Showing 15001 words to 18000 words out of 130520 words

Chapter 6 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8012

yunkura zata mike gami da yi musu godiya da
sallama, sai Faduwa ta mike ta jawo hannunta ta
zaunar. Ta ce, ''ba zaki tafi ba, sai mun ci abinci
safe (break fast)''
Umaimah ta yi murmushi, ta ce, ''na koshi, na
gode.
Abdul-Sabur da Faduwa suka hada baki. ''A'a sai
kin ci. Yaushe garin ya waye da har kika karya
kumallo?
Faduwa ta shiga kicin da sauri ta jona ruwan zafi
a buta (kettle). Ta jona toaster a inda ta shiga
gasa
musu biredi da wainar kwai, wato (sandwich).
Minti goma sha biyar ya yi yawa komai ya hadu
akan
dinning table. Ta umarce su da su karaso kan
tebur su ci abinci. Umaimah da Aabdul-Sabur da
suka
dade a zaune suna kallom Talabijin ba tare da
dayansu ya sake yin tari ba tun bayan shigan
Faduwa kicin, sai yanzu suka motsa suka karaso
kan dinning table suka zauna inda kowa ya shiga
hada shayi a cikin kofin da yake gabansu.
Faduwa sarkin surutu ta dubi Umaimah ta yi
murmushi, ta ce, ''Allah Sarki *yar yarinya mai
kyau, kina da kyau ga ki fara kamar *yan
kasarmu Misira kamar ba *yan Nigeria ba.
Sai Umaimah da Abdul-Sabur suka kalli juna
suka yi murmushi.
Abdul-Sabur ya ce, ''An ce miki babu farare
kyawawa a Nigeria? *Yan kasarku ne farare
kawai? ''Ina ne garinku a Nigeria? Faduwa ta
tambayi Umaimah.
Yayin da Umaimah ta yi murmushi, ta ce,
''Gombe''.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa ma san ke bafillatana
ce ina ganinki na gane haka.
Mamaki marar misaltuwa ka ke gani a idon
Umaimah, ta ke tambayar kanta da kanta a inda
ya
san Gombe har yasan Fulani ne a garin.
Da ya lura da hakan sai ya dubeta ya yi
murmushi, ya ce, ''Kina mamaki yanda na san
YARENKI ko? To kibar mamaki, mu dukka nan da
kika gani *yan asalin Nigeria ne, kuma Hausa/
Fulani. Umaimah ta daina juya shayin ta zuba
musu ido
tana kallon fuskokin kowannensu. Babu alamar
*yan Nigeria a tattare da su musamman ma
Faduwa. Ta ina za,a hada Faduwa Balarabiya sak
gashinta har tsantsarta mai laushi, farinta tas
babu digon baki a jikinta, hanci har baka irin na
Larabawan asali amma ace mata *yar Nigeria?
Lallai wannan ma so yake ya raina mata hankali.
Har ta ji
ta tsane shi, tana tunanin rusa duk nasihohin da
ya yi mata. Don a zatonta mai tsoron Allah ne a
she
makaryaci ne? Inji zuciyar Umaimah.
Faduwa da Abdul-Sabur sai dariya suke ta yi,
saboda kallon karyatawar da suka ga Umaimah
na yo musu baro-baro.
Faduwa ta tambayi Umaimah, ''Kina mamaki ne?
Ba ki yarda ba ko?
Umaimah ta gyada kai, ta ce ''Eh, ban yarda ba
gaskiya. Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''To
Faduwa kiyi
mata Hausa sai ta yarda.
Nan ma dai Umaimah ta sake zaro ido da taji an
ambaci yarenta na Hausa. Ta sake cika da
mamakin yadda yasan Nigeria har ya san kabilun
kasar.
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Umaimah ni da
ke kasarmu daya, YARENMU daya Hausa/Fulani,
ADDININMU daya musulunci. Da girmana na je
Ghana amma ni dan asalin Nigeria ne. Faduwa
ma *yar Nigeria ce saboda mahaifinta bakar fata
ne,
bahaushe dan asalin garin Sokoto, mahaifiyarta
ce *yar Egypt, amma a wajen mahaifiyarta ta
girma ita ta rike ta, duk da haka ta iya Hausa.
