Showing 66001 words to 69000 words out of 153964 words

Chapter 23 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3781

da ya samu ya kankaro da kyar ta sake subuce masa?

Ya mik'e daga zaunen da yake kan kujerar karatu ta cikin d'akinsa ya fad'a toilet. Tun bayan dawowarsa daga Nigeria,?har yanzu ba'a d'ora shi kan wani sabon case ba saboda haka yake hutunsa yadda yaga dama, baya ma shiga ma'aikatar tasu da wuri.

Bayan ya fito ne ya shirya cikin wata riga mai dogon hannu kalar ruwan toka da wando bak'i, ya dora wata katuwar jacket akai kalar maroon saboda sanyi da ake surawa cikin garin a lokacin sannan ya sunke kafafunsa cikin safa mai kauri itama.

Al'ameen mai kyau ne,? Fadeelah tasha fada... Irin samarin nan ne da ko daga nesa ka hango su cikin tarin mutane zaka ji zuciyarka ta tsaya akansu su kad'ai! Ita kanta mahaifiyarsa babban alfaharinta game dashi na kyawunsa ne. Saboda haka sai ya k'ara haskawa cikin kalar kayan, ya feshe jikinsa da turare sannan ya d'ebi wayoyinsa ya fita zuwa falo don samin abinda zai ci. Allah ya sani yayi kewar girkin Mami da Fadeela kamar me!

"A'a ga Ango fa ya fara kyallinsa tun yanzu."

Muryar wata daga cikin 'yanuwan Mami ta fad'a a sanda ya sanyo k'afa daga corridor zuwa cikin falon.

Zuciyarsa ta sake ruftawa cikin raminta sanda ya d'aga ido ya kalle su,?'yanuwa Mamin tasa ne da yawa a falon sannan ga kaya ma birjik ana ta hayaniya... Hayaniyar shirye-shiye... Shirye-shiryen aurensa da Hamida... Hamida dai 'yar kawar Mami... Mami dake tsakiyar falon a zaune fuskarta cike da farin ciki... Farin cikin ganin komai na tafiyar mata daidai ba tare da ta san me suka yi ba... Abinda suka yi shi da mahaifinsa!

Na zuwa neman Auren Fadeelah har Nigeria da sanya ranar bikinsu kafin ma nata data dad'e tana tanadinsa!

?%O??%

Ga dai Adam a garin Abuja.

Ga Fadeelah a garin Abuja.

Sannan ga mutanen Ikara har biyu,? Sa'id da Sadiya mai aikatau a garin Abuja.

Sannan kuma ga shirye-shiryen biki shima a garin Abuja.

Can k'asar turawa kuma ga Al'ameen tsumu-tsumu cikin k'arya da ya rufewa Fadeelah da kuma mahaifiyarsa dake shirin yi masa aure!

Toh me kuke tunani zai zo a gaba?=??

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

*22*

(&_&)

BAYAN WATA GUDA

Rayuwa ta cigaba da gangarawa a kowanne b'angare na duniya,? abubuwa na faruwa wasu kuma na shud'ewa, mutuwa, haihuwa, arziki,? talauci, mulki, nasara, shirye-shirye,? cikin wad'annan abubuwan babu d'aya da lokaci ya tsaida su.

A cikin haka ne kuma shirye-shirye da lokacin da su Daddy suka tsayar na auren Fadeelah da Al'ameen ke gabatowa, saboda haka sai ya zama kusan dukkan hidima irinta bikin Aseeya ta dawo kan Aunty Hadiza da kuma Mami wadanda suka tsaya akan abun, banda su ma Fadeelah ta lura kowa nata 'yan shirye shiryensa,? babu irin su Zahra dake ta tanadin kaya set-set wanda zasu shiga su fita su kuma gwangwanje kamar yadda suke fad'i.

Sannan su Farouk da Usman ma na shirin had'a Cocktail su da abokanansu a cewarsu Aseeyah bata barsu sunyi komai da bikinta ba, ga Hajiya Amarya ma data ce zata karrama mai sunanta tayi yininta guda a gida, kowa dai nata 'yan shirye-shiryensa banda ita... Ita d'in da take ginshik'i kuma Amaryar bikin.

A kullum ta tashi ta kalli hasken safiya, sai ta tambayi kanta wace irin rayuwa take yi ne? Ita ko a labari bata tab'a jin mutum mai cakud'addiyar k'addara irin tata ba. Misali game da ciwonta, a da bata tab'a barin kwakwalwarta ta yarda cewa ciwonta nakasa ne ba balle har ta nuna raunin da wasu zasu tausaya mata,?amma a yanzu hannu biyu tasa ta karb'i cewa kwakwalwarta ba daidai take da ta sauran mutane ba, ita d'in mai lalura ce da abinda ya raba ta da MAHAUKACI kad'an ne.

