Showing 9001 words to 12000 words out of 153964 words

Chapter 4 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3813

cikin cafteria a mik'e office d'in Malamin Maths d'insu ta nufa, Mr. Hawkins.

"Ina ganin ya kamata ki samu wanda zai dinga koya miki wani karatun daban a gida, makin ki ya b'aci da yawa, in zaki cigaba a haka bana tunanin zaki iya kaiwa gejin da ake nema wajen cigaba zuwa wani ajin."

Zuciyarta ta buga a cikin ramin k'irjinta, ta yaya zata maimata ajin da take tsawon shekara guda, ta yaya ma zata kalli Daddy tace masa rashin k'ok'arinta ya kai har ta maimaita aji?

"Zanyi iya k'okarina sir, zan dage in dinga ganewa, watakila in ka bani wani aikin naje nayi zan samu k'arin makin."

"Yaudarar kai kenan, ina fada miki ne ya kamata ki nemi malamin da zai dinga miki wani karatun a gida, sai ki iya samun maki mai kyau nan gaba amma a haka, ba zaki iya kaiwa inda ake so ba."

Ta d'anyi shiru tana murza 'yan yatsunta, ita ta san Daddy ba zai iya d'auko mata wani malami ba a yanzu. Kuma ta san in har ta amsawa Mr. Hawkins to ta yaudari kanta ne ta guntulewa kanta samun wata hanyar da zai iya kawowa ta taimake ta, saboda haka tace.

"Kayi hakuri sir, Babana ba zai iya d'auko min wani malami a yanzu ba."

"Saboda me?"

Yayi tambayar da zuciyarta ta san zata biyo baya, sai dai har ta bud'e baki zata yi magana k'ofar office d'in ta bud'e bayan bugu d'aya kawai da akayi.

"Ance kana kirana... sir?"

A cikin sakan d'aya kawai tunaninta ya tsaya cak!

Don a cikin sakan d'ayan kawai wannan muryar ta shiga kunnenta, muryar wanda ta tsani had'uwa dashi, wanda?zuciyarta ke gudunsa kamar irin gudun da bawa ke yiwa Shaid'an. Me ya kawo shi nan kuma bayan ta yiwa kanta katanga dashi daga cafteria? Sai kawai ta d'auki jakarta tace da mr. Hawkins ta gode sannan tayi hanyar k'ofa.

Ta rik'e numfashinta sanda tazo gifta shi, ko kad'an bata k'aunar ta shak'i kamshin turarensa wanda ta haddace shi a gefen lokarta.

Sai dai abinda bata sani ba shine alkalami ya riga ya bushe akan k'addararsu, Office d'in Mr. Hawkins shi ya zama jigon mafarin k'addarar dake jiransu a gaba!

****

"Bayan duka kuma abin ya kai har ga zagi? Daddy ya kamata muje makarantar nan, ba zan zauna kowa ya dinga takura musu don kawai wani dan isk** shugaban k'asar su ya basu damar...

Mami Saffiyya ta fad'a cikin fad'a tana ajiye bowl din miyar dankali akan dining table inda suka taru gabad'ayansu suke cin abincin dare.

"Kar ki k'arasa, yaran nan suna jinki." Daddy ya fad'a yana tauna abincinsa.

Zahra wadda ke zaune a gefensa, ita ta gama k'orafi akan wani d'an ajinsu dake zaginta, amma kamar ba akanta ake maganar ba, hankalinta ya tafi wajen raba abincinta da nikak'ken naman da aka had'a.

"Da gaske nake, bana tunanin shirunmu zai sa rashin mutuncin nasu ya ragu. " Ta sake fad'a sanda taja kujerarta ta kusa da Fadeelah ta zauna.

"Kana jin me nake fad'a kuwa?"

"Kowacce kalma, amma ba inda za kije, dole ne mu k'ara hakuri don makarantar yara ce k'anana, ba zai yiwu muje fad'a dasu ba, in har abun ya k'ara yawa ne sai ayi reporting."

Ba haka taso ba amma ba yadda zata yi, sai ta miko masa plate d'in salad tana fadin.

"Amma dai ko kiran malaminsu ne ya kamata ayi, don su san ba tsoronsu muke ji ba."

"Karki damu, abincin nan yayi dadi da yawa... Kin iya girki.!"

Sai murmushin dad'i ya maye gurbin fushinta.