Umaimah ta cika da mamaki, yayin da wasu
guma-guman farin ciki suka dinga dirgowa a
kahon zuciyarta saboda ta ba *yan gidata dafe
haba da hannu tana jinjina kai, fadi ta ke, ''Ikon
Allah, ashe
ku duk *yan Nigeria ne? Abdul-Sabur ya ce,
''Kwarai kuwa, kuma muna yawan zuwa idan ta
kama.
Ta juya ya dubi Faduwa ya yi dariya, ya ce da
ita,
''Bismillah, fara yara mata Hausa don ta yarda,
na ga har yanzu tana kokonto.
Faduwa ta yi dariya ta kurbi shayi, ta du bi
Umaimah har yanzu dai cikin harshen Turanci
suke magana.
Ta ce, ''Kanwata wai da gaske har yanzu kina
kokonto mu ba *yan kasarki ba ne?
Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ta ce,
''gaskiya ina dan tantama. Abdul-Sabur ya furta
kalmar Hausa, ya ce ''Da gaske muke yi, mu
Hausawa ne, har wasu lokutan ni da Faduwa mu
kanyi yaren Hausa, idan muna so mu yi maganar
da ba ma so a ji a cikin mutane.
Umaimah ta sankare a zaune, saboda ta san
ashe ya gama jin duk zagin da ta ke yi masa a
baya. Ashe yana sane yake kiranta da ''MAYE''
ramawa yake yi kenan?
Faduwa ta kaikaice cikin harshen Hausa ta ke
magana, duk da Hausar ba ta fita radau, amma
ana
ganewa tar!
LABARIN FADUWA.
Ta ce, ''Sunana Faduwa, sunan mahaifina Ahmad
Sokoto. Mahaifina bakar fata ne bakikirin kuwa,
dan asalin garin Sokoto ne gaba da baya.
Mahaifiyata mai suna Zainab kuwa *ya asalin
kasar Egypt ce, *yar cikin garin Cairo babban
birnin. Ita
dai ruwa biyu ce, mahaifinta ne dan Egypt,
mahaifiyarta *yar kasar Saudia ce, don haka ina
da *yan uwa a Saudia sosai.
Karatu ya kai mahaifina Egypt, tun yana dan
matashin saurayi shi da kannensa guda biyu
Mansur da Adamu.
Sun dade a Egypt har bayan sun kammala
karatun ba su koma kasarsu ba, suna kasuwanci
harma da aikin gwamnati, kasancewar mahaifinsu
mai arziki ne, yana yawan zuwa Egypt shi ma ya
zauna yana Hada-Hadar kasuwanci. Allah Ya
hada soyayya tsakanin mahaifana, aure ya
kankama a tsakanin fara da baki, duk da surutai
da kyamar abin da dangin mahaifiyata ke nunawa
a sanadiyyar auren nan Zainab kuwa idonta ya
rufe, saboda soyayya ta
ce ta ji ta gani zata aureshi haaka.
Daman a lokacin marainiya ce, a hannun dangin
mahaifinta ta ke, iyayenta duk sun rasu su duka
biyun tun ma tana karamarta. Aure ya tabbata
tsakanin Ahmad da Zainab da sharadin ba zai
koma Nigeria ba, a Cairo zai bar ta.
Zama na rufin asiri, saboda ya na da hali. Allah
Ya albarkace su da samun haihuwa *ya*ya biyu,
yayana Ibrahim da ni Faduwa.
Ina da shekara uku yayana yana da shekaru biyar
kakana ya rasu wanda ya haifi mahaifina, bayan
rasuwarsa ne aka takurawa mahaifina da
kannensa su dawo gida, tun da ba ran mahaifinsu
don su ci gaba da kula da kasuwanci da iyayensu
mata da kananan kannensu mata da maza.
Nan fa rigima sabuwa ta fara don mahaifiyata ta
ce ba zata biyo shi Nigeria ba, danginta kuma
suka ce
ba zai tafi ya bar ta da aurensa ba, sai dai idan
ya sake ta. Yayi-yayi ta yi hakuri su koma
Nigeria ko a
ci gaba da auren yana zuwa yana dawowa, suka
ce bazai yuwu ba, sai dai su rabu.
