Showing 87001 words to 90000 words out of 130520 words
Chapter 30 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
ta. Hakika zuciyarta tana matukar kaunar
Abdul-Sabur, son ba na wasa ba.
''To ashe na so in tafka kuskure da nake kokarin
kakaba masa Umaimah, ni nake sonsa, NI NA FI
CANCANTA da shi ba ita ba?
Uncle Hamza ka cuce ni da ka kakaba masa
*yarka kace ya aura, da ace ba shi da kowa
tabbas Abdul-Sabur zai so ni kamar yadda na ke
sonsa, don mun shaku.
Ta jawo wayarta a sanyaye ta kira lambar
Umaimah bugu daya ta bude ido daga baccin da
ta dan fara yi. Fatanta ace Abdul-Sabur ne, sai
ta ga Faduwa,
murna ta koma ciki. Ta amsa dukkanninsu
magana suke yi cikin rashin kuzari.
''Abdul-Sabur bai kira ki ba har yanzu Faduwa ta
tambayi Umaimah.
Ta ce ''Bai kira ni ba Anti Faduwa. Allah Ya sa
dai lafiya.
Faduwa ta ce, ''Insha Allah lafiya kalau Umaimah.
Zai kira, mu kwantar da hankalinmu.
Bayan sun ajiye waya sai kowannensu ya shiga
tunanin ba dai abin da yake addabarsa na so shi
yake addabar dan uwansa ba. Caf! Idan haka ta
kasance a kwai matsala ke nan. Ko da yake
wacce matsala ma, mutumin da babu wacce yake
so a cikinsu ya riga ya sami matar da zai aura
baturiya,
aka bibiya ma ya manta da su.
Haka su dukka suke tattaunawa a cikin
zuciyoyinsu.
Faduwa dai ta damu ta tantance wannan zargi da
zuciyarta ta ke yi mata reto kulum. Ta yanke
hukuncin gara ta sami Umaimah gar-da-gar su ji
ra'ayin juna. Saboda ita yanzu saura wata guda
kacal ta kammala karatunta don haka tana so a
cikin satin nan ta kaura cikin makarantar kacokan
don ta zana jarabawar karshe. Zai fi mata sauki
ta kaura cikin makaranta ta daina ma hango
gidan Abdul-Sabur, balle ta yi zaton zata hango
shi.
Tuni ita ma ta cike takardar tashi daga gidan har
ta yi musu cikon kudinsu na haya don ta zarta
shekara da watanni biyu. Ta ji tausayin Umaimah
ga shi su dukka zasu watse su bar ta tasan ba
zata ji dadin zama ba. Ita ma ta shiga jin nauyin
fadawa Umaimah za ta tashi don kada ta shiga
damuwa irin yadda Abdul-Sabur ya dinga larurar
fada musu da zai tashi.
Faduwa ce a kofar gidan Umaimah tana bugawa,
a rashin sa'a ba ta same ta ba, don haka sai ta
kira wayarta, Umaimah ta shaida mata tana
makaranta sai karfe hudu zata dawo.
Faduwa ta ce, idan ta taso ta zarce 'Sunway
pyramid' inda suka saba zama da Abdul-Sabur.
Umaimah ba ta tambaye ta me ysa ba, ta amsa
mata da, ''to, zan je insha Allahu. Karfe biyar da
rabi suka hadu a can Umaimah har ta
riga Faduwa isowa dan a tasi ma ta je, ta kai
motar wajen wankewa. Su ka rungumi juna don
murna,
saboda sun dade ba su haduba. Suna zama sai
ma'aikata suka jero musu sunayen abinci da abin
sha kala-kala.
Faduwa a koshe ta ke saboda daga gida ta ke,
Umaimah ce ta ke jin bakar yunwa. Don haka ta
zabi abinci har kala biyu, shinkafa da rabin kaza
sai jalof din taliya, kowanne ya zabi kalar lemon
da yake so.
Bayan an jere musu a kan tebur sai aka ajiye
musu risitin kudi. Babu wacce ba ta tuno da
Abdul-Sabur ba, me biya musu kudin duk abin da
suka ci, sai yau suka san ashe abincin da suke ci
mai tsada ne.
