Showing 117001 words to 120000 words out of 153964 words

Chapter 40 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3799

kuma yaji zancena da ita."

D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci, tsakanin shi da tsohon babu wanda ya sake magana, da alama kowannensu da irin tunanin dake faruwa akansa, tunanin Adam bai wuce na jiran tsohon ya k'arasa masa abinda yake nema ba, don ya yarda in har ya san duk wad'annan abubuwan, to abinda ya rage ma ba zai shige masa duhu ba.

.

.

.

.

.

.

.

.

Zuwa can tsohon yayi ajiyar zuciya sannan yace.

"Sule yaje wajena a wannan ranar bayan fitar Habiba."

Sule. Sule. Sule! Adam ya zana sunan a cikin kansa da manyan harafai, sai dai waye shi? A Babban gida yake? anya ya tab'a ganinsa kuwa?

"Amma bani da tabbas akansa don sai bayan awanni da fitarta sannan yazo, kuma abinda ya kawo shi ba sabon abu bane, dama yazo neman maganin? ciwon mahaifiyarsa kuma nace ya dawo a ranar."

"A ina ya same ka?" Adam ya tambaya kai tsaye.

"A cikin gidan da nake zaune inda nake ganin mutane."

"Ka tashi ka barshi shi kad'ai a lokacin?"

Bai amsa ba sai da ya d'ago ya kalle shi.

"Idan kana tunanin ya d'auki sassak'en gubar ne to ba abu me mai yiwuwa ba, babu wanda ya san inda nake ajiye magunguna na balle har a gansu, sai dai in nine na fito dasu."

Adam ya girgiza kansa.

"Ba tunani nake ya d'auki gubar ba, tunani nake yaga maganin a lokacin da ka fito dashi zaka kaiwa Habiba a matsayin gubar, kuma ya gane ba gubar bace."

Sai da tsohon ya bud'e baki cike da mamaki sannan ya gyad'a kansa.

"Kwarai sanda ya shigo ina dab da fita, don magariba ta k'arato kuma so nake in shiga Babban gida a lokacin da maza suka tafi masallaci, mata kuma ke d'aki suna sallah, don haka na fito da maganin yana ajiye a gefena."

Adam ya gyad'a kansa.

"Kuma kana da tabbacin kuma babu wanda ya ganka a lokacin da ka shiga wajen Habiban?"

"Ina dashi, na tabbata babu wanda ya ganni."

"Akwai..." Adam ya bashi amsa yana kallon fuskarsa.

"... Don ba Habiba ce ta turo ni wajenka kamar yadda kake zato ba, wani ne daban wanda ya ganka a lokacin da ka shiga."

Ga mamakinsa sai kawai tsohon nan ya bushe da dariya a maimakon murmushin da yake yi.

"Na fahimci kai lauya ne tun shigowarka nan yaro, kuma ba lauyan dake kare Habiba ba, A ina wannan yarinyar ta samu gatan mai d'auko mata lauya kamar kai?"

Adam ya girgiza kansa.

"Ba shine abinda ya kawo ni ba, so nake ka gaya min da gaske babu wanda ka gani a lokacin da zaka shiga wajen Habiba?"

Tsohon ya sake girgiza kansa.

"Hanyar shiga b'angaren Habiba a can k'arshen Babban gida yake, don haka ba waje ne da mutane suka fiye yawan zuwa ba, in banda Anna dake zaune a wajen da wuya kaga wani a hanyar."

"Anna... Anna, wacece ita?"

Kalmomin har karo suke wajen fitowa daga bakin Adam. Tsohon ya sake dariyar data zame masa jiki.

"Kar kasawa kanka wani fata, Anna mahaukaciya ce, ba abinda take ganewa balle tayi maka amfani."

Ba fata kad'ai ba, Adam ji yayi zuciyarsa ta d'auki k'addarar shari'ar kacokam! Ta maida kan Anna mahaukaciya. Dukkan wannan rikicin ya fara ne daga Babban gida, an kashe Hajiyar a cikin Babban gida, An d'orawa Bintu sharrin kisan a Babban gida, an shigar da k'ara kotu daga Babban gida, ya baro Babban gidan ya taho wannan luluk'in bincike.... Ashe watak'ila AMSAR na dai cikin BABBAN GIDAN!

"Wacce hanya ce zata yi mana sauk'in fita titi?"

Ya tambayi Jamil bayan komai ya kammala tsakaninsa da mutanen Mimbiri, ya gama da tsohon nan, yayi sallama da maigari har kuma sun saki Sa'id d'in da aka tsare a fadar Maigari.