Dole ya sake ta, sannan aka shiga rigimar daukar
yara, ya ce sai ya tafi da mu, ita kuma ta ce ko
da daya ba zata ba shi ba. Kamar daiza,a tafi
kotu aka samu tsofaffi suka shiga aka yi sulhu,
shi na mijin
aka ba shi, macen aka barni a wajenta, da
sharadin zai dinga kawo Ibrahim yana ganinta.
Ta yi ta kukan rabuwa da danta tana ji tana gani
aka tafi da danta, ni ma ina ji ina gani mahaifina
mai
sona, wanda muka shaku da shi ya tafi ya bar ni.
Gidan da muke ciki kato ne sosai, ina yarinya
sosai. A hankali har na soma mantawa da su,
mahaifiyata
da danginta kadai na sani, don su na budi ido na
ga ina rayuwa da su. Aka saka ni a makaranta
mai kyau, tun daga Nursiry har zuwa sakandire.
Sai da na shiga aji uku na sakandire sannan
Yayana Ibrahim ya zo Egypt,
kanin babanmu uncle Mansur ne ya kawo shi, a
lokacin ya gama sakandire. Kukan dadi Mamana
ta
yi data gan shi, don dama kullum addu,arta ke
nan ta ga danta, sai ta shirya zata je Nigeria sai
danginta
su hana ta. Mahaifinmu tunda ya tapi gida ya
manta da mu, ya auri mata biyu suna ta zazzago
masa
haihuwa, arziki ya kara bukasa.
Sai a lokacin na san Yayana Ibrahim, ashe
kamarmu daya da shi, dukka mahaifiyarmu muka
biyo. Fari ne sol sak balarabe sai dai ki ji Hausa
a bakinsa rangadadai irin ta Sakkotawa amma
babu digo daya a jikinsa da ya yi kama bakar
fata. Babu alamar wahala a jikinsa kasancewar a
can a cikin daula suke, babu talauci har sun fimu
jin dadi saboda Egypt ba kudi, ba albashin kirki a
ma'aikata, babu kasuwanci da zai kawo kudi irin
a Nigeria.
Na zaci ma ya kauro kenan da na ga Baffanmu
da ya kawo shi ya koma ya barshi. Da Ibrahim ya
yi
watanni hudu ya yi waya da *yan gida suka ce
masa sakamakon jarabawarsa ya fito sai ya ce
Nigeria zai koma ya yi jami,a.
Babu yadda mamanmu ba ta yi ba kada ya tafi.
Ya ce ya fi son ya tafi, saboda da can ya fi
sabawa.
Amma ya yi alkawarin duk shekara zai dinga
zuwa hutu tunda ya ga hanya yanzu.
Tabbas ya tausaya mana da ya ga muna ta
kame- kame babu wadata shi ma ba kudin ne da
shi ba,
tikitin zuwa da komawa ya ba shi, sai *yan canji
a aljihunsa.
Mun shaku dashi sosai a wannan watannin hudu
da ya yi damu. Munsha hira kala-kala, baya
gajiya
da jerin gwanon tambayoyin da na dinga jero
masa game da mahaifinmu da kasarmu da kuma
kannena na can. Allah Ya taimaka Mahaifina da
kannensa sun koya larabci don haka da Larabci
don haka da larabci muke magana, idan ta kakare
ya juya Turanci. Ni kuma na fara koyon Hausa a
wajensa kadan-kadan. Dalilina na yi masa
tambayoyi akan kasata Nigeria
shi ne, na karada cikin kawayena da cewa. Ni
*yar Nigeria ce, amma ban san komai ba akan
kasar, har
suke karyata ni. Amma da Ibrahim ya yi min
dalla-dalla na rubuta shikenan za su sha labari a
makaranta.
Bayan tafiyarsa ya sami damar shiga jami,ar
Ahmadu Bello Zaria, yana karantar Engneering. A
lokacin wayar land-line ta wadata babu wayar
hannu, koda yaushe yana bugo mana waya mu yi
ta hira, amma dai dai da rana daya Mahaifina bai
taba cewa a ba shi ni ko Mamana mu gaisa ba. ..
