Showing 105001 words to 108000 words out of 130520 words

Chapter 36 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8047

filin jirgi, wanda ya saka koriyar
shadda.
Umaimah ta yi shiru kamar mai tunani can ta ce
"Na tuno shi dogo, mai kiba, wanda suke kiransa
yallabai.
Aisha ta zabura ta ce "Eh shi, shima ya ganki ya
dasa. Kusan kullum sai yayi min waya ya
tambaya ko kin zo. Sai in ce masa zaki zo dai
baki zo ba yanzu.
Umaimah ta girgiza kai ta ce "Gaskiya suyi hakuri
ba zan iya kula su ba. Me yasa sai ni, duk a cikin
dalibai mata ga kyawawa ace sai ni kadai suka
sani za su dama.
Aisha ta kyalkyale da dariya ta ce "Ai kin fimu
kyau, gayu, iya tafiya da iya magana da turanci
shi yasa ya rude.
Suka sa dariya su dukkansu Aisha ta ci gaba da
cewa nima na hadu da guda daya tun acan
daman ya karbi lambata sunansa Mujahid. Shima
wajen kaninsa ya je Aliyu wanda yayi Inti Nilai.
Amma ni kin san ba irin ki ba ce me tsattsauran
ra'ayi, ni ina son shi, magana har ta yi nisa, ya
zo gidanmu yafi a kirga.
Umaimah ta yi dariya ta ce, "Allah Ya taimaka,
Ya barku tare, mu zo musha biki bayan mun
gama bautar kasa.
Aisha ta ce "Ai kin kai ni da nisa, kafin mu gama
za'ayi ma insha Allahu.
Ina Hanif kaninki kuwa?
Wannan yaron ya cika surutu har da cewa zai
dinga zuwa muna gaisawa, ban sake ganinsa ba.
Umaimah ta zabura ta ja wayarta ta ce, "Har kin
ma tuna min, na shigo gari ban kira Baban Hanif
na gaishe shi ba.
Daman da lambar wayarsa a cikin wayar sai ta
nemo sunansa ta kira. Da farko bai amsaba
kasancewar bai san lambar ba amma data ci
gaba da kira ba adadi sai ya dauka. Bayan sun
gaisa sai ta gabatar da kanta nan da nan ya
gane ta, yayi farin ciki da jinta a waya, ta shaida
masa ta shigo gari dazun. Yana kokarin ya ce ta
zo gidan sa ta sauka a wajen kawarta Lamijo sai
tayi sauri ta shaida masa tana gidan kawarta
Aisha Bingyal amma wani lokaci idan ta shigo
zata je.
Baban Hanif ya yi gyaran murya ya ce
"Lamabarki ce wannan?
Umaimah ta ce "Eh ita ce Baba.
Ya ce "To zan ajiye lambar, kina da labarin saura
sati biyu ku tafi Abuja bautar kasa?
Umaimah ta ce "Eh an fada min, mun yi waya da
Hanif ma dazu.
Suka dan jima suna hira sannan suka yi sallama
kafin su kashe waya kwatsam ta ji Baban Hanif
ya furta mata wata kalma wacce ko a mafarki ba
ta zaci maganar nan zata fito daga bakinsa ba.
Nan da
nan ta gigice ta dafe kirji tana ta salati a cikin
zuciyarta, hakika maganarsa ta firgitata kuma ta
daga mata hankali. Bata da mafita dan haka sai
ta amsa da "To Baba, na amince Allah Ya
tabbatar mana da alkhairi.
Saboda ba ta isa ya nemi alfarma a wajenta ta ki
yi masa ba, muddin dai bai sabawa addininta ba,
ya yi mata halaccin da babu wanda ya taba yi
mata irinsa a rayuwarta ba.
Daga karshe suka sake yin sallama ta ajiye waya
a sanyaye kai ka ce laka ce aka zare mata. Ta
dafe kai
da hannaye guda biyu tana ta karanta "Innalillahi
wa'inna ilaihi raji'un.
Aisha tambaya take, Sabitu ma tambaya yake
"Lafiya? Me ya ce miki?
