Showing 93001 words to 96000 words out of 130520 words
Chapter 32 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
zai yi
mata kayan gida gaba daya da kayan sakawa.
Sauran tazurai SAI GOBE DA YARDAR ALLAH ZA
KU JINI DA CI GABA.
MAKWABTAKA 40
Gidan amarya yayi kyau sosai kowa yana ta
yabawa game da yi musu fatan Allah Ya bada
zaman lafiya da zuriya ta gari, yayin da bako zai
halinsa, na kusa da na nesa suka fara tarkata
kayansu zasu koma gidajensu.
Umaimah da sauran kawayen Faduwa da suka
taho daga Malaysia suka kama hanyar komawa,
babu abunda suke yi ahanya sai yabawa da
wannan biki daya kayatar amma abunda suke
tambayar junansu sai suka rasa amsa, gashi sun
manta basu tambayi wadanda abun ya shafa ba.
Tambayar ita ce a ina amarya da ango zasu
zauna,
a Malaysia ko a Cairo?
Shin Faduwa zata bar hamshakin aikinta ta biyo
Sagir Cairo ko kuwa
shine zai baro aikinsa ya biyo Faduwa Malaysia?
Oho! Su dai suka sani shawara ta rage ga mai
shiga rijiya, wuyarta daman kafin ayi ne tunda
aka yi ta kwana gidan sauki duk yadda suka yi
yayi daidai.
Asuba ta gari Faduwa Sagir!!!
Faduwa da Umaimah suna yin waya akai-akai,
bayan dawowarta Malaysia ta yi mata godiya
hade da ban gajiya. Faduwa tana kira su gaisa
idan taga missed calls din Umaimah saboda wasu
lokutan Umaimah tayi ta kiran wayarta bata
dauka ba. Bata yi mamaki ba haka bata damuwa
saboda ta san yanzu Faduwa bata da lokacinta
sosai ta sami ango tana can tana yi masa labarai
kala-kala.
Allah Sarki so, kauna, bege!!! *
Babu abunda Umaimah ta sa a gaba yanzu sai
abu guda biyu kwarara, na farko: ta na so ta kara
zagewa wajen yin karatu dan ta fito da sakamako
mai kyan gaske.
Na biyu: tana sake-saken in da zata nufa bayan
ta kammala karatunta. Shin ta yi zamanta a
Malaysia ko ta koma kasarta tare da abokan
tafiyarta?
Kasancewar iyakacin abunda gwamnati ta umarce
su kenan su yi shine karatun digiri na tsawon
shekaru uku daga nan aka umarce su da su dawo
gida.
Visar su ma daga shekaru ukun ta kare haka za'a
dakatar da turo musu kudin ciyarwa, da kudin
makaranta. Sannan makudan kudin da Baban
Hanif ya ke ambalo mata ita da dansa da zarar
sun gama
zai daina. Babu kudi kuwa babu magana, babu
kuma zama a Malaysia dan sai da kudi. Sai ta
tuna ai tunda akwai sakamakon jarabawarta a
hannu zata iya fita neman aiki a kasar ta yi
zamanta kamar yadda Dr. Faduwa tayi, sai ta
tuna da nasihar da Abdul-Sabur yayi mata ta
karshe da ya ce ta koma gida cikin danginta ta
zauna bayan ta kammala karatunta saboda ta yi
kankanta ace tana zama a wata kasar ita kadai.
Abarkacin dinbun son da take yiwa Abdul-Sabur
ko suna tare ko basa tare, ko yana raye ko bayan
ya mutu, zata yi masa biyayya ta girmama
maganarsa. Nan da nan ta ji zuciyarta tayi
amanna zata bi abokan tafiyarta da zarar sun
kammala karatunsu.
Sannan ta koma tunanin yanda rayuwarta zata
kasance nan gaba idan ta koma Najeriya. Shin a
Dugge zata zauna ko a cikin Gombe zata kama
haya?
Anya kuwa za'a bar ta tayi zaman kanta?
Kai! Abunda kamar wuya, ba za'a bar ta bama
saboda ba al'adar Hausa Fulani ba ce wannan
Anya kuwa zata iya zama a Dugge kacokan?