Muna farrin ciki da ganinsa har ma yana taho
mana da tsaraba kamar su atamfofi, leshina
dinkakku sai
kukar kadi, garin masara, garin dawa, kubewa
bushasshiya, harda daddawa. Da yake Mamana
ta iya dafa abincin hausawa, zaman da ta yi da
Babanmu ya koya mata, yana sawa ta dafa
masa. Ni ma inajin dadin cin tuwo sosai, don
haka na dage na koya.
A lokacin da Ibrahim yake daf da gama jami,a ni
kuma na gama sakandire da sakamako mai kyan
gaske.
Kai tsaye jami,a na wuce suka bani medicine.
Kwakwalwa gareni, duk da ina da yawan surutu
da son wasa, amma a aji idan aka sami na daya,
to ni ce ta biyu.
Ibrahim ya yi farin ciki da samun labarin ina
karantar likita, ya kara min karfin gwiwa in dage
in kammala. Sai a lokacin ne ma na taba jin
muryar Mahaifina, Ibrahim ya bani shi a waya
muka gaisa ya yi min addu'ar fatn alkhari. Sai na
yi wa Mahaifina tambayar da ta girgiza shi jikinsa
yayi sanyi. Na ce,
'Baba, au daman kasan kana da *ya ta cikinka a
Egypt? Ka manta da ni dai-dai da rana daya baka
taba zuwa ka ganni ba, ko ka neme ni a waya ko
ka aiko da tikiti ka ce inzo in ganka, kuma inga
sauran *yan uwana?
Sai ya yi kasake ya kasa bani amsa, Mahaifiyata
ta fusata ta kwace kan wayar ta ajiye ta hau ni
da bambamin fada. Wai akan me zan ce ya aiko
datikiti in je Nigeria? Sai dai in bayan ranta zan je
Nigeria. Wai ina so in je nima su shanye ni kamar
yadda suka shanye Ibrahim, ya kasa baro
wajensu.
Sai na yi ta kuka ina ta takaicin irin wannan
kwamacalar aure da rabe-rabe tsakanin
Mahaifana. Da Ibrahim ya kammala karatu ya yi
bautar kasa,
sai ya taho Cairo ya zauna tare da mu da
takardunsa. Nan da nan kuwa ya sami aiki a
wani kamfani Albashinsa mai kyau ne, idan aka
hada da yadda ake biyan *yan kasa shi ya sami
kari saboda suna daraja abin da ya karanta, kuma
sun ga a Nigeria ya yi, Sai a lokacin na fara
fuskantar matsaloli da gore-
gore, saboda na isa aure ina da samari da yawa,
idan maganar aure ta taso ranga-ranga sai
iyayen mazan su bijire su ce ba a san ubana ba.
Ko kuma idan suka bincika aka san ni ba shegiya
ba ce, sai su ji cewa uban bakar fatane, ya gudu
ya bar mu sai a ce ba za,ayi ba. Dan haka ni ba
matar da zasu iya aura ba ce, dan zan iya
sulalewa watarana na gudu kamar yadda
Mahaifina ya yi.
An yi haka ya fi sau uku, babu abin da nake yi sai
kuka, Mamana da Ibrahim suna ta ba ni baki. Na
shirya zan tafi Nigeria wajen Mahaifina ya fi a
kirga, Mahaifiyata sai ta tubure ta ce bazan je ba.
Shi
ma kansa Ibrahim tunda ya zo ya fara aiki ta
hanashi zuwa Sokoto shima kuma Mahaifinmu
yana nuna halin ko'in-kula da mu, da zuwanmu
da rashinsa duk daya ne a wajensa, saboda
matansa na can sun dauke masa hankali akan
mu, sun fi so su manta yana da *ya*ya a Cairo,
*ya*yansu ne kadai *ya*yansa.
