Showing 87001 words to 90000 words out of 153964 words

Chapter 30 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3784

kotun da za'ayi shari'ar ya samu wani office mai kyau yayi hayarsa inda zai dinga ganawa da duk mutanen da zasu shafi bincikensa hankali kwance.

Sai dai bayan tsare-tsaren shari'ar, office d'in ya zama kamar wani waje dake kange shi daga komawa wajen Fadeelah, don ranar daya sake komawa kotun ma yayi magana da marik'anta, bai nemi ganinta ba.

Ya sake magana da Kawu Ibrahim, kuma ya k'ara samun duk wani sauran bayanin da yake nema daga gare shi, sai dai kamar yadda ya b'oyewa kansa shima bai shaida masa cewa ya san Fadeelah a America ba.

A daren da ya zama washegari za'a fara shari'ar, Adam ya kasa wani bacci cikakke, tunani fal ke yawo akansa game dayadda komai zai kasance, shari'ar Nigeria daban ce da wadda ya saba a America, yaga hakan akan case biyu daya k'alubalanta bayn dawowarsa, ba daga alk'alan kad'ai ba, mutanen nan suna da wani irin taurin kai da sai sunga abu k'iri da muzuru sannan zasu yarda, amma a America in har akwai shaidu na gaske da suka tabbatar da abu to shari'a zata iya yadda dasu ba sai anja da nisa ba.

Amman Nigeria, sai kowa yaga komai dalla-dalla tukunna, shi yasa tunaninsa ya kasa tsayawa waje d'aya,?lalube kawai yake yi a cikin kansa ta yadda zai fito da komai ya baiyana bayan tsawon shekaru da faruwarsa.

Idanunsa biyu tar ya kwana!

***

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

29

(&_&)

K'arfe goma na safiyar laraba sha biyar ga wata za'a shiga shari'ar, amma tun kafin takwas mutane suka fara tururuwar zuwa don samun wuri kafin ya cika, 'yan Babban gida kaf matansu da samarin 'yayansu, hannu kawai d'aya zai d'ebe wad'anda basu zo ba, sannan banda 'yanuwa ga jama'ar gari dama wad'anda suka tsinci zancen a titi, kowa yazo cike da zumud'in d'aukar rahoton yadda shari'ar zata kaya, musamman da jita-jita ta zaga koina cewa ai lauyan da zai kare yarinyar ma musamman daga America aka d'auko shi.

Sadiya. Tana daga cikin wannan cincirindon mutanen sai fara'a take sanye da wani leshi irin kwancen data samo a Abuja, wani zaice taron wani abin alkhairi daya same ta ake yi ganin yadda take ta zubar surutu tana k'ara nanata zancen da zata bayar a matsayin shaida daga gare ta.

"Gabana fad'uwa yake Salame, kin tabbatar kuwa da malam yayi aikin nan?"

Habiba data iso wajen bisa tattagowar da Kawu D'anjuma yayi mata ta fad'a tana duban k'awarta Salame.

"Na rantse da kabarin ubana Habi bani da shakka akan malamin nan, ni ban san sau nawa zan gaya miki hakan ba ki yarda, kin riga kin sawa zuciyarki k'ulafucin sai aikin na Kadunan nan ne zai ci, bayan da bakinki kika ce ai ko'ina ma sa'a ake samu kawai."

"Dole inyi shakka Salame, tunda har Kawu D'anjuma nace dake a k'ulle bakinsa daga zancena a lamarin nan bayan ita an kashe tan amma har yanzu yarinya na raye, kuma kina gani yadda aka sa Mudan ya tattago ni har nan a haka."

Ta fad'a tana kallon karyayyiyar k'afarta d'aya da kuma sandan da take dogarawa, a ranar da suka kama hanya zuwa Kaduna ne motar da suka shiga tayi hatsari, kuma wani abu na tsautsayi Salame ta fita babu ko kwarzane yayin da ita ta samu karaya a k'afa harda kuma gocewar k'ashi. Hakan ne yasa ta tattara kud'in da ta dad'e tana tarawa dubu d'ari da hamsin cif! Ta bawa Salame da tayi mata zancen wani sabon bokan da aikinsa ke ci kamar yankan wuka a nan gaba dasu kad'an.

"To me akayi da maza? Yanzu fa za'a fara shari'ar nan ko shiga bamu yi kinji me za'a ce ba, kar kiyi saurin yanke hukunci, don dama saida ya fad'a, aikin kisa da d'aure baki a lokaci d'aya abu ne mai wahala, don haka ki bari mu saurara dai mu gani."