Ba rayuwar kauye ba ce ta dame ta ba yadda
zata zauna a cikin *yan garin musamman
Matawata a matsayin Makwabciyarta, Inna da
Nene a matsayin iyayenta. Anya zata dauki
nauyin kyara da habaice- habaice da suke yi
mata ada?
Anya kuwa zata iya surfe, daka da bakace da cin
hatsi da dawa kullum?
Abun fa yana da wuyar jurewa bayan ta saba
figar kaji ta dawo tana figar zogale da yakuwa,
matar
data saba da shan juice da ruwan roba garai-
garai ta koma shan ruwan rafi bakinkirin da
kazanta. Wannan ci baya da yawa yake,
rayuwarma ba iri daya ba ce idan aka dawo
maganar ruwan lantarki
babu itama kwata-kwata ma balle ayi zancen
cajin waya, jin fanka ko Ac, babu setilait, balle
ruwan sanyi na firij.
"Haka Allah Ya yi da ni, bani da mafita sai yadda
Ya yi da ni. Tabbas akwai matsala bada wasa
nan gaba. Inji Umaimah ta fada a bayyane. Irin
wannan tunani shi ya sa Umaimah duk ta rame
sosai.
*
Faduwa bata dawo Malaysia ba sai da ta shafe
watanni uku cur a Cairo Allah ne kadai Ya san
dadin bakin da tayi a wajen aiki har aka bar ta ta
dade haka. Sai gata a gidan Umaimah kwatsam
ba zato ba tsammani ta ganta, nan da nan ta
cika da mamaki me hade da farin ciki. Tabbas
aure yana gyara mace, kana kallon Faduwa ka
san hankalinta ya kwanta, dan ta yi wasai bata
da wata matsala a rayuwarta yanzu. Kuma ko
ba'a fada maka ba kana kallonta zaka san tana
dauke da juna biyu. Ai
komai lokaci ne, in dai da rai ba'a fitar da
tsammani.
Faduwa tayi ta bawa Umaimah labarai masu dadi
irin yadda take zaman lafiya da mijinta da kuma
surukarta. Dimbun so, kauna kulawa Sagir yake
nuna mata, babu abin da ta rasa. Yanzu ma
lallabowa ta yi tayi musu dubara ta bar aiki a
Malaysia amma sai ta yi aikin *yan watanni
kadan sai ta hada ta kaura wajen mijinta. Aiki
kuwa zata yi shi acan daman Gwamnatin kasarsu
ce ta dauki
nauyin karatunta, duk da Egypt ba zasu biya ta
yawan kudin da ake biyanta a Malaysia ba.
Ba damuwa mijinta ya yi alkawarin zai dinga bata
fiye da abunda gwamnatin Malaysia take biyanta
duk wata.
*
A satin da dukka jami'oin su Umaimah zasu fara
zana jarabawar karshe suka yi shawarar su hadu
a Hostel din su Aisha Bingyal ayi addu'oi na
musamman dan neman sa'ar jarabawa, da kuma
fatan Allah Ya mayar da su gidajensu lafiya su
sami iyayensu lafiya, Allan kuma Ya taimaki
gwamnatin Gombe da kasarsu Nigeria gaba daya.
A lokacin da suka hallara gaba daya sai aka yi ta
gaggaisawa duk da yawansu sun san junansu
daman suna ziyartar juna kuma suna yin waya
akai-akai amma irin Umaimah duk bata san su
ba sai *yan kadan ta sani rin su Hanif, rabonta
da wasu tun ranar da suka hawo jirgi suka zo
nan kasar. Sai yanzu ta tabbatar bata kyauta ba,
kuma ta yi farin ciki da Allah Ya hada ta da
Abdul-Sabur har yai yaki waccan bakar akidarta,
dan badan
yanzu ta gyara halinta ba da ko wannan taron ba
zata zo ba. Itama kanta ta san bakin hali ne take
yi
a baya ba mai kyau ba ne. Sai gata yanzu a cikin
*yan uwanta tsundum suna ta hira ana ta
musanyan lambar waya. Zama da Faduwa ya yi
mata fa'ida dan ta sami ci gaba na yin faram-
faram
da mutane, a gaban kowa ka tashi kayi magana.
