Showing 51001 words to 54000 words out of 130520 words

Chapter 18 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8034

Na fara sakin jiki da
Salame, dimbun damuwar da nake ciki ta ragu
saboda tana dauke min kewa. Daga na shiga
gidanta sai ka ga ta tare ni da murna, ta yi ta
kawo min kayan ciye-ciye, yadda, yadda ku kasan
ta ba ni babu.
Na ji dadi da zama da Salame, na yi farin ciki da
Allah Ya bani madadin Matawata kawata, kuma
makwabciyata mai sona. Duk sanda zan je gidan
Lamijo tare da Salame muke zuwa, ta sa mijinta
ya
kaimu, ina baya suna gaba ana ta hira.
Umar sunansa, mutum mai yawan fara'a da son
hira,
har Lamijo ta ke zolayarmu wai kada fa mu
didare mu barta da zagayen baranda, ma'ana
kada dukka kawayenta ne a dalilinta muka san
juna, kada mu hade kai mu ware ta, don ta ga
shakuwar ta kai shakuwa.
Wata rana da daddare muna kwance a tsakar gida
ni da Umma, sai muke ta jiyo hayaniya a tsakanin
Salame da mijinta Umar su ma a tsakar gidansu,
da yake katangarmu daya da su. Hayaniya sai
karuwa ta ke yi, har yana cewa sai ya sake ta.
Na dafe kirji na tashi zaune, Umma ma ta zauna
muka shiga fargaba.
Ta ce, kafarta ke ciwo naje na ba su hakuri, na je
na ce inji ta ta ce su daina. Na saka gyalena
jikina yana
rawa har naje bakin kofa na juyo, na zo na
durkusa a gaban Umma.
Na ce, 'Umma ki daure ki zo mu shiga tunda
babu nisa, ki yi musu magana da kanki za su fi ji
tunda ke
babba ce, na ga kamar fadan ba karami ba ne,
tunda na ji dukkansu ransu a bace yake, kada ayi
batacciya.
Ta ce, 'To dauko min gyale na a daki.
Na shiga da sauri na dauko mata ina rike da
hannunta muna doddogarawa har muka isa cikin
gidansu. Muka iske su kaca-kaca kowa ido yayi
masa jajawur, baki yana kumfa da alama sun kai
kololuwar bacin rai. Yaransu suna ta kuka ga
wayoyinsu a kasa duk sun farfasa.
Umma tayi musu tsawa cikin ba cin rai ta shiga
yi musu fada tana nuna musu ba su kyauta ba.
Budar bakin Umar ke da wuya, sai ya ce 'Yauwa
ga Umaimar ki maimata abin da kika ce a kanta,
ni
kuma na shiga daki na dauko kur'ani mu yi
alwala mu dukka ukun mu dafa, Allah Ya wargaza
mai karya.
MAKWABTAKA 22
Sai na ji wata gagarumar fargaba yadda ku ka
san zuciyata zata fito waje. Na dafe kirji cikin
rawar jiki
da rawar murya na tambaye su, ''Lafiya, me na
yi?
Sai Salame ta aiko min harara sama da kasa, ta
murguda baki ta sake gyara damarar da ta yi ta
shirin dambe.
Ta ce, ''Kai da ita dukka munafikai ne, bakinku
daya, ko me zaku fada min ba zan yarda ba,
amanata kuke ci.
'Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. Allahumma ajirni
fi masibatin wa akhlif ni khairan minha.
Addu'ar da na fara fada ke nan a bayyane, yayin
da na dafe kirji da hannu daya na rike kai da
hannu
daya. Kan ka ce kwabo na rikice da kuka, yayin
da Umar ma ya fara hawaye don haushin kazafin
da ta
yi mana. Umma ma ta fusata ta ce, ''Duk ku yi
min shuru,
Salame wacce hujja gare ki ta cewa suna cin
amanarki?
Salame ta rike kugu tana girgiza idanunta mursisi
babu ko digon kunya, ta dube ni ta juya ta dube
shi. Ta ce ''Ga su nan da ran Allah ba zan musu
karya ba, ko a gabana ko a bayan idona ba su da
buri irin
su ga junansu su yu hira. Bini-bini sai ta shigo in
ta ga yana nan haka sai ta tarki cewa zata je
gidan Lamijo, shi kuma sai ya ce ku shirya in kai
ku. Ta madubi ma lekenta yake sai kuma ga
lambarta a wayarsa daga ta yi flashin sai ya kira,
ya fice kofar gida ya yi mata waya. Kila ma suna
haduwa a wani
wajen...
