Showing 78001 words to 81000 words out of 130520 words

Chapter 27 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8045

su dade suna yi.
Ta fuskanci dai-dai lokacin da suke gida sun
dawo daga makarantar islamiyya da ta boko
kuma ba su yi bacci ba.
Sai yau Hajiyar Abdul-Basi ta karbi
wayar suka gaisa faram-faram.
Alhamdulillah, mutum rahma ne'' inji Umaimah
dai-dai lokacin da ta tsinci kanta ta amsa wayoyi
har
sau shida a jejjere.
Hanif ne ya kira ta daga Najeriya ya bata hakuri
saboda bai kai sakonta da wuri ba, ya tabbatar
mata kuma gobe ne insha Allah ya shirya zuwa
'Dugge' neman gidansu zai kai mata wadannan
sakonnin.
Farin ciki ya rufe ta, ta yi masa godiya gami da yi
masa magiya kada kuma ya sake shiga wasu
safgoginsa wadanda ya saba yi, ga shi har ya
shafe wata guda cur a Najeriya bai je ya kai
sakonta ba.
Wannan karon dai ya tabbatar mata gaske yake
zai je.
Allah cikin ikonSa kuwa ya cika mata alkawari, ya
nemi gidansu a Dugge, ya kai mata sakon hannu
da hannun Baffanta da Sabitu ya damka.
Misalin karfe goma sha biyun rana a agogon
Najeriya wanda yayi dai dai da karfe bakwai na
dare a agogon Malaysia, wayar Hanif ta shigo
wayar Umaimah, shigowarta gida kenan daga
gidan Faduwa tana shirin dauro alwallar magruba.
Data dauki wayar maimakon ta ji muryar Hanif
tunda lambarsa ce sai ta ji yaren fulatanci ne
maimakon Hausar da suka saba yi. Muryar
tsohonta ta ji, Baffa yana ambaton sunanta cike
da farin ciki
marar misaltuwa. Ta daka tsalle don murna ta
fashe da kukan dadi. Fadi ta ke, ''Baffa ka yafe
min. Alhamdulillah da Allah Ya sa kana raye.
Shi ma kukan dadi yake yana hamdala da Allah
ya sa tana raye tana cikin koshin lafiya. Ya
shaida mata cewar ya kasance cikin dumbin
damuwa a lokacin da Abdu-Basi ya zo ya shaida
musu ba ya tare da ita.
Sabitu ma ya karbi wayar ya gaishe ta sannan ya
shaida mata sun karbi sakon da ta aiko musu sun
ji dadin sakon kudin nan sosai don ta aiko musu
a lokacin da suke tsananin bukatarsu saboda
al'amura sun tsananta a gare su, abincin ci ya yi
musu wahala, wataran a ci, watarana a rasa a
kwana da yunwa.
Sai ta fashe da kuka don tausayinsu, sai ta sake
godewa Allah da ya hore mata har ta kai
matsayin da zata taimaka musu.
Hanif ya shaida mata gari 'Dukku' suka taho don
su yi waya babu service a 'Dugge' har yanzu, ko
wutar lantarki ba su da shi balle ayi cajin waya.
Sai ta roki Hanif ya siya musu layin waya ya
saka musu a cikin wayoyin ya saka musu a caji
ya kuma kunna ya saka musu lambarta, sannan
ya koyawa Sabitu yadda a ke yin wayar. Lokaci
lokaci sai su dinga zuwa Dukku suna kiranta suna
yin magana.
Ta sake rokar Hanif ya karanta musu wasikar da
ta rubuto musu.
Hanif ya aiwatar da duk abinda ta bukata. Ya
sake kiranta da layin Baffa da na Sabitu suka yi
magana
da wayoyin dukka biyu. Suka sake daukar lokaci
suna hira, ta sake yi musu bayani yadda za su
dinga yi da wayar suna samunta duk lokacin da
suke bukatar yin magana da ita. Sun gamsu da
bayananta sosai, sannan ta ce su adana kudin da
ta aiko musu, su nutsu su ga irin sana'ar data
kamata su yi dan kudin ya yaukaka ya zama
babban jari, su sami na cin abinci a saukake a
cikin riba ba tare da uwar kudin ta wargaje ba.
