Showing 15001 words to 18000 words out of 153964 words

Chapter 6 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3769

don basa son kowacce irin alaqa ta had'a su dashi, kuma itama ta rantse in har ta hanyarsa zata iya sanin maths sai dai ta mutu a dak'ik'iya.

Toh amma meye amfanin rantsuwarta a yanzu? meye amfanin rantsuwar data san zata cutar dasu Mami ne, tunda suna iya bakin kokarinsu wajen ganin sun bata ilimin da bai zama dolensu akanta ba, ita kuma tana gefe tana shirin watsa musu k'asar kunya a ido koma abinda yafi hakan, tunda ya zasu ji a lokacin da aka gaya musu kud'in maimata aji zasu k'ara biya mata har na tsawon shekara daya?

Sai kawai ta kwanta akan gadon ta dukunkune jikinta, zuciyarta na gaya mata cewa kar ta sake ta soma bin shawarar da kwakwalwarta ke bata don baza su iya jurewa ba, ba zasu iya? jurewa mu'amala da mutumin da suka tsana ba, amma sai kwakwalwarta ta hasko mata ranar da za'a kafe sunanta b'aro-b'aro a jerin masu maimaita aji, watakila ma sunanta kad'ai za'a saka... Toh taya zata iya kallon idanun Daddy a ranar? kuma ta yaya zata iya cigaba da sakewa da Mami tare da tambarin wannan laifin a fuskarta?

Sai tayi k'arfin hali ta mik'e ta jawo jakarta, a aljihun gefe ta rab'a paper da Mr. Hawkins ya bata, wani waje da ba zai rik'eta sosai ba, amma duk da haka a lokacin sai da zuciyarta ya gaya mata cewar jakar ta k'ara nauyi. A hankali ta zaro ta, idonta ya manne akan number da kuma sunan dake jiki, Sunan wanda zuciyarta ta tsana fiye da duk wata halitta mai numfashi a doron k'asa, sai gashi yanzu a cikin hankalinta tana shirin kai kanta gare shi, bisa dalilin data kira da sunan abinda yafi kaddara!

A hankali ta kwafe number cikin dial log na wayarta, sannan ta tsira mata ido kamar tana so ta tsince guda d'aya daga ciki ko hakan zaisa kiran ya tafi cikin wata lambar daban, kuma mai lambar ya amince shine mai koya matan.

Me su Romilda zasu ce in suka ji me take shirin yi? wane irin tunani zasu yi akanta?? zuciyarta ta rad'a mata amma sai kwakwalwarta ta goge hakan, Ba zata iya raunana fatan su Mami akanta ba.

Bayan kusan rabin awa cikin muhawara kwakwalwarta tayi nasara. Hannunta yayi dialling number.

Sai dai kiran ba shiga ba ya katse, ta sake dannawa kusan sau uku amma ya dinga katsewa a hanya kafin ya kai ga shiga, watakila itama wayar tata bata goyon bayan wannan al'amarin ne.

Kiyi hakuri ba yadda zamu yi ne, ba zan iya b'ata ran su Mami ba.

Ta ayyana tana kallon screen d'in, kamar kuwa taji abinda tace wannan karon sai kiran ya shiga a take, kuma k'ararsa ya shiga bugawa tare dana zuciyarta, kamar a irin lokacin da dalibi ke kokarin binciko sakamakon jarabawarsa.

"Heelllooo..."

Tsigar jikinta ta mik'e yar! har zuwa tafin k'afarta, Muryarsa a lalace take kamar wanda ya amsa cikin bacci, ta kalli agogon gefen gadonta, karfe tara da rabi... ta yaya mutum zaiyi nisan bacci a wannan lokacin?

"Mhmmmm...."

Muryar ta sake fad'a a hankali jin anyi shiru, wannan karon sai da ta matsar da wayar kad'an don ji tayi kamar numfashinsa zai busa ne a cikin kunnenta.

"Naga kamar bacci kake yi, wani lokacin."

Ta daure ta fad'a sai dai bata sauke wayar k'asa ba.

"Nahh, ina jinki." Ya fad'a cikin wani lallausan turancin daya kwanta a sautinsa.

Taji kamar ta katse kiran kawai amma muryar Mr. Hawkins ta amsa a cikin kanta.

...ina baki shawara gwara ku fara da wuri, don jarabawa na kan hanya.

Ta san in har bata yi maganar a sannan ba, zata k'ara b'ata lokacinta ne don a yanzu haka ma an shafe kusan kwana uku da Mr. Hawkins ya mata maganar.