Ba ta rufe bakinta ba sai na rusa kuka na ce,
''Tsakanina da ke Salame sai Allah ya isa, kin yi
mana kazafi don ni ban taba sanin kalar lambar
Umar ba, ba mu taba waya da shi ba...''
Umar ya dube ta cike da takaici, ya ce, ''Salame,
ki ji tsoron Allah, ke makira ce, kuma idan ba ki
nemi
gafarar wannan baiwar Allah ba baza ki gama da
duniya lafiya ba. Zato kike yi kawai saboda
shaidan
ya yi miki huduba a zuciyarki. Waya kuwa da kika
ji ina yi ba da wata nake ba illa kanwar abokina
da aka turo bautar kasa a nan Gombe daga Kano,
ba tasan kowa ba a nan na hada ta da wata
mata ma'aikaciyarmu ta samo mata gidan haya
ta zauna.
Sunanta Aisha babu abin da ya hada sunan
Umaimah da nata. Sai Salame ta sake rikicewa
wai ita za mu mayar *yar iska, marar wayo shi
yasa kwana biyu idan zata dauki wayata sai ta
ga bana so, don kada ta ga lambarsa ne.
Takaici ya sa na fice ina sharbar kuka, na bar
Umma da sulhu. Ina shiga daki na fada kan katifa
ina rusa kuka, wayata ce ta yi kara, sai na ga
lambar Lamijo.
Gabana ya sake faduwa, na san labari ya isa gare
ta.
Na danna a sanyaye ina sauraron abin da zata
fada min, zagi ko kuwa rarrashi?
Na ji ta cike da fara'a sai ta ce min, ''Albishir!
Albishir!! Albishir!!! Har sau uku. Na tashi na goge
hawaye na dafe kirji na kagu na ji
abin da zata fada min.
Ta ce, ''Tafiyarku ta tabbata, an gama komai. Ki
shirya gobe ke da Hanif inji Alhaji mijina zai kai
ku
Abuja ku yi passport da takardunku na ainihi
(original) za ku kai federal ministry of education
da autentication.
Sai na yi ajiyar zuciya mai dadi, na kumshe ido,
na zabura na ce, ''Da gaske kike?
Alhamdu lillah
ke da mijinki Allah Ya saka muku da gidan
aljanna. Na gode, na gode. Godiya nake yi mata
har ta gaji da amsawa ta kashe wayar, sai na ji
zuciyata ta dan yi sanyi daga tafasar da ta ke yi.
Na tashi zumbur na fara hada *yar jakata ta
tafiya, duk da ba ta fada min kwanaki nawa zamu
yi ba,
na san dai dole zamu kwana don haka kaya kala
biyu na dauka, da katuwar ambulan da na saka
takarduna na makarantun da na yi (original
certificate).
Umma na shigowa na tare ta da farin ciki, na fara
shaida mata abin da Lamijo ta fada min yanzu.
Sai ta
tabe baki ta harare ni. Ta ce, ''Ni ba a zaman
munafunci da ni da cin amana, biri ya yi kama da
mutum, kwana biyu sai na jiyo ki a daki kina ta
waya wanda a da ba kya yi.
To ni lafiya nake zaune da MAKWABTANA ba zaki
zo ki raba ni da su ba. Idan kin san irin haka zaki
yi ta yi, to ki hada kayanki ki yi gaba, shegen
kwashekwashe ne da yarda irin na Lamijo ta
kwaso ki daga cewa wata daya an shude watanni
uku..
Ba ta rufe bakinta ba, sai na ji jiri ya kwashe ni
don tashin hankali. Na laluba bango na jingina na
zauna
na rike kai da hannayena biyu na takure ina ta
addu'a Allah Ya yi min agaji, dan na shiga garari,
na shiga masifa. Ba ni da mafita sai Allah ne
kadai zai fitar da ni.
Na kasa magana don ba ni da bakin da zan yi
mata bayanin komai ta yarda da ni. Ba ni da
masaniya a
bisa wayar dare da ta ce ina yi, bayan Lamijo
babu mai kirana a duniya, ni ma ita kadai nake
kira.
Sabon layi ne na siya saboda MAKWABTANA da
kawayena na Kaduna suna ta kirana suna yi min
maganar Abdul-Basi, wacce ta ke tayar min da
hankali, don haka na karya layin na watsar....
Umaimah ta ci gaba da sharce hawaye. Abdul-
Sabur ya sake luntsomowa cikin tausayinta,
kallonta kawai ya tsaya yana yi, yayin da
zuciyarsa ta ke suya tana konewa.
Yayin da Faduwa ce mai karfin halin yin magana.
Fadi ta ke, ''Allahu Akbar! Sannu yarinya, kin sha
takaicin rayuwa ashe.
