Showing 54001 words to 57000 words out of 153964 words

Chapter 19 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3786

Maria bata yi wani tunani sau biyu a kwakwalwarta ba ta tafi ta rungumeshi!

Ubangiji yaso kowa yana ta kansa ne a lokacin saboda haka ba'a sami wad'anda suka lura dasu ba, a sannan ne kuma na fahimci cewa duk wani bayanina ba zai tab'a tasiri akan Maria ba, ta riga ta had'e zuciyarta da ta Ahmad kuma ban isa in raba su ba, saboda haka na zura ido kawai na kalli abinda k'addara ta tanadar tsakaninsu.

Don kamar had'in baki a wannan lokacin sai sojojin suka shafe kusan kwanaki ashirin basu koma fagen yak'i ba, saboda haka alak'ar Maria da Ahmad sai ta samu bigiren yad'uwa,? har ta kai nima na sauko daga tunanina ina jin dad'in kasancewarta dashi,?saboda wata irin tsantsar kulawa da yake bata ta hanyoyi da dama, har saida ta kai yanayinta dama shigarta sun fara banbanta da namu, duk da cewar albarkacinta nima na canja sutura a irin kayayyakin da yake bata wanda yake yin aike ga masu gadin wajen su siyo mata. Kuma cikin ikon ubangiji babu wanda ya tab'a zargin komai daga gare ta balle har alak'arsu ta tonu.

A wannan lokacin ne kuma Maria ta same ni da zancen cewa ta canja addini ta koma na Ahmad, kuma ya gaya mata zai aure ta su koma can k'asar su bayan an gama yak'in, bance mata komai ba don bana iya hanata komai d'in daya dangance shi.

Sai dai Ahmad bai samu damar koya mata komai game da addinin ba yak'i ya sake dawowa suka tafi barmu cikin jiran tsammani, kuma a cikin wannan jiran ne wani babban al'amari ya faru.

Wanda shine samun cikinka, yazo a lokacin da muka shekara d'aya da rabi a sansanin, lokacin da muka riga muka saba da rayuwar wajen muka zama mutanen daji na k'arfi da yaji, har a sannan kuma su Ahmad basu dawo daga gab'ar yak'in ba. Ni na fara ganewa Maria tana da ciki kafin ma ita, kuma bayan mun tabbatar da hakan na shiga bata shawarar hanyar da zamu bi mu gudu tunda muna d'aya daga cikin manya da ba'a takura musu sosai amma Maria tak'i yarda, tace min baza ta tafi ta bar Ahmad ba alhali baima san da cikinta ba.

Kamar yadda na sani, itama ta san a wannan lokacin in sojojin dake gadinmu suka fahimci ciki ne da ita ba abinda zai hana su kashe ta amma soyayyar da take wa Ahmad ya rufe idonta gam da hangen hakan, saboda haka na rabu da ita muka cigaba da zaman jiran tsammanin da muke ciki a kodayaushe.

Wanda k'arshensa ya haifar da abubuwa da dama, na farko dawowar sojojin nan ba tare da Ahmad ba ko gawarsa, gashi ba wanda zamu je mu tambaya ace meye alak'armu dashi? Nayi iya kokarina in nusar da Maria ta hak'aura cewa Ahmad ya mutu amma ta kasa fahimtata, tace ai ba dukkaninsu ne suka dawo ba mu dai zauna zamu ganshi.

Na biyu komawar sojojin da sake dawowarsu bayan watanni biyu babu Ahmad, na uku sauran ma'aikatan da muke tare suka fahimta cewar Maria na da ciki,?na hudu, ganewar d'aya daga cikin sojoji matan dake gadinmu da k'ulleta da suka yi a wani d'aki wanda kowa ya san duk aka saka a ciki to baya wuce kwanaki biyu ba'a harbe shi ba, na biyar... Fito da ita nayi da kuma guduwarmu!

Na samu taimakon wata abokiyar aikunmu ne muka sato muk'ullin d'akin da aka kulle Maria cikin dare, daga nan muka bi ta wata hanya ta cikin k'arkashin k'asa da suka yi inda shima muka samo mukullinsa, matar nan ita ta taimake mu ta kulle k'ofar daga waje bayan mun shiga, amma duk da abinda ya faru da kyar na samu Maria ta yarda ta bini muka gadu daga wajen, tunaninta gabad'aya ya ta'allak'a ne cewa zamu tafi mu bar inda Ahmad zai dawo nemanta, don bata yarda cewa ya mutu ba har a sannan.