To haka dai ake ta fama ni ina a asibiti ina
samun kudi har na sayi mota, haka Ibrahim ma
yana aikinsa da motarsa. Mahaifiyarmu ta fara
jim dadin rayuwarta babu abin da ba ma ajiye
mata. Mun tashi daga dan karamin gida mun sayi
babba soasai da kayan alatu, matsalarmu daya
ita ce a wajen maganar aure.
Ibrahim ma ya sha neman aure ana hana shi
saboda ba'asan Mahaifinsa ba, idan kuma an san
akwai shi, to ana tsoron kada ya sulale watarana
shima ya gudu kamar yadda ubansa ya yi.
Babbar matsalata na fara girma, don na bawa
shekaru talatin baya a lokacin, duk kawayena duk
sunyi aure suna haihuwa, ni haryanzu abu ya ki
yiwuwa. Idan na zauna ina kuka sai Mahaifiyata
ta yi ta ba ni hakuri wai a hankali mijina zaizo
wanda ba zai damu da bincike na ba. Ta ce in ma
cire raina da cewar zanje Nigeria, saboda tana
tsoron wadannen mutane ba su da kirki, za su iya
salwantar min da rayuwata. Sai na tambayeta ''ta
ya ya za su cuce ni bayan ni jininsu ce, me yasa
ta aure shi tunda ta san ba su da kirki?
Ya akayi ita ba,a cutar da ita ba har ta zauna da
shi suka haife mu?
Da yake tana da fada sai ta rufe ni da masifa ina
ji ina gani laifi ya dawo kaina na koma ina ta ba
ta hakuri. Da naga kabilancin *yan Cairo ya yi
yawa a kaina wajen aure sai na yanke hukuncin
na auri
baki muzauna Egypt *yan Nigeria da yake akwai
su da yawa, ko kuma a cikin bakaken da suke
zuwa
Nigeria ganin likita a asibitinmu.
Duk inda na ga dan Nigeria sai na ji ina sonsa,
musamman Bahaushe, ko ba ya so sai na
tsokano shi da hira dan na sanar masa nima *yar
uwarsa ce har ma in yara masa YARENA na
Hausa, tunda na koya wajen Ibrahim, Mamana
ma tana ji kadan-kadan.
Ta haka sai na yi abokai da kawaye masu dumbin
yawa, ko sun koma Nigeria suna da lambata sai
mu
yi ta waya da su ina cika bakin watarana za su
ganni a Nigeria.Duk wani dan Nigeria da ya ke
zuwa Cairo, musamman asibiti idan ku ka
tambaye su Dr. Faduwa Ahmad sun sanni. Ina
son mutane saboda ina da yawan hira a
sanadiyyar hakan sai na hadu da manyan *yan
Nigeria ma su kudi da mulki, kamar ambassadors,
ministoci, kwamishinoni, *yan kasuwa manya-
manyan masu kudi.
Wasu suna sona da son fasikanci, wasu kuwa da
aure suke sona. Bana boye-boye, baro-baro nake
fadawa fasikan nan ni ba *yar iska ba ce, kada su
sake shiga harkata. Masu sona da aure kuwa
suna cewa idan sun aureni zasu tafi da ni Nigeria
ba za su barni a Cairo ba, sai na rusa maganar
dan na san
ma bazai yiwu ba don mahaifiyarta ba zata yarda
ba. Ni ma kuma bana son abin da zan jawowa
*ya*yana rabe-rabe kamar yadda na tsinci kaina.
Da na ga abin ba kararre ba ne, aure ya ki
yiwuwa saina yankewa kaina shawarar ko aikin
nawa ne
sai na bari na auri dan Nigeria na bi shi can mu
zauna. Har na taba tunkarar mahaifiyata da
maganar
aurena da Alh. Murtala wani Bakano ne, dan
kasuwa, yana da mata uku ni ce ta hudu, amma
duk ban damu ba.
Yana matukar so na, yana da kirki ga dukiya mai
yawa, saboda son da yake min bai ki ya raba
dukiyarsa gida biyu ya bani rabi ba. Kuka yake yi
da idanunsa akan na daure na aure shi, gidana
daban ba zai hada ni da iyalansa ba. Kuma zai
dinga kawo ni akai-akai ina ganin iyayena.
