ki yarda ya ce, tana zuwa asibiti awo,
kuma can zata haihu likitoci za su fi kula da ita.
Ai da ta haihu ya sa kaninsa Ja'afar ya zo ya
fada,
ya ce a zabo masu zuwa suna kamar mata goma,
za a aiko da mota a dauke su ana gobe suna.
Mahaifiyarmu ba ta je ba, saboda alkunya *yar
farinta ce, sai dai ta hada duk kayan da ta
tanada kamar su yajin daddawa, rigunan jarirai,
atamfofi masu arha, kwallin jarirai da guru da
layoyi irin namu na Fulani dai da ake daurawa
yara a wuya da hannaye. ( kafin ilimi ya shigo mu
musan babu kyau )
Ta hada su cikin ledoji ta ce akai mata.
Kishiyoyinta ne suka shirya su da sauran matan
dangi da ni muka tafi. Inna zata dawo Nene ce
zata zauna da ita, har sai anyi arba'in a haka aka
shawarta.
Muka je muka iske ta gida cike da mutane, bayan
mai aikinta Talatuwa, ga kanwar baban Abdul-
Basi a gidan tana kula da ita. Dakuna biyu ne
kacal a gidan, sai falo da bandaki daya da kicin.
Saboda taro dole ya koma gidan abokansa yake
kwana.
Nasiba ta saba da MAKWABTANTA masu kirki,
girke-girke kala-kala suke yi mana su kawo
mana.
Gidaje takwas ne a farfajiyar get din, an zagaye
da katanga doguwa. Sama da kasa ne flat guda
hudu
kenan, daga dukkan alamu gidajen haya ne a
unguwar Rimi, Kaduna.
Na tsinci kaina ina walwala a cikin birni, na
harhada labarun abubuwan da na gani a birni zan
ba wa Matawata idan na koma garinmu da Ilah
idan ya zo da sallah, don an ce za su zo sallah.
Sai naga duk mun zama *yan kauye a ranar suna,
saboda kwalliyar *yan birni ba irin tamu ba ce.
Bayan shudiyar atamfa da muka saka irin ta
Fulani da jagira da dige-digen baki dabe-dabe a
fuska, ga
wata damara da na ci duk a dole gayu ne na yi
na kure adaka, ni da iyayen nawa mu dukka, don
ma
Nasiba tana hanamu wani abun da ba karamin
kwaba fuskarmu zamu yi ba da baki..
Suka kwashe da dariya su dukka ukun.
Nima na kashe da daria.. Sai na tuna lokacin da
Mal. Habu Imamu yakai Hannah Makarantar
F.G.G.C Kazaure... Haka itama taci Uban damara
kamar zataje dandali...
Sai kuma Gobe idan Allah yakai mu.
Sai kuma kumin apuwa na rashin jina jiya saka
makon rashin wutan nepa.q
MAKWABTAKA 18
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai gefe muka koma
muna kallon makadan zamani irin nasu na
Kaduna.
Mun dai dauki hotuna wanda idan na gan su
yanzu sai na yi ta dariya, mun yi wani wuki-wuki
kamar ace kulle mu arce. Allah Ya raba mu da
duhun kai da talauci. Amin.
Su Faduwa suka hada baki su dukka suka amsa
mata da, ''Amin''.
Abdul-Sabur ya ce, ''Kinga birni daga dukkan
alamu ya birge ki. Kin yarda kin koma Ruga
kuwa?
Umaimah ta harare shi kadan, ta yi gatsine ta ce,
''Cabdi! Ban koma ba, kamar ka sani zama na na
yi ni da Nene har sai da aka yi arba'in.
''Ya sunan jaririn ko jaririyar da aka haifa?
Umaimah ta ce, ''Namiji ne, sunan Mahaifin
Abdul-Basi aka saka masa Salisu, amma
Babangida ake kiransa.
Da suka yi arba'in Nene ta ce, na shirya za mu
koma gida, sai na ki saboda har na shiga
islamiyya ni da
yaran makwabta. Ga wuta, ruwa, kallon talabijin,
bayan ruwan sanyi na firij da lemuna kala-kala
(juice) da fanka da A,c, ana dauke wuta sai a
tayar da Generator. Abinci mai rai da lafiya kala-
kala,
shinkafa kullum wanda a Ruga sai da sallah
kadai, nama, taliya, makaroni da dai sauransu.
A Central bank Abdul-Basi yake bautar kasa suna
biyansa ba laifi, amma mutum ne mai kokarin
ciyarwa. Sai a lokacin ne ma na fara koyon
Hausa don bayan Fullancin ba ma yin Hausa sai
kadan-kadan.
