Showing 111001 words to 114000 words out of 153964 words

Chapter 38 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3802

ne na can Kano, suma sun san Fadeelah lokacin da ta zauna tare da mahaifiyar tawa kafin rasuwarta, shi yasa suka zo don suyi muku jaje."

"Allah sarki, sannunku, sannunku... Sannu da zuwa, Mun gode wallahi."

Kawu Ibrahim ya fad'a yana sake mik'a musu hannu suka gaisa a karo na biyu, Kawu Bashir da Kawu Nura ma dake gefensa suma suka k'ara mik'a musu hannu suka gaisa.

Daddy ya sake gyaran murya yace.

"Daga can Kurkukun muke yanzu mun samu damar ganin _Warden_... Ina nufi shi shugaban prison d'in, yayi mana bayanin cewa su yanzu basu da ikon sakinta, daga can Kotun da aka kawo ta ne zasu iya yin magana sannan a iya maida ita can amma yace su babu abinda zasu iya yi."

"Kamar dai yadda wancan mutumin ya fad'a mana tun da fari." Cewar Kawu Ibrahim.

"Karka damu Alhaji, komai mai wucewa ne insha Allahu yarinyar nan zata fito komai ya zama tarihi." Cewar d'aya daga cikin bak'in Kanon nan.

"In Allah." Kawu Bashir ya amsa.

Kawu Ibrahim ya sake cewa. "Bana cire rai daga hakan insha Allah, tunda na san koi'na shi lauyan nata ya tafi zai dawo kafin a sake wani zaman, kuma saukinta ma yana tare suke da d'an gidan Nura..." Ya nuna Kawu Nura dake gefensa.

"... Ko bai fad'a ba za'a san inda suka je don mu anan bincike kawai yace mana zasu tafi."

Kowa ya amsa banda Daddy da ya d'an sunkuyar da kansa kawai, don baya son ya fad'a musu cewa ya saka ana tracking wayoyin Adam da Sa'id d'in amma har yanzu an kasa samun bayanin inda suke, da alama duk inda suke babu ma service d'in waya balle har tayi aiki, abinda ke d'aure masa kai kenan, ina zasu je da babu ko sevice d'in waya tsawon wannan kwanakin?

"Ya iyalin taka? Ina fata dai baka sanar da ita ba ko?"

Muryar Kawu Ibrahim ta katse shi, sai ya d'ago ya kalle shi, ya san yana nufin Mami Safiyya ne, don satinta d'aya kenan da komawa Abuja bisa matsawar da 'yanuwanta suka yi, don haka bata da labarin cewa an kai Fadeelah kurkuku, shima sai da Kawu Ibrahim ya kira shi ya gaya masa ne sannan ya nemi hutun sati d'aya ya taho, da cewa Mamin Kano zaije.

Ya girgiza kansa.

"Ban sanar da ita ba, tayi zaton ma ina Kano ba nan ba."

Kafin ya amsa Daddy ya cigaba da cewa.

"Dama kawu wata magana ce ta kawo mu..."

Ya sake cigaba bayan Kawu Ibrahim d'in da? sauran sun nuna sauransa.

"... Na san yanzu ba lokacin da ya dace bane, amma su wad'annan kawun nan nawa su suka bada shawarar gwara a sanar daku da wuri tunda yanzu kune da alhakin akan yarinyar nan."

Ga su Kawu Bashir da basu saba da maganar Daddy sosai ba, da kyar suke iya rarrabe kowacce kalma da yake fad'a cikin malkwalalliyar hausar sa da yaren turanci yabi ya nannad'e.

"Ba haka bane Alhaji Ahmad, damu daku duk d'aya ne a yanzu, tunda a baya ma kunyi abinda mu d'in zamu yi."

"Da wannan Alhaji, kuma mun gode da karar, amma shari'a ai ku ta tanadar."

Suka d'anyi murmushi bakid'ayansu sannan Daddy ya cigaba.

"Kawu kun san cewa lokacin da lamarin nan ya faru ana cikin shiryen-shiryen bikin Fadeelah ne ko?"

"Haka ne."

"Toh dani dasu wad'annan 'yanuwan nawa mu muka karb'i auren yarinyar daga wajen Baban yaron wanda yake daga dangin mahaifina, sannan tun bayan dawowata na sanar da kai cewa yaron bai samu damar k'arasowa nan zaria bane saboda ana tsaka da lamarin mahaifinsa ya rasu ya koma can American.."

"Haka ne, haka ne.. Ai kaima sai bayan da ka dawo daga gaisuwar sannan muka had'u."

