Showing 102001 words to 105000 words out of 153964 words

Chapter 35 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3811

kanta alkawarin cewa sai ta tarwatsa rayuwar Sadiq kamar yadda ya tarwatsa tata itama.

Sai ta hargitsa shi ta raba shi da duk wani sukunin rayuwa, sai dai hakan zai zo ne a gaba don yanzu ba ta shi take yi ba ko kad'an, ta 'yar'uwarta take. Duk da har yanzu basu yi wani had'uwar kirki da ita ba amma hankalinta a tashe yake kamar kowa, kowa d'in da bai had'a da jama'ar Babban gida ba, wad'anda a gaban idonta suke kafa hira ana rahar yadda shari'ar ke kai musu, don hatta labari ya fara yawo a cikin gari cewa an kusa yankewa Bintu hukuncin kisa itama, saboda a wannan d'an tsukin Kutama ya firfito da hujjojin da ko alk'alin ya fara gamsuwa dashi.

Yadda hankalin kowa ya tashi haka ma na Fadeelah ya fara rawa ganin yadda komai ya karkata d'aya bangaren, hakan yasa ta ture komai ta tambayi Adam d'in a wata rana da yaje ganinta.

Saboda kamar k'aida ya mayar da zuwa dubata cikin kowanne sati, har ya zama itama ta kan k'irga kwanakin da zasu kai ga zuwan nasa saboda ta sami kayan amfani... Zaman cikin kurkukun bai canja daga komai ba, amma rayuwarta a cikinsa ta canja dalilin kulawar da take samu daga Adam, bata da matsalar abin ci a yanzu ko ko na abin sha, sannan bata ko ciwon kai balle zazzabin saurayen da basa damunta a yanzu, magungunan komai tana dasu hatta vitamin C wannan, Adam ya canja mata komai ya kuma sauk'ak'a mata zaman wajen, hakan ya k'ara masa matsayi sosai a idanun su Mami har ma da Kawu Ibrahim a duk ganin da zasu yi mata ranar zaman kotun, amma ita a ranta ta yarda cewa yana kyautata mata ne kawai don amfanin kansa, saboda yayi ya rabu da shari'arta kamar yadda ya fad'a.

"Kin manta me na fad'a miki?" Lallausar muryarsa ta tambaya maimakon ya bata amsar abinda ta tambaye shi d'in.

Yana zaune daga kujerar tsallaken teburin data raba su, hannunsa rik'e da wata 'yar karamar jotter da yake d'iban bayanin wani abu da ya tambayeta game da Hajiya mai rasuwa. Tun zamansa a wajen sau d'ay????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? a ta kalle shi, a yanzu wani irin kwantaccen saje ya fito a kowanne gefe na fuskarsa, hakan ya fallasa mata cewar yawan aiki ya rage masa lokacin kula da kansa, hasken d'akin kuma ya k'ara fito da bak'in wannan gashin nasa da yake a taje kullum, a lokacin taji kamar ta tasho taje tasa hannu ta barbarza shi ya koma kamar yadda yake lokacin had'uwarta dashi, sannan ta d'auko mudubi ta haska masa kansa a ciki, watakila hakan zai sa ya bud'i baki ya gaya mata cewa shine dai Adam d'in da ta sani a da.

"Tun kafin a fara komai na gaya miki cewa mutanen nan sun tara isasshiyar shaida a hannunsu, so bai kamata kema ki biyewa mutane a tunaninsu ba, wannan duk barazana ce kawai lauyansu yake yi akan abinda suka bashi, na kusa gyara masa tunaninsa."

Ya fad'i hakan ne a hankali yana lumshe idanunsa, wani irin bacci ne a idonsa tun lokacin da muryarta ta fara yi masa bayanin daya tambayeta, gajiyar da yake ciki ta salallab'o ta rufe shi don ya manta yaushe rabonsa da bacci a cikin kwana biyun nan da shari'ar ke shirin dawowa hannunsa, tsabar yawan aikin da yake yi da kuma had'e- had'en bincikensa yasa ya ture bacci daga cikin priority list d'insa.. Ya riga ya zama addicted da yawan aikin dake gabansa shi yasa rashin baccin ma baya damunsa.

Fadeelah ta cukwuikuye ledar kayayyakin da ya kawo mata, sannan tace.

"Kana tunanin za'a k'ara wata guda ana cigaba da shari'ar?"

Ya sake lumshe idonsa.

