Showing 111001 words to 114000 words out of 130520 words

Chapter 38 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8041

zaka ci gaba da zama a Gombe to
sai ku zauna, idan babu sana'a sai mu koma
Dugge mu zauna idan kuma na sami aiki mai
kyau da zai sa na ciyar da kaina da iyalinka sai
mu zauna.
Sabitu ya ji tamkar ta yi mishi albishir da gidan
aljanna sai ya washe baki ya ce "Allah ma zai
hore mana mu ci gaba da zama har mu gina
gidanmu mu kwaso su Baffa su dawo birni. Me
za'ayi da zaman cikin daji?
Ke ma Allah Ya duba ki ya kawo miki wanda kike
so Abdul-Sabur.
Ta ji sanyi a ranta daya ambato mata sunan
abinda tafi so a rayuwarta, bayan iyayenta da
dan uwanta sai Abdul-Sabur. Ta sharce wani
zazzafan hawaye.
Ta ce "Ina jin rayuwata ta kusa karewa Sabitu,
saboda ba zan sami Abdul-Sabur ba gashi ba zan
iya son duk wadannan ba. Anya kuwa daga Abuja
zan dawo garin ba tafiya zan yi a rasa ni ba?
Hankali Sabitu ya tashi ya zabura ya ce "Kar kiyi
haka Adda Umaimah, zamanki a kusa da mu
shine arzikinmu, idan baki dawo dan ni da
*ya*yanki ba zaki dawo dan Baffa saboda ya
tsufa. Allah ne
gatanmu ke ce gatanmu. Kina karamarki Allah Ya
dora miki girma. Kin zamto kece uwa kece uba.
Ta yi kasake tana mai gasgata maganar sa,
tabbas bai yi karya ba idan ta tafi dukka mutanen
nan da ya karanto rayuwarsu zata tawaya.
Ta dago zata yi masa magana sai taga ya
kurawa wani abu ido daga bayanta, da alama
wani abu yake hange wanda ya bashi mamaki ko
ya firgita shi. Nan da nan ta ji hankalinta ya
tashi yayin data shiga fargabar waiwayawa kada
ta hangowa kanta a binda ya fi karfinta. Sabitu
menene, lafiya?
Bai amsa mata ba yayin data juya da kanta a
hankali ta dubi inda yake kallo sai kuwa ta firgice
da taga ashe abun da yake kallo yana daf da ita,
a tsaye a bayanta. Tayi sauri ta ja da baya ta
labe a bayan Sabitu yayin da mamakin da Sabitu
yake yi ya zama tamkar shafar mai ne akan
wanda ta shiga.
Bakinta ta dafe da hannayenta biyu saboda fatar
bakin ta ki rufuwa, ta ji kamar ba'a wannan
duniya take ba, mafarki take yi. Ta mika hannu a
hankali ta mintsini Sabitu dan ta tabbatar ba
mafarki take yi ba, sai ta ga ya zabura ya sosa
wajen sannan ta tabbatar a raye suke. Ta sake
shakar numfashi ta dire tabbas kamshin turaren
nan 'Dolce Gabbana' ne yake dukan hancinta. Sai
ta sake bude ido ta
duba ta sake dubawa gaskiya ne abunda take
gani ba gizau idanunta suke yi mata ba. "Tsarki
ya tabbata ga Ubangijin talikai mai kowa mai
komai. Haka ta fada a bayyane.
Hawayen farin ciki ne ya fara kwararowa wannan
karon, masu sanyi ne hawayen daga dukkan
alamu Allah Ya amshi addu'arta. Jama'a ku taya
ni canka wa taga ni ne haka?
Allah mai amsa addu'ar bawanSa a lokacin da Ya
so.
Abdul-Sabur Abdul-Rashid ta gani a gabanta
cikin kyakkyawar shiga farar shadda ce sol gami
da yanayi na farin ciki a fuskarsa. Ta ji kamar ta
daka tsalle ta rike shi sai ta saka gyalenta ta rufe
ido ta yi magana cikin rada ta ce "Sabitu gashi
nan.
Sabitu ya tambayeta cike da mamaki "Waye shi?
