Showing 39001 words to 42000 words out of 153964 words

Chapter 14 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3773

don al'adarmu Hausa-Fulani abu ne mai mutuk'ar kyau da burgewa.

Farouq wanda yafi kowa nuna damuwarsa lokacin tahowarsu, a yanzu yafi kowa sakewa cikin cousins d'insa da ya saba dasu wanda kullum suna kan hanyar yawon harkoki kala-kala tunda anan ya samu 'yanci har driving yake. Zahra ma ta samu su Sameera da Sahla 'yan uwan iyayinta sun had'u sun cigaba daga inda kowannensu ya tsaya.

Daddy ne kad'ai baya jin dadin zaman Nigeria sosai, don kullum cikin complain yake na yadda aiki yayi masa yawa ga kuma rashin wadatar kayan aikin sosai kamar yadda ya saba, sai dai Mami tace ya riga ya sawa ransa hakan ne tunda can ne tushensa don haka shima yanzu ya d'and'ana irin hak'urin da tayi daya d'auketa daga nata tushen.

Amma baya d'and'anawar don duk sanda ya samu saukin aiki ko yaya yake, zai tafi ne can wajen 'yan uwa da abokansa, don a yanzu haka ma baya nan satinsa guda kenan a can Washington.

Gidansu mai kyau anan cikin Abuja, sannan makarantar da su Zahra suke zuwa mai kyau ce ta kud'i, tunda a yanzu abubuwa sunyi musu sauk'i ba kamar America ba, ita da Farouq kuma sun fara zuwa University of Abuja inda mafi yawancin jikokin gidansu Mami ke yi.

Iyayen Mami gabad'aya sun rasu sai kishiyar mamansu guda d'aya, dattijuwa da suke kira da Hajiya Amarya, wadda ita 'ya'yanta uku ne a gidan, amma mahaifiyarsu Mami ita 'ya'yanta biyar.

Babban cikinsu, Baba Habibu 'ya'yansa biyar shima da matarsa Haj. Halima, dukkaninsu maza ne, Sadiq, Ibrahim, Aminu, Salim, da kuma Saifuddeen, Ukun farko sunyi aure sai biyu ne suka rage kuma dukkaninsu sun gama karatu suna aiki.

Daga shi sai Baba Sani, yana da mata Haj. Saddik'a amma Allah bai tab'a basu haihuwa ba har zuwa yanzu da suka manyanta.

Mama Balaraba itace ta uku, mijinta Soja ne kuma tana da 'ya'ya shida. Yusuf, Maryam, Asiya, Fatima, Sameera da kuma Mukhtar, Yusuf da Maryam duk sunyi aure, sai Asiya da Fatima dake jami'a, sannan Sameerah sa'ar Zahra da kuma Mukhtar duk 'yan secondary.

Daga ita sai Aunty Hadiza, wadda Rahma ce Babbar 'yarta, itama tare da mai bi mata Abdul suna jami'a, sannan Adnan da Sahla 'yan secondary. Babansu ma'aikacin Banki ne anan cikin Abuja.

Sai Mami Safiyya autarsu wadda karatu ya kaita America gidan ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????'yaruwar mahaifinsu ta had'u da Daddy a can ya aureta.

'Ya'yan Hajiya Amarya uku ne, Mami Hauwa, sa'ar Baba sani ce, amma ita a kaduna take zaune 'ya'yanta uku ita, Sulaiman, Abdulmalik da macenta d'aya Salma sa'ar su Asiya, sai dai basu fiye zuwa ba don gabad'aya yaran ma suna k'asashen waje karatu, mijinta professor ne kuma rik'akken d'an boko.

Daga ita sai Kawu Isma'il, wanda shima 'ya'yansa duk maza ne su uku, Abdullahi, Aliyu da Anas. Abdullahi ya fara aiki amma Aliyu da Anas duk suna jami'a.

