Showing 18001 words to 21000 words out of 130520 words

Chapter 7 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt

13 Dec 2024

8013

yi
mana
addu,ar Allah Ya sa wannan aure ya tabbata,
saboda yadda aka lura muna kaunar junanmu
matuka.
MAKWABTAKA 12
Tunda mahaifiyarsa taji labarin wannan liyafar da
muka yi, ta ga hotuna sai hankalinta ya sake
tashi,
ta kirani ta zazzage ni, wai nabar mata danta
kada na cinye shi. Na ga santalelen saurayi,
kyakkyawa na makale masa, to bari ta fada min,
ban isa na aure shi ba duk nacina kuwa. Wai
tasan duk hanyoyin da na bi na mallake mata da,
sihiri ne ita ma zata bi ta karbo danta daga
mugun hannu.
Na kame a zaune ina ta sauraronta, na ji tashin
hankalin da ban taba ji ba a duniya. Na tsani
wannan kalmar, 'SIHIRI'. Dana fadawa Mamana
abun da matar nan ta yi min sai ta girgiza kai ta
ce,
''Ki yi hakuri Faduwa, sannan ki yi addu'a sosai.
Ban fadawa Sagir cewa mahaifiyarsa ta zazzageni
ba, a can ya jiyo da hawayensa ya yi ta bani
hakuri,
ya ce, yafi kaunar mutuwarsa da irin wannan
kuncin da mahaifiyarsa ta ke so ta cusa shi a
ciki.
Na ba shi hakuri na fada masa nasihar da
mahaiyata ta fada min cewar, na yi hakuri,
sannan na yi addu,a sosai, babu abin da ya
gagari addu,a.
Tsafi ya kan ci mai shi, sihiri gaskiya ne, ana
yinsa idan Allah Ya nufa sai ya kama wanda aka
yiwa. Ta fada da bakinta kuma ta aikata, saboda
yadda naga Sagir ya sauya nan da nan. Idan ya
zo wajena muna hirarmu ta masoya cikin farin
ciki da annashuwa da zarar ta kirashi, sai ka ga
jikinsa ya dau karkarwa, muryarsa na rawa. Idan
ta ce masa. ''Kana ina? To duk inda kake ka taho
gida yanzun nan, na baka minitina goma idan ba
hakaba ranka zai baci.
Tana kashe waya zai mike tsaye ya ce ''Mamana
tana kira, na tafi, sai wani lokacin.
Ina masa magana baya saurarona a guje zai je
ya shige mota ya tafi ko waiwayena baya yi.
Sabanin da sai ya gama hirarsa zai tafi ko zata
yi waya sau dari.
Ashe duk wannan somin tabi ne, abin takaici na
gaba. Sai ma ta hanashi zuwa gidanmu, ga shi
kiri-
kiri munyi waya da shi ya ce min ya kamo hanyar
gidanmu. In caba ado in zauna ina jiransa, sai ya
yi min waya ya ce, ya koma gida mahaifiyarsa ta
ce ya dawo. Hakafa ya ke sanar min ba tare da
sakayawa ba, i dan ba dan furucinta da tayi min
ba da sai na
ce yanason kyauyaya mu'amalarsa da
mahaifansa sosai, to amma furucin da tayi ya
kauda komai.
Tun ana haka har ya daina tarkar tahowa wajena,
wayar ma jifa-jifa. Idan son sa ya yi min yawa
sai na dauki motata na je na ganshi a gidansa ko
a wajen aikinsa. Sai ta ji labari ina zuwa, sai ta
sa shi ya fara kora ta.
Wai ni Faduwa ni na zama abin kora a wajen
Sagir, bayan a da babu wadda yake son
kasancewa tare da ita kama ta.
Sagir ba ya son ganina, har ta kai ta kawo ya
fada min baro-baro da bakinsa.