Fadeelah na zaune a gefenta tana tauna abincinta a hankali, tunani take a cikin kanta in har yara k'anana zasu fara nuna kiyaiyarsu ga yara irinsu musulmai, me yasa take ganin hakan ba zai faru a makarantarsu ba? zuciyarta ta cika da d'aci sanda fuskar Adam ta shigo cikin tunaninta, wani mutum guda d'aya da ta tsana fiye da kowa, bata sani ba ko a rayuwarta ta baya akwai wanda ta tsana irin hakan, amma BAYAN TA MUTU, shine halitta na farko da taji bata sonsa, kuma bata sonsa har cikin zuciyarta.

"Do you know what the boy even said...?" Muryar Iman ta fad'a cikin kunnenta.

"Iman, Hausa!" Mami Saffiya ta katse ta.

"Cewa mata fa yayi 'Black' ba wani abu ba."

Abin ya bawa Fadeelah dariya, don daga yadda Zahra ta gama fadar yaron na zaginta wani zaice babbar magana ce.

"Kwalliyar me kika yi da daddaren nan?" Mami wadda sai yanzu ta lura da fuskar Zahra ta fad'a.

"Ba na hana ki saka wad'annan abubuwan a fuskarki ba..?"

Fadeelah ta kalli fuskar Zahran, bata san wane fad'a Mami zata yi ba da taga yadda ta yiwa gashinta d'azu Allah yaso taji shawararta ta canja shi.

"Mami dan Allah kwalliya fa ba haramun bace, so nake kawai inyi kyau."

"Kina da kyanki ba sai kinyi kwalliya ba Mamana, kawai kin matsu kiyi saurin girma ne."

Daddy ya fad'a daidai sanda Faruq ya sauko daga stairs.

"Yaya!" Iman ta kira sunansa da murnarta tana kallonsa, ya k'araso ya gaida iyayensa a hankali sannan ya zauna kusa da Iman.

"How's my sweetheart" Ya fad'a yana hargitsa gashinta. Mami ta miko masa plate d'in shinkafa ya gyad'a kansa alamun godiya. Daddy ya kalli Fadeelah.

"Dr. Gilbert ya kirani yace kinje wajensa kwana biyu da suka wuce, wai zancen kina fama da mafarkai da yawa."

"Eh Daddy." Fadeelah ta amsa a hankali.

"Amma ba wani abu bane yayi sauki yanzu." Ta k'ara akai amma duk da haka tana iya jin idanunsa na kallonta.

"Da gaske nake Daddy I'm fine."

"Amma baki tab'a zuwa wajensa ke kad'ai ba, kin tabbata ba wani abu?" Mami ta tambaya cikin tausayawa.

"Sannan bata fad'awa kowa zata je ba." Zahra tace tana juya idanunta.

Mami ta gallara mata harara wadda kowa ya san wata hanyar tace ta cewa? 'Dake ake magana?'

"Wallahi ba komai naji sauki." Fadeelah ta fad'a a hankali tana cusa wata lomar cikin bakinta.

Sai dai ita kanta ta san k'arya takewa kanta. Ciwonta yayi sauki a baya amma daga lokacin da ta fara irin wannan mafarkan, kwakwalwarta da duk wani abu mai hankali a jikinta na gaya mata cewa wani Babban al'amari na shirin faruwa da ita!

***

BAYAN KWANAKI BIYU.

Fastocin nan suka shiga yawo a makarantarsu Fadeelah, kuma hakan ya karb'u a wajen d'aliban makarantar sosai don k'ungiyar su Adam ta cigaba da printing wasu ana mannawa a koina na cikin makarantar, koina kuma ya had'a harda cikin toilets na mata da maza, ya zamana babu inda wani musulmi zai juya a makarantar bai ga kalmar b'atanci ga musulunci ba, ko kuma a dinga kiransu da sigar tsokana ana dariya.

Wasu sun damu wasu kuma basu d'auki abin da zafi ba, a cewarsu ai babu hannun hukumar makaranta don haka abin ba zai d'ore ba.

Saboda a lokacin ma malamai sun fara tsawatarwa wad'anda ke hassasa abun. Fadeelah tafi kowa takura ba don komai ba sai don ciwon kwakwalwarta, kwakwalwarta da bata iya jure duk wani abu da zai takurata komai k'ank'antarsa kuwa. Dalilin da yasa har a lokacin ta cigaba da fad'uwa ayyukan lissafi kenan, wanda a yanzu ta riga ta gayawa Mr. Hawkins cewa baza ta iya samun extra malami ba saboda Daddy yana iya kokarinsa wajen managing rayuwarsu ne, don har a lokacin Mami Saffiya bata samu aiki ba.

