Showing 66001 words to 69000 words out of 130520 words

Chapter 23 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8022

yadda rannan aka jeru ana
kallonta da su. Dadinta ma wancan lokacin akwai
Faduwa a zaune a gidan gaba, yau kuwa daga ita
sai shi. Shin wanne irin kallo da fassara mutane
za su yi mata game da wannan canjin da suka
gani?
Hannayenta da kafafuwanta har karkarwa suke da
ta zo shiga motar ta zauna a hankali ta rufo
kofar motar, ya ja suka fara tafiya. Duk da
makarantar babu nisa daga gidansu, amma ta
kagu su karasa
ya sauke ta ya tafi ya bar ta.
Tunda ta sunkuyar da kanta kasa ta damki
jakarta kai ka ce in an ce kulle zata ce cas ta
arta da gudu.
Kallo daya ya yi mata, sai ya dauke kai ya lura
da halin da ta shiga, don haka ya fasa jero mata
dimbum tambayoyin da suke cikin ransa.
Ya kunna CD yayin da wani kida mai dadi ya fara
tashi gami da wata zazzakar waka tana fitowa,
wakar ba da Hausa aka yi ta ba, haka ba da
Turanci ba ce. Ta dago da kai a hankali ta dube
shi, kauyanci ya hana ta jero masa tambayoyi
game da wakar. Ko ba ta fada ba tabbas ya san
tana so ta
tambaye shi wannan wanne yare ne? Da suka
hada ido sai ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa,
ya yi murmushi ya dube ta.
Ya ce, ''Kina da tambaya ne?
Ta ce, ''A'a.
Ya ce ''To ni ina da tambaya. Kin san sunan
mawakin kuma da sunan yaren da ya ke wakar?
Ta yi murmushi, ta ce, ''ba zan sani ba, saboda
yaren Hausa, Fulatanci da Turanci kadai nake ji,
shi
kuwa ba irin su ya ke yi ba. Ya gyada kai, ya ce,
''Haka ne, amma ai ya kamata ki tambaye ni
saboda ki karu, kin san tambaya tana kara ilimi,
haka duk yaron da zai yi kokari a rayuwarsa za ki
ga yana da yawan tambaya. Ko ba haka ba?
Umaimah ta yi murmushi ta gyada kai ba tare da
ta dube shi ba, kuma ba ta yi magana ba.
Ya ce ''Wannan mawakin sunansa 'Akuri Afomsa'
dan kasar Ghana ne, da yaren 'Asanti' yake
wakar.
Ya na magana akan soyayya yana fadar zafin
rabuwar da ya ji a lokacin da ya rasa
budurwarsa.
Umaimah ta dago da sauri ta dube shi, sai ya yi
mamakin kallon da ta yi masa tamkar tana
tuhumarsa da wani laifi game da furucinsa.
Ya dan yatsune fuska, ya ce, ''Lafiya ko na yi laifi
ne da na fada miki fassarar wakar? Ko dai kina
ganin
kamar ina tsokanarki ne dan kin baro Ilah ko
Abdul-Basi?
Ta girgiza kai ba tare da ta yi murmushi ba ko
magana.
Daga nan Abdul-Sabur ya ja bakinsa ya yi shiru,
don ya fuskanci duk nacinsa Umaimah ba zata
saba da
shi ba, ba ta da niyyar yin hakan.
Sabuwar waka ce ya sake sakawa, ita ma dai
mawakin Ghana ne mai suna 'Kwabula-Kwabula,
shima da yaren Asanti ya ke rerowa, Umaimah ta
tambaya.
''Ita kuma wannan akan me ya ke yinta?
Abdul-Sabur ya yi mamaki da jin wannan
tambayar ta Umaimah, sai ya ji farin ciki a ransa.
Ya ce, ''Ya na waka ne akan mutuwa da ta raba
shi da wadanda ya fi so a duniya, wato
mahaifansa, da kuma masoyiyarsa.
Umaimah ta yi shiru kanta a sunkuye a kasa tana
dagowa sai ya ga kwalla ta cika mata idanu.
''Lafiya kike hawaye? Abdul-Sabur ya tambaya
cikin gigicewa mai tsanani.
