Showing 93001 words to 96000 words out of 153964 words

Chapter 32 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3796

ya biyo Sa'id daga wajen kotun jiya yak'i komawa ya samu d'aki yayi kwanciyarsa.

Yaga alama kamar Sa'id d'in ya damu don da alama Awwal bashi niyyar komawa Ikara kwata-kwata, amma shi bai damu ba don ya san yana da faragar da in mutum talatin daga Babban gida zasu dawo k'ark'ashinsa a yanzu zai iya d'aukar nauyinsu. Ya dad'e da yarda cewa DANGI kowanne iri ne kuwa sune ginshik'in kowanne mutum a duniya.

Sa'id ya shigo ya gaishe shi sannan ya ajiye ledojin akan center table na falon.

"Yaya ina son anjima inje Ikara."

Yaji shi amma sai ya d'anyi shiru yana wani tunanin kafin ya amsa.

"Shi yasa nace maka kamata yayi mu sayi wata motar kawai, guda d'aya tayi kad'an a wannan zirga-zirgar."

A jirgi dukkaninsu suka zo, sai suka biya wani direba ya taho musu da motarsa.

"Yaya in dai ba kyauta zaka yi da ita in mun tashi tafiya ba, ni gani nake yi asarar kud'i ne kawai."

"Kyautar nayi niyyar yi da ita ai, naga Baba yana yawan zuwa cikin Zaria, kaga sai kawai Jamil (d'an kawu Ibrahim d'in) ya dinga kawo shi duk sanda zai zo tunda? ya iya driving."

Sa'id ya gyad'a kansa.

"Hakan yayi, zaiji dadi kuma Allah ya saka da alkhairi."

"Ameen." Fatar bakinsa ta furta ba tare da sautin ya fito ba.

Har Sa'id ya mik'e zai shuga ciki ya tsaida shi a ta hanyar kiran sunansa.

"Sai'd ya sunan abun da naga mata suna zanawa a hannunsu?"

Mamaki ya d'an kama shi.

"Yaya wai k'unshi?"

"Sunansa kenan?"

"Eh k'unshi ko lalle suke ce masa."

"Saboda me suke yi?"

"Saboda kwalliyarsu kawai, amma yawanci sai za'a yi bikin aure suka fi yinsa, musamman ita amaryar kusan dole ne ma tayi k'unshi."

...ranar da aka fara bikina ne, komai ya tarwatse, Sadiya ta gan ni sannan Mairo ma tazo nemana, ni kuma ganinsu ya tayar min da ciwo na, ban sake fahimtar komai ba daga hakan sai bayan na farka Mami tace min Al'ameen ya dakatar da d'aurin auren namu saboda halin da nake ciki.

Iya wadannan kalaman nata a lokacin da take bashi labarinta suka gutsiro suka haska cikin kansa, Ya Allah! Ya akayi ya manta da hakan, ya akayi ya manta daga ita har Kawu Ibrahim dasu Mami marik'anta sun shaida masa cewa a ranar da aka fara bikinta wannan hargitsin ya fara? Shine har zai zauna a cikin kansa yana yaba kwalliyar da ta yiwa wani?

Ganin Adam bashi da niyyar sake magana yasa Said ya juya ciki yana tunani me ya had'a k'unshi kuma da zancen wannan shari'ar.

Kusan minti talatin kafin ya iya goge tunanin k'unshin Fadeelah daga kansa, ya mik'e ya bud'a abincin? da Sa'id ya ajiye, sai dai lomar farko tunaninsa ya sake hasko masa ita, wane irin abinci take samu a wajen? Zata ma iya cin abinda suka bata tukunna? Ko zata iya ci ya san tashin hankalin da take nad'e cikinsa ba zai barta taci na kirki ba, dole ne ma ta fara ramewa akan sanda ya fara ganinta, sai rufe nasa kawai ya mik'e ya shiga ciki.

Wasa-wasa, tunaninsa ya dinga k'aruwa, duk wani abu daya zo yi sai ya kwatanta shi da halin da Fadeelah ke ciki a lokacin, saboda haka ya rasa sukuni ko kad'an, aikin nasa ma ya kasa k'arasawa, yana jin hirarsu Awwal da Sa'id amma ya kasa cewa komai, daga k'arshe wani yanki na zuciyarsa ya kasa daurewa, ya gaya masa cewar bazai rasa shari'ar nan ba don kawai yaje yaga Fadeelah sau d'aya, shi lauyanta ne yana da damar da ko tsakar dare ya tashi zai iya zuwa yace a fito masa da ita ya ganta.