''Faduwa ki rabu da ni, mu hakura da juna,
saboda kina jawomin sabani tsakani na da
mahaifiyata. Ni kuwa ba na son duk wani abu da
ba ta so, koda kuwa shine zabin raina. Sai na ji
jiri ya kwashe ni ina zaune na ji na kwanta can na
dago na dube shi, sai na ga bana ganinsa
sai duhu. Daga dukkan alamu suma ce na yi a
ofis dinsa ne, sai ganinsa na yi da abokansa sun
zagaye
ni suna shafamin ruwan sanyi a fuskata. Da na
warware sai na ga idanunsa sharkaf da hawaye,
wanda har yau ba ya kafewa muddin na tuna
Sagir ko na ji mai sunan sa, kuma ina tuna korar
karen da ya yi min daga rayuwarsa.
Da kyar na dauko jakata da makullin motata na
fito daga ofishin na bar shi da abokansa suna
tambayarsa me yake faruwa, don shima kukan
yake yi.
Tun daga ranar har rana irin ta yau ban sake
ganin Sagir ba ko na jiyo muryarsa a dodon
kunnena. Na
hakura da shi koda kuwa sonsa shine ajalina.
Faduwa ta rushe da kuka mai tsanani yayin da
tausayinta ya cika zuciyoyin Umaimah da Abdul-
Sabur, suma kwalla ta cika musu ido.
Lokaci mai tsawo babu wanda ya yi magana a
cikinsu, sai shasshekar kukan Faduwa ne ka
tashi.
Umaimah ta dinga shafa kafadarta tana jijjiga ta
tamkar tana lallashin dan jariri, kalmar ''Sorry.....
Sorry. Suke ta ambatowa Faduwa. Abdul-Sabur
ya ce , ''Yaya rayuwarki ta kasance ke da
mahaifanki?
Faduwa ta sharce hawaye ta ce.
''Wannan shi ne mataki na farko da na fara
takawa na tashin hankali a rayuwata. Daga nan
abubuwa marasa dadi suka yi ta biyo ni daya
bayan daya. Kusan kowanne dan Adam bisa kan
mizanin kaddararsa ya ke, to haka nima na yi ta
hawa
kaddarorin rayuwata.
Yayana Ibrahin ya kamu da ciwo, wanda aka rasa
kansa. Abu kamar wasa tun yana iya fita ya je
aiki har ya kasa fita. Tun yana kwance a
bangarensa har Mamana ta dauke shi ta dawo da
shi dakinta tana kula da shi, dom komai sai an yi
masa.
Gwaje-gwaje kala-kala an kasa gano kan ciwon
sa.
Kuma a cikinsa ya ke, ya shekara uku a kwance
babu abin da ake sai kashe kudi, sai da komai
namu ya kare, daman shi sun sallame shi a
wajen aiki, sun ba shi kudin sallamarsa ya kare a
magani (Wannan banzar dabi,ace da ke faruwa a
kowacce kasa, wai adan ma,aika ci ba shi da
lafiya, maimakon a taimake shi a dauki nauyin
maganin ciwonsa, wata kilama a sanadin kulawar
wajen aiki ya samu sauki, amma sai a yi biris da
shi karshe ma a yi masa tagonashi da takardar
sallama da dan kudin da ba zasu kashe masa
kwarnafi ba).
Duk albashina a magani yake tafiya, ta kai ta
kawo sai da na siyar da motata na biya masa
wani kudin gwaji (test) mai tsada. Daman shi
tasa motar tuni an siyar, haka mahaifiyata ta
sayar da komai nata abin da ya rage mana
kwangwarmin gidan da muke ciki kadai.
Faduwa ta sake fasa kuka mai cike da ban
tausayi.
Umaimah ta girgiza kai don tausayawa, ta ce,
''Allahu Akbar! Ba ku yi waya Nigeria kun
sanarwa da mahaifinku ba? Faduwa ta matse
hawayen da ke gurbin idonta,
cike da takaici ta ce.
''Waya sau nawa kuwa, na yi waya har na gaji.