Daddy ya sake gyara murya sannan yace.

"To gaskiyar abinda ke faruwa shine lokacin da za'a yi auren nan akwai wata 'yar rashin jituwa daga b'angaren mahaifiyar yaron, wadda ni ban san da ita ba sai bayan naje can tukunna sannan ita mahaifiyar tasa ta buk'aci da in zauna wai zuwa ranar aurensa don inyi masa walicci, ni kuma ban gane zancen ba sai na tambayi wane aure kuma bayan wanda muka baro anan Nigeria? A lokacin take gaya min cewa ai ita kwata-kwata bata san da aurensa da Fadeelah ba, ya rufe ta ne shi da mahaifinsa suka shirya komai don ita ta riga ta gama shirye-shiyen aurensa da wata acan."

Kawu Ibrahim da sauran suka shiga gyad'a kai na al'ajabin abin.

"A tak'aice dai Kawu yanzu ita mahaifiyar tasa tak'i yarda kwata-kwata da zancen aurensa da Fadeelah, tak'i yarda ma ta saurare mu, sannan ta hana yaron dawowa tace ma zata sallama shi daga gareta in har baiyi mata biyayya akan abinda take so ba."

"Mhm-mhm!" Muryar Kawu Ibrahim ta fad'a cike da tsantsar mamaki.

"Yanzu Alhaji kana nufin zancen auren ita Bintun babu shi kenan?" Kawu Bashir ya tambaya.

D'aya daga cikin 'yanuwan Daddy yace.

"Abinda muke nufi kenan Alhaji, shi yasa muka ce gwara a sanar daku tun yanzu don ku san me ake ciki."

"Haka ne gaskiya..." Kawu Ibrahim ya amsa.

"... Wannan ba zance ne da za'a barshi a ciki ba, kuma mun fahimci zancenku, wannan kamar ishara ce daga Allah akan yaron ban, uwa ba abin wasa bace da har za'a rufe ta akan babban al'amari irin wannan, watakila ishararsa ce ma tasa wannan al'amarin bai tashi ba sai a lokacin bikin... Allah ya nuna masa cewa albarkar uwa ba k'aramin abu bane.

Kuma ni banga laifin mahaifiyar tasa ba, ya sab'a mata kuma matakin da ta d'auka akansa bai yi tsauri ba, sai dai fatan Allah yasa ya fahimta kuma ya gyara kuskurensa... Bintu ba matarsa bace Allah ya riga ya k'addara, don haka sai dai muyi mata fatan samun wani mijin nagari in har ta wanku daga lamarin nan lafiya."

Magana ance jari ce! Wanda Allah ya bashi kuma ya samu baiwa mad'aukakkiya musamman in hakan ya had'u da kamala, Kawu Ibrahim ya tara dukkan wad'annan abubuwan biyu, shi yasa farat d'aya mutane ke nutsuwa dashi ko a ganin farko. Wad'annan kalaman nasa su suka burge 'yanuwan Daddy game dashi, zuciyarsu ta gaya musu lallai Fadeelah da suke wa kallon kitse a da da kuma yanzu da suka ji cewa danginta ne suka d'aure ta bata cancanci hakan ba... Don Dangin ma suna suka tara!

***

"Kina ganin da gaske ba zaki saurare shi ba?" Aunty Hassana matar Kawu Ibrahim ta tambaya Mairo data idar da sallah a gabanta.

Mairo bata d'ago da fuskarta ba balle ta kalleta, idonta na kan yatsunta tace.

"Aunty dan Allah, wallahi bana k'aunar zancen Sadiq yanzu."

Aunty Hassana ta gyara zamanta tace.

"Ai zancensa wajibi ne yanzu akanki Mairo, na san cewa da ciwo abinda kike ji amma 'ya'yanki nake jiye miki, yanzu ki duba ranar da aka zo da yarinyar nan yadda ta mak'ale a jikinki aka b'are ta da kyar, bar ganin ita yarinya ce kuma 'yarki, wallahi akwai hakki wanda ba lallai ya gogu daga kanki... Musamman na d'an da kika yaye lokacinsa bai kai ba, wallahi? ko yana cin abinci Mairo hakkinsa na nan yana bibiyarki.