Allah ya taimake mu har muka yi kwanaki biyu muna tafiya cikin dajin da bamu san kansa ba sannan sojojin suka farga da guduwarmu suka bazama neman mu, mun gane hakan ne ta yawan harbin bindiga da muke ji a kusa damu da kuma hango motocinsu da muka fara yi a can nesa damu, a lokacin tunanimu ya tafi kan me yasa zasu tada hankalinsu don mu 'yan aiki biyu sun gudu kawai,? amma muka kasa sanin dalili.

Bama taba tsayawa a waje d'aya? kullum cikin tafiya muke sai idan mun samu ruwa a waje ne kawai muke d'an tsayawa mu huta gajiyarmu, ubangiji ya sani daga ni har Maria bamu yi tunanin zamu tsallake dajin nan ba tare da an kama mu ba, amma cikin sa'a sai gashi har muka isa wani k'aramin gari basu ganmu ba, anan muka zauna tsawon wata guda muna aiki a wani k'aramin gidan cin abinci, inda da kyar suka bamu wajen kwana cikin sitonsu.

A wannan lokacin alak'ata da Maria kawai shine duk abinda nace mata muyi zata yi, amma ta daina min magana da kuma sani a harkokinta,? laifina take gani cewar na rabota da wajen da Ahmad yake, nima kuma ban damu ba saboda hankalina na kan yadda zamu daidaita rayuwarmu kawai, sai dai hakan bai yiwu ba saboda rashin lafiyar da muka fara a lokacin, Maria ce ta fara fama da wasu irin kuraje k'anana masu k'aik'ayi da suka feso a bayanta kafin daga baya su fara bin kowanne b'angare na jikinta, daga nan nima suka fito min a fuska sannan hannaye da duka jikina.

Ba tare da wani b'ata lokaci ba kuwa mai gidan cin abincin ya kore mu, muka je asibiti anan aka shaida mana cewar basu tab'a ganin cuta irin wannan ba, babu wanda yayi mana zancen biyan kud'in magani suka ce dole mu zauna don a bamu taimakon gaggawa, nayi tunanin da zuciya d'aya suka yi hakan, ashe tun kafin zuwanmu an riga an sanar da kowanne asibiti a kewayen cewa da zarar mun zo a kama mu.

Maria ce ta binciko wata takarda a d'akin da aka zaunar damu, wadda aka buga ta da sunanmu cewa mun gudo daga sansanin sojoji ne d'auke da wata cuta ta annoba da zamu iya shafawa mutane ko a iska ne don haka a sanar da hukuma da zarar an ganmu, anan muka fahimci dalilin da yasa sojojin nan suka damu da nemanmu.

Mun gudo daga asibitin cikin sa'a kuma mun sha wuyar b'oyewa mutane kafin mu had'u da wata tsohuwa wadda ta tausayawa Maria saboda tsohon cikinta ta sauke mu a gidanta, cikin 'yan kwanaki kuwa ciwonta yayi tsanani sosai har nakud'ar haihuwarka ta kamata, a cikin wannan ciwon Maria ta rik'e hannuna ta rok'e ni da in kula da abinda zata haifa kuma in shaida masa asalin mahaifinsa don kar ya k'are rayuwarsa irin tamu. Kwananta biyu cikin tsananin ciwon kafin ka fito duniya,?a ranar kuma hukumar asibitin nan suka gano inda muke aka shaidawa sojojin dake nemanmu.

Maria bata ko shura ba bayan fitowarka ta mutu saboda tsananin wahalar da tasha, Na san cewa idan har na gudu a lokacin nan to neman mu ba zai tab'a k'arewa ba, amma idan har suka ganni tare da gawar Maria,?kai zaka iya tsira daga nemansu, hakan yasa na rok'i tsohuwar nan data d'auke ka ta gudu don mu d'auke hankalinsu daga kanka. Ganina da kai na k'arshe kenan, sanda tsohuwar ta lullub'e ka cikin wani zani ta fita da kai ta k'ofar baya, ba tare ko anyi maka wanka na farko a duniya ba.

