Showing 120001 words to 123000 words out of 153964 words

Chapter 41 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3776

yarinyar da a yanzu yake jin zai iya komai don kare ta.

Ya mik'a hannunsa na hagu ya tsiyaya cikon kofi na k'arshe daga k'aton kwalin lemon dake gabansa.

Jibi ne.

Jibi ne ranar daya maka ta k'arshe a wannan shari'ar, kuma baya fatan daga jibin nan daga 'yan kallo har Alkalin wani ya k'ara takawa cikin kotun nan da sunan shari'ar Babban gida, ya riga ya tsara cewa daga gobe zai tattara komai ya kuma rufe komai d'in, sannan ya yarda har cikin zuciyarsa Allah zai taimake shi akan hakan.

Ya kai kofin bakinsa, ya kurb'i lemon, sanyin ya ratsa cikin k'irjinsa, sannan ya maida idanunsa ya sake rufe su, d'aya bayan d'aya jan hasken dake cikin idanun ya shiga haska masa abinda zai faru a gobe, jigo a ciki sune...

Ikara, Kawu Ibrahim, Sule.. Anna!

Iya wad'annan sunayen kad'ai yake hangowa.

Bai san cewa har da nasa sunan a cikin wad'anda k'addara ta tanadar ba!

****

WASHEGARI, 9:00 AM, IKARA.

"Babu inda zaki."

Kawu D'anjuma ya maimaita hakan karo na uku tun bayan shigowar Sadiya wadda ke magiya akan ya barta ta koma Abuja gidan aikinta.

"In kinga kin bar garin nan, to tabbas an gama shari'ar nan ne kuma komai ya lafa."

Sadiya ta muskuta ta sake muskutawa, ba fa zai yiwu ba, ta ayyana a ranta. Yau kwanan maganin da ta karbo a wajen boka shida kenan kuma ya riga ya shaida mata in har ya kai wani satin ba zaiyi aiki ba sai dai ta dawo ta sake karb'ar wani.

Yo ina kuma taga wani kud'in bayan kusan duka abinda ta samu ta nad'o a gidan Hajiyar ta kai masa da alk'awarin in har ta samu ta ajiye k'ullin maganin da ya bata a makwancin Alhajin Hajiyar, to shikenan ba zai k'ara mararin wata mace a duniya ba sai ita, kuma ko bai saki Hajiyar ba, to tabbas ne ita sai ya aure ta.

Ta yaya kuwa zata zauna akan wata dokar Kawu D'anjuma tayi wasa da damarta, in har yana tunanin yadda ya tsaida abubuwa da yawa a gidan da wannan zancen nasa na sai 'bayan an gama shari'a, haka itama zai tsaida tata rayuwar to kuwa bai isa ba, yayanta ne shi amma a yanzu da take gab'ar cimma k'udirinta, bata tunanin ko ubanta ne ya fito daga kabarinsa ya hane ta zata saurare shi. Fassarar tunaninta d'aya ce da karin maganar... Tayi nisa bata jin kira.

Ta sake gyara zama.

"Kawu gaskiya wannan ba hukunci bane, Hajiya fa ta rasu tsawon shekaru kenan ba wai zaman makokin ake yanzu ba, don haka bai kamata kawai don ana shari'ar bincike ace za'a tsaida abubuwa ba ciki kuma har da aikina, mutanen nan ma ai sun min mutunci, yau watana d'aya da d'oriya fa kenan a gida, inda wasu ne da tuni sun nemi wata sun rabu dani. Ya kamata a duba gaskiya."

"To su nemi wata mana, ai ba su kad'ai ne gida a habujar ba, duk sanda kika koma ba zaki rasa wani wajen ba. Karki manta cewa tun da fari fa ni ba son wannan aikin naki nake ba."

Yana rufe baki kuwa karaf ta amsa.

