Showing 96001 words to 99000 words out of 153964 words

Chapter 33 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3798

komai ba sai da ya had'iye yawu.

"Amma Muhammad D'anki ne Maryam, ki dubi girman Allah kar ki cutar da yaron da bai san komai ba." Muryarsa cike take da rok'o.

"Wallahi na yaye shi Sadiq, kuma bana fatan sake had'a kaina da duk wani abu daya dangace ka."

Bai iya cewa komai ba, itama bata sake cewa komai ba tayi gaba ta barshi anan, ya rasa mai zaiyi sai? kawai ya sunkuyo cikin motar yace da Zakkiya.

"Ko zaki bita?"

"Yaya wai ciki? Kaga gidan kuwa? wallahi babu wajen da zamu zauna... Sauro ma kad'ai damun Muhammad zaiyi."

Sai ya gyad'a kansa kamar k'aramin yaro sannan ya mik'e tsaye, daidai sanda su Saminu suka fito daga zauren na Babban gida.

"Alhaji ai bamu san ta fito ba, Kawu ne ya kira mu wallahi."

"Ta koma can gidan da muka fara zuwa tace anan zata kwana." Ya fad'a muryarsa a rikice.

"Wai can gidan namu?" Cewar Saminu da mamaki.

"Eh yanzu tayi kwana ta tafi."

"Ai na zata tare zaku wuce."

Sadiq bai amsa ba, sai ya zura hannu a aljihunsa kawai ya zaro kudin da shi kansa bai san adadinsu ba ya damk'awa Saminun.

"Mu zamu nemi wani wajen da safe zamu dawo, ga wannan ko zata buk'aci wani abun."

Saminu ya damk'e kud'in sannan ta gefen idonsa ya yiwa Isah alamar...

Me na gaya maka?

D'akinta tun na asali da babu komai a ciki sai tarin buhunhunan dusa na d'aya daga cikin mazan dake haya a gidan, nan Mairo ta shiga ta ture buhunhunan gefe tayi kwanciyarta, sannan ta bud'e wani shafin kukan sabo fil! kukan da aka kange ta daga yinsa tsawon shekaru, don Allah wadai take da kowacce rana da take iya tunawa bayan barinta Ikara, tana cikin mafi munin rayuwa amma har take iya farin ciki a wancan lokacin.

Ta yaya a yanzu zata iya rayuwa da sanin cewa bak'in cikinta ne ya kashe mahaifiyarta? Ga mahaifinta ma har ya bar duniya bata san matsayinta a gurinsa ba, sannan yanzu ga k'anwarta can cikin kurkuku a garkame ana barazanar yanke mata hukuncin da zai guntule rayuwarta, Ya Allah! Bata tab'a sanin cewa dangi suna da damar da zasu k'untata su kuma tarwatsa rayuwar d'ayansu ba sai a yanzu.

Da kyar ta yarda ta karb'i bargon da Saminu ya kawo mata wanda ya aro a wajen matar wani abokinsa da yayi sabon aure. Zuciyarta cunkus! Ta kwana da niyyar yiwa cikin garin Zariya tsinke, bata da kowa a duniya yanzu data fi kusanci dashi kamar k'anwarta Bintu,? a wannan daren.

A wannan daren Sadiq ya kasa runtsawa cikin tangamemen d'akin daya kama a wani guest inn, Zakkiya da Muhammad na kwance a d'akin dake gefen nasa yayin da shi yake ta juyi cikin tashin hankali, saboda tsabar rud'ewa ma ya kasa tashi ko sallah yayi yaji sauk'i, maganganun da suka zama tushen shigowar Mairo cikin rayuwarsa da fitarta a yanzu su ke ta mimatawa suna kuma haskawa a kansa.

Na rasa yadda zanyi Yusif, abubuwa sun taru akaina, mahaifiyata a kull?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? um neman in kawo mata take yi, dukkan d'awainiyar gidan ta dawo kaina ga kud'in makarantar yaran nan su Zakkiya don yanzu haka sunfi wata a gida, ga kud'in fanshon Baba da kyar ake samu, gashi ni kaina neman na bukatuna nake, don wallahi kaya yanzu zance maka basu fi kala biyar nake dasu ba kod'addu.

