Showing 126001 words to 129000 words out of 130520 words

Chapter 43 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8026

dan
tsukururun dakinta amma ta ga sun baje suna
baccinsu babu abinda ya dame su.
To menene babu a dakin?
An shimfida kafet, ga injin janareto ya kwana
yana yi, ga fanka, an fesa Shaltos duk an saka
net a bakin wundo da kofar shiga sauro ba zai iya
shigowa ba. Sannan ga firij da ruwan sanyi duk
Sabitu ya je birin ya taho da ma'aikacin Nepa ya
zo ya hada mata komai.
Ranar juma'a ake yin biki,
kawayenta daga Gombe mata kakaf sun hallara
kowacce ta ci ado, sai ga Lamijo, Umma da
makwabciyarsu Salma, Hanif ne ya kawo su a
motarsa.
Taro ya yi taro dan wasu da yawa ma amarya
bata sansu ba suka taho cin arziki, abinci dai mai
suna
abinci kowa sai da ya ci ya bar shi.
Amarya ta yi ta shigar kaya kala-kala ta na
canjawa kai ba zaka ce amaryar nan daga Rugar
nan ta fito ba saboda ta iya tsara ado.
Ma su daukar hotuna da bidiyo ma sun zo suna
ta daukar amarya da jama'arta,
Matawata ta kasa shigowa saboda kunya.
Makada daga Rugage daban-daban suka zo suka
hau wasa ba tare da an gayyace su ba. Sun sha
liki daga wajen Umaimah da kawayenta. Da
yamma baki suka zo daga Gombe irin su Lamijo
suka fara haramar komawa gida, idan zaka tafi
da himilin kayan biki za'a hadoka da leda-leda a
ciki akwai memo, kalanda kofuna, farantai duk
masu dauke da hotunan ango da amarya
kawayenta su Aisha sun yi kokarinyi mata duk
wadannan. Da yawa daga cikin kawayenta sun zo
da shirin kwana, kadan ne suka tafi.
Da daddare aka yi ta sa wasanni iri-iri har zuwa
sha biyun dare sannan aka tashi sai kuma gobe.
____
RANAR DAURIN AURE
Washe gari asabar ita ce ranar daurin aure za'a
daura da karfe goma sha daya na safe. Karfe
takwas saura mintina yara suka shigo gidan su
Umaimah kace-kace suka iske ta a cikin masu
girki suna ta faman hadawa bakinta shayi,
dankali, doya da wainar kwai, su ka ce ta zo in ji
wani mutum mai mota yana kofar gida. Babu
wanda ta kawo a ranta sai angonta Abdul-Sabur,
ta yi mamaki yadda suka
iso da wuri. Nan da nan ta daka tsalle ta shiga
daki ta canja kaya masu kyau ta fito, tana fitowa
kofar
gidasai ta ga ba Abdul-Sabur ba ne maimakonsa
Abdul-Basi ta gani dan haka ta ki ta karaso in da
yake kuma ta bata fuska babu ko annuri a
fuskarta.
Ya bude kofar mota ya fito cike da murmushi ya
tunkaro ta sai ta koma cikin zaure ta tsaya,
shima ya shigo gami da yi mata sallama. Amma
magana yake yi cikin nadama har da hawaye a
idanuwansa. Ya ce "Yanzu Umaimah kin yarda ki
rabu da ni ki auri wani bare wanda ba'a san
asalinsa ba?
Kin yarda ki rabu da ni har abada ni da
*ya*yanki?
Cike da gatsali ta ke amsa masa da "Eh
Ya ce "Na roke ki kada ki yarda a daura miki aure
da shi ki ce ni kike so a daura da ni, na yarda na
yi miki laifi a baya yanzu na canja.
Umaimah ta yi murmushin takaici ta ce "Ina ga
kamanta bada Umaimar daka sani ada ba ce kake
magana, a da ne duk yadda ka tsara min nake bi
bana iya yi maka musu, a lokacin dana dauke ka
miji, uwa, uba kuma yayana sai dai kash ka nuna
min duk ba haka ba ne, ashe na kai ka matsayin
da
baka cancanta ba, domin Uwa da uba ba zasu
kori dan su ba. Kana magana akan abunda kai
kanka
ka san ba mai yiwuwa ba ne, ina ga kamar kana
bata bakinka, ai ka makara. Yarana kuma Allah
Ya
raya min su.
