Showing 108001 words to 111000 words out of 153964 words

Chapter 37 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3804

Adam ba. Ina ya tafi? Yaush????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
e zai dawo duk tambayoyi ne da bata samu damar yi masa a lokacin ba saboda kiran wayarsa da akayi ya fita ba tare da sunyi sallama ba.

"Kowacce ta jawo tsinannen jikinta ta fito...! Ba zan shigo d'aki tashin kowacce sh*g*ya ba."

Muryar Matron Gaje ta shiga karad'e dogon corridon yayin da wasu k'ananan ma'aikata ke ta faman bud'e kowanne cell da mukullan hannayensu, Matron Gaje wata figaggiyar mace ce mai kwala-kwalan idanu, amma an fi tsoronta fiye da duk wata Matron a kurkukun, hakan yasa yau da aikinta ya fad'o kan block d'in kowa ya mik'e a hanzarce aka shiga kafa dogon layin fita a cikin corridon, amma Fadeelah bata motsa ba, don kowacce gab'a ta jikinta amsawa take da azababbiyar gajiya.

Jiya aka raba su sababbi zuwa wajen ayyuka kala-kala na kurkukun, inda ta tsinci kanta a b'angaren masu daka da surfe, Buhunhunan masara da gero ne gasu nan a zube fal! Da kuma turame da tab'are.

Babu wani b'ata lokaci taga duk matan da suka taho tare kowacce na d'aukan tab'arya suna kuma jan turamen zuwa inda wasu Matrons ke auna musu masarar, har rige-rigen d'aukan tab'arya mai kyau ake yi. Babu yadda ta iya, haka ta lalubi wata tab'arya itama ta d'auka, bayan tsawon wani lokaci a rayuwarta, Fadeelah tayi daka, tayi ta dukan masarar da aka bata har sai da bayanta ya k'age amma babu d'aya a cikin Matrons d'in nan data d'aga mata k'afa, awa hud'u a jiyan nan sai da ta shafe su wajen dakan masarar tun tana fad'uwa tana tashi har sai da ta horu da gajiyar ta daina jin komai, ta gama dakan sannan ta zirce masarar ta fitar da dusar cikinta kamar yadda taga sauran sun yi, bayan nan kuma aka basu gero, suka surfa, suka wanke, sannan suka hau dakansa shima.

"Gwara ki tashi Binbi... Matron Gaje shegiyar kanta ce, yanzu zata lalata miki rayuwa." Kenken ta fad'a tsaye a bakin gadonta.

Binbi, tsakanin jiya da yau sunan har ya fara binta, don 'yan d'akin sun d'auka kuma suna gayawa duk wanda ya tambaye su sunanta shi, Babu wanda ya k'ara jin maganarta tun ranar da aka kawota, sai dai ta san suna jin sheshshek'ar kukan dake kwace mata cikin dare idan ta tuno rayuwarta ta baya da kuma sanadin zuwanta wajen nan...Dangi!

Mutanen da bayan iyaye su ke da alhakin kare martabar duk wani mutum a duniyar nan amma ita suke tozarta tata martabar.

Wadda aka kawo su tare sunanta Shema'u, amma a jiya taji suna kiranta da Shisha don ita ta shiga cikinsu, ta karb'i dukkan nasihohi da kuma maganganun da suke gaya mata har ta saba suna hira, ita Allah ya taimaketa ta rabu da takurawarsu tun a safiyar jiya da Lalita ta saka doka a d'akin.

"Kar sh*g*yar da ta kuma takurawa Binbi a cikinku, musamman ke Kenken, idan kun kyaleta kwana nawa ne zata sauko ta neme mu? Kun san dai halin sababbi irinsu, in kuma akwai wadda take son asirinta ya tonu kar ta fasa, idan aka kama yarinya kar 'yar kaza-kazar data sake ta kira suna na."

Bata tab'a magana da K'atuwar matar ba, amma a cikin zuciyarta ta gode mata da wannan gargad'in da tayi musu, duk da cewa kuwa bata fahimci komai a cikin zancen nata ba, ita dai ta san ta samu sauk'in yawan takura mata da suke yi, sai dai kawai yanzu suyi ta binta da ido.

Zazu, wannan mai kama da k'abilar ta juyo sanda ta kai bakin fita daga cell d'in.

"Kenken ki kyaleta, idan Gaje taci uw*rta zata gane ne."

"Ki sauko kafin ta k'araso, ba zaki so abinda zata yi miki ba." Muryar Kenken ta k'ara fad'a sanda ta isa bakin k'ofar.

"Kowa ya fito, bani da lokacin b'atawa akan kowacce 'yar isk*."