Ta dade kanta a kife sai can ta dago ta dubi
kawarta cike da damuwa.
Ta ce "Aisha ina zan saka kaina? Yaya zan yi da
taron mazan nan da suka addabe ni?
Aisha ta zabura ta dafa kafadarta ta ce "Baban
Hanif ma cewa yayi yana sonki ko?
Daman ni nasan za'a rina, wai an saci zanin
mahaukaciya.
Sabitu ya ce "Wannan shi ake kira ga akuya ga
kura. Ya ya za'a yi da Lamijo kenan?
Umaimah ta ce "Kai, ka rufe mana baki maganar
manya ce wannan, kawata idan muka isa gida
zan baki labari.
Sabitu ya kyalkyale da dariya ya ce "Au haka ne
ma abun?
Ina cikin zamana zaki zo ki saka ni a cikin
maganar.
Daidai lokacin suka iso katafaren get din gidan su
Aisha, me gadi ya taso da sauri ya wangale get
sika kutsa da motar cikin gidan.
Makeken gida bangare-bangare ya kawatu da
fulawowi an kewaye gidan kai ka ce Hotel ne ba
gida ba.
Umaimah ta ce "Bari mu gaisa da su Mama sai in
yiwa Hanif waya ya zo ya tafi da Sabitu gidansu
tunda shi namiji ne.
Aisha Bingyal ta ce "A'a akwai bangaren baki
maza ko sun kai guda nawa zasu zauna ba tare
da wani ya takurawa wani ba.
Umaimah, ku saki jikinku wannan gidanku ne
babu mai gajiya da ku, muna son baki. Kin san
nice *yar auta a gidanmu dukka yayuna mata ne
guda hudu duk sun yi aure.
Umaimah da Sabitu dai sai kallon gida suke suna
masu annuri dan yau za su yi kwanan dadi ga
fanka ga Ac ba sauro balle kwari irin na Dugge.
Cikin katafaren falo suka fara shiga ta yi musu
izini su zauna tana zuwa, ta wuce zuwa kicin ta
bawa mai aiki izinin ta kawowa baki ruwa da
lemo sannan ta fito ta wuce zuwa bangaren
Mamarta,
dan ta sanar da mata cewar bakin sun karaso.
Sabitu ya dubi Umaimah ya yi dariya ya ce "Adda
Umaimah, Allah Ya baki kudi da ikon gina mana
gida irin wanna a birni. Ko kuma Allah Ya baki
miji mai arziki mu zo mu huta.
Umaimah ta yi dariya ta dafe kirji dan jin dadin
kalaman Sabitu.
Ta ce ''Allah Ya biyewa bakinka dan kanina.
Suka dinga shan lemuna kala-kala ko ruwa ba su
kalla ba, suka sami kek da meat pie suka dinga
ci.
Sai da suka dan jima a zaune sannan Aisha da
Mamarta suka fito, Umaimah da kaninta suka
silalo
daga kan kujerun da suke zaune suka kwashi
gaisuwa. Ta umarcesu da su koma su zauna
akan kujera, amma suka ki zama suka ci gaba da
zama akan kafet saboda kunya da girmamawa
irin ta Fulani.
Mama tana zaune, Aisha na zaune a kusa da ita.
Aisha ta ce "Mama ita ce Umaimah *yar
makarantarmu da nake baki labarinta, ita ce
babbar aminiyata mai sona nima ina sonta. Suka
yi dariya su dukkansu.
Mama ta ce "Ai kuwa ina shan labarin Umaimah
tun daga can ai mun taba gaisawa ma a waya,
sai yau Allah Ya nuna min Umaimah *yar
mutanen Dugge.
To sannunku da zuwa kawar Aisha. Ke da
Yayanki ne ko?
Umaimah ta dago da sauri ta dubi Sabitu ta yi
dariya ta ce "Kanina ne Mama.
Mama ta ce "Na ganshi ne kamar babba da yake
namiji ne ya fi ku girma, amma kamarku daya.
Aisha ta ce "Sabitu mu je in kai ka dakinka sai ka
dan huta.