Ta fashe da kuka ta yi wuf ta fada cikin gida ta
bar shi anan a durkushe ya rike kai yana fitar da
zazzafan hawaye na nadama. Dakyar ya mike a
hankali ya nufi motarsa dan yaga yara sun fara
zagaye shi suna kallo dan su abun kallo baya yi
musu wuya a kauye.
Gidan Dagaci ya nufa anan ya iske Baffa da
Sabitu da sauran jama'a ana ta share-share ana
shinfidawa baki tabarmi da kilisai ana shirin
daurin aure, kowa ya tsorata da ganinsa saboda
mummunan lafazinsa da yayi a baya. Amma sun
saki jikinsu da suka ga bai shigo da suffar fada
ba ko tashin hankali. Ya je ya durkusa a gaban
Dagaci sai ya kece da kuka na nadama.
Ya ce "Yanzu haka zaku yi min ku hana ni auren
matata ku bawa wani bare?
Alhali ina sonta, *ya*yanta suna neman
kulawarta.
Dagaci ya girgiza kai ya ce, "Ni da Baffan
Umaimah bamu da yadda za muyi da kai sai dai
mu yi maka fatan Allah Ya baka wata amma baka
bi hanyar da za'a dawo maka da matarka ba.
Ka zo ka sake bata magana kwanakin baya,
zaginmu ne kadai ba ka yi ba.
Takaici ma ya hana Baffa da Sabitu yin magana.
Babu abinda Abdul-Basi ya ke sai kallon tsala-
tsalan shaddojin da suke jikin Baffa, Sabitu da
Dagaci , kana ganin dinkunan nan kasan ba'a
kasar aka yi su ba dan dinkunan ma abin kallo
ne,
ya san duk Abdul-Sabur ne ya dinko musu.
Ya kasa tashi ya tafi sai yake ji tamkar zasu ji
tausayinsa su fasa daurawa da Abdul-Sabur a
daura da shi. Amma ina sai ya ji ana cewa ga
ango ya iso shi da tawagarsa, nan fa aka dinga
shigowa da darukan naman kaji, kek, da su meat
pie, bayan lemuna masu sanyi a cikin kankara
kula-kula duk
ango ne yayi oda daga Hotel har da ma'aikatan
da zasu dinga rabawa su bawa kowa.
Tabbas wannan daurin auren ya fita daban da na
sauran daurin auren da aka taba yi a garin.
A lokacin da Angon Umaimah ya shigo farfajiyar
gidan Dagaci babu abinda kake hangowa sai
walkiya kai kace yau aka ciro shi daga leda ya
sha fararen kaya dinkin babbar riga ta sha
surfani, ko ka ki kallonsa da idanuwanka
hancinka zai jiyo maka daddadan kamshinsa.
Yana gaisawa da jama'a domin waje ya
cika makil har wani baya iya ganin wani, bayan
hayaniyar jama'a, karar gangar makada sai tashi
take.
Daga gidan Gwamnati ma su Baban Hanif motoci
da yawa suka ciko haka abokan Umaimah maza
su Hanif kenan suma sun hallara, kusan kowa da
motarsa ya zo. Jami'an tsaro wato *yan sanda
motoci biyu aka kawo daga Dukku don su
tabbatar da zaman lafiya saboda furucin da
Abdul-Basi ya yi.
Sai ga Abdul-Basi a gaban Abdul-Sabur suna
kallon-kallo, mamaki ya hana Abdul-Sabur rufe
bakinsa har sai da Abdul-Basi ya taso ya zo ya
mika masa hannu suka gaisa sannan ya ji sanyi a
ransa,
ya tabbatar ba yaki ba ne ya kawo shi sulhu ne.
Tabbas Abdul-Sabur ya ji tausayinsa sai dai ya fi
jin tausayin kansa dan ya fi shi son Umaimah, ba
zai iya hakura ya bar masa ita ba.