Sai autarsu, Aunty Iyami asalin sunanta Aisha, Shekaru biyu kenan da aurenta wanda shine zuwan su Mami Nigeria na k'arshe. Ta haifi 'yan biyu wanda shekararsu d'aya yanzu, Hanifa da Hanif.

Wani abun burgewa a zuri'arsu Mami shine suna da mutuk'ar had'in kai 'yan gidan, mutum d'aya ce ta fita zakka wato Mami Hauwa, don kafin tazo ganin Mahaifiyarta ma aiki ne balle ta tuna da 'yan uwanta, gashi mijinta yana da kud'i sosai amma bata da taimako, ko 'ya'yanta ma haka suke, Shi yasa a abubuwa da yawa kowa ma mantawa yake dasu.

Maza sun fi yawa a jikokin gidan, hud'u ne suka yi aure, uku 'ya'yan Baba Habibu sai d'aya d'an Mama Balaraba sannan mace d'aya Maryam da ita kad'aice tayi aure a cikin matan.

***

Lokacin da Fadeelah ta sauka k'asa da niyyar zuwa kitchen, Su Mami na zaune su shida a falo suna hira, da Haj. Saddika matar Baba Sani, kasancewar ita a gidan b'angarensu yake sai Mama Balaraba, Aunty Hadiza da kuma Aunty iyami, sai 'yar tsohuwa Hajiya Amarya.

Ranar Asabar ce, kuma kamar kowanne k'arshen mako a sabon tsarin da aka fara su Mami na zuwa gidan mahaifiyar tasu ne gabad'aya da 'ya'yansu don sada zumunci, sai dai kusan matan ne kawai suke zama, don mazan ko sun zo, 'yan mintuna kad'an ne kawai zasu tafi harkokinsu, Baba habibu ne kad'ai wani lokacin zai kai har magariba yana zaune ana hira, sai dai yau baya nan yayi tafiya Lagos.

Kafin Fadeelah ta shiga kitchen tana jiyo dariyar da suke tayi wa Mami Safiyya kan wani abu data fad'a, har Aunty iyami na cewa anya baza su tattara su koma k'asarsu ba kuwa don wai ko su Faruq ma har yanzu basa iya fad'ar wani abin a hausa.

A cikinsu gabad'aya, daga Mama Balaraba sai matar Baba Habibu sune kad'ai basa sakar mata fuska sosai, amma su Aunty Hadiza babu ruwansu sun karb'eta kamar yadda Mami ta karbeta cikin rayuwarsu da farko, musamman Hajiya Amarya, yadda take mata baya banbantuwa dana jikokinta ko kad'an, kuma kullum ta ganta sai ta tuna da mai sunan da aka saka mata... k'anwar hajiyan Daddy, wadda taji a bakinta cewar hatsari tayi ana dab da bikinta ta rasu.

A kitchen d'in, ta tarar da Saifudden d'an gidan Baba Habibu yana sirka lemo da ruwa, bata tab'a ganin mutum mara son sanyi irinsa ba amma duk da haka kullum cikin mura yake, watakila yanzu babu lemon ne sai a fridge shi kuma yaga ba zai iya hak'ura ba, ta gaishe shi a hankali sannan ya matsa mata ta d'auki ruwan, har taje bakin k'ofa ya tsaida ita cikin dusashiyar muryarsa ta alamun mai mura.

"Rahma tana nan?"

Ta d'aga kanta.

"Eh, tana nan."

Yayi shiru kamar zai bata sak'o sai kuma yace.

"Shikenan kawai."

***

Sanda ta fito daga kitchen d'in, ta tsinci muryar Abdullahi, d'an gidan kawu Isma'il yana magana zaune a gabansu Hajiya, su Zahra, Sameera da Sahla na gefensa kowaccensu fuskarsu tasha kwalliya d'al da ita ga kayayyaki da takardu kamar na? certificate a hannunsu.