Ta yi sauri ta sharce hawaye da gefen gyalenta.
Ta girgiza kai ta ce, ''Wani abu na tuna shine ya
sani
kuka.
Abdul-Sabur ya ce, ''Yafindo ko? Yi hakuri ba ke
kadai ba ce marainiya. Ki tuna fa ni da Faduwa
babu uwa babu uba, gara ke da sauki tunda Baffa
yana nan. Fatanmu Allah Ya gafarta musu, Ya
saka su a aljanna, Allah Ya kai mu inda suka je a
sa'a.
Babu wanda zai yi saura a duniya.
Ta sake surnano da hawaye mai radadi, ta ce,
Amin.
Shi wannan mawaki bai yi waka akan yara
kanana da suka rasa uwarsu ba alhali bata mutu
ba?
Abdul-Sabur ta ji hankalinsa ya tashi da wannan
tambayar tata, ya fahimci da *ya*yanta da ta
baro ta ke.
Sai ya girgiza kai, ya ce, ''Bai yi waka a kansu
ba.
Amma ai yaro don ya rabu da mahaifiyarsa alhali
tana raye a duniya bai zama maraya ba, za su
hadu wata rana.
Dai-dai lokacin da ya zo makarantar ya sami
waje ya tsaya sannan ya yi mata fatan samun
nasarar jarabawa. Ta amsa da, ''Na gode, sai
anjima.
Ta yunkura zata fice, sai ta ji ya kira sunanta. Ta
juyo da jajayen idanunta da suka jike sharkaf da
hawaye, ta dube shi.
Ya ce, ''Ina wayarki?
Ta yi saurin sunkuyar da kai kasa, amsa ta
gagare ta.
Ya yi ajiyar zuciya ya ce, ''Kin baro ta a gida ko?
To abin da nake bukata a wajenki shi ne, ki yi
min
alfarma ki nemo min lambar wayar Hanif a wajen
abokanku, na san suna waya a junansu, ke ce dai
ba kya waya da su. Ki karbo min lambar ina so in
yi amfani da ita. Yau nake so kada ki ce min
kuma kin manta. Ta gyada kai da alama dai ta
cika da mamaki amma bata iya tambayarsa
meyasa ba. Ta fita daga motar,
tana shirin rufowa ta sake ji ya ambaci sunanta,
sai ta fasa rufe kofar ta amsa masa cikin ladabi.
Ya ce, ''Karfe nawa zaki tashi ne yau?
Ta ce, ''Karfe sha biyu. Ya ce, ''Ni sha daya zan
tashi zan biyo miki mu koma gida, sai in karbi
lambar Hanif din, kada ki manta ki karbar min.
''Me zaka yi da lambar Hanif?
Ta tambaya cike da damuwa.
Ya fada cike da gadara, ''Me ake yi da lambar
waya bayan kira?
Zan kira shi ne kawai, kada ki damu bawai zan
tona ki ba ne daga inda kika buya. Insha Allahu
sai alkhairi.
Ta dan yi jugum can ta gyada kai, ta ce, ''Zan
tambayo maka lambar amma sai da yamma zan
dawo gida, kada ka damu ba sai ka zo daukana
ba. Ya gyada kai, ya ce, ''Ba damuwa, sai kin
dawo din,
Allah Ya bada sa'ar jarabawa.
Ta amsa masa da, ''Amin na gode.
Ta gaggauta rufo masa kofar mota ta yi saurin
barin wajen. Ta kuwa yi sa'a babu jama'a a
farfajiyar makarantar sosai, kasancewar sassafe
ne. Abdul-Sabur ya dade a zaune a cikin mota
kamar ba shi ne mai saurin nan ba, ya kasa
tukawa ya tafi kasancewar damuwa, tausayi gami
da jimamin hawayen da ya gani ya zubo daga
idanuwan
Umaimah.
Tabbas Umaimah ta kasance abar tausayi, kuma
abar tausayawa. Ta kasance marainiya, kuma ta
bar danta ko *ya*yanta tamkar marayu.