Sabitu ya tashi yana biye da Aisha,
Umaimah ma ta bi su suka fice zuwa wani
bangare a can waje, falo,
daki daya da bandaki, babu abinda babu tamkar
dakin wata amarya. Umaimah ta bude jaka ta
ware masa kayansa kala biyu ya zuba a durowa
sannan ta tafi da jakar kayanta a ciki bayan sun
nunnuna
masa duk yadda zai yi amfani da kayan ciki.
Dakin Aisha suka wuce akan bene sai da
Umaimah ta jinjimawa dakin saboda ya kayatu ga
girma, kai kace filin kwallo ne. Katafaren gado da
kujerunsa, ga kayan kallo duk daki daya,
kayataccen bandaki
mai kyau kai ka ce na tangaren ne kamar ka
kwanta ka yi bacci a ciki.
Wanka Umaimah ta fara yi sannan aka aje mata
abinci kala-kala ita da kawarta suna ci suna ta
hira har suka koshi, tabbas ta tuna Malaysia a
yau musamman da sanyin Ac ya ratsa ta. Bayan
ci sai kwanciya, Umaimah ta kwanta hakarkarinta
akan lallausar katifa saboda gajiya, sai ta tsinci
kanta tana mai aiyanowa a ranta dama ace
gidanta ne nan ita da abun kaunarta Abdul-Sabur
sai ta ji
kwalla ta cika mata ido. Nan da nan ta tuno da
Faduwa sai ta jawo wayarta a sanyaye ta dubo
sunan Faduwa ta kira ta.
Bugu daya Faduwa ta amsa tun kafin ma
Umaimah ta yi magana Faduwa ta ambaci
sunanta. Cike da mamaki Umaimah ta tambaye
ta "Ya aka yi kika san ni ce tun ma ban yi
magana ba?
Faduwa ta ce "Dare da rana ina jiran in ji kiranki
daga Nigeria, dan haka ina ganin lambar Nigeria
sai na san kece duk da yanzu *yan uwana suna
yawan kirana daga Sokoto.
Umaimah ta ce "Kira nayi in ji yadda kike ciki. Kin
haihu lafiya ko?
Faduwa ta ce "Ai na yi fushi tunda baki neme ni
ba tuntuni, sai yanzu.
Umaimah ta ce "Allah Sarki Antina kin san
Rugarmu ba mu da waya, yanzun nan na fito
birni, na sayi layi.
Faduwa ta ce "Na haifi *ya mace gata nan
kamarta daya da ni sak, na saka mata suna
Umaimah.
Sai Umaimah ta daka tsalle ta diro daga kan
gado dan murna har da hawayen dadi ne yake
kwarara Ta ce "Anti Faduwa, da gaske Umaimah
sunanta?
Ai kuwa zanzo har Cairo wata rana musamman
dan in ga takwarata. Amma na ji dadi na gode,
Allah Ya
raya ta, Ya yi mata albarka.
Faduwa ta ce "Amin, ga Sagir ku gaisa shima
yana tambayar ki, zai sake fada miki sunan baby
ki ji. Ai shi zaki fi yarda da maganarsa.
Faduwa ta mikawa maigidanta waya cikin
harshen turanci suka gaisa da Umaimah ya sake
shaida
mata sunanta aka saka. Ta yi masa godiya da
taya shi murna, gami da yiwa jaririya doguwar
addu'a.
Daga karshe ta yi sallama da su suka kashe
waya.
Daidai lokacin Aisha Bingyal ta idar da sallah ta
dubi Umaimah ta ce "Aminiyarki ce Faduwa ta
haihu?
Ai da kin bani ita mun gaisa, dan tana da kirki.
Umaimah ta ce "Tana da kirki sosai ma kuwa,
har sunana ta sakawa *yar jaririyar data haifa,
shiyasa kika ji ina ta tsalle. Zan baki lambarta sai
ki kira ta ku gaisa, ta sanki sosai, kiyi mata
barka.
Faduwa da Abdul-Sabur ai aminaina ne na
hakika, na ji dadin zama da su, ba zan taba
mantawa da su ba kuma ba zan daina kaunarsu a
raina ba har abada.