Aka hau rigaye-rigayen biyan kudin a junansu
daga karshe Faduwa ta yi sauri ta mikawa
ma'aikacin kudi.
Ta ce ''Nice babba, na karbi girman da Abdul-
Sabir ya dauka a baya.
Idan ina waje duk abin da kika ci ni zan biya miki,
kanwata.
Umaimah ta yi murmushi, ta ce ''To na gode
Antina.
Umaimah tana cin abinci suna hira har ta koshi
ta ajiye sauran sannan Faduwa ta gyara zama ta
zare farin gilashin da yake fuskarta, ta dubi
Umaimah. Ta ce, ''Umaimah, kin rame sosai, ba
ki cika walwala ba, me yake damunki.
Umaimah ta girgiza kai, ta ce,''Karatu ne saboda
darasi ya kankama yanzu a makaranta, babu hutu
sosai.
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Bayan wannan
akwai kewar Abdul-Sabur ko?
Umaimah ta dan yi murmushi ta ce, ''Hmm, ya za
a yi?
Haka sabo ya ke.
Faduwa ta ce, ''Kun taba yin wata magana da
Abdul-Sabur game da ni?
Umaimah ta firgita da jin wannan tambaya, yayin
da kanta ya juye.
''Ban fahimce ki ba? Umaimah ta fada a gigice.
Faduwa ta ce, ''Mun yi maganarki da shi na zaci
ya furta miki
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Bai furtamin
komai ba, me ku ka ce?
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Tunda bai fada
miki ba, bai dauki maganar da muhimmanci ba.
Umaimah ta ce, ''Ni ma na yi maganarki da shi,
ko ya taba fada miki?
Faduwa ta gyara zama, ta ce, ''Don Allah fada
min abin da ku ka ce, bai taba fadamin ba
wallahi.
Umaimah ta girgiza kai ta ce, ''A'a, ba sai na
fada miki ba. Da dai kin fada min naki ne sai in
fadi nawa.
Suka kwashe da dariya su dukkansu.
Faduwa ta ce, ''Irin na yara ke nan, ki fara fada
min sai in fada miki. Umaimah ta yi ajiyar zuciya
ta ce, ''Ce masa na yi ya aure ki, kun dace.
Faduwa ta zabura ta dafe kirji ta ce, ''Ya aka yi
tunaninmu ya zamto iri daya?
Ni ma shawara na ba shi na ce ya aure ki.
Umaimah ta rike baki don mamaki.
Faduwa ta girgiza kai, ta ce, ''Bai ba ni amsa ba
har sai ranar da ya yi mana bankwana ya shaida
min Uncle Hamza ya ba shi *yarsa ita zai aura.
Umaimah ta yi shuru kamar mai takaici, can ta
gyada kai, ta ce, ''Tabbas ni ma irin wannan
amsar ya ba ni da na sake tuntubarsa da
maganar a lokacin da ya rage saura awa guda
jirginsu ya tashi.
Suka yi tagumi su dukka biyun suna tunani da
alamar damuwa a fuskokinsu. Har zuwa lokaci
mai
tsawo babu mai magana a cikinsu.
Faduwa ta nisa sannan ta dago ido sama tana
kallon silin rumfar da suke zaune a ciki. Tayi
murmushi ta ce ''Ada ban sani ba sai yanzu na
tantance ashe ni nake son Abdul-Sabur. Ashe ni
da kaina, ni nafi son Abdul-Sabur, rashin sani yafi
dare
duhu, gashi ashe kema kin yi min sha'awarsa har
nake kokarin turaki ni in koma baya.
Umaimah tayi murmushi ta ce, ''Ina kyautata
zaton abunda ya faru da ke shiya faru da ni. Na
so in hada soyayyarku ashe ni ce mai sonsa sai
yanzu nima zuciyata ta gama tantance min.
Faduwa ta kura mata ido tana kallonta, itama
Umaimah ta zuba mata ido suka dade suna
kallon juna.
Faduwa ta yi murmushi ta ce ''Ashe matsalarmu
iri daya ce kenan?
Yanzu ina mafita?
