Showing 12001 words to 15000 words out of 130520 words
Chapter 5 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
na sa kafata sai na ganshi ko da kuwa kasar
na
bari. Anya kuwa wannan mutum ne?
Ta hada girar sama da kasaa, don tasan ta yi
masa laifi kada ma ya ga fuskar tambayarta wani
abu.
Sai ta cika da mamaki a lokacin da ta ga
fara,arsa yadda ka san ba ta taba saba masa ba.
Ya yi mata
sallama gami da yi mata sannu da dawowa.
Ta gyada kai kawai ba ta amsa masa ba, suka ci
gaba da tafiya babu abin da yake yi illa kakkare
ta da yake, don kada a matseta a lungu saboda
karatan da suka cunkushe cikin jirgin. Jirgi ya
cika
makil saboda kowa ya na so ya koma gida, don
dare ya yi. Har yanzu su duk a tsaitsaye suke sun
rike igiya babu kujerar zama. Motsi kadan ta yi
sai ya juyo ya kalle ta cikin tattausar murya yake
yi mata sannu. Sai ta ji kamar ta kurma ihu don
takaicin ya shiga harkarta. A haka dai har suka
karasa 'Maharjalela'. Babu yadda ta iya, dole ta
fito dan niyyarta ta ki fita a wuce da ita wata
unguwar,
sannan ta dawo idan ya tafi. Kamar yasan haka
ta ke nufi, sai da ya tabbatar ya saka ta a gaba
suka fito tare.
Tafiya kawai take kanta a sunkuye a kasa,
tambaya kala-kala da labaru ya ke rero mata,
wadanda basu shafe ta ba, ba su shafi tsarin
rayuwarta ba. 'Yes ko 'No kawai ta ke jero masa.
Har suka sauko daga
tashar jirgin suka nufo gida. Tambayrta yake, ya
ya kwarin jikinta, cikin ya daina ciwo ko?
Ta dago kai ta dube shi a fusace ta galla masa
harara ta girgiza kai don takaici gami da dorawa
da dan siririn tsaki.
Cikin harshen turanci suke magana ta ce, ''Kai....
Kai Abdul-Sabaur, bazan boye maka ba, a
gaskiya kana takurawa rayuwata da yawa. Ka
sani na baro garinmu, kasarmu na zo kasar da ba
a taba sanina
ba, ni ma bansan kowa ba, saboda gudun takura.
Me yasa zaka nemi saika sanni dole? Bana son
damuwa, don Allah ka yi hakuri ka daina shigar
min harka, na fi jin dadin rayuwata ni kadai.
Murmushi ya yi mata, ya ce, ''Allah Sarki yarinta.
Umaimah ki yi hakuri, ki kara hakuri, ko ba ki
fada min da baki ba, na san kin takura a
yanayinki da
nake gani, na san na dame ki. Amma ita rayuwar
duniya da kike gani kowa hakuri yake da ita,
kuma
kowa yana da matsala, wata matsalar ma har ta
fi ta ki. A matsayinki na musulma ai ba wannan
hukuncin za ki yanke ba na tahowa inda ba
asanki ba, kuma ki ki yarda ki saba da kowa idan
kika yi haka kamar kinyi fushi ne da kaddarar da
Allah Ya dora miki. Musulmi na gari yana fara,a
yana
mai godiya ga Allah a lokacin da yake cikin
tsanani. Ba ki taba jin kissar nan ta wani mutum
ba? Wanda bakin cikin duniya ya dame shi, ya je
Ka'aba yana dawafi, yana cikin damuwa, yana ta
addu'a. Sai ya hadu da wata mata, wacce suke
zagaye tare. Fara'a matar ta ke ti fuskarta cike
da annuri, gata
kyakyktawar gaske. Sai ta burge shi ta bashi
sha'awa ya ji dama shine ya sami irin farin cikin
da take ciki. Tun yana fada aransa, har ya fito ya
tambayeta.