Wani abu dana tabbatar in cewa ko ka rayu a wannan lokacin dole hakan ya haddasa maka wani ciwon, don kazo duniya ne cikin wani irin hargitsattsen yanayi.

Ba wai hawaye ba, kuka ne sosai ya taho cikin idanun Adam, amma sai ya girgiza kansa alamun A'ah,?komai ya riga ya wuce, ya shud'e tare da lokaci mai dad'ewa, don haka koya zubar da hawayen babu amfani a yanzu,?yasa yatsansa guda d'aya ya d'auke guntuwar kwallar da taru a gefen idonsa... Ashe asalin ciwon kwakwalwarsa kenan, shi yasa iyayensa na can suka kasa gaya masa dalilin da ya haddasa masa shi, tunda sun same shi ne tare da ciwonsa. Tsaya, ta yaya ma suka same d'in?

A hankali ya maida idanunsa kan guntun rubutun daya rage ya cigaba.

Bayan sojojin nan sun kama ni an kuma binne gawar Maria,?sai na fahimce cewa ashe suna neman mu ne don kar mu shiga cikin mutane mu yad'a musu ciwon ba wai don su kashe mu ba, aka kaini wani babban asibitin sojoji inda ake warkar da sauran 'yan sansanin namu, wanda kowannensu ya girgiza jin mutuwar Maria, sai dai ba wanda na bud'i baki na shaidawa cewa ta haihu kafin ta mutu, watanmu biyar a asibitin cikin kulawa kafin a sallami kowannenmu da d'imbin kud'i a matsayin ladan wahalar da muka yi a sansanin yaki.

Ranar da zan bar cikin asibitin nan,? na ziyarci d'akin adana hotuna na sojojin nahiyar, a cikin hotunan fursononin da suka sadaukar da rayuwarsu a wajen y'akin, naga hoton Ahmad. A wannan lokacin ne kuma duk kukan rashin k'awa kuma 'yar'uwata dana tara tsawon watanni biyar ya b'alle daga idanuna, Maria taso Ahmad da zuciyarta guda kuma taso musu rayuwa mai kyau a gaba, amma hakan bai yiwu ba, ni d'in da ban tsara komai ba, ni na rayu kuma na sami tarin dukiyar da zan iya yin komai da ita a lokacin.

Naji cewa zan iya bayar da komai har kuwa da rayuwata a lokacin in da wani zai iya canja k'addarar Maria da Ahmad. Ya dawo musu da rayukansu, sannan ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarsu ta yadda komai zai tafi kamar yadda Maria ta tsara a mafarkinta.

Bayan barina asibitin, na koma gidan tsohuwar nan na nemeta don in karb'e ka ka girma a wajena, amma abin mamaki babu inda ban shiga ba amma ban ga matar ba,?sai a lokacin na gane gangancin da nayi,?na dank'a ka a hannun wadda ban sani ba, sai dai wane zabi nake dashi a lokacin?

Shekaruna goma tsakanin birni da wannan k'arami garin ina neman bayani akan wannan tsohuwar amma ban samu ba, sai a cikin shekara ta gama sha biyu ne na sami labarin mutuwarta daga wani mutumi a cikin garin,?yace min shekaru hudu baya, mota ta kad'e ta a gefen titi kuma ba wanda ya ganta da wani yaro k'arami.

Sai na shiga bin gidajen marayun dake wannan yankin ko ta kaika can ne, amma ban same ka ba saboda haka na k'addara cewa ka mutu,? kuma k'uncin yayi min yawa saboda haka na tattara komai nawa na bar k'asar, na komo Ingila na bud'e wata sabuwar rayuwar da ban tab'a jin dadinta ba saboda na k'addara cewa in har na sami dad'in rayuwa ban yiwa k'awata adalci ba wadda ta mutu cikin k'unci.

A yanzu cikin kwanakin nan ne nake yawan mafarki da Maria rik'e da kai hannunta lokacin data haife ka, hakan yasa na fara tunanin cewa baka mutu ba kenan, saboda haka na cigaba da bincike akanka har zuwa yanzu da nake rubuta wasik'ar nan,? na kudirta a raina cewa idan har na same ka zan shaida maka labarin iyayenka dalla-dalla fiye da yadda yake a rubuce yanzu, idan kuma bamu had'u ba, na tabbata a dunk'ule wannan zai ishe ka sanin komai, don idan har na mutu da nauyin da mahaifiyarka ta bar min, na tabbata ba ita kad'ai ba ko waye yaji labarin nan ma ba zai yafe min ba.