Umaimah ta cije lebe ta kasa ci gaba da magana,
har sai da ta dauki lokaci mai tsawo ta yi ajiyar
zuciya, ta ci gaba da cewa.
''Rayuwa ke nan tana da wahala, fatanmu dai mu
gama da duniya lafiya. Yaro ya ji dadi idan na
tuna
sanda nake karama ban san bakin ciki ba. Ga
uwa ga uba, ga *yar uwa, ga dan uwa, ga kawa
ga saurayina.
Ba ni da aiki sai rawa da waka, walwala da
nishadi kullum amma dubi lokaci guda Allah Ya
kwace duk
wannan farin cikin ya koma kadaici, ku san kowa
nawa ya kare, ba ni da komai, ku san kowa ya
tsane ni. Allah mai yadda Ya so da bayinSa. Na
gode maSa a kowanne hali Ya bar ni a ciki.
Abdul-Sabur ya gyada kai, ya ce, ''Kinyi gaskiya
yarinya, Allah Yana jarrabar bayinSa ta kowacce
hanya. Ki ci gaba da tawakkali Allah Zai yaye
miki komai da izininSa, Ya hada ki da madadinsu,
Ya dawo miki da wasu daga cikin farin cikin da
kika rasa.
Umaimah ta gyada kai cikin gamsuwa, ta ce,
''Haka ne, na gode.
Faduwa ta ce, ''Yaya na ga kuna kokarin
kammala labari alhalin ba ki gama ba mu karshen
labarin ba. Yadda aka yi kika zo Malaysia da
rabuwarku da su.
Umaimah ta ce, ''Ai kawai na fuskanci Ummar
Lamijo ta gaji da zamana so ta ke ta kore ni, *yar
ce
take tausarta kullum. Na shiga daki na kwanta
babu barci, sai tunani da kuka har asuba.
Na tashi na shirya da sassafe ina jiran isowar
Hanif da Babansa. Karfe bakwai da rabi a cikin
gidan ta yi musu, suka iske Umma a zaune a
tsakar gida, ni kuma na gama shara ke nen. Muka
gaisa da su na dauko jakata na rataya na
durkusa na yiwa Umma sallama ta amsamin da
kyar. Sai ta dinga fada tana sake nanatawa 'a yi
dai a hankali, kuma ko me mutum zai yi yayi bisa
amana.
Da alama dai surukinta bai fahimce ta ba, amma
ni na fahimci abin da ta ke nufi, tunda na zama
maci amana zan kwacewa Lamijo miji ke nan. Shi
kuwa bawan Allah hidima yake yi min saboda
dansa da matarsa da yake matukar son abin da
su ke so. Muka tafi hanyar Abuja cikin
hadaddiyar mota CRB ruwan zuma, sabuwa ce
Gar! A ledarta, sai kamshi da sanyin AC ke tashi.
Hanif da mahaifinsa suna ta
farin ciki annuri fal a fuskarsu, ina baya ina yake
da kyar nake kakalo hira da dariya, amma fa
hawaye
na ke sharcewa a boye. Ba mu karasa Abuja ba
sai Lamijo ta kira shi, ta dinga zazzaga magana
cikin daga murya, sai na ga ya kalle ni ta madubi
yayin da ya ce bari zai kirata idan mun isa, yana
tuki ne.
Ya yi sauri ya katse wayar, tun daga lokacin na ji
ya daina magana, da alama ransa ya baci, jikinsa
ya yi sanyi, sai na shiga fargaba kada fa zuga
Lamijo suka yi ta shiga zargina.
Kai tsaye muka wuce Federal ministry of
education daga shigarmu Abuja, ba mu bi layi ba
muka bibbiya aka buga mana tambari a jikin
takardunmu (stamp) shaidar zamu yi karatu a
kasar waje. Sannan muka wuce Ministry of forin
affairs suma kai tsaye ya wuce da mu
kasancewar yasan wasu daga cikin ma'aikatan
don ya yi aiki sosai a wurare daban-daban a nan
Abuja.
Kafin la'asar har mun gama ya wuce da mu
gidansa, da yake unguwar Asokoro. Gida ne
babba da get ga wajen ajiye motoci, manyan
faluka biyu da wajen cin abinci (dinning area),
dakuna hudu
kowanne da bandakinsa sai katon kicin guda
daya. Mai aikinsa inyamuri da matarsa a boy's
kuarters, su ne masu share gidan.
An share tsaf an goge, an yi mana girki an jera
akan tebur dan sun san da zuwanmu.