Ta sha addu'ar fatan alkhairi, da shi albarka daga
wajen Baffa da Sabitu.
Daga karshe ta yi masa godiya suka kashe waya.
Saboda dadi Umaimah ta durkusa gwiwoyinta
dukka biyu a kasa ta daga hannayenta biyu sama
tana yi wa Allah godiya da ya fara warware mata
matsalolinta. Ta yiwa Abdul-Sabur addu'a da
fatan
alkhairi da fatan Allah Ya saka masa da gidan
aljanna shi da yayi mata sanadiyyar nemo
iyayenta
da *ya*yanta dan ba dan shi ba da wannan
tunanin ba zai taba kawowa a kwakwalwarta ba.
Farin ciki ya hana ta daurewa, nan da nan sai ta
bugawa Abdul-Sabur waya kafin ta yi masa
bayani
ma ya fuskanci tana cikin nishadi. Ta shaida
masa dimbun farin cikin da ya same ta yanzu a
sanadiyyar jin muryar Baffanta da kaninta Sabitu.
Sai ya ji dadi shi ma a ransa, ya taya ta murna
ya kuma sake mata nasihohi masu ratsa jiki
game da yadda Musulmi ya kamata ya zauna da
Musulmi dan uwansa. Ya sake gargadinta da ta
zauna da kowa lafiya a duk inda take ta rike
mutum da daraja ko yaya matsayinsa yake a
rayuwa, don mutum yana da daraja a wajen
mahaliccinsa, ba abin wulakantawa ba ne.
Umaimah ta yi masa alkawari zata bi duk
nasihohin da ya yi mata, kuma zata ci gaba da
saka shi a cikin addu'arta bisa kokarin da ya yi
mata wajen ceto rayuwarta daga kunci zuwa farin
ciki.
Daga dukkan alamu Abdul-Sabur ya fi ta jin dadi,
fadi ya ke, ''Alhamdu lillah, nima na gode miki.
Tana godiya yana godiya har suka katse waya.
Allah Akbar! Allah mai musanya duk abin da Ya
so Ya canzu.
********************
Tuni Faduwa ta kammala makarantar koyon tukin
mota a cikin wata daya da sati daya, aka buga
mata 'driving licence' dinta aka ba ta. Har ta
zamto tana tuka motar Abdul-Sabur tana kai
Umaimah Makaranta ta dauko ta, da yamma
kuma ta tuka su fita yawo. Da farko tsoro ne ya
hana Umaimah kwarewa a tuki, amma gori da
tsokanar da Abdul-Sabur da
Faduwa suke yi mata itace ta sanya zuciyarta ta
dake ta kuduri niyyar dagewa ta koya.
Tabbas tana kokari matuka don Abdul-Sabur ya
kan fito ya tsaya ta barandar baya ya ga
wucewarta a cikin motar Makarantar ita da
Malamin da yake koya mata, har sun fara hawa
manyan titina.
Allah cikin ikonSa a satin da zasu koma
makaranta a satin Umaimah ta ci jarabawarta ta
makarantar
koyon tuki, aka bata satifiket da 'driving licence.
Tana ta tsalle da murna a lokacin da ta karbo,
don taya bera-bari har hotuna Faduwa ta dinga
yi mata dauke da satifiket din a hannunta. Ta sha
yiwa Umaimah hotuna ita kadai, sannan suka yi
da Faduwa, Abdul-Sabur ne ya dauke su, sanan
aka yiwa Umaimah da Abdul-Sabur, Faduwa ta
dauke su. A halin yanzu duk inda za su je
Umaimah ce take
tuka su. Tabbas hannu ya fada sosai ma, ta san
dokokin tuki ko'ina tana kai kanta har wani gari.
Don ita ta tuka su suka je har 'Mantin' Garin su
Hanif, da yake hutu ya kare ya dawo daga
Najeriya.
Ta je ta karbo hotunan da su Baffa suka aiko
mata. Hotuna ne da yawa, bayan na Baffa da ba
Sabitu har da na *yan garinsu kamar na matan
Babanta Nene da Inna, ga na kawayenta da
*ya*yansu. Ta
cika da mamaki taf a lokacin data ga hotunan
Matawata da Ilah, sai ta zabura ta wurgar don
firgici. ''Lafiya? Faduwa, Abdul-Sabur da Hanif
suka tambaye ta.