Aka daura aure a bisa Sadaki mafi kankanta
yadda Allah Ya ce suna neman albarka a aurensu.
Idan ka tona zuciyar Abdul-Basi a yau gawayi ya
fita haske baki kirin da ita saboda bakin ciki, haka
idan da za'a bude zuciyar Abdul-Sabur a yau tafi
nono fari saboda farin ciki.
Bakin ango ya kasa rufuwa dan murna, da ka
gama daurawa aka ci aka sha. Sai ango ya aika
aka kira amarya da kawayenta suka firfito
kowacce da katon gyale saboda maza.
Umaimah ta yi ta gaisawa da baki aka dinga
daukar ango da amarya da jama'a a hotuna.
Umaimah ta je ta durkusa a gaban Baban Hanif
ta gaishe shi gami da yi masa godiya daya samu
ya zo, ya yi mata fatan alkhairi gami da addu'ar
Allah Ya basu zaman lafiya gami da yi mata
nasihu akan ta bi mijinta su zauna lafiya.
Daga karshe ya zaro katuwar ambulan ya mika
mata ya ce ayi hakuri ga gudunmawarsa babu
yawa, ta karba ta yi masa godiya sosai.
Uhumm lallai kuwa babu yawa Naira na dukan
Naira har Naira dubu dari biyu ce a cikin ambulan
din.
Ango da amarya suka kebe suna tattaunawa, ya
dube ta duba na tsananin kauna ya yi dariya. Ya
ce "Kin yi kyau amaryata.
Ta kyalkyale da dariya ta ce "Ka fini kyau
angona.
Su ka yi ta tuntsura dariya jama'a suna ta
sha'awarsu. Ya shaida mata tare suka taho da
mata su Khausar kenan itama da kawayenta *yan
Abuja,
Ummana Fuse da tawagarta daga Ghana, *yan
Gwarzo ma zokar da su, ya baro su a Gombe
Hotel guda ya kama musu.
Ya shiga maganar yadda za'a shirya daukar
mutane masu tafiya Gombe wajen Dinner amma
banda
tsofaffi da yara. Su tsofaffi mata sai gobe za'a
aiko da motoci a dibi masu zuwa rakiyar amarya
Abuja dan haka yau ma su Nene sabon yini zasu
aiwatar a junansu. Saboda yawan masu son zuwa
Umaimah ta ce a kawo manyan bus ayi ta kwasa
kawai har yadda motocin zasu kare.
Haka kuwa aka yi aka turo motoci da yawa, kafin
a tafi Umaimah ta je ta yiwa Baffa sallama gami
da neman gafararsa, yana kuka tana kuka ya yi
mata nasiha masu ratsa jiki, suka tuno da Yafindo
da Nasiba sai kukan ya sake karuwa.
Daga nan ta nufi gidan Dagaci shima ta yi masa
sallama yayi mata
fada akan ta bi mijinta gami da addu'a Allah Ya
ba su zaman lafiya. Umaimah da jama'ar da suke
da amfani a wajenta ne sune suka shiga tsala-
tsalan motoci, *yan gayyar sodi na jiki sune suka
sami
shiga bus saura kuwa dole sai dai su yi hakuri
saboda motocin sun cika. Har an tayar da motoci
za'a tafi sai Matawata ta fito da gudu ta zo jikin
motar da Umaimah take ciki tana kwankwasa
gilashin, kuka take yi wiwi tana ambaton sunan
Umaimah.
Hankalin Umaimah ya tashi ta ce direba ya tsaya,
ta bude kofa ta fito da sauri ta rike Matawata
tana tambayar ta "Lafiya?
Matawata ta sake rusa kuka ta ce "Umaimah, ki
yafe ni kiyi hakuri na san na zalunce ki a rayuwa,
na dade ina miki zalunci ba ki taba daga kai kin
tanka min ba.
Daga karshe dubi yadda rayuwarki ta daukakawa
ni kuma dubi yadda na kaskanta. Ki taya ni bawa
Ilah hakuri shima na cuce shi dana
raba shi da wacce yake so. Umaimah, ke Ilah
yake so ba zai daina sonki ba kuma, ni na sani
dan Allah ku yafe min ni na raba soyayyarku.