Zafafan hawaye ya dinga digowa daga cikin
idanuwansa, har ya isa makaranta. Ya tuno da
mahaifansa musamman mahaifiyarsa da ta sha
fama da su suna kanana. Mutuwa ta dauke ta ga
shi yanzu sun kawo karfin da za su iya
taimakonta,
amma ba ta nan. Tabbas duk mutumin da ya yi
kokarin raba uwa da danta imaninsa ragagge ne,
saboda tsananin soyayyar da uwa ta ke yiwa
danta. Allah ne kadai isasshe, Shi ne mai rayawa,
kuma mai kashewa, bayan Shi babu wanda zai
raba soyayyar nan.
*****************
Abdul-Sabur bai sake haduwa da Umaima ba sai
bayan kwanaki uku, wato ranar asabar da
yamma.
Tabbas ya san gudunsa ta ke yi shi yasa ba ta
yarda ta hadu da shi ba. Yana kwance akan
doguwar kujerar falonsa ya hangota a tsaye akan
baranda tana shakar daddadar iskar da ta ke
busowa a yammacin wannan rana bayan da
ruwan saman da aka yini ana yi ya dauke dif!
Ya yi wuf ya mike ya fito barandarsa sai gasu
kiri- kiri suna kallon juna. Ya yi mata murmushi
gami da yi mata cikakkiyar sallama. Ta amsa
masa ita ma
gami da gaishe shi.
Ya amsa mata cike da fara'a, ya ce ''Ya ya
jarabawar?
Karatun ne ya sa kika buya?
To Allah Ya taimaka. Ta ce, ''Amin. Ga sakonka
ma na karbo ba mu hadu ba shi yasa ban baka
ba.
Ya ji dadi da jin haka, sai ya yi dariya, ya ce,
''Yauwa na gode, amma ki ajiye min zuwa gobe
da safe misalin karfe goma na safe mu hadu a
gidan Faduwa. A ciki-ciki ta amsa masa, daga
dukkan alamu ya fara takurawa rayuwarta fa.
Tana jin nauyinsa ba zata iya yi masa musu ba.
Abdul-Sabur ya lura da canji daga fuskarta,
amma sai ya yi kamar bai san ta yi fushi ba, ya
ci gaba da
yi mata tambayoyi game da jarabawa, eh ko a'a
kadai ta ke ambato yayin da ta shiga tunanin
yadda zata shige gida ta rabu da shi.
Da ya gane sai ya yi mata sallama ya shige
abunsa ya barta a tsaye tana hararar kofarsa.
Asuba ta gari Umaimah Bello!!
****************
Washe gari ranar Lahadi kenan ta dade tana
sake-sake a ranta ta ji kamar ta je gidan Faduwa
su hadu
ko kada ta je. Karfe goma har ta wuce da minti
goma Umaimah na zaune a falonta bayan ta
shirya
tsaf ta kasa tashi ta fito.
A bayyane ta ke mita, ''Wai shi wannan mutumin
ba zai daina shiga harka ta ba? Lallai-lallai sai
ya yi min katsalandan a cikin al'amurana? Ni
daman tunda na
ga ya siyo min waya na san akwai abin da yake
shiryawa. Ina ruwansa da lambar Hanif?
Wayarta ce ta dau kara, ta zabura ta dauko ta
duba, lambar Faduwa ce ta shigo. Sai bayan da
ta gama hararar wayar gami da siraran tsaki
guda uku a jejjere, sannan ta dannan wayar ta
kunbura kumatu ta rada sallama kamar dole.
Baiwar Allah, Faduwa ba ta san abin da ake yi
mata ba a nan, ita sai fara'arta ta ke tana
kyakyata dariya.
Ta ce, ''Umaimah kin tashi kuwa? Ga mu nan a
nan mun hadu muna jiranki.
''Kun hadu kuna jirana ke da su wa?
Umaimah ta tambaya cike da kidimewa.
Faduwa ta sake kyalkyalewa da dariya ta ce,
''Matsoraciya, mai gudun mutane. To mu biyu ne
ni da Abdul. Ta murguda baki sau biyu, sannan ta
ce ''Na fito ina hanyar zuwa gidanki ma.
''Sai kin karaso''. Inji faduwa. Sannan suka kashe
wayar su dukka biyun.
Bayan ajiye wayarsu da kimanin mintina biyar,
Umaimah Bello ta bayyana a gaban Abdul-Sabur
da Faduwa.