Ya ce, 'Yah ke wannan mata, ke kuwa wanne irin
farin ciki kike yi haka ne? Daga ganinki ba ki da
matsala a duniya. Sai matar ta sake yin
murmushi, ta ce, 'bawan Allah ni ce kuwa nake
da damuwa, saboda mai gidana ne ya tafi kiwo
tunda safe bai dawoba har dare ya
yi, ashe mutuwa ya yi a can, sai na aika babban
dana ya je ya nemo shi daya tafi shima maciji ya
sare shi ya mutu, ma kaji shiru na fita neman su
na bar karamin jariri kafin in dawo gida na zo na
tarar
kura ta cinye shi. Na dawo bani da kowa yanzu a
duniya Allah Ya karbe abunSa. Godiyar Allah ce
kawai da wadatar zuci yasa kaga ina dariya.
Tun daga wannan lokaci mutumin ya daina
damuwa da matsalarsa ya ji ashe shi tashi
matsalar shafar mai ce. To haka akeso musulmi
na gari ya kasance.
Umaimah ta dubeshi yayin da jikinta ya yi sanyi,
ba ta kara magana ba har suka shiga bakin get.
Ta kama hanyar gidanta shima ya nufi
bangarensa.
Kalmar karshe da ya furta a gare ta, ita ce,
''Bissalam. Ta amsa da ''Ma'assalam.
Ta wuce gida yana mai tsananin mamaki da irin
kwakwalwa da dadadan kalamai masu tausasawa
irin na Abdul-Sabur. Mutum ko shaidan ne sai
jikinsa ya yi sanyi idan ya fara yi maka nasiha.
Tabbas Abdul-Sabur mutum ne mai rikon addini
da iya xama da jama. Amma ita duk da haka bata
tunanin taci gaba da zama a gidan nan, don ta ga
sannu a hankali Abdul-Sabur zai sa ta saba da
MAKWABTA, ita kuwa ba ta son su saba sam.
Sai yau Abdul-Sabur ya fara jin sanyi a ransa a
game da Umaimah, yau ce rana ta farko da ta
fara bude bakinta ta yi masa doguwar magana,
har da ya yi tunanin ko batajin turanci ne sosai
shi yasa ba
ta son magana. Sai ya ji ta iya Turanci sosai, sai
ka ce a kasar Turawa ta yi karatun tubalinta
(Primary da secondary). Daga dukkan alamu zaici
galaba a kanta, ya fara rusa mata bakar akidar
nan da ta saka a ranta, ta kin gaisawa da
makwabtanta.
Asuba ta gari Abdumaimah !!!
******************************
A lokacin da Dr. Faduwa ta ga Umaimah a tsaye
a kofar falonta sai da ta razana, a lokacin data
bude kofa tana shara da sanyin safiyar lahadi. Dr.
Faduwa cike da mamaki ta tsurawa Umaimah ido
tana kallo, don tana kokonton ko ba ita ba ce, ko
kuma mafarki ta ke yi? Umaimah ta lura da
hakan, don haka sai ta yi murmushi ta gaisheta.
Dr. Faduwa ta tambaya, *Yan mata kuwa, daga
ina?
Umamimah ta yi mamaki da jin wannan
tambayar, don haka sai ta kasa amsa mata.
Ta ce, ''Tabbas za ki yi mamakin ganina a
gidanki a yau, kuma a dai-dai wannan lokaci,
amma kada ki
yi mamaki alkhairi ne ya kawo ni. Ko ba ki san
sunana ba na san kin san fuskata, ni
makwabciyarki ce, sunana Umaimah Bello. Dr.
Faduwa ta yi murmushi, ta ce, ''Na gane ki
Umaimah, zo ki zauna.
Suka dungumaa suka isa cikin falo suka zauna.
Yayin da Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ba
tare da ta san ta inda zata fara ba.
''Ina sauraronki *yan mata''. Inji Faduwa.
Umaimah ta dago a hankali ta dube ta, ta yi
murmushi.
Ta ce, ''Na zo na gaishe da ke, kuma na ba ki
hakuri, sannan na yi miki sallama zan tashi daga
gidan nan yau, shi ne na ga ya dace na yi muku
sallama. Don Allah ki taya ni fadawa abokinki
Abdul-Sabur.