"Kawu zancen son aiki yanzu bai taso ba, an riga an rufe maganar nan tun farkon tafiyata, jikina zan bautar ba na wani ba don haka ba ruwanku."

Kawu D'anjuman ya d'anyi jim! Ganin yadda ta amsa masa maganar gatse-gatse ba kamar yadda ta saba a baya ba. Sai ya gyad'a kansa kawai sannan ya k'ara jaddada maganarsa.

"Babu inda zaki sai an gama shari'ar nan Sadiya, inda ke wata mai hankalin ce ba sai an gaya miki ba, kishin mahaifiyar ki kad'ai ya isa yasa ki gane hakan, amma na fahimci tun bayan aurenki na biyu kwakwalwarki ta toshe, in banda duniya babu komai yanzu a gabanki."

Maganar tayi mata zafi duk kuwa da ta san hakan ne, amma sai ta kawar ta hanyar yin wani guntun murmushi kafin ta bashi amsar da ta shayar dashi mamaki.

"Ai kuwa k'arya ne ace bana kishin Hajiya wallahi, naga waye ma ya farfad'o da shari'ar in bani ba, ina ce ai daga Bintun har 'yaruwar tata ni na gano su a can Abujan, don haka kuwa in ba'a yabawa aikina ba ai ba'a zageshi ba. Sannan duk toshewar kwakwalwata Kawu ai ba ni na kai shari'ar nan kotu ba, bani nayi abin kunyar kai 'yar d'anuwana kotu ba, iyakata shaida. Sannan kuma na tabbata babu sunana a wad'anda za'a nunawa Alhaji (Tana nufin mahaifinsu) a matsayin masu tada husuma bayan ransa.

Tana fad'in haka ta mik'e, tayi hanyar fita, bata ko kalli fuskarsa ba dake cike da mamakin nuna masa ainihin halinta da tayi, dama biyayyar da take masa a da fiye da rabi saboda abin hannunsa ne ba wai matsayinsa na yayanta ba, a yadda take hango kanta a yanzu kuwa ita mai arzikin kanta ce. To meye ma? Ai manta wannan 'yar maganar zaiyi da zarar ta kawo Alhajinta a matsayin manemin aurenta.

A k'ofar d'akin taci karo da Yahya, sarai ta san zancen shari'a yazo yiwa Kawu D'anjuman don haka bata ko kalle shi ba ta zura wani kwancen takalmi mai tsini da Hajiyarta ta bata sannan ta nufi hanyar barin sashen, daga Bintu har Hajiyar da aka kashe yanzu basa gabanta... Wanda yake da rai ko kuma abin mora ai shi duniya ke yayi ta ayyana hakan a ranta tana tafe tana gurd'ewa saboda yadda tsinin takalmin ke shigewa cikin k'asa, lissafawa kawai take da taje d'aki zata buga wayar Hajiyar ta shaida mata gobe zata taho, zuwan da daga shi kuma sai dai ta dawo Ikara a d'aura mata aure ta koma a matsayin matar gida!

Kawu Yahya ya bita da kallo sannan ya tab'e baki ya juya. Yafi kowa jiran ranar da zata koma aikatau d'inta, don tun farko yana d'aya daga cikin wad'anda suka sa baki Kawu Danjuman ya barta ta tafi, ba don komai ba sai irin uwar masifar dake tsakaninta da matarsa, kullum babu ranar da zata zo ta fad'i ba'aji kansu ba, sau da yawa ma har da dambe. amma kuma duk da haka shiri suke sosai da Babbar 'yarsa, don a lokacin da yarinyar ke tashi, matar tasa ta yar da ita saboda kunyar 'yar fari, ita Sadiyan ce ta d'auketa ta kula da ita har ta girma, don ko aure tayi da ita take tafiya.