Umaimah ta yi dariya ta ce, ''Ai magana ta wuce
Anti Faduwa, tunda Abdul-Sabur ya tafi bai sake
waiwayar daya daga cikin mu ba, sannan ya riga
ya zabi wacce yake so bai zabi daya daga
cikinmu ba.
Faduwa ta ce, ''Misali da ace zai dawo ya ce zai
aure mu, mu dukka biyun zaki yarda mu zauna
tare?
Wannan magana ta Faduwa ta gigita Umaimah
sannan ta bata mamaki matuka. Dan haka sai ta
gagari bada amsa.
Faduwa tayi *yar siririyar dariya ta ce, ''Ina
tausayinki fiye da kaina duk da nasan nima abar a
tausayawa ce shiyasa na hakura da son Abdul-
Sabur ina ganin ba zan samu ba dan na yi masa
girma. Na ga ke da shi zaku fi dacewa
musamman yadda na ga ya damu da shiga
harkarki. Na so in hada wannan soyayyar cikin
rashin sani ashe kema kin min irin wanna
sha'awar hakan ya jawo rudewar tunanin Abdul-
Sabur ya yanke shawarar ya bar mu kawai mu
dukka saboda baya so ya batawa kowannenmu
rai.
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Nima na fara
tunanin shine dalilinsa na tafiya ba waya. Anti
Faduwa ina sonki, ina son ki sami miji na gari
kamar Abdul-Sabur.
Daga sanda muka hada miji daya daga lokacin
zamu fara kishin junanmu komai na rashin dadi
zai iya faruwa. Ina da kishi sosai musamman ma
yanzu dana mallaki hankalin kaina kuma na sami
zabin zuciyata Abdul-Sabur, ba kamar Abdul-
Basi ba wanda aka hada ni da shi. Na san irin
zafin kishin dana dandana a lokacin da naga
Abdul-Basi da Zulayha suna son junansu, da
kuma sanda naga Matawata da Ilah suna son
junansu. Barci da abinci sai da ya gagare ni ci.
Ba zan iya jera kishi da ke ba saboda duk
Malaysia ba ni da tamkar ku. Ina nan akan baka
ta ina son Abdul-Sabur amma ba zan iya aurensa
ba saboda ke, na bar miki ki aure shi. Idan Abdul
ya aureki kin yi dace da miji na gari, kuma in dai
muna raye na yi miki alkawarin zan yi miki yaki
har sai kin same shi da izinin Ubangiji.
Faduwa ta yi murmushi yayin da idanunta suka
cika da kwalla.
Ta ce, ''Umaimah, ta yaya zaki taya ni yakin
neman soyayyar Abdul alhali ya sami wacce zai
aura, *yar
uwarsa, gata baturiya?
Umaimah tayi murmushi ta ce, ''Allah Ya
halaktawa maza su auri mata biyu, uku ko hudu
dan haka koya auri waccan zai iya aurenki.
Faduwa ta matse dan guntun hawayen daya fara
tsattsafowa daga idanuwanta.
Ta ce ''Ko kina so ki taimaka in sami Abdul-
Sabur ai sai mun gan shi a gabanmu amma kuma
yanzu baya nan ya tafi baya ko waiwayarmu.
Umaimah ta nisa ta ce, ''Na ji a jikina Abdul-
Sabur zai dawo. Kuma duk inda muka kai ga yin
kewarsa na tabbata ya fi mu kewar rashinmu
saboda nasan halinsa na yawan jin tausayi da
damuwa da
mutane, sannan yana mayar da matsalar wani ta
zama matsalarsa.
Faduwa ta ce ''Lallai kin san halayen Abdul-
Sabur kema, kamar yadda na san shi nima. Bari
in fada
miki abunda ba ki sani ba tun daga kan Sagir ban
taba son wani da namiji a duniya ba sai yanzu
dana
hadu da Abdul shiyasa abun yake bani tsoro.
Yanzu a rayuwa duk wanda nake so ya bi bayan
Abdul-Sabur, shi ma kuma ya zo ya tafi kamar
yadda Sagir ya tafi. A rayuwata ba zan taba
samun abinda nake so ba kenan?
Sai ta rushe da kuka mai tsanani.