Duk lambobin da Ibrahim ya ba ni na kira daya
bayan
daya. Daga ta gidanmu, danginmu da abokansa.
Na sanar musu halin da Ibrahim ya ke ciki, kuma
tunda sauran lafiyarsa ya buga waya ya fadawa
Babanmu.
Ashe boye mana ake yi shima a kwance yake irin
ciwonsu iri daya (cancer) ce a hunhunsu, shi ma
can duk kudinsa ya kare a neman magani.
Sai su yi ta min hanya-hanya wai za,a turo daya
daga Baffannina ya zo ya duba shi. Na gaji dai
na fito baro-baro na shaida musu kudi ne babu,
ko ba zasu zo ba suturo mana da kudin asibiti.
Sai alkawuran karya, ko sisinsu ban gani ba.
Allah Ya karbi ran abinsa, yayana Ibrahim ya rasu
ranar wata litinin a asibiti. Kuka mai tsanani
Faduwa ta ke, yayin da Umaimah ta dafe kirji, ta
ce. ''Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.
Abdul-Sabur ya dafe kai, ya girgiza don
tausayawa, amma bai iya cewa komai ba, sai
girgiza kan da yake cikin tsananin jimantawa.
Cikin kuka Faduwa ta ci gaba da magana. ''Allah
Ya sa mutuwa hutu ce, din da wata cutar gara
mutuwa, tsananin wahala babu irin wacce bai sha
ba, ko ruwa ba ya tsayawa a cikinsa, sai ya
amayo da shi, ya rame ya yi baki, gashin kansa
ya kade. Ba magana sai kaga hawaye na zuba
daga idanunsa idan masifar tayi masifa. Sai ni sai
Mahifiyata muka rage ga talauci saboda albashin
ma ba ya isa ta, dumbin bashin da yake kanmu
nake biya duk wata, wanda muka ranta aka biya
kudin asibiti. Duk da kokarin da nakeyi ina ta biya
ban daina fuskantar cin mutunci daga
wadanda suke bina bashi ba, suna ganin cinye
musu zan yi.
Hakika ni da ita ba ma jin dadin rayuwarmu.
Saboda rashin Ibrahim ga babban tabon da ya
tafi ya barmu da shi, mun kasa mance tsananin
wahalar da ya sha a sanadiyyar ciwon.
Mun yi waya Nigeria mun shaida musu mutuwar
Ibrahim, wasu da yawa sun kira suna yi mana
gaisuwa. A lokacin ne ma aka ba wa mahaifina
kan waya ya yi min magana, muryarsa na rawa
yake
bani hakuri akan abin da ya yi mana, ya shaida
min shima a kwance yake bashi da lafiya sai an
kwantar an tayar. Tsananin tsanar da na yi masa
sai ta ragu son da na
kullace shi sosai, na yi da-na-sanin da ya zama
mahaifina tunda ba ya kaunarmu, ba ya kula da
mu. Amma a lokacin da yayimin wannan bayanin
sai na janye tsanar.
Na yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya, daga
yadda na suffanta ciwon na gane irin ciwon
Ibrahim ne,
don haka na cire rai da shi a rayuwa.
Tun daga wannan lokaci hankalina ya yi Nigeria,
na ji ina so na zo na gana da mahaifina tunda
ransa.
Saboda ban san shi ba sai a hoto, ga babu dan
uwana Ibrahim shi ne daman ya san su, wanda
ko ba ran mahaifinmu zai iya kawo ni na ga
dangin ubana ko da kuwa aurena ne ya zo.
Mahaifiyata ta dage ta ce ba zan je ba, don ba
son mu suke yi ba. Tana tsoro kada ma na zo su
cuceni,
ko su hada baki su hallakar da ni, tunda ta ji
labari su *yan Nigeria suna da hadamar gado,
kuma za su iya yin komai a kan gado . Kuma ta
fuskanci matansa ba sa son mu, da akwai yadda
za su yi da sun soke sunanmu daga cikin
*ya*yansa, *ya*yansu ne *ya*ya.
