Showing 30001 words to 33000 words out of 153964 words

Chapter 11 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3778

motsi ba balle yayi magana har zuwa lokacin da hannun shugaban ya d'auko wannan file d'in daya gani d'azu a hannun John, a sannan ne yaji zuciyarsa tayi wani irin motsin da shi kad'ai ya san ma'anarsa.

"Case ne akan wani mutumi da ake zargi da kisan kai daga can garin Alaska, an neme shi an rasa sai a yanzu ake tunanin ya gudo daga garin yazo nan ya bud'e sabuwar rayuwa a matsayin malamin makaranta, saboda haka babu hanyar da za'a tabbatar da hakan sai ta 'Private investigation'.

Saboda haka zaka b'ad da kamannika sannan kaje makarantar da yake a matsayin d'alibi, kabi dukkan wasu hanyoyin da zai amince da kai a harkokinsa yadda zaka sami enough evidence d'in da zamu iya tunkararsa, daga nan sai ka dawo kotu ayi handling case d'in."

Saurararsa kawai yake yi amma kwakwalwarsa ta gagara saita maganganun akan layi d'aya, yaje wata makaranta a matsayin d'alibi? ta yaya hakan zai yiwu? ta yaya zai rage shekarunsa? me yasa ma sai shi d'in?

"Saboda kaine mai k'ananan shekaru duk cikin ma'aikatar nan kuma kai ne kad'ai baka tab'a magana da media ba ba ka fara aiki bada dad'ewa ba, babu wanda ya sanka sosai, sannan akwai wanda zai kula da harkar kammaninka a gefe guda, shi zai saita ka akan duk abinda zaka bi ka koma irin yanayin d'aliban makarantar."

Bai yarda da zancen ko kad'an ba, don? ya riga ya san su waye suka yi masa cunen wannan aikin, amma kamar yadda shugaban ya fad'a ne a farko ba yadda ya iya dole ne ya amsa, saboda haka ya gyad'a kansa sannan yace.'

"Na fahimta kuma zanyi dukkan k'ok'arina ranka ya dad'e babu matsala, a bani files d'in da kuma sauran abubuwan da zan buk'ata."

Watak'ila ya fahimci cewa dauriya kawai yayi ya fad'i hakan, don maimakon ya amsa sai ya kira sunansa da wani irin amo? mai jan hankali.

"Yes sir."

Ya amsa shima cikin malalaciyar muryarsa.

"Idan har kayi nasara a wannan case d'in, na tabbatar maka ni da hannuna zan yi signing cewa a baka leave na shekara guda."

Sai ya d'ago da fuskarsa sosai ya kalle shi, da gaske yake zai nema masa hutu har na tsawon shekara guda? a hankali yaji wani abu kamar sabon k'arfi da kuma son case d'in ya gifta a zuciyarsa, yaji cewa dama zai iya gama aikin a cikin 'yan kwanaki kawai!

"Amma akwai wani hanzari ba gudu ba Steve, mutum da zaka yi binciken akansa, yana da tsananin k'in wannan addinin na musulunci, saboda haka abinda zaka fara yi shine had'a k'ungiyar da zata dinga sukar wannan addinin, ta nan zai fara lura da kai bayan ka shiga k'ungiyarsa ta kwallon k'afa sannan..."

Adam bai san zancen da ya cigaba da yi bayan ya fad'i cewa sai ya zama mai sukar musulunci ba, ubangiji ya sani shi BA MUSULMI bane amma musulunci bai tab'a damunsa ba don ya san abubuwa da yawa game dashi, kuma yana ji a jikinsa cewa ba zai so ya zama mai takurawa mabiyansa ba.

Sai dai mafitar da yake nemarwa kansa tafi k'arfin wannan a lokacin, saboda haka daga wannan lokacin yabi umarninsu ya aske gemu da sajensa, ya barbaza gashinsa da kullum yake a kwance sannan ya shiga bin duk wata hanya da mutumin da aka d'auko ke nuna masa yadda zai koma yaro matashi mai irin shekarun samarin makarantar.

Daga wannan lokacin kuma, k'addarar rayuwarsa ta had'u ta kanannad'e data Fadeelah!

***

"Deelah, saura wad'annan plates d'in na can sama."

Mami ta fad'a lokacin da Fadeelah ta taka can saman kata tana mik'o mata kayayyakin da suka dad'e basu yi amfani dasu ba, kayayyakin data rasa meye amfanin d'ebo sun da ake yi.