Saboda in ba rashin hankalin ba ta rasa abinda tunaninta ke janta akansa yanzu,?ita fa ta damu da Al'ameen d'in nan har ta bashi hanyar daya sake neman aurenta a karo na biyu, amma a yanzu duk sanda ta gama waya dashi, sai komai ya tsaya mata cak! Ta kasa farin ciki, ta kasa sakewa kuma ta kasa karb'ar al'amarin hannu biyu duk da irin kulawar da yake nuna mata. Mami tace wai hakan ba wani abu bane, wai duk macen da za'ayi bikinta haka take ji, wai shi auren wani abu ne mai girma dake canja rayuwar d'iya mace.

Amma wallahi ita abinda take ji a ranta gani take yafi k'arfin taraddadin aure, ji take kamar mutuwarta ce ke shirin k'arasowa, kamar a kowanne motsawar lokaci zata iya bud'e ido taga mala'ikan d'aukan rai a gabanta ko kuma taji nauyin k'asar kabari akanta.

Bayan haka kuma ga wani azababben k'ulafacin son 'yanuwanta daya fara damunta, wad'annan dai 'yanuwan nata da bata iya tuna ko fuska d'aya a cikinsu, saboda da ace ana samun d'an adam d'in da yake zuwa babu dangi a duniya, da tuni ta dad'e da saka kanta cikin wannan layin.

Amma sanin cewa dole tana dasu d'in ne yake sawa in ta waiga taga Mami nata shirye-shiryen bikin, sai ta hango lokacin na Aseeyah da gabad'ayansu Mamin harda mahaifiyarta ake ta wannan hidimar, amma ita yanzu inda za'a d'auke harkar mutuntaka da kuma kyautatawa babu d'aya a cikinsu da zai mata wannan wahalar.

Da a cikin DANGINTA take fa? Tare da iyayenta wad'anda suka haife ta, ta san ko babu kyautatawar ita hakk'i ce akansu da dole ne su sauke, suna ma tunawa da ita a yanzu? Ko suna ma da rai tukunna? Tunda kafin zamanta ya koma wajen Hajiyar Daddy a wancan lokacin anyi cigiya kamar wanda ya yar da kwabonsa na k'arshe a duniya amma babu wanda yazo yace shi d'anuwanta ne, hakan ne yasa a baya ta cire tunaninsu a ranta ta rungumi rayuwar su Daddy kawai, amma me yasa komai ke shirin dawowa sabo a yanzu? Da irin wannan abun da take ji me ya raba kwakwalwarta da matakin hauka ?

"Kara ta sosai mana a wuyan na gani in ta zauna,?kin san ba mai saukowa bace."

Mami ta fad'a tana kallon Fadeelan dake zaune akan stool na gaban mudubi tana rik'e da d'aya daga cikin sark'okin da suka baje akan gadon d'akin, wata 'yar k'aramar riga ce a jikinta dake nuna bata dad'e daga tashi daga bacci ba amma su Mami har sunje siyayya sun dawo.

"Wai tsoron sarkar kike ji ne?" Fatima dake ta fito da wasu daga kwalayensu ta fad'a tana kallon fuskarta ta cikin mudubin.

"Naji kamar tana da nauyi ne." Muryarta ta amsa a hankali.

"To mik'o ta nan tunda kika ce nauyi Deelah na san ba sakawa zaki yi ba."

Ta juyo a hankali ta mik'a mata idonta na kallon sauran kwalayen sark'okin. A satin daya wuce ne Al'ameen ya aikowa Mami da zunzurutun kud'in da bata san wane adadi na miloyoyi suka tsaya a kid'in Nigeria ba da cewar ayi mata siyayyar kaya (lefe kenan) da kuma wani sh'ani na bikin.

Bata san me yasa ba amma haka kurum jikinta yake bata cewa bikin nan ba daidai yake da kowanne ba, akwai wani abu tsakanin Al'ameen da Mami da suke b'oye mata, sai dai bata da hujja ko shaidar menene shi.

"A cikin atamfofin nan akwai wata mai lemon gree da milk ko?" Mami ta tambaya tana kallon Fatima.

"Anya kuwa kamar lemon green da brown ne sai wata mai lemon green kawai koh?"

"A'a gaskiya ni naga mai irin wannan kalar, yaya Hadiza ce fa ta d'auko ta ma ina tunawa."