Nasiba ta ce a bar ni a wajenta, bayan ta yi
shawara da maigidanta ya amince a sallami
Talatuwa mai
aiki, ni na ci gaba da taya ta raino da aikin gida.
Farin ciki ya rufe ni na ci gaba da zamana, Nene
kadai aka mayar Dugge a motar da Baban Abdul-
Basi ya aiko a dauke ta, bayan an hada mata
goma ta arziki, da nata da na iyayenmu...
Faduwa ta ce, ''An daurawa jaririn guru da layun?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Mun daura masa
mana,
Babansa ne ya ciccisge ya zubar ya yi mana
fada, ya ce ba ya so a sake daura masa irin
wannan. Nan birni ne ba sa yin irin wadannan
abubuwan.
Abdul-Sabur ya ce, ''Sai suka saka ki a
makarantar boko?
Umaimah ta ce, ''An saka ni a makarantar boko,
nima da girmana na shiga makaranta ajin *yan
Nursery duk na fi su girma. To ban iya komai ba,
duk sa'annina a aji uku suke na firamare, ban
damu ba ina jin dadin sabuwar makarantata da
kuma sabuwar rayuwata.
Yaya Abdul-Basi ya ga da gaske na kasa koyon
ABCD sai ya dage duk ranar asabar da lahadi da
safe ko a ranakun aiki da daddare yana koyamin
har da duka da bulala idan yaga ina noke-noke
bana so na koya. Dole na tsaya na dinga koyo,
har haushi Nasiba ta ke ji wataran idan ta ga ya
dake ni,
tana ganin ya takurawa rayuwata. Ya kan ce
mana nan gaba za ku san gata nake yi muku ba
zalunci ba ne. Ita ma dai suna nasu karatun idan
ya gama da ni, ita ma dai da kadan ta wuce
ABCD.
Islamiyyar matan aure ya saka ta tana zuwa
ranar asabar da lahadi daga takwas na safe zuwa
karfe
goma sha biyu. Sai na rike mata danta ta je ta
dawo.
Rayuwa ta fara yi mana kyau, can ma a Ruga
wadata ta fara iske su, don kansa da kafarsa
Yaya Abdul-Basi yana kai musu kayan abinci
buhu-buhu, haka ma Babansa da yake mai arziki
ne kuma mai yawan kyauta yana aika musu.
Sai da na shekara ba mu je gida ba, da muka
tashi zuwa sai muka je a gogenmu, lokacin birni
ya fara ratsa jininmu. Sai muka zama abin
sha'awa a wajen *yan garin Dugge, suna addu'ar
dama su ne mu. Na
iske Ilah ya zo gida ganin gida, sai farin ciki ya
lullube mu. Na gan shi ya yi baki ya rame, amma
fa akwai karatu. Ni da dan guntun abin da na
koya zan kureshi, sai na ga ashe ya min nisa
fintinkau. Ya iya rubutawa ya karanta kur'ani, ni
da shi da kawata Matawata ne muke zama muyi
ta ba wa juna labari, kowa ya bada labarin garin
da yake da abubuwan da suka faru. Na ke ta
basu labarin Kaduna da irin hadaddun da nake
tare da su a gida
da makaranta. Na dinga nuna musu yadda ake
rubutun boko, da irin kayan dadin da ake ci a
birni,
ga wuta ga ruwa da kayan more rayuwa.
Matawata ta yi ta bamu labarin dandali da
sababbin wakokin da aka fitar wadanda ba mu
iya ba,
saboda ba ma nan.
Ilah ya ba mu labarin Kaltingo da irin duka, bara
da aikin da suke tika a makarantarsu ta almajirai.
Yana cikin ba mu labari na fashe da kuka saboda
tausayinsa shi da dan kanina Sabitu. Sai shi ma
Ilah ya fara kuka, Matawata tana bamu hakuri.
Na riga shi komawa Kaduna a garin na bar shi,
nan ma sai da muka yi kukan rabuwa ni da Ilah
har da Matawata ma ta sha kuka.
Allah Sarki, sabo turken wawa.
Abdul-Sabur da Faduwa sai jinjina kai suke yi
saboda tausayawa.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''Muka dawo
Kaduna muka ci gaba da rayuwarmu, mu hudu a
gida. Ni da Babangida a dakinmu daya, Nasiba da
mijinta a daki daya.
Bankin Yaya Abdul-Basi ya yi bautar kasa ne
suka rike shi ya fara aiki a wajen, suna biyansa
kuwa albashi mai kyau. Ya sauya mota, ya sauya
mana kayan gida gaba daya (furniture). Da a
risho muke girki ya siyo mana gas cooker ya ga
Nasiba ta sake hankali da wayewa zata iya
amfani da gas don ada tsoro yake ji karta tashi
gobara.