"Komawa hanyar Abuja yanzu tafiya ce mai nisa kuma hanyar bata da kyau, daga nan yafi kusa da Keffi, gwara ku fita keffin sai ku d'auki hanya ta titi ku koma yafi sauki."

Hakan suka yi kuwa, Jamil yayi sallama da wan mahaifinsa sannan yabi su har wata mararraba da ta d'auki hanyar fita k'aramar hukumar keffin daga nan shi kuma ya sami motar da zata koma k'auyensu, suka rabu bayan Adam yayi masa alkhairin da yake ganin zai koma k'auyensu ne a matsayin attajiri!

"Ba irin tunanin da ban kawo akaina ba duk da irin bayanin da suka yi min, gani nake kamar k'arya suke wani abu ya faru da kai ne, wallahi har na fara hasko yadda zan caka musu wuk'ar dake jikina don su barni in fita in nemo ka...."

Sa'id ya shiga fad'a bayan sun rabu da jamil sun d'auki hanyarsu, Adam bai katse shi ba har sai da ya kai k'arshe, idonsa na kan titin birjin da suke bi sannan yace.

"Sa'id wacece Anna?"

"Anna?" Ya tambaya cike da mamakin me ya kawo sunanta kuma a wannan halin.

"Of course, ita."

"Wani abu ya gaya maka game da ita? Cewa yayi ta san wani abu?"

Sa'id ya jero tambayoyin bi da bi, Adam ya cije lebb'ensa alamun baya son doguwar magana a lokacin, fahimtar hakan da Sa'id yayi yasa ya d'an kalli gefe hannunsa dunk'ule akan bakinsa kafin yace.

"Anna 'yar Babban gida ce itama, mahaifiyarsu d'aya da Babana, ta gamu da matsalar aljanu ne tun aurenta na farko, hakan yasa ta zama kamar bata da hankali sosai kowa yake gudunta, amma tana da nata hankalin don tana iya fahimtar wasu abubuwan."

"Wasu abubuwan kamar me?"

"Misali zata ci abinci kuma zata yi ibadar ta kamar kowa, kawai dai bata fiye tsabtace jikinta bane kuma tana saka shirme a maganganunta, amma bata da mantuwa, in har ta san abu, komai dad'ewarsa baya b'ace mata."

Adam ya gyad'a kansa yana jin kamar a lokacin ya tashi sama ya ganshi a Ikara kawai, kamar ya zuk'e duk tsawon tafiyar dake gabansu ya matseta cikin taku d'aya.

"Me ya faru? Me Malam Salisun yace maka?" Sa'id ya yanke shawarar tambayar bayanin da baiyi masa ba.

"Zan fad'a maka."

Ya fad'a cikin harshen turanci sanda yabi motar gabansu yasha wata kwana... Ya fad'i hakan ne kawai don ya rabu dashi, amma k'aidar bincikensa shi baya had'awa da kowa, baya gayawa kowa abinda yake ciki sai dai a ga sakamako kawai.

Har Sa'id ya bud'e baki zai sake magana wayarsa dake kan cinya ta shiga ruri, yayi saurin kallonta,? Ya Allah! Ya akayi bai lura ba cewa sun shigo waje mai service ba, da sauri ya d'ago da ita cike da begen sautin kiran da yayi kewarsa tsawon kwanaki.. Bak'uwar namba ce da bai santa ba, ya d'an kalli Adam da idonsa ke kan titi kafin ya d'auka.

"Hello... Eh Sa'id ne... Eh muna tare dashi... Okay tohm."

Sai ya mik'owa Adam d'in wayar.

"Da kai ake son magana."

Kamar bai ji shi ba don da alama yayi nisa cikin tunani, sai kuma ya mik'o hannu ya karb'a sannan ya kara ta a kunnensa. Gaisuwa kawai Sa'id ya iya tsinta a cikin maganar da yayi kafin dogon bayanin da muryar ciki ke masa ya canza yanayin idanunsa zuwa wani abu da zai rantse ya kuma rantsewa bai tab'a gani tare da Adam ba, iya tsawon zamansa dashi.

Tashin hankali...

Tsantsar sa!

****

Basu sami airpot a Keffi ba, don haka dole suka k'arawa motarsu mai suka k'arasa cikin garin Abuja da kyar saboda yadda k'asan motar ya kwararrab'e da irin gurzar data sha cikin daji.