Saboda haka bai bari wani tunanin ya danne wannan ba, ya tashi ya shirya ya d'auki muk'ullin mota ya fita. Motarsa ce amma ta zama kamar ta Sa'id saboda ko a can Abuja yafi shi amfani da ita, shi yasa bai san abubuwa da yawa a cikinta ba, a yanzu ma yana kunna ta ya hau titi, wak'ar dake cikin Cd da Sa'id d'in ya sanya ta fara playing.

I can be your hero baby..
I can kiss away all the pain..
I will stand by you forever..
You can take my breath away.

Sai ya maida kansa ya jingina da saman kujerar, saboda yadda sautin wak'ar ya karad'e motar a volume d'in da Sa'id ya barshi.

Am I in too deep?
Have I lost my mind?
Well I don't care... You're here tonight!

Adam ya lumshe idanunsa yana kallon titin, ji yake kamar kowanne baiti dashi ake yi!

****

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

(&_&)

"Kai inda zaka san duk duniya ba inda munafunci yake tasiri kamar Babban gida, ace wai baturen nan yazo amma kowa haba-haba yake dashi, kai ba zaka ci kowa yana wajen ba sanda aka kafa dandalin Allah ya tsine masa."

Isah d'an gidan Kawu Bashir ya fad'a sanda suke zaune a dakalin dake gaban wani k'aton gida na k'asa bayan maghriba tare da wasu 'yanuwansa da abokansa. Saminu d'an gidan ne ke sayar da rake a wajen saboda haka sai ya zame musu kamar dandali, harda ba siya yazo yi ba sai ya zauna a shiga hira.

"Kud'iii...! Ake gaya maka yaro, kaima kayi kud'i ka gani wallahi har babanka durk'usa maka zai yi, har ka mutu kuwa in kana dasu baza ka taba jin mai zaginka ba." Cewar wani abokinsa.

"To yanzu ma meye ba'ayi ba, shi baban nawa da yazo kaga wani sussunkuyar masa da kai da yake yi, ance fa har zancen shari'ar sai da suka yi dashi."

"Ai shi yasa kullum nake cewa Sa'idu ya haye wallahi, don ance fa yanzu ma aiki yake nema masa a can Abujan." Cewar Saminu yana kankare rakensa.

"Yanzu ai kwa fad'i hakan..." Wani Ibrahim d'an bayan layin ya sako baki.

"Sanda ya dage yana karatunsa, ba daku ake kafa hirar wai shi ya nacewa boko zai je ya dawo ya same ku ba, daya gama ya fara zama a shagon babansa wace irin dariya ce ba'ayi daku anan ba, yanzu ai gashi nan tana kai masa."

"Ni yazu duk ba wannan ba..." Cewar Aminu yana gyara zamansa.

"... Rayuwata ce ta shiga kwale-kwale zuwan mutumin nan wallahi, don tunda yazo Asma'u ta fara canja min fuska, itama ta shiga layin haukan dake tashi a cikin gidan wallahi."

"Haukan me?" Buhari ya tambaya yana gaftarar raken hannunsa.

"Au wai kai baka san me akeyi ba? Lallai an barka a tasha wallahi." Cewar Saminu.

"Dan Allah me yake faruwa?" Ya tambaya da zumud'i.

"Tsaya in fara tambayarka a hankalinka kwana biyun nan baka ga yadda ake bawa Kawu Ibrahim wani girma bane?"

"Eh na lura kuwa don d'azu ma ina ji Ramatu tana cewa 'yarta ko za'a kai masa me?"

"Toh yanzu duk Babban gida, ba zan d'ebe maka kowa ba sai masu yara k'anana, fata suke Kawu Ibrahim ya had'a ya'yansu aure da wannan baturen hatta su 'yanmatan kuwa, duk hankalinsu ya koma kansa don sunga yadda yake jin maganarsa."

"In dai Kawu ne kuwa zasu yi su gama ne, don in baiyi niyyar abu ba, babu mai saka shi."

Kafin d'aya daga cikinsu ya sake cewa wani abun, suka hangi tahowar wata mulmulalliyar mota da tayo full light jan layin kuma daidai saitin Babban gida inda suke zaune.

"Toh 'yan gida sai su shirya ga wani baturen nan."

"Kai haba?" Cewar Isa yana d'ago da kansa.

"Duba da kyau ka gani, duk layin nan ka san ba mai wannan motar kuma ku kad'ai ne ke da 'yanuwa masu irin wannan k'ashin arzik'in."

"To kuma an ta zuwa kenan?" Cewar Saminu yana kallon motar da babu tantama saitinsu ta take tahowa.