Koda na fadawa mahaifiyata wannan labari, sai
ya dora hannu aka ta yi min kukan mutuwa. Ta yi
ta kiran lambar *yan uwanta wai su yi maza su
zo ga Faduwa zata kashe ta.
Nan da nan kowa ya zargayo a gigice suka tarar
ba kisan hannu zan yi mata ba, kisan zuciya zan
yi mata.
Nan da nan suka taru suka hada baki babu
wanda ya amince min. Ibrahim ne kadai ya ke
bani goyon baya, shi ma ba a tashi daga taron ba
sai da aka tsige shi tas. Aka ce ba shi da hankali,
ya za a yi ya bawa kanwarsa wannan muguwar
shawara na auren namiji mai mata uku, kuma dan
Nigeria narasa rike aure, wadan da ba su san
muhimmancin haihuwa ba.
Dole na yiwa Alh. Murtala sallama muka rabu, ba
shi kadai ba ma akwai wani babba mai mulki shi
ma
daga Abuja yake, ya kawo Mahaifinsa asibitin da
nake ciki muka saba, har soayyaya ta shiga.
Matarsa daya da *ya*ya biyar shi ma da na fada
a gida aka hana ni. Sai na hakura da maganar
aure gaba daya, tunda na rasa miji a Egypt, an
hana ni auren *yan Nigeria.
Sagir dan asalin Cairo ne, sannan dan sanda ne.
Shine tsohon saurayina da muka hadu da shi tun
bayan da na kammala sakandire, tashin farko
daman mahaifiyarsa ta ce ba ta yarda ba, ba zai
aure ni ba. Dan bani da sali, *yar uwarsa zai aura
mai cikakken asali ba ruwa biyu ba.
Yana sona sosai ya kasa rabuwa da ni, duk da
yasan aurenmu ba zai yiwu ba, yana ganin kamar
wata rana zata iya yarje masa ya aure ni. Ashe
ita ba ta san ma muna tare ba har tsawon
shekaru da yawa, sannan ya sake gabatar mata
da ni a matsayin wacce zai aura. A take ta nuna
mishi sai dai idan bata raye, ba zai aureni ba.
Ina kuka, yana kuka ya ce shi bazai rabu da ni
ba, kullum yana gidanmu, idan ina gida idan kuwa
bana gida ina asibitin da nake aiki, to zaka anshi
a kusa da ni, sai dai idan nasa aikin ne ya
hanashi zuwa.
Mahaifiyarsa tana kiransa sama da sau goma
kafin yabar wajena, kai ka ce duba ta ke yi.
Muddin ya zo
sai ta gane sai ta yi ta kiransa. Ka ji tana
magana cikin fushi, kasaita da daga murya.
''Sagir, kana ina?
Cikin fushi da takaici yake amsa mata.
''Mama ya kike tambayata kamar karamin yaro da
zai bata a Cairo?
Sai ta ce, ''Kana tare da wannan tsinanniyar
Faduwar ko? To ka dawo gida yanzun nan, nan
da awa guda maza-maza ka karaso.
Sai ta kashe waya a fusace bayan kamar mintuna
biyar sai ta kirashi kuma.
Ta ce, ''Ka taho ne?
Sai ya ce, ''Zan dai taho yanzu. Idan ta ji shuru
bai iso ba, sai ta sake kira.
Ta ce ''Ya banji karar motoci ba, bayan ka ce min
kuma kana hanya?
Aikin kenan sai raina ya baci na ce ya tashi ya
tafi.
Ana nan-ana nan ni da shi kullum muna ta
shawarwari yadda zanu bullowa wannan
matsalolin. Mun shirya duk yadda zamu yi
rayuwar
aurenmu cikin farin ciki. Tsalelen gida ya gina ya
zuba kayan alatu. Ya nuna min bangarena da
bangarensa da kuma bangaren *y *yanmu idan
mun haifa, tunda ko yaushe muna hasashen
zamuyi aure har ma mu hayayyafa..
A gidan muka yi liyafar cikarmu shekara goma
sha biyu da haduwarmu (12 anniversary). Muka
gayyaci kawaye da abokai, muka yanka kek, aka
yi mana hotuna. Kowa ya tausaya mana ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login