Na ji ba dadi don na sawa raina ina son zuwan,
to amma babban dalilin da yasa na hakura ba ni
da kudin jirgi.
Muna nan haka rayuwa ba dadi, rana daya ba
zato ba tsammani zuciyar mahaifiyata ta buga,
sai dai
kawai ta fadi aka dauki gawarta. Tsakaninta da
yayana shekara guda dai-dai.
Nima mutuwa ce kawai ban yi ba, saboda na
girgiza, na dimauce zan iya cewa dai na zautu
tamkar kwakwalwata ta tabu. Ta fashe da kuka
mai tsanani. Ya yin da Umaima da Abdul-sabur
suka razana har suna hada baki ''Mama ce ta
mutu?
Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta
tafi ta bar ni, ni kadai a duniya. Tun daga wannan
Lokaci na daina zuwa aiki kwata-kwata.
Faduwa ta gyada kai ta ce, ''Mamana ta rasu, ta
tafi ta bar ni, ni kadai a duniya. Tun daga lokacin
nan na daina zuwa aiki kwata-kwata don ko naje
shirme zan yi, yanayin aiki na kuwa sai da
nutsuwa. Babu yadda dangin mahaifiyata ba su yi
ba na je aikina nayi hakuri na maida komai ba
komai ba. Na fada musu baro-baro, ba zan je ba,
tun *yan ofishinmu na ba ni dama suna daga min
kafa har
suka fara turomin da doguwar wasikar gargadi
(warning letter) cewar, ko na dawo aiki, ko a kore
ni. Daga karshe dai naga wasikar kora daga aiki,
ban damu ba daman haka nake so. Na hada *yan
abubuwan da aka ba ni na daga cikin dan abin da
Mahaifiyata ta bar min na gado,
na sayi tikiti na kaura Saudiya wajen danginta na
can na zauna da su a 'Tayif.
Bayan mutuwar Mahaifiyata na kira lambar
gidanmu ta Nigeria ina so na shaidawa Mahaifina
rasuwarta, sai matarsa ta dauka, na ce ta bashi
muyi magana, ta ce min ba ya kusa. Na shaida
mata
sakon da zata fada masa, a shelake ta amsa min
gami da ajiye waya tun ban gama magana ba.
Sai na kira Baffana daya daga cikin su wanda
yake zaune a Kano Baffa Mansur na shaida masa
abubuwan da yake wakana, ya yi min alkawarin
zai sanar da shi idan ya je duba shi, don shi ma
jikin ya tsananta.
Na yi kuka, kullum cikinsa nake yi har yau saboda
bani da kowa, ba ni da komai, daman dai na san
Allah (S.W.T) ne kadai gatana.
Rayuwata ta tsananta a 'Tayif' ba na ganin dai-
dai duk inda na je sai naga kaman ana min kora
da hali, sun kosa da ni. Duk da masu arziki ne
abinci da sutura ba sa wuya sai na ga suna yi
min habaici game da mijinsu suna gudun kada
mazansu su ce suna sona saboda Allah Ya yi min
fara'a, hira da saurin sabo da mutane.
Duk na tsargu na fara zama mujiya a cikin
jama,a.
Dole na tarkato na dawo Cairo don na tantance
cewar na wuce zama a gaban wasu. Na zo na
bude gidana na zauna, ina cin dan abin da na
samo, daya kare sai na fara shiga garari.
Egypt ba kudi ba kamar Saudiya ba komai a
wadace, a Egypt ma'aikaci mai daukar albashi
kukan babu
yake yi, albashin bashi da yawa balle ni da bana
aiki. Bayan shekara ne na ga ya dace na kira na
ji jikin
mahaifina tunda kozai mutu babu mai kirana ya ji
hakin da nake ciki, ina kira gidanmu, wani kanina
mai suna Salahuddin ne ya dauk wayar, sai yake
shaidamin ai mahaifinmu ya shekara da
mutuwa...