Muryar Gaje ta biyo baya, ba yadda ta iya haka ta share kwallar dake shirin fito mata ta sallalb'o ta diro daga gadon, tabi dogon layin da ya fita har waje don daga yanayin yadda take jin muryar Gaje, ta san da gaske zata iya azabtar da ita.

"Kece Bintu Abubakar?"

Wata Matron ta same ta a layin sanda suka fita waje. Ta tab'e baki tana kallonta bayan ta amsa.

"Ba laifi dole su rikice akanki, amma abin ne yayi yawa kamar wani tashin duniya?"

Fadeelah bata fahimci me take nufi ba saboda haka ta cigaba da kallonta kawai.

"'Yanuwanki ne suke neman rikita kurkukun nan saboda an k'ulle musu 'yar gwal, mun gaya musu akwai ranakun da ake ziyara amma sunki fahimta sai da suka san yadda suka biyo ta hanyar shugaban wajen...."

Shikenan! Wahalarta ta k'are, Su Kawu Ibrahim sunzo taimakonta, ta san ko bata bar wajen nan a yau ba zasu saka a canja mata cell.

"Ki biyoni." Matar ta fad'a sannan ta cigaba da cewa.

"Akwai damar da ake bayarwa anan mutum ya amsa kira sau d'aya a wata, kin ci sa'a an bani izinin ku gaisa, kuma minti biyar kawai ba dad'i ba k'ari."

Zuciyarta ta d'an karye jin cewa a waya ne zata yi magana dasu, taso a zahiri zata gansu IDO DA IDO, don Allah ya sani 'yan kwanaki kawai rabonta dasu amma tayi kewarsu kamar watanni biyu.

"Ki gaya musu..." Cewar Matron d'in tana sauke murya k'asa-k'asa sanda suka shiga wani d'an siririn d'aki mai d'auke da kan waya d'aya."

"...Idan suka biyo ta hanya ta, a sauk'ak'e zasu dinga ganinki
bama ta waya ba kuma babu wani tashin hankali."

Fadeelah ta gyad'a mata kai sau d'aya sannan cikin zumud'i ta d'auki wayar ta kara a kunnenta.

"Assalamu Alaikum."

"Wa'alaikum salam Fadeelah."

Muryar Daddy ta amsa harda d'an saurinsa, sai ta rufe idonta a hankali sannan ba shiri kwalla ta ziraro kan kumatunta, muryarsa kad'ai kamar komawarta gida taji a cikin zuciyarta.

"Barka da rana Daddy."

"Barkanmu dai Fadeelah, ashe abinda ya faru kenan kiyi hakuri kinji? Muna nan muna ta fafutukar a fito dake, kuma insha Allah muna sa ran zasu saurare mu."

"Tohm..." Muryarta na rawa ta amsa.

"Na san da wuya, amma kiyi kokarin kwantar da hankalinki kinji? Komai zai zo k'arshe, bama samun wayar Adam ne amma da zarar ya dawo zaki fito insha Allah."

"Insha Allah Daddy." Ta asake amsawa tana gyad'a kai, hawayenta na d'iga a k'asa.

"Ga kawunki, tare muke dashi."

"Toh.."

"Bintu..." Muryar Kawu Ibrahim ta fito a gajarce.

"Na'am Kawu..."

Sai da ta amsa sannan ta fahimci lokacin kiran ne ya k'are shi yasa muryar tasa ta katse, damarta ce ta yanke ba tare da ta ko shaida musu hanyar samun wata damar ba ta hanyar Matron d'in, _Wannan wace irin minti biyar ce?_

Ta juyo a hankali ta kalli Matron d'in, taji duk abinda ya faru don haka bakinta a tab'e tace.

"Kar ki wani damu, ai ba'ayi miki hukunci ba tukunna, duk sanda kika fita zaman shari'a kya gaya musu, in kuma sun damu da yawa da kansu ma sa nemo ni."

Fadeelah bata fatan bayan fitarta ta k'ara dawowa wajen nan, amma ta san hakan wani mafarki ne a iska don haka ta kalli gefen rigar Matron d'in inda aka rubuta sunanta ta karanta, saboda amfanin goben da bata san a yaya zata zo mata ba.

... bama samun wayar Adam ne..

Kalaman Daddy suka dawo cikin kanta sanda ta zira k'afarta waje, basa samun wayar Adam? Toh ina ya tafi haka? Suma basu sani ba kenan? Don da Daddy zai fad'a mata yace bai dawo daga waje kaza ba, amma basa samun wayarsa yana nufin suma nemansa suke kenan?

