Showing 63001 words to 66000 words out of 153964 words

Chapter 22 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3812

a ranar juma'a.

Zainab ta tab'e baki tana yanka albasa kan kwad'on zogalen bishiyar tsakar sashenta data dafa tace.

"Haka dai ake cewa, amma waya sani ko dadironta ta tafi, tunda ansha zaman gida shekara da shekaru ba bazawari."

"Ke Zainab mutuniyar taki kike wa wannan zaton?"

"Wace mutuniyar tawa? Ai shi yasa nace miki kin dad'e baki shigo gidan nan ba, tun yaushe na fita harkar wannan munafukar, ke ni gidan nan ma yanzu in gaya miki in kika d'auke manya irinsu Kawu Danjuma, to ko shi Rabi'u da nake zamansa ba wanda zan d'ebe ince miki baya ji da nasa munafuncinsa, kallon kowa nake yi kawai."

Ladi ta jinjina kanta.

"To Allah ya kyauta! Ni a tunanina duk wannan baya rasa nasaba da yadda Habiba ta kankane kusan komai na gidan nan."

"Ke raba kanki, ai yanzu ba cikin gidan nan kad'ai ba har a waje kusan kowa da Hajiya yake kiranta, makkarta biyu fa."

Wannan karon Ladi ce ta tab'e nata bakin.

"Wato kema ba kya ganin laifinta kenan, shikenan ta had'e ku gabad'aya gidanta shanye, ai ni? tunda na shigo gidan nan bayan watanni biyu kawai da rasuwar Hajiya Balaraba na san abinda Habiba ke fata ya faru,?ta samu damar watayawa ta juya kowa yadda take so kamar yadda ta maida mijinta,?shi yasa dama basa tab'a shiri da ha..."

"A'a Ladi tsaya! Ya naji kina neman karkace hanya ne ki danganta rasuwar Hajiya kuma da Habiba, meye had'in anan? Abu da ya riga ya shud'e kowa kuma ya san wannan tsinanniyar yarinyar ce ta kasheta ta gudu."

"Kinga nifa ba wani abu nace ba,? nufina tunda babu Hajiya a yanzu,? habiba ta samu damarta ne?kawai ba wani zance ba."

Zainab ta juya ta cigaba da yanka koren tattasai kan had'in zogalen sannan tace.

"A'a to, ai gwara inji ne da kyau don kin san fa har yanzu zancen na gaban hukuma, su Kawu d'anjuma sun sha alwashin sai dai in ba'a ga Bintu a duniyar ba,? amma babu abinda zai hana su mik'ata gaban hukuma a rataye ta itama."

"Ina zancen da ake cewa ta MUTU?"

"Babu inganci a cikinsa gaskiya,? tunda Rabi'u yace min a motar da akace ta hau anyi hatsarin, mutum d'aya ne kawai ya mutu shima wani tsoho, amma ita ance bata ma ji rauni ba kawai dai an samu akasi an sallameta ne kafin daga nan gida a isa can kanon."

"To Allah ya kyauta, amma ni wallahi 'yar tausayi take bani,? ba uwa ba uba sannan ga wannan bak'in fenti haka?"

Zainab ta shiga yanka wani k'aton tumatir jawur dashi sannan tace.

"Meye abin tausayi anan Ladi, bak'in halin uwa ne fa ta d'auko, ko kin manta yarta Mairo ma guduwa tayi da saurayi tun iyayen na da rai, ai ni wallahi a zaman yarinyar gidan nan har bana son a aiko ta sashena, kinga wannan d'an banzan farin nata da yalolon gashin nan, mayya sak! nake kallonta."

Ladi ta kyalkyale da dariya harda buga cinya sannan tace.

"Allah ya shiryeki Zainab, maita ai ba'a fari take ba."

"Ke dai bar mutum kawai, ai shi yasa a ranar da Hajiya ta mutun nan, na zage iya k'arfina nima na shiga aka jibgeta don wallahi bana d'auke kokonton yawan laulayin yusufa (d'anta na biyu) daga ita ne,?don ina dab da haihuwarsa ta dawo gidan nan."

Ta fad'a daidai sanda ta gama yankan tumatirin, sannan ta saka k'aton cokali ta juya shi tsaf komai ya had'e, ta janyo wani k'aramin filas dake gefen tabarmar da suke kai ta d'ebi na maigidanta da yaran da suka tafi makarantar allo sannan ta juyo musu da ragowar suka shiga ci.

Sai dai basu kai ga saka loma ta biyu a bakinsu ba, Salihu babban d'anta ya rugo cikin tsakar gidan sakale da allonsa a hammata.