Zuciyarta babu dadi, amma tana karfin hali tana
ta yin murmushi da ba ta shirya ba. Da ta duka
ta gaishe su sai ta sami kujera a gefen su ta
zauna tana mai tsananin fargabar abin da zai ce
mata.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya karkata gaba
dayansa yana dubanta, ya ambaci sunanta
sannan ya dora da bayanai.
''Umaimah, dalilin da yasa na ce ki nemo min
lambar Hanif ba wani abu ba ne illa ina so ki kira
shi da
layinki ku gaisa, ba wai in kun gaisa yau shikenan
ba, a'a ku ci gaba da gaisawa har ma ku dinga
ziyartar juna tamkar ke da kaninki Sabitu.
Dalilina shi ne, ko za ki ki kula kowa a Malaysia
bai kamata ki ki kula Hanif ba, saboda dalilan da
kika fi
ni saninsu. Hanif mai kaunarki ne, haka
mahaifinsa ya yi miki halaccin da bai kamata ki
yarda su ba.
Umaimah ta zuba masa ido kawai tana kallonsa,
ji ta ke tamkar ta kurma ihu saboda dabaibayin
da yake shirin lauya mata. Tabbas gaskiya yake
fada mata,
kuma ta yarda da hakan, amma fa ba karamin
aiki yake shirin ya ballo mata ba a safiyar
wannan rana.
Ta fada a ranta, ''Me ya kawo ni wannan gida da
zama da har na hadu da mutum mai naci da
shisshigi? Na yi da sanin saninka Abdul-Sabur.
Gaskia dole na tada Umaimah ta koma wani
anguwar daban. Wannan takuran da mai yayi
kama..
MAKWABTAKA 29
Ba ta gama tunaninta ba ya katse ta, ya ce, ''Ina
lambar tasa?
A sanyaye ta mika masa karamar takarda wacce
ke dauke da sunan Hanif da lambar wayar daga
kasan sunan. Ya karba ya duba ya tabbatar
lambar ingatacciya ce, sai ya dago ya dube ta.
Ta yi kicin-kicin da fuska tabbas ba za a dauki
lokaci mai tsawo ba zata fashe da kuka. Don
haka sai ya murtike fuska ya fuskanci ana fara
lallashinta zata rushe da kuka, koma ta sami
damar yin fushi ta fice.
Ya fada cikin kasaitacciyar murya, ''Ba ni
wayarki.
Ta mika masa nan da nan. Ya tambaye ta,
''Akwai kudi?
Ta girgiza kai, ta ce, ''Ban san ko akwai kudi a
ciki ba. Ya shiga duba wayar ya ga ko sau daya
ba ta kira
wani ba balle a kira ta bayan Faduwa babu
wanda ya taba kiran wayar. Ya yi ajiyar zuciya ya
girgiza
kai saboda takaici. Akwai kudi a ciikin wayar
saboda layin da aka siya da kudi a ciki.
Faduwa ta tsura musu ido tana kallon ikon Allah,
tabbas ba don Abdul-Sabur ya gargade ta da
kada ta yi magana ba, da tuni ta tunzura
Umaimah da magana.
Ya saka lambobin ya yi sabin sunan Hanif,
sannan ya kira shi. Bugu daya ya dauka, Abdul-
Sabur ya yi masa sallama, sannan ya gabatar da
kansa. Ya ce, ''Sunana Abdul-Sabur, daga Kaula
Lumpur, dan uwan Umaimah ne. Ina fatan ka san
Umaimah Bello ko?
Daga dukkan alamu Hanif ya cika da mamaki. Ya
amsa cikin sauri.
Kwarai na san Umaimah. Lafiya, me ya faru da
ita?
Abdul-Sabur ya ce, ''Lafiya kalau, wannan ma
lambarta ce sai yanzu ta hada waya, shi ne zata
yi maka magana.
Abdul-Sabur ya mikawa Umaimah waya ta karba
a sanyaye. Sai da Hanif ya ji muryarta ya saki
jikinsa
ya tabbatar ita din ce. Ya tambaye ta tambayoyi
masu yawa, sai ta kasa amsawa nan da nan
hawaye ya fara kwaranya.