"Toh bari in duba." Cewar Fatima ta mik'e ta tafi can d'akin Mamin inda kayan suke.

A lokacin ne kuma Fadeelah taga dama ce gareta da zata fad'awa Mamin abinda ke cin ranta.

"Mami."

Ta kira sunan da dukkan dauriyar da take da ita a lokacin.

"Al'ameen har yanzu bai fadi inda zan zauna ba, kunyi maganar dashi ne?"

Zata iya rantsewa wani abu ya gifta cikin idon Mamin kafin ta girgiza kanta tace.

"Bamu yi ba deelah, amma me yasa zaki damu kanki tunda dai ai in an d'aura auren ba zai barki anan ba."

"Mami karatuna nake tunani,? so nake in san matsayarsa tun tanzu kafin a koma hutun."

"Fadeelah karatu ba matsala bane, duk inda ya d'auke ki ya kaiki a duniya zaki cigaba da yinsa, nasha gaya miki Al'ameen bashi da matsala ko kad'an, wallahi duk abinda kike so shi zai yi."

"To Mami Aunty Miryaamah fa? Ni fa har yanzu banji kuna zancenta ba, banji ana cewa suma suna nasu shirin ba, sannan shima banda lokacin da yace min ta amince da zancen auren baya tab'a son in d'auko masa zancenta, dan Allah Mami in da wani abin ki fad'a min."

Ka san abinda mutum yake ji a lokacin da yake son nusar da k'aramin yaron da mahaifiyarsa ta mutu cewa ba zata tab'a dawowa ba? Sak haka Mami taji sanda Fadeeelah ta fad'i hakan, ta yaya zata gaya mata cewa Aunty Miryamah bata san da zancen auren nan ba kwata-kwata? Ta yaya zata gaya mata cewa Al'ammen ya roke ta ne kamar hauka kan ta taya shi boye wannan sirrin don ya sami Fadeelah a rayuwarsa? Ta yaya zata gaya mata cewa suna hasashen Aunty Miryaman zata saduda ne in taga an kai k'arshen komai?

"Mami, Mami, Umma ce ke kiranki."

Rahma ta katse komai sanda ta shigo cikin d'akin rike da wayar Mami da mahaifiyarta Aunty Hadiza ke kira,? bata jira konai ba kuwa ta kara mata a kunne.

"Yaya wayar na can falo ne wallahi..." Cewar Mami cikin wayar.

"Mrs. Skeleton ya akayi ne?" Rahma ta fada sanda ta juyo ta kalle ta.

Wani murmushi ya subuce a kumatun Fadeelah,? tace.

"Nice kwarangwal d'in?"

"To ba gashi nan ba..." Ta amsa tana zama a gefen gadon.

"Duk kin bi kin fita haiyacinki tun yanzu."

Ko waye a takalmina zai fita haiyacinsa Rahma.

Ta amsa hakan a cikin tanta ba tare da ta furta ba.

"Kinga deelah..." Cewar Rahman tana kamo hannunta.

"Ki kwantar da hankalinki fa, Aseeyah tace min ba wani abu wallahi mijin ma watarana in kika tashi ji zaki yi haushinsa kike ji, sannan ko ni da zan auri miskilin yaya Saifudeen ban d'aga hankalina kamar ke da kullum Al'ameen d'in nan ke tare dake yana nuna miki kulawa ba."

A daidai sanda Rahman ta fadi haka,? wayarta ta zabi lokacin ta shiga ruri na alamar shigowar kira,?idonta ya kai kan sunan.

Al'ameen ne.

Ta juya ta kalli Rahma dake kallonta sannan Mami dake magana tana ta had'a sarkokin nan, da Fatima ta shigo a lokacin tana nuna wa Mami atamfar data d'auko, sai ta dawo da idonta kan wayar.

A wannan lokacin ta yarda cewa ba zancen karatunta ba, ba zancen wajen zama ba, ko zancen Aunty Miryaamah mahaifiyarsa bai isa ya canja k'addararta da Al'ameen ba, sai dai wani abin kuma daban, wani abu da zai shallake tunaninta!

***

RANAR D'AYA GA FARKON WATA.

Harabar gidan Mami na d'auke da mutane tsilla-tsilla yayin da wajen yake yab'e da wani tsantsareren decoration mai d'aukan hankali, mazaunin kujeru kad'ai da zagayen teburinsu abin kallon ne, don tun kafin wajen ya fara cika da mutane akwai robobin lemu na ruwa da kuma kayan marmari fal wanda suka fi k'arfin duk mutanen da zasu zauna a kowanne tebur.

