Showing 129001 words to 130520 words out of 130520 words
Chapter 44 - MAKWABTAKA COMPLETE DOCUMENT BOOK Writing by Jamila Umar Tanko .txt
a hannun *yar Uwarsa.
"Samun naku shine namu. In ji almajiri Sabitu.
"Allah Ya bada zaman lafiya, mu mun tafi
Umaimah sai watarana. Haka kowannensu yake
ta fada a lokacin da suka shiga motocinsu zasu
tafi.
Dakyar aka banbare Babangida da Bilal daga jikin
Umaimah, sai hankalin ta ya sake tashi matuka.
Umaimah bata daina rusa kuka ba, wannan karon
kukan na bakin cikin rabuwa da *yan uwa da
kuma gida ne, dan kowa yabar gida, gida ya bar
shi. Tana ji tana gani kowa ya tafi ya bar ta,
Aisha da Umaimah suka rungume juna suka yi ta
kuka ba adadi har sai da suka saka jama'a da
dama kuka. Saboda tausayi, tabas sabo turken
wawa ne.
Faduwa da Sagir dinta kuwa ba su yi sallama
gaba daya ba zasu tafi su dawo dan ba yanzu
zasu koma Cairo ba sai ta zaga dangi ta nuna
mijinta da *yarta.
Bayan ta zagaya gidan danginta na Abuja,
Kaduna da Zariya zasu wuce su gaisa da dangi.
Sai ta wuce Kano nan ma akwai su daga nan sai
su wuce Sokoto mai dungurungum in da cibiyar
take, daga dukkan alamu zata dade a kasar.
Abdul-Sabur ne ya dauki nauyin basu mota da
direban da zai kewaya ko ina dasu.
***
Kowa ya yoye babu kowa kuma gida ya rage
daga amarya sai angonta sai kuma so da kauna
sa suke tsakani.
Dan Ummana Fuse ma da mai aikin da aka
daukar mata duk gidan Khausar suka gudu, da
taro ya watse sai ta ji zaman babu dadi, suka
tafi can zasu yi kwanaki sannan su dawo.
Dakyar Abdul-Sabur ya lallasheta ta shigo gidan
daga bakin get, ya dauko nankici daga aljihunsa
mai kamshin gaske ya mika mata, ta karba a
sanyaye ta goge hawaye. Cikin tattausan lafazi
yake magana.
Ya ce "Yanzu Umaimah har kuka kike yi dan *yan
uwanki sun kawo ki wajena sun tafi sun bar ki?
A tunanina ni ne kadai mutum daya tak da zaki
so ki dauwama tare da ni.
Ta gyada kai ta ce "Haka ne. Ya ce "To meyasa
kike kuka alhali kin gama kukan rabuwa da Baffa
tun acan?
Idan baki manta ba na taba fada miki cewar kin
daina zubar da hawaye daga ranar da kika hadu
da ni. Ki yi shiru ki daina kuka Umaimah Allah ne
gatanki, Abdul-Sabur ne gatanki. Kin rabu da
maraici daga yau, kin rabu da takaicin da namiji,
kin rabu da cin amanar makwabtanki kuma kin
rabu da babu insha Allah.
Farin ciki ya rufe Umaimah ta yi sauri ta durkusa
a gabansa ta yi masa godiya, ya girgiza kai ya
mika
hannu ya tashe ta tsaye. Ya ce "Ki daina yi min
godiya, ke dolena ce babu abinda ba zan iya yi
miki shi ba aduniya.
Ta yi murmushi ta lumshe ido ta ce "Ko baka
fada ba na san da haka, na yarda da tarbiyarka,
ka cika dan halak. Na maka alkawarin nima zan
zama baiwarka babu abinda ba zan iya yi ba in
har zan
kyautata maka.
Ya yi ajiyar zuciya ya yi murmushi ya ce "Na
yarda da tarbiyyarki nima kuma na yarda da son
da kike yi min na tsakani da Allah. Mu je daki mu
yi alwalla mu yi sallah raka'a biyu mu godewa
Allah, mu
kuma roke Shi Ya kare mu daga duk wata fitina
da ke cikin aurenmu.