"Komai yana hannun Allah, amma a yanzu da shariar zata dawo hannuna... Ba zan ja da nisa ba, zan fito da komai a d'an k'ank'anin lokaci insha Allah."

"Me kake nufi da shari'ar zata dawo hannuka?"

"Lauyansu ya gama fito da duk shaidunsa, yanzu turn d'inmu ne, mu zamu yi leading shari'ar."

Yadda ya furta kalmar 'Mu' d'in ta fito kamar lokacin da suke tutorial d'in nan ne, sannan ya bada ma'ana kamar ita dashi sun zama team a yanzu. Ta rasa tunanin cewa Adam ne zaiyi leading shari'ar ya sata jin sassauci a zuciyarta ko kuma yadda ya had'e shi da ita cikin jimla guda ne.

Tunaninta ya shiga lalube kan wane irin shaidu zai gabatar amma muryarsa ta katse ta... Muryarsa da ta saba da ita a yanzu.

"Mu cigaba?" Ya tambaya.

Sai ta sake cukwuikuye hannun ledar sannan ta cigaba da abinda take gaya masa kafin tayi tambayar data katse su.

"Bayan haka, akwai ranar da Inna Saratu ta aike ni Babban gida in kaiwa Hajiya goro, bani da wani wayo a lokacin sosai amma ban so zuwa ba, saboda ko tare da ita muka je a gaban idonta ma masu zagina da habaici Allah yayi yawa dasu.

Mutum na farko dana fara gani kafin in kai b'angaren Hajia Aunty Sadiya ce, ta fito da tulin wankinta tana yi tana biyo wasu wak'okin hausa, tana ganina tace inzo in tayata wai ba don kar na mata jagwalgwalo bama da ta bar min gabad'aya..."

Adam saurarenta kawai yake yi amma baya fahimtar ma'anar abinda take cewa, jin muryarta yake kamar sarewar dake busawa a hankali tana kwad'aita masa baccin da yayi kewarsa tsawon kwanaki biyu.

"...Sai muka fi kusan awa guda muna yi kafin ta saka ni in shanya mata, daga nan na hadu da Aunty Saratu matar Kawu Nura kafin k'arasa wajen Hajiyar, ta aike ni can Kasuwar rana in siyo mata kayan abinci, tafiya mai nisa ce tsakanin nan da kasuwar ga rana, ga k'ank'ata ta, amma bata duba komai ba ta tura ni, na tafi na b'ata don ban gane hanyar dawowa ba sai kusan yamma, hankalin Aunty saratu ya tashi akayi ta nema na.

Masu neman nawa sun tafi ni kuma na dawo na shiga na kai mata, kuma ko a jikinta tace in ajiye nan k'ofar d'akinta. Daga nan nayi wajen Hajiya, ina ta sauri inje in kai mata goron dake k'ulle a jikina kafin wani ya sake ganina, hakan yasa naci karo da Yaya Sule a zauren shiga wajen nata, ya danno wani zagi sanda ya damk'o wuyana ya d'aga ni har sama..."

Jin yadda take ta bayani ba tare da yace komai kamar da farko ba yasa ta d'ago da kanta ta kalle shi, mamaki ya dirar mata a lokaci d'aya sannan ta zare ido tana kallonsa...

Ya jingina kansa baya kad'an da kujerar da yake zaune, ya karkata fuskarsa, ya rufe idonsa, dogwayen gashin idon sun bi sun kwanta luff akan junansu sannan numfashinsa na fita a hankali...

Bacci yake yi!

****


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

*33*

*(&_&)*

Bata san a wane irin yanayi motar ke tafiya ba don babu taga ko guda d'aya da zata nuna mata hakan, saboda haka ne ma bata san wace irin rayuwa ce ke gudana a waje ba, wannan wajen da a kodayaushe ke haskawa cikin mafarkinta.

Ta juya b'angaren hagu ta kalli sauran fasinjojin dake tare da ita, kamar yadda idanunta suka shaida mata ne tun farkon shigowarta.. Babu ko mai kamar Habiba a cikinsu balle ita kanta, ta gefenta wata Babbar mace ce mai d'aurarriyar fuska, akwai wasu mata biyu da fuskar su ke nuna tsoro da kuma tashin hankali kamar kusan duk sauran dake cikin motar.