Kuma ita taki ganewa, gani take tunda nayi karatu na fita da first class ba inda zanje in rasa aiki, taki fahimtar cewa abin ba'a nan yake ba, wallahi Yusuf kullum nazo kwanciya sai nayi kukan rashin mahaifina, tunda sanda yana nan bukatuna ne kawai akaina. Kuma yanzu bana ganin laifin yawan fad'an da suke yi da ita a da, don Mama mahaifiyata ce amma wallahi bata da uziri ko kad'an akan bukatun rayuwa, gani take kawai daka fita zaka samu ne ka kawo mata, bata damu da kome zai faru kafin a kawo matan ba.

Yusif d'in dake cikin idanunsa a wancan lokacin ya kyalkyale da dariya gami da bugun gefen kafad'unsa.

Shege Kwaro! Ai ni na san za'a zo nan kallonka kawai nake dama, ace har ni zan maka tayin abu ka fara kawo min qabli da ba'adin Allah yace Annabi yace, ub*n waye bai san Allah ba, kai rayuwar nan fa ina gaya maka yanzu ko ita kanta ibadar sai da kudi take tafiya, yanzu dai kalle ka, kaine shegen a ajinmu mai cinye komai, ni kuma irin masu nane muku don mu samu na assignment d'in nan, amma wani ya shigo yanzu wallahi cewa zaiyi almajirin gida na ne kai.

Ya b'ata rai a lokacin gami da jan tsaki.

"Ba sai ka zage ni ba Yusif na san duk wannan abin daka lissafa, yanzu dai ka gaya min in zaka taimake ni ko a'a, don gashi yamma har ta fara yi kuma ban koma na kai musu komai ba."

Yusif ya sake kyalkyalewa da sariya kafin yace.

"Ni na isa in ki taimakonka, amma dai ya kamata ka fara sanin cewa d'an adam baya d'aukewa wani talauci ko?"

"Na sani."

"Yawwa kwaro, dad'i na da kai ganewa yanzu zan baka abinda zai ishe ka zuwa gobe sai ka dawo muyi magana, tunda kace yamma tayi."

Minti uku bayan hakan, Yusif ya fito daga d'akin dake jikin tamfatsetsen falon da suke ciki rike da 'yan bandir na sababbin kud'i fil!.

"Dubu hamsin ne wannan kwaro, kaje ka sai muku abinda zaku ci zuwa gobe sai kazo muyi magana a nutse, tunda naga duk hankalinka yayi gida yanzu."

Daga lokacin da yasa hannunsa ya karb'i kudin nan, daga wannan lokacin ya tashi daga Sadiq d'in da mahaifinsa ya mutu ya bari, ya koma Sadiq d'in da zai iya bin kowacce hanya don faranta ran mahaifiyarsa, saboda washegari kuwa goma a gidan Yusif tayi masa, wanda shi bai fito ba sai wajen sha biyu na rana tukunna.

"Kana ji ko kwaro, na yanke shawarar taimakon ka ne saboda irin naka taimakon da kayi min a makaranta, shi yasa zan fad'a maka wannan sirrin da ko Uwata bata sanshi ba.

Ka san inda zaka samo mace mai kyau?"

Yayi sororo yana kallonsa.

"Mace mai kyau kuma Yusif?"

"Kwarai ita zata zama jarinka."

"Ban gane ba."

"Yawwa kwaro, ba wani abu ne mai wuya ba, wata k'ungiya ce ake shiga da farko, ba wai ta tsafi bace ko ta wani abu, su kawai jinin hailar Mace kyakkyawa suke bukata na watanni tara kawai, idan har na kai ka, ka amince zaka yi, to zasu baka rabin wasu mak'udan kud'i ne daga ranar da ka kai musu na farko, sannan zasu baka k'arashen a ranar da ka kai musu na k'arshe, daga nan ka gama dasu Kwaro, sai dai kayi ta cin dukiyarka da tsinke ka shiga kasuwancinka ka cigaba da habb'aka."

Yayi shiru yana juya zancen.

"Ba dai ce min zaka yi akwai haramun a ciki ba?"

"Da wannan Yusif, tunda bamu da tabbacin me suke yi da jinin nan, idan wani abu ne da zai iya cutar matan fa?"

"To ina ruwanka? da ka gama da ita sallamarta kawai zaka yi ta koma inda ta fito, in ma mutuwa tayi ruwanta... Kawai dai sai kayi taka tsan-tsan ne a zaman naku kar kaje a samu matsalar haihuwa."

Ya sake yin shiru.

"Kwaro kar kasa fa inyi nadamar gaya maka zancen nan."

"Ba haka bane Yusif, a ina zan samu Mace mai kyau yanzu? Yanda nake a talaka na?"