Bayan an bude taro da addu'oi sai aka rarraba
kur'anai aka yi ta karantawa har tsawon awa
guda, sannan aka sami yaro daya ya tashi ya
dinga zaiyano bukatunsu da suke a wajen Allah
sauran kuma suna amsawa da 'amin'
Sannan kowa ya tashi daya bayan daya ya
gabatar da kansa da kuma makarantar da yake
da kuma abunda yake karanta sannan duk wani
shawara ko wani ra'ayi sai ya tashi ya fada. Su
dukka suka hada baki su roki mai girma
gwamana ya kara musu watanni uku bayan sun
kammala karatunsu don su jira sakamakon
jarabawarsu kuma suyi
bikin yaye dalibai (Graduation ceremoney).
Saboda da yawansu idan suka koma basu da
kudin jirgin da zasu dawo wannan biki. Duk da
bikin ba dole ba ne amma tarihi ne idan aka ajiye
hotuna *ya*ya da jikoki zasu gani.
Aka ci, aka sha, sannan kowa ya kama hanyar
garinsu, akasarinsu duk suna jan mota kadan ne
babu mota a hannunsu idan baka da ita sai ka
shiga ta abokanka ku tafi. Amma gaba daya
motocin na haya ne, akwai wuraren da akayi na
musamman dan bada mota haya, yini guda Riggit
saba'in, kwana daya Riggit dari da hamsin.
Umaimah ce kadai Allah Ya taimaka ta mallaki
motarta. Ko yaya zata yi da motar idan ta tashi
tafiya?
Ita ba kwali ba ce balle a linke a saka a kaya ba,
sannan idan za'a aunta a container kudin awon
yayi linkin balinkin kudin da aka sayi motar.
Allah Ya nuna mana dai ranar tafiyar nan mu ga
yadda za'a karke da motar nan.
Jarabawa ta kankama har sati uku zasu yi suna
abu daya, dan haka Umaimah bata baccin daya
wuce awa uku a rana sai karatu, dan haka kallo
daya zaka yi mata kaga kunburi a idanuwanta.
Babu inda take zuwa daga gida sai makaranta, a
sati ma sau daya take kunna wayarta ranar lahadi
tayi magana da *yan gida. Ta shaidawa duk wani
mai kaunarta daya taya ta addu'ar samun
nasarar cin jarabawa. Itama addu'a take kuma
karatu take tun
karfi, dan karatune kadai gatan ta a duniya. Ita
talaka kuma *yar gidan talakawa likis, ga babu
mijin da zai tsaya mata. Wa zai bata in bata yi
karatun ba?
Sanda take da mijin ma a dalilin rashin aiki da
sana'a ne ya sa aka tsane ta. Aka yi mata
wulakanci, dole ta yi karatu ta sami aikin da zata
dogara da kanta, dan ta agaji iyayenta da *yan
uwanta na ruga wadanda babu abinda suka sani
daga fura, nono sai dawa da hatsi.
Allah Ya yi jagora Umaimah Bello!!!
Ranar da Umaimah ta fito daga jarabawar karshe,
sai ta ji tamkar an zare mata kaya daga jikinta ta
ji ta zama sakayau babu wani nauyi akanta
kuma.
Tana da kyakkyawan zato ta gama tsarge gaba
daya jarabawar data zana, bata tunanin akwai
wata
tambaya da bata amsa daidai ba ko kuma wacce
ta amsa sama-sama.
Fyedewa take daga kai har wutsiya, bata
marmarin ta sami Credit sai dai Distinction.
Sun sami tabbacin Gwamna ya amince su kara
watanni uku har su karbi takardar sakamakonsu a
hannu. Yara suna ta murna wadanda iyayensu
suka yi musu alkawari zasu zo har Malaysia bikin
Graduation dinsu, ita bata da wanda zai zo mata
amma bata damu ba saboda tasan Baban Hanif
zai zowa dansa, zata je wajensa dan shine uwa
kuma uba a wannan zaman karatun.