Abdul-Sabur ya yi murmushi ya karaso daf da su
ya mikawa Sabitu hannu suka gaisa. Ya ce
"Sunana
Abdul-Sabur Abdul-Rashid. Nan da nan Sabitu ya
gigice da murya ya yi kabbara gami da hamdala.
Ya ce "Ka cika dan halak yanzunnan maganarka
muke yi...
Bai rufe bakinsa ba Umaimah ta zungure shi wai
yayi shiru. Abdul-Sabur ya dubi Umaimah ya yi
dariya.
Ya ce "Kada ma ki hana shi fada na gama jin duk
abunda kuke fada tun dazu nake tsaye a bayan
motar nan da kuke jingine babu abinda ban ji ba.
Yanzu da ki ka ganni maimakon ki zo wajena
kuma sai kika koma gefen Sabitu ki ka labe. Ko in
koma
bakya farin ciki da ganina?
Umaimah ta matso kusa da shi tana mai fara'a
da dariya amma fa kukan dadi take yi hawaye
face-face a idonta ta gaishe shi cikin muryar
kuka.
Ya girgiza kai sannan ya zaro hankici fari kal mai
kamshi daga aljihunsa ya mika mata.
Ya ce "Ba zan amsa miki ba kina kuka, goge
hawayen ki Umaimah ki daina kuka, ina mai
shaida miki daga yau kin daina zubar da hawaye
muddin ina raye sai dai bayan raina in Allah Ya
yarda.
Farin ciki ya lullube Umaimah da kaninta a
bayyane.
Abdul-Sabur ya ce bamu da isasshen lokacin da
zamu yi doguwar magana ina nan tare da Sabitu
har ki je ki dawo. Umaimah da kaninta suka
tsaya suna kallonsa
duba irin na rashin fahimta, sai ya yi murmushi.
Ya ce "Na ce kada ki damu ki je camp dinki ki
fito zaki same ni tare da Sabitu anan zan zauna
in jira ki.
Ki je ki shiga mota ku tafi ga su Hanif can na
hango suna ta shiga motoci da kayansu. Sabitu
ya ta da jakar kayanta ya kai mata mota.
Umaimah ta zama tamkar an zare mata laka
kallon Abdul-Sabur kawai ta ke yi har yanzu da
sauran kokonto a cikin zuciyarta tana ganin
kamar mafarki take yi ta kasa yarda gaskiya ne.
Tafiya ta ke a hankali kamar wacce kwai ya
fashewa a ciki tana tafe tana waiwayensa yayin
daya tsaya cak yana kallonta shima, amma
murmushi kawai yake yi ya san abun da yake
damunta.
Sabitu har but din motar da zata shiga ya kai
mata akwatinta sannan ya shiga cikin motar har
kujerar da ta zauna, ya yi mata sallama, ya yi
mata rada bata san me yake cewa ba kasancewar
hankalinta baya jikinta tana can tana kallon
Abdul-Sabur.
Motoci sun cika taf da dalibai kowa ya zauna
yayin da motocin suka fara tafiya a layi.
Idon Umaimah akan Sabitu da Abdul suke, tana
kallonsu kawai yayin da su ke daga mata hannu,
dariya kawai suke kyalkyatawa saboda sun ga ta
susuce gaba daya ta zama kamar doluwa wacce
bata gane komai.
Alhali kuma ba doluwa ta zama ba ta kamu da
mamaki mai tsanani ne.
Ikon Allah Ya wuce da haka Umaimah Bello.
Allah Ya kiyaye hanya !!!
AI KAWAI SAI RANA ITA YAU ZAN CI GABA...
Abdul-Sabur ya dawo ga Umaimah .
Dole na sheke shi kawai...
Dan Aunty.
MAKWABTAKA 48
Har su Umaimah suka fita daga garin Gombe
hankalinta bai dawo jikinta ba, tunani take kawai
mai rikitarwa game da abunda idanuwanta suka
gane mata.
Aisha ta zungureta ta ce "Lafiyarki kalau kuwa,
tunanin me kike yi haka?
Kada fa ki damu kan ki akan wadannan mutane ki
zaba ki darje a cikinsu babu na yarwa, gaba daya
suna da abunyi kuma suna sonki. Amma ni nafi
so a auri kawunmu
Bilyaminu. Ko ba haka ba Khadija Jauro?