"Tambaya mai kyau, don ka san sai sun ganta ma k'iri da muzu, sannan za'a yarda a fara harkar da kai... Yanzu kawai k'auye zamu je inda za'a sami irin fulanin nan, mu juye zuciyar wata yarinya kawai ta rabu ma da 'yanuwanta ta biyo ka kamar yadda nima nayi, azo kawai a fara harka, da ta gama amfani ka sallameta ta koma garinsu."

Ya sake yin shiru yana lissafi a cikin kansa.

"Ba wahala fa kwaro, ni zan ranta maka kudin da za'a kaiwa malami yayi asiri in mun samo yarinyar, sannan zan dinga gaya maka yadda duk wata zaka kai musu jinin nata, da yadda zaka fara fito da arzik'inka a hankali har ka sami wata sana'ar da zaka kafu akanta in ma aikin gwamnatin ne ka samu yadda zaka gujewa zargi. Ka san ina sonka Sadiq shi yasa na bud'e maka cikina haka, in ba haka ba kai baka isa kaji wannan ba wallahi."

Bai ce dashi komai ba har a lokacin, shiru kawai yayi yana lissafi cikin kansa, lissafin da a k'arshe yaje ya dawo ya kuma yarda da kautacciyar hanyar da Yusif ya kwad'aita masa, hanyar da ta had'o da k'addarar Mairo cikin rayuwarsa, don a washegari tafiya ta kama shi Ikara zuwa janaizar matar wani aminin mahaifinsa, inda anan yaga Mairo wadsa ta dace da dukkan wata siffa da Yusif ya zayyana masa.

Babu jimawa suka yi asirin nan da shi da Yusif suka je duka binne a wani kabari cikin k'auyen Talfa, kuma Mairo ta rabo mahaifarta ta biyo shi, Yusif ya ranta masa isassun kudin daya aure ta dasu a lokacin bisa cewa mahaifiyarsa da 'yanuwansa da yayi bata da iyaye, sai wata mata kurum da ya biya ta zauna a wajenta har akayi bikin.

A wata na farko kuma ya d'auki jininta ya kai wa shugabbannin k'ungiyar da Yusif ya sanya shi cikinsu, kuma a wannan watan ya fara rik'e makudan kudin da bai taba mafarkin irinsu a rayuwarsa ba.


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

(&_&)

"Kinga abinda nake gaya miki ko Salame? Shi yasa nace dake ki d'auke ni mu tafi can k'auyen 'yar uwar nan taki inda ba mai sanin inda nake, amma kika kafe cewar wai hakan ne zai jawo a zarge ni, to yanzu gashi na zauna d'in ma amma ban fasa shiga zargi ba."

"Kalli nan kiga Habi, zamanki anan fa ba mai d'orewa bane, naji su Yahya suna magana da lauyan zasu san yadda za'ayi a fitar dake, kuma hakan shi zai sa ki gane cewar gwara zaman naki, da kin gudu yanzu su Yahyan zasu tsaya miki haka ne?"

Habiba juyar da kanta gefe ga barin kallon Salame.

"Wallahi wajen ne babu dad'i Salame, ga sauro, ga duhu, ga makewayi had'e da inda kake ciki, ga d'an banzan wari, ga fargaba sannan ga babu mai taimaka min haka zan ta kama bango ina kokarin mikewa.

Abu d'aya dake sawa inji dama-dama shine in na tuna kince min aikin malamin nan yana hanya, sai inyi tunanin ko yau ko gobe asirin nan na iya ci."

Salame ta nisa.

"Ni kaina tunanina kenan don baki ga yadda ya dad'a tabbatar mun cewa jinkirin da aka samu da niyyarsa ne ba kafin in yarda, ina gaya miki kwanan nan baturen nan zai d'ebi kunya ya koma inda ya fito, don har sunan lauyan naku sai da na fad'a masa ya bashi sa'a.

Habiba ta girgiza kanta.

"Layaunsu dai Salame, don na gaya miki asirin Niger tuni ya fara karyewa, tunda aka kawo ni fa banda su Sadiqu ('ya'yanta) a babban gida ba wanda ya lek'o ni."

"Kar ki damu ai zaman duniyar kenan Biba, ba yadda za'ayi komai ya tafi maka daidai in mun d'and'ana wuya yau, gobe dad'i zamu fantsama cikinsa don tabbas ance bayan wuya sai dadi."