Daga can jikin k'ofar motar idonta ya kai kan wata k'aramar yarinya bak'a mai manyan ido tana ta share hawayen dake zarya a fuskarta, a k'iyasinta baza tace yarinyar nan ta wuce shekaru sha uku ba amma ta san dole ne ta gota hakan tunda har mummunar k'addara ta jefo ta cikin wannan yanayin da take kan hanyar zuwa wajen da za'a tsareta kamar dabba.

Ko kad'an bata damu da sanin abinda ya kawo yarinyar ba balle sauran, saboda ta yarda kamar yadda k'addara ta jefo ta nan haka ma kowannensu zai iya tsintar kansa a ciki, damuwarta d'aya ce, wane irin kallo su suke mata?

Ta juyar da kanta gefe a hankali ta kalli fuskarta a jikin bak'in fentin motar, dishi-dishi inuwar fuskar me kawai ya fito don haka bata san wane irin yanayi ke jiki ba, wane irin yanayi ne ya sauka a jikinta tun daga lokacin da wani mutum ya shigo cikin d'an k'aramin cell d'inta a wata safiya.

"Kece Bintu Abubakar?"

"Eh." Ta amsa daga can k'asa inda take tsugunne.

"Bisa umarnin da aka yanke jiya a wannan koton za'a maida ke cikin kurkuku sai lokutan da za'a zauna shari'arki sannan za'a dinga kawo ki nan."

Maganar ta fito kamar a mafarki, ta kasa bada ma'ana a cikin kanta... Wai za'a kaita kurkuku, ta yaya za'a kaita kurkuku? Wata mace sanye da kayan masu tsaro da suka shigo tare ta nufo inda take ta mik'ar da ita, al'amarin yayi mata girma a cikn kanta, taji bangwayen cell d'in suna shirin had'ewa da ita.

"Ke kad'ai kin isa bama buk'atar tarkacenki."

Mutumin ya sake fad'a yana kallon ledar kayayyakinta dake ajiye a gefe, matar ta shiga k'ok'arin saka mata ankwa, tunaninta ya sake kwancewa, ta fahimci a sannan yake nufin za'a tafi da ita.

"Saboda me za'a kaini prison? Me yasa baza'a barni anan har a k'arasa shari'ar ba? Laifin me akace na sake yi?"

Ta jero tambayoyin tana kallonsa da dukkan wata ma'anar rud'ani.

"Hajiya laifin da ake zarginki dai shine, kuma ai ke kin ma dad'e anan akan wasu, k'aidar kotun nan zama in ya wuce biyu kurkuku ake tura mitum saboda bamu da waje da yawa, amma ke wajen zama biyar fa akayi akanki kina nan.."

Ya fad'a yana kallon cikin folder dake rik'e a hannunsa, zama biyar! Zama biyar d'in da lauyansu Kawu danjuma ya gama fito da duk shaidunsa, Wannan kalmar kad'ai ita fahimtar da ita cewa da akwai ayar tambaya akan wannan hukuncin, in ba haka ba me yasa sai da Adam baya nan hakan zai faru?

"Lauya na ya sani? Kun fad'awa 'yanuwana?"

Yayi wani guntun murmurshi.

"Koto ce ke da hakki akanki yanzu Hajiya ba wai 'yanuwanki ba, don haka in sun zo zasu sani, sannan lauyanki dole a gaya masa mana in ya dawo, don ina zai dinga samunki in ba can ba."

Matar ta gama saka mata ankwar sannan ta cafki saman hannunta alamun ta fara tafiya, sai ta juya ta sake kallonsa.

"Dan Allah malam ka ara min wayarka inyi kira minti d'aya dan Allah."

Guntun murmushinsa ya karu a sannan.

"Hajiya da alama kin manta matsayinki anan ne, waya gaya miki?kina damar 'yancin kira? Sannan ko za'a barki ai sai da sharad'ai, ba wai in baki waya kamar a titi ba."

Ta sake girgiza kai ta a kallonsa.

"Dan Allah minti d'aya kawai zan kira 'yanuwana."

Ya girgiza kansa shima.

"Na gaya miki za'a sanar da 'yanuwanki..."

Ya kalli matar dake rik'e da ita.

"Hadiza, ja ta muje."

Kafin ta sake wata magana matar taja hannunta zuwa wajen cell d'in, ta wata doguwar hanyar daban da inda ake bi da ita ganin bak'i suka bi, don haka idonta ya gane mata tarin cells a jere kowanne cunkushe da mutane hud'u ko sama da haka, akwai na mata daban da kuma na maza, ashe da mutane da yawa a wajen bata sani ba? Wani irin kokari Kawu sulaiman yayi har aka bata wannan cell d'in ita kad'ai ba tare da kowa ba? ihu da maganganu suka yi ta fitowa daga kowanne cell da suke wucewa.