Bata san lokacin da ta sulale ta tsugunnan a wajen ba, Ina Adam zai je da har zai k'i fad'awa ko Kawu Ibrahim kuma kuma a kasa samun wayarsa? Wane irin bincike zai tafi alhali anan take tsananin buk'atarsa?

Kwallar d'azu ta shiga k'ok'arin tunkud'owa daga idonta amma muryar Matron d'in nan ta katse ta daga baya.

"Tashi in maida ke, bana son duk wata masifar da zata had'a ni da Gaje."

Yinin ranar ya shud'e cikin matsananciyar wahala da azaba kamar na jiya, suka gama dukkan buk'atun waje, aka maido su... Fadeelah ta dawo cikin cell d'insu Kenken, ta kwanta akan katifar Binbin, aka kad'a k'ararrawar shirin kwanciya, Tara daidai haske ya d'auke daga kaftanin rukunan d'akunan kurkukun, a hankali kuma hiraraki da maganganu suka yi ta kad'ewa har tasirin duhu ya rinjayi dukkan wani mai rai, nauyin bacci ya kanainaye idanuwa amma banda nata.

Idanunta a tsaye suke kyam sunyi jawur saboda tsananin azabar da take ji a jikinta da kuma cikin zuciyarta... Cikin zuciyarta da dukkan tunaninta ke taruwa yana kuma d'ebewa wajen son hasaso tambayoyin dake lilo tare da k'addarar rayuwarta.

Ina Adam Ya tafi?

Me yasa yak'i gayawa kowa wajen da zashi?

Wane irin bincike yaje yi?

Wane irin waje ya shiga da waya zata kasa k'arasawa?

Ko dai wani abu ya faru dashi ne?

Bata tab'a tunanin zata samu amsoshinta da wuri ba sai a washegari wajen k'arfe biyar na yamma lokacin koyon sana'o'i, tana rab'e daga can k'arshen k'aton hall d'in da mutane suka rabu kashi-kashi wajen koyon karatun yak'i da jahilci da kuma sana'o'i, bata shiga cikin kowacce k'ungiya ba don haka ta rab'e daga nan tana kallonsu, zuciyarta na k'okarin tunkud'o mata rayuwarta ta baya amma tana turewa.. A yanzu ta yarda cewa akwai wasu k'ofofi a cikin kanta da ya kamata ta k'ulle su zuwa wani lokaci.

Kenken ta d'ago mata hannu daga can k'ungiyar masu koyon takalmi, ta juyar da kanta gefe, a duk cikinsu itace tak'i daina bibiyarta, bata san cewa zuciyarta ta k'ara kyamar mu'amala dasu ba tun daga gargad'in Lalita akanta.

"Wacece Bintu Abubakar?"

A lokaci guda wata murya ta karad'e hall d'in daga cikin lasifika daga can farkon inda wasu Matrons d'in suke gadinsu.

"Bintu Abubakar..." Kiran ya cigaba da karad'e wajen, Fadeelah ta shiga juya kanta koina don ganin wata ta taso amma ba wanda ya mik'e, Ta yaya za'ace duk tarin matan nan ita kad'ai ce mai irin sunan nan? Me tayi da za'a neme ta?

"Bintuuu Abubakar...!"

Sai da ta tabbatar babu wadda ke shirin mik'ewa a cikin tarin matan wajen sannan ta mik'e a hankali ta nufi can gaban.

"Kece Bintu Abubakar?"

Matron d'in ta tambaya kamar gatse.

"Eh."

"Lauyanki ne yazo ganinki."

Zuciyar Fadeelah tayi fiffike ta tashi sama, ta zagaya kaftanin wajen.

Adam ya dawo, Ita dama ta san ba abunda zai same shi, ba zaiyi nisan da zai barta cikin wahala ba.. Wani abu ne kawai ya rik'e shi amma ya gama ya dawo, zai sa a maida ita can wannan k'azamin cell d'in da a yanzu take masa kallon Rahma.

Ta kasa saita bakinta wajen kokarin yin murmushi sanda aka saka wata Matron d'in ta jata hanyar d'akin ganawa da bak'i na kurkukun. Kamar lokacin karatunsu ne a cikin library, kamar kuma lokacin da take ganinsa a cikin kotu, _Isolated places.._ wajajen da babu mutane ya zame musu wajen had'uwa a kodayaushe.

Suka isa k'ofar ginin wajen, Matron d'in ta bud'e suka shiga... K'aton waje ne mai d'auke tarin kujeru fal, kuma farare kamar tattabaru, amma bata damu da k'arewa wajen kallo ba, in har ta gama tattaunawa da Adam, nazarin wajen zai biyo baya.

"Gashi can yana jiranki..."