Suna kitchen ne gabad'ayansu a ranar Asabar, ita tana d'ebo kayayyakin, Mami kuma tana ware wad'ansu sannan ta mik'awa Zahra dake bakin sink ta shiga wankewa.

Beeem!

Wayarta dake ajiye daga gefen k'afarta akan durowar data taka tayi k'ara alamun shigowar message, ta sunkuyo da kanta daga tsayen sanda k'arfin ganin gilashin idonta ya nuna mata d'an k'aramin hoton fuskar Al'ameen da kuma sak'onsa a gefe.

Dan Allah ki gaya min baki yi fushi ba, I'm so sorry sai yanzu naga message d'inki wallahi.

Tayi murmushi kad'an sannan ta d'aga kanta ta cigaba janyo wasu kofuna, ta tashi ne da safe taga sak'onsa na mata barka da safiya, bayan ta gama breakfast ta tura masa da cewar ta gode ya weekend d'insa? bata ga reply d'insa ba sai yanzu kusan k'arfe d'aya na rana, ta san cewar a yadda ta tambayar ba wai dole ne ya turo mata da amsa ba, amma haka kurum taji zuciyarta ta d'an damu, ta dinga kallon wayarta da jiran message d'insa a duk abun da take yi, har sai da ta kai duk bayan minti d'aya sai tayi bud'e ta, ta duba.

Beeem!

Wani message d'in ya sake shigowa, ta sunkuya fuskarta da sauri.

Please ki min magana mana, I'm sorrryyy!

Wani dad'i ya ratsa ta a take.

"Ga wani green kwali can na toaster mik'o shi."

Mami ta katse tunanin dake shirin faruwa akanta.

"Mami dan Allah kar kice shima wanke shi za'ayi, seriously na gaji Allah."

Zahra ta fad'a tana zare idonta akan kwalin, daga gefen idanun Fadeelah tana ganin yadda Mamin ta gallara mata harara.

"Zaki yi min shiru anan ko kuwa, yaushe rabonki da wanke plates a gidan nan."

Beeem!

K'arar wani message d'in.

Da gaske fushi kika yi?

"Jawo kwalin mana deelah, a hankali."

Sai ta d'aga kanta ta shiga k'ok'arin d'aukowa.

Beeem!

Memory loss girl, you there?

Beeem!

Ki min magana.

Beeem!

Babe?

Sai ta sunkuyo gabad'aya sanda ta mik'awa Mami kwalin, hannunta duk k'ura ta d'auki wayar, Idanunta suka manne akan sak'onsa na k'arshe... *Babe* Ya salam ya Allah! ita fa ya kira da haka, taji wani irin dad'in da bata san dalilinsa ba ya shiga ratsata.

Beeem!

Wani sak'on ya k'aru akan na k'asa.

In kira ki?

Sai ta shiga danna keybord d'in dake k'asa da sauri.

A'a gani nan.

Sai kuma ta k'ara da...

Ina wani aikin ne shi yasa kaji shiru.

Beeem!

You just save a life!

Ta cije k'asan lebb'enta da k'arfi jin hakan.

Beeem!

Kiyi hak'uri, naje wani interview ne shi yasa ban amsa miki da wuri ba.

Sai ta rubuta k'arya irin ta kowacce Mace.

Ba komai fa, ni na manta ma da text d'in.

Beeem!

Aikin me kike yi?

Kitchen.

Beeem!

Mrs chef! hannunki mai albarka ne, shi yasa tun daga nan, naji fingers d'inki na k'amshin curry.

Ba girki nake ba Mr. predictor, gyara ne.

Beeem!

Yayi kyau, na fara koya miki.

Me fa?

Beeem!

The pet names, gashi nima kin fara saka mun suna, wa ya san a ina zamu tsaya...

Murmushinta yayi k'arfin da ya kusan zama dariya.

"Fadeelah, mik'e ki mik'o min kwandon can na gefe."

Mami ta dawo da ita cikin zagayen duniyar da suke daga wadda Al'ameen ke neman kai zuciyarta.

A wannan ranar, komai ya k'ara kala a idanun Fadeelah, duniyar tayi wani haske da kyalli, iska tayi sanyi, korayen bishiyun unguwarsu suka k'ara kyau a ganinta, ta cika da wani irin nishad'in da take ganin kowa ma irinsa yake ji duk saboda zuciyarta da yatsun hannunta na tare da Al'ameen a cikin wayarta.

