Showing 21001 words to 24000 words out of 153964 words

Chapter 8 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3768

ta sauka daga cikin motar, kwakwalwarta na ta aunawa da tarawa ne akan maganar da ya fad'a mata, da ace akwai wani abu dake damunta bayan matsalar kwakwalwarta, da tun farkon zuwanta asibiti Dr. Gibert ya fad'a mata ko kuma a yanzu da take ganin Dr. Florence ta san da hakan.

Ta yaya za'ace don kawai yaga takardunta ne zai yanke hakan, shi kad'ai ransa? kuma har yana fad'in taje tayi shawara ta samo matsalarta, sai yanzu sosai ta fahimci rainin hankali k'arara a cikin zancen.

A baya tayi kokarin goge tunani irin nasu melissa a cikin kanta amma a yanzu kwakwalwarta ta fara gano ingancinsa, dole ne akwai wani dalilin da yasa ya kawo kansa cikin rayuwarta, akwai wata manufarsa daban da yake son cimma, kuma tayi wa kanta alkawari in har da ita yake tunanin amfani yayi koma me yayi niyya to sai dai su rasa damarsu su duka biyun!

Da haka ta k'arasa k'ofar gidan nasu, ta tsaya a barandar ta danna door bell dake gefe.

"Aunty deelah! kin san su waye suka zo?"

Iman ta fad'a da k'arfinta sanda ta wangale k'ofar.

"Su waye?" Ta tambaya sanda ta shigo ciki tana kokarin cire takalminta.

"Aunty Miryama dasu Haneey! Kuma kin san me? wai sun dawo nan gabad'aya."

Gabanta ya fad'i a lokaci d'aya, ta juyo da sauri ta kalleta.

"Nan ina?"

"Nan garin mana, anjima ma zamu je muga sabon gidansu! Dad'i nake ji sosai... Haneey tace tana da games d'in su Moana da yawa kuma har da..."

Daga nan corridor d'in tana iya jiyo muryoyin mutane dake ta tashi daga falo, Aunty Miryamah 'yar uwar daddy ce ta dangin mahaifinsa dake zaune a garin Vegas ita da mijinta Balarabe da kuma 'yayansu guda uku duka mata.? Fatimah, Sa'ar Zahra guda d'aya, sai wadda ta girmi Iman Aysha da kuma sa'ar Iman d'in Haneefa.

A farkon zuwanta k'asar nan, lokacin Aunty Miryaman da 'ya'yanta sun zo hutu,? matsalar da ta fara samu daga wajenta ne, don ba irin fad'a da maganganun da bata yi ba, akan rik'e ta da Daddyn yace zaiyi, ta dinga ziga Mami Saffiyya da shawara kala-kala akan kar ta yarda da zamanta sai da Daddyn da kansa ya taka mata birki sannan tayi shiru.

Ta fahimci ita macece da bata tab'a son wani ya rab'e ta ita da 'ya'yanta, don duk shirin da suke da Mami Saffiya ma, su Zahra basu cika zuwa gidanta ba don ko sunje d'in ba wata kulawar kirki suke samu ba.

Ta k'arasa cikin falon jikinta a sanyaye sanda Mami Saffiya ke fad'in.

"Har kin dawo deelah, nayi zaton sai nan da awa d'aya."

Aunty Miryaman dake zaune a gefen Mami ta juyo jin hakan, tana sanye cikin doguwar riga bak'a ta abaya, ta had'e girar sama data k'asa kamar mai shirin lailayo zagi.

"Eh, Mami bamu fara ba tukunna sai jibi."

Ta fad'a muryarta a hankali sannan ta tsugunna har k'asa ta gaishe ta.

"Lafiya." Bakinta ya motsa kad'an ba tare da wani sauti ya fito ba, sai ta juya gefen Mami tace.

"Dama har yanzu wannan yarinyar tana nan? kinyi kokari wallahi Saffiya kinyi k'okari!"

A baiyane yake tun da bata tab'a b'oye kiyayyarta ko a gabanta ne kuwa.

Fadeelah na ganin yadda Mami ta d'anyi murmushi alamun bata ji dad'in hakan ba, sai ta mik'e da sauri tayi hanyar d'akinsu amma kafin ta isa kunnenta ya jiyo mata Aunty miryaman na fad'in.

"Kuma har yanzu tana fama da wannan ciwon haukan?"

Ta rufe k'ofar da sauri sanda kowannensu ya d'ago ya kalleta. Zahra da sa'arta Fatima nata danne-danne cikin Ipad dinta yayin da Iman ke nunawa Haneey stickers d'inta na cartoons, d'ayar Aysha na daga can jikin zanenta tana kallo.