Ta girgiza kai, hawaye mai radadi ya sirnano
mata.
Ta yi murmushin karfin hali. Ta ce, ''Hoton Ilah
da Matawata suma suka aiko min shine yasa na
firgita.
Faduwa da Abdul-Sabur saka hau rige-rigen
daukowa su gani. Tabbas mutanen ruga ne sosai,
babu digon birni a jikinsu.
Faduwa ta yi dariya, ta ce, ''Allah na tuba,
Umaimah ina ke ina aure da wannan bawan Allah
'Ilah?
Ina ke ina kishi da wannan 'Matawata? Ai ko ada
ma ba ajinki ba ne balle yanzu. Idan kika ga Allah
Ya yi ikonSa Ya hana bawansa abunda kake so
to ka
rungimi kaddara kawai kayi hakuri, Allah Shi Ya
san me yake nufi, kuma me zai faru, dan abun
nan da kake so ba alkhairi ba ne a wajenka. Da
Ya hana ki auren Ilah, alkhairi ne don Ya yi niyyar
daukaka ki fiye da su. Ki yi fatan auren mijin da
ya dace da rayuwarki kawai, tsakaninki da su sai
taimako na
musulunci.
Abdul-Sabur ya ce da Faduwa, ''Ke rufe mana
baki, an fada miki akwai maganar kudi, wayewa
ko kyau a soyayya ne?
Ai shi so ba ruwansa da bakauye ko dan birni.
Suka kyalkyale da dariya su dukka aka ci gaba da
kallon hotuna. A wata ambulan daban Umaimah
ta
buda, nan kuma hotunan *yan Gombe ne wato na
Bilal da Babangida kowannensu an yi masa shi
kadai, sannan da wanda aka yi musu a tare su
biyu. Sun girma sosai, kuma da kyan kamarsu
tamkar a gaban mahaifansu su ke. Kamarsu daya
sak tamkar uwa daya uba daya.
Umaimah ta dafe kirji ta rushe da kukan dadi, sai
ta sumbaci hotunan gami da daga ido sama ta
godewa Allah da Ya raya mata *ya*anta, basu
tagayyaraba bayan tahowarta.
Su Abdul-Sabur ma suka karbi hotunan suka
kalla tabbas sun taya ta murna, yaran sun ba su
sha'awa,
kyawawan *ya*ya gaba daya sun juye kamannin
Umaimah.
Faduwa mai son yara sai ta hau rungume hoton
tana sunbatar hotunan.
Dukkan godiya ta tabbata ga ubangijin talikai,
mai kowa mai komai.
****************
Da sati ya zagayo ranar Alhamis da yamma
Umaimah tana daura alala a kicin dinta, saboda
Faduwa ma ta tarki yin Alalar don Faduwa tana
son alala sosai, amma ba ta iya yi ba. Tana ta
sauri ta gama ta zuba ta kai mata ita da Abdul-
Sabur.
MAKWABTAKA 34
Ta ji ana bugun kofar gidanta da karfi ana kada
kararrawa ba adadi. Da sauri ta fito daga kicin a
gigice tana zaton ko ba lafiya ba. Ta fara lekawa
ta huda kafin ta bude don ta ga ko waye, Faduwa
ta gani duk a gigce ta ke, amma tana fara'a daga
dukkan alamu alkhairi ne ya kawo ta.
Cikin gaggawa ta bude kofa, kafin ta ce wani abu
Faduwa ta yi caraf ta rungume ta tana tsalle.
Umaimah dai dariya ta ke taya ta gami da
tambayar ta, ''Lafiya? Me ya faru? ''
Albishirinki? Inji Faduwa.
Umaimah ta ce ''Goro fari tas-tas.
Faduwa ta ce, ''Sai kin ba ni goro zan fada miki.
Umaimah ta yi-ta yi Faduwa ta fara fada mata
inyaso ta dauko mata goron. Faduwa ta ce,
gaskiya sai an
ba ta goro zata fada, don albishir din babba ne.
Umaimah ta cika da mamaki matuka, ta ce, ''To,
bari
na je daki na dauko miki goron sai ki fada min.