Da wannan zancen Salame ta rufe bakin Habiba daga sake wani k'orafi amma daga ita sai ubangijinta suka san irin fargabar dake dukan zuciyarta.

Lokacin da lauya Bashir Kutama ya iso harabar cikin kotun, wasu ma'aikatan gidan jarida da kuma na rediyo da suka sami labarin abin suka tare shi tun daga wajen motarsa.

Bayan sun sanar dashi abinda ke tafe dasu ne d'aya daga cikin 'yan jaridan ya tambaye shi.

"Yallab'ai me zaka iya gaya mana game da wannan case d'in? Yaya kake ganin shari'ar zata kasance?

Kutama ya kalli camerar da aka saita don d'ukarsa hoto da murmushi sannan yace.

"Wannan shari'a ce mai sauki, a duk case d'in da na tab'a yi ban ma tab'a cin karo da mai sauki wanda komai yake a fili irin wannan ba, saboda haka abinda zan iya cewa shine zamu yi nasara nan da k'ankanin lokaci insha Allah."

"To yallab'ai me zaka iya cewa game da abokin takararka wanda akace kwararre ne tun daga k'asar America."

Ya sake wani murmushin mai kama da dariya sannan yace.

"Kow sarki ne a garinsu, don haka abinda zance fili nan ga mai doki, Allah ya bawa mai rabo sa'a!"

A wannan safiyar ta laraba dai, idanun Adam suka sami abincin da suka yi yunwarsa tsawon kwanaki, don dole ce tasa shi ya sake neman ganin Fadeelah kafin a fara zaman kotun, a cikin kwanaki hud'u kawai, kammaninta sun fara canjawa daga yadda ya ganta da farko, hasken farinta ya ragu sannan idanunta sun fara zurmawa cikin raminsu.

"Ki cire damuwa a ranki, komai zai tafi daidai da yardar Allah, zamu fuskance su kuma zamu yi nasara kinji?"

Babu yadda ya iya dole ya fad'a mata hakan cikin sigar lallashi, don ta fahimci duk irin k'arfin halin mutum akwai taraddadi ranar da zai fara shiga kotu a matsayin wanda ake zargi da kisa.

Bata kalle shi ba tace.

"Habiba tazo?"

Sai ya ya lumshe idonsa yana kallon yadda gashin idonta ya had'e dana k'asansa kamar a rufe suke, hakan ne kad'ai ya bashi damar iya kallonta hankali kwance.

"Kawu Ibrahim yace tazo, amma ban ganta ba."

Sai ta gyad'a kanta kawai alamun ta fahimta, sannan tayi shiru bata k'ara cewa komai ba.

Har ya mik'e tsaye sai kuma ya juyo ya kalle ta yace.

"Ina so ki yarda dani, kar ki bari duk abinda zaki ji daga bakin mutane ya raunana fatanki na samun nasara, baki da laifi don haka insha Allah zaki kub'uta."

Bata d'ago da kanta ba kuma bata ce komai ba haka ya juya ya fita, sannan mai tsaron da ya rako ta ya bata umarnin tashi don ana dab da fara zaman shari'ar a lokacin... Shari'ar data gujewa a baya, shari'ar dake shirin canja akalar rayuwarta.

***

Kotun ta cika ta kuma tunbatsa don har saida aka rufe k'ofa da wasu mutanen a waje. Zaune daga jerin wajen masu saurare, Kawu Ibrahim ne a gaba sai daga gefensa wasu daga cikin 'yan Babban gida masu irin ra'ayinsa a ciki har da Abdullahi daya zo tare dasu Mami, layi biyu bayansu kuma muk'arraban Kawu D'anjuma ne su Yahya, sulaimaman, da sauransu. Su Mami na daga bayansu ita da Aunty Hadiza da kuma Fatima wadda tayi tsuru-tsuru don har ga Allah ta shiga damuwar ganin Fadeelah a wannan matakin. A layi na k'arshe kuma, Nasir abokin aikin Adam ne daga can ma'aikatarsu wanda yazo a daren jiya a matsayin wakilin ma'aikatar.

Daga nan kuma duk mutanen Babban gida ne da kuma cikin Ikara mazansu da matansu kowa da irin abinda ke k'ulle a zuciyarsa.

Daga gaba teburin masu shari'ar kuma lauya Kutama ne zaune a gefensa da wasu k'ananan lauyoyin biyu masu taimaka masa.

Adam na zaune, daga gefensa kuma wani k'aramin lauyan gwamnati ne da kotun ta bashi don ya taimaka masa ta hanyar rubutu mai suna Jabir. Adam sanye yake cikin kaya na kowanne irin lauya amma sai ya fita daban da kowanne lauya dake cikin wajen, saboda yadda kalar hular ta kwanta akan fatarsa ta kuma fito da duk wata ilhama da kwarjininsa.