"Kai don ub*nka haka ake shigowa gidan mutane ba sallama kamar wani kafiri?"

Ta daka masa tsawa lokacin da yaja birki a gaban tabarmarsu.

"Ina sauran suke?" Ta katse rawar zancen da bakinsa ke yi.

"Suna can gindin motar suna kallo."

"Motar wa kuma?"

"Mama, Mama wani balarabe ne yazo daga Makka a cikin wata had'addiyar mota, tun muna addu'ar tashi muka ganshi ya wuto mu, yanzu haka dukka su Kawu sun cika wajen Kawu d'anjuma jingim!"

Ita da Ladi kallonsa kawai suke da mamakin yadda ya rikice haka.

"Wajen Kawu Danjuman yazo?"

"Eh mana, kuma naji su yaya Sule suna fad'in wai d'anuwanmu ne!"

***

"Sule me ya faru ne haka?" Me akeyi?"

Kawu Ibrahim ya tambaya sanda ya shigo gidan shida babban d'ansa Harisu da la'asar lis! Daga zagayen gonakinsa da suka dawo.

Banda tarin yara birjik da suka wuce a k'ofar gida sun yanyame wata mota,? yanzu kuma ya shigo gidan yaga kusan duk samarin da ba'a fiye samunsu a wannan lokacin ba suna tsaitsaiye kan hanyar shiga sashen Kawun.

Sule ya d'an sunkuyar da kansa ya gaishe shi sannan yace.

"Kawu bak'o akayi ne daga wata k'asar ina jin, kuma naji su Kawu Sulaiman suna cewa wai d'an gidan Baba Ahmadu ne."

Cak! Bugun zuciyarsa ya tsaya na wasu 'yan dak'k'ai, ya kalle shi sosai sannan ya tambaya.

"Wane Baba Ahmadun?"

"Wanda dai ake bada labarin cewa ya b'ata shekarun baya da ak..."

Ai bai ko tsaya saurarar k'arashen ba ya wuce su duk ya durfafi hanyar sashen Kawu Danjuma. Tun daga adadin takalman dake cire a waje zuciyarsa ta tabbatar masa cewa zancen Sule gaskiya ne, don yaushe rabon da a hudu duk a irin wannan lokacin? Sai ya cire nasa daga gefe shima sannan yasa kai cikin d'akin.

Zai iya cewa kowa na nan, yayyensa dama k'annensa da suka manyanta, irinsa masu uzirin nesa kad'an ne basa nan sannan ga Kawu d'anjuma zaune a tsakiyar shimfidarsa, sai dai duk lura da wannan yazo ne bayan siffar Ahmadu k'aninsa daya hanga zaune a gefen Kawu d'anjuma,? Ahmadunsa sak! Kaninsa da duk fad'in babban gida daga shi sai k'anwarsu jummai ne suke uwa d'aya uba d'aya.

Amma wannan da yake gani Fari ne ba bak'i ba, sannan in ka d'ebe lallausar sumar kansa, to ba abinda zai banbanta shi da wancan Ahmadun daya bar gida a irin wannan shekarun.

Kwanan nan zan hutar da kai yaya, kwanan nan zaka manta da wahalar noman nan, sai dai kana zaune ka saka ayi maka, kwanan nan yaya!

Maganar wancan Ahmadun ta dawo cikin kansa tar! Maganar da ita ta zama magana ta k'arshe da ta shiga tsakaninsa da d'anuwansa, don daga wannan ranar Ahmadun yayi b'atan damo daga cikin rayuwarsu gabad'aya, aka neme shi aka rasa.

"Karaso mana Ibrahim, taho kaga ashe bamu sani ba Ahmadu ya mutu ya bar jininsa a duniya."

A hankali Kawu Ibrahim ya k'arasa ya zauna a gefen d'an baturen Ahmadun da yake gani.

"Wannan yayan mahaifinka ne da suke uwa d'aya uba d'aya."

Kawu d'anjuma ya fad'a sanda ya juya yana kallonsa, sai dai yana rufe baki Sa'idu ya d'auka, ya fad'i abinda kawun ya fad'a sak amma da turanci.

"Baya jin hausa Ibrahim sai turanci, yace daga America yazo."

Kawu d'anjuma ya tari mamakin daya nuna akan fuskarsa.

"America kuma Kawu? Shi Ahmadun can yaje ya haife shi?"

"I, nima abinda nace kenan, da mamaki da d'aure kai amma gashi yazo da shaidun da suka nuna shi d'an nasa ne."

"Ko ba shaida Kawu na yarda wannan d'an Ahmadu ne, zan iya tsayawa gaban ko waye kuwa in tabbatar da hakan."