"Kin fara lesson d'in?" Zahra ta tambaya lokacin da Fatiman ta maida kanta kan abinda suke yi, ba tun yau ba ta fahimci dukka 'ya'yan halinsu d'aya da mahaifiyarta, Aysha ce kawai mai d'an saukin kai a cikinsu. A baki su 'ya'yan musulmai ne, amma a d'abia da tarbiyya basu da banbanci da 'ya'yan turawa, akwai layi mai kauri tsakaninsu da 'ya'yan Mami.

"A'ah Zahra, sai jibi tukunna."

"Amma ko waye ya raina miki hankali wallahi, zaman da kika yi a banza kenan?"

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba, don a yanzu zancen Aunty Miryamah ya shafe na Adam a cikin kanta.

Ta ajiye kayanta sannan ta shiga band'aki tayi wanka, har ta shirya ba wanda ya kula ta a cikin 'ya'yan itama bata bi kansu ba ta saka doguwar riga mai k'aramin hannu sannan ta d'aure gashinta cikin bun.

Har zata fita a haka, ta tuna da Aunty Miryama saboda haka ta d'auko hijaabinta ta zura. Sanda tazo wuce su ta falo, kanta na k'asa saboda haka bata ga irin banzan kallon da Aunty Miryaman tabi ta dashi ba.

Tana shiga kitchen ta cire hijaabin ta fara kokarin had'a tea don haka kawai taji bata sha'awar cin abinci.

"Fadeelah."

Mami ta kira sunanta sanda ta shigo kitchen d'in. Da murmushinta ta juya ta kalle ta.

"Dan Allah kar ki saka zancen Miryamah a kanki ya dame ki, tun farko bata fahimce ki bane amma na tabbata tunda yanzu sun dawo kusa damu komai zai gyaru insha Allah."

"Insha Allah Aunty, ba komai." Ta fad'a da murmushi ba tare da ta tabbatar da abinda ta fad'a ba, don daga yanayin Aunty Miryamah bata tunanin ko tunda aka haife ta suke tare zata tab'a sonta.

A hakali ta juya ta cigaba da kokarin zuba sugar da take yi a cikin madara. Sanda ruwan zafin dake cikin kettle ya tafasa take zubawa, lokacin taji motsi a bayanta, tayi zaton Mami ce saboda haka bata juya ba har ta gama had'a tean ta.

"Uhmm... ina kike ganin zan ajiye wannan?"

Da wani irin sauri ta juyo jin muryar namiji a bayanta.

Ai kuwa karaaf! idanunta suka shiga na cikin wani saurayi?daga bakin k'ofar kitchen d'in, yana tsaye hannayensa rik'e da manyan ledojin siyayya. Kallo d'aya tayi masa idanunta suka gano mata wani irin tsantsaren kyau da kamala.

Fararen idanu tas! d'an siririn hanci a tsaye masu k'ananan k'ofofi na shak'ar iska kawai, gira mai kauri, dogwayen gashin idon da har inuwarsu ake gani akan fatarsa, d'an siririn leb'e dake tsakiyar wani kwantaccen saje... sai a lokacin kuma ta tuna irin rigar jikinta sai ta juya baya da sauri ta lalubo hijaabinta ta zura, kanta cike taf da mamakin WAYE SHI kuma me yake yi a tsakiyar kitchen d'insu.

Sai dai muryar Aysha data shigo a lokacin, ta amsa mata dukkan tambayoyin a cikin jimla d'aya.

"Ya Al'ameen kazo inji Mommy zamu tafi yanzu."

Sai k'afafunta suka k'ame cike da tsananin mamaki, wannan d'an Aunty Miryaamah ne? Tayi zaton ai Fatima ce babbar 'yarta, ya akayi bata tab'a ganinshi ba?

Taji k'arar sanda ya ajiye ledojin akan counter kitchen d'in sannan muryarsa ta biyo baya, wata husky murya mai zurfi da kuma kwarjini, wadda ta fito da zallar matsayinsa na namiji.

"I'm sorry, kiyi hakuri na ganki a haka."


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

07

(&_&)

Tana tsaye daga bayan wata had'addiyar mota hannayenta rike da ledojin siyayyar nan wad'anda ta rik'o bisa umarnin Mami a lokacin da suka rako su Aunty Miryaman dake shirin tafiya.

"Toh shikenan idan ya dawo zamu yi maganar dashi, kince ma kuna buk'atar wata motar ta kai yara makaranta ko?"

