Showing 138001 words to 141000 words out of 153964 words

Chapter 47 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3808

safe. Ba Sa'id kad'ai ba, hatta Adam sai da ya tsaya kalli tsarin kayan da aka jera a gidan wanda suka k'ara fito da kyan fasalinsa, daga falo, dining area har zuwa kitchen komai cikin kala biyar yake, grey, ash, white, silver da kuma zirin bak'i a wasu wajajen, bai tab'a tunanin cewa mata suna da fasahar da zasu tashi abu mai kyau irin haka ba.

Ya d'an jingina da kujerar falon yana kallon adon wasu k'ananan flowers da aka jera a saman Tv, fatansa d'aya ne a lokacin, ubagiji ya bashi damar da zai iya jan hankalin Fadeelah ta zauna dashi, don rabuwarsu ba mutanen babban gida kad'ai zata shafa ba har da nata iyayen da suka baje kokarinsu wajen gani sun kyautata gidan aurenta haka.

Idonsa ya kai zuwa hanyar shiga d'akunan kwana dake gefe, ya san dole ne Fadeelah tana d'aya daga ciki a yanzu haka, clutching the lip of her veil as his wife, his bride!

Ya lumshe idonsa a hankali, zai so ganinta kwarai amma ya san ba shawara bace yaje wajenta a lokacin.. Don ba lallai ne taso ganin fuskarsa ba a yanzun da saboda shi ta rabu da komai na rayuwarta ta baya.

Said ya fito daga hanyar kitchen a lokacin bayan ya ajiye wasu kayan, sai kawai ya juyo ya mik'a masa ledar kayan cimar daya siyo yace.

"Ka kai mata wannan tana ciki."

Daga haka bai jira amsarsa ba ya wuce shi ya nufi hanyar wajen dining, inda anan corridon shiga d'akinsa yake.

***

*NB*

_*Bani da mallaki akan wakokin dake cikin chapter nan.*_

*BAYAN NA MUTU!*

?AYSHA SHAFI'EE

42

(&_&)

BAYAN SATI BIYU.

Hasken rana ya shigo ta tsakanin wata siririyar hanya a jikin labulen d'akin, a k'aida kamata yayi ta zuge labulen d'umin ranar ya shigo ko ya rage azababben sanyin da tiles d'in k'asa ya d'auka, amma kuma bata son hasken ko kad'an saboda ciwon idonta dake shirin dawowa a dalilin rabuwarta da glass na tsawon lokaci.

..Muhammad ba zaka kyaleta ba? In nazo wajen nan zan zaneka fa?

Fadeelah ta d'an rufe idonta kad'an saboda yadda Mairo ke ihu ta cikin wayar da suke yi tana rabon fad'a tsakanin 'ya'yanta, ta cusa yatsanta cikin barbajajjen gashinta daya baje akan pillow, tashinta kenan a lokacin don wayar Mairon ce ta farkar da ita, ta d'aga kai ta kalli agogon d'akin k'arfe goma na safe amma har su sun tashi suna bidirinsu, ta murza idanunta da tana k'okarin saita ganinta har a lokacin Mairo na sulhu ta cikin wayar.

"Ya salam ya Allah! Ace yaro baya ko magana amma sai tsabar rashin ji... Ita kuma tayi ta masa kuka?" Ta fad'a bayan wani lokaci.

Fadeelah tayi murmushi sannan tace.

"Dan Allah yaushe zaki kawo min ita? Kinga kema sai ki huta."

"Ai ba don next week zasu koma makaranta ba tattaro miki ita zanyi wallahi, amma dai zan tambayi babanta may be tazo miki wani? weekend d'in."

Ta mik'e zaune sannan tace.

"Har naji kamar inzo d'auke ta wallahi."

"Kar ki damu zata zo, kinji kuwa an yankewa Habiba k'afa d'aya?"

Maganar ta daki tunaninta, tace.

"Yaushe?"

"Shekaranjiya Aunty Hassanah take gaya min, wai tun daga cinya don ciwon yaci k'arfinta."

Bata san me zata ce ba don haka tayi shiru kawai, zuwa can kuma ta daure tace.

"Allah ya bata lafiya."

Watakila Mairo ta fahimci halin da zuciyarya ke kokarin fad'awa ne don sai tayi saurin canja zancen da cewa.

"Kin tambaye shi kuwa zuw asibitin?"