Umaimah ta bishi suka shiga daya daga cikin
maka-makan dakunan da suka jere a saman
bene. Babu
abinda yake tashi a cikin dakin daga sanyi Ac sai
kamshi na alfarma.
Tabbas idan kana cikin dakin nan ba zaka san
yanayin da gari yake ciki ba, dare ko rana, zafi ko
sanyi, guguwa ko ruwan sama. Dan haka ango da
amarya suka yi lif a cikin ni'ima basu sake
tunawa da hayaniyar waje ba, sai ka rantse babu
bil adama a cikin gidan nan.
Asuba ta gari Abduumimah.
Abdul-Sabur yana jin dadin zama da amaryarsa
sosai ya same ta mace mai ladabi da biyayya da
godiya. Ba ta da kwadayi haka bata karya da
dogon buri irin na *yan matan zamani, duk
abunda ya bata sai ta karba da murna ta yi
godiya.
Ga ta mace mai kunya da tsoron Allah dan
akwaita da ibada, ya yarda da ita ya san ko baya
nan ba
zata ci amanarsa ba. Tana masa biyayya matuka
dan bai taba hana ta abu ta yi ba, haka bai taba
saka ta abu tayi masa musu ba. Abunda ya kara
masa sonta shine tana kula sosai da tsohuwar
kakarsa wato Ummana Fuse. Ita ce mai yanken
farcenta, ta tsefe ta wanke, ta kitse mata
gashinta.
Haka kawai sai Umaimah ta shiga kasuwa ta siyo
mata atamfofi ta kai mata dinki, ta kawo ba tare
da
kowa ya sani ba kuma da kudinta. Sai dai
Ummana Fuse ta fada musu shiyasa Khausar ma
take matukar son Umaimah har take fadawa
Abdul-Sabur cewar ashe ta so tayi kuskure da ta
so hana shi auren Umaimah a Malaysia.
Rayuwa kenan duk wanda yayi zalunci tun daga
duniya zai fara ganin ba dai-dai ba. Sai ga
Faduwa ta dawo daga Sokoto wurjanjan a gidan
Umaimah hankalinta a tashe. Har hankalin su
Abdul-Sabur ya
tashi da suka ganta a haka, kafin ta basu labari.
Ta fayyace musu irin abubuwan da ta gani a
Sokoto shine ya tayar mata da hankali. Suka
gyara zama suka tambaye ta me ta gani?
Ta zauna ta basu labarin komai ta ce "A
sakamakon hanata gadon
Mahaifinta da suka yi sun hadu da bala'ai kala-
kala gidan gaba daya babu wanda ya ci gaba.
Talauci ya
ruftowa, matan Babanta da *ya*yansu haka ma
kawunnanta komai ya kare.
Gaba daya kuka suke suna neman gafararta wai
sunsan sun zalunce ta, yanzu abincin da zasu ci
ma ya gaggaresu. Sai ita ta dinga taimaka musu
duk da *yan kudin da suka rage ya kare a can.
Yanzu ma akwai alkawuran da ta yi zata aiko
musu da kudi idan ta koma Cairo. Har da masu
rokarta a cikin kannenta wai zasu biyo ta Cairo
ta samar musu aiki koda share-share ne saboda
talaucin ya ishe su, ta
ce a'a ba sai sun biyo ta ba zata dinga yi musu
aike.
Abdul-Sabur ma yayi alkawari idan ya tashi bayar
da taimako zai dinga kai musu agaji. Sati guda
cur Faduwa da Sagir suka sake yi a gidan su
Umaimah sunji dadin karramawar dasu Umaimah
suka yi musu sun ji dadin zama a Abuja
dan an kewaya da su ko ina, suna ta sha'awar
ango da amarya yadda suke zaune lafiya cikin
tsantsar so da kauna. Ba'a son ransu suka rabu
ba, sai suke ji kamar su ci gaba da zaman kamar
yadda suka zauna a Malaysia. Idan suka zauna
sai su raba dare suna hira, har sai da Sagir ya
fara koyon Hausa sabida tsabar Hausa da yake ji
idan suka hautsine da hira.
Kyautar girma su Abdul-Sabur suka yi musu,
suka kaisu filin jirgi suka hau suka tafi Abdul-
Sabur yayi musu alkawari zasu zo Cairo suma su
kwana biyu
Asuba ta gari Abdulmaimah!