"Kut!" Cewar Buhari.

"Allah yasa da gaske kuwa wani baturen ne yanzu in samu wajen zuwa wallahi."

Ya fad'i hakan ne daidai sanda motar ta tsaya gaba kad'an dasu, kuma ba da wani b'ata lokaci ba k'ofar gaba ta mai zaman banza ta bud'e, sannan wata mace ta fito daga ciki.

Hasken kwan lantarki, hasken farin wata da kuma hasken fitilar motar dake gefe ya shaida musu siffar wata kyakkyawar matashiyar mace sanye da dogon hijabi, basu take kallo ba k'ofar Babban gidan dake gefensu nan ta kafe idanunta ba ko k'itawa tana kallo, duk cikinsu ba wanda ya gane ta saboda haka suka sake bin mutumin daya gito daga mazaunin direba da kallo shima.

Sai dai me? Saminu na d'ora idanunsa akan mutumin daya zagayo inda macen ke tsaye wani tunani ya d'arsu, da sauri ya sake maida idonsa kan macen, ai kuwa bai san sanda ya saki raken hannunsa ba sannan bakinsa ya lailayo wani irin zagi.

"Ashe Sadiya da gaske take kenan? Jama'a baku gane ta bane? Mairo ce fa."

"Wace Mairon? Da yawansu suka hada baki wajen tambaya.

"Mairo dai ta gidan man, k'anwata!"

***

Gabanta fad'uwa yake yi a lokacin da dukkan wata ma'anar tsoro ta duniya, likacin da tayi ar ba da tsirawa barandar k'ofar gidansu kuma mahaifarta, barandar kofar gidan waje ne da Babanta yake zama tare da abokansa kullum bayan sallar magriba, wani lokacin har ta fito musu da abincin dare suci anan sannan suyi isha kafin ya shigo gida.

Sai ta motsa kafafunta ta nufi ciki, ba abinda take fahimta na gefenta har ta shiga cikin zaure na farko wanda banda shafen farar k'asa, bai canja ba ko kad'an daga yadda yake, zaure na biyu ma yana nan d'auke da d'akuna guda uku na yayyenta maza a wancan lokacin. ('Yayan Gwaggo lami.)

Daga nan sai k'ofar da zata kai ka cikin gidan, tun kafin ta shiga, kwakwalwarta ta tuno mata da yadda cikin gidan yake, k'aton tsakar gida mai d'auke da bishiyar darbejiya wadda take kamar ruhin gidan don kusan komai a k'ark'ashinta ake yi, sai
daga gefen dama kuma d'akin iyayensu jere cikin layi kowanne ciki da rumfa, dakin Baba da wani store da yake ajiye amfanin gonarsa sune a farko kafin a kai ga nasu inartata, sai daga d'aya bangaren mai kallowa kuma d'akuna biyu ne kowanne falle d'aya, na farko na saukar baki ne sai kuma nata da Baba ya ware mata tun daga sanda ta shiga boarding.

Kicin da makewayi suna daga b'arin hagu na k'aton tsakar gidan sannan kuma garkensu in an zagaya baya.
Sai dai me, tana karya kafarta cikin tsakar gidan, wata irin hayaniya ta daki kunnuwanta, hayaniyar da har ta k'are rayuwar gidan kaf bata taba sanin makamanciyarta ba.

"Na rantse da mahallicina sai dai ayi uw*ar da za'ayi yau a cikin gidan nan amma sai na kwaci hakkina, bashi har wata nawa."

"To ba sai ki kwata ba mu gani, in kin isa ke 'yar halak ce Safiya ki shiga d" akina ki yashe shi tsaf shine zan yadda kin damu da bashinki."

Idanun Mairo suka gane mata mata fal an taru a k'asan wannan darbejiyar sai rik'e mutum biyu akeyi wanda da alama sune masu fadan, bata yi ko sallama ba amma da idon wata daga cikinsu ya hangota sai tace.

"Wa'alaikum salamu shigo."

Jin hakayasa kusan duk suka maida hankalinsu kan k'ofar kafin wata ta sassauta murya tace.

"Larai, kinga dai ga bakuwanan, kiyi wa girman Allah ki hak'ura kar..."

Kalmar Bakuwa ta daki Mairo a tsakar kai, itace bak'uwa? Itace yau ta zama bak'uwa a gidan ubanta?

"Sannu da zuwa Hajiya, Gwaggon kike nema?"

Wata Dattijuwar mace ta fada tana kokarin durkusawa Mairo, sai tayi saurin fakatar da ita ta hanyar cewa.