Ta shiga dakinta ta yi diri-diri ta rasa ma me
zata dauko mata. Ta rasa mene wannan abu da
Faduwa
ta ke ja mata rai kafin ta fada mata.
A zuciyarta ta ke magana, ''To ko Abdul-Sabur
ne ya amince zai aure ta, shi yasa ta ke murna?
Haka ne ma labarin, ina jin ya fada mata ni na ce
ya dace ya aure ta shi yasa zata yi min albishir.
Ta jawo jakarta ta bude ta dauko kudi Riggit dari
biyu, wanda ya yi dai-dai da naira dubu tara, ta
kawo mata. Faduwa ta karba, sannan ta cewa
Umaimah ta rufe idanunta. Tunda ta kagu ta ji
sai ta
yi sauri ta rufe idanunta.
Faduwa ta ce, ta miko hannayenta duka biyu.
Umaimah ta yi yadda ta umarce ta. Da faduwa ta
saka mata abu guda biyu kowanne hannu guda
daya sai ta umarci Umaimah ta bude idanunta ta
gani.
Da ta bude ta duba sai ta kasa fahimtar abin da
Faduwa ta ke nufi. Mukulli ne guda biyu a
kowanne hannunta.
Ta tambayi Faduwa cike da rashin fahimta,
''Mukullan me ye wannan? Faduwa ta ce,
''Mukullan motocinmu ne ni da ke kowa daya.
Umaimah ta turo baki ta ajiye mukullan akan
tebur ta ce, ''Anti Faduwa, wallahi kin cika son
wasa.
Wacce irin mota kuma, ya za a yi ki ce mukullin
motata? Na dora abinci akan wuta bari na je na
duba kada ya kama.
Ta shiga kicin da gudu ta ci gaba da daura alala
tana jefawa a cikin ruwan zafin da yake a kan
wuta.
Faduwa ce ta sake debo mukullai ta biyo ta kicin
ta ce, ''Wallahi da gaske nake mukullan motarmu
ne.
Umaimah ta tsaya tana kallonta tana mamakin
irin wannan son wasa da tsokana na Faduwa.
Faduwa ta ce, ''Na ga alamar har yanzu ba ki
yarda da ni ba, to gama daura alalar ki zo mu
sauka kasa
sai ki ga zahiri.
Umaimah ta gama sannan ta dauko gyalenta ta
biyo Faduwa kasa. Kai tsaye Faduwa ta shige
wajen da aka tanada don ajiyar motoci. Ta je ta
bude wasu motoci guda biyu iri daya, sai dai
bambancin fenti. Saboda mamaki sai Umaimah ta
kame a tsaye
tana kallon Faduwa da motocin da aka fi hawan
irinsu a Malaysia 'persona' Har yanzu da ragowar
kokonto a cikin zuciyarta, tana ganin kamar wasa
Faduwa ta ke yi mata.
''Me yasa Abdul-Sabur zai yi tunaninya saya
mana motoci?
A wanne dalili? Umaimah ta ke fada a cikin
zuciyarta.
Faduwa ta ce, ''Zabi daya wacce kala kika fi so,
baka ko ruwan tokar? Cikin rawar jiki Umaimah
ta ce, ''Duk wacce kika zabar min.
Faduwa ta ce, ''Ki dauki ruwan tokar tunda na fiki
haske, sai in dauki bakar.
Ta mikawa Umaimah mukullin motarta a hannu
yayin da Umaimah ta ji tamkar a mafarki, wai yau
ita ce a kasar waje, har ta mallaki mota wanda
tunda take a rayuwa ta ke matukar sha'awar duk
macen data ga tana tuki. Bata taba saka ran zata
yi mota ba a rayuwarta. Duk da dan Adam ba ya
fitar da rai da samun rahamar Ubangiji. Allah
Yana iya mallakawa bawanSa mulki, dukiya, lafiya
ga wanda Ya so, kuma Ya hana idan Ya so.
Umaimah ta yi tsalle ta kankame Faduwa suka
hadu suka sha tsalle-tsalle suna murna su biyu.