Yanzu kuma dawowarta ance masa ta koyo wasu k'arin d'abi'un na wulakanci, don ance tunda tazo ko ruwan gidan bata sha sai na roba, kud'i ne tazo dasu mak'il a cikin jakarta wanda yake da tabbacin sato su tayi don ba'a biyan 'yan aiki irin haka. Fatansa d'aya ace yanzu Kawu D'anjuman ya bata izinin tafiya ne tun kafin taja ra'ayin 'yarsa tace itama zata bi ta.

Kamar zai shiga ciki kuma sai ya fasa, zuciyarsa ta bashi shawarar yabi bayanta yaji abinda ya faru, don haka ya maida takalmansa ya juya.

****

10:00 AM, IKARA.

K'arfe goma daidai Sa'id ya faka motar daya tuko daga cikin garin Zariya jikin katangar Babban gida. Babu bata lokaci Adam ya bud'e murfin k'ofarta ya fito.

Ya kalli k'ofar shiga Babban gidan wadda ke wangale kar mai yi musu maraba, idonsa kuma ya kai kan samarin dake zaune a baranda wad'anda suka taso ganin tsayawarsu, sannan ya juya ya kalli k'atuwar motar 'yansandan da suka taho da ita, wadda ke k"ok'arin tsayawa a bayansu.

A yau komai zai k'are.

Ya ayyana hakan a zuciyarsa.

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

39

(&_&)

Babbar kotun dake cikin jihar Zariya ta zauna akan shari'ar da Iyalan Malam Idris Musa suka shigar game da k'arar 'yar d'anuwansu Bintu Abubakar Idris bisa zarginta da kashe mahaifiyarsu Hajiya Balaraba.

Bayan duk wasu bayanai na gabatarwa, Alk'ali ya d'ago ya kalli Adam yayi magana cikin harshen turanci.

"The defense may begin to present its case."

Tafintan dake gefe yana fassara dukkan magana daga turanci zuwa Hausa, Hausa zuwa turanci ya fassara hakan kamar yadda ya saba.

"Lauyan mai karewa zai iya fara gabatar da hujjoji da kuma shaidunsa."

Adam ya mik'e a hankali daga mazauninsa ya taho gaban Alk'alin, takunsa cikin nutsuwa yake sannan babu abinda mai kallo zai iya tsintowa a yanayinsa, ya tsaya a daidai saitin gaban alk'alin sanda gefen idonsa ya hango Fadeelah wadda ke zaune daga can k'arshe a teburin magatakarda, kanta a sunkuye yake tana kallon yatsunta, don haka bai hango idanunta ba, wad'annan idanun da suka yi barazanar karya zuciyarsa a d'azu daya fara ganinta...

Yana tsaye daga saman benen koton a lokacin bayan ya gujewa masu neman rahoton dake ta bibiyarsa tun daga wajensu Kawu Ibrahim, shi da Jabir ne, (mataimakin aikinsa) wanda ke nuna musa sakamakon bincikar lafiyar kwakwalwar Anna da yasa ayi a wani asibitin kud'i.

Dama tun dawowarsa Jabir ya shaida masa cewa yanzu case d'in Fadeelah yayi girman da har ya isa kunnen Media kuma an samu k'arin wasu gidajen rediyo da suka nuna ra'ayinsu akan shari'ar har ma sun samu sunyi magana da Kutama, saura shi suke nema ido rufe a yanzu.

Ba sauraran Jabir yake sosai a lokacin ba, rabin hankalinsa na kan gate d'in shigowa kotun da yake iya hangowa daga inda suke tsaye, saboda kamar kowa a wajen shima jiran k'arasowar Fadeelah yake yi.

"A k'arshe dai babu wani ciwo da result d'in yake nunawa, don haka su sun fi danganta matsalarta da rashin kulawa kawai, amma ni a nawa hangen ina ganin kamar har da matsalar aljanu ( spritual problem) da kuma rashin samun fahimtar hakan daga 'yanuwanta balle har a bata agaji."