"Inna Amina nake nema?"

"To fa? Kuma a gidan nan aka kwatanta miki ita?" Cewar wata data k'araso.

Muryarta na shirin rawa tace.

"A gidan nan take, matar gidan ce."

"Ai Amina a gidan nan d'aya ce, kuma watan daya mutu ma suka tashi, tunda taje gida wankan haihuwa bata dawo ba."

"Ita wadda nake nema babba ce."

"To Hajiya anya kuwa nan ne?"

"Sai dai ko a tambayo Gwaggon." Cewar wata matashiya goye da d'a."

"To Inna Saratu fa?"

Matashiyar tayi dariya tace.

"Hajiya ni kad'ai ce Saratu a gidan nan amma ni ba Inna bace."

"Kinga bari dai a kaita wajen Gwaggon, shigo muje Hajiya."

Sai ta taka ta bita ba musu, sauran matan na tsaye sai kallonta suke yi kamar sun ga wani abin mamakin, amma ita ba tasu take yi ba, idonta na kan ginin d'akunan gidan, komai yana nan yadda yake sai k'ara tsufa da yayi, ga tarkace nan a jibge koina, mamaki ya kamata, ta tuno sanda koina yake fes! Sanda zata d'auki tsintsiya ta share tsakar gidan nan duk girmansa. Kafin ta waiga ta hango k'ofar d'akinta suka sha kwanar da zata kaisu garke.

Sai dai a yanzu ba garken ne a wajen ba, gini ne a tsaye kyam na bulo har da fentinsa kalar ruwan madara.

"Salamu Alaikum, Gwaggo bak'uwa kika yi."

Kubra ta fad'a sanda ta tsaya a k'ofar d'akin.

Numfashin Mairo yayi kokarin zarcewa sanda muryar Gwaggo Lami ta kwararo daga cikin d'akin, gwaggo lami dai data sani Uwargidan mahaifinta.

"Bana son rainin hankali Kubra, wace bak'uwa zanyi a daren nan? In zancen? kud'inki ne banda canji."

Da wannan fadan, wannan fad'an dai da kowa ya santa dashi tayi maganar.

"Alqur'anin Allah bakuwa kika yi, lek'o ki ganta." Cewar Kubran.

Kamar ba zata leko ba sai kuma can ta d'age tattararren labulen ta zuro fuskarta, kallo d'aya ta yiwa fuskar Mairo ta mik'e ta fito.

"Ya rabbis samawati wal'ardi! Kar dai Mairon Amina nake gani? Mairo kece? Daga ina? Dama da gaske Sadiya take ta ganki?

Mairo kawai kallonta take yi da mamaki itama, itace dai Gwaggo lamin da ta sani amma tsufa ya kamata fatarta duk ta yamushe sannan jikinta ma ya tsomare.

"Gwaggo nice na dawo, ina Innata take da Inna saratu, na tambaye su sunce basu gane ba."

"Au da kuka had'u da Sadiyan bata shaida miki ba? Ai Amina ta mutu babu dad'ewa da barinki gida, Saratu kuma tana can Kaduna tayi aure."

Mairo ta hadiye yawu mai zafi cikin makogwaronta, abinda Sadiya ta fad'a gaskiya ne kenan, mamarta ta mutu.. Innarta mai tsananin sonta wadda ta raini ta da dukkan kulawa, daidai da rana d'aya bsta taba bari kunya irin ta uwa da d'iyar fari ta shiga tsakaninsu bud'e zuciyarta take ta fad'a mata komai, don ta maida ita kamar k'awa ko kuna k'anwa da bata da ita.

Wani irin kuka da bata shirya masa ba ya faso daga bakinta sannan ta durk'ushe a wajen.

"Au, au... Yanzu kika san ciwon Uwa Mairo? ai na zata dadi soyayyar saurayi tasha gaban komai a wajenki, kin san komai ai kika tsalkake kika bar baiwar Allah nan, wane irin bakin ciki ne bata k'unsa a dalilinki ba, wane irin zagi da habaici ne bata d'andana daga jama'ar gari dana babban gida ba? Wanda hakan ya jawo mata ciwon zuciyar daya kaita kabari? Sakayyar dake tsakaninku wannan sai ubangiji Mairo, amma Allah ya sani ki zalunci matar nan."

Mairo ta san halin Gwaggo lami sarai, ta san irin zuga da makircinta kuma ta san bata tab'a son mahaifiyarsu ba, amma ta yarda da duk kalaman da take fada a lokacin, don ta yarda duk wanda zai gaya mata sab'anin hakan ma ya rufe ta ne.

