Showing 6001 words to 9000 words out of 153964 words

Chapter 3 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3815

faruwa ne saboda wata damuwa--"

Abinda yake shirin fad'a min shine gajiyar makaranta da kuma yawan karatun dake shiga kwakwalwata ne suka jawo min yawan mafarkan ba wai wani abu ba, saboda haka in ragewa kaina abubuwa sannan---"

"Kuma ki dinga hutawa, sai na ganki a wani appointment d'in."

Ya k'arashe tare da tata zuciyar.

"Thank you, zan k'okarta."

Ba wani taimako daya bani yau.

Zuciyarta ta ayyana sanda ta rataya jakarta ta nufi hanyar fita, sai dai kafin ta tura k'ofar wani dogon mudubi daga gefe ya d'auki hankalinta, ta juyo a hankali ta kalle shi, ta kalli kanta, sannan ta kalli siffarta dake tsaye sanda hoton wata 'yar siririyar matashiya ya kallota ta ciki.

Fuskarta d'auke take da kamanni irin na fulanin k'asar Nigeria da take gani a hoto, sai dai tata fes! babu irin tsagun fuskarsu da internet ke nuna mata. Ta cikin kalar ruwan k'asar idon tana iya hango damuwa fal da kuma rashin kwanciyar hankali a k'asan su, a kowacce rana dake wucewa, fuskarta na k'ara zama bak'uwa a wajenta ne, tana jin kamar wani ne daban yake son kwace jiki da zuciyarta, ya ture nata ruhin gefe.

A ranakun data fara zuwa wajen nan, lokacin da Daddy ya kawo ta da kansa ranar appointment d'inta na farko, zuciyarta na rike da wani fata ne, fatan cewa damuwarta zata yaye, rayuwarta zata haska kamar yadda komai na wajen yake cikin kala mai kyau, Amma a yanzu bayan shekara d'aya da watanni ta sarewa wannan fatan kamar yadda ta lura Dr. Gilbert ma ya fara sarewa al'amarinta... ya rage yi mata yawan murmushi da bata fatan warkewa. Watakila matsalarta tafi k'arfinsa ne.

Nayi sirranta da yawa.

Zuciyarta ta rad'a mata.

Dole ne in dinga cin abinci da yawa.

Tana fita daga office d'in, wata tsohuwar Baturiyar dake zaune ita kad'ai a waiting area ta mik'e ta shiga rik'e da sandar dogaronta, a lokaci d'aya kanta ya sara sanda ta kalli sandan, saboda haka tayi hanyar waje da sauri bata ko tsaya kiran da receptionist ke mata ba na tayi booking wani appointment kafin ta wuce.

Daga Clinic d'in zuwa Bus stop mafi kusa tafiyar minti goma ce, haka tayi ta bin hanyar idonta a k'asa, hannunta na dama damk'e da jakar ratayenta kamar hakan ne zai kare abinda take gudu kar ya faru.

Bai fi mutane sha biyu ba a Bus Stop d'in saboda haka ta sami damar tsayawa daga cikin 'yar rumfar, sai dai ta gefen idonta tana iya ganin yadda baturen dake tsaye a kusa da ita ke kallonta, wani tsoho ma ya kyallaro da idonsa ta saman jaridar da yake karantawa sannan wata mata ta sak'e damk'e hannun d'anta. Kamar ita d'in bomb ce dake shirin tashi a kowanne lokaci.

"Hola..!"

Direban Bus d'in data tsaya ya d'ago min hannu sanda na taka k'afarta cikin motar, tana yawan hawa motarsa saboda yana tsayawa a stop d'in kusa da makarantarsu, shi mutumin k'asar spain ne kuma kamar yadda yaren spanish yake mai mafi rinjaye akan duk wani yare bayan turanci a Washington, baya tab'a mata turancin... yace tayi kama da matan k'asarsu don haka shi yarensa zaiyi mata.

"Buenas tardes. (Barkanki da rana.)"

Murmushi ya sub'uce a fuskarta, ganin mutane basa tab'a zama d'aya, wasu na gudunta wani kuma na son yi mata magana.

"?C?mo est?? (Kana lafiya?)"

Ta tambaya sanda ta mik'a masa Metro-card d'inta, don zama tare da Romilda k'awarta a makaranta yasa ta fara iya maida gaisuwa.

"Estoy bien, gracias. (Lafiya k'alau, Nagode.)"

Ya mik'o mata katin bayan ya cire iya kud'insa, ta nufi can k'arshe ta zauna daidai sanda wayarta tayi k'ara.

"Kina ina?"