Adam bai san me yace ba, amma sai ya zab'i daidai wannan lokacin ya matso gabansa sannan ya rik'o hannayensa, iya hasashensa ya yarda cewa duk cikin mutanen nan wannan shine madadin mahaifinsa, uwa d'aya uba d'aya yafi k'arfin komai.

Kwalla mai d'umi ta gangaro kan kumatun Kawu Ibrahim, don gani yayi sak! Kamar k'anin nasa ne ya dawo gabansa yake neman gafararsa, sai shima ya damk'e nasa lallausan hannayen da suka shaida cewa ko daga ina yake, bai tashi cikin wahala kamar Ahmadunsa ba.

Tiryan-tiryan, Adam ya zauna ya shaida musu tarihinsa da kuma na iyayensa da yaji daga Magareth, shakka babu sun tausayawa irin rayuwar da d'anuwansu ya tsinci kansa, sannan kuma Adam yasha godiya da jinjina kan kokarin da yayi har ya nemo su bai kyamaci cewa su dangin nasa basu zo a irin wajen daya taso ba.

Kawu Ibrahim shi ya shaida masa sai bayan shekaru biyu da b'acewar Ahmad ne suka sami labari cewa wani aboki ya had'u dashi daya kwad'aita masa sana'ar shigar da kwayoyi k'asashen k'etare da cewar kud'i ake samu masu yawa, kuma daga nan basu k'ara jin labarinsa ba.

Da wannan Adam ya had'a ya fitar da cewar an kama mahaifinsa ne a kokarinsa na shigar da kwayoyin k'asar America kuma aka mik'a shi kurkuku daga nan, tunda kuma k'asa ce da bashi da kowa haka ya zauna har zuwa lokacin da aka zo aka d'ebe su zuwa filin yak'i inda anan ya hadu da mahaifiyarsa.

A wannan ranar Adam yaga k'auna kala-kala ba daga iya mutanen babban gida ba harda sauran gidajen da duk su Kawu suka san akwai wad'anda suka san Ahmadu cewa ga d'ansa ya dawo suzo su ganshi. Ba kowa ke iya magana dashi ba saboda haka har yara haka yayi ta binsu da gaisuwar hannu ba tare da ya damu da banbancin tsaftar jikinsu da nasa ba, Abinci kuwa har daga can bakin layi haka akayi ta aikowa daga gidaje-gidaje cewa na saukar d'an bature ne... Al'ada dai irin ta mutanen da wayewar zamani bata ratsa su sosai ba.

Kuma babu kyankyami balle tunanin wani abu haka Adam yasa hannu ya d'andana abincin mafi yawan kwanukan nan ba tare da ya san sunan yadda aka sarrafa ko abu guda da yake ci ba.

B'angaren Kawu Ibrahim aka shirya masa d'aki guda na musamman ya kwana anan, rana ta farko a rayuwarsa Adam ya kwana cikin rufin wani irin gini da bai taba gani ba,? rana ta farko daya kwana a d'akin da babu kyale-kyale irin wanda ya saba sannan rana ta farko daya shigo cikin kabilarsa da bai tab'a gani ba. Sai dai tunda babu sauro kuma akwai fankar dake juyawa da wutar lantarki, sai yayi wani irin bacci da rabon da yayi shi tun zamanin da bai san wanene shi ba, yayi bacci da zuciyarsa sakayau babu wannan nauyin daya saba ji a kodayaushe.

Kamar kullum yau ma babu fashi, abu na k'arshe da ya gifta cikin idanunsa shine nata idon, sai ya lumshe nasa cikin nata a hankali kamar mai son yin magana da ita.

***

Washegari, da tarbar cima ta musamman ya bud'e ido, kayayyaki ne barkatai na duk kayan da suka san zai iya cinsu, saboda haka sai da ya cika cikinsa taf sannan ya shirya ya fita cikin jagorancin Sa'id, da ya zama tafintansa tun jiya.

A falon Kawu Danjuma ya zauna,? inda manyan mutane da dama suka yi ta zuwa ana gaya masa cewa suma 'yanuwa da abokan arziki ne na dangin mahaifin nasa, hatta matan cikin Babban gida daga tsofaffinsu har kanana sai da suka zo ganinsa.

Anan ya fahimci cewa asalin 'ya'yan Babban gida wato sauran 'yanuwan mahaifinsa su ashirin da biyu ne,? kuma hud'u ne kawai a ciki suka rasu,? banda mahaifinsa sauran goma sha bakwai d'in duk suna cikin Babban gida da 'ya'yayensu da kuma tarin jikoki dake tasowa gasu nan birjik!