Aisha ta yi dariya ta ce "Musamman ma Abdul-
Sabur din, shi so na musamma kike yi masa
bayan na MAKWABTAKA. Suka yi dariya su
dukkansu.
Aisha ta tashi daga kan abin sallah ta cire
hijabinta ta linke ta zo ta zauna akan gado kusa
da Umaimah.
Ta ce "Yauwa, har kin tuna min ma da maganar
Baban Hanif, kin ce zaki fada min abunda ya ce
miki.
Umaimah ta kalle ta tayi murmushi ta jawo filo ta
ringisa.
Ta ce ''Uhum, ashe baki manta ba kema?
Ni ma wallahi tun dazu maganarsa ta tsaye min a
rai, har na fara tunanin da ace akwai inda zan
kaura da garin nan zan bari in tafi inda ba'a taba
sanina ba, zai fi min sauki.
Aisha ta harare ta, ta ce "Irin yadda kika yi mana
a Malaysia za ki sake yi musu a garin da zaki
kaura?
Ai duk in da kika je dole ki sami wadanda zasu
saba da ke, sai sun sanki dole, kamar yadda kika
saba da Faduwa da Abdul-Sabur.
Umaimah ta ce "Haka ne, dan gaskiya ko a
mafarki ban zaci akwai ranar da zan saba da
makwabtana ba su Faduwa, sai gashi daga baya
bani da tamkarsu har ban so muka rabu ba.
Baban Hanif yayi min wata magana wacce a
wajena ba mai yiwuwa ba ce, kuma idan ban
amince ba tabbas ba zai ji dadi ba kuma ban
kyauta masa ba.
Aisha ta ce "Me ya ce miki, cewa ya yi yana
sonki zai aureki?
............
Eh cewa yayi xai aure ni, nikuma a duniya banga
wanda nake so da kauna ba irin Dan Aunty...
Kuma shi xan aura...lols.
Ehem yan uba kunji dai da bakin Umaimah wanda
tace xata aura dan nima bayin kaina bane a dole
xan aure ta...
MAKWABTAKA 46
Aisha ta ce "Me yace miki, cewa ya yi yana sonki
zai
aure ki?
Umaimah ta ce "Cewa yayi daya daga cikin
abokan aikinsu ne ya ganni ya ce yana sona, ya
biyo ta wajensa.
Hmm, Baban Hanif ya na sake maimaita min
cewar Alh. Nura ogansa ne yana jin nauyinsa
sosai. Ina jin yasan halina yana tsoron kada in
wulakanta masa oga. Ya dami Baban Hanif wai
ya nemo masa lambar wayata, wai idan na
amince zai ba shi lambar yanzu. Nauyinsa nake ji
ba zan iya cewa kada ya ba shi lambata ba, sai
na ce ba damuwa ya bashi lambar, sannan ba
zan iya wulakanta mutumin da ya kawo min ba
ko da a bayan idonsa ne, sannan ba zan iya
aurensa ba saboda Abdul-Sabur nake so.
Yaya kika ga za'ayi yanzu?
Tabbas ina cikin wani hali Aisha. Umaimah ta
sulale ta kwanta saboda tashin hankali.
Aisha ta dade a zaune tana kallon Umaimah daga
dukkan alamu tana jin tausayinta, sai can ta
matso kusa da ita ta dafa kanta.
Ta ce "Gaskiya sai yanzu na fara fahimtar
matsalarki kawata, ba wai dan kina son Abdul-
Sabur ba ne yasa na fara jin tausayinki ba, ni na
fi so ma ki cire shi a lissafinki. Naga alama
cunkushewar maneman ne da suka fara yi miki
yawa, zai yi wuya ki tantance wanda ya fi a
cikinsu. Yanxu haka na turawa Bilyaminu
lambarki dazun nan da muke cin abinci, ya ce zai
kiraki dan ni na fi yi miki sha'awarsa fiye da
yallabai saboda shi Bilyamin matashi ne, me
mata daya da *ya*ya kadan ba kamar yallabai ba
matansa biyu, sannan da tulin *ya*ya sai dai
akwai tulin kudi. Ga na bangaren Baban Hanif
daga gani shima me kudi ne, dubi duk kudin
Baban Hanif ya ce wancan ogansa ne ya fishi
kudi kenan, lallai akwai Naira. Ko baki aure shi
ba zaki sami kudi a wajensa.