Sai ta kifa kanta akan tafin hannunta gashinta ya sunkuyo a barbaje, sannan ta girgiza shi kamar Mairon zata gani. Yau asabar ya kama sati biyu kenan da fara sabuwar rayuwarta ta aure, kuma a cikin wad'annan kwanakin, ta samu wani nutsatstsen hutu da kwanciyar hankalin da har hakan yasa zuciyarta ta fara wankuwa game da abubuwan da suka faru da ita.

Watakila don ta d'an rabu da hayaniya ne kwana biyu saboda tun sanda aka kawo ta babu wanda ya sake zuwar mata, hatta su Aunty Saratu a waya suka yi sallama, kuma ba sai wani ya gaya mata ba ta san su suka tsara hakan don ko kowa ra'ayin kansa ne k'in zuwan da taga su Zahra da suka dawo a cikin satin saboda k'arewar hutun makaranta, amma su d'in ma har yanzu sai a waya kawai take ta fama da kaud'insu.

Wayar da Mamin ta bawa Sa'id ya kawo mata sabuwa a kwalinta, kuma a ranar da suka yi waya ta gaya mata cewa akwai kud'i a account d'inta na banki... tun wannan kud'in data tura mata lokacin bikinta da Al'ameen, a yanzu da aurenta ya koma kan Adam, an samu gudunmawa sosai daga Babban gida da kuma su Aunty Saratu don haka bai fi rabin kud'in aka tab'a ba.

Shi yasa yanzu da idonta ya dame ta da ciwo take son taje asibiti a duba ta kuma ta sake glasess, tana son siyo kayan zane ma sannan tana son taje inda zata siyo wasu 'yan k'anan abubuwa da take buk'ata, amma duk hakan ba zai yiwu ba sai da izinin mijinta. Haka Mairo tace kuma itama ta san baza ta iya fitar ba sai da izininsa.

"Bintu kina jina kuwa?" Muryar Mairo daga cikin wayar ta dawo da ita daga wannan dogon tunanin.

Sai tayi saurin d'ago da kanta sannan ta amsa.

"Na gaya miki ki bari ko zuwa nan da next week ne sai ki tambaye shi tukunna, amma ko gidan Mami kika je yanzu sai ta miki magana."

Gidan Mami. Ta maimaita kalaman a cikin kanta, a da nan take kira da gida, amma yanzu saboda tasirin wasu kalamai da kuma 'yar walima, kalmar 'Gida' a wajenta ta canja daga wajen su Mami zuwa nan... Gidan Adam!

Ta shiga gyara gashinta da yatsun hannunta don Mairo bata san komai game da yadda zaman shirun nan d'in ya fara damunta bane, a yadda kowa ya sani su biyu suke rayuwa a gidan, amma a zahiri ita kad'ai take dabdalarta a cikinsa, don hatta washegarin ranar da aka kawo ta lahadi, Adam bai yini a gidan ba sai dare ta ganshi.

Ita dashi a yanzu kamar wasu makwabta ne kawai dake rayuwa a kusa da juna, ta san dai kullum zasu gaisa idan ya dawo daga aiki ko kuma wani lokacin da safe in zai fita harma ya tambayeta wani abun amma bayan nan bata fiye ganinsa sosai ba, don bata zama a inda zata ganshi d'in ko yana gida, sai dai ta jiyo motsinsa kawai daga nan cikin d'akinta.

Alkawarin daya d'auka yana nan rataye a cikin zuciyarta yana reto, don haka ta zab'i bin wannan hanyar ne saboda tana ganin itace maslaha game da irin zaman da zasu yi, ta yarda in har ta nesanta kanta dashi rabuwarsu zata zo mata sauki a duk ranar daya tsayar zai sallameta. Domin bata so tarihi ya maimaita kansa, wancan karon a makarata kawai suke had'uwa amma data bari zuciyarta ta saba dashi, ba k'aramar wahala tazo tasha ba wajen kewarsa.

Bayan haka kuma akwai wasu banzayen sak'e-sak'e da zuciyarta keyi in har tana gabansa, shi yasa ma dole ta kaucewa ganinsa tun kafin ta makara wajen ceto zuciyar tata. Dad'in da take ji d'aya ne, duk irin sak'e sak'enta bata tab'a tunanin Al'amin ba, don taji nasihar da Mami tayi mata akan hakan shi yasa ta d'auki tunaninsa ta kai zuwa can wani sak'o a zuciyarta kamar yadda take fata shima ya manta da ita ya karb'i zab'in mahaifiyarshi hannu biyu.