Gwamna ya ci gaba da turo musu kudin ciyarwa
na wata-wata daya saba turo musu, kwatsam
tana zaune a gida sai ta ji sako ya shigo wayarta
tana dubawa taga Alert ne daga banki, Baban
Hanif ne ya turo mata da kudin daya saba ba su
duk shekara amma wannan karon gida hudu ya
raba miliyan, wato dubu dari hudu da hamsin-
hamsin ya turawa kowannensu, kasancewar ba
zasu sake shekara ba za su koma.
Farin ciki ya rufe ta dan daman tana da bukatar
kudin sosai, duk da tana da wadataccen kudin da
ta boye a banki, a cikin sabon nan dai take so ta
yi tsaraba ta tsakuri wasu kuma ta hada da
wadancan na banki ta yi guzurin na cin abinci a
Dugge dan babu me bata a can. Tana shirin kiran
Baban Hanif tayi masa godiya sai Hanif ya kirata
da murnarsa zai shaida mata yaga alart, an turo
masa da kudi. Sai ya
ji itama tana murna ta shaida masa ta ji nata
alart din. Suka taya juna murna suka ce zasu kira
Baba su yi godiya.
Umaimah ce ta fara cin sa'ar samun Baban Hanif
a waya ta dai-daici yana ofis a lokacin, ta yi
masa
godiya gami da manyan Addu'oi na fatan alkhairi
har sai da ya ji zuciyarsa ta karaya kamar zai yi
mata kuka. Cikin kuka ta ke shaida masa irin
farin cikin da yake saka ta da yadda ya ceto
rayuwarta harta zama mutum sosai, ta zama
*yar gata har mutane suke yi mata kallon kamar
wata *yar gidan hamshakin mai kudi ce, alhali
*yar talaka ce likis daga Ruga.
"Ba komai, kada ki damu, ki daina kuka
Umaimah. Amsar da Baban Hanif ya ke ta fada
kenan. Daga karshe suka yi sallama suka kashe
waya.
Tun daga ranar Umaimah ta shiga lissafin
abubuwan daya kamata ta saya na tsaraba, ba
karamin kaya zata loda ba idan ta ce kowa sai
tayi masa tsaraba a garinsu. Dan *yan rugarsu
babu wanda ba zai saka ran samun tsaraba ba,
kuma ko me takai musu duk rashin tsadarsa zasu
yi farin ciki da shi don basu taba samun irin sa
ba.
Ta dauko biro da takarda tayi ta rubuto sunayen
wadanda zata yiwa tsaraba da kuma jimlar kudin
da zata kashe. Ai abun ne da yawa wai mutuwa
ta shiga kasuwa.
Abu na farko da take taka tsan-tsan shine duk
yadda za'a yi sai ta raba kudinnan ta adana rabi
ta
dawo da su Nijeriya, shi zata ajiye tana kashewa
dan kada ta tagayyara, in yaso sauran ta yi
tsaraba da su. Haka kuwa aka yi a nutse take
shiga kasuwar China town, kasuwar Nilai wacce
akafi sayar da yadiddika, da kuma shagunan
bakin hanya dan sunfi arha fiye da a cikin Malls
duk da ba su kai na cikin Malls kyau da kwari ba.
Ta ci sa'a kuwa a lokacin shaguna duk sun rage
kudin kaya ma'ana suna 'sales'. Dan haka ta
sami kaya da araha sosai,
ta saisayi takalman 'Bincci' cikin rahusa, ta
sayawa Baffa da Sabitu yadina kala goma-goma
da takalma
kafa biyar-biyar, tabbas suna da matsalar suturu.
Ta sayawa Dagacin garinsu yadina masu kyau
kala biyu da takalmi na sarauta. Sai ta sayi
yadiddikan maza masu yawa wanda zata rabawa
mazan garinsu. Baban Hanif kuwa tsadadden
yadi ta saya
masa gami da agogo mai tsada da turare
(disigner)
duk da tasan komai yana da shi fiye da wannan.
'Yaba kyauta tukuici kuma 'zo ka ci tuwon har ya
fi tuwon dadi. Inji masu iya magana.
Nene da Inna ma atamfofi ta saya musu kala
bibbiyu zata hada musu da takalma, sannan ta
jido alewowi masu yawan gaske, sarkoki da *yan
kunnaye, zobuna da turarruka masu rangwamen
kudi na tsaraba.