Tsanar da take wa Adam ta k'ara yawa a ranta, saboda ta yarda cewa tunda ta fad'o cikin sabuwar rayuwarta, wannan shine hargitsi mafi muni daya tab'a faruwa da ita, Ashe ko kusa ba hakan bane, mafi hargitsin rayuwarta ya fara ne a wata ranar laraba da daddare.

A ranar sun dawo daga wajen wanki tana jera kayansu cikin wardrobe ita da Iman dake taya ta ninkewa, Su Mami gabad'aya suna falo.

"Jiya na karanta wani labari a tablet d'in Zahra." Iman ta fad'a daga kan gado inda take ninkin, ita kuma tana zarya tsakanin gadon tana d'iban kayan.

"Labarin 'yan Nigeria ne, akan wata yarinya da bata jin magana sosai, tayi ta rigima da mutane da kuma 'yan gidansu, sunanta wai 'BINTU'"

A lokaci d'aya Fadeelah ta tsaya tsakiyar d'akin, bata ce komai ba kuma bata taya Iman dariyar da take yi ba, tarin mafarkan da take yi masu d'auke da sunan Bintu suka haska a cikin kanta lokaci guda, Tunaninta ya hargitse a take ta shiga jin alamun muryoyin dake binta a mafarkin suna kiranta da sunan Bintu.

A take kuma wani b'arin na kwakwalwarta ya shiga bugawa da sauri, sannan fuskoki suka shiga haskawa cikin kanta kuma suna d'aukewa a lokaci d'aya.

"Na san suna Bintu." Ta fad'a a hankali.

"A ina?" Iman ta tambaya.

"A cikin mafarkina."

Ta amsa tana juyowa a hankali rik'e da kayan data d'iba.

"Ni ban tab'a sanin wata Bintu ba, kuma na san dai duk wanda kika sani mun san shi."

Bata amsa ba saboda wani irin azababben ciwo da kanta ya shiga sara mata.

"Me ya faru?" Iman ta tambaya. "Me ya same ki?"

Bata amsa ba, don baza ta iya amsawar ba, ciwon kwakwalwarta ne ya tashi kamar yadda yake yi a d'aid'aikun lokuta, hankalinta ya gushe ya zamana babu maraba tsakaninta da mahaukaci.

Zuciyarta na bugawa ta fara bugawa da k'arfi kamar zata faso ta fito daga kirjin nata sannan kanta ya cigaba da sarawa kamar ana buga mata guduma, yayi nauyi, ya kuma yi zafi, taji babu abinda take bukata kamar wani yasa wuka ya sare mata shi.

Hankalinta yayi nisa da tunaninta, kamar yadda yake faruwa a irin hakan, saboda haka b'arin zuciyarta mara hankalin ya bata shawarar tayi gudu kawai ko zata sami sauki, ba tare da wani tunanin ba kuwa ta matsa wajen windon d'akin, ta? bud'e shi sannan ta dira waje, tabi ta bayan gidan ta tsallake 'yar k'aramar katangar data zagaye gidan sannan ta shiga gudu kan titin unguwar, gudu take da dukkan zuciyarta amma babu abinda yayi sauki game da ciwon kan.

Taji tana son tayi ihu, tayi gudu har sai numfashinta ya k'are, ta dinga bin iskar tana wuce mutanen dake wucewa ta kan titin, motoci, gine-gine, ta fita daga unguwarsu ta fad'a wata, ta iso cikin wani park ta mik'e cikinsa, duhun bishiyun ya dinga gizo a idanunta.

Bata san ina zata ba, fatanta kawai yawan gudun ya tsayar da azabar dake faruwa a kanta.

****

Adam yana zuwa cikin park d'inne a duk lokacin da kwakwalwarsa ta hargitse, ciwonsa ya tashi. Yana zuwa ne don samun nutsuwar da zai saita tunaninsa ya koma, walau da rana ko da daddare duk sanda ciwon nasa ya tashi.

Sai dai wannan karon shigowarsa kenan, idanunsa suka hango masa abinda ya sashi tsantsar mamaki, bai san kammaninta sosai ba amma ya tabbata itace, ita d'in da ya gani a office d'in Mr. Hawkins kwanakin baya.

Sai dai shigarta ta yanzu da wancan lokacin ta banbanta, a baya jikinta a rufe yake sannan fuskarta lullub'e take da mayafin dake nuna shaidar addininta, a yanzu k'aramar riga ce a jikinta sannan gashinta a kwance yana tashi cikin iskar!

Bai santa ba, amma tabbas ya san a lokacin wani abu ba daidai yake tare da ita ba, kuma tana buk'atar taimako, daga yadda take lulawa ma cikin duhun wajen daya tabbata bata san ina ne ba. Sai kawai ya ajiye jakar hannunsa yabi bayanta!