Kwalla ta cikawa Umaimah ido tana tausayin
kanta amma ta fi jin tausayin Faduwa, ta shiga
tunanin hanyar da zata bi ta share mata wannan
hawayen da ya ke ta shatata.
Hmm..
In da akwai wanda ya shirya a gidan nan yayi
magana na bashi faduwa...
MAKWABTAKA 38
Sai ta dafa kafadar Faduwa tana girgizawa kamar
me lallashin yaro karami.
Ta ce, "Share hawayenki yayata, aure lokaci ne
insha Allahu zaki yi aure kuma sai kin auri wanda
kike so.
Faduwa ta yi dariya ta sharce hawaye ta ce,
"Haka ne Umaimah amma baza ki gane halin da
nake ciki ba ne, kin ga ke kin taba yin aure har
kin haifi da gashi har yanzu ke yarinya ce da
kuruciyarki ko nan da shekaru goma kika kai baki
yi aure ba, babu matsala sosai da sauran ki. Ni
kuwa fa shekaruna suna ta tafiya babu aure,
babu haihuwa, babu takamaimai mai sona.
Astagfirullah, ba wai ina korafi ba ne akan nuna
gajiyawaba, a'a nasan Allah Ya na sane da ni
kuma na gode maSa a duk halin dana tsinci
kaina.
Faduwa da Umaimah suka surnano da hawaye
masu radadi a lokaci guda saboda tsananin kunar
da zuciyoyinsu suke yi, daga nan babu wanda ya
sake cewa komai suka yunkura suka mike tsaye a
lokaci guda, suka taka da kafa inda ake ajiye
motoci suka shiga,
Umaimah ce ke tuka motar Faduwa suka nufi
gida.
Faduwa ta dubi Umaimah ta ce, "Na dade ina son
inyi miki sallama saboda bansan yadda zaki ji ba
ne idan na fada miki da wuri kafin lokacin ya zo.
Yanzu abin ya zo daf da faruwa dole in sanar
miki. Irin yadda Abdul-Sabur yayi mana har nake
ganin laifinsa da bai yi mana sallama da wuri ba,
ashe abu ne mai nauyin fada dan zai bata zuciyar
masoyi.
Umaimah ta kalle ta duba na rashin fahimta.
Faduwa ta yi dariya ta ce, "Saura wata daya mu
kammala karatunmu, zamu fara jarabawar karshe
shiyasa gobe nake son in kaura Hostel din cikin
makaranta in yi jarabawa a nutse zai fi min
kwanciyar hankali saboda rashin Abdul-Sabur ba
kara min taba ni yayi ba har naji bana son zaman
gida.
Umaimah ta girgiza kai kawai ba tare da tasan
abunda zata ce mata ba, abubuwa biyu ne suka
soki zuciyarta. Na farko: tsananin son Abdul-
Sabur amma ya zama haramiyarta ko ta gan shi
ba yadda
zata yi ta same shi.
Na biyu: takaicin rashin Faduwa daga gidansu,
zata zama ta rasa kowa, ma'ana ungulu zata
koma gidanta na tsamiya. Irin rayuwar
kadaicin data sha fama a baya. Hawaye mai zafi
ya sirnano daga idanuwan Umaimah ta ce, "Allah
Ya baki sa'ar cin jarabawa. Ya kaddara
saduwarmu. Amin
Da suka isa wajen ajiye motocin dake gidan sai
suka yiwa juna sallama akan sai gobe da safe in
Faduwa zata tafi zata shigo ta yi mata sallama.
Umaimah ta shiga gidanta, Faduwa ma haka su
dukka suna dandana kuna da zugin ciwon son
Abdul-Sabur da ciwon rabuwa da juna.
Haka kuwa aka yi, washegari da safe Faduwa da
kawayenta da suka zo tafiya da ita sai suka
shigo
gidan Umaimah zata yi mata sallama, tana
ganinsu ta rushe da kuka sai tausayinta ya kama
su.
Faduwa ma kuka take dan ta san tsananin kunar
zucin da Umaimah zata ji a sanadiyyar zaman
kadaicin da zata yi, suka taru suna lallashin
Umaimah suna bata baki.
