Showing 114001 words to 117000 words out of 130520 words
Chapter 39 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
bai sami yadi da atamfar
matarsa ba kala dai-dai, na Dagaci kuwa daban
ne sunfi tsada sun fi yawa. Sai ka ji bakin masu
zakewa dazu yayi lukus babu abinda yake tashi a
wajen sai kalmar albarka da ake jerowa Abdul-
Sabur.
"Ina Umaimah?
Kowa sai ya tambayi Sabitu.
"Tana wajen bautar kasa. Inji Sabitu "Au kasar
ma bauta mata ake yi?
An bar Musulunci kenan.
In ji wadanda basu fahimci abunda ake nufi ba.
Sabitu da Abdul-Sabur suka sha dariya har suka
godewa Allah.
Karkara kenan!!!
Abdul-Sabur ya yi sallama zai koma Baffa ya ce
sai Sabitu ya zauna ba zai bishi ba. Zo ka ga
tashin hankali a idanuwan Sabitu, a yaren Hausa
da fulatanci babu kalmar da bai furta ba dan yiwa
Baffa bayanin da zai gamsu cewar zamansa a
birni
shi yafi masa alkhairi, kai har da guntayen turanci
daya koya a wajen Abdul-Sabur da Umaimah a
dan zaman da suka yi saida ya yara.
Abdul-Sabur ma ya taya shi bawa Baffa baki,
sannan ya hakura ya bar shi suka tafi tare.
Banda dariya babu abinda suke yi a hanya,
musamman Abdul-Sabur ya sha dariya.
Kafin su fita daga garin sai da Sabitu ya roki
Abdul-Sabur ya tsaya akofar gidan rabin ransa
Aliya. Ta
fito suka gaisa da masoyinta wanda Allah Ya
yiwa lidifi ya sha kwana nan da nan, babu
kamarsa duk a samarin garin.
Abdul-Sabur yayi mata kyautar bajinta yayin da
Sabitu ya shiga cikin gidan ya gauraye iyayen da
kannenta da ruwan Naira. A take mahaifinta ya
sanar masa shi kadai suke jira ya fito a daura
aure. Sabitu ya tabbatar musu da zarar Umaimah
ta dawo za'ayi komai, watakila ma a hada bikinta
da nasu ayi tare nan da wata biyu. Murna wajen
Aliya da iyayenta bata misaltuwa, suka yi musu
rakiya har bakin kofar mota suka ga
tafiyarsu.
Abdul-Sabur ya kara tausayawa rayuwar
Umaimah, ko a labarin data basu bai zaci haka
Rugar take ba kauyen kayayau, basu san ma anci
gaba ba a duniya rayuwarsu kawai suke yi a cikin
daji. Sai ya
shiga mamaki ace anan aka haifesu iyaye da
kakanninsu. Ya kudiri niyyar aurenta da taimaka
musu, su ma suji dadin da *yan birni suke ji.
Bayan tafiyarsu da kwana biyu sai ga iyayen
Abdul-Sabur maza a cikin mota bus sun iso garin
Gombe daga Gwarzo. Tuni harya musu waya ya
sa sun shirya tahowa, aka kawo su a cikin daya
daga cikin motocinsu na haya daya rabawa *yan
uwansa marasa aikin yi suna jigila suna samun
na cefane.
MAKWABTAKA 49
Kafin su karaso ya riga ya tanadar musu
dakunan da zasu sauka a Hotel din da suke, dan
su huta,
suna isowa suka ci abincin da suke so. Washe
gari aka dunguma su dukkansu tare da Sabitu da
Abdul-Sabur suka tafi Dugge. A gaban Dagaci
aka dire komai gami da kudinsa na aure, sun
karbi kudin amma a bisa sharadin sai an bisu
garinsu Gwarzo an gani, dan haka aka zabi
zakakuran maza guda biyar harda mahaifin Ilah
Baba Jani aka tafi da su. A ranar aka wuce
Gwarzo kasancewar dare bai yi ba.