?%O??%

_Wane irin ciwon kwakwalwa Fadeelah take dashi?_

_Wane irin ciwo ne da Adam?_

_Wace irin k'addara ce ke shirin had'asu?_


BAYAN NA MUTU!

(&_&)

03

K'arar jiniyar motar Amblunce ita ta wuce gudun da yake yi zuwa cikin duhun bishiyun da yarinyar ta shiga, kuma kafin ya k'arasa motar ta tsaya sannan ya hangi tarin mutane sun fito daga cikinta, kowannensu yayi cikin bishiyun ba tare da sun damu su rufe k'ofofin motar ba.

Sai yaja birki ya tsaya daga inda yake, tunda taimakon da yafi nasa ya riga shi isa gareta. Cikin abinda baifi minti d'aya ba sai gasu sun dawo d'auke da ita a kwance jikin kafad'ar d'aya daga cikin mazan biyu, yayin da d'aya ke rik'e da waya yana magana, daga inda yake tsaye yana iya hango tashin hankali k'arara akan fuskarsa.

Sauran mutanen suka shiga k'okarin fito da gadon dake bayan motar Amblunce d'in don a d'ora ta akai. Sai a lokacin ya lura da kayan jikinta sosai, tana kwance a kafad'ar mutumin sanye da 'yar k'aramar riga mai hannun vest, gashinta ya kwanta kan kafad'unta. Haka kurum sai yaji ba dad'i, yadda ya ganta a makaranta ta rufe jikinta ya san a hankalinta baza ta so wani ya ganta a hakan ba.

Yana kallo suka rufe motar sannan suka yi hanyar fita cikin sauri har a lokacin mutumin nan dake zaune a gaban motar nata waya cikin rud'ewa, idonsa yabi fitilin motar har suka b'acewa ganinsa.

A zuciyarsa, yayi fatan ta samu sauki.

***

Muryoyin suna fita a hankali ne a kusa da ita sosai, kamar kuma sun dad'e suna maganar amma sai a lokacin hankalinta ya fahimci me suke cewa.

"Ban san ya akayi na kasa ???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?fahimtar taje retrival stage ba, yanayin mu'amalarta da komai yana nuna har yanzu tana kokarin fahimtar kewayenta ne..."

Muryar farko ta fad'a, mai zurfi da kuma nauyi. Namiji ne ta tabbata.

" ...abin da mamaki ace har tayi kwarin da zata fara re-accessing past d'inta." a lokacin taji kamar zata iya tuna sunan mai muryar amma d'ayar data shigo ta katse ta.

"It's a good sign, hakan ya nuna kwakwalwarta na da k'arfin da zata iya warkewa ne a d'an kankanin lokaci."

Mace ce wannan mai siririn sauti kamar an fik'e shi.

"Ba kowa ne kuma ke experiencing creative reimagination a farkon mataki irin haka ba, dole ne ta fita daga haiyacinta."?
Namijin ya sake fad'a.

"Zata samu sauki na tabbata, tana da karfin hali.. tayi kokarin kwantar da ciwonta a baya, har ta iya shiga cikin mutane, so wannan ma zata k'ok'arta na sani."

Akwai wani k'arshe a cikin muryarta sanda ta fad'i hakan, (Fata! Hope.) Zuciyarta ta bashi suna cikin harshen turancin da suke magana.

K'arar motsin injinan dake zagaye da ita suka shiga kunnenta kafin Namijin ya sake magana.

"Zuwa yaushe zata iya farkawa?" Muryarsa ta tambaya cikin damuwa.

"Duk lokacin da jikinta ya shirya, ta shiga cikin halin da ita kad'ai zata iya fassara shi, jikinta yana buk'atar ya karb'i komai tukunna kafin ta iya fahimtar wasu abubuwan."

Shiru ya biyo baya daga nan, don haka a cikin wannan shirun Fadeelah ta bud'e zuciyarta zuwa hasashen inda take. Asibiti ne ta tabbata kuma muryar farko ta Namijin nan tayi mata kama da Dr. Gilbert, amma mamakinta shine me yasa ta tsinci damuwa irin wadda ta daina gani a wajensa? tayi zaton matsalarta tafi k'arfinsa da har ya daina d'orawa kansa damuwa akanta.