Faduwa ta ce, "Ai gari daya muke, zamu dinga
haduwa akai-akai, kina da mota ina da mota duk
sanda muka yi niyyar ganin juna sai mu ziyarci
juna. Kuma zamu hadu a ranar Graduation din
mu.
Umaimah ta sharce hawaye ta ce, ''Insha Allah
zan zo, Allah Ya kaimu.
Umaimah ta jawo mayafinta zata yi musu rakiya
sai suka ce ta yi zamanta sun gama cika kaya a
motoci,
tafiya kawai za su yi har sun fitar da motocin
kofar gida.
Umaimah ta koma ta zauna akan kujera a
sanyaye har yanzu bata daina zubar da hawaye
ba, tana ji
tana gani Faduwa ta tafi ta barta. Ta bude wundo
tana leken su Faduwa har suka shude sannan ta
sulale ta tsuguna a gaban wundo,
sabon kuka ya kece mata. Babu abin da ta tuna
sai sanda Abdul-Sabur ya nace a dole sai sun
saba da ita, ya daure da duk irin wulakancin data
dinga yi musu a jejjere. Allah Sarki! Suka ci gaba
da lallashinta suna ta bin ta har sai da ta yarda
ta saba dasu amma yau ga rabuwa ta raba dukka
sun watse sun barta ita kadai kamar mayya a
gidan,
yanzu sai ta ci abinda zata ci.
Tayi kuka harta godewa Allah sai da ta gaji da
kanta ta daina ta hakura saboda babu mai
lallashinta. Kwayar idanuwannan farare sol sai da
suka yi jajawur kai ka ce garwashi ne aka rura,
yayin da kanta ya daure da ciwo kamar zai tsage.
Ta rarrafa ta sulale ta kwanta akan doguwar
kujera sai shesshekar kuka take da ajiyar zuciya
kamar
yarinya *yar goye.
Barci ya dauketa mai nauyi ta yini tana yi.
*
A daddafe take daurewa tana ci gaba da rayuwa
tabbas ba karamin kokari take yi ba data ci gaba
da
zama a gidan, ji take tamkar ta tashi tabar gidan
sai ta tuna ashe ba zaman gidan ba ne
matsalarta wadanda ta saba da su ne ta rasa, su
ne damuwarta ko ina ta koma ba ganinsu zata yi
ba.
"Me yasa na yarda na saba da su alhali sun san
tafiya zasu yi su barni. Umaimah take fada a
bayyane.
Kusan kullum suna yin waya da Faduwa shi ne
ma yasa take samun saukin damuwar da take
ciki,
amma da karatu ya yi karatu ko ta kira wayar
Faduwa sai ta jita a kashe. Musamman da suka
fara
jarabawa Faduwa sai ta yi sati guda ba ta kunna
wayarta ba.
Umaimah ta rungumi kaddara a dole take sabawa
da kanta zaman kadaici. Kullum sai ta kira
*ya*yanta a waya su yi ta hira, shi ne kadai
samun saukin kuncin da take ciki. Sannan kuma
tsohonta da kaninta idan suka fita birni sai su
kirata, idan ta ji muryasu suna cikin kosjin lafiya
sai ta ji sanyi a ranta nan ma. "Haka Allah Ya so
yi da ni, haka Ya ke son Ya ganni.
Umaimah ta fada a lokacin da ta saka abinci a
gaba ta kasa ci saboda kewar Abdul-Sabur.
Hawaye mai zafi ya sirnano daga idanuwanta ta
girgiza kai.
Ta ce ''Raba zuciyata da son Abdul-Sabur ba
karamin tashin hankali ba ne. Hakika ban taba
son wani da namiji ba a duniya irin yadda naji son
Abdul-Sabur. Allah Ya yayemin sonsa dan ya
zama cuta a gare ni, ya tafi ya bar ni da ciwo
kuma ko ya
dawo ma kwalelena dan na yiwa Faduwa alkawari
zan bar mata shi. Tabbas zan dauwama cikin
kunci
muddin zuciyata ta rasa Abdul-Sabur. Meye ma
ya kai ni furta masa ya zo ya auri Faduwa, gashi
nan mun yi biyu babu mu dukka. Dama ace
sanda Faduwa ta fada masa cewar ya aure ni, ta
fada min
halin da ake cik da ba zan yi garajen yi masa
maganar ya auri Faduwa ba. Na san shine kadai
dalilin da yasa ya bar mu, mu dukka.