Kowa ya kalli Nasiba da danta ya san suna cikin
jin dadi da kwanciyar hankali, kyakkyawan yaro,
lafiyayye, dan gata mai kama da mahaifiyarsa.
Duk wani abu na sakawa, ci, sha ko na wasanni
irin na yara Yaya Abdul-Basi ya siyowa dansa,
saboda tsananin son da yake yi masa. Haka
Nasiba ita ma
duk wani abu na kwalliya da ya gani a wajen
makwabta ko matan abokansa zai siyo ya kawo
mata. Ni ma haka, duk abin da nake bukata ba ya
kyashi yana siya min...
Abdul-Sabur ya ce, ''Allah Sarki, Allah Ya sakawa
Abdul-Basi da alkhairi.
Umaimah ta yi murmushi, tare da jinjina kai, ta
ce, ''Amin. Nan da nan rayuwa ta sauya mana,
duhu ya
kauce, haske ya zo. Mun sami ilimi a maimakon
jahilci, mun samu rufin asiri a maimakon talauci.
Yaya Abdul-Basi yana farin ciki da ni, saboda ina
kula da dansa sosai, kai ka ce ni na haife shi,
saboda yadda yake sona har fiye da mahaifiyarsa.
Allah dai Ya sakawa wannan mijin yayar tawa da
alkhairi, don ya koyar da ni abubuwa da dama.
Wadanda ko a makaranta ban koya ba. Mutum ne
mai tausayi da kulawa, tattali da sanin darajar
dan
Adam. Idan ya so akwai sakin fuska a yi ta wasa
da dariya, idan ya ki sai ya sha mur don ba ya
son raini, daga ni har matar tasa sai mu nutsu
idan muka ga irin yanayin. Ina gama Nursery sai
kwakwalwata ta bude sai aka cilla ni gaba, daga
aji daya sai na tafi aji uku, daga uku sai na yi
biyar. Gaskiya ne na cancanci a tsallake min aji,
don Yaya Abdul-Basi ya koyar da ni tsaf a gida.
Dai-dai lokacin na fara girma, shekaruna sun kai
goma sha uku a duniya. Haka idan na je garinmu
sai na nutsu na daina baragada, saboda na ga
yadda kowacce mace ta ke kama kanta.
A lokacin Ilah ya dawo gida don ya yi sauka, ya
zama kato har da gemu. Sai muka shiga gaisuwa
ta
mutunci da girmama juna gami da jin kunyar
juna. Sai a lokacin na tabbatar har yanzu Ilah
yana raina bai sauya ba. Ina sonsa matuka, ina
jin dadin hira da shi.
Matawata ta sha mamaki da ta ga har a lokacin
ban daina kula Ilah ba, ta zaci na yi samari a
birni, na
manta da shi, ba ta san a birni ni kwaila ba ce,
duk da ina samun samarin bana kula su Ilah ne
kadai a raina.
Ilah ya zama malam kowa sai ya durkusa yake
gaishe shi, yara da manya da tsofaffi mata da
maza.
Ya bude makarantar Tsangaya, ma'ana
makarantar allo a kofar gidansu shi da *yan
uwansa kolawa ne suke koyar da karatu sosai irin
su Alifun, Ba,un, an daina karatun dadirga da
dirge. Yakan shiga gidajen iyayenmu mata ya
koya musu. Na ji dadi da ganin wannan sauyi a
Rugarmu.
Kanina Sabitu shi bai dawo ba, don bai karasa
sauka ba. Amma an ce ya kusa saukewa, wata
shekarar zai dawo gida. Tunda ya tafi ba mu
hadu ba shekara da shekaru, ko zai zo hutu ni
bana nan.
Idan na zo shi kuma sai ace ya tafi. Ina so na
gan shi don ance ya girma har ya fini girma. Ni
ma dai ina ta yakar jahilcin da ya mamaye
iyayena mata da maza. Ina ta kokarin koya musu
sallah don dai duk tsawon shekarun nan ba sallar
suke yi ba, dungure ne kawai.
Baffana da Yafindo ne kadai suka yarda suke
gyarawa, Inna da Nene ki suka yi suka ce ba ni
da kunya, yaushe aka haife ni da zan koya musu
sallah?
Haihuwa ta tsayawa Nasiba ita da mijinta, sai
suka shiga damuwa suna ta yawo a asibitoci
ganin likita.
Babangida ya girma har ya shiga pree-nusery. Ni
kuma na shiga sakandire mai kyau mai tsada,
Federal Girls college da take unguwar Malali, ina
zuwa ta jeka-ka-dawo. Ina aji biyu na sakandire
na je garinmu Dugge hutu, ni kadai ce ma na je a
lokacin ban da Nasiba.