Khadija da take zaune a kujerar gabansu ta
waiwayo tana dariya.
Ta ce "Gaskiya mu dai muna kamun kafa ayi
mana kara a auri kawunmu, dan ya mutu a sonki
kuma da gaske yake.
Umaimah ta yi murmushin karfin hali ta matse
hawaye ta ce "Abdul-Sabur na gani ya zo.
Aisha ta tsaya tana yi mata kallo irin na rashin
fahimta har ta fara tunanin ko ta fara zautuwa
ne.
Umaimah ta dubi Aisha tayi dariya ta gyada kai
ta ce "Da gaske nake na san abunda na ke fada a
haiyacina nake. Ba ki ganshi ba a tsaye shi da
Sabitu suna dagamin hannu?
Aisha ta ja doguwar ajiyar zuciya ta ce "Na ga
wani mutum fari, dogo, tare da Sabitu.
Da gaske shine?
Umaimah ta yi fari da ido ta dafe kirji ta ce "Yau
kamar an jefa ni a aljanna nake ji, Allah abin
godiya
Ya amsamin addu'ata ya kawo min Abdul-Sabur.
Ta kankame Aisha tana ta murna.
Daga dukkan alamu itama ta taya ta murna duk
da ta shiga tunanin yadda zata dubi idon Alh.
Bilyaminu ta fada masa Umaimah ta sami mai
sonta ba.
Khadija ta waiwayo da sauri ta dube su, ta ce
"Me nake ji kuna cewa, kawun nawa aka yiwa
kishiya?
Aisha ta kalli Umaimah itama ta kalle ta suka
juyo gaba daya suka kalli Khadija a firgice ba tare
da sun san me zasu ce mata ba, dan maganar
tana da nauyi da kuma kunyar fada.
Umaimah ta yi murmushi ta fara magana cikin
tausayawa ta ce "Banki kawunki ba Khadija,
amma wanda nake maganar sa shine wanda
muka yi alkawarin aure da shi shekaru biyu da
suka wuce.
Khadija ta yi murmushin karfin hali ta gyada kai
ta ce "Shikenan ba damuwa Aisha zamu san
yadda zamu fadawa Kawu zai fahimce mu.
Umaimah zamu so ki auri wanda kike so kema
dan mu ma nan da kika ganmu duk wadanda
muke so muka zaba mu aura.
Aisha ta ce "Gaskiya ne Khadija, kowa yana so ya
auri wanda yake so.
Umaimah ta ji dadi da suka fahimce ta sai ta yi
dariya ta yi musu godiya. Sannan kowaccensu ta
juya ta ci gaba da karanta littafi da take
karantawa (novel).
Umaimah ta zaro wayarta ta kunna yayin da
sakonnin suka dinga shigowa rututu wasu daga
Faduwa na gaisuwa ne, wasu na Alh Bilyaminu na
so da kauna ne, wasu daga Alh Nura tambayarta
yake yi yaushe zata shigo gari.
Sai wasu sakonni da yawa da wata lambar MTN.
Ta cika da mamaki a
lokacin data fara karanta sakonnin da aka turo
mata da sabuwar lambar, sai daga karshe ta
gane
mai sakon daya rubuta sunansa Abdul-Sabur.
Masha Allah!!!
Ta cika da murna da ta sami lambar Abdul-Sabur
amma ta shiga mamakin yadda aka yi ya sami
lambarta.
Bata gama dubawa ba ta ji an kira ta da lambar,
sai ta tabbatar rabin ranta ne ya kira ta. Sai
kuwa ta yi sauri ta amsa muryarsa kadai ta ji
yana yi mata sallama sai ta lumshe ido dan dadi.
Abdul-Sabur ya ce "Gani nan da kanina Sabitu
muna maraici kin tafi kin barmu.
Umaimah ta yi murmushi ta girgiza kai ta ce
"Allah Sarki, ai zan dawo kwanannan. Ina ka sami
lambata naga sakonninka yanzu dana kunna
wayar?
Ya yi dariya ya ce "Ni dana damu da ke ai duk
motsinki na sani, haka a Malaysia ba ke kadai ki
ke rayuwa ba ina biye da ke har ranar da kuka
tafi filin jirgi za ku taho Nigeria.