Mami ta fad'a sanda suke cigaba daga tattaunawarsu daga bayan motar nan, wadda a cikinta yaran Aunty Miryamah ne dasu Zahra da zasu je su gano sabon gidan da suka tare.

Yana zaune daga mazaunin direba, ya saita mudubin gefensa yana kallonta tsaye daga gefen su Mamin, headphone ne a kunnensa wanda k'arfensa na sama yabi ya nutse luf! cikin sumar gashin kansa irin ta jinsin larabawa, a karo na biyu data kai idonta cikin mudubin suka had'a ido sai ta koma bayan Mami a hankali ta kare kanta.

A cikin zuciyarsa, tunani ne fal! na son sanin ina Mami ta samo wannan 'yar kamilalliyar budurwar da kuma sanda tazo, tunda shi dai ya san ko a wajen 'yan k'annensa bai tab'a jin zancenta ba duk kuwa da yana yawan ji suna hirar su Zahra, ya k'ank'ance idonsa kad'an yana hango gefen fuskarta ta tsakanin fuskar Mamin data tsaya a bayanta, haka kurum yaji yana da interest na son sanin wacece ita.

"Goben idan kin shigo sai muje mu siyo curtains d'in."

Aunty Miryama ta fad'a sanda ta zagaya can gaba zata shiga motar, har Mami tayi gaba tabi baya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?nta sai kuma ta juyo tace.

"Deelah wannan a booth za'a saka su... Al'ameen bud'e mata booth d'in."

Aunty Miryama da bata kai ga shiga motar ba ta juyo tabi ledojin hannun Fadeelan da wani irin kallo, kamar tana shawarar fasa amfani da kayan ciki ne tunda hannayen wadda tak'i jini sun tab'a. Har zata yi magana sai fitowar Al'ameen ta katse ta.

"Button d'in yak'i dannuwa daga nan, bari in gani..."

Ya rufe k'ofar motar, ya zagayo baya daidai inda take tsaye, yayi mata murmushi mai nuna alamun sannu sanda ya danna mukullin motar, booth d'in ya shiga d'agawa da kansa. Bata ce komai ta shiga k'ok'arin had'a bakin ledojin don ta saka, sai ya sunkuyo da hannunsa k'asa ya karbi na hannu d'aya, muryarsa mai zurfi kamar maganad'isu ta ratsa cikin kowanne senses na jikinta.

"Ban tab'a ganinki a gidan nan ba... Zan iya tambayar yaushe kika zo?"

K'amshin sassanyan turarensa ya busa a hancinta sai ta sakar masa ledojin cikin hannunsa ba tare da ta shirya ba, haka kurum taji ta takura a gabansa.

"Last year." Kwarjininsa yasa ta amsa hankali ba tare da ta d'ago da kanta ba.

"Fadeelan last year, ya akayi ba wanda ya tab'a fad'a min kinzo?"

Ta d'ago da kanta da sauri ta kalle shi jin ya ambaci sunanta, tunda take bata tab'a jin wanda ya fad'i harafan sunan daidai kuma yayi mata dad'i kamar shi ba, idanunta suka shiga cikin nasa farare tas! sai dai bata yi wani nisa ba muryar Aunty Miryama daga baya ta finciko ta.

"Baza ta iya sawa bane?"

A tsorace ta juyo ta kalli gaban motar,?Mami na amsa waya yayin da Aunty Miryaman ke tsaye a jikin k'ofar motar ta had'e girar sama data k'asa tana kallonsu, sai dai shi bai saurareta ba don sake sunkuyowa yayi ya karb'i na d'aya hannun nata ya saka a booth d'in.

Sai ta juya da sauri ta koma hanyar cikin gidan idanunta na kallon yadda tafin hannunta yayi ja saboda nauyin kayan.

"Mommy wacece ita? Baku tab'a fad'a min tazo ba."

Ta jiyo muryarsa sanda yake komawa gaban motar.

Amsar da Aunty Miryaman ta bashi? cikin harshen turanci ta daki kunnuwanta ba shiri ta bud'e k'ofar falon ta shige.

"Uwarka ce Al'ameen, dole ai a gaya maka in tazo."

***

"Dan Allah Deelah kar ki saka damuwar Miryama a cikin kanki, kiji da tarin abubuwan da suke gabanki, na gaya miki insha Allah zata fahimce ki tunda sun dawo nan gabad'aya."

Mami ta fad'a sanda ta shigo gidan ta tarar tana wanke plates d'in da akayi amfani dasu.