Idan ka kalli mazaunin amarya kuwa, ba zaka tab'a son d'auke idonka da wuri ba don adon al'adar gargajiyar dake jikinsa abin sha'awa da zai ka shagala wajen kallinsa, ga tsofaffi ma har hakan ya tuna musu da lokacin k'uruciyarsu a doron duniya. Daga saman rumfar kuma wani rubutu ne mai kyalli dake haska harafan...

'Barka da zuwa Kamu da Walimar Fadeelah Ahmad Malik!'

A harabar wajen ba mutane sosai sai tsilla-tsilla,?amma cikin gidan dank'am yake da tarin jama'ar dake ta fafutukar shiryawa wasu kuma na k'arasa packaging kayan souvenirs d'in da za'a raba, ga 'yan aiki birjik har da na gidan Hajiya Amarya da Aunty hadiza ta tattaro sai faman aikin wanke-wanke suke da kuma d'ora abinci bayan wanda akayi ordering da za'???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a raba a wajen.

Mami kam! bama ka ganin inda take,? don minti d'aya ne ka ganta minti d'aya kuma duk gidan sai a nemeta a rasa. Usman na ta bin Fatima yana rokon wai sun gaiyato abokansu ta taimaka in abincin yazo akai musu can boys quaters d'in Faruk, su Zahra kuwa d'akinsu guda suka cika da k'awayensu da suka fara zuwa, in banda kwalliya,? hira da kuma waya da samarin da aka had'a agenda dasu ba abinda ke wanzuwa a d'akin. Fadeelah bata da dangi amma wallahi a ranar nan ba mai gane hakan, don kowa daga b'angarensa yayo gayya daidai gwargwado ta mutanensa.

Sai dai duk wannan bidirin da akeyi a cikin gidan, ita Amaryar na can band'akin dake cikin d'akin Daddy inda shi kad'ai ne ba mutane ta k'ulle kanta, ta rufe 'basin' na zama sannan ta hau ta dunk'ule jikinta akai, idonta a tsaye suke kyam! kan wayarta tana kallon zunzurutun adadin kud'in da suka shigo account d'inta na banki daga account d'in Mami.

"Fadeelah kud'in kayan d'aki ne wannan, in kinje duk abinda yayi miki ki siya kiyi amfani dashi, tunda kinga baza'a d'ebi kaya har can ba."

CAN! can yana nufin k'asar America,? inda dai ta baro take murnar ta dawo tushe ta inda rayuwarta zata gyaru ta inganta watakila ma har ta samu waraka daga ciwonta, ashe wannan burin zance ne a iska kawai! Tarihi ne zai sake maimaita kansa kamar yadda ya faru ga Mami, da aure ya d'auke ta cak! ya tsame ta daga cikin 'yanuwa zuwa wata nahiya ta duniya. A baya gani take Mami tayi mutuk'ar k'ok'ari data iya zaman can d'in,? sai yanzu ta gane ashe ba kokari tayi ba, abu ne da ba yadda zaka yi dashi....

Ba zaka iya sa k'afa ka ture ba ko kasa hannu ka tsige shi, manne yake cikin k'addararka da ba mai iya canja hakan sai ubangiji!

Allah ya sani ta riga ta gama fahimta a yanzu auren ne kwata-kwata bata so, shi yasa take jin kamar zata mutu, amma kuma tana son Al'ameen, irin son da take ganin tsananin kirkinsa da kuma tsananin kyawunsa, bayan haka bata jin komai a ranta game dashi amma ta yarda cewa iya wad'annan abubuwan kad'ai zasu saka taji dad'in zama dashi,? sai dai inda ta baro zata koma fa? Wajen da a yanzu bata da kowa sai nasa DANGIN, wanda yake k'unshe da mahaifiyarsa da har yanzu bata san matsayinta a wajenta ba. Ya dai ce mata yau zasu taho, amma bata san 'SU' wa da wa ya k'unsa ba, abinda tafi rik'ewa kawai shine zasu zo su tafi da ita, CAN inda sabon DANGIN data samu a yanzu ma zata yi musu nisa.

Tasa bayan hannunta ta share kwalla mai d'umin data taru a idonta, ita haka ubangiji ya kaddaro mata rayuwarta, daga nan sai can, daga wuya sai dad'i daga dad'in kuma a koma wuyar, fatanta d'aya a yanzu shine ta samu farin ciki tare da Al'ameen, farin cikin da zai d'ebe mata wasu abubuwan.

K'ofar band'akin ta shiga bugawa da karfi sannan muryar Aunty Hadiza maman Rahma ta biyo baya.