Yayin da
tsurarun jama'ar da suke wajen suka jeru suna
kallonsu, su ma fuskokinsu cike da murna sun
fuskanci abun alkhairi ne ya same su. Da yake
Faduwa duk ta sansu sai ta dinga jawo su tana
sanar musu yau aka yi musu kyautar su. Ba ta
fadi wanda ya saya musu ba, amma dai ta ce su
zo gidanta gobe da yamma zata yi gagarumar
liyafa.
Faduwa da Umaimah ne suke tsaye a kofar gidan
Abdul-Sabur suna kwankwasawa. Da alama ba
ya zaune a falo saboda sai da ya jima kafin ta
bude.
Daga dukkan alamu ma daga wanka ya fito
saboda jikinsa a jike da ruwa yake, yana sanye da
doguwar riga jallabiya.
Yaune karo na farko da Umaimah ta tako
bangarensa (block) ballantana ta shigo gidansa.
Ya yi matukar mamaki da ganinta, kallo daya
zaka yi masa ka tabbatar da hakan. Ya yi musu
iso suka shiga suka zazzauna a falo, yayin da ya
nemi izininsu sannan ya shiga daki ya saka
kayansa riga da wando (jeans & T.Shirt) ya fito
ya zauna tare da su. Suka gaishe shi sannan
Faduwa ta fara bayani. Ta ce, ''Abdul ka fadawa
Umaimah da bakinka ko zata yarda saboda na ga
alama har yanzu ba ta gama yarda cewar
wadannan motocinmu ne ba, kai ka sayo mana.
Abdul-Sabur ya kyalkyale da dariya, ya ce,
''Umaimah, me ye abin mamaki?
Ai tunda ku ka daure ku ka koyi mota, mallakar
motar ba wahala ba ce tunda basu da tsada a
Malaysia. Ni na ga ya dace in ba wa kowaccenku
ku huta da hawa motar haya, tafiyar kafa ko
hawa jirgin kasa.
Umaimah ta silalo daga kan kujera ta durkusa ta
yi masa godiya, gami da dogayen addu'o'i na
fatan alkhairi. Yayin da Faduwa ma ta silmiyo
daga kan kujera ta durkusa itama a gabansa ta
rangada godiya.
Abdul-Sabur ya ce, ''Haba-haba meye haka? Ya
za ku durkusa min kamar wanda na ba ku
duniya?
Allah na tuba nawa motocin nan suke da har za
ku dinga irin wannan doguwar godiya? Ku tashi
ku zazzauna. Fatana Allah Ya kiyaye tsautsayi da
asara.
Suka amsa da, ''Amin''. Suka koma suka
zazzauna.
Faduwa ta ce, ''Ina gayyatarka liyafa (lauching)
din bude motocin gobe a gidana da yamma. Zaka
iya
gayyato abokanka guda biyu ku zo tare. Abdul-
Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''A'a Faduwa ba na
son bidi'a. Me abun hada liyafa don kin yi mota?
Kin ga abin da yasa wataran ba ma shiri ko, kin
cika rawar kai. Umaimah me ya kamata ku yi?
Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''Godiya ga Allah.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yauwa, haka ya kamata a yi
ba holewa ba.
Faduwa ta zabura ta ce, ''To liyafa ba ciyar da
Musulmai ba ce a sami lada?
Abdul-Sabur ya ce, ''Party za ki hada sosai da
kek, da kunna disko na san sai kin cashe. Bayan
haduwa da mata da maza a waje daya wadanda
ba muharramanku ba. Ni dai ganina tunda mu
dukka ukun nan mun sauke alkur'ani, mu kwana
a daren yau muna karatu har sai mun sauke
kur'ani. Mun ci
sa'a kuwa yau alhamis ce daren juma'a, mu
godewa Allah da Ya ba mu lafiya, arziki da zaman
lafiya. Sannan mu yi wa iyayenmu da *yan
uwanmu musulmi da suka mutu fatan neman
gafara da aljanna ya kuma kai mu a sa'a idan
tamu mutuwar ta zo. Mu yi fatan Allah Ya raba
mu da sharrin karfe
lafiya, Allah Ya sa a tuka su lafiya, a rabu lafiya.
Sai kuma mu yiwa kasarmu ta gado addu'a, wato
Nageria fatan zaman lafiya da yalwal arziki da
wadata, mu yiwa sauran kasashenmu addu'a
kamar su Ghana, Cairo da Malaysia kasashen
musulunci Allah Ya kare Musulmi da addininSa
Musulunci.