Ta dafe kirji ta bude baki tana mamaki ta fada da
karfi, har su Aisha suka dago ido suna kallonta
Ta ce "Da gaske?
Me yasa kayi mana haka?
Meye hujjarka da kayi hakan?
Ya yi dariya ya ce "Ina da hujjoji masu yawa sai
mun hadu zan fada miki dalilina na yin haka.
Yanzu zamu tafi da Sabitu 'Emerald Royal Hill
Hotel' acan na ke daman mu ci gaba da zama,
dan satina biyu a garin nan yanzu.
Mamaki ya sake lullube Umaimah har ta ji ta fara
tsorata da al'amuran Abdul-Sabur. Ya yi mata
fatan Allah Ya kiyaye hanya, suka kashe waya.
Hotel suka nufa a cikin tsaleliyar motarsa
'ACURA' dakin Sabitu na kusa da dakin Abdul-
Sabur.
Dadin duniya dai Sabitu yana ji a wannan yanayi
na zaman Hotel duk da sai da Abdul-Sabur ya yi
kwana biyu yana gadinsa yana nuna masa yadda
zai yi amfani da kayan ciki. Famfon ruwan sanyi
dana zafi bandaki, kunna Ac karawa da ragewa,
kunna talabijin da kashewa. Amma daya koya
masa ya gane sosai sai yake cin gashin kansa
shi kadai a dakinsa.
Abdul-Sabur ya cika masa firij da yake dakin
kayan dadi kala-kala, sai da azahar suke fitowa
suyi sallar azahar a masallacin kusa da Hotel din,
sannan su shiga mota su shiga gari. Manyan
gidajen cin abincin garin ba wanda basa zuwa,
haka duk wani wajen shakatawa na garin sun je
sun huta kamar 'Kanawa Forest' da Zamfarawa,
dan haka tun Sabitu baya iya shan ice cream da
su shawarma sai da ya koya zama da Abdul-
Sabur.
Idan Sabitu ya ci ya koshi baya sanin sanda yake
yage baki yayi ta bawa Abdul-Sabur labarin
abunda ya faru game da rayuwar Umaimah.
Tabbas Abdul-Sabur ya gamsu, ya daina tantama
Umaimah tana sonsa ko bata sonsa kamar yadda
Faduwa ta bashi labari.
Ya kudiri niyyar aurenta dan bashi da matar data
fi dacewa da rayuwarsa irinta don ita ce kadai
macen daya taba ji yana so a rayuwarsa.
"Sabitu meye abun yi, daga ina zan fara neman
auren Umaimah?
Tunda daman ni da ita mungama fahimtar juna ni
take jira. So nake in bata mamaki kafin ta dawo
an gama shirya magana komai.
"Abdul-Sabur ya tambayi shawara.
Ya yi gyaran murya gami da gyara zama dan ya
ji tambayar babba ce.
Ya ce "Gaskiya babu abinda Baffa ya fi so irin ta
yi aure a cikin *yan kwanakin nan kuma ta yarda
ta zabi wanda take so ta aura ko wanene.
Ta bamu labarinka tatas ni da Baffa dan haka ya
sanka.
Yanzu mu je ka gaishe da Baffa, Dagacin garinmu
da sauran tsofaffin garin.
Tabbas jama'ar garinmu ba zasu karbe ka ba
zasu kushe ka, zasu ce kai bare ne ba'asan
asalinka ba. Duk da daman cewa zamu yi kai dan
Gwarzo ne ba zamu ce kai dan Ghana ba ne.
Amma kada ka damu
in dai Baffa ya yarda da kai Dagaci zai yarda da
kai musamman idan aka aika masa kyautar
Shaddoji
da Yadina, sauran mutanen duk su gama
surutunsu sai mu toshe kunnuwanmu.
Abdul-Sabur ya yi dariyar jin dadi ya lumshe ido.
Ya ce "In dai dan wannan ne an gama, ba
damuwa gobe sai mu kama hanyar Dugge.
Haka kuwa aka yi washe gari da safe, babbar
kasuwar suka nufa a inda suka yi ta jidar
shaddoji, yadiddika da atamfofi masu yawan
gaske suka cike but da kujerun bayan motan,
sannan ya sayi lemuna (juice) katan-katan har
sai da Sabitu ya dinga hanashi saboda sayayyar
ta cika yawa. Suka dinguma suka shiga Dugge da
hantsin ranar lahadi a lokacin satin Umaimah
biyu da tafiya.