Abdul-Sabur bai bi su ba shi da Sabitu suka ci
gaba da zaman jiran Umaimah a Gombe. Kwana
biyu su Baba Jani suka yi a Gwarzo suka dawo
Gombe wajen Abdul-Sabur cike da farin ciki
saboda an karbe su sosai sun ji dadin zama da
Kanawa. Da suka je Dugge suka korawa Baffa
bayani sai kowa yayi amanna da wannnan aure.
Gari gaba daya ya dauka Umaimah zata auri
Bakano, masu kushewa nayi saboda hassada irin
su Matawata, masu yabawa nayi irin su Ilah,
gashi dai yana matukar takaicin rabuwa da wacce
yake so, amma ya san ya rasa ta har abada dan
haka tsakaninsa da ita sai addu'a da fatan
alkhairi.
Asuba ta gari Ilamaima!!
***
Ranar da su Umaimah suka cika sati uku cif a
NYSC Camp da yake kuwa, ranar ne zasu fito
daga camp za'a bawa kowa takardar da zai kai in
da zai yi aikin bautar kasa. Yawanci dai duk inda
ka cike takarda nan za'a kai ka kamar yadda su
Umaimah suka cike Gombe can din dai aka basu.
Amma ba'a fara raba musu takardun ba sai da
suka gudanar da fareti ga FCT Minister. Taro yayi
taro kusoshin Nigeria sun hallara a safiyar
wannan rana ta litinin. Umaimah Bello ce a gaba
dauke da tutar Nigeria a hannunta a lokacin da
ake gudanar da faretin, su dari biyu aka zaba
masu yin fareti daga cikin dubban *yan bautar
kasa. Bayan Umaimah an zabi Aisha Bingyal,
Hanif da wasu maza guda biyu sune daga
Gombe.
Umaimah bata ankara ba sai ta tsinci Abdul-
Sabur a gabanta yana daukarta a hoto, tabbas ya
bata mamaki dan ko a ranar sun yi waya amma
bai fada mata ya zo gari ba. Ta hango Sabitu ma
a gefe ko shima sunyi magana a waya a safiyar
nan amma bai fada mata suna Abuja ba, dan
Abdul-Sabur ya saya masa waya yanzu, ashe ma
a lokacin suna Abuja dan ta san anan suka
kwana, ba zai yiwu ace ranar
suka zo ba.
Da aka gama fareti sai FCT Minister ya fara
bayanai yana basu shawara da nasihu akan su
zama *yan kasa na gari masu rikon amana dan
su ne manyan gobe da zasu zama shugabannin
kasar nan. Aka dauki lokaci mai tsawo, da ya
gama jawaban su Umaimah suka raka su shi da
*yan rakiya har mota da fareti. Hakika faretin
bana ya yi kyau sosai an tsara shi, kuma kayan
NYSC ya yiwa Umaimah kyau
sosai, Sabitu da Abdul-Sabur sun yi farin ciki da
ganinta a cikin wannan fareti abun alfaharinsu ne.
Bayan tafiyar shugabannin sai kowa ya nufo inda
dan uwansa yake.
A lokacim da su Aisha Bingyal suka nufi wajen
wakilan Gwamnan garinsu da aka turo, ita kuwa
Umaimah sai ta nufi wajen rabin ranta da dan
uwanta, sai suka hautsine da murna. Matan
dukka Gombe aka dawo da su mazan ne zasu yi
a Abuja,
dan haka a dunkule aka basu takardarsu zasu tafi
da ita can za'a rarraba su in sunje.
Abdul-Sabur ya tambayeta in da take so a kaita,
ta ce makarantar sakandire ta garin Dukku take
so ta je ta yi koyarwa amma ta ji ana cewa duk
wacce tayi computer banki za'a kai ta.
Sai yayi murmushi ya ce aransa "Waye zai bar ki,
ki wahalar da kan ki kiyi aiki a banki?
Babu yadda za'ayi ta bi su Abdul-Sabur a
motarsu saboda dukka za'a dunguma a koma
kamar yadda aka zo.
Dakyar ta bawa Abdul-Sabur hakuri ya hakura ya
kyale ta dan cewa yayi ba zata shiga bus ba sai
dai su tafi tare da ita a motarsa. Sun jima suna
hira sannan ta tafi ba dan taso ba sai dan kowa
ya shiga mota da kayansa, ita kadai ake jira.