A ganina haka ne kadai hanyar da zamu bi mu
godewa Allah ba tare da mun saba maSa ba.
Sannan kafin ku fara hawa motar kowaccenku ta
dafa saman motarta ta yi wannan addu'a
''Allahumma inni as'aluka min khariha wa khaira
ma fiha wa khaira ma jabaltaha alaihi, wa'uzu
bika min sharrinha wa sharri ma fiha wa sharri
ma jabaltaha alaihi.
''Ya Allah ina neman alkhairinta (mota) da
alkhairi da yake tare da ita da alkhairin da Ka
halicceta akai
kuma ina neman tsarinKa daga sharrin ta da
sharrin da yake tare da ita da sharrin da Ka
halicce
ta akai.
Su dukka suka yi amanna da maganarsa, suka
gasgata shi.
Umaimah ta mike tsaye ta ce, ''To karfe nawa
za'a fara saukar kur'anin kuma a ina zamu hadu?
Don zan je duba tukunya na dora abinci.
Faduwa ta ce, ''A gidanki za'a taru bayan sallar
isha'i na ga kina da kur'anai da yawa, idan mun
ci alala sai mu fara karatun. Abdul kada ka ci
abincin dare yau ka zo gidan Umaimah ka ci alala
daga gani
zata yi dadi, saboda ta sha hanta da kwai ga
albasa da attaruhu.
Abdul-Sabur ya yi dariya, ya ce, ''Ban cika son
alala ba da dai danwake ne. Umaimah ta yi caraf
ta ce, ''Zan yi maka danwaken yanzun nan kuwa,
ka zo ka ci.
Ya yi murmushi, ya ce, ''Na kuwa gode. Bari na je
masallaci na yi sallar magruba da isha'i daga
nan sai na yi sallama da gida don karatun zai kai
mu har asuba kun ga daga can sai mu yi jam'i
mu yi sallar asuba. Sannan kowa ya tafi gida yayi
bacci da safe.
Ina fatan dai babu wanda ya ke da lecture ko test
da sassafe gobe a Makaranta?
Su dukka suka ce ba su da lecture balle
jarabawa.
Umaimah da Faduwa suka fito daga gidan Abdul-
Sabur suka nufi gidajensu yayin da shi kuma ya
shiga bandaki ya dauro alwala dan Almuru
(Magaruba) ta kawo kai, ya rufo gidansa ya nufi
masallaci.
Karfe takwas da rabi bayan sallar Isha'i Abdul-
Sabur ya biya ta gidan Faduwa ko zama bai yi
ba,
ya iske ta a shirye tsaf sanye da hijabinta ta idar
da sallar isha'i dan haka sai ta rufo gidanta ita
ma suka
dungumo zuwa gidan Umaimah.
Bugu daya suka yiwa kofar sai ta zo ta bude
musu.
Babu shakka sun yi farinciki da ganin Umaimah,
domin yadda ta karbe su da farin ciki. Ta tsaftace
gidanta kal-kal-kal ko kwayar tsinke babu a
kasa. Kai ka ce harshe aka saka aka sude tiles
din gidan.
Kamshin turaren wuta tururu daga shigowarsu
kamshin ya daki hancinsu.
Umaimah sanye ta ke da riga da siket na
material,
sannan ta saka dogon hijabi daga dukkan alamu
daga sallah ta idar da carbi a hannunta. Kan
dinning table kai tsaye ta wuce da su inda ta
tsara shi ta kawata da food flask da jugs na
alfarma,
ga farantai da cokulla a gefe.
Daman su dukka ukun tsananin yunwa suke ji,
sai suka zauna gaba dayansu kowa ya jawo
farantinsa
da cokali. Umaimah ta bubbude kowanne flask
sai kamshi tururu ya daki hancinsu. Alala ce a
flask daya, dan wake a daya flask din, yayin da
daya flask din hadaddiyar shinkafa ce 'fried rice'
tasha curry, hanta, peas da karas. Yayin da flask
din karshe farfesun kaza ne mai romo da yawa an
dafa da dankalin turawa sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login