Daman motar na shiga garin, *yan garin suka
tabbatar Umaimah Bello ce, ai kuwa a kofar gidan
motar ta tsaya. Sai aka tsaitsaya ana jiran aga
fitowarta daga mota da irin shigar da ta yi a yau,
sai suka ga wayam! Babu Umaimah daga Sabitu
sai tsalelen bako daga gani babu tambaya kudi
ya ratsa shi. Baffa ya fito cike da dimbun mamaki
amma ya cika da fargaba da bai ga *yarsa ba,
fadi yake yana sake maimaitawa "Ina Umaimah,
ya banga Umaimah ba?
Da fatan tana nan lafiya?
Sabitu ya yi sauri ya amsa masa dan ya ga tsoho
ya shiga damuwa da yawa. Ya ce "Umaimah tana
nan lafiya kuma cikin koshin lafiya da dinbun farin
ciki da kwanciyar hankali.
Sai Baffa ya yi ajiyar zuciyar jin dadi sannan ya
juya ya dubi Abdul-Sabur ya yi masa fara'a da
sannnu da zuwa, kallo irin na rashin fahimta
Baffa yake yiwa Abdul-Sabur.
Da sauri Sabitu ya shiga cikin gida dan ya
daukowa bakonsa tabarma dan ya zauna, dan
yaga Baffa da su Nene sun bi layi suna kallonsa
kallo irin na kauyanci.
Inna ce ta bi Sabitu tana tambayarsa, suna
neman labari su ji waye shi daga ina ya zo kuma
me ya zo yi?
Sannan a ina suka baro Umaimah?
Sabitu bai bata cikakkiyar amsa ba cewa ya yi
"Idan tayi tsami zaki ji Inna, me kike ci na baka
na zuba.
Ke da bako ya sauka a gidanki.
A zauren kofar gida aka yiwa Abdul Sabur
shimfida suka zauna tare da Baffa, Sabitu na
zaune a gefensu. Baffa yayi-yayi da Sabitu ya
daukowa bako ruwa.
Sabitu ya ce "A koshe yake.
"Ya aka yi ka san a koshe yake?
Inji Baffa.
Sabitu ya ce "Ko ni dana rabe shi a koshe nake,
yanzu ba zan iya shan wannan bakin ruwan na
garinku ba balle shi. Su dukka suka kyalkyale da
dariya. Bayan Abdul-Sabur ya gaishe da Baffa sai
ya tambaye shi lafiyar mutanen gida, sunayen su
Nene fal a bakinsa. Sai Baffa ya sake cika da
mamaki ya san ko waye wannan ya yi musu farin
sani amma abun daure kai shine bai taba ganinsa
ba a rayuwa.
Sabitu kadai zai warware wannan dabaibayi, ya
gyara zama ya fara yiwa Baffa bayanin ko waye
Abdul-Sabur da kuma abunda yake tafe da shi.
Tabbas daga gani babu tambaya Baffa ya yi farin
ciki matuka kuma yayi amanna da wannan
magana, baya kokonto saboda yasan Umaimah
shi take bege kuma take jira. Ya yi musu fatan
alkhairi da fatan ayi biki lafiya.
Babu abinda Abdul-Sabur yake yi sai washe baki
da godiya, ji yake yau kamar an bashi mukullin
aljanna. Ya gyara zama ya dubi Baffa akunyace,
sai ya sunkuyar da kai kasa ya sosa keya. Ya ce
"Baffa inaso ayi bikin nan da wata uku ko
biyu. Amma yaya ka gani?
Sabitu ya ce "Nan da wata guda ma mu a shirye
muke.
Baffa ya ce "Eh to ban ki ta taku ba, amma a bari
dai Umaimah ta dawo sai mu ji sanda take ganin
zata gama shirinta, ni yanzu ai ba nine da
magana ba tunda babu abinda zan yi mata.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya ce "Baffa ai ina
ganin babu wata siyayya da Umaimah zata yi
daga kayan sakawa, kayan daki, ko abincin *yan
biki duk ni zan yi.