"Wallahi fa Mama, kawai Nasir ne yace inzo muje zai d'auko mamanshi daga wajen bikin yaye wasu masu koyon kwalliya da akayi wanda har da k'anwarsa a ciki, shine fa muna zuwa naga yaran nan a wajen wai suma har dasu aka yaye, sai d'aukan hotuna ake yi dasu, wai ita Zahra ma har wata kyauta aka bata don tafi su sanin wasu tips d'in kwalliyar. Ashe har watansu biyu suna zuwa babu wanda ya sani."

Cikin tsananin fushi Mami Safiyya ta kalle su tace.

"Waye ya baku kud'in da kuka je kuka biya su?"

Zahra tafi su sanin halin Mami, don haka kai tsaye tace.

"Abbansu Sahla muka tambaya."

"Ai dama wallahi sai da na kawo a raina, in ba Abba ba wa zai basu kud'in nan."

Cewar Aunty Hadiza, don sarai ta san halin mijinta wajen shagwab'a yara.

"Yanzu Audullahi tunda kaga wajen, d'aukarsu ka maida su kuce musu ba'a san sun biya daga gida ba, su maido muku da kud'in."

"Hajiya kud'i fa sun riga sun tafi tunda har an gama ba mai dawo dasu, sannan dan girman Allah sunana Abdullahi, haba dan Allah."

Haj. Saddika tace.

"Babana kaima ka san fa haka ta iya fad'a ba yadda zaka yi."

Yace.

"Wa? Hajiya a da kenan, amma ranar da kunne na ni da Salim muka ji tace Abdullahi sak!, don baya nan ne da ya tabbatar muku wallahi."

"Ai dama akwai randa za'ayi sa'a ta fadi hakan." cewar Mama Balaraba.

"Kai ku kyale ni dashi nace Audullahin, je ka kaini kotun k'oli a tsire ni."

"To ba gwara kai bama tana k'arasawa..." cewar Aunty iyami.

"Abdul da take kira da Auduwa fa."

Sai dukkaninsu suka kyalkyale da dariya har da su Zahran da aka tasa a gaba da farko.

***

Wata ranar Laraba, Farkon azumin watan Ramadan kuma ana saura kwana biyu dawowar Daddy daga Washington, Rahma da Fatima suka zo gidan Mami da niyyar d'aukar Fadeelah suje siyayyar kayan Sallah wanda Baba Habibu ya ba basu kudi gabada'ya har da ita, wannan itace sallarsu da zasu yi ta farko a Nigeria, bayan zuwansu.

"Wai har wata siyayya ake yi da yawa? ni nayi zaton kayan da za'a saka ranar idi ne kawai."

"A k'auyenku na k'asar turawa kenan, anan garin activities ake had'awa har sai kin gaji, don ma bamu da sarki ne da kinga hawan doki na kwana da kwanaki."

"Eh acan ma ana activities d'in amma baya wuce ranar idi dai."

Fatima tace.

"Dan Allah ku taso mu tafi ko zamu samu mu dawo da wuri, wallahi azumin yau da d'an wuya."

Bayan sun gama siyayyar a cikin wani katafaren shago da Abdul da Faruq suka kaisu, suka iso wajen biyan kud'i inda daga bayan cashier akan rataye 'yan alawowi da kuma magazines ko 'yan riguna don k'arin talla, anan idanun Fadeelah suka hango mata wata magazine guda d'aya ta fashion daga gefe ajiye cikin wani rack, hoton wani kyakkyawan saurayi ne a ciki mai kama da tsantsar jinsin shuwa ko fulani, amma ba wai kammaninsa ne suka d'auki hankalinta ba, A'ah gashinsa, style d'in gashinsa yadda ya kwanto gaban goshinsa a barbaje... sak! irin yadda Adam ke yiwa gashinsa ne.