Zuciyarsa tayi nauyi ta kuma tsaida bugunta na wasu dakikai lokacin da aka shigo da Fadeelah cikin wajen, irin abinda yake gudu kenan gashi ya fara faruwa tun ba'a je koina ba, ina ga kuma ya bari sun fahimci juna?

Alkali Bashir Uba Ali (mai jagorantar shari'ar) ya shigo cikin kotun a daidai wannan lokacin, mai sanarwa ya d'aga muryarsa ya bada umarnin a mik'e da cewar zaman kotu ya fara kuma alk'ali ya zauna.

Bayan zamansa ne kuma, Alkalin yayi gyaran murya yace.

"Za'a iya zama, wannan shari'ar zata fara ne tsakanin masu shigar da k'ara da suka taru akan hakan da kuma wadda ake zargi Bintu Abubakar. Zamu iya farawa."

Bayan kowa ya zauna, Alk'ali ya juya ga Kutama yace.

"Shin masu shigar da k'ara suna da abinda zasu ce?"

Kutama ya mik'e tsaye a take.

"Kwarai ya maigirma mai shari'ah, kamar yadda kowa ya samu labari an shigar da wannan k'arar ne shekaru hud'u da suka wuce bisa zargin yarinyar dake zaune anan Bintu Abubakar wadda a lokacin shekarunta sun kai sha takwas akan kisan kakarta, ta hanyar sanya mata guba a cikin kokon da take dama mata a kullum safiya.

Amma k'arar bata kai ga isa mataki na gaba ba, sai yarinyar ta tsere a washegarin ranar da tayi kisan, anyi nemanta har zuwa garin Kano inda bayan bincike aka tabbatar da inda ta nufa kenan, kuma motar data hau d'in tayi hatsari a lokacin, amma aka samu? sab'ani kafin hukuma ta isa ma'aikatan asibitin suka sallameta bisa rashin sanin ainhin dalilin rabuwarta da gida.

Kuma tun daga wannan lokacin bata k'ara waiwayar gida ba, saida a bisa fad'in marik'anta, sunce ta samu gushewar tunani ne a dalilin gatsarin nata wanda babu wata kwakwakwarar shaida data nuna hakan, don a lokacin da aka ganta, da bakinta ta furta cewa ta gane kowa kuma ta san laifin da ake zarginta dashi."

Ya juyo da idonsa kad'an ya kalli Adam fuskarsa d'auke da murmushi.

"Hakan na nuna cewa tana sane da laifinta kenan, kuma tana guje masa ne tsawon wannan lokacin, ya mai girma mai shari'a, akwai tarin hujjojin dake tabbatar da aikatuwar laifin nata wanda zasu zo a gaba kad'an. Nagode."

Ya koma ya zauna, Alkali ya juyo kan Adam dake nazarin komai da dukkan wata kafa ta fuskarsa yace.

"Masu karewa suna da abinda zasu fad'a?"

A hankali Adam ya mik'e tsaye sannan muryarsa mai taushi ta shiga kunnen duk wani mahaluki dake wajen cikin nutsuwa.

"Ya mai shari'a, Bintu bata aikata laifin nan ba, bata kashe kakakarta ba kuma ba kuma bata tab'a samun ra'ayin kashe ta ba, wasu sunyi amfani da damarsu akanta ne sun isar da niyyarsu ta kashe kakar tata, wanda a gaba cikin wannan shari'ar zan fito da hakan insha Allah, saboda haka da muryar adalci nake kira da kar kotu tayi saurin yanke hukunci ga yarinyar da bata da laifin komai."

D'an wannan tak'aitaccen bayanin ya gamsar da Alkalin wanda har haka yasa ya gyad'a kansa sau d'aya sannan ya juya ga Kutama.

"Masu shigar da k'ara zasu cigaba?'

"Kwarai ya mai girma mai shari'a kamar yadda na fad'a a baya, akwai tarin hujjojin da zai sa kowanenmu ya yarda cewa wannan yarinyar dake zaune fuskarta na nuna kammani irin na salihan mutane, kwararriyar mai kisa ce ..."

"K'orafi ya mai shari'a."

Muryar Adam ta katse bayanin kutama.

Alkali ya gyad'a kansa.

"K'orafinka ya karb'u, bai kamata mai zargi ya tabbatar da abinda shari'a bata yanke hukunci akansa ba."

Kutama ya duk'a kansa kad'an sannan yace.