Baffa ya ji hawayen dadi ya rikito masa babu
shiri ya barke da kuka. Musamman da Sabitu ya
fara jido masa Yadiddika da Shaddoji da katan-
katan din lemuna (juice) yana jifgewa a gabansa
sai da
zauren nan ya cika makil.
Baffa sai fadi yake yana sake maimaitawa
"Menene wanan?
Na maye wannan?
Ina zan kai duk wadannan kaya?
Abdul-Sabur ya ce "Baffa duk naka ne ka diba ka
dibarwa *yan uwa da abokan arziki.
Baffa ya girgiza kai ya ce "Abdul-Sabur wannan
ya yi yawa ai sai a zage ni a gari ace naga
wanda yafi Abdul-Basi kudi shiyasa na bashi
*yata.
Sabitu ya zabura ya ce "Baffa ina ruwanka da
jama'a?
Ka rabu da mutum ka kama Allah babu abinda
bil'adama zai yi maka banda ya kai ka ya baro
ka, ya dawo yana yi maka dariya idan ta
kwabe.
"Kirawo su Nene suzo su gaisa da surukinsu.
"Baffa ya aiki Sabitu.
Sabitu ya kira su daman a shirye suke da
gyaleluwansu a yafe a jikinsu, sai suka yi zuruf
suka biyo shi. Suka zo suka zube a gabansa, nan
da nan Abdul-Sabur ya tsuguna ya gaishe su.
Baffa ya nuna musu Abdul-Sabur ya ce shi zai
auri Umaimah, ai kuwa kowacce sai da ta zabura
suka hau kallon-kallo cike da rashin fahimta.
Baffa ya sake nunnuna musu wadannan himilin
kayan da ya kawo musu sai suka hau murna
suka calla buda.
Suka taya Sabitu jidar kaya suka yi ta lodawa a
dakin Baffa har ya zamanto babu inda mutum zai
sa kafa.
Baffa, Sabitu da Abdul-Sabur ne suka tafi gidan
Dagaci, bayan Baffa ya aika a kirawo duk wani
shahikinsa, da abokinsa ya zo gidan Dagaci zasu
gaisa da bako. Ba'a dauki lokaci mai tsawo ba
aka taru. A sanda aka fara bayani zuciyar Abdul-
Sabur ce take ta harbawa dan fargaba kada a
sami wadanda zasu hana a bashi farin cikin
rayuwarsa Umaimah.
Sai ya shiga karanto musu addu'a.
Baffa ya gabatar da Abdul-Sabur sai kowa ya
zura masa ido yana kallo, a kunya ce ya duka ya
sake gaishesu irin ta girmamawa duk da wasu
basa iya jin Hausar sosai sai fillanci. Koda ya
fara fadar abunda yake tafe da Abdul-Sabur sai
waje ya rude da hayaniya. Wasu harda fada da
kumfar baki wai ina za'akai maganar Abdul-Basi?
Amsar da Baffa ya basu shine Umaimah ta ce
bata son ta sake zama da Abdul-Basi saboda
wulakancin da yayi mata abaya.
Dagaci ya ce abari yarinya ta dawo a tambaye ta
wanda tafi so shi za a bata.
Sabitu ya zabura ya ce "Ga wanda Umaimah tafi
so dan ita ta bada izini ya kawo sadakinta
yanzu. Aka hau kallon-kallo a tsakaninsu dan sun
ji magana ta nutsa ba ma kudin na gani ina so ba
ko kudin gaisuwar uwa da uba kudin sadaki gaba
daya Sabitu ya ambata.
Dagaci ya ce "Ba za a karbi kudi a hannunsa shi
kadai ba sai ya kawo magabatansa sannan a
binciki asalinsa. "Ba damuwa, wannan mai sauki
ne, haka kuma ya kamata.
Iyayena zasu zo kuma za'a zabi wasunku a je
garinmu a gani. "In ji Abdul-Sabur.
Sai ya fara musu yayyafin Naira suka fara washe
baki.
Sabitu ya ce "Ai godiya tana gaba idan na je na
dauko muku himilin kayan daya kawo muku ku da
matanku.
Baffa ya ce, Sabitu ya je ya dauko musu ya bar
kadan. Babu wanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login