"Takurawar da ake yiwa musulmai ne a can Vegas yafi yawa akan nan, har wasu mutane sun jefi Aysha a ido sai da aka mata surgery shine mijinta yace gwara su dawo nan garin tunda ko ba komai akwai 'yan uwanta a kusa, shi kuma yana can sai ya samu hutu zai dinga zuwa.

Jiya suka iso kuma unguwar da ya kama musu gida babu nisa daga nan, don haka gobe zamu je gidan gabad'aya zan taya ta siyayyar wasu kayayyakin."

"Wallahi Mami ba komai fa ni ba wai damuwa nake yi ba, na fahimci kawai jininmu ne bai had'u ba kuma zan dinga k'okari ina kaucewa hanyarta insha Allah, saboda haka gobe ma in zaki je ba lallai ne in biki ba."

"Ai ba zai yiwu ba kuma, kema kamar kowa ce a gidan nan don haka baza'a taba ware ki a komai ba, kuma itama ta haka ne zata saba dake. Sannan ki k'ara hakuri akan abinda tace wa Al'ameen d'azu, na san kema baki sanshi ba, shine babban d'anta lokacin da kika zo yana England ne a makaranta."

Da murmushinta tace.

"Mami kuwa sai cewa kike inyi hak'uri kamar wani laifi aka min, wallahi na rantse miki ba komai ni banji wani abu ba."

"Toh Allah yasa, naso su Zahra ma sun bari sai gobe muje gabad'aya, yanzu dole sai sun saka shi ya dawo, wai ina Farouk yaje ne? Al'ameen d'in yana ta tambayarsa."

"Stadium, Ball."

"Haka ne wato yau babu Tahfeez."

Har ta juya zata fita, Fadeelah ta juyo a hankali ta kira sunanta.

"Mami me ya faru da kantin daddy kwanakin baya?"

Sai ta tsaya cak daga bakin k'ofar cike da mamakin yadda akayi zancen da suke b'oyewa ya fito.

"Waya fad'a miki wani abu ya faru deelah? me kika gani?"

"Sau biyu ina jin yana amsa wayar dake ke da alak'a da zancen kantin ne, kuma na san ba haka aka saba ba."

Sai Mami ta lalubo ajiyar zuciya ta d'ora a kirjinta, da farko tayi zaton ko Fadeelan taji tattaunawarsu da Daddy ne a jiya.

"Babu komai ba abinda ya faru, watakila zancen sabon xubin d'in da zasu fara ne yasa yake yawan wayar."

Sanda ta fad'i hakan, Fadeelah na iya hango rashin tabbacin maganar a idonta, sai dai bata son matsawa akan abinda bata yi niyyar gaya mata ba, saboda haka tace.

"Gobe zanje wajen Dr. Florence bayan makaranta."

"Kina da appointment ne?"

"Patients d'inta basa buk'atar appointment, kowa zai iya zuwa bayan ranar data maka fixing."

"Toh kar ki dad'e tunda zamu fita."

A baya duk ranar da tace zata je wajen Dr. Gilbert Mami ko Daddy zasu tambaye ta akan me zata je, amma tunda ta koma wajen Dr. Florence ta kula sun daina hakan, sun yarda cewa a yanzu ciwonta keb'antaccen abu ne da ba kowa ya kamata ta dinga zancen dashi ba.

Itama kuma sai ta godewa Allah da bata tambaya ba, don bata san ta yadda zata yi bayanin cewa zata je tambayar rainin hankalin Adam ne ba.

A wannan daren data zo kwanciya, tunanin hoton fuskar Al'ameen ya cika kanta, ba wai don bata tab'a ganin mai kyau irinsa ba, A'ah.. sai don bata taba ganin mai kyawu da tsarin halittar da yayi mata kwarjini irinsa ba. Ta tabbata da Mahaifinsa yake kama wanda akace balarabe ne don babu abinda ya had'a siffar Aunty Miryaamah data fi kama da turawa da tasa.

Ta jawo wani d'an k'aramin throw pillow ta rungume lokacin da shirun d'akin da duhunsa ya shaida cewa Zahra ma ta ajiye wayarta tayi bacci. Dole ne ma ta goge zancen kwarjini Al'ameen a ranta tunda dai ba abinda hakan zai k'are ta dashi kuma ta riga ta sani baza ta so koda tunaninta ya rab'i duk wani abu daya kasance daga hanyar Aunty Miryama ba, balle kuma jininta.