Bayan gaisuwa kuma abinda kad'ai ke had'a ta da Adam shine abinci, don a?cikin wancan satin data gaji da kame-kamen abin ci a gidan ne tayi girki ta had'a dashi, kuma wannan ma gani tayi rashin kyautatawa ce k'iri-k'iri ace shi da gidansa da kuma kayan abincin daya kawo amma ta dafa ta barshi da neman na siyarwa, don hatta Awwal d'in da yazo yayi mata siyayya ma shi ya turo shi, saboda haka sai ta k'udirce a ranta cewa zata yi ko don ta samarwa kanta lada kafin damar ta sub'uce mata, tunda Allah ba ruwansa da tsarinsu, a wajensa shi mijinta ne da in ta kyautata masa zata samu ladanta. Kuma taji dad'i da shima ya karb'i hakan a matsayin kyautatawa kawai, baiyi tunanin cewa tana neman cusa kanta ne wajensa ba.

Watak'ila kuma wannan yanayin zaman nasu yana d'aya daga cikin abinda ya dad'a kwantar da hankalinta ta samu nutsuwa a cikin 'yan kwanakin nan. amma kuma yanzu kad'aicin ya fara so ya dameta don haka take son ta d'an fita, kuma ta san in dai ta tambaye shi zai barta, matsalarta kawai shine kowa sai yayi magana in yaji ta fitan, don ga Mairo nan ma ta fara.

Sai ta koma da baya ta sake kwanciya akan gadon sanda Mairo ta cigaba da cewa.

"Bintu abinda nake so ki fahimta shine daga ke har shi wannan shine aurenku na farko, kuma kowa ya san a yadda auren yazo don haka ki bari hankalin mutane ya d'an d'auke daga kanku tukunna, zuwa wani lokaci ba wanda zaice wani abu don kin fita."

Zuwa wani lokaci. shima haka yace mata, zuwa wani lokaci zai rabu da ita, to ta yaya kuwa zata yi ta zama babu abinyi har 'Zuwa wani lokaci?'

Sai dai har ta bud'e baki zata yi magana, ta tsinci k'arar knocking a jikin k'ofar d'akin, babu shiri ta mik'e zaune idanunta d'auke da mamaki.

"Waye?" Tambayar ta fito daga bakinta tun kafin ma ta san ta ma ta fad'a, kuma a take taga wautarta k'arara, waye zai mata knocking da safe in ba wanda suka kwana suka tashi tare ba? To bai tafi aiki ba dama? Sai ta juyo da fuskar wayarta ta kalla, a lokacin wayar da suke yi da Mairo ta katse... Abinda ta gani ya k'ara sawa ta zare idanu, yau asabar! Hutun k'arshen sati! yana gida! Ya salam kwata-kwata ta manta don a wancan k'arshen satin yayi tafiya Katsina ne tsawon kwanaki uku wanda ya had'a har da litinin.

Ba shiri tayi wulli da wayar ta lalubi ribbon akan gadon ta d'aure gashinta, sannan ta jawo hijabin sallarta ta zura, ta kalli fuskarta a mudubi kafin ta wuce bud'e k'ofar, babu kwantsa a idonta amma ta sake murje shi sannan ta kwantar da gashin girarta.

Yana tsaye kuwa sanda ta bud'e k'ofar, sanye cikin farar T-shirt da wando 3-quater, sannan gashin kansa a barbaje, zuciyarta ta matse don rabon da ta ganshi a haka tun lokacin da suna America, wai baya jin sanyi ne? Shima ita d'in yake kallo, sai dai shi ba kallon nazari yake mata ba, kallo ne kamar na wanda ya kama mai laifi, taji zuciyarta ta matso cikin mak'ogwaronta sannan iska tayi mata wuyar shak'a, ko dai tayi masa laifin ne?

"Kin tashi lafiya?" Muryarsa mai zurfi ta gaisheta kafin ta gama tunanin, nata hankalin gaisuwar yazo.

Kunya ta ratsa ta, sai tayi saurin sakin hannun k'ofar sannan ta gaishe shi.