Umaimah, wannan fa ba abin damuwa ba ne, ana
hada samari biyar ko goma har mai rabo ya
samu ya aura, ba abin damuwa bane. Za ki iya
kula su dukka, ba dai gaisawa ba ne a waya ko
kuma suzo ki fita ku yi hira shikenan fa.
Umaimah ta ce gaba da karanta "Lahaula wala
kuwwata illa billahil aliyyil azim.
Dan ta shiga garari.
Wayar Umaimah ce ta dau kara bata yi mamaki
ba dan ta kikkira mutane da yawa ta san yanzu
an fara sanin lambarta. Ta mika hannu a sanyaye
zata dauka sai Aisha ta yi sauri ta sura ta duba
lambar,
kallo daya ta yiwa lambar ta shaida lambar
Bilyaminu ce. Sai ta yi dariya ta ce "dan halak
Bilyaminu ne da gaske fa yake kawata, dan Allah
kada kiyi masa wulakanci.
Ta danna da sauri ta karawa Umaimah a kunne,
cike da takaici Umaimah ta ke magana.
Yayi farin ciki da jin muryarta sai ya rikice gaba
daya ya hau rawar jiki, cewa yake wai zai baro
Kaduna a yau ya zo dan ya ganta a gidan su
Aisha da daddare.
"Allah Ya kawo ka lafiya. In ji Umaimah ta kashe
waya a fusace. Kafin Aisha ta yi magana sai
wayar Umaimah ta sake yin kara alamar kira ake
yi, ta zaci Bilyaminu ne sai taga wata lamba ce
daban, bata yi mamaki ba dan zai yiwu yana da
layika da yawa, ta danna ba tare da walwala a
fuskarta ba. Wannan karon salon maganar da
muryar ba irin ta dazu ba ce. Dan haka sai
Umaimah ta yi kasake tana sauraron abunda zai
ce, har yanzu magana yake yi cikin kasaita.
"Ko bada Umaimah nake magna ba ne? Ya
tambaya "Ita ce" in ji Umaimah
Ya ce "Kina magana da Justice Nura, ni ne wanda
Alh Nasir ya yi miki maganata, yanzu ya turo min
lambarki.
Sai Umaimah ta zabura ta tashi zaune dan
fargaba yayin da Aisha ma ta zare ido tana kallon
ta.
Aisha ta shiga yi mata rada tana tambayarta
"Lafiya, me yake ce miki.
Umaimah ta daga mata hannu alamar ta tsaya
tana zuwa. Umaimah ta gaishe shi cikin
girmamawa.
Ya ce "An ce kin shigo gari, zaki kwana biyu ko?
Yana kokarin ya ce zai zo wajenta ya ganta su
gaisa. Sai ta yi sauri ta ce ai a yau zata koma
Dugge sai dai idan ta sake shigowa. Ya ce "Ba
matsala zan saka direbana ya kawo miki sako ya
dauke ki ya kai ki Dugge sai ya gano min gidanku
saboda gaba idan zan je ya kai ni.
Umaima ta ce ai bata gida yanzu haka tana cikin
tasha har ta hau mota zata koma amma wani
lokaci idan ta dawo sai su je direban ya ga gidan.
Ya ji ba dadi amma ya yi mata uziri. Yana
tantamar bata san ko shi waye ba shiyasa take yi
masa wargi yana saka ran daga sanda ta gan
shi, ta san matsayinsa zata shiga hankalinta.
Suka yi sallama suka kashe waya.
Umaimah ta dora hannu a kai ta mike tsaye ta ce
"Aisha wannan ba Bilyaminu ba ne, wanda Baban
Hanif ya fada min ne shine ya kira shima
maganar zuwa yake yi min. Aisha yau zan koma
Rugarmu na
fasa kwana a nan.