Haka ma Abdul-Sabur bai so ya rabu da
Umaimarsa ba amma ya dangana ya san anjima
zasu hadu, a Gombe.
Sai ga su Abdul-Sabur sun rigasu karasawa da
yamma likis, nan ma haka sai da aka sha jawabai
a sakateriya sannan aka sallame su bayan an
bawa kowa takarda ta cike inda take so tayi aiki,
suka tafi
akan su dawo gobe su ga inda aka kaisu sai su
fara registration. Da aka fito daga sakateriya sai
ta hadu
da su Abdul-Sabur, yake tambayarta yadda take
so ayi. Ita kanta bata san yadda zata tsara
rayuwarta ba saboda dai zamanta a Gombe ita
kadai ba zai yiwu ba. Ta san dai yau a gidan su
Aisha Bingyal zata kwana washe gari zasu je in
da zasu kai takarda sauran zaman kuma bata
san yadda zata yi ba.
Abdul-Sabur ya bata shawara kada ta damu
kanta wannan mai sauki ne shi yasan yadda zai
tsara mata, ta yarda da hikimarsa dan haka bata
damu da sai ta ji abunda yake shirin tsarawa ba,
tasan zai yi mata yadda take so. Shi ya dauke su
a motarsa ita da kawarta ya kai su gida, suka
tsayar da shawara
gobe zai dawo ya kai ta sakateriya da bankin da
zata kai takarda.
Abdul-Sabur da Sabitu suka koma Hotel din da
suke yayin da Umaimah da kawarta suka shiga
cikin gida bayan sunyi wanka, salla da cin abinci.
Dan dare ya yi, sai suka kwanta amma bacci ya
gagara babu abinda suke sai sabon babi da suka
bude na hirar Abdul-Sabur.
Aisha ta kalli kawarta Umaimah ta yi murmushi
ta ce "Naga alama angon nan naki yana ji dake
fiye da yadda kike ji da shi.
Dadi ya lullube Umaimah ta yi dariya ta ce "Allah
ko?
Ashe kin lura da haka abinda nake fada miki
kenan ada kika kasa fahimta ta.
Abdul-Sabur daban ne da sauran maza, yana da
tausayi matuka da kulawa ba'a cika samun
namijin da zai iya dawainiya da matarsa ba irin
yadda yake yi, halinsa ne kuma a cikin jininsa.
Aisha ta harare ta, ta ce "Daman na san yanzu
zan ji bakinki radai kina bayani, in dai akan
Abdul-Sabur
ne kin fi kowa iya bayani. Yanzu mu duk kin
watsar da namu mazan da muka kawo miki, da
kika sami Abdul-Sabur ko?
Ya zaki yi da Baban Hanif da ya kawo miki
abokinsa kika ki aurarsa?
Umaimah ta ce "Wannan ai mai sauki ne tuni ma
aikin gama ya gama, mun yi waya da shi na
masa bayanin komai kuma ya gamsu da ni. Shi
mai ilimi ne kuma mai ganewa, yayi min addu'a
gami da
fatan alkhairi. Ya ce in bari ya san yadda zai
fadawa Alh. Nura yadda ba zai damu ba.
Kin san Baban Hanif ya san Abdul-Sabur sosai a
waya ashe a ranar ma Hanif ya kai Abdul-Sabur
sun gaisa da Babansa.
Kinga tunda shi ba yaro ba ne ai zai gane akwai
soyayya a tsakaninmu tunda ya biyo ni har
Nigeria.
Aisha ta yi tagumi tana kallon bakin Umaimah a
lokacin da take zuba bayanai. Ta yi ajiyar zuciya
ta ce "Yanzu shi Abdul-Sabur din da maganar
aure ya zo, ya fada miki zai aure ki?
Umaimah ta ji zuciyarta ta harba da ta ji wannan
tambaya ta yi shiru can ta girgiza kai ta ce
"Muna waya kullum amma bai ce min komai ba
haka Sabitu ma bai ce min komai ba.