"Ina sanar da kotu cewa akwai hujoji na mutane da kuma abubuwa wanda zasu tabbatar da zargina, amma kafin in fara kawo komai, ina son kotu ta fara da mutanen da kisan ya faru a kewayensu don muji ta bakinsu."

Alkali ya gyad'a kai yana kallonsa.

"Zanso in kira shaida ta farko, Sadiya Muhammad wadda k'anwa ce ga mahaifin ita Bintun da ake zargi da kisan."

Daga cikin masu saurare, Sadiya ta mik'e ta taho wajen tsayuwar masu shaida.

Magatakarda yace. "Ki fad'i sunanki kuma ki fad'i kowacce kalma dalla-dalla don za'a rubuta."

Cikin muryar dake shaida zumud'i Sadiya tace.

"Sunans Sadiya Muhammad, k'anwa ga mahaifin Bintu marigayi. S-a-d-i-y-a M-u-h-a-m-m-a-d.

Kotun ta d'auki shiru a lokacin da ake rantsar da Sadiyan kafin ta k'araso ta tsaya.

"Sadiya ina son ki shaidawa kotu kina da aure ko baki dashi?" Kutama ya fad'a tsaye a gabanta.

"Bani da aure a halin yanzu, amma a baya nayi aure sau biyu na fito."

"A shekarun baya, lokacin da Bintu take tare da Hajiya kina gidan ko bakya nan."

"Ina gidan don ba'a fi shekara da mutuwar aure na ba a sannan."

"Hakan na nufin kin san irin alak'ar dake tsakanin Hajiya da Bintu kenan?"

"Kwarai na sani."

"Zaki iya fada mana wani abun?"

"Tun tasowar Bintu dama bata son Hajiyar mu, bisa tarbiyar da mahaifiyarta ta d'ora ta akai na k'in mu dangin ubanta saboda mun nuna cewa bata da asali sanda aka tashi auro ta, don hakan ko bayan da iyayenta suka mutu rik'onta ya dawo wajen Hajiyar da wannan akidar ta taho a ranta, kuma aka sami akasi Hajiya bata maida ita makarantar bokon da take zuwa ba saboda BABU ta yau da kullum.

Sai wannan abun ma ya k'ara d'arsa tsanar hajiyar a zuciyarta, shi yasa mamakina kad'an ne lokacin da aka ce ta kashe Hajiyar tunda tun a baya dama ba wata cikakkiyar tarbiyya ce da ita ba."

Fadeelah na daga can gefe idanunta kyam akan Sadiya, tana sauraren yadda take had'a karya da gaskiya waje guda tana tada wani sabon labari.

"Ta wace hanya kuke zargin ta kashe Hajiyar?"

Sadiya ta girgiza kanta.

"Ba zargi muke ba ai ranka ya dad'e, a cikin damun kokonta ta saka mata guba, tunda kowa ya san cewa tunda ta dawo gidan nan itace mai dama mata koko a kowacce safiya."

Kutama ya gyad'a kansa da murmushi yace.

"Kotu ta gode da wannan gudunmawar taki kwarai malama Sadiya."

Sai ya juya b'angaren Adam yace dashi.

"Your witness.."

Adam ya d'anyi shiru idanunsa na nazarin Sadiya daga inda yake kamar zai taso sai kuma ya girgiza kansa yace.

"Bani da tambaya akanta."

Hakan ya bawa kowa mamaki, Alkali ya kalle shi yace

"Baka da tambaya Barrister Adam?"

Ya sake girgiza kansa yace "Babu ya mai shari'a."

Da wani irin murmushi na k'eta kutama ya juya yace.

"Ina so kotu ta bani dama in gabatar da shaidata ta biyu ya mai shari'a."

"Kotu ta baka dama."

Kutama ya juya baya yace.

"Zan so in kira Sule wanda yake d'a ga wan Mahaifin Bintu."

Sule ya mik'e daga cikin mutane ya k'araso gaba, ya fad'i sunansa aka rantsar dashi sannan ya k'araso gaban Kutama.

"Sule, me zaka iya shaidawa kotu game da rasuwar Hajiya?"

Sule ya gyara tsayuwarsa sannan yace.

"A safiyar da Hajiya zata mutu ni ta bawa sak'o cewa in gayawa Bintu ta kai mata kokonta, kuma bayan ta had'a ta kai mata har gubar tayi aiki a jikinta, mu muka fara shiga d'akin dani dasu Salisu, sannan mu muka d'auke ta muka kaita har asibiti inda aka shaida mana cewa guba taci mai k'arfin gaske tayi sanadiyar mutuwar tata."

"Sule, a lokacin da kaje gayawa Bintu ta had'a kokon Hajiya me take yi?"