Sak'on ya fad'a daga lambar Mami Saffiya cikin yaren Hausa.

_"Minti Ashirin zata dawo dani yanzu."_

Ta tura mata hakan da turanci don bata iya rubuta Hausa sosai, sannan ta k'ara gyara zaman rolling d'in mayafinta tana kallon titinan da suke wucewa. Duk sanda ta fita da yamma sosai irin haka, lokacin da fitilun garin ke walk'awa cikin idanunta, sai taji kamar yaune rana ta farko data iso cikinsa.

Da tunanin hakan kuma, idonta ya hasko mata wad'annan iyalin da suka zama gatanta.

Ahmad Malik da suke kira da Daddy, Babban likitan hak'ori ne anan garin Washington, mahaifinshi asalin African-American ne na k'asar nan, Ya auri mahaifiyarshi 'yar Nigeria ne a wani course-work da suka je yi garin Kano na wayar da kan mutanen Nigeria akan shan magunguna asibiti tun a wancan lokacin, anan suka had'u a matsayin d'aya daga cikin Nurses d'in asibitin da suka sauka, ya aureta bayan shekara d'aya da zuwansu kuma tsawon rayuwar aurensu kaf! a America suka yi ta, sai bayan ya rasu ne sannan ta buk'aci Daddy ya maida ita Nigeria cikin 'yanuwanta.

Daddy shine kad'ai d'anta saboda haka shi ya cigaba da rayuwarsa a nan da matarsa Mami Saffiya wadda take 'yar uwar mahaifiyarsa itama. Soyayyarsu ta fara ne tun suna yara lokacin da duk suke zuwa Nigeria ziyara, amma bata yi k'arfi ba sai bayan da ita Saffiyan tazo karatu America ta zauna a gidansu, kasancewar duk wani d'anuwansu in wani abu ya kawo shi k'asar a gidan nasu yake zama.

Bata ko kammala karatun nata ba akayi auren nasu a lokacin shima mahaifin Daddy yana raye, saboda haka bayan rasuwarsa mahaifiyar tasa ta barshi da matarsa ta dawo wajen 'yanuwanta Nigeria inda itama ajalinta ya riske ta a can.

Daddy mutum ne mai kamala, nutsuwa da tsananin hakurin da yake iya jurewa halin matarsa Mami Saffiyya, don ita macece mai kaud'i da kuma mita, sai dai tana da tsanani kirki da kuma hira, ga hidima baza ka tab'a ganinta ta rasa abin yi ba.

Tana da mutuk'ar kishin yare da al'adarta, shi yasa bata tab'a bari yaren hausa ya mutu a gidan kasancewar duk wanda yaga 'ya'yanta ma ba zaice sun had'a jini da Africa ba, yanayin abinci, iskar can, kammanin mahaifinsu da kuma farar fatarta yayi rinjaye wajen rufe had'insu da hausawan Nigeria.

D'ansu na farko Faruq, kusan halin mahaifinsa ya d'auko, don bayan tsabar nutsuwarsa, murd'adden miskili ne da in ba Mami ta bud'e halwar fad'anta ba, sai yayi sati bai kula kowa a gidan ba bayan gaisuwa. Shekararsa 17, ita ta girme shi da shekaru biyu amma ya fita aji a makaranta.

Zahra ita ake kira da baibai d'in d'an uwanta, ta d'auko wasu halayen na Mami amma nata har sun zarta sun kai iyaka. Tana da magana, iyayi da kuma ji da kai, sannan idonta na kan kowa a gidan, ta san hanyar da zata yi ta san abinda mutum ke k'ullawa shi kad'ai a cikin d'aki. A shekara Goma sha hud'u kawai ta san duk wata harkar kwalliya da wani abu da zai saka mace kyau, Fadeelah zata iya cewa ma ta fita wayo a wasu abubuwan.

Iman 'yar shekara shida, yarinya ce da ba ruwanta, tana cin komai kuma tana yarda da duk abinda ka gaya mata, burinta a kullum baya wuce kallon cartoon d'in Disney da kuma fatan ta tashi watarana taga ta zama d'aya daga cikinsu.

***

"Aunty deela ta dawo!" Iman ta fad'a lokacin da Fadeelah ta bud'e k'ofar falon.

"Yey na dawo!" Ta amsa da irin muryarta sanda ta zube mayafi da jakarta a kusa da ita, tayi kissing kumatunta amma bata ko kalle ta ba don idonta na manne kan Tv tana kallon cartoon d'inta na yau da kullum, 'Wrect it Ralph'.

"Me ya tsaida ke har k'arfe biyar? the last time da zan iya tunawa baki ce min zaki ko'ina ba."