Jabir ya k'arashe zancensa daidai sanda motar dake d'auke da tambarin kurkukun mata ta karyo kwana cikin wajen, ba shiri ya sakarwa Jabir takardun hannunsa yace masa ya jirashi sannan ya juya yayi hanyar sauka k'asa.

Yallab'ai me zaka iya cewa game da yadda wannan shari'ar ke tafiya?

...kana ganin zaka yi nasara bayan duk shaidun da aka gabatar?..

...me zaka iya cewa akan yau da zaka karb'i shari'ar?

Yallab'ai da gaske ne akwai wata alak'a tsakaninka da wadda ake zargi da laifin?

....zaka iya gaya mana meye ainihin dalilinka na karb'ar wannan shari'ar?..

Masu neman rahoton suka yanyame shi daga k'afar benen daya sauko, bai ko saurare su ba ya ratsa ta cikin su ya nufi inda motar kurkukun ke kokarin parking, sai a sannan suma suka kula da hakan saboda haka suka rufa masa baya da sauri amma cikin sa'a sai masu tsaron da suka fito daga cikin motar suka tsaida su da tunanin Fadeelan zasu je yiwa magana.

Amma shi ya samu wuce su har zuwa gabanta, a lokacin ta fito daga motar kanta a sunkuye tana k'okarin cire takalmin k'afarta daya hard'e cikin riga, don haka mai tsaron dake rik'e da ita ce ta fara yi masa magana.

"Yallab'ai ba'a a bamu damar kowa yayi mata magana ba don haka ciki kawai zamu shiga da ita."

Ta fad'i haka ne bayan karanta Id-card d'in dake sak'ale a wuyansa wanda ya nuna mata shi lauya ne, sai dai shi idonsa na kan Fadeelan don haka yaga sanda ta lura da tsaiwarsa a gabanta da kuma sanda ta d'ago gabad'aya ta kalle shi.

Abinda yake hasashe ne ya tabbata a lokacin... Idanunta sunyi fari kuma sun d'ashe d'as! Babu abinda ya iya gani a cikinsu sai tashin hankali, rud'ani da kuma firgici, sannan a lokacin tana kallonsa da dukkan wani mamaki na duniya, don haka in ma tayi murnar ganinsa wad'annan abubuwan sun danne hakan.

Ya had'iye yawu cikin mak'ogwaronsa sanda ya lura duk wani mahaluki dake cikin kotun ya d'ora hankalinsa a kansa, tun daga d'azun bai sake ganinta ba kuma basu yi wata maganar kirki ba saboda hayaniyar mutane da kuma shirye-shiryen zaman kotun, amma tun daga d'azun bai san sau nawa zuciyarsa ta rantse sai ya d'auki fansa akan Kutama ba, sai ya kuntata masa kamar yadda ya yiwa idanun da ya shiga kowanne k'alubale na rayuwarsa ya fito tare dasu. Ya gyara tsaiwarsa daidai saitin alk'alin, sannan ya d'anyi gyaran murya kad'an ya fara magana.

"Ya mai girma mai shari'ah, daga lokacin da aka shigar da k'arar nan zuwa yanzu, mun saurari hujjoji daga b'angaren masu shigar da k'ara da kuma bayanai daga b'angaren shaidun da aka gabatar, wanda dukkaninsu suna tafiya ne kan irin tunanin abokin aikina, saboda haka duk wasu maganganu dashi ko shaidunsa suka tsaya anan suka fad'a, sunyi su ne bisa rashin sanin gaskiyar lamarin nan da kuma ainihin wanda ke bayan laifin.

A yau zan fito da komai kuma zan baiyanawa kotu yadda rasuwar marigayiya ta kasance da kuma wanda ke da alhakin wannan kisan. Ba kamar yadda kotu ta d'auka bane tun farkon shari'ar nan, babu laifin Bintu wadda Lauyan masu shigar da k'ara ke zargi ko kuma wadda ake zargi daga baya wato Habiba."