Aisha ta ce "Ta yaya kikasan zai aure ki bai auri
wancan baturiyar ba da aka bashi?
Umaimah ta yi shiru can ta sulale ta kwanta ba
tare da ta sake yin magana ba haka ba bacci ba
ne ya dauke ta ba tsabar jujjuya maganar Aisha
take yi a cikin kwakwalwarta.
Tana jiyo munsharin Aisha tuni bacci ya dauke
ta, ita kuwa fargaba ta hana ta.
Amma ta kan tuna abunda Abdul-Sabur ya fada
mata aranar da zasu tafi Abuja a bakin mota, ya
ce ta daina kuka in dai yana raye karshen
hawayenta ya zo.
Tana mai tsananin fargaba kada dai ace Abdul-
Sabur ba da aure ya zo mata ba. Wa zata aura, a
ina zata saka ranta da zaman garinsu?
Asuba ta gari Umaimasabur!!
***
Washe gari karfe goma na safe a kofar gidan su
Aisha Bingyal ta yiwa Abdul-Sabur da Sabitu
daman sun yi waya ta shirya dan haka suna fada
mata sun iso sai ta fito a shirye tsaf cikin
kayanta na NYSC.
Kayan nan sun yi matukar yi mata kyau, kamar
dan ita aka yi.
Ta shiga gidan baya ta zauna ta gaishe su
sannan ta fadi inda za'a fara zuwa, sun zama
*yan gari sai taga sun kutsa ta hanyoyin da bata
taba sani ba. Ko ina aka zo wucewa sai ta ji
Sabitu ya ce "Ga inda muka zo ran nan cin kifi,
kaza ko shan askirim.
Tabbas ta gastata Sabitu ba karamar hutawa ya
yi ba a cikin sati ukun nan tana iya ganin shaida
a jikinsa. Fatarsa ta yi luwai-luwai, ya goge
wajen saka suturu sababbi, ga wayewa wajen iya
magana har dan turanci yake jefawa.
Tabbas Abdul-Sabur alkhairi ne a rayuwarta,
saboda ta dubi yadda ake tarairayar dan uwanta
balle ita. Sabanin Abdul-Basi wanda ko doguwar
hira baya yi da ita balle
kaninta, ta san da Abdul-Sabur ne ba zai yadda
akai Sabitu yawon Almajiranci ba a wancan
lokacin ba. A makarantar boko zai saka shi.
Kafin azahar Abdul-Sabur ya gama taya
Umaimah yin komai, amma ya kirkiro wasu dalilai
da dole sai an yarda da shi, aka bata hutun sati
biyu kafin ta fara zuwa aiki, GT bank aka kaita.
Abdul-Sabur ya ce da ita idan tana so ta tafi
Dugge yanzu ta dauko kayanta su tafi idan kuma
tana so ta kara hutawa su bari gobe da sassafe
sai su tafi.
Har ta ce gara su tafi ayau, sai Sabitu ya ishe ta
da magiya akan ta bari ta sake hutawa sai su
tafi gobe.
Ta san abunda yake nufi kauyen ne baya so ya
koma, zaman birni yake so sai ta tausaya masa
ta bari sai goben.
Abdul-Sabur ya yi dariya ya ce mata "Ke ce *yar
kauye, an rufe ku har tsawon sati uku a daji daga
ku sai sojoji, bari a zagaya gari da ke ayi miki
sayayya ki dan sha Ice cream.
Ko Sabitu?
Umaimah ta kyalkyale da dariya ta ce "Ba zan ci
amanar kawata ba in je in sha ni kadai in barta,
mu biya mu dauko ta ita ta ma fini sha'awar
shan Ice cream.
Abdul-Sabur ya ce "Kira ta awaya mu ji in da
take sai mu je mu dauko ta.
Da Umaimah ta kirata a waya sai ta shaida musu
tana sakateriya, ta kare abunda take tana jiran
direba ya zo ya mayar da ita gida.
Umaimah ta ce "To gamu nan zamu zo daukar ki,
ki hana direban zuwa.
Bata dade tana jiransu ba suka bayyana a
gabanta, ta shiga mota suka tafi.