"Wankin kayanta take yi, kuma wankin ma da kyar ta karbe shi a ranar don har saida nasa baki sannan ta d'iba."

"A baya dama haka take yi?"

Sule ya girgiza kansa.

"Ko kad'an, ana bata zata tashi tayi."

Zuciyar Adam ta tabbatar masa da wani tunani a lokacin.

"Hakan na nufin a ranar bata yi niyyar wankin bane saboda ta riga ta shirya..."

"K'orafi ya mai shari'a." Muryar Adam ta katse kutama.

"Mai zargi yana kokarin bawa mai shaida sabon ra'ayi."

'K'orafi ya karb'u, lauya ya kiyaye."

Kutama ya sunkuyar da kansa sannan ya koma ga Sule.

"Sule a lokacin da kuka shiga d'akin, Bintu tana ciki?"

"Kwarai tana ciki don a gaban gawar ma muka same ta kuma idonta babu alamun tashin hankali balle hawaye."

Sai a lokacin da Sule ya fad'i haka ne sannan Fadeelah ta fahimci ma'anar kalaman Adam na d'azu.

...kar ki bari duk abinda zaki ji daga bakin mutane ya raunana fatanki na samun nasara, baki da laifi don haka insha Allah zaki kub'uta."

Kutama ya juya ga Alk'ali.

"Ina fatan kotu ta fahimci abinda hakan ke nufi, Bintu bata tab'a tunanin cewa wani zai shigo kafin ta tabbatar da mutuwar Hajiya har taje ta fad'a ba, shi yasa suka same ta a wannan yanayin na rashin alhini."

Ya juya ga Salisu yayi masa godiya sannan ya juyo ya kalli Adam yace.

"Your witness..."

A karo na biyu, Adam ya girgiza kansa sannan yace.

"Bani da tambaya akansa."

"Yayi kyau Barrister Adam, Dama gaskiya d'aya ce kuma a koina ba'a iya kalubalantarta."

Wannan maganar tasa kotun ta rud'e da hayaniya jama'a, Kutama ya jira har akasa surutun ya sassauta sannan ya kira shaidansa na gaba. Habiba.

Da kyar ta taso tana dogara sandanta aka rantsar da ita sannan ta tsaya.

"Hajiya Habiba, zaki iya gaya mana meye matsayinki a Babban gida?"

"Na'am?" Muryarta ta amsa a cikin kotun, Kutama ya sake maimaita mata tambayar a hankali.

"Ni matar wan mahaifinta ce."

"Ance mahaifin nata yana da yayye da yawa harda wanda ba uwa d'aya suke ba, shi wanda kike aure yaya alak'arsu take da mahaifin nata?"

"Uwarsu d'aya, shine d'a na biyu a wajen marigayiyar."

Ya gyad'a kansa alamun fahimta.

"Habiba kina a ina safiyar da Hajiya ta rasu?"

"Ina b'angarena ban ma fito da wuri ba sakamakon d'ana k'arami bashi da lafiya a lokacin, sai daga can naji hayaniya na lek'a aka ce dani wai Hajiya ce ta rasu."

"Me kika yi bayan nan?"

"Na tafi can b'angaren Hajiyar inda akace Bintun na can kuma ita ta saka mata guba a kokon data sha."

"Ance a ranar Bintu ta zarge ki da cewar ke kika had'a kokon ba ita ba."

"Wallahi k'arya take min ranka ya dad'e, na gaya maka ma ni ban ma fito da wuri a ranar ba kuma..."

"Kwantar da hankalinki Habiba, ai kowa anan yasa k'arya take miki, so nake kiyi tunani ki gaya mana shin akwai wani abu daya tab'a had'aku ne da har kike ganin zata iya dora miki wannan laifin."

"Eh ranka ya dade kowa ya san Bintu yarinya ce mai rashin kunya, to ni kuma a lokuta da yawa ina yawan kwab'arta akan hakan, kamar yadda dai marigayiya take k'okarin nusar da ita abubuwa a kullum, watakila saboda haka ne bayan ta kashe hajiyan, ni kuma ta nemi d'ora min wannan laifin."

Kutama ya gyada kansa.

"Na fahimta, bayan haknan akwai wani abu da zaki iya k'ara mana game da abinda kika sani?"

Habiba ta girgiza kanta da sauri.

"Allah ya sani ranka ya dad'e, ni ban fiye shiga harkar mutane ba, kowa zai min shaidar hakan, saboda haka ba zan iya cewa komai game da ita ba."

"Na fahimce ki Malama Habiba, na kuma fahimci irin abinda kike ji a yanzu, sharri bashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login