Sannan ni ban san zamanku da yaron nan ba, amma duk wanda zai ganki ya san baki wahala a gidansa ba, 'yanuwansa har cikin gidan nan sun zo kuma babu alamun akwai rashin jituwa tsakaninku, laifi ne ya riga yayi miki kuma kowanne d'an adam a duniyar nan baya iya shallake abinda Allah ya tsara masa, mijinki yayi nadama Mairo, ki dubi irin wahalar da yake sha a garin nan, daya tafi da ya dawo, bakya ko bari ya ganki. Suma kuma su Kawun naki ban san me suke jira ba, kowa ya zuba miki ido kina zaune da aure a ka, an kasa gaya miki cewa abinda kike yi kuskure ne..."

"Kuskure..." Mairo ta maimaita kalmar, sautin muryarta a hankali.

"... Na dad'e a cikin kuskure Aunty, rabin rayuwata kaf a cikin kuskuren take, 'ya'yan da kike magana ma duk a cikin kuskuren na same su, Sannan shi Sadiq d'in shine abu mafi kuskure daya tab'a faruwa a rayuwata."

Aunty Hassana ta mik'e daga inda take zaune ta k'araso gabanta kan sallayar ta zauna, sai a sannan Mairon ta d'ago ta kalle ta.

"Da gaske ke kika haifi yaran nan kuwa Mairo? Da gaske ke Uwa ce? Kin san yadda uwa ke jin ciwon rabuwa da 'ya'yanta kuwa? Bari in gaya miki kin san dai ba nice matar Kawunku ta farko ba ko? Amma wallahi 'ya'yan marigayiya duk da suka yi aure sai da naji ciwon rabuwa dasu, ina ga wanda ka haifa kuma? Dan Allah Mairo ki lalubo soyayyar uwa ki tausayawa 'ya'yanki, wallahi babu wanda zai hana ki komawa wajen mijinki tunda har yanzu da aurensa akanki."

Hawaye suka gangaro kan fuskar Maryam, ta share su a hankali.

"Yanzu Aunty saboda 'ya'ya sai in zalunci kaina in koma wajen mutumin daya cuce ni?"

"Rayuwar macen kenan Mairo wannan shine kamashon zama macen, kuma ba'a kanki aka fara ba, mata da yawa sun sha sadaukar da farin cikinsu akan 'ya'yansu kuma sai kiga Allah ya baka Rahma ta wani b'angaren."

"Ki duba fa Aunty, saboda shi Bintu tak'i saurarata har yanzu, tun tana yarinya na san ita ba mai rik'e abu a rai bace, shi yasa hankalina yake dad'a tashi, ina tunanin wane irin bak'in ciki taji daya manne tsanata a ranta tun daga wancan lokacin har yanzu, Ga iyayena ma Aunty, duk sun rasu da bak'in cikina a tare dasu, Gwaggo lami tace sanadiyata ma Inna ta kamu da ciwon daya haddasa mutuwarta..."

Ta girgiza kanta da sauri.

"... A zab'ina, bana jin zan tab'a iya yafewa Sadiq balle har na koma gare shi."

Aunty Hassana ta d'an juyar da kanta gefe, yadda Mairo ta kasa fahimtar ta haka itama ta kasa fahimtar irin tunaninta.

Sai dai Allah ya riga ya tsara cewa a wannan ranar dai Mairo zata fara saukowa daga ak'idarta don basu wani dad'e a haka ba suka tsinkayi sallama daga can k'ofar b'angaren.

"Wa'alaikum Salam, Maraba."

Aunty Hassana ta fad'a sanda ta mik'e zuwa k'ofar falon da suke ciki.

"A'ah, wa nake gani haka kamar Saratu? Da gaske ita d'in ce kuwa... maraba ku shigo."

Sunan na 'Saratu' ya amsa a cikin kan Maryam, ta d'ago da idonta da sauri sanda Aunty Hasanah ta bar bakin k'ofar, wata mata ta shigo, sannan wata, sannan kuma mai suna Saratun da zuciyarta ta ayyana mata.

Aunty Saratu!

Aunty Saratunsu dai matar Mahaifinta.

Sa mik'e da sauri har tana tuntub'e da hijabin jikinta, k'afafunta na rawa ta isa gare ta, zuciyarta kuma na bugawa ta kalli fuskar data zama dattijuwa akan ta Aunty Saratun da ta tafi ta bari ta bari a baya.

Ga d'imbin mamakin Mairo sai ji tayi ta jawo ta jikinta ta rungume, sab'anin yadda Bintu ta juya baya sanda ta ganta.