Muna shiga Alhaji ya nunawa kowannenmu daki
daya nasa da bandakai a ciki, kowannenmu ya
shiga don ya kimtsa kamar wanka da sallah. Da
muka idar muka fito dinnin table don cin abinci
saboda muna jin yunwa. Kunyar Alhaji da ladabi
ya hana na zauna akan teburi daya mu ci abinci,
suka yi ta rokona na ki hawa mu ci, sai Alhaji ya
ce, Hanif ya zuba min ya kai min dakina. Na
shiga daki na ci abinci yayin da nake jiyo hirarsu
a falo. Can na ji Alhaji yana Magana a waya yana
cewa. ''Lamijo me yake faruwa ne, wai Umaimah
ba kawarki ba ce? Waye ya zuga ki? To ni
gaskiya bana son haka, kuma tafiyar nan kamar
ta tafi ta gama tunda an gama yi mata komai.
Idan kinga ba ta tafi ba to Hanif ma ba zai je ba
ke nan. Haba me yasa ku mata ba ku da tunani
ne?
Tunda abun naki har da zargi to bari na bar
gidan na je hotel na kwana. Na bar ta da Hanif
su kwana, gobe zamu dawo da sassafe har mun
gama abin da zamu yi''.
Inji Alhaji yake karadi a waya shi da matarsa,
kawata, aminiyata Lamijo, a kokacin da take
tuhumarsa, ta ke zargin kada ya ce yana sona ko
mu ci amanarta a Abuja.
Sai na dafe kirji na mike tsaye yayin da na ji
tamkar ba a raye nake ba, dama na hadiyi zuciya
na mutu mana na huta. Anya kuwa lafiya irin
wadannan bala'ai suke ta rufto min?
Duk mutumin da na amincewa sai ya ci amanata.
Na tambayi kaina da kaina, yayin da nake
magana a bayyane. 'Me yasa kowa ya tsane ni
yanzu alhali kuwa ada kowa yana sona?
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Na durkusa ina fada yayin da kuka ya hana ni
sakat, na kasa ci gaba da cin abincin, ga yunwa
ina matukar ji ko abincin safe ban ci ba, sai dan
lemo da Alhaji ya siya mana a hanya.
Hanif ne ya yi ta kallonsa a falo yana ta
nishadinsa,
amma ni kadai a dakina ina ta juyi babu barci
saboda gagarumar fargaba da kunar zuci. Yadda
na ga dare haka na ga safiya na tashi da wuri na
yi wanka na takure a lungu gado. Hanif ne da
sassafe yake buga min kofa, wai na fito na zo mu
karya kumallo, Babansa ya yi waya ya ce mu
shirya da wuri ga shi nan zai zo mu wuce
Gomben.
An shirya mana abin karin kumallo na gani na
fada an jera akan dinnin table. Tura abincin nan
kawai nake yi a cikina ba don ina jin dadin ci ba,
sai saboda kada yunwa ta kashe ni ko kada Hanif
ya gane ina cikin halin damuwa. Hira kawai yake
yi min cikin farin ciki da dokin zamu je Malaysia,
sai ya ce da ni ya ga kamar yanzu ban damu ba
alhali a da har na fi shi dokin tafiya. 'Eh ko 'a'a
kawai nake ta binsa da shi har muka kammala,
sai muka ji tsayuwar motar Alhaji ya iso. Ya aiko
ya ce ace mu fito ba zai shigo ba.
Muka debo kayanmu muka fito muka iske shi a
zaune a cikin mota, gaba daya ya daina wannan
fara'ar tasa. Cikin sanyin jiki na gaishe shi ya
amsa min cikin sanyayyiyar murya, muka shiga
mota muka tafi.
Hanif ne kadai mai walwala da surutu ni da
Babansa dai to ga mu nan ne dai kawai babu mai
son yin magana.
La'asar sakaliya suka sauke ni a kofar gidan
Umma na yi musu godiya da sallama na shiga
gida su kuma suka wuce.
Na yi mata sallama, fuskarta babu fara'a ta amsa
min, na shaida mata mun iso, ko ta kalle ni ma ta
dauke kai. Sumi-sumi na shiga dakina sai na
firgita da na ga an hada min dukkan kayayyakina
da na baza a gidan a lungu daya. Kamar
takalmana, sosona daga bandaki da dai sauransu.
Katifar da na lallaye da zanin gado an jingineta a
tsaye. Daga nan jikina ya ba ni zamana ya zo
karshe a gidan nan, don haka na shiga tunanin
inda zan nufa,
Abu na farko da na fara yi shi ne, na ware kayan
da na fi so kamar kala biyar na bar sauran don
ban san yadda zan iya kinkimar rusheshiyar
akwatin nan na shiga gari ba. Na zuba a karamar
jaka, soso, brush da makilin gami da takalma
kala biyu. Saura na dura su a cikin babbar
akwatin na rufe na jingineta a gefe. Na shimfida
katifar na hau na zauna a hankali. Ina cikin
fargaba musamman da na ji tahowar Umma.