Mami Saffiya ta fad'a daga can k'ofar kitchen hannunta rike da cokalin girki, ta k'arasa gareta amma kafin tayi magana ta zura mata cokalin a baki da zummar taji mata yanayin girkin.

"Mhmmm, gishiri yaso yayi yawa, a yanka dankali a ciki."

Mami ta daki goshinta da tafin hannu.

"Hai Allah, yaushe zan dinga gane awon gishiri ne?"

"Kar ki damu Mami, da nayi kud'i zamu hayo chef, kin daina girki a gidan nan."

Muryar Zahra ta fad'a daga kan couch tana kokarin zana gira akan tata da ta fik'e.

"Me kike yi haka?" Fadeelah ta tambaya tana kallon yadda ta fente kumatunta da blush bayan hakan.

Zahra ta juya idanunta kafin ta d'ago ta kalleta.

"Duh! sabon style d'in saka blush ne, Karki damu zanyi miki anjima in nayi wa Iman nata." Ta fad'a tafin hannunta kantafi cikin iska.

Iman daga can gefe ta juyo tace.

"Amma nawa ya fito sosai kamar na Venoloppe." (yarinyar cartoon din da take kallo.)

"Kar ki damu honey, sai yafi nata ma kyau."

Ta amsa tana tand'e bakin da take shirina zana masa janbaki, Fadeelah ta girgiza kanta kawai sannan tabi bayan Mami kitchen d'in.

"So ya interview ya kasance?"

Ta tambaye ta sanda ta tsaya gaban gas ta shiga juya miyar dake kai, Mami na yanka dankalin, ta d'aga kafad'unta duka biyun sannan tace.

"Ban sani ba, amma dai sunce zasu neme mu."

"Ku?"

"Eh, zamu kai wajen mu sha biyar."

"And..."

"Ni kad'ai ce Musulma."

Fadeelah a girgiza kanta sanda Mamin ta juyo tana zuba dankalin a miyar.

"Baza su tab'a kiranki ba."

"Na sani, amma zan sake duba classfied adverts d'in, baza a rasa wani waje ba."

Ta fad'a idonta baya kallonta, tsaf kuma Fadeelah ta gane me hakan yake nufi.

Baza ta tab'a samun aiki ba in har ana cikin wannan rikicin na k'okarin hana musulmai irinsu rayuwa a America.

***

"Daddy, dan Allah!"

Zahra ta fad'a tana buga kafarta cikin shagwab'a sanda suke hanyar makaranta. Kullum da safe shi yake sauke su a makaranta kafin ya wuce wajen aiki, Zahra da Iman makarantarsu daban, Fadeelah da Faruq haka, sai dai babu nisa tsakani.

"Nace ba zai yiwu ba koh? you're fifteen ta yaya zan fara baki tuk'i? kalli yayanki ki gani, wata shekarar zai shiga sha takwas amma baya tab'a k'orafi."

Faruq dake gaba ya d'ago da kansa daga danna wayar da yake yi, ya gallara mata harara ta mudubin gefe. Daddy ya cigaba da cewa.

"..Ba zai yiwu ba, ke yarinya ce har yanzu."

Ta turo bakinta cikin b'acin rai sannan a hankali tace.

"Banda yanzu, nima daidai nake da kowa."

Fadeelah kad'ai ta san me hakan yake nufi, don ita da Mami kad'ai suka gane tana murnar mensturation d'inta na farko ne ranar da ta had'a walima ita da k'awayenta.

Makarantarsu aka fara zuwa suka sauka ita da Faruq, Zahra ta dawo gaba a lokaci d'aya, ta saita mudubin gaba tana k'ok'arin fito da gashinta ta cikin nad'in hijaab d'inta, Iman na baya hankalinta ya tafi duniyar chocolate d'in da take sha.

"Sai na ganki." Kawai Faruq yace, ya rataya jakarsa ya nufi cikin makarantar kamar ita d'in wani wajen zata daban.

Tabi bayansa ta cikin d'imbin d'aliban d'in dake ta harkokinsu da niyyar zuwa lokarta ta duba ajin da take dashi, don har yanzu time table d'inta hargitse mata yake.

Tana ta sauri ta lalubo paper daga cikin tarin litattafanta, don Allah ya sani bata son ta had'u dashi balle shi ya ganta ma, ta san tabbas zata ga wani abun da zai b'ata ranta a sanyin safiyar da bata fara saka komai akanta ba, me yasa ne ma k'addara ta had'a number lokarta kusa da tasa ne? me yasa bata nesanta shi da ita ba kamar yadda take hangensa a baya?