Ta biyun kuma tabbata Dr. Florence ce, wata babbar likita da ba kowa ke iya ganinta a asibitin ba sai in har cutar mutum tayi k'arfi da yawa, kenan abinda ya faru da ita har yayi k'arfin da Dr. Florence ce zata iya dubata? Bata fahimci komai a cikin zancensu ba amma ta san dole ne bayan farkawarta tayi magana akan abinda ya same ta don haka dole ne ta shirya,?ta san amsar da zata bawa dukkan tambayoyin dake jiranta, tayi ajiyar zuciya a hankali, k'arar monitor d'in dake gefe ya shaida cewa yayi registering hakan.

Tsoro ya shige ta kad'an don ta san in har zata nemo abinda Dr. Florence zata tambaya dole ne ta dawo da abinda ya faru cikin kanta, abinda ya sanya ta fita daga haiyacinta, tunaninta ya dulmiya cikin kanta, a? yanzu bata iya hasaso komai sosai, abinda ya faru na shirin b'acewa daga cikin kanta, kamar yadda mutum ke hasashen mafarki bayan ya farka.?

Ta sake yin ajiyar zuciya a hankali... monitor dake gefe ya sake shaida cewa ya d'auki hakan. Tunaninta ya nutsa cikin kanta, ta shiga lalube cikin? duk wani tunani daya tab'a zama a kanta, wad'anda ta sansu tun lokacin da sabuwar rayuwarta ta fara, komai daidai yake, komai yana nan kamar yadda ta san shi.

Sai dai daga can karshe ta lalubo wani sabon tunanin da bata san dashi ba, a cikinsa ta hangi wata yarinya tana tafiya cikin duhu, bata iya ganin fuskarta amma tana iya kwatanto gajiyar da take ji a lokacin don tayi tafiya mai nisa ta cikin duhun titunan dake bayanta, jikinta na rawa ta cikin cukurkudadden hijabinta.

Ta kasa gane wacece yarinyar da kuma inda ta ganta, a ina ta ganta da har zata shiga cikin tunaninta?kwakwalwarta ta shiga lalube amma tunaninta ya kasa nemo amsar hakan, ta sake tafiya wani b'angaren a cikin kanta amma sai ta daki bango.

Anan tunanin ya k'are kuma babu komai sai abinda ta wuce a baya, kamar ansa wani abu ne an goge sauransa don ta san ba nan ne k'arshe ba, kamar kwakwalwarta ta lalace ne daga nan.

Taji ranta na shirin b'aci, zuciyarta ta shi bugawa da k'arfi sannan hannayenta suka damk'e cikin tafinsu.

Monitor dake gefe ya nuna rahoton haka k'arara akan screen dinsa, a lokacin taji alamun taku na tahowa wajenta sannan muryar Dr. Florence ta kira sunata a hankali.

Fadeelah.

****

"Kina buk'atar a kashe fitulun?" Dr. Florence ta tambaya tana kallon yadda ta kasa bude idanunta sosai tun bayan lokacin da ta farka.

"A'ah a barsu, ina son hasken." Muryarta ta fito kai tsaye babu alamun wani ciwo ko rikicewa.

"Na san kinyi mamakin ganina a maimakon likitan da kika saba gani Dr. Gilbert, ba wai hakan na nufin ciwonki yafi karfinsa bane, kawai ya d'an d'auki hutu ne ni kuma zan maye gurbinsa."

K'arya take, ciwona yafi k'arfinsa ne.

Fadeelah ta ayyana a ranta, wane hutu Dr. Gilbert ya d'auka bayan yanzu ta gama jin muryarsa cike da damuwa anan? ta fadi hakan ne don kawai ta d'auke hankalinta kar ta damu akan abinda suke tunanin babban al'amari ne. Bata san cewa rikicewar data tayi na farko ya wuce ba, kuma tunda ta bud'e idonta ta ayyana cewa hakan ba zai sake faruwa ba da ita ba.

Don irin wannan ciwon kan yafi duk wanda ta taba fuskanta a baya shi yasa ta kasa tsaida rikicewarta, amma kamar yadda suka fad'a ne, a baya ta karb'i ciwonta da hannu biyu ta tallafi kanta, a yanzu kuma data fahimci ciwon nata na sake k'aruwa ne zata gayawa b'arin kwakwalwarta mai lafiya haka, ba zata sake yarda ciwon yayi galaba a kanta ba, ta daure a baya kuma zata daure ma yanzu, zata daure ta fuskanci dukkan matsalolinta a yadda rayuwa ta kawo mata, ita ba mai rauni bace!

"Na fahimta." Ta amsawa likitar tunda ta nuna alamun tana jiran amsarta ne. Sai ta gyada kanta sannan tace.

"Na san zaiyi miki wuya ki tuna abinda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login