Tana shigowa sai ta harare ni ta harari katifarta
da na shimfida ta tabe baki ta ce, ''Umaimah,
yanzu
dare ya yi idan Allah Ya kaimu gobe ki shirya da
sassafe ki koma garinku ki jira fitowar tafiyarku a
can. Bana son zamanki a gidan nan tunda kin
fara jawo min fitina, ina tsoron rayuwa,
musamman *yar
autata da nake son dorewar zamanta a gidan
mijinta.
Ta zaci zan razana da maganganunta sai taga ko
kadan ban rude ba. Na ce mata, ''To Umma Allah
Ya nuna mana goben lafiya, na gode ma da
karamcin da aka yi min, Allah Ya saka da
alkhairi''.
Ta fice a fusace, tana fita hannuna yana
karkarwa sai na kira Lamijo don na sanar mata
gobe zan koma gida. Na yi mata godiya da
sallama na roketa idan tafiyarmu ta zo ta
sanarmin ta waya. Don na ga akwai waya a
Dukku zan dinga fitowa ina kiran ta kullum ina jin
labarin tafiya.
Sai taki amsa wayar, har ta fara katsewa
(rejecting), ina kira sai ta katse. Muka dinga haka
fiye da sau
goma, mamaki cike da zuciyata. Daga karshe sai
na tura mata rubutaccen sako na yi mata duk
wadannan bayanai. Har gari ya waye ba ta ba ni
amsa ba. Na daina kuka saboda masifar ta yi
masifa, addu'a kawai nake yi ina neman mafita,
ina so Allah Ya musanya min da muhallin da ya fi
irin wanda nake ciki daraja da kwanciyar hankali.
Na shirya na fito rataye da karamar jakata na bar
babbar a dakin. Na durkusa a gaban Umma na
gaisheta..
Na ce, ''Zan tafi Sai ta hararenim ta ce, ''Ban
ganki da kaya ba?
Na yi murmushin takaici, na ce, ''Zan je na samo
mai tasi ne yanzu zan dawo. Ta tabe baki ta ce,
''Kina da kudin motarko?
Na yi murmushi na ce, Eh Ban sani ba ko idan na
ce ba ni da shi zata ba ni ne ko ba banin zataiba,
oho. Ba ni da kudin kirki a jakata, *yan canji ne
kawai wanda bai wuce ya kai ni tasha ba.
Dan Aunty..
MAKWABTAKA 23
Ina fitowa na ci karo da Salame da mijnta Umar,
har yau inajin haushin kallon banzar da ta yi min,
ta yi tsaki da tsartar da yawu ta bude gaban
motar mijinta ta zauna, ta daka masa tsawa. Ta
ce, ''Ja mu je mana, wa kake jira?
Ya fisgi mota ya tafi suka bar ni, sai a lokacin na
fara kuka. Ina tsaye a kofar gida na dubi gabas
da yamma, kudu da arewa ban san inda zan nufa
ba.
Na yi ta tafiya da kafa na nufi hanyar tashar
garinmu da nisa sosai, amma da kafa na je.
Sannan na tuna ba ni da kudin da zai kai ni
garinmu.
A bakin tasha a kofar shagon wata tsohuwar
mata mai siyar da abinci da ma'aikatanta da
yawa, na zauna na huta. Sannan na karasa
gabanta na durkusa a gaban Hajiyar na gaishe ta
ina hawaye,
na sanar mata ina so na dinga tayata aiki, na ce
amma ba ni da wajen zama.
Da farko ta ki amincewa, amma da kawarta ta ce,
''ki dauki kyakkyawar yarinyar nan ko don saboda
ita ma za ki sami samu masu saya kin san
mazan nan suna da son kyawawa. Ai wannan
yarinyar kadara ce kar ki bari ta kubuce miki. Sai
na ji zuciyata ta harba, na kasa gane abin da
matar nan ta ke nufi. Nan da nan Hajiya babba ta
yarda ta umarce ni da na shiga cikin shagon da
kayana, sai da magriba suke tashi sai mu
dunguma mu tafi gida.
Na shiga shagon kujeru ne da tebura yayin da duk
masu dafa abincin sun yi kama da karuwai, suka
hau yi min kallon banza saboda hassada. Dana
ajiye jakar kayana a loko sai na koma bakin
baranda na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login