Ta kashewa Babangida da Bilal kudi sosai saboda
a manyan Malls tayi musu sayayya, kaya *yan
Ingila masu tsada ta sayawa kowannensu riguna,
wanduna da takalma kala biyar-biyar gami da
alewowi masu tsada na musamman saboda su
*yan birni ne tasan sun san duk irin wadannan.
Bata daina siyan tarkace ba har sai da aka shiga
satin da zasu tafi, ta fara hada kaya a cikin wasu
tafka-tafkan jakunkuna guda uku, bayan nata
manya-manya guda uku.
Sannan ta shiga yiwa kanta da kanta sayayya,
duk wani abu na amfanin yau da kullum sai da ta
saya saboda kada ta je can ta rasa, lamar su;
Suturu, Makilin, man shafawa, man wanke kai.
Kayan kwalliya irin su: hoda, jan baki, jagira, man
lebe, su ma *yar karamar akwati ta cika taf. Ta
daure kayanta tsaf kafin ranar Graduation dinsu,
ta shiga binciken inda zata kai ta auna kayanta
zuwa
kasarta. Sai da aka shaida mata bata da
damuwar awo tunda su dalibai ne kuma an gama
jarjejenitar da kamfanin jirgin da zai kwaso su
za'a barsu su wuce da kayansu duk yawansu.
Sannan Gwamna zai aiko da wakilansa su zo su
tafi da su, zasu san yadda za'ayi kowa ya wuce
da kayansa koda kudi ne zasu biya musu, dan
kudi ba matsalarsu ba ne a gwamnati.
Kowacce Jami'a ranar da za'ayi nata bikin yaye
dalibai daban ce amma dai dukka a cikin sati biyu
za'ayi kuma dukka makarantun na birni, dana
kauye a cikin babban birnin Malaysia zasu yi
Kaula Lumpur, cikin manyan Hotels din da suke
cikin Bukit bing tang.
MAKWABTAKA 41
Ranar talata za'ayi na makarantar su Umaimah a
Hotel din da su Abdul-Sabur suka yi na su. Wato
'J.W Marriotte. Dan haka tun ranar lahadi iyayen
yara da jami'an gwamnati suka iso birnin
Malaysia suka sauka a manyan Hotels anan cikin
'Bukit bing tanga.
Shirye-shirye su Umaimah suke yi tun kafin ranar
ta zo bana wasa ba.
Abubuwa sunyi mata yawa har bata samu ta je
ta gaishe da Baban Hanif ba a inda ya sauka sai
dai Hanif ya hadasu a waya sun gaisa. Ta shaida
masa ita ce aka dorawa nauyin yin jawabi a
wajen shiyasa take ta zuwa gwaji kullum a
makaranta ta ke yini. Yayi farin ciki dajin haka
kuma ya ce kada ta damu ta ci gaba da yin abun
da
yake gabanta.
Ranar talata Daliban nan dukka guda dari, iyayen
wadanda suka zo, da wakilan gwamna guda
ashirin sune reras a zaune a gaba. Sai ka rantse
a Nigeria suke kuma a Gombe yadda yaren
fulatanci da Hausa suke tashi a wajen. Saboda a
kungiyance suka shigo babu zancen sai su
Umaimah sun raba musu katin gayyata.
Wadannan *yan Nigeria na bangaren Gombe
kadai,
akwai *yan Nigeria daga garuruwa daban daban
wadanda suma gwamnatinsu ta biya musu ko
iyayensu. Wasu daga arewa, kudu yamma da
gabancin Nigeria. Suma da iyayensu, sauran
kuma fararen fata ne. Taro yayi taro, an cika
sosai har ya fi na su Abdul-Sabur cika saboda
daliban da suke digiri sun fi masu Master da PHD
yawa.
Sai da kowa ya hallara sannan aka bayar da
sanarwar shigowar dalibai wadanda suka taru
domin su wato su Umaimah Bello. Tana daga
gaba-gaba sanye suke da riga da hular
Graduation. Suka shigo a layi yayin da aka dinga
daukarsu a hotuna,
ana ta tafawa, har suka zo suka zazzauna a inda
aka tanadar dominsu.