Dr. Faduwa ta dade tana dubanta ba tare da ta
san abin da zata fada mata ba, saboda mamaki
da takaici.
Can ta yi murmushin karfin hali, ta ce, ''Daman
kin shekara ne a gidan ko ba kudin shekara kika
biya ba?
Umaimah ta sunkuyar da kai kasa ta yi dan
murmushi. Ta ce, ''A,a kudin shekara na biya,
yanzu watannina tara ina dai so na tashi ne
kawai.
''Saboda kin tsani MAKWABTANki ko? Faduwa ta
fada cikin gatsali. Sai tambayar ta yi wa
kwakwalwar Umaimah nauyi,
cike da mamaki ta dago da sauri ta dubi Faduwa
tana tuhumarta da idanu.
Dr. Faduwa ta sake zaro ido ta dubeta duba irin
na ido cikin ido, ta ce, ''Kwarai kuwa zaki tashi
saboda
kin tsani makwabtanki, suna takura miki da
gaisuwa. Sun ishe ki da yi miki sallama a duk
sanda ku ka hadu a bakin get a matsayinku na
musulmai ku dukka. Babu wannan kaunar ta
musulmi da
yake yi wa dan uwansa musulmi a zuciyarki.
Sai hawaye ya cikawa Umaimah ido ta girgiza
kai, ta ce, ''Ba haka ba ne, ina dai so na tashi ne
kawai don ra'ayin kaina.
Faduwa ta gyada kai, ta ce ''Bazan hana ki yim
abin da kike so kiyi ba, haka ba zan sauya miki
ra'ayinki
ba, kuma ba zan daina yi miki addu'a ba, da
fatan alkhairi a rayuwarki ko ba kya tare da mu.
Sai dai ina so ki sani kuma ki saka a ranki, kin yi
asarar makwabci na gari, mai mutunci da tausayi
da sanin ya kamata, wato Abdul-Sabur. Kin tsane
shi har tsanarsa ta shafe ni, to ki cire ni ma a ciki
don ni tuni na cire shafinki a rayuwata, tunda ba
kya so a bawa juna hakkin makwantaka na rabu
da ke.
Abdul-Sabur ne ba zai iya ba, du ba ki ga duk irin
wulakancin da kike yi masa amma bai damu ba,
kuma bai daina ba. Kar ki dauka don ke mace ce,
kuma mai kyau, a,a
ko maza ne haka yake kula da MAKWABTA, don
shi cikakken musulmi ne, mai rikon addini duk
wata sunnah Manzon Allah (S.A.W) yana rike da
ita. Bari na baki wani labarin da ba ki sani ba, ba
don Abdul-Sabur ba, da babu wanda zai san kina
cikin gidanki kin kwana kina ciwo. Ke ko mutuwa
kika
yi babu wanda zai sani, don babu wanda ya
damu da rayuwarki. Shi ne ya damu da ke, ya ke
lura da
shige da ficenki, ya ke lura da motsinki a lokacin
da kike cikin gidanki. Har ya gano ba ki da lafiya,
kamar wancan lokacin da ya sani na zo na duba
ko lafiya ya yi sati baiji motsinki ba, kika tula
masa
kasa a ido, kika ce mu fita harkarki. Ni daman
tun daga ranar nai alkawari na rabu da ke.
Amma da ya zo min da maganar ciwo in daure in
zo in taimake ki a matsayina na likita, dole na je
na duba ki saboda zuciyar musulunci da tsabagen
magiya da wa,azin da ya saka ni a gaba yana yi.
Don haka ki kula da duniya, kuma kisan darajar
mutum, ki tabbata za ki mutu halinki na gari shi
zai bi ki, kuma shaidar mutane itace shaidar
lahira. Umaima ta doka uban tagumi tana mai
surnano da hawaye. Ta dade ba ta iya furta
kalma daya ba, tana dubam Faduwa tana
sauraron labarin da ta ke ba ta na Abdul-Sabur
tun daga farko har karshe.