**
Allah cikin ikonSa ya cikawa Abdul-Sabur gaba
daya burinsa daya kudira na taimako, gaba daya
alkawuran daya dauka sai da ya cika su, tun
kafin shekara ta zagayo. Shi yayi komai a auren
Sabitu da Aliya, haka Ilah da Furera, amma Baffa
ya hana su tarewa a Gombe ya ce su ci gaba da
zama a Dugge anan suka saba iyaye da kakanni.
Gidajen sumunti Abdul-Sabur ya giggina musu a
garin masu kyawun gaske, haka gidan Baffa gaba
daya aka sauke na kasa aka kafa na siminti,
sannan ya ginewa Dagaci nasa shima na siminti,
sai suka haskaka garin. Ya gina katafaren gida a
cikin Gombe a unguwar masu kudi, na Umaimah
ne idan sun zo gari suke sauka. Dan zamanta a
Gombe ya so ya fi na Abuja yawa saboda tana da
abubuwan yi a garin dole sai tana nan zai yiwu.
Abdul-Sabur ya fahimce ta, bashi da matsala ga
saukin kai idan ta taho sai ya biyo ta su zauna.
Umaimah bata manta da mutanen garinsu ba.
Abubuwan da garin zai ci gaba take yi musu
hanya a gwamnati, ana saka su a cikin lissafi
yanzu.
Rubutu take yi a jaridu da mujallu akan a dinga
tunawa da Rugage ana tallafa musu da abubuwan
more rayuwa kamar irin na burni. Dan suma
mutane ne, *yan kasa, kuma *yan jiha. Dan suna
jefa kuri'a idan lokacin zabe ya zo, saboda haka
suna da alhaki akan gwamnati.
Nan da nan ake sauraron kiranta dan su Hanif
sun sami aiki a cikin gwamnati sune a gaba-gaba
ana
damawa da su a siyasa da mulki.
A kowacce ma'aikata Umaimah sai ta ga kawarta
ko abokinta ne da suka yi karatu a Malaysia
masu rike da wajen dan haka nan da nan
takardarta take isa gaban gwamna, kuma su
saka baki ayi mata abunda take so.
An kai ruwan fanfo garin Dugge, wutar lamtarki,
service din waya, anyi titina, da uwa uba
Makarantar boko da malamai kwararru.
Da kanta ta zo ta tara iyayen yara ta yi musu
nasihu na wayar da kai akan su saka yaransu a
makarantu
dan su yi ilimi kamar yadda ta yi, suma su
inganta rayuwarsu.
Tabbas Umaimah ita ce babbar musali, ita ce
abar da zasu yi kwaikwayo da ita, nan da nan
suka yi amanna da wannan kira nata su saka
*yan*yansu a makarantu.
Makarantun Islamiyya ta bude da kanta ta dauko
malamai kwararru ta zuba suke koyarwa har da
Sabitu da Ilah, tana biyanzu albashi duk wata....
Shafin karshe a shafe yake ma'ana rubutun ya ba
ce don haka na ke sanar da ku cewa mun yi
Bankwana da MAKWABTAKA ayau.
Kuma nima nayi bankwana daku ayau.
Alhamdulillahi.
Ina godewa Allah da yardarSa da Amince war Sa
daya nuna mana wannan lokacin na ranan karshe
a littafin Makwabtaka.
Ina mai godiya a gare ku en uwa da addu'oin ku
da fatan alkhairi a gare ni. Nagode.. Nagode..
Nagode sosai Allah yabar xumunci.
Ina kuma mai nemon afuwa da yafiya ga duk
wanda na batawa ko wani maganar da baiji dadi
ba ko wajen jinkirin post ko wajen kuskeren
rubutu da sauran su.
Na yafewa kowa tsakani na da ku baki daya.
Allah ya yafe mana kura-kuren mu baki daya
manya da kanana.
Aamiin.
Sannan ina mai nemon addu'r ku Auntyna bata
jin dadin jikin ta kwana biyu kuma nima mun
koma makaranta dukka muna baran addu'o'i
daga bakunan ku masu Albarka.
Allah yabiyawa kowa bukatun sa na Alkhairi...
Aamiin.