"Tana ina? Nan ta shigo?"

Muryarsa Saminu ta karyo kwana,ya shigo tare dasu Isa a bayansa.

"Wallahi itace kuwa, sannu da zuwa? Mairo, ashe zaki gane hanya?"

Saminun ya fad'a yana kallonta.

"Zan zage ka Saminu, Mairon kake wa Sannu da zuwa? Ko baka gane ta bane."

"Na gane ta mana Gwaggo, yanzu muka gama gaisawa ma ai da mijin nata. Kinga Mairo ba nan ya kamata fa ki shigo ba, Babban gida zaki wajensu Kawu, nan duk 'yan haya ne ba wata tsiya ba, tashi muje mu raka ki."

Gwaggo lami kawai sakin baki tayi tana kallon yadda su Saminunke kokarin tashinta tsaye, zuciyarta ta d'arsa mata cewa tabbas Mairo ba'a wulakance tazo ba, daga yanayin fatar jikinta ma kawai zaka tsinci hutu a ciki.

Da kyar su Saminu suka raka ta Babban gida inda kafin isarta labari ya zaga gidan gabad'aya har wad'anda suka fara gyangyadawa ma sun mik'e. Wajen Kawu D'anjuma su Saminu suka shigar da ita inda kamar a wajen Gwaggo lami shima bata samu wata rarbar arziki daga gareta ba, yace shi bashi da ta cewa akanta tunda bashi ta yiwa laifi ba, iyayenta da yanzu basa duniyar sune alhakinsu ke kanta bashi ba, don haka ta tashi tabi mijinta su koma inda suka fito, duk sanda ta sake take so kuma tazo ta gaishe su, shi ba zai k'i amsa gaisuwarta ba.

Sannan kai tsaye ya shaida mata cewa bayan tafiyarta k'anwarta Bintu ta kashe mahaifiyarsu ta gudu, kuma yanzu da suka gano ta an maka ta a kotu har anyi zaman farko. Hadiyar zuciya ne kawai ya rage Mairo bata yi ba jin cewa da gaske ne su Kawu saida suka kai Bintu kotu, ita tayi zaton su Kawu Yahya sun zo tafiya da ita ne kawai don tsoratarwa ba wai har abin ya kai kotu ba, saboda wallahi har cikin ranta ta yarda cewa Mairo ba zata iya kisa, bayan Aunty saratu duk duniya kaf! Tafi kowa saninta, don ko Innarsu tana? d'aukanta ne a matsayin 'yar Aunty Saratu ba tata ba.

Ganin irin karb'ar data samu daga wajen Kawu D'anjuma, sai kowa ya shiga d'ari-d'arin tunkararta, don tun bayan da Adam yazo kowa ya sakar masa fuska suka fuskanci b'acin ran Kawu D'anjuma sosai, don janye tallafin da yakd bawa mutane da yawa dake rayusa a k'arshinsa yayi, don haka sun horu na mai sake iya tarbar Mairo hannu biyu.

Saminu da Isah ne kawai suka yita nan da nan da ita, har zuwa duk wajen wanda ya kamata ta gani a Babban gidan.

"A ina zaki kwana?"

Sadiq ya tambaya sanda ta foto daga Babban gidan wajen goma na dare. Duk abinda akeyi suna rakab'e a mota shi da zakkiy da kuma Muhammad da har alokacin ke baccinsa, ba wanda ya neme su don haka shima baiyi kokarin kai kansu ciki ba, to yaje yace me? Shine wanda ya gudu da 'yarsu ya kuma aureta ba tare da saninsu ba?

"A gidanmu." Ta bashi amsar a gajarce idonta baya kallonsa."

"Amma..."

"Sadiq dan Allah ka barni kawai."

"Sai ya gyad'a kansa sannan yace.

"Muhammad fa?"

Zai iya rantsewa sai a lokacin ta wulkita idonta cikin motar ta kalli Zakkiyar dake rik'e dashi sannan kai tsaye tace.

"Na yaye shi."

"What? Maryam yaye? Shekararsa d'aya fa?"

"Ban damu ba." Ta bashi amsa.

"A yanzu ban damu da duk abinda ya shafe ka ba Sadiq don na fahimci ka san komai, sanda muka shigo garin nan banyi maka kwatancen gidanmu ba, amma kai tsaye ka kai motarka har can, kenan kana sane da inda 'yanuwana suke duk tsawon lokacin nan, amma ka kyale ni, ka nesanta ni dasu tunda kai kana tare da naka."

Bai ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login