Adam. Wani halitta guda d'aya da har yau zuciyarta ta kasa manta shi balle alkhairinsa, tayi kokarin shafe duk wani abu na rayuwar washington dan ta bud'e sabon shafi na rayuwar da take ganin itace tata, ciki kuwa harda k'awayenta su Melissa da bata biye hirarsu a social media, sai dai lokaci zuwa lokaci su gaisa kawai, balle kuma 'yan uwan Daddy na can da dama ba wani sabawa dasu tayi ba.

Sai dai mutum guda biyu ne kawai manne cikin tunaninta, Al'ameen da duk sanda taga su Rahma tare da samarinsu musamman in suna waya sai ta tuna shi a wannan kwanakin da suka shafe tare kullum mak'ale a waya cikin wata guda d'ayan nan tal!, ko kuma duk sanda wani abu ya bata dariya sai zuciyarta ta hasko mata hotonsa, don shine mutum na farko daya fara koya mata wata hanyar nishad'in ta daban a sabuwar rayuwarta.

Amma Adam zata iya cewa kusan kullum yana mak'ale ne cikin ranta, Allah ya sani a cikin shekara guda data rabu dashi ba zata ce ga wata rana data zo har ta fad'i bata ga wani abun daya tuna mata dashi ba, kai wani lokacin hatta ta cikin reflection d'in cokali kawai sa ta hango fuskarsa a ciki, tun abin na damunta har dai tazo ta yarda cewa, kirkin da yayi mata ne kawai ya manne tunaninsa a cikin ranta.

Sau da yawa sai tayi tunanin cewa zai iya nemanta a wancan layin da a yanzu ba zaiyi amfani a k'asar nan ba, amma kuma sai taga me zai nemeta yace? abinda ya had'a dasu ya riga yazo k'arshe kuma for crying out loud har yanzu shi ba musulmi bane, ina wannan ragowar tsanar da bata gama fita daga ranta ba?

"Muje Deelah.."

Rahma ta katse tunaninta sanda ta mik'o mata wasu daga cikin ledojin da aka d'ura kayansu. Ta karb'a sanda idonta ya sake kallon magazine d'in, fuskar Adam ta haska a maimakon ta kai, da wannan lumsassun idanun nasa yana kallonta.

"Kun san Allah, wata shekarar sai dai ku nemi mai kawo ku siyayya, don ba zai yiwu kuzo ku shanya mu a mota wajen awa guda a banza ba."

Abdul mai bin Rahma ya fad'a sanda suka koma wajen motar.

"Toh uban 'yan mita, shi Faruq dake tuk'in ma baiyi magana ba sai kai." Cewar Fatima, Rahama tace.

"Rabu dashi wata shekarar ma ina zai ganmu, sai dai ya kai 'yan matansa, yayi jiran banzan nan gaske."

"Ai gwara wannan, dama ni na matsu a senda ku wallahi, in banda aike ba abinda kuka sani, ku dai kawai azo ayi muku."

Sun gama saka kayan a booth suna shirin shiga motar amma zuciyar Fadeelah ta kasa nutsuwa, hango magazine d'in nan kawai take yi tana ganin kamar Adam ne zata tafi ta barshi a baya.

Suka shiga motar, farouq ya tayar, yaja suka bar harabar parking lot d'in,? zuciyarta ta tsinke, idonta ya hango mata ranar da suka yi sallama da Adam, sai ta kasa daurewa.

"Faruq dan Allah ku tsaya, nayi mantuwa ban siyo wani abin ba."

"Me kika manta?" Rahma ta tambaya.

"Wannan mayafin da Asiya tace a d'auko mata? mun siyo ai."

"A'ah, wata magazine ce naga wani abu da zan duba a ciki, bari inyi sauri."

Bata ko bari Faruq ya juya ba, ta fita daga motar, ta shiga ratsawa ta tsakanin motocin dake jere a wajen har hanyar data sada ta da k'ofar shagon ta baya, ta dinga wuce mutane akan benen daya kaita hawa na uku, ta k'arasa wajen inda ake biyan kud'in nan... Sai dai me?