"Na tashi..." Muryarsa ta sake fad'a mata a hankali cikin speaker wayar kamar wanda bai gama wartsakewa ba, taji kamar taja tsaki amma sai wata zuciyar ta gargad'e ta. Ba yanzu ya kamata ta fara kwance d'aurin data tanada ba.

"Sunana Fadeelah Malik."

Ta fad'a kuma tayi shiru shima yayi shiru, me yasa zata yi shiru kamar tana jira ne yace wani abu game da sunan.

"Nice wadda Mr. Hawkins yace zamu.." Sai tayi saurin canja hakan.

"... zaka min lesson na Maths."

Shiru ya biyo baya sannan muyarsa ta sake?fitowa a hankali.

"Oh... Yarinyar!." Ya? fad'a alamun kwakwalwarsa ta tuna masa.

"Na gane, zan kiraki gobe a makaran..."

Dib! ta kashe wayarta.Ta fahimci abinda yake nufi don haka bata ga amfanin sai ya kai k'arshe ba. Ta wullar da wayar gefe sannan ta jawo jotter ta, zuciyarta cike da nauyi ta rubuta.

Alhamis, 9:36 pm.

Na karya alkawari, saboda sadaukarwa.

Ta mik'e ta shiga toilet, tayi alwala sannan tayi sallar Isha'i, tana idarwa ta nufi wajen alon zanenta, kusan wata guda kenan zanen dake kai bata k'arasa shi ba. Zanen gida ne a cikin daji mai yawan bishiyu da shuke-shuken fulawoyi, a gabansa akwai wata fadama kwantacciya, zanen yayi kama da lokacin da akayi ruwa aka d'auke, Daga can gefe akwai wajen da babu komai, ta rasa a baya me tayi tunanin zanawa a wajen don yana da fad'i sosai amma ta kasa tunawa, sai kawai ta yanke shawarar zana dutse wanda zai zama kamar ana hango shi daga can nesa ne.

Ta d'auko pallette (Abin zuba kaloli) ta cakud'a Acrylic kalolinta akansa sannan ta d'auko sababbin brushes, tunda wanda tayi amfani dasu sun dad'e a bushewa bata wanke ba. Ta saka siririn glasses d'inta sannan ta maida hankalinta kacokam! wajen zana hoton dake cikin kanta.

Zane, wani abu ne da ta tsinci hannunta nayi tun farkon sabuwar rayuwarta, bata da sanin cewa tayi shi a baya ne ko kuma taga ana ayin, ta san dai kawai ta samu hannunta da son zana taswirar abubuwa da yawa wanda take son fito dasu daga cikin kanta. Dalilin da yasa Daddy ya kaita wata painting school ta tsawon wata biyu kenan kafin shigarta makaranta, kuma a yanzu haka ta sayar da zanenta guda uku wad'anda aka kai kantin Daddyn, Grocery store d'in da ya bud'e a gaba dasu kad'an.

"Nayi zaton kince fad'uwar rana zaki zana anan wajen."

Muryar Zahra ta fad'a tsaye daga step d'in k'ofar d'akin, a lokacin tayi kusan minti talatin tana zana rabin dutsen. Ta juyo ta kalle ta sannan ta dawo da ganinta kan zanen, kuma hakane, faduwar rana shine yayi daidai a wajen tunda yanayin kamar na yamma ne.

"Wallahi na manta ne, bari in gyara."

"A'a ki barshi.. Dutsen ma yayi. Kinga sai a kasa gane wane irin yanayi ne a wajen, yamma ko safiya?"

Da ta sake kallo kuma sai ta ga hakan ne, ta girgiza kanta da murmushi tace.

"Rana ta farko da kika fadi abu mai amfani."

"Ko kuma rana ta farko da kika bar zuciyarki ta fahimce ni ba."

Sai tayi murmushi kawai ta juya ta cigaba da zanenta.

***

"Da gaske kike?"

Romilda da Melissa suka had'a baki wajen fad'a, idanunsu a zare da tsantsar mamaki, Fadeelah ta damk'e rigarta ta baya yadda baza su gani ba.

"Da gaske nake, ba yadda zanyi bani da wani zab'i bayan hakan, ba zan iya b'ata ran su Mami ba."

Melissa tayi tagumi da duka hannayenta biyu sannan tace.

"Bayan duk k'okarin da muka yi don kar mu shiga hanyar mutanen nan, sai a yanzu da muke ko kike ganin kin kusa cimma hakan zaki b'ata komai?"

Romilda ta girgiza kanta, cikin turancinta mai cakud'e da spanish tace.