Salame ta fad'i hakan ne da kokarin kaucewa fitowar dariyar k'etar da? zuciyarta ke aunawa Habiba tun shigowarta wajen, idan ta kalli duk yadda ta fita haoyacinta ga idanu kwal! a waje, sai kuma ta? hango kud'inta dubu d'ari da hamsin cif! A cikin sif d'inta ta gida.

Yo ni mahaukaciya ce kamar ke Habi zan d'auki kudi irin haka in kaiwa inda babu tabbas d'in nasara? Ko da nasarar ma ni na tara irinsu ne da zan?kaiwa wani mak'iyin Allah k'aton banza ya lafe? Ke dai da baki yarda da lamarin ubangiji ba yi ta sa rai!

A can wani d'aki na ganawar bak'i dake cikin kotun kuma Mami ta kalli Fadeelah tace.

"Ba yadda bamu yi ba amma wallahi sun hana mu shigowa da waya, Al'ameen yana ta son magana dake tun safe yake ta kirana."

Ta fad'a rik'e da hannun Fadeelan.

"Fatima ma tana waje ita da Abdullahi, tun safe muke tsaye anan baki ga da yadda aka bar mu muka shigo ba sai da Abdullahi ya basu kud'i tukunna, shima suka ce wai mutum biyu ne kawai zasu iya ganin naki, amma kowa yana gaishe ki Deelah, daga kan su Zahra har su Aseeyah ba wanda baya kira yaji me ake ciki, Hajiya Amarya ma ta damu sosai wallahi."

Jin yadda muryarta ta fara rawa yasa Fadeelah ta mik'o d'aya hannunta ta damk'e nata da duka biyun.

"Mami dan Allah... dan Allah ki rage damuwar nan insha Allah komai warware, Allah zai dube mu, Allah yana bayan mai gaskiya a kodayaushe."

Muryarta a tsaye take kyam, tsayen dake nuna cewar ba zuciyarta kad'ai ba, hatta ruhinta ya dad'e da karb'ar al'amarin nan, don tayi duk wata damuwar data zarce tunanin d'an adam ta zarta har ta kai mak'urar da komai ma yanzu kallonsa kawai take, an dad'e da k'ure malejin da hankalinta zai tashi akan wani abun.

"Tabbas haka ne..." Cewar Aunty Hadiza.

"Allah yana ganin komai Safiyya, sannan ga wannan lauyan shima yana iya kokarinsa, za'a yi nasara insha Allah."

Adam. Fadeelah ta furta sunan a ranta, Allah ya sani bayan dogaronta ga Allah, ta gutsira wani b'angare na fatanta akansa, duk da cewa reto yake yana lilo don bata gama yarda dashi ba har yanzu, amma wani b'ari na zuciyarta ya fara yarda cewa ya san abinda yake yi tun daga zaman kotun da akayi, akwai wani abu game da yadda yake bin komai a nutse da kuma irin maganganun da yake gaya mata. Ya Allah! Yake gaya mata? Yaushe ta ma ta k'arasa ganinsa tun bayan ranar da za'a fara shari'ar.

Mami tasa hannunta d'aya ta d'auke kwallar da ke shirin taruwa a idonta.

"Haka ne insha Allah komai zai zo ya wuce." Ta d'an shak'i numfashi kad'an sannan ta cigaba da cewa.

"Daddy ma gobe zai taho, na san ba lallai ya samu zaman kotun ba."

"Allah ya kaimu lafiya, ni dai fatana kar shari'ar nan tayi tsawo da yawa, Allah ya baiyana komai cikin k'ank'anin lokaci."

Aunty Hadiza ta sake fad'a, dukkansu suka had'a baki wajen furta Ameen, amma na Fadeelah iya fatar baki kawai ya tsaya, babu sautin.

"Deelah ya cikin wajen yake? Da sauk'in zama?" Mami ta tambaya.

A lokaci guda idonta ya hango mata duhun cikin cell d'inta da kuma azababben warin dake tashi daga toilet d'in da Allah kad'ai ya san adadin mutanen da suka amfana dashi, ga saurayen da kamar da gayya ake koro su, sai tayi murmushi a gefen lebb'enta tace.

"Mami ba wata matsala waje ne kawai na kwana, kuma ba'a had'ani da kowa ba ni kad'ai ce a ciki."

Daga murmushin kad'ai kowa zai fahimci cewa ba haka taso fad'a ba ita kanta, don haka Mami ta jawo hannunta ta janye hannun bak'ar jallabiyar da ba'a tab'a barinta ta canja ba.

Ilai kuwa tabo ne jazur na cizon sauro yarab- yarab dashi a jikin hannun nata kusan koina kuma.