*
A lokacin da Umaimah take shirin fara jarabawar
2nd semester wanda ita ce zasu gama level two,
shekara me zagayowa war haka zata gama
karatunta na digiri gaba daya itama.
Faduwa ce ta kirata a waya take sanar mata
cewar bikin yaye su (Graduation ceremony) ranar
litinin karfe goma na safe a 'Nilai Spring Hotel.
Umamai ta taya ta murna
game da yi mata alkawari zata ji insha Allah,
amma ta tanadar mata Katina biyu zata zo da
kawarta Aisha.
A ranar litinin da misalin karfe tara da rabi na
safe Umaimah Bello da kawarta Aisha Bingyal
suka bayyana a kofar 'Spring Hotel' ba su shiga
ba. A bakin Hotel din suka tsaya suna jiranta, dan
Umaimah ta yi mata waya ta ce tana hanya. Ba'a
dade ba sai gata nan a cikin motarta ta shigo
farfajiyar Hotel din, ta wuce kai tsaye wajen da
aka tanada dan ajiye motoci. Ta fito sanye da
riga da hula wato graduation gown. Tayi kyau
kuwa a
cikin kayan, da saurinta wajen Umaimah ta nufa
sai ta rungume ta cikin dumbin farin ciki. Sannan
Umaimah ta gabatar da kawarta ga Faduwa wato
Aisha Bingyal, sai suka gaisa. Faduwa ta mika
musu Katina guda biyu kowa daidaya.
Ashe duk yawanci jama'ar da suke tsaye bakin
kofar Hotel din jama'ar Faduwa ne, tabbas
jama'arta har sun fi karfin katinan da suke
hannunta. Ta dinga bi tana gaggaisawa da
bakinta daya bayan
daya tana ta mimmika musu Katina, da Katinan
hannunta suka kare sai ta ciro wayarta ta kira
kawayenta ta roke su da su zo su sammata
Katinansu na ta sun kare, ga sauran jama'a da
yawa basu samu ba.
Babu wanda yayi mamaki ko yaji haushi a cikin
jama'ar da suka rasa kati, kowa ya san halinta
na jama'a da yawa. Kawayenta suka shaida mata
gasu nan zuwa suna kan hanya sun kusa
karasowa zasu zo mata da katinansu da suka yi
saura.
Anan bakin kofar shiga Hotel su Umaimah suke
tsaye har yanzu basu shigs ba duk da sun samu
katinansu a hannu. Jama'a dai na ta duruwa
shiga cikin hotel yayin da Umaimah take kyasawa
Faduwa hotuna iri-iri.
Wata murya ce ta kwalla kiran sunan Faduwa,
nan danan sai kowa ya juya ya dubi in da kiran
ya fito,
wani tsalelen saurayi ne ya fito daga cikin tasi ya
tunkaro in da suke tsaitsaye. Nan da nan suka ga
Faduwa ta cika da dumbin mamaki marar
misaltuwa, ta bude baki, ta dafe kirji da
hannayenta biyu, sannan ta kame a tsaye, ba ta
iya motsawa ba.
Yana mai tsananin murna da fara'a cike a
fuskarsa.
Yana karasowa inda take sai ya mika mata hannu
yana so su gaisa, sai tayi wuf ta kauce yayin da
zazzafan hawaye ya fara kwaranyowa daga
idanuwanta, nan da nan larabci ya barke daga
bakunansu, su dukka biyun.
Faduwa ta yi fushi fuskarta a murtike sai ta
balbale shi da fada, tana masa nuni da hannu ya
tafi bata son ganinsa, yayin da shi kuma yake
bata hakuri kamar zai yi kuka. Daga karshe sai
ya durkusa kasa gwiwoyinsa dukka biyu a
durkushe a kasa, ya barke da kuka yana fadin.
"Ma'alesh, Afuwan yah Faduwa.
Hankalin kowa