"Kuma kin san munce zamu taya ki samo wani solution d'in bayan hakan koh? me yasa zaki yanke hukunci a lokaci d'aya, me ya canja ra'ayinki haka?"

"Duk abinda zamu samo ba zai wuce abu guda uku ba, na farko ko ku kuce zaku koya min, wanda wasu topics d'in kuma baku kware akansu ba, ko kuma in shiga summer classes da hutu, in zaku fahimta kuma duk abu d'aya ne da yanzun... kwakwalwata bata iya gane lissafi a cikin mutane, hanya ta k'arshe da zamu iya samowa shine muce zamu nemi wani a cikin makarantar nan ya koya min, amma ku kalla ku gani..."

Ta fad'a tana nuna wata poster a gefensu dake nuna b'atanci ga musulmai.

"Da wannan abin wa kuke tunanin zai b'ata lokacinsa don koya min karatu?"

Gabad'ayansu suka yi shiru cikin tunani kafin Melissa ta kalle ta tace.

"Kafin ki kira Adam a jiyan, kwakwalwarki tayi tunanin me yasa shi d'in ya yarda zai koya miki bayan yana daga cikin masu yad'a irin wannan abubuwan?"

Tunanin hakan ya dirar mata a lokaci d'aya, tabbas yaci ace tayi wannan hangen... Me yasa duk fad'in makarantar shi kadai kaddara ta tsamo a matsayin wanda zai koya mata karatu? ita d'in da bata ko kai shekara guda a makarantar ba kuma ba kowa ne ya kai ga saninta ba... ko dai hakan yana daga cikin wani shirinsu ne? amma kuma sai tayi tunanin wane shiri zasu yi akanta ita kad'ai sab'anin sauran musulman dake makarantar. Fuskarta ta nuna damuwa amma tayi saurin ture ta gefe, a yanzu ta riga ta saka kanta cewa zata yin kuma bata son ta bawa su Melissa damar da zasu raunana dauriyarta.

"Ban sani ba.." Ta fad'a tana d'aga kafad'unta, "..watakila don bai san ko ni wacece bace, kuma ina fatan in ya sanin yace ya fasa, Sai Mr. Hawkins ya samo wani."

A haka hirarsu ta cigaba tana kare duk wata hanya da suke kawowa wajen sukar shawarar data yanke, ita kanta har mamaki tayi na yadda bakinta yake furta yak'ini akan abin, bayan can cikin zuciyarta fanko ne.

A lokacin da period ta uku ta shiga, Fadeelah ta samu kanta da yawan kallon screen d'in wayarta haka kawai, ta rasa gane dalilin da zai sata yin hakan, amma sai zuciyarta ta kare ta da cewar don wayarta na silent ne bata son tayi missing kiransa lokaci ya dad'a tafiya.

Tare take yin AP Biology da Melissa,? saboda haka tare suka tafi Ajin wanda ya kasance period na hudu a ranar,? kamar kowanne class d'in Biology, science lab ne mai d'auke sinks da kuma kujeru a tsakani. Mrs Rease ta shigo rik'e da folder ta a hannu, dogon gashinta a yau nannad'e cikin bun.

"Good morning class, Today we will..."

Muryarta ta cigaba da karad'e ajin tsawon period d'in, kuma duk da cewa hankalin Fadeelah a rabe yake gida biyu ba abinda bata fahimta a topic d'in ba, Biology yana d'aya daga cikin subjects d'in da take mutuk'ar so kuma take ganewa, watakila kuma don malamar ta iya koyarwa ne kamar yadda kowa ke fad'i.

Daidai lokacin da aka kad'a kararrawar gama class d'in, daidai lokacin kararrawar vibration na wayarta ya kad'a, wayar ta shiga motsi akan table d'in gabanta yayin da Number jiya da k'arfe tara da rabi ta nu??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na akan screen d'inta.

A hankali ta d'aga ta kara a kunnenta sanda hayaniyar ajin ta ragu saboda fita da ake tayi.

"Hellloo..."

Sai ta matsar da wayar kad'an saboda yadda muryar ta sulale cikin kunnenta, me ya same shi ne wai? yau ma baccin yake yi?"

"Kin shigo makaranta?" Nadadden turancinsa ya tambaya kafin ta iya cewa wani abin.

"Eh." ta amsa a takaice.

"Okay." Ya fad'a sannan kiran ya katse. Ta sauke wayar a hankali tana kallon yadda kiran ya b'ace daga fuskar wayar.

"Kin san cewa daga yanzu kin sa kanki cikin masifa ko?"

Melissa ta fad'a daga gefenta, sai ta gyad'a kanta a hankali ba tare da ta kalleta ba.