****

Washegari lahadi, da daddare bayan sun gama cin abincin dare, Daddy ya tara su a falo gabad'aya, ya shaida musu wani abu da basu tab'a zato da tsammani ba, cewar ya nemi aiki a wani asibiti dake Nigeria garin Abuja, (Garinsu Mami) don abubuwa sunyi masa yawa anan ba zai iya affording komai ba, don haka su taya shi da addu'a zuwa wani watan yake sa ran samun bayani daga wajensu.

A lokaci d'aya kwakwalwar Fadeelah ta gaya mata cewar wannan shawarar ta Mami ce, don ba tun yau ba ta fahimci tana zaman cikin turawan nan ne kawai saboda nauyin igiyar aure, amma tunaninta da zancenta a kullum yana mahaifarta, shi yasa tayi amfani da wannan damar ta lallab'a Daddy ya nemi aiki a Nigeria inda take da tabbacin zai samu don Nigeria ba kamar Turai bace da likitoci masu fasaha irin Daddy suka yawaita.

Sai a sannan ta k'ara fahimtar manufar Mami na rage kayan gidan, tunda sun kusa tashi meye amfanin ajiyarsu.

Kamar yadda Iman ta cika gidan da murna wannan daren haka itama nata tunanin ke ta tsallen murna saboda tana ganin kamar komawa Nigeria, zai tallafa wajen warkar da ciwonta da wuri, idan har tana cikin kewayen da zata dinga ganin abubuwan da suka shafi rayuwarta ta baya.

Zahra ce kad'ai taga alamun bata yi farin ciki ko b'acin rai da zancen ba, ita ta tunanin yadda zata siya make-up kit da wasu inner wears da ta gani online take. Amma Farouk ya damu sosai da tunanin zai rabu da abokansa da ya riga ya saba dasu.

A lokacin da tazo kwanciya text d'in Al'ameen na Goodnight ya nuna tar! akan screen d'in wayarta, sai taji kamar wani b'angare na zuciyarta yana fad'a mata ne cewa in har ta koma Nigeria, zata tafi ne ta barshi anan... ta tafi da b'arin zuciya guda d'aya!

Saboda haka a cikin baccinta tayi wani irin mafarki mai d'auke da abubuwa kala-kala! wanda muhimmi shine akwai Al'ameen a cikinsa sai dai d'auke da muryar Adam, ko yaya bud'e baki yayi magana maimakon muryarsa sai taji wannan malalaciyar muryar ta Adam kamar tana busawa ne a hankali cikin kunnenta.

***
*BAYAN NA MUTU!*

?AYSHA SHAFI'EE

*10*

*(&_&)*

A cikin kwanakin da Mami ke lissafawa na ragowar lokacin daya rage musu a k'asar turai, abubuwa suka cigaba da gudana bi-da-bi, sababbi da kuma al'amuran yau da kullum na rayuwa. Daga cikin sababbin akwai wata irin shak'uwa mai k'arfi data shiga tsakanin Al'ameen da Fadeelah, har ya zamana cewa babu ranar banza da zasu shafe awa biyar basu ji lafiyar junansu ba ta hanyar waya ko chatting d'in da hannunsu ke mak'ale akai.

Wani abu ne da ita kanta Fadeelan bata san sanda ta jefa kanta a ciki ba, ko kuma ace ta bari Al'ameen din ya jata don a sati uku kad'ai yasa tana jin kamar ta sanshi ne tsawon shekaru uku ne, tana jinsa kamar wani aboki ko d'anuwanta namiji data rasa a baya.

Hatta Mami ta lura sosai da canjawar Fadeelah amma tunaninta bai tab'a kawo mata cewa wani abu ne tsakaninta da Al'ameen ba duk kuwa da yawan zuwa gidan da yake yi a cikin kwanakin bayan, tarin zirga-zirga da d'awainiyar dake kansa.

A gefe guda kuma karatunta da Adam yana cigaba da gudana?ta hanyar bi da dukkan abubuwan data lissafa masa daki-daki. Wani abun ma sai taga kamar wasa ne ko shirme, sai ana cikin yi idan ta fara gane lissafin, sannan ta fahimci yayi ma'ana.

Ranar da suka zo kan inda ta rubuta
hobby d'inta na sauraren alqur'ani, shiru kawai tayi tana kallon yadda ya saita MP3 d'in da ya siyo kafin ya ware sassanyar volume d'im k'irar sheikh Mahir a cikin library d'in, sannan suka fara topic na goma sha uku a lissafinsu, kuma har suka kai k'arshe karatun bai fasa rangad'owa ba.