Zuwa wannan lokacin Sa'id ya fahimci me ake ciki don kiran waya ne barkatai ke ta shigowa wayarsa bi da bi na neman Adam, kasancewar shi wayarsa basu ma san inda take ba cikin tarkacen motar, kuma dukkanin kiran suna dangantuwa ne da labari d'aya, cewa bayan tafiyarsu kotu ta tura Fadeelah kurkuku wanda hakan ya faru da sa hannun lauya mai shigar da k'ara Kutama.

Sai dai abinda bai fahimta ba shine irin rud'anin dake haskawa cikin idon Adam, haushin abinda Kutaman yayi ne ko kuma me? Shi fa ya kasa gane wace irin alak'a ce tsakanin Adam da wannan case d'in, ko kuma yace Bintun ita kanta, don ba zai yiwu ace duk wannan wahalar da kashe kud'in da yake yi saboda Kawu Sulaiman bane kawai, har yaushe ya sanshi da zai ta sadaukar da kud'i da lokacinsa saboda shi haka? Yafi danganta cewa akwai wani abu tsakanin Adam d'in da Bintu.

Tunda ance ta zauna a America tare da marik'anta, zai iya yiwuwa ya santa ne tun a can, sai dai kuma kansa ya sake k'ullewa da tunanin in har su san juna me yasa daga shi har ita ba wanda yayi maganar hakan.

Ya juya ya hangi fuskar Adam d'in dake tsaye tare da wani dillalin sayar da motoci, inda suka tsaya zasu saida motar tasu bayan isarsu cikin garin Abujan, a yanzu ya fahimci cewar jinin mahaifinsa na hausawa ne kawai ke yawo a jikinsa, amma dabi'unsa kaf irin na al'adar turawan daya tashi a cikinsu ce, baya tab'a fad'in abinda yake ciki sai dai a ga sakamako kawai.

Bayan da kyar an samu wani makaniki ya sayi motar, suka tsaya anan gidansu na Abuja suka kintsa jikinsu kafin lokacin tashin da jirgin da Adam yayi musu booking, Sa'id yaso su huta zuwa washegari amma yaga babu niyyar hakan don haka ya rik'e ra'ayinsa. K'arfe hud'u da 'yan mintuna jirgi ya d'aga dasu daga filin tashinsa na Nnamdi Azikiwe International Airport zuwa filin saukar jirage na garin Zaria.

Sa'id ya riga ya yiwa Awwal waya kafin su taso don haka tun kafin saukarsu yana tsaye a harabar wajen rik'e da muk'ullin motar da suka bar masa anan gidansu na Zariyan.

****

".... Bayan tafiyarka da kwana biyu muka sami labari wai an d'auke ta daga nan cikin kotun zuwa wata kurkuku ta mata dake can hanyar barin gari, wallahi babu irin kokarin da ba muyi ba amma ma'aikatan kurkukun sun k'i saurararmu, sunce sai dai mu koma can kotun da aka kawo ta, daga nan ne za'a iya wani abu, kuma a can mun rasa wa zai saurare mu..."

Banda wad'annan kalaman na Kawu Ibrahim babu abinda ke maimaitawa a cikin kan Adam. Ya rufe idanunsa tsam! Ya k'ara jingina da kujerar cikin jirgin, ya kasa yarda wai Fadeelah na kurkuku a lokacin, ya kasa yarda cewa tafiyarsa ta jawo mata fad'awa mummunan halin da yafi wanda ya barta a ciki, yaya zuciyarsa ke ji ma sanda tana tsare a kotun balle yanzu kuma an gwamutsa ta cikin wata k'azamar rayuwa... kurkukun da ya sani a k'asashen da suka cigaba ma yaya suke balle kuma ta nan Nigeria?

Sannan ya kasa barin tunaninsa ya hasko yadda ta koma yanzu, musamman wad'annan idanun nata, sun d'ashe saboda wahalar rayuwar da bata saba ba? Sunyi zurfi? Sunyi fari? Ko kuwa dogwayen gashin jikinsu sun zube saboda rashin abinci mai inganci?

Ya rantse a cikin kansa ya kuma rantsewa in d'aya daga cikin wannan ya tabbata sai Kutama ya biya koda kuwa bayan shari'ar ne... Don ji yake kamar idanun nata a manne da zuciyarsa suke saboda tun daga ranar da k'addara ta had'a shi da ita, basu tab'a barinsa ba, tare dasu ya shiga duk wata gwagwarmaya ta rayuwarsa ya fito.