MAKWABTAKA 10
Umaimah ta matse hawaye ta dubi Faduwa ta
fara magana cikin sassanyar murya a sanadiyyar
sanyin da jikinta ya yi. Ta ce, ''Duk abinda kika
fada min gaskiya ne kuma nasan duk kuskuren da
nake yi, in takaice miki ko a mafarkina Allah Ya
nuna min gaskiya. Domin ina yawan mafarki akan
makwabtana, sai na ga na shiga hali na tsoro ko
na halaka, sai na ga Abdul-Sabur ya zo ya fitar
da ni. Na san Ubangijina Yana nuna min darajar
makwabtana. Ko a daren jiya na ga na fada rami
Abdul-Sabur ya zo ya fito da ni,
wasu lokutan shi kadai, wasu lokuta har da ke.
To ashe ke nan Allah Ya na nuna min cewar,
kuskure nake yi ke nan da bana kula ku? Nasan
ina cikin halaka saboda rashin kyautatawa
MAKWABTA,
bana so wannan dalili ya sa na halaka shi ne na
yanke hukuncin na tashi kawai.
Dr. Faduwa ta tambaye ta cike da mamaki, ta ce,
''Kin gwammace gara ki tashi daga gidan ki
sauya hakinki na zauna da makwabtanki lafiya?
Umaimah ta sunkuyar da kanta kasa can ta dago
ta dubi Faduwa ta gyada kai. Ta ce, ''Tabbas ina
da dalilina da suka sa ba zan sauya ra'ayina ba
akan MAKWABTA.
Faduwa ta shiga jinjina kai ba tare da ta sake
cewa komai ba. Tsabar mamaki Umaimah ta ke
ba ta, ga
ta *yar yarinya sai taurin zuciya. A hankali
Faduwa ta mika hannu kan teburin da ke gabansu
ta dauko wayarta ba ta yi wata-wata ba, ta
danno lambar Abdul-Sabur. Ba jimawa ya amsa
cikin harshen
Turanci suke magana.
Faduwa ta fada cike da zolaya, ''Kai da Allah
tashi daga baccin nan mu mata ma mun tashi
tun asuba
balle kai namiji. Ya sake yin juyi ya yi mika, ya
ce, ''Ki kyale ni, yau ba ni da wurin zuwa.
Ta ce, ''Ko baka da wurin zuwa a da, yanzu ka
sami wajen zuwa. Ka zo gidana za ku yi sallama
da makwabciyarka, mai shirin tashi daga gidan
nan da sanyin safiyar nan. Sai ya mutsike ido ya
ce, ''Ban fahimce ki ba Faduwa, wa kenan?
Ta yi dariya, ta ce makwabciyarka wacce gidanka
ke kallon nata.
Ya shiga jero mata yambayoyin da ba ta san
amsarsu ba. ''Me yasa zata tashi? Me akayi
mata? Kewa ya fada miki zata tashi? Inji Abdul-
Sabur.
''Ni ma ban sani ba, ga ta a gidana ka zo kawai
ku yi sallama.
Tana gama fadar haka ta kashe wayar.
Ya dade a zaune bai iya tashi tsaye ba, don yana
tunanin mafarki yake yi. Can dai ya katse tunanin
da yake yi, ya mike tsaye. Kai tsaye ban daki ya
shiga ya yi wanka.
Fiye da minti ashirin bai fito ba, Faduwa ta sake
rangada masa waya, ya ce ga shi nan zuwa. Aka
shafe mintuna biyar bai bayyana ba, har
Umaimah ta fara kosawa zata tafi, Faduwa na
lallashinta ta yi
hakuri ya zo. A karo na uku Faduwa ta kira shi,
sai ya tabbatar mata ba zai zo ba ya san karya
ta ke yi shi har ya koma ya sake kwantawa.