"A cikin masu rasuwar mata uku ne, kuma suma wasu daga cikin 'ya'yansu suna nan tare damu, wasu sunyi aure,?wasu kuma suna can wajen dangin iyayensu maza."

Kawu Ibrahim ya fad'a masa bayan zuwan mutanen ya lafa a ranar, Sa'id na daga gefe yana fassara masa.

"Amma d'aya daga cikinsu ita bata yi aure ba ta rasu,?wadda itace k'anwarmu jummai da muke uwa daya uba daya da ita nida mahaifinka, d'ayan kuma magidanci ne k'anninsu Kawu Jamilu d'an gidan Hajiya balaraba dana shaida maka itace ta k'arshe mai rasuwa a cikin matan gidan.

Yana da ma mata uku da 'ya'ya takwas shima, shida duk maza ne babarsu d'aya kuma yanzu haka suna zaune a can gidan nasa,?sai kuma mata biyu da suma babarsu d'aya, d'aya matar ita bata haihu dashi ba har ya rasu."

Haka kurum sai Adam ya samu kansa da tambayar ina mata ta biyun da kuma 'ya'yan nata.

"Ita ta rasu tun kafin rasuwarsa 'ya'yan kuma basa nan yanzu haka."

Da wannan Kawu Ibrahim bai k'ara komai akai ba, don tunaninsa bai bashi cewar daga shigowarsa cikinsu ya dace ya fara sanin wasu munanan abubuwan ba. Sai yamma lis! sannan Adam ya samu keb'ewa da Sa'id wanda ya fara sabawa dashi a lokacin,?babu wata kwana-kwana ya shaida masa cewa yana son ya musulunta ne... yana son komawa addininsu da kuma na mahaifinsa.

Maganar ta daki Sa'id ya tsaya kawai yana kallonshi, yanzu dama shi ba musulmi bane kenan? Ta yaya to sunansa ya zama Adam? Tabbas ya san a labarinsa ya fad'a musu cewa turawa ne suka raine shi, amma ba shi kad'ai ba ya san har ga Allah duk cikinsu babu wanda ya kawo wannan tunanin akansa. To ta yaya ma zasu yi bayan wannan kamilalliyar siffar tasa na nunawa wasu cewa shi balarabe ne ma.

Babu wani b'ata lokaci ya shaidawa su Kawu Ibrahim, kuma anan cikin falon Kawu D'anjuma aka MUSULUNTAR da Adam, ya koma Adam na gaske don ya zab'i sunansa akan canjin wani tunda ko a musuluncin sunan mai ma'ana ne, daga nan Kawu Ibrahim ya d'ora Sa'id kan alhakin koya masa abubuwan da suka shafi tsarki na musulunci da kuma karatukan daya kamata ya sani a yanzu tunda shima Sa'id da d'an iliminsa.

Cikin kwanaki biyar a garin Ikara, Adam ya sake sosai cikin 'yanuwansa kuma ya san abubuwa da yawa na al'adar bahaushe tsantsa! Watakila rashin sabon wani abu kan takura shi a wasu lokutan, misali ruwan wanka,? na sha da kuma harkar d'aukewar wutar lantarki, amma daidai da rana d'aya bai bari hakan ya hauro kan fuskarsa ba, har mamaki Sa'id yake na yadda yake sakewa yaci abincinsu,? gashi kuma a cikin kwanaki biyar d'in kawai ya fara iya rik'e wasu kalmomi na hausa.

A sannan ne kuma ya shirya tafiya don bayan zuwansa Nigeria a ranar ya hawo wani jirgin zuwa Kaduna,? inda ya kwana d'aya anan washegari kuma ya sayi mota sannan bisa jagorancin wad'ansu, ya d'auko direban tasha ya kawo shi har cikin Ikara.

Saboda haka yanzu zai koma can ABUJA ne inda d'aya daga cikin manyan ma'aikatar da yake aiki dasu a America yayi recommending d'insa zuwa wata k'ungiya irin tasu ta lauyoyi mai zaman kanta anan Abujan. Kawu d'anjuma ne ya bada shawarar cewa sai dai ya tafi tare da Sa'id don ya dinga k'ara wayar dashi akan abubuwan Nigeria da kuma harkar karatun addininsa ma.

Ai kuwa babu wani kokonto Sa'id ya had'a kayansa ya bishi tunda dama ya gama karatunsa anan ABU ta zariya kuma yanzu ba abinda yake sai taya mahaifinsa aiki a shagon awonsa.