Abinda ya d'aure mata kai game dashi kenan, idan har zai iya sauraren alqur'ani na tsawon awa d'aya, me yasa a baya zai shiga cikin masu yad'a b'atanci akan addinin alqur'anin?

Bayan haka kuma, zuciyarta ta gano wani b'angare daga cikin halinsa a kwanaki biyar na kowanne sati da take shafe awa guda tare dashi, ta fahimci cewar yana da sauk'in hali ba kamar yadda take hangensa a baya ba, saboda duk irin maganganun da take gaya masa basa tab'a b'ata ransa sannan duk abinda tace in dai ya duba yaga hakan ne, to ba musu zaiyi... sai dai in har ba daidai bane to bama zai saurare ta ba zai bi hanyarsa ne, wanda sai yayin kuma zata ga cewa nasan ne daidai.

"Zan iya tambayarka wani abu?"

Ta tambaye shi a wata rana bayan sun gama karatun, A lokacin saura topics uku kwata-kwata su gama guda ashirin da biyun da zasu yi, don yadda kwakwalwarta ke ganewa a yanzu yasa suke yin sauri sosai, dama ya fad'a mata a baya...

... sauran karatun abu mai sauki ne da zamu iya gama shi in har ba matsalar.

Maimakon ya amsa sai ya juyo kawai ya kalle ta da lumsassun idanunsa, sannan ya kalli gefe kad'an, ba tun yau ba ta fahimci cewa bai fiye son kallon idanunta ba akan dalilin da bata san shi ba. Yanayin nasa ya nuna alamun yana saurarenta ne, don haka tace.

"Tambayar bata danganci karatun nan ba."

Yatsanta d'aya ya nuna paper da suka gama kacaccalata da lissafi.

"Kar ki damu ina jinki."

Ta d'aga kanta game da had'iye yawu kad'an sannan tace.

"Meye tunaninka game da addinina?"

Sakan d'aya, biyu, uku, hud'u... kamar bai ji abinda tace ba, kafin ya motsa kad'an sannan ya dawo da idonsa kanta.

"Me yasa kika tambaya?"

A yanzu ta riga ta zaba da lazy muryarsa don haka kai tsaye tace.

"Saboda tun da ka shigo makarantar nan, kana d'aya daga cikin masu yad'a b'atanci game dashi, har zanga-zanga kuka had'a kan a hana mu zuwa da hijaab makaranta, dalilin da yasa na..."

Sai kuma tayi shiru hannunta da take alama wajen bayanin ya mak'ale a iska.

Adam ya sake lumshe idonsa a hankali yana kallon nata idanunta da a kullum yake jin kamar suna zuk'e k'arfin jikinsa ne duk sanda yake tare da ita, ko bata k'arasa ba, ya riga ya san me zata fad'a kuma itama ta san ya sani, ya gyara zamansa kad'an sannan yace.

"Abinda nake yi a makarantar nan wani abu ne da ya zama dole na ba wai don ra'ayi ba ko saboda ina da ak'idar hakan, kuma daga lokacin da zan k'arasa aikin dana keyi, zan barshi ne har abada.

Saboda haka addininki bai tab'a damuna ba leelah, don na yarda cewa a duniyar nan kowa yana da damar da zai bautawa ubangijinsa ta irin sigar da yaga dama, abu muhimmi shine mu duk d'in bayinsa ne kuma akwai ranar da zamu koma gare shi da adadin tawakkalin dake zuciyoyinmu."

Ta fahimci k'arshen zancen amma bata fahimci farkon ba wanda da alama personal problem d'insa ne, saboda haka tace.

"Abinda ka fad'a kusan haka ne, mu duk bayin Allah ne kuma zamu koma gare shi watarana da adadin Imanin dake zuciyarmu, sai dai ba ta kowace hanya ya kamata mu bauta masa ba. In ma kalli wannan Maths d'in da muke yi ka san ba ta kowacce hanya muke binsa ba, akwai tsararriyar hanyar da dole sai ka bita sannan zaka yi daidai, ni ada ai wata hanyar nake bi daban inyi lissafina kuma ya tafi ba daidai ba, sai da na had'u da kai sannan kake d'ora ni kan hanyar da take daidai.