Faduwa ta girgiza kai ta yi murmushin takaici,
yayin da Abdul-Sabur da Umaimah suka zazzare
ido don tashin hankali.
''Ya rasu amma ba su fada miki ba? Im ji Abdul-
Sabur.
Faduwa ta fashe da kuka, ta ce, ''Ba su fada min
ba,
saboda bana cikin lissafin *ya *yansa. Raina ya
yi matukar baci, na yi ta fada, a lokacin na kira
Baffanaina daya bayan daya na wanke su tas da
bakaken maganganu, na ce yanzu har Mahaifina
ya shekara ya shekara da rasuwa a kasa fada
min. Sai
suka hau kame-kame wai saboda suna gudun
kada zuciyata ta buga abubuwan su yi min yawa,
ga mutuwar dan uwana da mahaifiyata, ya za a
yi a fada min mutuwar mahaifina, daman so suke
a kwana biyu tukunna.
Babu abin da na ce musu, sai na kashe waya, na
fi sati ina kuka a daki ni kadai, sai da kanwar
mahaifiyata ta zo ta tambaye ni ko lafiya? Na
shaida mata duk abin da ya faru.
Nan da nan ta hado taron gaggawa, kowa sai da
ransa ya baci da ya ji abin da aka yi min, suka ce
ai ba za a zura musu ido aci gaba da cutata ba,
dole a kwatarmin hakkina tunda sun nuna ba su
san mutunci ba, sai an raba abin da ya bari da ni.
Suka ba ni waya na kira gidan a gabansu na bude
magana(speaker). Cikin harshen Hausa na yi
magana dasu a waya dangina basu ji abin da
muka ce ba, amma na fassara musu daga baya
abin da aka ce.
Matan Babana na tambaya me da me Mahaifina
ya bari? Suka hau kame-kame wai bai bar komai
ba,
duk sun kare a asibiti. Ko gidan ma da suke ciki
na aro ne.
Sai na katse waya na bugawa Baffa Adamu waya,
shi yana jin larabci na tambaye shi gadon
Mahaifina,
sai ya ce fili ya bari guda daya. Da na kira Baffa
Mansur kuwa shi ma a cikin harshen Larabci
mukayi magana, kowa yana ji. Sai ya ce baibar
komai ba sai shaguna guda uku a kasuwa da
mota biyu tirela.
Daga jin haka mun san ba su da gaskiya, don
haka aka ce na shirya kawai na tafi Nigeria, na je
na shigar da kara na karbi hakkina. Suka
hadamin kudin jirgi, amma sai da na sami wanda
ya ke da
tabbas ya san gidanmu na sokoto amma a Abuja
yake a zaune. Don haka Abuja na nufa gidan da
matarsa su ma sakkwatawa ne, unguwarsu daya
da mahaifina ni kuma a asibitinmu na sansu sun
kawo dansu wata shekarar muke waya da su har
bayan sun tafi. Hira ta kawo hira suka gane
mahaifina...
Umaimah ta gyara zama ta ce,''Ya aka yi kika
je?''
Abdul-Sabur ya ja doguawar ajiyar zuciya, ya
gyada kai. Ya ce, ''Ikon Allah, rayuwa kenan.
Yaya ta kasance tsakaninki da su?''
Faduwa ta tabe baki ta ce, ''Inda ranka a duniya
za ka sha kallo. Wasu mutane gani suke kamar
ba
zasu mutu ba, sun kauro duniya ke nan, ba sa
tsoron Allah. Sun manta inda wancan ya je su
ma za su je ne ko ba jima ko ba dade. Da na isa
Nigeria garin Abuja aka kai ni garinmu Sokoto
cikin gidan Babana. Sai ga ni a zaune a falonsa,
ga ni ga hotunansa a kusa da ni, amma baya nan.
Allah Ya yanke haduwarmu har abada.