"Ke nazo gani Maryam, ina sauka garin nan aka shaida min kin dawo, ban ko zauna na runtsa ba na taho don in gasgata zancen nan mai kama da mafarki, Alhamdulilahi.. Alhamdulilahi.. Alhamdulilahi! Amina tayi gaskiya, wallahi daman tace min zaki dawo, tace Mairo ba zata tab'a barin mahaifarta har abada ba.. Tace ke d'in mai tsananin biyayya ce da son?'yanuwa, tace k'addarar da Allah ya tsara miki ce tazo da hakan amma wallahi ta yafe miki duniya da lahira. Ni shaida ce Maryam, daga ita har Babanki sai da suka yafe miki kafin su bar duniya!"

Mairo ta rufe idonta a hankali hawaye mai d'umi ya shiga gangarowa kumatunta har yana d'iga kan hijabin da Aunty Saratun ke sanye dashi, ji tayi kamar anja wani gingimemen dutse can gefe an sauke shi daga kanta. Ganin Aunty Saratu a wannan lokacin ya zame mata kamar wani ruwan sama da ya sauko ya wanke rabin matsalolinta a lokacin.

A wannan ranar kuma daga ita har su Kawu Ibrahim suka ji cewar Adam ne yaje har gidan da take aure a can Kaduna, ya labarta mata duk abinda ake ciki na al'amarin Bintu ya kuma nemi alfarmar da tazo ta bada shaida a zaman da za'ayi na gaba.

Kawu Ibrahim ya jinjina kansa cike da mamakin yadda akayi Adam ya iya nemo gidanta har yaje, da gaske ne abinda ya fad'a kenan, Binciken ya tafi, amma to bayan ya bar Kadunan ina ya sake tafiya har tsawon wannan lokacin bai komo ba?

****

BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

36

(&_&)

"Mami ki saurare ni dan Allah..."

Muryar Al'ameen ta fito ta cikin wayar dake kare a kunnen Mami Safiyya, ta girgiza kanta sannan ta amsa masa cikin yaren turancin da suke magana.

"Wallahi Al'ameen ba zai yiwu ba, Daddy ya d'auki zafi sosai akan maganar nan, yace abinda muka yi babban kuskure ne, sannan ni kaina na san nayi ba daidai ba...na biye maka akan abinda ko a musulunce bai dace ba, don haka kayi hak'uri kawai, Allah yayi iyakar mu'amalarka da Deelah kenan, shi yasa ma komai ya faru kafin akai ga d'aurin Auren.

Kayi wa mahaifiyarka biyayya shi yafi, don kamar yadda yanzu kake da ita kad'ai a duniya haka itama kai kad'ai take dashi, su Aysha mata ne, duk daren dad'ewa zasu yi aure su barta, amma kai zaka zama mai kula da ita har k'arshen rayuwarta, don haka babu wanda zai so ka bijere mata ko ka rab'u da wani abu da baza ta so ba. Uwa tafi k'arfin komai, bayan biyayyar ka ga Allah tata biyayyar ce zata sa ka rabauta a duniya da kuma lahirar saboda haka dan Allah Al'ameen ka hak'ura da Fadeelah, wallahi don ka rasa ta babu abinda zai faru da kai ko ya ragu a rayuwarka.

Rahmar Allah yawa ne da ita, ba sai da Fadeelah kad'ai zaka samu farin ciki ba, na tabbata itama wannan zab'in ta Maminka alkhairi ce a wajenka, wuyar ta a zauna Al'ameen amma na san zaka fahimceta har ta zame maka matar rufin asiri, kai d'in mai kyakkyawar mu'amala ne ba wanda zai zauna da kai ya kasa fahimtarka... Dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka saki ranka ayi auren nan, Fadeelah kuma ka cigaba da taya ta da addu'a an kusa kammala shari'ar kuma muna sa rai zata fito insha Allah."

Bi da bi, kowacce kalma ke shiga kunnen Al'ameen yana jin kamar maimaici ne akan irin maganganun da kowa ke gaya masa.

... Don ka rasa ta babu abinda zai same ka.

Basu san cewa komai ya riga ya same shin ba, komai ya riga ya cakud'e masa, ya riga ya zama kamar d'an adam d'in da aka sassak'a da k'arfe, wanda abin juya shi ke hannun mutane da yawa, ya rasa duk wani emotion balle har yayi iko da kansa.

Kamar komai na rayuwarsa, wannan karon ma mahaifiyarsa tayi jagoranci da hukuncinta, tun yana yaro bata tab'a barinsa yayi abu bisa ra'ayinsa ba, hatta kaya ko abinci bai isa ya zab'a ba sai wanda ta bashi, bayan ya girma kuma bai tab'a son zama lauya ba, burinsa ya karanci harkar Computer, ya iya sarrafata ya fitar da abubuwan zamani daga cikinta amma? tace tafi son ya karanci aikin lauya, abinda taso yi kenan a karatunta amma bata sami dama don haka shi yayi... Zai iya rantsuwa bai tab'a sanin ranar da ta barshi ya zab'i wani abu da yake ra'ayinsa ba sai in har abu ya zama dole ne sai shi d'in zaiyi.