Umaimah ta matse hawaye ta ce "Daina kuka
Matawata, na ya fe miki tuntuni kuma na yi miki
alkawari ina tare da ke zan dinga taimakonki ta
kowacce hanya. Kar ki damu zo ki shiga mota mu
tafi Gombe zan baki wasu kayan ki saka acan.
Kayan jikinta duk sun kode tamkar almajira sai
tsamin dauda take aka saka ta agidan gaba, da
Aliya ce a zaune a wajen Umaimah ta roketa ta
koma wata motar.
Faduwa da Aisha suka dinga kallon ikon Allah.
Sannan suka kama hanyar Gombe.
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 54
Da suka isa Gombe a gidan su Aisha, Umaimah
da tawagarta suka sauka sai da karfe takwas na
dare za'a fara gudanar da bikin.
Da yamma bayan sun idar da sallar la'asar
Umaimah da kawarta Aisha suka sulale kowacce
sanye da katon hijabi kamar masu lekawa kofar
gida ba tare da kowa ya san inda suka tafi ba,
suka shiga motar
Aisha suka fice Umaimah ce me tukawa. Ba su
tsaya a ko ina ba sai a kofar gidan iyayen Abdul-
Basi.
Mamaki marar musaltuwa kake gani a fuskokin
*yan gidan, daga shigowar Umaimah sai suka yi
carko-carko manyansu da yaransu suna kallonta,
gashi gaba daya gidan kowa ya hallara kamar
wadanda suke meetin. Alhaji shi ma yana nan,
Hajiya ma tana nan, ga Abdul-Basi zaune akan
kujera ya rike kai dan takaici yayin da
idanuwansa suka yi jawur saboda kuka. Daga
dukkan alamu haduwar nan da akayi gaba daya
hakuri aka taru ana bashi kuma ana yi masa
nasihar maganar.
Shigowar Umaimah ya sa kowa ya shiga zargi
kala-kala amma abunda kowannensu ya fi zargi
shine Umaimah ta fasa auren wancan ta dawo
wajen Abdul-Basi.
Ya mike tsaye a zabure yana mai fara'a gami da
zuba mata ido yana saurare.
Sun yi musu sallama tafi a kirga aka rasa mai
amsawa saboda kowa ya fita hayyacinsa.
Umaimah ta zo ta durkusa a gaban sirikinta ta
gaishe shi ta juya ta gaishe da Hajiya, Aisha ma
haka ta gaishe su suka amsa cike da fara'a da
sakin fuska. Sannan suka gyara zama,
Umaimah ta fara da cewa. "Alhaji, jiya aka daura
min aure.
Alhaji ya gyada kai ya ce "Alhamdulillah, na taya
ki murna Allah Ya bada zaman lafiya.
Abdul-Basi na tsaye akansu sai ya sake matsowa
kusa, kalma daya ya ke so ya ji ta furta ita ce ta
ce "Bana son wancan na dawo wajen danka
Abdul-Basi, maimakon haka sai ya ji ta ce.
"Yau ne za'ayi Dinner da daddare anan garin,
gobe lahadi za'a kai ni Abuja can ma za'ayi wani
bikin,
shine nake so a taimaka a bani yara suma su zo
wajen bikin ayi hotuna da su saboda tarihi.
Sai kowa ya yi juyi na takaici, musamman Abdul-
Basi wani dogon tsaki ya ja. Har zai yi magana, a
fusace Alhaji yayi masa tsawa ya ce ya rufe
masa baki babu ruwansa da wannan maganar,
ba'a raba
uwa da *ya*yanta ba dan ma a gidan wani zata
je da kyauta zai bata *ya*yan in har zata iya
rikewa,
rikon da sai Uwarsa. Daga dukkan alamu Hajiya
ma magana take so ta yi amma tsoro ya hanata
dan ta
san itama tsawar zai yi mata a gabansu, dan
ransa a bace yake.