"I'm sorry na tashe ki ne?" Ya furta a hankali cikin sigar damuwa wanda ya cakud'e da taushin muryarsa. Watakila d'azu ta manta bata fad'i cewar muryarsa ma na d'aya daga cikin abinda yasa take k'ok'arin kauce masa ba, don har yanzu duk sanda zai mata magana ji take kamar yana rad'a mata ne a kunne, bata san kuma yaya zata ji ba in har da zai lalubi kunnen nata ne ya rad'a mata. Wata murya a cikin kanta ta rafka salati, kina da hankali kuwa Fadeelah? wane irin tunani kike yi haka alhali yana tsaye a gabanki? amma wata muryar ta kare ta da cewa to meye? Ai ba haramun bane don kinyi wannan tunanin akansa.

A wajen kanta kuma, lallausar muryarsa ta sake maimata mata tambayar da yayi.

"Na tashe ki daga bacci ko?"

Sai tayi saurin girgiza kanta cikin riba biyu, ta bashi amsa kuma ta kad'e wad'ancan muryoyin biyu.

"A'a na tashi dama, kawai dai ban fito bane."

Ta k'ara da cewar.

"Na manta yau saturday, ban san kana gida ba."

"Nima banso na fito dake yanzu ba, wasu ne suka zo wai bak'in ki ne daga mak'ota."

Da turanci yayi maganar, watakila bai san yadda zai fad'i kalmar 'mak'otan' bane don har yanzu hausarsa bata zauna sosai ba don ma dai yana kokari ne, amma wad'anne irin mak'ota ne zasu shigo mata da safe haka? Ta san dai mata biyu dake mak'otaka dasu a gefen gidan sun shigo mata kwanakin baya,? amma yanzu kuma bata san waye ba... Bari dai taje ta gani koma su waye d'in, bari ta fincike kanta daga wannan yanayin mara kyau da take shirin fad'awa, saboda haka ta gyad'a kanta kawai tace bari taje su gaisa, amma maimakon ya bata hanya, sai ya k'ara matsowa dab da ita ya tsaya, hannayensa sunk'e cikin aljihun wandonsa.

"I want to ask you something. (Ina so in tambaye ki wani abu)"

Bata kalle shi ba, amma tana iya jin tsawonsa kamar na dutsen zuma a gabanta, don haka ba shiri zuciyarta ta shiga tsere, me kuma zai ce mata bayan yace bak'i suna jiranta? wani abu yayi girma a cikin mak'ogwaronta saboda tana iya jin tasirin kallon da yake mata a jikinta, hakan yasa ta dunk'ule yatsun k'afarta.

"Me yasa kike guduna?"

Bata san lokacin data saki k'afar tata ba sannan ta d'ago da idonta ta zare su akansa,

Me? Ta ina ina wannan tambayar ta taho? Ya akayi ya gane? Waye ya bashi shawarar ya tambaye ta? Saboda me ma zai tambaye tan?

Sai ta girgiza kanta.

"Ni ba gudunka nake yi ba, ina ganinka kullum, ta yaya zan guje ka."

Kusan gaskiya ta fad'a, don tana da hujjar kare kanta, shi kansa ya sani babu ranar da ba zasu ba kuma inda zai bata dama ma, tsaf zata lissafo masa kowanne kaya daya saka tun bayan tarewarta gidan, a jere ba tare da tsallaken koda rana guda ba. Ta had'iye yawu kad'an tana aikawa zuciyarta kallon mamaki, don ko ita kanta bata san ta rik'e hakan ba sai yanzu.

Ga mamakinta sai yayi murmushi sannan ya gyad'a kansa kamar ya fahimta ko ya yarda da ita kafin yace.

"In kin gama da bak'in naki, akwai maganar da nake son muyi."

Ya k'ara jefa mata wani kallon kafin ya juya ya tafi. Tabi bayansa da kallo sannan ta rufe idanunta alamun Allah ya kawo mata agaji, don bata san wane irin yak'i zata yi da zuciyarta ba in har suka zauna yin maganar.

***

Adam ya lumshe idanunsa sanda yake zaune a wani side falo dake hanyar zuwa kitchen, waya ya gama yi yanzu da abokin aikinsa Nasir akan wani case da suke yi tare, Nasir d'in ya nemi daya shigo ne don su fitar da sakamakon wani sauti da aka tace musu game da shari'ar da suke yi ta wani saurayi daya kashe k'anin mahaifinsa, amma kai tsaye ya shaida masa cewa ba zai iya fitowa ba, don a ko k'ofar gida baya son fita, hutu yake buk'ata irin wanda ya dad'e rabonsa dashi.