Fatansu Kawu Ibrahim da wannan mutumin marik'inta shine yanzu a dawowarsa yasa a fito da ita daga kurkukun a maida ta cikin kotun, amma shi ba wannan ne shirinsa ba, ya riga ya yiwa kansa alk'awari cewa daga jibi da zai kama ranar da za'a sake zaman shari'ar, k'afafun Fadeelah baza su sake takawa su koma wani k'azamin waje ba, zai k'are shari'ar a ranar ya kuma dank'a mata 'yancinta a tafin hannunta, 'yancin da zai wanke ta a idon duniya kuma 'yancin da zata zaga koina a cikin Ikara da kuma shi kansa Babban gidan ba tare da wani mai zarginta ba... Abinda ya rage masa kawai yanzu shine Allah ya tabbatar da wannan alkawarin daya d'auka.

A hanyarsu ta shiga cikin gari bayan sun sauka daga jirgin, ya kira Jabir, wannan k'aramin lauyan da kotu ta bashi a matsayin mataimaki, shi ya gaya musu sunan kurkukun da Fadeelah take da kuma kwatancenta, yana iya ganin mamaki k'arara a fuskar Sa'id lokacin da ya cewa Awwal ba gida zasu nufa ba sai yaje yaga Fadeelah tukunna.

Har saida Sa'id d'in ya tambaya, Ba sai gobe ba? ya girgiza kansa kawai, ta yaya zai iya wani bacci bai je ya ganta ba? Ta yaya zai iya runtsawa baije yaga wad'annan idanun ba...

Awwal cike da d'okin tuk'i kuwa yayi ta bin kwatancen map d'in da Jabir ya turo masa ta wayar Sa'id, don shi in za'a d'ora masa bindiga a lokacin ba zaice ga inda tasa take ba sai dai a shigar da harsashin kawai.

Zuciyarsa tayi girma kamar gingimemen gate d'in da suka tarar a k'ofar kurkukun, aka bud'e musu suka shiga bayan ya nuna I.D Card d'insa. Bayan sunyi parking kuma wani daga cikin masu gadi ya shigar dasu har wajen receiptionist inda suka tarar da wata d'irkekiyar mace zaune akan desk d'in wajen fuskarta babu ko d'igo na alamun rahma. Zuciyar Adam ta sake matsewa da tunanin har kwana nawa Fadeelah tayi tana rayuwa da irin wad'annan mutanen.

Matar ta d'auki wani kan wayar intercom bayan ya gama yi mata bayanin WAYE SHI da kuma abinda ke tafe dashi.

"Receiptioninst area. Akai Bintu Abubakar waiting room, lauyanta yazo ganinta."

Tana fad'in haka ta ajiye kan wayar sannan ta mik'a masa I.d Card d'insa da ta duba, daga nan ta umarci wata Matron a gefenta da ta kaishi shi kad'ai can waiting room d'in, su Sa'id kuma su jira shi anan.

Lauyanta. Adam ya maimaita kalmar a zuciyarsa sanda matron d'in ta jashi zuwa wata k'ofar, yaya Fadeelah zata ji in akace mata lauyanta ne yazo ganinta?

**

"Lauyanki ne yazo ganinki."

Wata Matron ta fad'a tsaye akan Fadeelah, a lokacin k'arfe shida da 'yan mintuna ne na yamma, tana zaune a harabar masallaci an idar da sallar magriba, tafin hannunta da yayi sab'a da kuma alamun kanta take bi tana d'ayewa a hankali yayin da Kenken wacce sai bayan an idar da sallar tazo ke zaune a gefenta tana bata labarin da ba ganewa take ba.

Tun da take a rayuwarta bata tab'a ganin naci irin na matar ba, ko kad'an rashin kulatan da take yi baya damunta, haka za tayi ta binta kullum da labarai marasa kan gado wanda ita bata fahimtarsu, a yau har sawa tayi aka canja mata aiki daga b'angaren surfen da aka kaita zuwa kicin, babban aikin da ta lura kowa ke rububinsa a kurkukun, don aikinsa a sauk'ake yake an riga anyi komai kan ya k'araso kicin d'in kuma abinci sai dai mutum ya ture shi. Don haka sauk'in aikin da ta samu a yau yasa kantar hannun nata ta d'add'ago har da sab'a.

Ta d'ago da fuskarta ta kalli Matron d'in dake tsaye akansu, akwai banbanci mai yawa tsakanin Fadeelan da ta shigo cikin kurkukun 'yan kwanakin baya kad'an da kuma yadda take a yanzu, ta rame, tayi duhu, lallausar sumar kanta ta dunk'unk'une saboda rashin gyara, leb'b'enta duk yayi sab'a saboda bushewa sannan ga wani k'aton tabo a saman girarta na ciwon da taji da k'arfen gado.