Ba 'yan kallo ba hatta sauran lauyoyin dake zaune sai da suka k'ara tsaida idonsu akansa jin ysla ambaci cewa babu laifin Habiba.

Adam ya d'an murza yatsunsa na dama sannan ya fad'i abinda ya kwana ya tashi dashi a ransa.

"Ina neman Kotu ta bani damar gabatar da shaiduna."

Alk'ali ya gyad'a kansa.

"Kotu ta baka dama."

"Zanso in kira Bintu Abubakar a matsayin shaidata ta farko."

Sunan ya fito kai tsaye kuma ya daki tunanin kowa a wajen, hakan ya sanya tashin 'yan maganganu daga wajen 'yan kallo, hatta Alk'alin saida ya gyara zaman gilashinsa ya k'ara kallonsa.

"Tana cikin jerin sunayen shaidun da ka bayar?"

"Sunanta yana ciki ya mai girma mai shari'ah."

Alk'ali ya gyad'a kansa.

"Kotu ta baka dama."

Sai kawai ya juya ya kalli inda Fadeelan ke zaune, idanun da yake jin ciwonsu na tsaye suna kallonsa amma wannan karon fayau suke, babu mamaki ko rud'ani irin na sauran mutanen dake bayanta, bata san zai kirata ba amma bata tsorata ba, ya lura ta dad'e da cire kalmar tsoro daga zuciyarta tun daga lokacin da ta karb'i shari'ar nan..._ranar da ya fara ganinta, sanda ta ture mamakin ganinsa tayi masa bayanin komai dalla-dalla, da kuma ranar da za'a fara zaman kotun, sanda yaje lallashinta a matsayin wadda zata fara shiga kotu da zargin kisa, amma bud'ar bakinta tambayarsa kawai tayi 'Habiba tazo?'

Fadeelah ta mik'e daga inda take zaune, zuciyarta a dake ta nufi wajen tsayuwar masu shaida.

Magatakarda yace. "Ki fad'i sunanki kuma ki fad'i kowacce kalma dalla-dalla don za'a rubuta."

Idanunta na sunkuye amma muryarta a tsaye kyam! tace.

"Bintu Abubakar, _B-i-n-t-u A-b-u-b-a-k-a-r_

Kotun ta d'auki shiru a lokacin da ake rantsar da ita, mafi yawan mutane daga cikin 'yan kallo hannayensu motsi suke na k'aguwa a fara shari'ar. Daga teburin zaman lauyoyi kuwa Kutama ya kalli mataimakinsa suka yi murmushi a tare.

Adam ya matsa jikin akwatin da take tsaye bayan gama rantsuwar, amon muryarsa a tausashe fiye da k'aidar yadda yake ya fara magana.

"Na san zuciyarki tana cikin wani irin hali yanzu Bintu, rayuwarki ta hargitse kuma an k'untata miki ta hanyoyi da dama akan laifin da baki aikata ba, na san cewa kin shiga wata mummunar rayuwar da baki tab'a sani ba akan zargi kawai, an saka ki..."

"K'orafi ya mai shari'a!" Muryar Kutama ta karad'e wajen, idanun kowa ya juya kansa amma banda na Adam da Fadeelah.

"Lauyan mai karewa yana b'atawa kotu lokaci da kalaman da basu da amfani."

Alk'ali ya girgiza kansa.

"K'orafi bai karb'u ba."

Adam bai jira zaunawar Kutama ba ya cigaba.

"Kar ki damu kanki, wannan shar'iar gabad'aya an fara ta ne don a wanke ki daga zargin nan, sannan mafi yawan mutanen da kike gani anan..."

Yatsansa d'aya ya nuna sama sannan yayi alamun zagaye, ma'ana gabad'aya kotun.