Ya kurb'i coffe d'in daya had'a a hankali sannan ya koma da baya ya jingina da kujerar, yau sati biyu kenan da tarewarsu a gidan, kuma a cikin wad'annan kwanakin yana tunanin ya cimma tsarinsa na bawa Fadeelah isashshen lokacin da hankalinta zai kwanta, don a yanzu ya lura fatarta tayi haske?kamar yadda take a baya sannan idanunta sun washe kamar madara, babu wannan d'ashewar, babu firgici a cikinsu balle kuma wani tunani.

Shi yasa a yanzu yake ganin kamar lokaci yayi dashi da ita zasu zauna suyi magana ta fahimta, don ya fara shiga damuwa game da yadda ta kasa sakin jikinta dashi har yanzu, ba abinda ke had'a su sai gaisuwa kawai, daga nan kuma ba zata k'ara cewa komai ba sai in har shi ya tambayeta wani abun, sannan in ba ma gaisuwar ba baya ganinta kwata-kwata, in ta shige d'akinta shi da ita sai gobe kuma. Da farko shima ya taya ta gudar masan ne don kar ya takurata, amma yanzu kuma abin ya fara damunsa.

Gani yake abinda take yi laifinsa ne, tun farko shi ya saka mata wani fatan da yasa har yanzu ta kasa karb'arsa a matsayin mijinta, watak'ila da baiyi mata wannan alkawarin ba da yanzu abubuwa sun fara tafiya daidai tsakaninsu wanda hakan ne fatansa, don baya son a samu b'ullar wata matsala ko yaya take da zata kai ga sanin su Kawu Ibrahim, Shi yasa dole ne ya kawo k'arshen duk wata diramar dake faruwa a zuciyarta kafin ya rasa ta inda zai fara.

Bayan wani lokaci yaji k'arar motsi daga kitchen, hakan ya tabbatar masa cewa bak'in nata sun tafi kenan don haka ya mik'e ya ajiye kofin hannunsa ya nufi can.

A tsaye ya same ta, ta juya baya tana aikinta yayin da kitchen d'in ya gauraye da k'amshi kala-kala, ta canja kayan jikinta zuwa wata doguwar riga kalar yellow mai haske, bai sani ba ko telan da yayi d'inkin bai san awonta bane amma anyi kasan rigar ne yana ja har k'asa wanda ya dad'a fito da kyawun d'inkin, wani abu ya wuce cikin mak'ogwaronsa don tayi masa kyau gaskiya, musamman kalar kayan da suka fito tar a cikin kalolin baki da ruwan toka na kitchen d'in, sai ya zama kamar an saka kala ne akanta ita kad'ai.

Allah ya sani duk da ba wani sabo suka yi ba har yanzu, amma yana jin dad'in zama da ita don ya saba da rayuwa a gidansa yanzu, ya yarda da duk maganar da malaminsa ya gaya masa a ranar da Sa'id ya fara shaida masa cewa yayi aure.

"... aure rahma ne Adam, yana da darajoji mai tarin yawa, kai kanka a yanzu zaka fi jin kanka ka zama mutum kuma zaka sami nutsuwa fiye da kowanne lokaci, sannan ko a idanun Al'umma girmanka sai ya ninku akan da..."

Ya yarda da hakan saboda yanzu ko su Sa'id girman da suke bashi daban ne, sannan shi kansa ya kwana biyu rabonsa da zuwa wajensu, a kullum ya tashi daga aiki tunaninsa na kan hanyar komawa gidansa ne kawai, inda zai dawo ya tarar da ita kuma ya kwanta da tunanin cewa wad'annan idanun da yake bacci dasu kullum, a yanzu suna 'yan taku nesa dashi ne kawai.

Gashi kuma ya fara sabawa da cin abincinta,?kalolin girkinta dake had'ewa tsakanin American dishes da kuma na nan Nigeria, watakila kuma zuciyarsa na d'okin ganinta ma a kullum, ganin simple shigarta mai kyau kamar yanayin kayan gidan, watarana ya kanji kamar ya gaya mata cewa tayi kyau! Amma in ya fad'i hakan,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login