Sai a yanzu rana d'aya kawai daya riga ya kai wani minzali da ko a shari'ah zai iya zab'awa kansa abu, don ya bud'i baki ya fad'i ra'ayinsa sai ta sake cewa A'ah, kuma kowa ya amince cewa ya?cigaba da binta a haka? Ya lumshe idanunsa a hankali, fad'ar Allah ne cewa babu wata halitta a doron k'asa da zata zama cikakka... Tunda ya taso a rayuwarsa bai ga abinda Allah ya rage shi dashi ba sai wannan.

"Al'ameen kana jina?... Yaushe ne bikin?"

Muryar Mami ta shiga kunnensa, sai ya k'arasa rufe idanunsa gabad'aya kafin ya amsa.

"Tace farkon wani watan mai kamawa."

"Toh Allah ya kaimu, su Zahra zasu zo insha Allah, in da hali ma zan had'a su da wasu cousins d'insu."

Ba wai fatan lokacin yazo yake ba amma jin ta d'ebe kanta yasa yayi saurin tambayar.

"Mami ke fa?"

Ta girgiza kai kamar yana ganinta.

"Da wuya Al'ameen, Miryaamah ta d'auki zafi a lamarin nan, ni kaina ba zan iya kai fuskata gabanta a yanzu ba, mu bari dai zuwa wani lokaci sai inzo in ziyarce ku insha Allah."

'KU' tana nufin shi da Hamida, Hamida a matsayin matarsa... Abinda ya kasa haskowa a cikin kansa har yanzu, ya kasa rusa wannnan mafarkin daya gina a cikin kansa na irin rayuwar da zaiyi shi da Fadeelah.

A yanzu baya iya hango yaya rayuwarsa zata kasance a gaba, don ya san ba zai iya hak'urin rasa Fadeelah ba... Ya rasa ta a farko kuma ya kasa hak'urin!

****

MIMBIR????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
I, 10:15 AM.

K'auyen Mimbiri, wani waje ne dake tsakanin babban birnin tarayya na Abuja da kuma garin Niger, k'auye ne k'arami da ko gwamnati bata san dashi ba saboda babu ko wutar lantarki balle ayi maganar ruwa, hanyar samun ruwansu ta jikin wani k'aton dutse ne dake bayan garin inda yake fitar da tsaftataccen ruwa mai sanyi wanda hakan ya sanyawa mutanen cikinsa d'orarriyar lafiya da kuma kuzari, gine-ginen cikin k'auyen na asalin k'asa ne da azara, k'asar ma ba irin wadda ake sarrafata zuwa bulo ba, don yanayin gidajen nasu babu fasali balle tsari.

Yarensu kuwa Hausa ce amma mai cakud'e da garhariyar yaruka kasancewarsu a tsakiyar garuruwa. Kamar yadda k'auyen yake k'arami, haka mutanen cikinsa basu da yawa, banda gangarawar shekaru ma da suka zo da aurarraki da kuma hayayyafa, a da baifi a k'irge su zuwa 'yan dozinnai ba.

Hanyar zuwa cikinsa bata da kyau, don da kyar aka fitar da ita 'yar siririya ta tsakanin gonaki. A shekarun baya ma babu hanyar, sai da aka yayyanka gonaki daga can hanyar babban titi sannan aka fitar da ita, 'yar k'arama mai cike da gargada wadda duk kyawun abun hawa sai yayi tangad'i akanta.

Babban abin taraddadi a k'auyen Mimbiri shine zuwan Bak'o, abu ne sabo da ba kasafai yake faruwa ba, saboda in har ka hangi wani akan hanyar shigowa k'auyen, to d'aya daga cikin 'yan d'aid'aikun 'yan uwansu ne da suke fita birni yin sayayyar kayan masarufi, ko kuma a wasu lokuta 'yan wani k'auye dake can nesa dasu su shigo cin kasuwarsu, amma shima ba koyaushe ba, duk ranar kasuwa kusan su kad'ai ke cin kasuwarsu saboda k'arancin mutanen kewayen da suka ma san da zamansu.

Sa'id ya juyar da kansa gefe yana mai k'ara sautin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login