Zuciyarta ta maimata abinda Mstron d'in ta fad'a sannan tasa jan fenti ta soke shi, tayi zaton ta sallami Kutama da kalmomin da ba lallai ya sake waiwayarta ba, me kuma ya sake dawo ya gaya mata? K'ara tallata mata muhimmanci shaidun wajensa zaiyi ko kuwa gaya mata za?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 i yi ya saukar da farashinsu?

Wai lauyanta... Lauyanta, ta sake maimata kalmar a zuciyarta, haka ya kira kansa ma a wancan zuwan nasa na farko, ya yaudari hukumar kurkukun suka shigo dashi wajenta ya kuma yaudare ta, ta kai kanta gabansa... Amma ba'a cizon mumini a rami d'aya, ba dai k'afarta ta sake takawa taje wajensa ba, don bata fatan ko a kotun idonta ya sub'uce ya sake kallonsa.

"Bana buk'atar ganinsa Matron Salame, ace masa kawai ya tafi."

"Saboda me? Kina sane kuwa cewa jibi za'a sake zaman shari'arki? Ko wajen nan ya fara yi miki dad'in zama ne?"

Wata doka ce a kurkukun cewa ba'a k'in amsa maganar Matron, don hakan kad'ai zai iya jawo maka yini guda a d'akin duhu, d'akin da zaka ji kamar an maida kai cikin mahaifiyarka ne saboda duhu da kuma rashin iskarsa, ba don haka ba da Fadeelah tayi shiru kawai, don sabon abinda ya shiga cikin jerin abubuwan data tsana shine 'Rashin son magana'.

Ta girgiza kanta.

"Bana buk'atar ganinsa ne kawai."

Sak! Wad'annan kalaman su Matron Salame ta koma ta maimaitawa Adam.? Shima ya maimaita su a zuciyarsa ya kuma maimaita su a fili.

Fadeelah bata buk'atar ganinsa... bata buk'atar ganinsa?

"A ina take yanzu?"

Kai tsaye ya tambayi Matron d'in wadda bata kawo komai ba ta amsa.

"Suna Harabar masallaci."

Ai tana rufe baki, bai jira komai ba ya shiga tsallake tarin fararen kujerun dake wajen ya nufi k'ofar zata kaishi cikin kurkukun, k'ofar da zata kaishi wajenta!

Matron salame na k'okarin dakatar dashi amma bai ko saurareta ba, ganin da gaske yake shiga zaiyi yasa tayi gaba da sauri, amma cikin rashin sa'a sai tayi tuntub'e da wata kujera ta fad'i har k'asa, k'ashin k'afarta ya gurd'e nan take!

****

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

38

(&_&)

Basu barshi ya ganta ba.

Bai samu ya k'arasa inda zai ganta ba don kamar yadda ya kwana da sani ne, kowacce kurkuku a cike take da masu tsaro kota'ina da mutum bai isa ya k'arasa ciki ba, musamman wajen kwanan d'aurarrun, kuma a lokaci irin na dare.

Ya rufe idonsa ruf! Gashin sama ya hard'e da na k'asa, lalube kawai yake a cikin kansa tun bayan dawowarsu gida, yana neman wannan dauriyar da yayi amfani da ita a baya, dauriyar da yayi shekara guda cif yana yawo da taswirar idanunta a cikin tunaninsa, don ya yarda wannan dauriyar ita kad'ai ce zata iya kwantar da hankalinsa a yanzu.

Kwana guda ba komai bane akan shekara guda.

Ya ayyana hakan sannan ya bud'e idanunsa a hankali daidai sanda iskar daminar dake shirin shigowa ta kad'a a harabar wajen, k'arfe d'aya ne na dare a lokacin, don haka garin na Zariya yayi bak'i da kuma shiru, Musamman a irin wajensu da babu mutane sosai, ya tabbata su Sa'id ma sunyi nisa cikin bacci don tun bayan da suka yi jam'in sallolin dake kansu, ya lalubi hanyar d'aki ya shige, amma shi har yanzu ko gezau idonsa bai yi ba.

Ya riga ya saba, duk sanda yaci karo da case mai sarkakiya, tarin tunanin cikin kansa baya tab'a barinsa ya runtsa, balle kuma irin wannan case d'in daya shafi wani sabon b'ari na rayuwarsa (Dangi) da kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login