Umaimah tana ta murna sai godiya take yi masa,
ya nuna mata dakinsu ya ce ta shiga ta dauko su
da kayansu su je asha biki lafiya. Su Umaimah
suka tashi suka shiga dakin tana daga labule tayi
sallama
suka gane muryarta zo kaga tsalle, ihu, da
danewa.
Ta shaida musu ta zo daukarsu zasu je biki dan
haka su dauko akwati su zuba sababbin kayansu
ta taya su zabe aka cika akwati suka fito tayi
musu sallama suka fice sai harara amma babu
wanda ya isa ya ce su dawo, ga Alhaji a zaune,
ya kasa, ya tsare, ya raka.
Da daddare aka fara gudanar da bikin Dinner,
waje yayi kyau, abinci ya wadata masu dadi
kala-kala, jama'a sun hallara har su Lamijo.
Bangaren *yan uwan ango daban, bangaren
abokan ango daban,
na *yan uwan amarya daban, haka amarya da
ango bangarensu daban wato 'high table.
Amarya da ango sun caba ado sun yi kyau sosai
kuma sun dace da juna, kowa yayi sha'awarsu,
*ya*yanta sune aka saka a gaban ango da
amarya yayin shigowarsu, kayansu iri daya kuma
sun rike fulawa.
Ba'a tashi daga shagali ba sai karfe goma sha
dayan dare ana ta rakashewa. Hotel din garin nan
dai-dai ne Abdul-Sabur bai kama ya zuba
bakinsa ba. Aka tsayar da shawara washe gari
lahadi da sassafe kowa ya shirya ya fito za a
kama hanyar tafiya Abuja kai amarya.
Haka kuwa aka yi da sassafe aka turo motoci
Dugge aka debo su Nene da jama'arsu a zo aka
hadu aka kama hanya, motoci sun yi guda dari
kowacce ka samu kaduru kawai. Haka motar
amarya da kawayenta daban ta ango ma da
abokansa daban. A jere aka tafi ana ta nishadi a
hanya sai tafiyat bata yi musu nisa ba. Allah cikin
ikonsa aka isa da wuri.
ABUJA
Ashe anan ma Abujar lafiyayyiyar liyafa aka hada
musu makeken wajen yin bikin nan mai tsadar
gaske wato 'M and B Gardern'.
Shamsuddin mijin Khausar ne ya hada musu
wannan. Manyan gidaje
aka tanada na saukar baki, gidan maza daban na
mata daban anan kowa ya baje yana hutawa
ba'a
je gidan amarya ba tukunna sai bayan an dawo
daga Dinner da daddare. Kafin su iso an tanadar
musu abinci kala-kala, kowa ya ci amma ya rage
waje a tunbinsa in da zai dura abincin da za'a ci
a
wajen Dinner anjima.
Umaimah ta dankawa Aisha amanar *ya*yanta ta
ce ta dinga kula da su a wajen bikin daga nan
har zuwa Gombe bayan biki ta mayar da su
gidansu amma ta ci gaba da ziyartarsu tana
tambayarsu abubuwan da suke so, sai ta kira
Umaimah a waya ta fada mata ita kuma zata
turo mata ko meye ta kai musu.
Aisha ta yarda ta karbi amana dan tana da son
yara kasancewar bata da kanne.
Kafin taga yadda hali yayi tana da burin ta
daukosu ta rike su nan gaba kamar yadda Alhaji
ya bata zabi ta san Abdul-Sabur bawan Allah ba
zai ki ba.
Wajen bikin ma (Hall) abun kallo ne haka duk
inda ka waiga fararen fata ne suke haskawa wato
turawa abokan Abdul-Sabur ne suka zo daga
Ingila, Indonosiya da Malaysia. Sai ga babban
bako ya shigo wajen aka gabatar dashi sai kowa
ya mike tsaye saboda girmamawa wato Uncle
Hamaza.
Wannan ne karo na farko dalili ya yi dalili ya taba
zuwa Najeriya, a dalilin Abdul-Sabur. Su ba'a
wahalar da su wajen kai su Gombe ba aka hada
musu ta su liyafar anan. Ba kowa aka bari yaje
ba sai wayayyu hadaddu.