Fadeelah ta juya ta kalli inda Matron d'in take nunawa, a lokacin taji kamar wani yasa kwari da baka ya harbo wannan zuciyar tata da tayi tsuntsuwa ta tashi sama, zuciyar ta juya ta kuma juyawa sannan ta fad'o k'asa wanwar!

Kutama yayi murmushi daga inda yake zaune yana kallonta.

****

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

(&_&)

Ya sake sakin wani guntun murmushin yana k'are mata kallo.

"K'araso ki zauna mana." Fadeelah taji amon muryarsa ya amsa a wajen kamar yadda ta saba jinsa a kotu.

"Me ya kawo ka wajena?"? Tata muryar ta fito a karye, karyewar ganinsa a maimakon wanda zuciyarta ke nema.

"Alheri 'yanmata, Alheri irin wanda kike nema."

Kanta ya d'aure, wane alheri ne zai had'a ta dashi? Me zai kawo shi wajenta?

"Nayi zaton babu Alheri tsakanina da kai."

"Shi yasa nace ki karaso ki zauna don in cire miki zaton."

Ta girgiza kai, ta yaya zata saurari mutumin dake kokarin hallaka ta? Wata irin shaida ce bai bayar ba don shar'iah ta d'aure ta?

"Babu abinda zan tattauna da kai, Nagode."

Ta juya ta nufi k'ofa.

"Shikenan in baki damu da jin me ya kawo ni ba na san zaki so sanin inda Lauyanki yake."

Cak! K'afafunta suka tsaya jin hakan, lauyanta! Adam yake nufi. Ta juyo da sauri ta kalle shi.

"Kamar yaya? Ina yake? Wani abu ya faru dashi ne?"

Bai ce komai ba kawai ya nuna mata kujerar gabansa, ta kalli kujerar, ta hango amsoshin tambayoyin da tayi masa sannan tayi ajiyar zuciya ta k'arasa ta zauna.

"Hajiya Bintu, zan fara da gaya miki dalilin zuwa na tukunna kafin muje ga abinda kike son ji... Ina tunanin kin san cewa ni ba lauyan gwamnati bane ko?"

Ba tace komai ba ya cigaba, yatsunsa hard'e kan teburin dake gabansu.

"Ni lauyan kasuwa ne, 'yanuwanki sun d'auko ni ne sun biya ni na shiga shari'ar har na tara isassun shaidun da suka kawo ki har cikin kurkukun nan."

Yayi tunanin jin muryarta a yanzu, amma bata sake cewa komai ba, tayi shiru kawai tana cigaba da kallonsa.

"Bayan wad'ancan shaidun kuma da na bayar a kotu, a yanzu haka ina da kwararan shaidu guda biyu?da a gaba zan gabatar, kuma ina tabbatar miki cewa in har na fito dasu babu abinda zai hana a zartar miki da hukunci na k'arshe akansu.

Sai dai kuma zuciyata na gaya min cewa bai kamata a bar yarinya irinki ta k'are rayuwarta a kurkuku irin wannan ba saboda na san ba lallai a yanke miki hukuncin kisa ba, kotu zata yi miki rangwame a barki a nan wajen har iya rayuwarki.

Don haka ne kwanakin baya na yanke shawara, na sadaukar da nasarar da zan iya samu a shari'ar nan, naje na sami lauyanki kafin tafiyarsa na gaya masa cewa zan iya siyar muku da wad'annan shaidun biyun da nake dasu a yanzu, in kuma baku lagon sauran abubuwan da 'yanuwanki suka bani, amma fur! Yak'i saurarata a lokacin.

Game da duk bayanan dana tara, na yarda baki da laifi a cikin wannan al'amarin Bintu, duk da cewa ban san waye ainihin mai laifin ba amma tausayin irin rayuwar da shari'ar nan zata kaiki yasa nazo wajenki, abinda nayi da kuma wanda nake yi yanzu kuskure ne ko a cikin aikinmu, amma na ture komai saboda kawai in taimake ki.

A yanzu kin kwana biyu a cikin kurkukun nan Bintu, kinga irin rayuwar da ake kwad'antawa, kuma na san baza ki so ki dauwama a cikinta ba, baza ki..."

"Me kake so?"

Muryarta ta katse shi a tsaye babu wani gargada.

Ya d'an tsaida idonsa a kanta, maganar da tayi a kusa dashi ya tabbatar masa cewa bai tab'a jin muryarta ba, amma sai ya ture hakan ta hanyar kaurara muryarsa sannan ya fad'i abinda ya dad'e yana shirya masa.