"Na sani."

***

Melissa tana da wani class d'in, saboda haka ita da Romilda ne kad'ai a cafteria suna cin abinci, a hankali take tauna abincinta tana saurarar mitar da Romildan keta nanatawa akan zancen Adam.

Wayarta tayi k'ara alamun shigowar sak'o.

Ki same ni a bayan makaranta.

Alhamdlilah, ta ayyana a ranta, in har baya son a gansu tare hakan yayi mata daidai, don itama abu na k'arshe da zata so a rayuwarta shine wani ya san da alaqar dake shirin faruwa a tsakaninsu. A hankali hannayenta suka shiga cikin message d'in, ta rubuta.

I'm a freshman (ni sabuwar d'aliba ce) ba'a barinmu mu fita bayan makaranta.

Sakan d'aya, wani k'arar message d'in ya shigo.

Ki same ni a wajen store.

Wata mab'oyar, yayi daidai! abu na farko da baza su sami matsala akansa ba kenan. Sai da ta gama cin abincinta tsaf! sannan tace da Romilda zata je lokarta, ta fad'i hakan ne saboda bakinta ba zai iya furta cewa zata je wajen Adam ne ba.

A jikin wata k'ofa dake fuskantar Store d'in ta hange shi, yana tsaye ya juya bayansa yana kallon can bangon ginin da baya b'ullewa. Zuciyarta ta dagule a take, ta lumshe idanunta sannan ta kalli k'afafunta dake tafiya, k'arya zata yiwa kanta in har tace wannan ba shine abu mafi muni daya tab'a faruwa da ita tun da ta fara sabuwar rayuwarta ba.

Ya juyo da fuskarsa jin takunta.

"Kin san dad'ewar da nayi ina jiranki?"

Sai yanzu ta tabbatarwa kanta cewa a baya bata tab'a jin muryasa ba, don yanzu ma bata canja ba, kamar yadda taji ta a waya ne ta zata bacci yake... a lalace kamar baya cikin haiyacinsa sosai.

Ta tsuke bakinta kawai ba tare da ta amsa ba, idanunta na k'asa.

Shima bai nemi amsar ba, sai ya d'age hannunsa zuwa sama, alamun ya cusa shi cikin gashinsa ne yayin da d'ayan ke rik'e da wata folder, sai ya mik'o mata kafin tayi tunanin meye a ciki.

"Nayi magana da Mr. Hawkins, zamu fara ranar monday, awa d'aya bayan an tashi kullum, a Library. Wannan Topics d'inku ne watannin da akayi, ki duba su kafin monday."

Ta karb'i Folder ta bud'a ta, paper d'aya ce a ciki mai d'auke da jerin sunayen topics d'in.

"Sai na ganki."

Sautinsa ya sake fad'a a hankali sannan ya gifta ta ya wuce.

Kwakwalwar Fadeelah ta tsaya cak! da aiki yayin da k'afafunta suka manne a wajen, me ya d'auke ta? Dak'ik'iyar da har baza ta iya rik'e sunayen topics ba?

Idonta ya sauka akan wasu daga cikin sunayen.

_" Pythagoras_
_" Numeric and Geometric Patterns_
_" Functions and Relationships_
_" Algebraic Expressions_
_" Algebraic Equations_
_" Geometry of Straight Lines...._

Ta cije lebb'enta na k'asa a hankali, ranar monday zata fara kwance wannan d'aurin data tanada!


*?%O??%*


*BAYAN NA MUTU!*

?AYSHA SHAFI'EE

*05*

*(&_&)*

RANAR ASABAR.

"Lokacin yarintata a tsakanin shekarun 1980's zuwa 1990's, ni da yayyena biyu ne kad'ai musulmai a makarantarmu, kuma nasha had'uwa da k'alubale da yawa a lokacin saboda ni kad'aice macen dake saka dogon wando a maimakon k'aramin da ake sakawa na wasanni, ni kad'aice wadda bata zuwa fati irin na rawa da makaranta ke had'awa, sannan sunana yasha jawo min habaici da izgilanci ba'a wajen d'alibai kad'ai ba har da malamai.

Shi yasa a yanzu nake k'ok'arin cusawa 'ya'yana alfaharin kasancewarsu musulmai da kuma juriyar dogaro da kansu a lokaci irin wannan. A watannin baya ne 'yata ta biyu ta shaida min cewa yara da yawa a makaranta na mata kallon kyama saboda hijaabinta amma bata tab'a basu damar da zasu tunkareta ba saboda bata damu da sanin gurb'ataccen tunaninsu game da addinita ba, a wannan lokacin nayi mutuk'ar farin ciki akan karfin hali da kuma juriyar dana hango a cikin idanunta, na san cewa tarbiyar dana ke mata ta fara tasiri akanta."