Zabgi amarya ta zuba kyau dan ba a gida aka yi
mata kwalliya ba, a kanti aka yi mata kuma
baturiya ce ake biya take shirya amare dan haka
idan har baka san Umaimah ba sosai, sai ka ce
an canja ta, ba ita ba ce.
Dan gaba daya ta sake saboda kyau, kayan
jikinta ma abun kallo ne.
Da zarar Abdul-Sabur ya dube ta sai ya fara
godiya ga Allah da Ya bashi Umaimah.
Daga wajen Dinner aka dauko amarya sai aka nufi
gidanta, Allah mai halitta ita kanta amarya bude
baki ta yi tana kallon kayan alatu da ginin gidan
kansa. Wasu abubuwan ma basu taba ganinsa ba
duk zaman da suka yi a Malaysia. Ya dankara
gida
ya zuba kayan alfarma faluka kala-kala kowanne
da kalar kujerunsa da labulayensa haka dakuna
daban-daban gadaje iri-iri *yan kamfani.
Haka bangaren Ummana Fuse itama ya hadu kai
ka ce itama amaryar ce, katon falo, dinning area
da dakuna guda biyu kowanne da bandakinsa a
ciki,
a ranar ta tare da kayanta ita da danginta na
Ghana.
Khausar kuma ta tafi da danginsu na gwarzo
gidanta suka sauka acan.
Babu abinda Umaimah take yi sai kukam dadi,
ana ta lallashi gami da yi mata murna da
addu'oin Allah Ya dauwamar da ita a gidanta ya
basu zuriya ta gari. Kowacce ta ga kyakkyawan
gida sai ta makale
ta ce anan zata kwana, manya suka ce ba za'a
batawa amarya da ango gidansu ba kowa ya fito
ya tafi masaukin da aka ajiye su dazu ga motoci
can a kofar gida suna jira.
Dakyar amarya ta roka aka barta da kawayenta
guda uku su taya ta kwana, Aisha, Faduwa da
Khadija sai kuma *ya*yanta su Babangida.
Abdul-Sabur ma a wajen abokansa ya kwana a
hadadden Hotel din nan Nicon, amma fa su
dukkansu amarya da angon a zaune suka kwana
bacci ya gagare su dan murna da begen junansu
suka hana masu taya su kwana bacci sai hira ta
barke.
Washe gari bayan kowa ya yi wanka daman
Abdul-Sabur yayi magana abin karin kumallo da
masu Hotel, sai suka shiryowa baki abinci kala-
kala sai abunda kake so zaka zuba kowanne gida
an mika na su.
Bayan kowa ya ci sannan aka sake haduwa a
gidan amarya, aka dinga hayaniya ana raye-raye
aka sake kallon abun da ba'a karewa kallo jiya
ba,
sannan aka yi ta daukar hotuna ba adadi.
Daga karshe aka dinga jifgowa amarya
gudunmawa da yawa daga bangarori daban-
daban.
Kudi mai sunan kudi kuwa baya kirguwa, a take
ta zama miloniya saboda manyan attajirai abokan
Abdul-Sabur turawa basa harka da Naira daga
Pounds sal Dallars haka suka dinga zarowa suna
mika mata. Kawayenta da *yan Uwan ango sun yi
kokari sun hada mata kudi da yawa. Haka Hanif
ma ya aiko mata katuwar ambulan da kudi Naira
dubu dari ya ce shi da sauran abokansa maza
suka hada mata.
Faduwa da Sagir ma kudinsu mai yawa a
ambulam suma kuma Dalla ce suka bata.
Ga babba da kansa Uncle Hamza ya yi musu
yayyafin Pounds, gudunmawarsa ta fi ta kowa
yawa.
"Shin mafarki nake yi ko idanuwana biyu?
Umaimah take tambayar zuciyarta. Dan ta rasa
da bakin da zata yi wa jama'a godiya. Sai kuka
kawai
take yi da alama ana yin kukan dadi dan ita ta
rabu da kukan bakin ciki kuma a rayuwarta.
"Talauci a sauka lafiya, marhaban da zuwan
arziki"
Inji zuciyar Sabitu a lokacin da yake hango kudi
yana ta ambaliya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login