"Fadeelah bud'e k'ofar mana,?me kike yi? Ga mutane har sun fara zuwa baki shirya ba."

Sai ta kashe wayarta a hankali sannan ta d'ora saman sink, bata da yadda zata yi fa, bata da zab'i babu ma mai bata zab'in... Komai tafiya yake kawai kamar yadda ubangiji ya tsara, ita nata kallo ne kawai!

A hankali ta bud'e k'ofar.

"Ga mai kwalliya nan tun d'azu muke neman..."

Sai maganarta ta katse ganin hawaye shab'e-shab'e a fuskarta.

"Haba 'yanmatan Mami, kukan ne tun safe har yanzu? Girma ne fa ya hau kanki meye abin masa kuka?"

Sai ta jawota ta rungume ta a faffad'an jikinta, kamar dama hakan Fadeelah ke jira sai ta dunk'ule kanta cikin kafad'unta ta shiga rera shi a hankali, irin mai zurfin nan dake tasowa tun daga k'asan zuciya.

"Haka kowa ke ji Fadeelah, ba ke kadai ce ba kowacce mace irin wannan zafin rabuwar sai ya hau kanta, amma komai yana wucewa ne a d'an kankanin lokaci, da kanki watarana in kinzo ma zaki tashi ki tafi gidanki..."

Maganganu masu taushi da kwantar da hankali Aunty Hadiza tayi ta rad'a mata a kunne har da kyar ta samu ta shawo kanta, ta tsaida kukan nata da kyar sauran ya koma k'asan zuciyarta ya shiga jiran wani lokacin. Sannan ta saka ta ta koma band'akin ta wanke fuskarta kafin ta zauna gaban mai kwalliyar dake jiranta da k'aton akwatinta, ba yadda ta iya haka ta d'anyi mata murmushi sannan ta fuskance ta, sai daga baya kuma tayi tunanin meye amfanin ma murmushin bayan ta ganta ta gama kuka yanzu.

"Bari inje in turo miki Fatima da kayan da zaki saka."

Aunty Hadiza ta fad'a sannan ta bud'e k'ofar d'akin ta fita, da kyar ta samu Fatiman a cikin taron jama'ar gidan ta bata muk'ullin wardrobe din Mami da cewar taje ta d'auko kayan Fadeelah ta kai mata. Daga nan ta nufi masaukin k'awayenta da suka fara taruwa a lokacin, ta tarar wata Nafisa daga cikin k'awayen nata tana ta bada labarin sabuwar 'yar aikin da tayi da bata gajiya kamar inji.

"Ke nifa yanzu tiles d'in barandar wajen gidana ma fa sai ki kalli fuskarki kamar mudubi saboda tsabar yawan mopping."

Wata Jamila tace.

"Dan Allah daga ina take nima insa a samo min 'yar garinsu?"

"Daga Ikara take wai, sunanta Sadiya kuma bazawara ce wallahi ba yarinya ba."

"Ina ne Ikara?"

Aunty Hadiza ta tambaya tana zama cikinsu.

"Can wajen hanyar Zariya ne inji ta."

Daidai lokacin da Sadiyan ta k'araso rik'e da d'an matar, ta gaishe su d'aya bayan d'aya sannan ta karb'i jakar kayansa ta shiga canja masa rigar daya b'ata.

Basu cigaba da hirarta ba sai suka canja wata,?amma kasancewar ita Sadiyan taji su tun farko,?sai tayi kwafa a hankali sannan ta maimaita abinda ta kudirtawa ranta tun farkon zuwanta gidan.

Kaina nake gyarawa waje baiwar Allah, zamanki a gidan nan ya kusa k'arewa!

Fatima ta k'araso a daidai lokacin nan d'auke da manyan ledoji na kayan Fadeelah, ta mik'awa Aunty Hadiza muk'ullin sannan tace.

"Aunty ba mai taya ni dan Allah,? wallahi kayan da nauyi."

Caraf! Nafisa ta kalli 'yar aikinta Sadiya tace.

"Bar saka masa kayan nan ki mik'o min shi, taya ta ku kai kayan nan sai ki dawo."

Sadiya ta mik'e da sauri ta mik'e ta mik'a mata yaron da jakar?sannan ta kinkimi duka ledojin hannun Fatima tabi bayanta dasu zuwa d'akin da ake shirya Amarya Fadeelah!

?%O??%

=?
?

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

23

(&_&)

RANAR DAYA GA FARKON WATA.

ASOKORO, ABUJA.

Ta juya miyar dake zab'alb'ala kan gas d'in gabanta a hankali yayin da gwalantun d'anta Muhammad dake zaune a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login