Ta zaro paper ta kalla, tana da English yanzu ita kad'ai, anjima History tare da Melissa, sai commerce gabad'aya da k'awayenta biyun Romilda da Melissa... Arrgh! tana da Maths ma yau, Babban abin tsoronta kuma Babban abinda bata ganewa a makarantar, kwakwalwarta toshewa take da an fara taji kanta ya fara ciwo, kamar lokacin da mutum ke son tuna wani abu da bai tab'a saninsa ba.

Duk da hayaniyar cikin hall d'in na sauran students dake wucewa sai da taji sanda ya tsaya ta gefenta da kuma sanda k'amshin turarensa ya ziyarci hancinta... Ranta ya b'aci a lokaci d'aya, zata iya rantsewa ba ranar da zata zo wajen lokar nan bata had'u dashi ba, dalilin da yasa ta tsani ajiye wani abu nata mai amfani a ciki kenan.

Da k'arfi, ta banka k'ofar locker sannan ta juya da niyyar barin wajen, sai dai wasu tarin fastocin dake fad'owa daga cikin locker tasa suka sata tsayawa, kuma idonta ya kai kan rubutun jikinsu kafin tayi tunanin tsallakewa.

*Back up you terrorists!...Muslim sucks!"*

(B'atanci game da Musulmai.)

?%O??%

FIKRAH WRITERS ASSOCIATION.

BAYAN NA MUTU..!

*?AYHA SHAFI'EE*

*02*

*(&_&)*

Idan mutum ya duba ma'anar tsana a shafin yanar gizo, za'a fassara maka kalmar ne da lokacin da tsananin k'iyaiyar wani abu ko wani ya d'arsu a zuciyarka saboda wasu dalilai na rayuwa dake sa mutum cikin fushi, fushin da zai ta yad'uwa yana fito da tsiron wasu laifukan da zasu dad'a habb'aka tsanar.

Kuma in dai har tsanar tayi masauki, to komai kankantar abu zai dinga k'ara ta ne, balle kuma babban abu, babban abu irin wanda Fadeelah ta gani a wajen mutumin da ta tsana yanzu a rayuwarta. Shima kuma ya tsani ire-irenta saboda suna saka hijaab, suna sallah, suna azumi, sannan basa cin fiye da rabi na kalar abincinsu... ko kuma a saukak'e kawai ace saboda su d'in Musulmai ne!

A lokacin da ta k'addara ta kawo ta k'asar America ana dab! da fara zab'e na sauyin Shugaban k'asa ne, kuma takurar da akewa musulmai ko kad'an bata kai haka ba sai a yanzu da canji yazo na sabon d'an takarar daya lashe zab'en, canjin daya tab'a kowa, kuma ya tab'a rayuwar duk wani musulmi dake cikin k'asar America.

Saboda tun kafin hawansa ya fito kiri-kiri ya nuna kiyaiyarsa ga Musulmai ya kuma dad'a k'arfafawa wanda suke da akida irin tasa hakan, sai ya zama musulmai suna fuskantar tozarci a fili kuma har ta kai ma ana shirin hana wasu musulman dake waje shigowa k'asar.

Kuma suma kamar kowanne musulmi a k'asar suna fuskantar wannan k'alubalen don a kwanakin baya har wasu sun daki Zahra a cikin motar makaranta saboda ta saka baki wajen hirar siyasar sabon shugaban k'asar da akeyi. Gashi kuma a satin daya wuce an kori Mami Saffiyya daga wajen aiki saboda tace ba zata bi ka'idar sabuwar shigar da suka sanya na cire hijaab ba.

Allah ya sani komai nata YA MUTU a baya, amma zuciyarta na rik'e da son addininta, tana mutuk'ar samun nutsuwa a cikinsa, don ta tabbata ba zuwanta gurin likita ko magani ne ya tallafi kwalwalwarta a baya ba, k'arfin imanin da take dashi game da addininta ne.

Sai gashi a yanzu da cikin makarantar nan ya zama waje d'aya da take iya sakewa bayan cikin gidansu?shima za'a takura ta a cikinta. Mutumin da a yanzu ta tsana fiye da kowa a makarantar yana cikin kungiyar dake shirin datse walwalarta. Don me yasa kuwa baza ta damu ba?

"Toh don me yasa zaki damun?"

Romilda ta fad'a daga gefenta tana tauna sandwich d'inta cikin baki, Suna zaune a cafteria ne bayan fitowarsu daga class na uku a ranar, commerce.

"Naga dai bamu kad'ai ne musulmai a makarantar nan ba, saboda haka bamu kad'ai zasu takurawa ba."