Ya ce, ''Anti Umaimah, me na miki ba kya
nemana?
Na kira Samir dan ajinku rannan na ce ya ba ki
waya in gaishe ki ya ce ba kya yi masa magana,
ba zai kai miki waya ba. Na kira Aisha Bingyal ita
ma ta ce ba kwa magana ba zata kai miki waya
ba. Na shigo garin naku ranar wata lahadi na
ziyarci gidajen dukka *yan garinmu, na rasa
mutum daya
da ya san gidanki balle a rako ni. Haba Umaimah
meye duniya? Me yasa kike gudun *yan kasarku,
*yan uwanki don kin zo kasar fararen fata.... Ta
katse shi cikin kuka, ta fara magana, ''Hanif, ba
haka ba ne, ba gudunku nake yi ba
wallahi wasu dalilaina suka sa na ware kaina
daga gare ku. Ka yi hakuri Hanif, ka cewa Baba
ma ya
yafe min don Allah.
Sai dukka biyun suka fashe da kuka,
kuka ya ci karfin Umaimah har ta cire wayar
daga kunnenta ta kifa kai akan gwiwarta.
Abdul-Sabur ya yi sauri ya karba ya ci gaba da
magana da Hanif.
Hanif ya matse hawaye, ya ce, ''Na dade ba ni da
lafiya watannin baya, ke ce ta farko wacce
Babana ya tambaya saboda yana ganin ke ce
tamkar *yar uwata makusanciyata, ke ya kamata
ki zo kaina don har na fita hayyacina. Ya yi
mamaki da aka ce ba a san inda kike ba, kuma
tun ranar da muka iso rabona da ke kenan. Ya yi
takaicin barina da kika yi, har yau yana tambaya
ta ke. Na shaida masa kina nan lafiya, kuma kina
Makaranta abokaina *yan makarantarku suna
ganinki.
Ko sanda ya turo mana da kudi watanni biyu da
suka wuce ya ce in je in neme ki, in tambayeki ki
kin sami kudin da ya turo miki? Shine lokacin da
nake ta yiwa su Samir waya ba su nemo min ke
ba, na zo da kaina ban ganki ba na hakura na
koma,
sannan na shaidawa Baba ban ganki ba.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Hanif kada ka
damu, yanzu ga ka ga Umaimah, ga lambarta nan
ka dauka. Kuma ka turomin da lambar Babanka
ta wannan layin yanzu zata kira shi. Hanif ya
sake matse hawaye ya ce' ''To, zan turo
maka yanzu.
Suka yi sallama suka kashe waya.
Ba jimawa sako ya shigo Abdul-Sabur ya duba ya
ga Hanif ne ya turo lambar Babansa.
Ya dago ya dubi Umaimah har yanzu ba ta dago
da kanta ba, tun sanda ta kifa kai akan cinya ba
ta daina kuka ba.
Ya ambaci sunanta, ta dago a hankali da jajayen
idanuwanta ta dube shi.
Ya ce ''Goge hawayenki ga lambar Baban Hanif
zan kira ku yi magana. Hanif ya ce Babansa ya
turo muku kudin da ya saba turo muku duk
shekara. In ban manta ba kin ce miliyan dai-dai
yake ba ku ko?
Yana tambaya wai kin sami kudin a account
dinki?
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh kudin ya shigo.
Abdul-Sabur ya zazzare ido don mamaki ya
kurawa Umaimah ido sai ta sunkuyar da kai kasa
ya juya ya dubi Faduwa ta buga tagumi tana
kallonsu. Ya sake juyowa ya kalli Umaimah
sannan ya tambaye ta.
''Da kika sami kudin kin kira Baban Hanif kin yi
masa godiya?
Ta girgiza kai ta ce, ''Ba ni da lambarsa shi yasa
ban kira ba. Ya yi shiru har zuwa lokaci mai
tsawo, ya kasa magana. Can ya dago ya dubi
Umaimah wacce har yanzu ta ke sharce hawaye
da hankicin da Faduwa ta miko mata.
Ya ce, ''A ganinki kin kyauta da ba ki yiwa
mutumin da ya aiko miki da wadannan makudan
kudi godiya ba
Ta yi shiru ba ta amsa masa ba.
Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, ''Allah Ya kyauta. Don
ya fuskanci al'amarin Umaimah ya girma har
yana so ya
fi karfin tunaninsa.
Sannan ya matsa lambar Baban Hanif. Ta yi ta
ringin har ta katse bai amsa ba, yayin da Abdul-
Sabur ya ci gaba da kira ba kakkautawa.
Hankalin Umaimah ya tashi matuka zuciyarta ta
hau dukan uku-uku tana fargabar abu biyu.
Na farko, yadda Alh. Nasir zai karbe ta don dole
zai yi fushi da ita saboda gaskiya ta tapka masa
laifi. Na biyu, tana fargabar kada a kira shi a
gaban Lamijo kawarta kishi ya kamata alhali sun
boye mata zuwanta Malaysia.
Ta yi zumbur ta mike tsaye kamar wacce aka
mintsina. Ta ce, ''Kada ka yi masa maganata, sai
ka tabbatar ba a gida yake ba saboda labarin da
na baku game da yadda muka yi da matarsa
Lamijo.
Kafin Abdul-Sabur ya ce wani abu Alh. Nasir ya
kira lambar da yaga Missed call rututu. Kafin ya
amsa
Abdul-Sabur ya ce da ita ta kwantar da
hankalinta ta koma ta zauna ya san abin da zai
ce masa.
Ya dannan da sauri ya amsa, ''Hanif dan albarka,
ya naga ka canja layi kuma, ko ka yarda wayar
taka ne? In ji Baban Hanif.
Abdul-Sabur ya dukar da kai kasa, ya ce, ''Alhaji
ina wuni. Ba Hanif ba ne, yanzu dai Hanif din ya
turo min da lambarka. Sunana Abdul-Sabur
Abdul-Rashid, ni ma dan kasarku ne Nigeria.
Kana hanya ne ko kana gida? Ina so na yi
magana da kai.
Alh. Nasir ya ji hankalinsa ya tashi matuka sai ya
zaci wata matsala ce ta sami dansa, musamman
da
ya sha rashin lafiya kwanaki. Yana fargaba ko
ciwon ne ya tashi.
Nan da nan jikinsa ya dau bari, muryarsa ta yi ta
makyarkyata ya tashi zaune daga kwanciyar da
yake. Don alokacin da Malaysia suke karfe goma
sha daya na safe, a Nigeria kuma karfe shida ne
na
yamma banbancin awanni bakwai ne a tsakani.
Alh. Nasir ya ce, ''A'a, ai na fito kofar gida muna
shirin yin sallar magruba. Lafiya, me yake faruwa
ne?
Abdul-Sabur ya ce, ''Lafiya kalau Alhaji kada ka
damu, tunda sallah za ku yi idan ka idar ko gobe
da safe za muyi maganar.
Alh, nasir ya girgiza kai, yayin da ya yi wuf ya
mike tsaye. Ya ce, ''Ba damuwa, ina ma Abuja ni
kadai ne, ba'a kira sallar ba.
Abdul-Sabur ya yi mumushi, ya ce, ''To ba
damuwa ranka ya dade, a nan ina tare da *yarka
kuma kawar matarka Umaimah.
''Umaima Bello! Umaimah!!
Alh. Nasir ya tambaya ya sake nanata sunan.
Abdul-Sabur ya ce, ''Sai yanzu ta hada waya tun
zuwanta ba ta da waya. Muka kira Hanif ya turo
mana lambar wayarka.
Alh. Nasir ya ce, ''Wannnan wacce irin rayuwa
ce?
Me muka yi mata da ta ke gudunmu? Haba
Malam kai ma ka san Umaimah ba ta kyauta min
ba.
Taimako da nake mata ba zan fasa ba saboda
don Allah nake yi, a wajenSa nake neman lada.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''Ka yi hakuri
Alhaji, ba yanzu zaka fahimce ta ba, ni zan yi
maka
bayanin dalilinta. Kamar yadda ka sani Umaimah
tana da matsaloli da tashin hankalin rashin uwa,
*yar uwa, miji da kuma danta da dan *yar
uwarta.
Alh. Nasir ya gyada kai, ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login