"Deelah ki daina b'oye min abu dan Allah, in baki sani ba har fuskarki haka take."

"Wallahi Mami babu zafi, cizon ne kawai, kuma ni bana ma jin sauron."

"Waya baki shawarar sanya bak'in kayan ne ma Fadeelah, ai dole su k'ara takura ki." Cewar Aunty Hadiza.

Mami ta juya ta kalle ta tace.

"Yanzu ya zamu yi? Gashi basa bari a shigo da komai."

K'ofar wajen ta bud'e kuma babu b'ata lokaci Adam ya sanyo kansa ciki.

Dukkaninsu suka juya suka kalle shi yayin da Fadeelah ta tsinci wani abu game da bugun zuciyarta ya canja, sai?kawai ta sunkuyar da kanta kan yatsunta ba tare da ta amsa sallamarsa da su Mami ke amsawa ba.

Ya k'araso ciki, sannan ya gaida su Mamin, mamaki ya kamata jin yadda muryarsa ta sauk'a kasa alamun tsugunnawa yayi, wai har yaushe yazo Nigeria ne ya iya al'adunsu? Mami ta shiga tambayarsa game da aikin nasu yana bata amsa daki-daki, har sai da Aunty Hadiza ta dakatar da ita don ji tayi kamar tana son ya gaya mata k'arshen shari'ar da ba wanda ya sanshi ne.

"To Deelah bari mu tafi sai gobe insha Allah, ki kula da kanki kinji?"

Cewar Mamin lokacin da suka mik'e. Sai tayo saurin jawo rigarta ta rufe hannunta ganin ya juyo da idonsa kanta shima.

A hankali ta had'iye wani dunk'ulen abu mai zafi cikin makogwaronta, duk wanda aka kai makarantar kwana alhali baya so, shi kad'ai ne zai fahimci abinda taji a lokacin, shi kadai ne zai ji makamancin abinda taji a lokacin da iyayensa suka juya suka tafi aka barshi a sabuwar duniyar da bai san koda mahaluki guda ba daga shi sai 'yan kayansa.

Kwata-kwata bata ji sallamar Aunty Hadiza ba ma har suka fita daga d'akin. Kwalla ta taru a idanunta, amma tayi saurin dakatar da ita, tuna cewa Adam na tsaye a kanta.

Ya nazarci fuskarta daga inda yake tsaye, ta canja kwarai daga yadda tazo wajen amma kammaninta suna nan, musamman wad'annan idanun nata... bashi take kallo ba a lokacin ba amma ya gansu sanda take kallon su Mami, yanzu m kamar kullum ne, duk sanda ya kalle su sai yaji kamar mayen k'arfe ne a ciki dake jansa zuwa gare ta, saboda haka ya d'auke idonsa kan bakinta, d'an surut dashi kamar ta shafa masa wani abun...

Ya Allah! Sai ya janye idonsa da sauri sannan yayi gyaran murya.

"In ga hannunki..." Muryarsa a hankali, mai zurfi, kuma a tsare ta fad'a.

Ba shiri Fadeelah ta d'ago da fararen idanunta ta kalle shi. Yana tsaye daga baya kad'an ya zura dukkan hannayensa biyu cikin aljuhun wandonsa.

"Me kace?"

"Nace ki nuna min hannunki." Ya sake maimaitawa muryarsa fik'e da wani iko mai sanyi.

"Saboda me?" Ta sake tambaya don ta kasa gane me yake nufi da ta nuna masa hannunta.

Ya cije lebb'ensa kad'an kafin yace.

"Saboda na tambaya."

Sai ta dag'e siririyar girarta d'aya alamun tamabaya itama.

"Me ya kawo hannuna cikin wannan shari'ar?"

Maimakon ya amsa sai kawai taga ya fara tahowa inda take hannayensa duka biyun a aljihun wandonsa, sai da yazo gabanta sannan ya zaro su ya tsugunna daidai saitin gwiwoyinta, kuma bata yi wani tunanin me zai yi ba yasa duka hannayensa biyun ya janyo nata.

Abu biyu suka had'e cikin kwakwalwar Fadeelah a lokacin, farko wannan k'amshin nasa ya cika kowacce kwayar halitta ta hancinta da kuma cikin kwakwalwarta, his musky male scent. Na biyu kuma sanyin tattausar fatar hannunsa daya sauka akan nata, taji tsigar hannun da ya zama d'an mitsisi akan nasa gabad'aya ta tashi. A sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login