Umaimah ta shiga linke kaya tana zubawa a jaka,
a gigice take.
Hankalin Aisha ya tashi ta shiga lallashin
Umaimah amma kamar zuga ta take yi, har da
rantsuwa Umaimah take yi ba zata kwana ba
tafiya zata yi.
Umaimah ta juya ta dubi Aisha wacce ta yi
kasake a gefe tana kallon ikon Allah dan ta rasa
me ma zata fada mata ta yarda da ita.
Ta girgiza kai ta ce "Yi hakuri ba laifina ba ne
dole ce ta sa zan tafi, ki kira Bilyaminun ki ce ya
fasa zuwa ba zan kwana a Gombe ba. Za ki iya
ce masa daga gida aka ce in koma yanzu.
Kafin Umaimah ta rufe bakinta wayar Aisha ce ta
dau ruri sai su dukka suka zurawa wayar ido a
tsorace. Aisha ta dau ki wayar a hankali ta duba,
sai ta dago ta kallo Umaimah ta zazzare ido.
Ta ce "Dayan ne shima yake kira, Yallabai ne, na
san ma maganar lambar wayarki zai yi min.
Umaimah ta zabura ta ce "Kada ki bashi lambata,
Aisha ki rufamin asiri dan Allah.
Aisha ta dannan waya da sauri, bayan sun gaisa
kamar kullum ya tambaye ta lambar abar
kaunarsa Umaimah. Sai Aisha ta saka wayar a
'speaker' yadda Umaimah zata ji da kunnuwanta
abunda yake tambaya.
Aisha ta ce "Ranka ya dade, idan ta zo da kaina
zan kira ka ku gaisa ka karbi lambarta.
Ya ji dadi da bayanan Aisha yayi mata godiya
suka yi sallama suka kashe waya.
Umaimah ta gyada kai ta ce cafdijam! Zaman
birni yafi karfina. Ina zan kai wadannan mazan?
Gara in koma Ruga in yi zamana ba waya balle
wani ya kira ni, kada ma ki dinga fada musu
sunan garin mu dan akwai wanda zai iya shiga
garin ya nemo ni.
Aisha ta ce "Ai na san matsalarki son Abdul-
Sabur ne ya hana ki son kowa, amma meye
laifinsu da zaki dinga gudun su dan suna sonki.
Umaimah ta ce "In bana son kowa sai Abdul-
Sabur a duniya ai ba laipina ba ne Aisha.
Dole Aisha ta jawo gyalenta ta biyo bayan
Umaimah wacce tuni har ta rataya jakarta ta fara
saukowa daga matattakalar bene da sauri kai ka
ce da karfi za'a kamata a aurar. Suka shiga dakin
Mama ,
Umaimah ta durkusa a gabanta tayi mata
sallama.
Mama ta cika da mamaki da ta ji Umaimah ta ce
zata tafi yanzu alhali ance kwana biyu zasu yi.
To me yasa zasu tafi?
Aisha ta ce "Mama, waya aka yi daga gidansu
aka ce su dawo sun yi baki daga nesa.
Mama ta dauko kudi da turare ta bata sannan ta
dauko yadin maza ta ce a bawa Sabitu. Umaimah
ta yi godiya suka fito zuwa bangaren Sabitu. A
mimmike suka tarar da shi yayi dai-dai akan
kujera a falo yana kallon talabijin, ga fanka gami
da Ac dukkansu ya kure, falon sanyi garau.
"Samun waje wai *yar caca da yado.
In ji masu iya magana.
Umaimah bata san sanda murmushi ya kubce
mata ba ganin yanayi na hutu da walawa da ta
ga Sabitu ya shiga duk da tasan yau ba zata
kyauta masa ba idan ta ce ya taso su koma
Dugge.
Ya zabura ya tambaye ta "Lafiya?
Ta ce "Lafiya kalau.
Har yanzu dai a zaune yake cike da rashin
fahimta yana kallon Umaimah da Aisha cike da
damuwa.
Aisha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Kai ma ka
tambaye ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login