Kamar haka bauta ga Allah ma yake, akwai tsararriyar hanyar da ubangiji ya turo manzanninsa su nuna mana don mu bauta masa a daidai, ba sai ranar da zamu koma gare shi sannan muga cewar mun b'ace hanya ne kamar yadda nake yi a lissafina na da ba, sanda zan d'auko hanya daidai, sai daga baya in kauce in tafi wani shirmen daban.

Saboda haka yadda Mr. Hawkins ya aiko ka don ka nuna min yadda ake lissafin nan daidai, kamar haka ne Allah yake aiko manzanninsa don su nuna mana hanyar bauta masa daidai, don idan muka ce zamu bi kowacce hanya zamu b'ata ne."

"Me yasa to kuke ganin musulunci ya zama shine hanyar daidai a cikin kowanne?"

"Saboda tarin dalilai da yawa, a cikin alqur'anin da muka gama ji yanzu da kuma sauran litattafan, har da Bible d'in da kuke..."

"Ni ba christian bane." ya katse ta tun kafin ta k'arasa, sai ta d'ago sosai ta kalle shi, idanunta cike da mamaki.

"Bani da addini." ya fad'a mata amsar da bata tambaya ba.

Sai ta gyad'a kanta a hankali kafin tace.

"Idan har baka da addini kuma kana da irin wannan tunanin akan musulunci, na yarda cewa kai ba kafiri bane gabad'aya, kana wani mataki ne da k'okorinka zai iya tsallako da kai hanyar gaskiya."

Da alama maganar ta bud'e wani b'angare na kwakwalwarsa kuma ta saka shi tunani, irin tunanin da baya son yi a gabanta, saboda da sauri ya kawar da kansa sannan ya bud'e jakarsa ya zaro wayarsa.

"Lokacin mu ya cika leelah, sai gobe kenan?"

Ta d'aga kanta a hankali sannan ta tattara kayanta ta cusa a jaka ta mik'e tsaye, shima ya mik'e.

"Sai gobe?" ya sake tambaya a hankali, itama ta sake d'aga kai kawai sannan ta nemi hanyar k'ofa.

Kafin ta isa gate d'in makarantar, motarsa ta tsaya a gefenta, ya sauke glass d'in sannan ya sunkuyo da kansa kad'an.

"Zan iya kai ki gida?"

Ta matse hannun jakar a jikinta sannan tace.

"Ka barshi kawai ina samun mota duk sanda na fita."

An dad'e da wuce lokacin da take gaya masa duk maganar data fito bakinta don ba amfanin yin hakan ga wanda ta fara gani kyautatawarsa a yanzu. A hankali ya maida glass d'insa ya rufe sannan yaja motar ya wuce ta.

Amma daga wannan ranar sai ya zama kamar tayin yana d'aya daga cikin karatunsu ne, a kowacce rana baya sun fito zai tambaya in zai iya kaita gida ita kuma ta tankwab'e hakan.

Sannan a kowacce wucewar rana da fitowar wata, zuciyarta na k'ara bude wasu kofofin ne da take fahimtar halayensa masu kyau, hirar addini ma sai ta sami gurbi a lokacinsu, sau da yawa shi zai fara tambayarta wani abun da zata yi ta bashi iya amsar data sani tana kuma kawo masa banbanci musulunci da sauran addinan, har ta kai in ya koma gida zai duba wani abun a yanar gizo yazo ya nuna mata.

Har ta kai hira tsakaninsu ta zama ba wani abu sabo ba, har ta kai shashashar zuciyarta ta fara rage yawan duhun tsanarsa a cikin zuciyar tata, har ta kai su Melissa ma sun sauko daga tunanin da suke akansa... sannan har ta kai zuciyarta na tuna shi bayan sun rabu har tayi hirarsa a wani waje, hirar yadda ta tsane shi kamar annoba a baya da yadda kirkinsa yazo ya canja tunaninta, sannan hirar data zama sanadin bud'e wani sabon shafi a rayuwarta!

"Wai me yasa kike yawan zancen Adam d'in nan ne Fadeelah?"

Al'ameen ya tambaya ta cikin wayar da suke yi a wani dare. Earpiece ne a kunnenta saboda haka ta danne giyar motar da take driving a cikin game d'in da take yi sannan tace.

"Na gaya maka yana da kirki sosai, ban tab'a tunanin haka halinsa yake a baya ba, sannan baka ga tarin topics d'in dana iya ba saboda shi, kuma yana da son musulunci don ya rage abubuwa da yawa da yake yi a makaranta, yanzu kuma jikina yana bani kamar ta hanya ta zai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login