"Yallab'ai an sallame ta ne?..."

"Oga mu kuma fa? Ya za'ayi ne?"

"Baby, prison za'a kaiki, zan zo in fitar dake..."

Rikicewarta bata bari ta fahimci dukkan abinda suke cewa ba. Wannan bak'ar motar rufaffiya na jira a harabar kotun sanda suka fita, ta juya ta sake kallon mutumin.

"Dan Allah yallab'ai ka taimaka min in kira 'yanuwana dan Allah."

Bata san wane irin tunani ne ya canja ra'ayinsa ba, don tsayawa kawai yayi ya d'an kalleta na wani lokaci sannan yace.

"Okay, amma minti d'ayan kawai da kika ce, Hadiza juyo da ita."

Ya fad'i hakan ne don kar sauran securites d'in dake can jikin motar su hango su, ya zaro wata 'yar k'aramar waya daga aljihunsa ya mik'o mata.

Sai dai tana karb'ar wayar, wani tunanin ya dirar mata... Wa zata kira? Daddy zata kira ta gaya masa har Mami taji hankalinta ya k'ara tashi ko kuma Kawu Ibrahim zata k'ara rikitawa ta gaya masa komai ya cigaba da cakud'ewa? Me zai yi a yanzun da Adam baya nan? Wa zai zo ma ya tunkara?

Adam kad'ai shine wanda ya kamata ta kira, shi kad'ai ne zai iya wani abin a yanzu amma baya nan kuma bata da numbersa kamar yadda ta tabbatar wannan karamin ma'aikacin ma bashi da ita, in har za'a samu sai a wajen manya irinsu Kutama ko wanda shari'ar tata ta shafe su, ta juya a hankali ta kalli motar dake tsaye ana shigar da wasu matan ciki, sannan mutumin dake tsaye a gabanta yana jiran wayarsa... Babu wannan lokacin, sai ta girgiza kanta kawai sannan ta mik'a masa wayar.

"Na fasa, na gode."

Tafiyar cikin motar mik'ak'iya ce da bata da niyyar k'arewa, ga zafin injin bodin da suke zaune ga kuma warin man fetur wanda ya had'e dana jikin matan dake gefenta, amma Fadeelah bata damu da hakan ba, ta riga ta d'auke tunaninta dama kwakwalwarta baki d'aya daga cikin motar, ta tafi can wani lokaci baya, wasu zamaninnika da suka shud'e....

Tana zaune Inna saratu na yi mata kitso a tsakar gidansu, bata kai shekaru goma ba a lokacin, yayin da innarta ke ta zarya tsakanin kicin da inda suke alamun girki take yi, Mairo ta shigo rik'e da alqur'ani, ta tashi ta tafi da gudu ta rungumeta, kin siyo min yaya? Kin siyo? Ta tambaya tana tsalle a gabanta, Mairo tace ba'a samu ba Bintu mai siyarwar bata zo ba... Mairo! Inna saratu ta kira sunanta daga can inda take zaune, sai tayi murmushi sannan ta zaro wasu kayan?wasa na k'asa daga cikin hijabinta...

Tana tsaye a cikin ofishin Principal d'in makarantarsu na primary, Yarinyar tana da mutuk'ar k'okari Alhaji, Principal d'in ke fad'awa Babanta dake zaune a kujerar gabansa, Shi yasa muka ce ba sai tayi aji na biyar ba daga na hud'un ma zata iya yin jarabawar shiga sakandire, Babanta ya juyo ya kalle ta fuskarsa d'auke da murmushi na alfahari...

Suna tafe ita da Mairo akan wata hanya da babu mutane sosai, Tsaya anan ina zuwa, Mairo ta fad'a sannan tayi gaba, tabi inda ta nufa da kallo, wani saurayi ne tsaye sanye da fararen kaya, hasken yammacin ya haska manyan kyau na fuskarsa, da isar Mairo gabansa ya mik'o hannayensa duka biyun ya kamo nata, sai ta juya bayanta da sauri ga barin kallonsu...