Aranar babu abin da basu ci sun bari ba haka
kuma suka ciko ledoji da himilin siyayya, kama
daga kayan kwalliya zuwa kayan ciye-ciye.
Umaimah sayayyar wata guda ya yi mata, duk
wani abu da zata nema ya saya mata har da
kayan abinci, sai da but din motarsa ya cika taf!
Da kyar yake rufuwa dashi zasu tafi Dugge gobe.
A take Aisha ta gasgata cewar Abdul-Sabur ya
bambanta da sauran mazan Africa, ba dukka ba
ne suke da irin wannan. Ta yi amanna kawarta ta
aure shi, dan shi ya fi cancanta ta aura duk a
cikin mazajen da suka fito nemam aurenta.
Daman dai shi take so idan ma bashi ta aura ba
ba zata sami nutsuwa ba.
Ba su dawo gida ba sai da magaruba Aisha ta jidi
ledojinta cike da kaya tana ta godiya suka shiga
gida,
Umaimah bata dauki komai ba banda ledar Yogot
da lemuna sai snakc wanda zasu ci a cikin dare
amma sauran sai a Dugge.
Bakin Sabitu kadai take kallo yayi jage-jage da
naman kaza, Ice cream kuwa robar kawai yake
kafawa a baki yayi mata shan koko, a take yake
wurgar da dan tsinken da ake hadowa a cikin
robar Ice Cream din, dan ba zai bata lokacinsa ba
wajen cakula. Hararar duniyar nan da kifta ido
Umaimah ta yi masa dan ya fahimta ya ja aji
amma ina! Abu ya ci tura.
Ba Abdul-Sabur take ji ba, Aisha ta fi ji ana
harkar yanga shi kuma yana kwafsawa. Ta kudiri
niyyar mayar dashi makaranta ko ta yaki da
jahilci ce ba zai ci gaba da zama da duhun kai
ba.
Ta fuskanci Abdul-Sabur yana san Sabitu sosai,
yana bashi dariya yana kyakyatawa, shi yake
zuga shi ma yake sake tuburewa.
Da su Umaimah suka shiga gida da kawarta suka
sami abun yi wato hirar Abdul-Sabur, suna yaba
irin kirkinsa.
Haka ma Abdul-Sabur da Sabitu babu abin da
suke yi sai hirar Umaimah suna yaba nutsuwa,
hankali da mutuncinta.
Asuba ta gari.
***
Karfe tara na safe suka fito garin Gombe suka
kama hanyar Dukku tafiya suke cikin lafiyayyiyar
mota mai sanyin AC, gami da sautin kida mai
dadi,
wakarta ya saka mata ta 'Akuri Afomsa' bayan
ya bata wancan CD ashe yana da wasu.
Ta yi dariya ta ce "Bayan na kwace maka wancan
ya aka yi ka sami wani?
Ya yi dariya ya ce "Saboda ke na samo wani
nakeji kullum, kin sa nima yanzu ina son wakar
nan.
Haka dai suka yi ta hira nan da nan suka ga sun
isa Dugge, babu gajiyar tafiya a tare da su. Sai
su Umaimah kwatsam a Dugge yayin da yara
suka baibaye bakin mota suna tsalle, sun ga
Umaimah mai basu alewa ta zo. Suka taya
Sabitu jidar kayan aka kai cikin gida, dakin Baffa.
Zo kaga washe baki da murna a wajen su Nene,
yanzu kam suna son Umaimah dan ta zama
mutum, basa kyararta.
Muryar Matawata Umaimah take jiyowa ta jikin
zana tana gidan iyayenta, tana ta zage-zage tana
habaice-habaice.
Wai duk wanda ya ce tukunyar
wani ba zata tafasa ba tasa ko dumi ba zata yi
ba.
Tunda Umaimah ta hanata zama a gidan mijinta
itama kuwa idan tana raye ba zata barta ta yi
aure
ba sai dai idan babu bokaye a gari. Hankalin
Umaimah ya tashi ranta ya baci sai ta fara kuka,
su Nene suka kaita daki suna lallashi, suka ce
kada ta kula ta. Matawata ta zautu bata da
cikakken hankali, Ilah ya ki mayar da ita ya ce
har abada
baya sonta shine ta zama kamar me tabin
hankali.