"..sunzo ne don ganin kin fita daga wannan halin kin samun 'yancinki na rayuwa tamakar a baya. Wasu 'yan kad'an ne kawai da suka yiwa lamarin wata fahimta suke tunanin akasin hakan, amma ba wani abu ne babba ba, tunda an bamu damar magana yanzu zamu fahimtar dasu gaskiyar komai, zamu gyara musu tunaninsu su san cewa baki da laifi kuma ba zaki iya aikata irin wannan lafin ba..."

Ya d'anyi shiru yana kallonta, yana kallon yadda maganganunsa suke aiki a fuskarta kafin yace.

"Ina so ki kwantar da hankalinki ki bawa kotu amsar komai dalla-dalla kuma kamar yadda kika sani, ki sani cewa duk abinda kika canja komai k'ank'antarsa kotu zata iya ganewa kuma zai iya zame mana k'alubale wajen ganar da mutanen nan gaskiyar labarinki."

Ya rufe bakinsa da 'yan sakanni kafin muryarta ta fito, kuma a cikin amon muryar daga Adam har Alk'ali suka tsinto nasarar amfanin da maganganunsa suka yi.

"Zan fad'i komai kamar yadda yake kuma na sanshi, ban taba gayawa kowa k'arya akan shari'ar nan ba kuma insha Allah ba zan fara yanzu ba."

Adam ya d'an juya ya kalli yanayin fuskar Alk'alin sannan ya cigaba.

"Zaki iya fara gayawa kotu me ye alak'ar ki da marigayiya Hajiya Balaraba?"

Fadeelah ta gyad'a kai har yanzu idanunta na kallon yatsunta tace.

"Ni 'yar d'anta na hud'u ce, ma'ana ni jikarta ce."

"A wajenta kike zaune? Ko kuwa sai bayan wani lokaci kika koma?"

"Sai bayan rasuwar mahaifina da aka raba gado sannan na koma wajenta."

Muryarta har yanzu a tsaye take sai dai da alamun sassauci.

Daga cikin 'yan kallo, Mairo ta d'auke kwalla da hannun hijabinta, k'ok'ari take sosai kar kukan daya taru a fal a k'irjinta ya fito fili.

"A lokacin kina da shekaru nawa?"

"Na shiga shekara ta goma sha hud'u."

"Yaya alak'arku da ita take bayan kin koma wajenta?"

"Tun kafin in koma wajenta, Hajiya bata k'aunata a dalilin rashin sonta da mahaifiyata tun farko, don haka bayan na koma wajenta hakan bai canja ba."

"Bai canja ba ta yaya?"

"Ta yarda har ta yanke karatuna da shekara biyu ina zaune a gida ba abinda nake sai hidimarta da ta duk wanda ya rab'e ta."

Adam ya had'iye wani guntun yawu kafin yace.

"Me ya faru ranar da Hajiya ta rasu?"

Tiryan-tiryan Fadeelah ta shiga zaiyano duk wani abu da kwakwalwarta zata iya tunawa daya faru a wannan ranar da ta zama sanadin tarwatsa rayuwarta. Shirun kotun ya amsa da yadda kowa yayi tsit! yana sauraronta.

Adam ya gyad'a kansa bayan ta kai k'arshe, idonsa na kallon dogwayen gashin idonta yace.

"A rayuwar zamanki ta gidan, na tabbata zaki san gabad'aya mutanen cikin Babban gida da kuma iya wad'anda Hajiya tafi mu'amala dasu. Haka ne?"

Fadeelah ta gyad'a kanta.

"Bayan Aunty Sadiya da take 'yarta, Hajiya tafi shiri da jikokinta akan matan gidan."

"Zaki iya lissafo sunayen wasu daga cikinsu."

Ta sake gyad'a kai.

"Akwai su yaya Fatima, Hadiza, Jamila, Abu, Nafisa da duk sauran irin sa'anninsu da suka yi aure. A maza kuma akwai Salisu, Auwal, Sa'id, Yakubu, Amadu da kuma yaya Sule wanda kullum yana tare da ita."

An zo gab'ar, an zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login