Ta jero addu'o'inta sannan ta rufe idanunta a hankali, amma sai hoton fuskar Al'ameen ya sake yiwa idanun nata rumfa!

Sai kawai ta d'ora filon a sama ta binne kanta cikinsa.

***

"Maganar Gaskiya ni bana tunanin mutumin nan niyyarsa ta koya miki karatu ce, in ba haka ba me yasa zaice wai kina da wata matsalar dake baki san da ita ba?"

Romilda ta fad'a sanda suke zaune a k'afar benen hanyar classes d'in dake hawa na uku a makarantar inda ba'a fiye wucewa sosai ba, suna k'arasa zana wani format na architecture da aka basu aikinsa.

"Sannan ta yaya ma za'a ce duk tsawon lokacin nan ba wanda ya tab'a fad'a miki hakan daga asibiti sai shi kawai, idan nice ke daga yanzu ba zai k'ara ganina ba."

Melissa ta fad'a kanta na kan zanenta, sai kuma ta d'ago ta tattara dogon gashinta ta tufke shi a baya, saboda yadda yake wa fuskar tata rumfa.

Fadeelah tayi ajiyar zuciya a hankali tana nata zanen, abinda suka fad'a haka ne tunaninta itama, amma babu zancen cewa kar ta koma wajensa, ta riga ta rufe wannan babin da kwarin gwiwar cewa zata iya, zata sadaukar da nata farin cikin don ganin bata b'atawa su Mami ba, saboda haka tace.

"Yau zanje Clinic idan har Dr. Florence ta tabbatar min da bani da wata matsalar bayan ciwona, zanje muyi ta ta k'are dashi, in zai koya min fine! in kuma ba zai iya ba, na samu wata hanyar da Mr. Hawkins zai canja min wani kenan.

Abinda Romilda ta fad'a yasa ta d'ago da kanta ta kalle ta.

"Bana tunanin zai tab'a bari hakan ta faru, sai idan har ba zai shafi dalilin da yasa ya shigo cikin rayuwarki ba."

A lokaci d'aya sai zuciyarta ta cilla kan wannan tunanin da itama ya d'arsu a ranta.

Wane dalili ne ya shigo dashi cikin rayuwarta?

***

"Barkanki da zuwa! Kina da appointment ne yau?"

Receptionist d'in Clinic d'in ta tambaya a lokacin da Fadeelah ta tsaya gaban kantar ta. Ba sau d'aya ba sau biyu ba, tasha tantamar shekarunta a cikin kanta, don wani lokacin sai tayi kama da babbar mace wani lokacin kuma yarinya, gashinta a kullum zube yake a gefen kafad'unta bak'i sid'ik yasha gyara yana kyalli, sannan idanunta kalar ruwan toka ne da duk sanda ta kalle su sai taji kamar tana son ta nemo wani abu daga cikinsu.

"Bani da appointment yau, nazo ganin Dr. Florence ne."

Tayi mata wannan murmushin da kowacce sakatare ke mannawa a fuskarta sannan ta juya kan computer, ta danna harafan da suka had'a sunanta.

"Kin goge appointment d'inki na ranar Asabar baki zo ba, haka ne?"

Haka ne. Bata zo satin daya wuce ba, wannan satin data yanke shawarar zuwa wajen Adam a Alhamis d'insa, a juma'a kuma ta had'u dashi ya bata sunayen topics d'in, saboda haka Dr. Florence bata da masaniyar alak'ar ta dashi kenan ko kuma dukkan abinda ta rubuta game dashi a cikin jotar ta, Ta ayyana a ranta cewa bayanin da zata yi mata zaiyi tsawo kenan.

"Kiyi hak'uri amma rashin zuwanki yasa kinyi missing sak'on Dr Florence, ta tafi wani aikin garin Alaska ranar Monday kuma sai nan da sati uku zata dawo, saboda haka yanzu file d'inki yana hannun Dr. Martins in kina so zaki iya ganinsa yanzu don yana ciki."

Sai tayi shiru kawai tana kallonta, kwakwalwarta na k'irga adadin sati uku a cikin kanta, don ba sai tayi tunani ba ko ta laluba, zata jira ta ne har zuwa sanda zata dawo kamar yadda ta tab'a yi lokacin da Dr. Gibert yaje New York tsawon wata guda.

Don ta tsani cewar duk sanda likitanta yayi tafiya sai taje ta maimata abubuwa da dama a wajen wani sabon, sannan in ya dawo kuma ta sake maimata abinda aka d'ora ga wanda ya dawo. Matsalarta ma a yanzu Dr.Martins ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login