Jawabai daga bakunan shugabannin kasar da
shugannin makaranta, sai caraf aka kira sunan
Umaimah Bello wacce zata zo tayi jawabin
maraba da zuwan baki sannan tayi bayani game
da wani cos data iya shi sosai fiye da sauran
dalibai,
shekaru biyar da suka shude ba'a taba samun
dalibin daya ci A1 a kos din ba sai Umaimah.
Bayan mai gabatarwa ya wasa ta, ya kodata, ya
yaba da kwazonta, sai ya bukaci data fito ita da
wani dan Indiya mai suna Muhammad Parwez,
suka fito tare suka hau kan stage. Ihu da tafi
kawai ake tayi yayin da ake daukar su a hotuna
tamkar hasken walkiya, kai ka ce ruwan sama
za'ayi hadari ne ya hado walkiya take ta
haskawa. Ba bakake kadai ba ne suke daukarsu a
hoto ba har da fararen fatar ma suna ta
daukarsu.
Babu wanda Umaimah take ganewa a wajen
saboda idanuwa sun yi mata yawa amma hakan
bai sa ta rude ba, saboda zama da Faduwa yasa
ta goge wajen iya magana a gaban kowa. Tabbas
Umaimah da Parwez sun burge kowa a wajen
yadda suke turanci da kuma bayanai akan
Computer Project Management' kai ka ce su suka
kirkiro Computer soft were. Lallai sai yanzu ta
tabbar da Faduwa ta iso wajen nan data ganta a
gabanta, ta hau har kan stage tana daukarta a
hotuna. Da suka kare sai suka koma suka zauna
ana ta tafa musu.
Baban Hanif ya ji dadi sosai, ya ji Umaima
tamkar *yarsa ta cikinsa. Ya godewa Allah daya
bashi damar taimakonta har ta sami ilimi, yarinya
ashe mai hazaka ce a kunshe a cikin Rugage, da
a haka
rayuwarta zata kare a banza. Bai yi nadamar
makudan kudin daya kashe mata ba.
Sannan aka fara kiran dalibai da suka fito da
sakamako mafi kyawu, da aka kira dalibi na farko
Umaimah Bello ce ta biyu wacce ta fito da 1st
class yayin da aka hautsine da murna ana ta
tafawa,
daukar hotuna har ya fi na dazu.
Allahu Akbar sai Umaimah ta fashe da kukan dadi
bayan data karbi sakamakonta a hannu, ta juyo
ta
kalli dubban jama'ar da suke taya ta murna, sai
ta daga musu kwalin sama ta nuna musu. Ta
tabbatar
banda Allah babu wanda zai zabi talaka likis, *yar
gidan talakawa, bakauyiya Ya bata wannan
matsayi da daukaka. Banda Allah babu wanda zai
zabe ta ita kadai daga cikin *yan kasarta ya ce ta
fi
kowa.
Ta tuna Baffanta, Sabitunta, marigayiya
Yafindonta da marigayiya Nasibarta yadda suka
yi rayuwarsu a baya. Tabbas Allah Ya so ta da
rahamarsa shiyasa ya raya ta dan Ya bata
babbar kyauta, ko a mafarki bata taba zaton zata
taka wannan matsayi ba.
Babu abinda take fadi a fili da kuma a boye sai
kiran
''Alhamdulillah''
Sai a lokacin ta kalli jama'ar da suke tururuwar
daukanta a hotuna, ta gane Faduwa, ta gane
Hanif, sannan da ta sake wurga ido gefenta sai ta
hango wani mutum wanda ko a mafarki ta ganshi
tabbas bacci zai katse saboda razana. Nan da
nan tayi sauri ta kawar da idanuwanta daya gefen
don bata son ta sake ganinsa, sai ta yi kicibus da
wata fuska wacce take tunanin ko idanuwanta ne
suka fara yi mata gezau. Taji zuciyarta ta harba
bom! Kai kace
tayar mota ce zata fashe. Ta sake bude ido ta
dube su sosai cikin firgici da mamaki marar
misaltuwa, su dinne dai mace