Sai da ya ji ta yi magana cikin fushi, sannan ya
shiga bata hakuri gami da yi mata alkawari ga shi
nan zuwa. Bai wuce mintuna biyar ba ya bayyana
a falon Faduwa, sai da ya ga Umaimah ya
gasgata maganar Faduwa, don har ya taho bai
yarda ba. Mamaki mabaiyyani ya fito daga
fuskarsa, ya dubi
Umaimah ya dubi Faduwa, can dai ya zauna,
sannan ya sake yi musu sallama suka amsa a
lokaci guda. Har zuwa wasu *ya dakikai babu
wanda ya yi magana a cikinsu, sannan Faduwa ta
dubi Umaimah.
Ta ce, ''Ga shi ya zo kuma kinyi shiru.
Umaimah ta sake dukar da kai kasa ta ce, ''Ko
bai zo ba na ce ki yi masa sallama zan tashi yau
daga gidan nan. Ina muku godiya da fatan
alkhairi.
Abdul-Sabur ya gyara zama ya dubi Umaimah ya
ce ''Yarinya, me ya sa za ki tashi ke da ko
shekara ba
ki yo ba a gidan nan? Sannan ga makarantarku a
kusa da gidan ko mota ba kya hawa? Ina kike so
ki
koma? Umaimah ta dago a hankali ta dube shi,
ta ce, ''Damansara zan koma.
''Damansara? Inji Abdul-Sabur da Faduwa suka
tambaya a lokaci guda.
Umaimah ta gyada kai ta ce, ''Eh, Damansara.
''Damansara ta yi nisa da makarantarku, kin san
da cewa sai kin shiga mota ko? Sabanin nan da
kike zuwa makaranta da kafa. In ji Abdul-Sabur.
Umaimah ta gyada kai, ta ce, ''Eh na sani.
Abdul-Sabur ya cika da mamaki, ya ce, ''Me yasa
kike so ki tashi? Anyi miki laifi ne na ga ko
shekara ba ki yi ba? Ta gyada kai, ta ce, ''Eh
Faduwa ta yi ajiyar zuciya, ta ce, ''Babu irin
tambayoyin da ban yi mata ba da nasihohi amma
ta
ki ji don haka ka kyale ta ka yi mata fatan alheri,
don idan ka takurata da tambaya ma kuka zata
yi.
Abdul-Sabur ya yi shiru yana tunani, can ya dubi
Umaimah.
Ya ce, ''Akwai wata matsala ne da ta sa dole za
ki bar gidan nan?
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ba komai.
Ya juya ya dubi Faduwa ya ce, ''Ke ma ba ta fada
miki dalilanta ba? Faduwa ta tabe baki, ta ce, ''Ni
a su wa da zata fadamin? Amsar da ta ke baka
ita ta bani.
Abdul-Sabur ya shafa dan siririn gemun da ya
zagaye bakinsa, ya ce, ''Nasan dalilinki Umaimah,
mu ne matsalarki, musamman ma ni da kike
ganin ina takura miki. Ki yi min alfarma ki zauna
har zuwa lokacin da za ki cika shekara, nan da
watanni uku ni zan tashi na bar gidan. Ki ci gana
da zama a nan
saboda ya fi kusa da makarantarku, tunda
makarantarmu tana Subang Jaya, ni zan koma
can kusa da makarantarmu. Faduwa ba ta da
matsala ita ba zata takura miki ba, daman ni
nake takurawa ta je wajenki.
Umaimah ta sake dunkufar da kai kasa saboda
nauyin maganar da Abdul-Sabur yake yi.
Can ta bude baki zata yi magana sai ya dakatar
da ita.
Ya ce, ''Kar ki damu, alfarma kawai na ce ki yi
min, na san akwai takura, amma don Allah ki
daure kar ki tashi, ki zauna.
Umaimah ta girgiza kai, ta ce, ''Ina so na tashi
ne kawai ba don ku ba, har ma na sami gida a
can na
biya na wata uku.
Abdul-Sabur ya ce, ''Wannan ba matsala ba ce,
kina iya cewa kin fasa tunda ba ki shiga ba, kuma
ba ki bata musu lokaci ba, za su dawo miki da
kudinki.
Faduwa dai ta dade tana dubansu ta cika da
al'ajabi.