Sarah Muhammad, wata dattijuwar mace ta fad'a zaune a jerin zagayen kujerun sanda layi yazo kanta. Fadeelah ta k'ifta idonta a hankali daga inda take zaune tana kallonta, suna zaune ne a cikin fad'ed'en d'akin taron dake cikin ginin wajen 'MUSLIM SUPPORT GROUP' (k'ungiyar tallafi ta musulmai.)

A watan baya daya wuce ne Mami Saffiya ta samu labari daga k'awarta cewa k'ungiyar ta bud'e zauren tattaunawa tsakanin mata da yaransu game da k'alubalen da suke fuskanta a yanzu, wanda ake saka ran haka zai taimaka wajen k'arfafa zuciyar yaran da wasu masu rauni wajen fuskantar duk irin k'alubalen da zai zo musu.

Zahra ta motsa kujerarta a gefen Fadeelah alamun gajiyawa sanda matar dake gaba ta shiga nata bayanin.

"Dani da k'anwata mu kad'ai ne ke azumi a cikin watan Ramadan, k'awayenmu sai suyi ta tambaya 'Yanzu baza ku ci komai ba tun daga safe har fad'uwar rana? ko ruwa baza ku sha ba?', duk sanda lokacin cin abinci yayi sai mu tafi can d'akin karatu mu k'are lokacinmu."

"Saura awa nawa lokacin ya k'are...?" Muryar Zahra ta rad'a a cikin kunnenta.

"... Na gaji wallahi."

Fadeelah ta d'aga kafad'unta.

"Ban sani ba amma watakila nan da
wasu awannin biyun."

"Ya salaam ya Allah!" Ta fad'a tana jefa kanta saman kujerar.

Sarai Fadeelah ta san me Zahra ke kewa, Wayarta. A tsawon wata gudan da suka fara zuwa wajen nan, suna barin gabad'aya wayoyinsu ne a mota, kamar yadda tsarin Mami ya tanadar.

"... Ni da iyayena munsha mutuk'ar wahala wajen wayar da kan hukumar makarantar dana ke a lokacin su san cewa hijaabin da nake sakawa yasha banbanci da tsarinsu na cewar ba'a yarda d'alibai su saka hula a makarantar ba, da kyar suka fahimci cewa hijaabin yana daga cikin 'yancina kuma ba zai zama watarana na saka watarana na cire ba kamar yadda hula take.

Amma duk da haka nasha fuskantar k'alubale daga wajen d'aliban, k'alubalen da bana son 'ya'yana su fuskance shi, shi yasa a yanzu na tura 'yata wata makarantar musulmai mai zaman kanta dake West Valley City."

"Kinyi hukunci mai kyau Zeena..."

Shugabar k'ungiyar, Amani Omar ta fad'a, da yawansu suka gyad'a kansu kafin ta cigaba.

"... Abune mai kyau yadda kowannenmu ke fitowa yana fad'ar irin nasa k'alubalen da kuma tsoronsa, na yarda cewa hakan hanya ce mai b'ullewa da zata sa mu yak'e su.

Kuma ina fatan dukkanin mu mun k'aru daga bayanan da muka ji, Sannan akwai wani babban abu dana ke son in jawo hankalinmu akai, dole ne sai kowanenmu sai yayi taka tsan-tsan da kewayensa da kuma irin mutanen da zai dinga mu'amala dasu a yanzu.

Idan baku manta ba a shekarar data wuce ne cikin daren ashirin da bakwai na azumin Ramadan muka sami labarin kashe wata yarinya 'yar shekara 17 da daddare bayan ta fito daga McDonald's bayan gama cin abincin Iftaar d'inta zata koma masallacin k'ungiyarsu don yin sallar taraweeh, mutane da yawa sunyi kuka kuma sun jajanta akan tunanin wace irin America muke ciki da har za'a samu masu kashe yarinya k'arama irin haka don kawai tace ita musulma ce.

Saboda haka ya kamata mu iyaye musa ido sosai akan 'ya'yanmu, a lokacin yarintarmu da ake mana kallon bare, yafi sauki akan yanzu da 'ya'yanmu ke fuskantar zalinci da muzantawa k'iri-k'iri, don haka dole ne a kullum mu tashi da wannan tambayar a cikin kanmu... Ta yaya zamu kare kanmu da kuma 'ya'yanmu daga irin wad'annan mutanen?"

Wani k'aton abu da Fadeelah bata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login