Tana lek'e ta tagar d'akin Mairo, Mairo na zaune a gefen katifarta tana rusar kuka yayin da jamila k'awarta ke rarrashinta a gefe, Na san yaya Aliyu yana da kirki kuma yana da halaye masu kyau amma wallahi Jamila bana sonsa a matsayin mijina Sadiq kad'ai nake so, Jamila ta kalle ta sannan tace, Baki tsane shi ba kenan?, Mairo ta girgiza kanta, Ban tsane shi ba, matsayin da ake k'ok'arin bashi a rayuwata kawai na tsana...

Tana kwance a wani d'aki mai cike da mutane, hawaye na bin fuskarta yana jik'a filon da take kwance, hannunta na hagu d'aure da allurar k'arin ruwa, daga can gefe Inna saratu ce zaune a tsakiyar 'yanuwanta tana ta hawaye wasu na rarrashinta, wasu daga cikin mutanen d'akin suma kuka suke yi, wasu na jan carbi yayin da wasu ke karatun alqur'ani, wata tsohuwa ta shigo ta tsugunna a gaban Inna Saratu muryarta na rawa tace, sai hak'uri Saratu ki d'auki dangana irin ta mai sunanki uwargida a gun khalilullahi... Abubakar ya tafi (Babanta), yabi Amina (Innarta) muma duk nan jiranta muke....

Har Sule ne zai saka ki aiki ki kasa yi masa sauri? Hajiya Babba ke fad'a yayin da take tsugunne a gabanta, Ki zauna lak'aki magariba ta tarad dake saboda baki so yi ba? To kuwa yau baki da abinci dare, yadda kika kwana jiya haka yau ma zaki kwana in yaso yunwar ta kashe ki...

Tana tsugunne gaban Hajiya Babba sanda jikinta ke girgizawa bakinta na fitar da wannan farar kumfar, sannan idanunta a zare tana kallonta, kallo irin na zargi da mamaki...

Tana kwance a dandaryar kwaltar titi, wani azababben ciwo na amsawa a cikin kanta, jini na zuba ta hancinta, daga can gabanta wata k'aramar yarinya ce kwance cikin jini, rigarta ta yayyage sannan naman cinyarta na wani gefe ya zaftare, ta tuno sanda maman yarinyar ke biya mata addu'a a farkon tashin motarsu, _subhaanal-lathee sakhkhara lanaa haathaa.._ Wasu mutane suka zo suka durk'usa gaban yarinyar, d'aya daga cikinsu ya tambaya, Tana da rai? Yanzu muka kai mahaifiyarta waccan motar ta rasu! Idanunta suka rufe a hankali ta koma cikin nata ciwon...

Tana zaune cikin falon Hajiyar Daddy, suna tsintar wake ita da Ladi, Hajiyar na daga kujera tana cin wani dambun zogale da ladi tayi tana ta santi, Anya ladi ba zamu cire mangwaron tsakar gidan nan a dasa zogale ba kuwa? Kar fa rani yazo mu rasa inda zamu samu, Dukkaninsu suka kyalkyale da dariya...

Mami Safiyya na tsaye daga cikin wani had'adden filin shak'atawa tana kiranta, Deelah sauke ta haka ku taho muci abinci, ta juya ta kalli Iman da take turawa a lilon, Aunty deelah sau d'aya dan Allah, Iman tayi magiya, bata saurareta ba ta d'ago ta cak daga kan lilon tana dariya tana k'okarin sauka suka nufi wajensu Mami Safiyya, Daddy, Faruk da Zahra da suka zagaye wasu tarin kwanuka akan dardumar dake wajen...

Tana tare da Al'ameen, a cikin wani kanti na siyar da litattafai, ya zagayo ta bayanta ya zuro mata wani littafi daya bud'a cikinsa, Akwai wannan sunan a wanda kike nema? Ya tambayeta, ta girgiza kanta tace Judy ne sunan macen, sai ya rufe shi ya juya wata kantar neman wani, idanunta suka bishi da kallo, yana da kyau, mata nawa ne zasu so kasancewa dashi a wannan lokacin? Sai kuma kunyar kanta ta kama ta, ta juya ta cigaba da bincika kantar dake gabanta...

Tana zaune a cikin d'akin karatun makarantarsu, suna lesson ita da Adam, da kaloli suke amfani a ranar saboda haka ta nutsu a cikin aikin daya bata tana tayi, ta d'ago da kanta taga ya tsura mata ido, Me ya faru? Ta tambaye shi, baice komai ba kawai ya ya lumshe ido sannan ya d'ora yatsansa d'aya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login