Idan har wasik'ar nan ta isa gareka d'an Maria, inaso ka san cewa mahaifiyarka tace in shaida maka ita bata da dangi amma ka nemi 'yanuwan Babanka a can k'asar Nigeria a wani gari mai suna IKARA! Asalin sunansa shine Ahmad Muhammad.

Adam na kaiwa daidai nan a karatunsa wata takardar check ta zamo ta fad'o gefen k'afarsa, a hankali ya mik'a hannunsa ya d'auko ta, idonsa ya gane masa zunzurutun ku'di cikin adadi na dalar k'asar ingila.

Da sauri ya sake juyawa ya karanta layi d'aya daya rage a jikin wasik'ar.

... Idan har na mutu, dukiyata gabad'aya taka ce d'an Maria, idan kuma har ba'a same ka ba, na sadaukar da komai ga gidajen marayu da tsofaffi marasa DANGI irina da mahaifiyarka.

A hankali ya ninke check d'in ya ajiye shi a gefe, abinda yake gabansa yanzu ya tabbata mutuwa ce kawai zata iya tsada shi, labarinsa bai k'are ba, hasali ma yanzu komai ya fara, a take yaji zuciyarsa tayi fiffike ta yiwa garin IKARA tsinke!

?%O??%

Ko kun tuna cewar Bintun da muka fara had'uwa da ita a farkon labarin nan daga IKARA take?

Wane k'ulli ne labarin nan ke shirin kwancewa?

Insha Allah next update zai zo kafin ranar Lahadi.


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

18

(&_&)

<ص?<ض?

Dangi anata taro...
Ko'ina d'aukacin masoya,
Aure ake na manya, lallai amaryar fa? tayi dace...
... Angonki ya kasance mai hak'uri da tausasawa.
<ض?<ص?

Kamar yadda wak'ar ke fad'a, k'aton hall ne wajen cike da dangi na birni da k'auye, b'angaren amarya da kuma b'angaren ango, kowa yazo don shaidawa da kuma taya murnar auren Aseeyah da Angonta mai suna Idris Makama.

Duk inda ka duba mutane ne cikin kwalliya da farin ciki,?gashi wajen yasha had'adden decoration tunda bayan kamu da akayi a jiya, wannan itace walima guda d'aya tilo da aka za'a gabatar sai kuma gobe Asabar a d'aura aure, ayi yini sannan a kai amarya baki d'aya.

Lokaci ne irin wanda Amarya da Ango basu dad'e da isowa ba, M.c ya rik'e su a tsakiyar fili yana tsokanarsa kala-kala sannan kuma yana kiran dangi su zo su nuna musu kara ta hanyar lik'i, adai lokacin kuma masu rabon abinci sun fara aikinsu na kawowa tebur-tebur, don haka banda hayaniya da kuma k'arar kid'a,?wajen a cakud'e yake da zirga-zirgarsu da kuma ta masu gajen hakurin cewa ba'a kawo abincin wajensu ba.

Fadeelah na zaune a wani tebur daga can gefe cikin k'awayen Fatima da suke ta hirarrakinsu suna d'aukar hoto, irin ankon jikinsu shi itama ta sanya, anyi mata d'inkin doguwar riga mai simple design data zauna b'am a jikinta, telan su Fatima da bai san awonta ne ba yayi dinkin,?don haka sai rigar taso ta matse ta daga sama,? sai ta d'ora light pink mayafi irin kalar ashoken dake kanta. Ita bata san k'awayen Fatiman da take zaune cikinsu ba kuma ba zata iya shiga cikin hirarsu ba saboda haka tayi shiru kawai tana kallon hada-hadar mutanen wajen, a cikin zuciyarta kuma dad'i take jiwa Aseeyah sosai, yadda ta kasance 'yar cikin dangi masu yawa da k'aunarta haka, gani take Aseeyah ta riga ta gama samun rabin nasarar rayuwa irin wadda ita take nema a yanzu ido rufe.