Ya tafi ya barsu da d'imbin alkhairi na kud'i yadda hatta k'ananun yara a babban gida sun shaida da zuwan BATURE ADAM!

***

A B U J A

"Kin Amince?" Al'ameen ya tambaya a hankali cikin wayar.

"Me Maminka tace?" Muryar Fadeelah ta biyo bayan wani lokaci.

Yawu ya zarce cikin makogwaronsa, a hankali ya tattara saura ya had'iye sannan ya amsa.

"Da da yanzu ba d'aya bane Fadeelah,? idan Mami bata so ki a da ba, yanzu komai ya canja ai,?saboda haka karki damu yadda mahaifina ya bada goyon bayansa haka itama bata ce komai ba."

Maganar da nauyi, kuma yarda da ita da wuya, amma zai mata k'arya ne? Zai fadi abinda ba haka ba alhali duk daren dad'ewa dai zata je ta fuskanci Aunty Miryaman?

"Kinyi shiru Fadeelah, ko sai zuciyata ta k'arasa fitowa ne waje gabad'ayanta?"

"To me kake son ince Al'ameen?"

Ya lumshe idanunsa kadan jin yadda ambaton sunansa da muryarta ya ratsa ko'ina a jikinsa.

"Cewa zaki yi na amince da kai Al'ameen kuma ina sonka da dukkan ruhina."

Murmushi ya sub'uce mata, tana murza yatsunta cikin junansu tace.

"Ko ban fad'a ba, hakan ba zai canja komai ba,?karka manta fa Daddy har Kano yaje sunyi maganar da 'yanuwan hajiyarsa."

"Wallahi zai canja Fadeelah,?zai canja abubuwa da yawa fiye da zatonki,?so dan Allah ki fad'a min, ko kin manta irin rabuwar da muka yi ta k'arshe ne kafin barinki America?"

Wallahi bana sonka Al'ameen, kuma bana tunanin zan tab'a sonka!

Maganar baya ta haska tar cikin kanta, lallai d'an adam ba'a bakin komai yake ba kuma baki shi ke yanka wuya, da ace a lokacin da take fadin hakan za'a nuno mata sanda take kokarin yin abubuwan da zata burge shi da kuma yanzu da aka saka ranar aurensu, watakila zata hak'a k'asa ne ta shige don kunya. Shi yasa a kullum yanke hukunci cikin fushi baya tab'a zama alkhairi don ko ka yanke din, a haka hukuncin ubangiji zai zo danne naka, kak'i tsira da komai sai tarin kunya da kuma dana sani!

"Ki fad'a min." Taji muryasa tayi k'asa sosai kamar har sai da numfashinsa ma ya busa akan fatar kunnenta.

"Ina sonka Al'ameen, ina sonka saboda na yarda da kai kuma kaima ka yarda dani a lokacin da ko ni ban yarda da kaina ba, ka bani farin cikin da wani bai tab'a bani irinsa ba,? saboda haka duk abinda zance ko na fad'a a baya, k'aryar zuciyata ce wannan."

A hankali Al'ameen ya lumshe idanunsa sannan babu gargada ya fadi kalaman dake azabtar da zuciyarsa a kullum.

"Ban san lokacin da na fara sonki ba Fadeela,?watakila babu farko kuma babu k'arshe, kin riga kin zama wani b'agare na jikina kuma ina sonki ba tare da tsoron komai ba ko son samun wani abun, sai don kema ki soni? kuma ki bani damar da zamu k'are rayuwarmu tare har abada."

Ta koma da baya ta jingina da allon gadon da take zaune sannan murmushi ya sake subucewa a kumatunta.

"Na baka wannan damar Al'ameen,? ka riga ka sameta sai dai fatan Allah ya sada mu da alkhairin dake cikinta."

Bata ko jira ya amsa 'Amin' din ba ta katse kiran da sauri sannan ta janyo filon gefenta, ta rungume shi sannan ta cusa kanta cikinsa dad'i na nukurkusar zuciyarta!

Al'ameen ya sauke wayar daga kunnensa a hankali, tunani biyu na ratsa shi,?Farko dad'in kasancewar ya shawo kan Fadeela a yanzu kuma komai zai tafi tsakaninsu. Na biyu ruftawar da zuciyarsa tayi ta bar wani tangamemen rami game da k'aryar da yayi mata, k'aryar da ya san duk daren dad'ewa zata zo ta fahimta,? watakila ma ba sai an kai ga daren dad'ewar ba gaskiya zata baiyana kanta.

Amma ya zaiyi ne in ba haka ba? Bari zaiyi komai ya sake cakud'e masa irin farko? Damarsa ta biyu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login