Na ga kannene rututu, dangi kamar tururuwa
kowa ya taho ya ga Faduwa, suna murna ina
murna, yayin da aka dinga jeremin kwanukan
abinci da kyaututtuka iri-iri kamar Muhutai,
atamfofi, leshina, kwarya da dai sauransu. Kowa
so yake ya yi hira da ni, kai ka ce suna sona.
Wasu daga cikinsu kauyawa ne futik babu boko,
wasu kuwa *yan gayu ne masu kudi. Su ka ce
ma idan na huta zasu kai ni Kano, Kaduna da
Abuja wajen *yan uwa (cousins) da suke auren
manyan masu kudi a can.
An ba ni su a waya mun gaggaisa na ce musu
idanna na gama da sokoto za,a kawo ni sun yi
murna da jin haka. Wasu turanci muke yi da su,
wasu Larabci, wasu kuwa hausa kawai suka iya
sai mu yara.
Sai da na shafe kwanaki goma cur babu wanda
ya yi min maganar gadona, sai dai a gaisa, a yi
hira
wasa da dariyaa, a tulo min abinci da kayan
marmari a gyaramin gado na kwanta in yi bacci
washe gari in tashi a ci gaba da haka. Sai na
nemi a taro min kannen Mahaifina da manyan
kannena da iyayensu mata, duk muka hadu a
babban falon gidan.
Na bude baki na yi magana cikin harshen Hausa
yadda kowannensu zai gane. Na ce, na zo ne na
karbi gadon mahaifina don na kasa ganewa duk
wanda na tambaya me ya bari, abin da zai
fadamin daban ne. Me ya bari, kuma ina nawa
kason?
Sai aka hau kallon-kallo, wata matarsa wacce ita
tafi tsana ta ta dinga bayani irin na rashin
gaskiya, wai gidan nan kawai ya bari duk asibiti
ya cinye kudin,
an siyar da kadarorinsa gaba daya. Gidan ma ba
dukka ba dole sai an siyar da rabi an biya masa
bashin da ake binsa.
Ni kuma abin da na gida dai an gama raba shi,
don naga kowa ya kama nasa bangaren an yi
toshe-toshe da like-like.
Baffa Adamu ya ce na yi hakuri na koma kasarmu
idan komai ya daidaita za a turomin da kashina.
Na fusata na ce da shi, ina fili da ka fada min
yana da shi?
Na juya na dubi Baffa Mansur, da ya ce min yana
da shaguna a kasuwa, na tambayeshi. Na ce,
''Ina shagunan da ka fada min ya bari a kasuwa
da motoci? Duk ba ni da kaso a ciki ke nan?
Na yi kuka sosai don takaici na dube su
dukkansu na ce, ''To na gane abin da dukka kuke
nufi, kun
cire ni daga cikin *ya*yan gidan nan, kun rabe
gadon ku banda ni. A wajen Allah ina da hakki ku
ka danne, to duk wanda ya ci kashina ko da
kwayar zarra ce ban yafe ba, zai biya ni a ranar
da bashi da abin da zai ba ni sai ladansa. In da
Mutumin daya tara dukiyar da ku ka cinye ya je
dukkanmu nan zamu je, kuma ba kowa ya jawo
min wannan wulakancin ba sai shi da kansa
Mahaifina da ya nuna muku ni ba komai ba ce,
kuma bai damu da ni ba.
Sai suka hau timin tsawa da fada, wai kada na yi
musu rashin kunya. Kannena har da masu cewa,
za su dake ni idan na sake yiwa iyayensu rashin
kunya. Da yake zuciyata ta kekashe ban yi shiru
ba ni ma fadan na ke na ce su zo su dake ni idan
sun so ma su kashe ni.
Aka shiga tsakani aka kai ni bangaren masaukina.
Cikin dare Baffa Adamu ya aiko na zo gidansa
yana nemana. Da farko na ki zuwa sai da ya aiko
matarsa
ta zo, ta tafi da ni ya dauke ni a mota ya kai ni
gidan wani dattijo, a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login