Ta fad'a cikin turancinta mai cakud'e da yaren Spanish. Fadeelah ta juyo ta kalle ta.

"Shine matsalar, don kawai bamu kadai za'a takurawa ba sai kice kar mu damu? bamu san me suka shirya ba? ba mu san k'ank'anta ko yawansa ba da zamu ce ba zai shafe mu sosai ba."

Melissa dake tsallaken teburin da suke zaune ta gyara zaman dogon gashinta zuwa bayan kunne sannan tace.

"Deelah, kome suke shiryawa ni na san hukumar makaranta bata san da zaman k'ungiyarsu ba, don haka za'a taka musu birki da zarar sun fara."

Turancinta a kwance yake fita ba irin na Fadeela dake a warware kona Romilda mai cakud'e da yarenta ba, don ita haifaffiyar baturiyar America ce kuma ba musulma ba, amma duk da haka k'awancensu na tafiya daidai kasancewarta mai saukin kai da kuma fahimta.

Fadeelah ta buga kanta cikin hannayenta tare da yin ajiyar zuciya.

"Kamata yayi kawai ace na yaga fastocin nan a lokacin da na gansu."

Romilda ta girgiza kanta.

"A'ah Deelah, a dai yanzu gwara da baki fara ba, gwara da baki yi abinda zai sa ya fara lura dake ba balle har mu shiga cikin lists d'insu don ko kin yaga zasu sake yin wasu ne."

Ta sake yin ajiyar zuciyar tana d'ago da kanta. Ta san cewa shi bai santa ba, baima tab'a lura da ita ba a cikin d'imbin matan da suke cikin makarantar, Amma ita zuciyarta ta dad'e tana bidirin tsanarsa, tsana irin wadda d'an adam ke yiwa annoba!

"Kin je kiran Mr. Hawkins kuwa?" Romilda ta katse shirunta, a hankali ta girgiza kai.

"Me ya faru?" Mellisa ta tambaya.

"Faduwa nake yi a komai na Math, makina yayi k'asa da yawa. " Ta bata amsa muryarta a hankali.

"I'm sorry, ya kamata ki same shi gaskiya, ki gaya masa irin ciwon kwakwalwarki na san zai baki wani aikin ne da zai d'ago ki."

"Zanje." Ta amsa.

"Insha Allah." Ta k'ara akai.

"Mun tab'a zancensa bai zo ba kuwa..."

Muryar Romilda tasa ta wulk'ita da idonta gefe kuma a lokaci d'aya hoton fuskarsa ta shigo cikin ganinta.

Adam Steve, Saurayin da yafi kowanne tashe da d'aukaka a makarantar saboda dalilai biyu, fasahar kwakwalwarsa da kuma tsananin kyawunsa wanda ya had'e cikin kammani irin na Africa da kuma mutanen k'asar Turkey, tsananin kyawun da ya jawo masa girman kai da kuma tarin d'abi'u na d'agawa wanda baya hana d'aukacin matan makarantar suji kamar su bauta masa don kawai ya kula su.

Yana tafe rik'e da lemo cikin wani taku na tak'ama da kuma Izza, Dylan babban abokinsa na d'auke da tray din abinci a gefensa yana masa magana, amma shi in banda lemon ba komai a hannunsa don ba wanda zai iya bada shaidar ranar da aka ga yaci wani abu a makarantar, kafin a ganshi a cafteria d'in ma aiki ne.

Tana iya ganin yadda yawanci fuskokin mata ke binsa da kallo kamar yaune rana ta farko da ya shigo makarantar, da kuma yadda wasu ke cije lebbensu kamar suna hana kansu ihu ne saboda mahaukaciyar kwakwalwarsu na gaya musu cewa shine k'arshen burinsu.

Sai dai duk wannan hank'oron nasu yana bajewa ne a iska, Adam bai tab'a kula d'aya daga cikinsu ba kamar yadda aka san duk wani saurayi mai irin qualities d'insa nayi,?mata da yawa sun sha yarfa kansu wajen masa shishshigi don baya tab'a damuwa da kowa sai tarin abokansa da suke harkar karatu tare, mutane sunce yana da wani bak'in tarihi ne game da mata, amma abinda fadeelah ta sani shine bak'in tarihinsa bai hana shi yad'a tozarci ga addininta ba.

"Inaga ina da abinyi fiye da zama anan." Ta fad'a tana d'aukan jaka da wayarta ta bar teburin.

"Baki ci abincin ba..."

"Bana jin yunwa, sai na ganku a aji."

Daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login