Baffa da Abdul-Sabur ma suka shigo tsakar gida
suka ji da kunnensu abunda take cewa sai suka
shiga har dakin Umaimah suna bata hakuri.
Allah Sarki yarinya ta zo da farin cikinta amma
har an bata mata rai, ta shiga fargabar yadda
zata kasance da ci gaba da zama da Matawata a
matsayin Makwabciyarta ta din-din-din.
Abdul-Sabur ma ya ji hankalinsa ya tashi, dan
ada jita-jita yake ji bai san abun har ya kai haka
ba. Da suka koma zaure suka kebe Baffa ya bashi
labarin abunda ya faru tatas a ranar da Umaimah
zata tafi,
Sabitu yana karin bayani. Abdul-Sabur ya gyara
zama ya shawarci Baffa, ya ce "Gara a yi sauri
ayi
bikin nan daga nan zuwa wata guda saboda kada
ma zamansu tare ya tsawaita ta ci gaba da bata
mata rai.
Baffa ya ce "Zan yi farin ciki da hakan amma dai
zan tuntubi Umaimah da maganar tukunna.
Da Abdul-Sabur zai tafi sai ya damko kudi mai
yawa ya bawa Sabitu da Baffa ya sake ambalowa
ya bawa Sabitu ya ce ya bawa Umaimah, ya
mikiwa Nene da Inna kudin da tunda suke a
rayuwarsu
basu taba mallakar irinsu ba,
sannan ya yi ta rabawa mata da suka zo yiwa
Umaimah sannu da
zuwa.
Sabitu ya kira Umaimah dan su yi sallama da
Abdul- Sabur zai tafi, bai ji dadin yadda zasu
rabu ba idanuwanta sharkaf da hawaye. Yana
zaune a cikin mota yayin da ta kama kofar motar
ta tsaya babu
walwala a fuskokinsu su dukka.
Abdul-Sabur ya nisa sannan ya girgiza kai ya ce
"Na san yadda kike ji, babu dadi, akwai takura,
amma ki ci gaba da yin hakuri komai mai wucewa
ne, watarana za ki ga kamar ba'ayi ba. Zan tafi
yanzu kuma gashi ban san yadda zamu sake
haduwa ba tunda ba ku da waya balle in kira. Na
daukar miki hutun sati biyu a wajen da za kiyi
aikin bautar kasa, idan ya cika kije kisa hannu
(signing) kawai, ba sai kin kwana ba ki dawo gida
yanzu.
Dan zan je can in ga manajan bankin mu daidaita
ba sai kin je ba har tsawon wata guda, kafin a
tsayar da shawara a ga yadda za kiyi zaman, dan
gaskiya zamanki a gidan su Aisha bai dace ba.
Hankalin Umaimah ya tashi matuka musamman
da ta ji ya ce zai tafi bai san sanda zasu sake
haduwa ba.
Sai hawaye ya barke mata ba tsayawa, nan da
nan ta gigice har sai da shima ya razana.
Ta tambaye shi, "Ghana zaka tafi ko Ingila?
Ya yi dariya dan ya fuskanci bata san abunda ya
ke faruwa ba.
Ya ce "Yanzu dai Gwarzo da Kano zan koma, ina
kasar zuwa wani dan lokaci.
Ta cire rai da shi ta ga alama ba da niyyar
aurenta ya zo ba, dan duk abun nan da ake bai
taba yi mata maganar aure ba.
Tabbas zata iya rasa rayuwarta sanadiyyar
bugun zuciya muddin ya tafi ya bar ta bai aure ta
ba.
Fargaba ta hanata tambayarsa, ya auri baturiya
ko bai aura ba, ga takurawa kuwa basa yarda ayi
musu kishiya.
Dan Aunty..
MAKWABTAKA 50
Duk bayanan da Abdul-Sabur yake yi mata bata
ganewa, tana can tana tunani mai nauyi akan
yadda zata dauwama da zama a Dugge da yadda
zata rabu da masoyinta. Yayi mata magana ya