Can ta ce, ''Ai kin fada dazu kin ce saboda mu
zaki tashi saboda kin san ba kya kyautatawa
makwabtanki. Allah Ya ke nuna miki a mafarki shi
yasa kike so ki tashi ba kya so ki halaka, don ba
za
ki iya sauyawa ba.
Abdul-Sabur ya sake lankwashe kafa daya akan
daya yana girgizawa, kallon Umaimah kawai yake
yi yana so ya ji amsar da zata bayar, sai ta
sunkuyar da kanta kasa don ba zata iya dubansa
ba.
Ya ambaci sunanta cikin wata sanyayyiyar murya,
ya kara da cewa.
Umaimah, me ye matsalarki ne a gaba daya
rayuwarki?
Ta dago a hankali ta dube shi da luhu-luhun
idanuwanta da suka cika da hawaye. Sai ta
girgiza
kai alamar babu komai.
Ya ce, ''Ko ba ki fada ba, duba daya za a yi miki
a san kina da matsala. Kin baro kasarki Nigeria
kin zo
Malaysia da zummar yin karatu kamata ya yi ki
kasance cikin walwala, ko ba a ganki da kowa ba,
ya kamata a ganki da kawaye *yar kasarku,
amma babu kowa ke kadai kike rayuwarki. Babu
ko daya
da na taba ganin ku tare. Babban abin da ya ba
ni mamaki shi ne, na lura ko wayar hannu ba ki
da
shi, ba kya kiran *yan gida su ma ba sa kiranki.
Ta yaya za,a yi ace iyayenki su turo ki wannan
kasa mai nisa su manta da ke ko a waya ba
satuntubarki.
Umaimah ta fara kuka wiwi, kan ka ce kwabo
hankalin Faduwa da Abdul-Sabur ya yi
mummunan
tashi. Faduwa ta zaro toilet paper ta mika mata
don ta share hawayenta. Sai suka shiga
lallashinta suna ba ta hakuri.
Abdul-Sabur ya girgiza kai, ya ce, ''yi hakuri ki
daina kuka, ba ke kadai ba ce mai matsala, mu
dukkanmu nan da kika gani muna da matsaloli
manya-manya, wadanda da zamu bude miki mai
yiyuwa ma ki ji taki shafar mai ce akan tamu.
Amma kinga mun ci gaba da rayuwa, muna
gaisawa da
mutane, muna da kawaye, muna dariya ba ma jin
haushin kowa saboda munyi tawakkali, mun
dogara da Allah Shi Ya dora mana, Shi zai yaye
mana. Haka ake so duk wani musulmi ya
kasance,
akwai irinmu da yawa a duniya masu matsaloli da
suka linka naki sun yi hakuri suna ratuwarsu cikin
walwala idan kin gansu ma ba za ki taba zaton
sun taba yin kuka ba a duniya, amma suna bude
baki
suna fada miki matsalarsu sai kin yi musu
hawaye.
Umaimah ina mai baki shawara ki cire damuwa a
ranki, a matsayinki na musulma duk abin da ta
dame ki, ki roki Allah Ya yaye miki, idan wani abu
kika rasa ki yi addu'a Allah Ya musnya miki da
mafificin alkhairi. Kada kuma laifin wani ya shafi
wani kamar yadda kika hada mu gaba dayan mu
kika tsana, ba a yin haka, kin ji kanwata. Ina
fatan
zaki dauki shawarata ki fasa tashi, ki kawo mim
rasitin na biyan kudin da kika yi na sabon gidan,
zan je na yi musu magana za su dawo miki da
kudinki In shaa Allah idan har ba kya son zaman
a gidan ni zan tashi nan da watanni uku, sai ki ci
gaba da zuwa makaranta hankalinki a kwance.
Daga karshe ina yi miki addu,a Allah Ya yaye miki
damuwar da ke damunki, Ya ba ki hakuri, Ya
sauko
miki da walwala a cikin zuciyarki. Ya kare ki daga
sharrin masu sharri. Ya ba ki sa,ar jarabawa.
Umaimai tana sharce hawaye tama amsa masa
da ''Amin.''.
MAKWABTAKA 11
Ta