Allah ya riga ya karrama d'an Adam da rahamomi da yawa, a ciki kuwa harda sanyashi da yayi cikin mutane masu irin jinsinsa da ake kira da DANGI, ta dad'e da fahimtar cewa duk wata d'aukaka da nasarar da mutum zai samu a duniya in har baya cikin danginsa, to wallahi ko meye zai tashi a banza ne. Shi yasa har gobe take jinjinawa Mami Safiyya yadda ta iya barin wannan tarin dangin kaf! ta tafi k'asar da bata da kowa sai miji da 'ya'ya.

A hankali ta juya ta janyo jakarta daga bayan robobin ruwa da lemon dake ajiye kan table d'insu sannan ta zaro wayarta daga ciki. Ba tare da ta kunna ba ta kalli fuskarta akan duhun screen d'in, itafa har yanzu bata yarda cewa fuskarta take ka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?llo ba,?don an fente ta ne gabad'aya da abubuwa kala-kala a inda Fatima ta jata akayi musu kwalliya, irin dai wadda ke kan fuskar duk sauran 'yanmatan wajen da kuma su Zahra da take hangowa a gefe, sai dai su in ta kalle su sai taga kammaninsu suna nan, musamman ma dai Zahra da?tun da ta saba yin abarta.

Amma ita in ta kalli kanta sai taga kamar wata ce daban take kallo, don an k'ara fik'e komai na fuskar, an fito da ita d'al kamar wata 'yar tsanar da aka b'are a leda.

"Lalalala, gaskiya ya Fatima tayi kok'ari, yau kece kika yi kwalliya haka? Aunty deelah kin ganki kuwa? Kamar a sace!"

Ta tuno abinda Zahra ta fad'a sanda suka iso wajen, su kuma su Zahran sun fito zasu je taho da k'awayensu.

Ta kai hannu zata taba kan hancinta sai d'aya daga cikin k'awayen Rahma dake zagaye a teburinsu ta dakatar da ita.

"Kina tab'awa yanzu kwalliyar zata yi dabbare-dabbare, ki barshi kawai."

Tayi mata murmushi kawai ba tare da ta amsa ba, ta lura tunda suka zauna take son yi mata magana,? ita kuma bata iya sabon farad d'aya ba.

Beem!

A lokaci d'aya wayarta tayi haske alamun shigowar sak'o.

Na kira Mami ban same ta ba, kun isa wajen ne?

Al'ameen ne, kuma ta tabbata bai kira Mamin ba, kalmar 'Ku' tana nufin ita kenan, so yake yaji in ita tana wajen ne kafin ya k'araso. Wannan shine sabon yaren da suka fara.

"Eh kowa yana nan. Ka iso ne?"

Beem!

"Eh nazo, zaki fito ki nuna min inda Mami take? Ba zan dad'e ba."

Tayi murmushi ita kad'ai.

"Kana ina?"

Beem!

Ina harabar wajen."

"Okay, gani nan."

Sati biyu da kwanaki, kokarin Fatima da kuma dabarunta ya juya waccan bahaguwar alak'ar data fara tsakaninta da Al'ameen a farkon zuwansa.

Hakan kuma ya dad'a tafiya ne da yawan zaman Al'ameen a gidan, don sun riga sun gama aikin daya kawo su har abokan aikin nasa sun koma, shine kawai Mami ta rik'e shi da cewar ya tsaya ayi bikin Aseeyah don yaga al'adar bikin Nigeria da bai tab'a gani ba, saboda haka ya k'ara sati biyu akan komawarsa.

Komai ya fara ne da shawarar Fatima ta farko,? taje ta gayawa Mami cewa magungunan da take sha bata jin dadinsu ko zasu gwada zuwa asibiti taga likita sosai, ta san sarai Mami shi zata ce ya kaita don hidimar bikin Aseeyah tayi mata yawa,?saboda haka da murnarta ta gaya masa, kuma bai ruguza komai ba yace ta shirya suje.

Ya kaita wani asibitin kud'i mai kyau ba tare da ya katbi ATM d'in Mami ba,? akayi mata shigen check up d'in da ta saba da irinsa a washington aka kuma bata tulin magunguna, daga nan aka basu appointment cewa bayan kwana hudu su dawo, sai ya zama kafin cikar kwanaki hud'un nan a kullum zasu gaisasannan ya tambaye ta yadda take jin maganin a jikinta, a rana ta uku kuma ya shaidawa Mami cewa abokan aikinsa zasu zo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login