A lokacin mummunan labari ya zo mana an
kashe samarin garinmu su biyar a hanya gaba
dayansu abokan Ilah ne, har da yayansa daya
Abashe.
Ashe *yan fashi ne duk dare suke fita su tare
hanya da mugayen makamai su kashe su kwace
dukiya.
Ilah ya yi kuka sosai ya razana matuka, yake ba
ni labari bayan an yi sadakar bakwai. Ya ce, sun
sha
cewa ya zo su yi sana'ar da za su sami kudi ya
bar maluntar nan, sai ya ki binsu, bai san me
suke ba,
amma yasan jahilai ne ba abin kirki suke yi ba.
Shi kuwa da darajarsa a gari kowa yana gaishe
shi, malam sama malam kasa ina shi ina biyewa
zauna-gari banza? Ya ce, ko ranar da za a kashe
su ma tare suke kwance su shida a daki daya
suka farka cikin dare suka ce ya zo su je wani
waje, sai ya ki zuwa suka fice suka barshi, sai
gawarsu ya gani da safe.
Allahu Akbar! Allah Ya shiryi zuriyarmu gaba
daya....
Abdul-Sabur da Faduwa sai girgiza kai suke don
babu dadi abin.
Umaimah ta langwabar da kai cikin sanyin murya,
ta ce, ''Sai na ji Ilah ya kara burge ni, na ji na
sake sonsa. Ya tambaye ni yaushe nake so mu yi
aure don mahaifinsa ya ce ya kamata ya fitar da
mata ya yi aure, duk sa'anninsa sun hayayyafa.
Yana gama fada min haka sai na ji kunyarsa ta
lullube ni, na rufe ido na tashi da sauri na shiga
gida. Na ji dadi da jin batunsa, duk da bana son
kauye, amma idan dai zan auri Ilah na yarda na
dawo Ruga mu zauna tare.
Na kira kawata Matawata na bata labarin yadda
muka yi da Ilah na ce ta je ta bashi amsar
tambayar da ya yi min don na kasa fada masa
amsa saboda kunya. Na ce ta ce masa ya tura
Babansa ya je ya sami Baffana su yi maganar na
san Baffana zai kira ni ya tambaye ni ko ina
sonsa. Ni kuma sai na ce eh,
shikenan sai a cire ni daga makaranta mu yi aure.
Matawata ta ce, ''to shikenan, bari in je in same
shi gashi can a tsaye a kofar gidansu.
Ta tafi wajensa ina lungu a labe ina lekensu, a
gabana ta isa wajen Ilah suka kebe suna magana,
daga nesa nake bana jiyo abin da suke fada. Sai
na ga Ilah yana fada yana wurga hannu, sannan
ya juya ya shiga gida a fusace.
Hankalina ya tashi na je da gudu na tambayi
Matawata me ya ce? Sai ta tabe baki ta ce, ''Ya
ce shi ai bai ce zai aure ki ba, bayan kin je birni
samarin birni sun lalata ki me zai yi da saura?
Sai na sankare a tsaye hawaye ya cika min ido,
na daure na shiga gida ba tare da na bari an san
halin
da nake ciki ba, kwana da kwanaki. Kullum
Matawata na gefena tana zuga ni wai na rabu da
Ilah fa dan iska ne, ba malamin kirki ba ne, kawai
yana labewa da guzuma ne yana harbin karsana.
Ko wannan fashin da abokansa suke yi tare suke
zuwa, shi da yake malami ne sai ya tauna layar
zana ya bata. Wani lokacin naki yarda da
maganarta, wani lokaci kuma na yarda dom ina
ganin ma a wanne dalili zata min karya ni da
aminiyata kuma MAKWABCIYATA?
Idan muka hadu da Ilah sai ya harare ni, nima na
rama ya wuce, na wuce alhali muna tsananin son
juna. Sai na ji garin ya fita a raina ma gaba daya,
gara na koma Kaduna. Na shirya na tafi ba tare
da hutu ya kare ba...
Abdul-Sabur ya yi shuru yana kallonta, can ya ce,
''Amma me ta ce masa? Anya kuwa ba hadaku ta
yi ba?
Umaimah ta ce, ''Hadamu ta yi mana, ba abin da
na fada mata ta je ta fada masa ba. Ashe ce
masa ta yi na ce ya fita harka ta, ni yanzu ba
ajinsa ba ce, sai dan boko. Wai na ce me zanyi
da almajiri, gardi mai bara?
Faduwa ta ce, ''Subhanallahi. Ita kuwa a wanne
dalili ta yi miki haka?
Kafin Umaimah ta yi magana, Abdul-Sabur ya ce,
''Hassada don ita ba ta da saurayi?
Umaimah ta runtse ido ta zubo da hawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login