"Ki sa 'yanuwanki su sayi shaidun wajena, ni kuma nayi miki alkawari zanyi sanyi a b'angarena yadda zaku iya yin nasara."

Ya k'ara da cewa.

"Ba lallai sai lauyanki ya sani ba tunda tun farko yak'i amincewa, in har kun siya shaidun zamu yi komai ne a rufe."

"Wad'anne irin shaidu ne?"

Sai yayi guntun murmushi jin hak'ansa ya fara cimma ruwa.

"Idan muka yi ciniki zaki gansu, kuma ina mai tabbatar miki ba za kuyi dana sanin karb'e su daga hannuna ba."

Fadeelah ta cije k'arshen lebb'enta tana kallonsa, tunani take a cikin kanta ina ma tana da recorder ta nad'i maganganunsa tun daga farko! _ya riga ya san baki da ita ai._ Zuciyarta ta rad'a mata.

"Wannan damarki ce Bintu, damar da idan ta kub'uce zaki zo kina dana sanin ta tsawon rayuwarki."

Muryarsa ta sake fitowa cikin sigar hila, sai tayi wani guntun murmushi wanda ya fito a bushe kan lebb'enta, ta sunkuyar da kai ta kalli yatsunta sannan ta d'ago ta kalli idanunsa dake nuna jiranye.

"Kana tunanin kai kake da k'addarar rayuwata a hannunka?"

Lauya ne shi, mai kama da dillali, wanda ya san ma'anar duk wani motsi da futucin kostomansa, don haka a take ya gane ina maganarta ta dosa. Ya saki nasa murmushin shima mai fad'i da zurfi.

"Kin b'arar da damar kenan?"

Fadeelah tace.

"Na cillar da ita, b'ari wani lokacin a rashin sani ake yinsa, amma jifa babu wanda zaiyi bai kudirta hakan ba."

Ya tab'e baki kad'an, da dai murmushin sannan yace.

"Sai ince miki barka da shigowa sabuwar rayuwa, Binbi!"

Sunan ya dake ta, kamar dukan gudama a tsakiyar kai amma bata nuna ba, balle ta nuna mamakin yadda akayi ya sani don ko Matron d'in data rako ta zata iya fad'a masa. Ta sake cije lebb'enta kad'an sannan ta tambayi abinda yasa tun farko ta saurare shi.

"Ina lauyana ya tafi?"

Sautin dariyarsa ne ya fito kafin amsarsa, dariyar data tsinto ciwon tayinsa da ta tankwab'e a ciki.

"Hajiya Bintu kin tab'a ganin inda mai siye ya kushe kayan mai siyarwa sannan ya nemi da yayi masa kwatancen wajen wani mai siyarwar?"

Ta tamke k'asan lebb'enta data cije kamar zata datsa wajen, ya kamata tun farko ta hango wannan amsar, Babu ta yadda za'ayi Kutama ya san inda Adam yake alhalin ko Kawu Ibrahim bai sani ba. Sai ta mik'e tsaye kawai ba tare da ta ko kalle shi ba, ta ture kujerar data zauna sannan ta juya tabi ta cikin sauran fararen kujerun ta nufi hanyar fita daga wajen.

Kutama ya bita da kallo, ji yake kamar hayakin tiriri ne ke fita daga kunnensa saboda haushin yadda ya fito da zalamarsa gaban yarinya k'arama irinta ita kuma ta watsa masa k'asar kunya a ido. Ya gyad'a kai a hankali sannan ya rantse a cikin ransa sai ya toshe duk wata k'ofa da zata iya sawa suyi nasara, yadda zata shafe tsawon rayuwarta tana takaicin abinda tayi masa.

Matron d'in dake tsaye a bakin wajen tabi Fadeelah da kallo sanda ta fito tazo ta wuce ta, mamakin halayyarta ya sake kamata, tun sanda aka kawo su ta lura yanayinta daban ne dana masu laifi da yawa da ake kawowa, bata nuna tsoro game da abubuwa da yawa na wajen, zuciyarta a dake take kamar a baya ta fuskanci wani abu da yafi k'arfin zaman kurkukun nan.

Da k'arfi ta tsaida ita ganin tana neman yin nisa. "Ke tsaya nan in maida ke!"

Fadeelah ta ji ta amma bata tsaya d'in ba, da kowanne taku k'irga kwanakin da suka rage a sake zaman shari'arta take yi, ta san ko'ina Adam yaje kuma komai rintsi zai dawo a sannan!

***

A cikin garin Ikara, cikin Babban gida, b'angaren Kawu Ibrahim, Daddy ya kalli Kawu Ibrahim yace.

"Wad'annan 'yanuwan mahaifiyata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login