Wajen da magazine d'in take fanko, babu ita ba alamarta sai sauran gasu nan rututu!

"Dan Allah wata magazine da na gani yanzu a wajen nan nake nema."

Mutumin ya kalli wajen data nuna sannan yace.

"Yanzun nan aka siye ta wallahi, ina tunanin ma kin had'u da matar da ta siya a hanya."

"Ya salam! Babu wata kuma?"

"Babu irinta gaskiya, amma ga wasu na fashion d'in nan..."

"A ina kake ganin zan sami irinta?" Ta katse shi da sauri.

"Kai, kusan ta wata shida baya ce fa, ta dad'e ne anan ba'a siya bane da sai ince ki duba k'asa ko wasu shagunan, amma yanzu da wuya gaskiya ki same ta wannan watan, sai dai kamfanin amma..."

Bata tsaya jin k'arshen zancen ba, ta bazama k'asa hawa na biyu, ta tambayi cashier d'in nan shima yace mata Babu, haka tayi ta bi waje-waje cikin shagon nan amma babu alamun magazine d'in nan mai irin gashin Adam. Daga k'arshe ta koma wajen cashier ta tambaye shi yanayin matar data siya, ya zaiyana mata cike da mamakin me zata yi da magazine d'in haka.

Sai da ta tambaya sannan itama taga shirmenta, matar fa ta riga ta gama siyan kayanta ta tafi, a ina zata ganta? Haka ta koma wajen su Rahma da suka fara mamakin dad'ewarta da nauyin zuciya.

Sanda tazo kwanciya a wannan daren data k'ara hasko hoton magazine d'in a idonta, da sanda ta juya baya ta tafi ta barta, da sanda ta juya bayan sunyi sallama da Adam ta tafi ta barshi tsaye a jikin motarsa, sai taji wani abu mai kama da kwalla ta cika idanunta!

***

BAYAN SATI DAYA.

A lokacin an shigar tsakiyar azumin Ramadan Daddy ya dawo, wata ranar Lahadi ce da daddare bayan ansha ruwa Faruq da Abdul da yanzu suka zama direbobin k'arfi da yaji suka je suka d'auko shi, su a can airpot d'in ma suka sha ruwa saboda sai da suka jira saukar jirgin tukunna.

Gidan ya rud'e da murna sanda ya shigo su faruq suka biyo bayansa da kaya. Iman ta d'ane shi tana ta ihu yayin da bakin Mami ya kasa rufuwa, shima murna yake sosai don hatta Zahra sai da ya d'aga ta har sama, a cikin sati uku kawai sunyi kewarsa kamar shekara uku.

"Naga wannan abin a hanya na siyo miki."

Muryar Faruq ta fad'a daga gefen Fadeelah sanda ya shigo janye da wani akwati da bana Daddy bane.

"Wanne?"

"Kadaya yake ko me?"

Ta zare idonta da sauri, ta gane kad'anya yake nufi, wani abu da take mutuk'ar so tun daga ranar data fara shansa a wajen Hajiya Amarya.

"Da gaske kake Faruq?"

"Allah kuwa, yana mota bari in ajiye wannan in d'auko miki."

Ai tana jin yace mota tabi ta bayansa da sauri ta fita daga falon, yadda suka yi parking motar a harabar gidan tana fuskantar ta ne, don haka taga booth daga baya a d'age amma bata damu da tunanin me yasa ba'a rufe shiba, ganin ma sauran kofofin motar duk a bud'e suke.

Ta san Abdul ne yayi driving don haka ta gefen kujerar mai zaman banza ta zagaya ta bud'a, ilai kuwa, sai ga kad'anya fal a ciki wata yellow leda, ranta yayi fari k'al a take, sai dai kuma a taken farin cikin nata ya rugurguje har garinsa, tsantsar mamaki ya maye gurbinsa!

Taji sanda aka sauke booth d'in motar, sai dai kafin ta iya juyawa wannan muryar ta shiga cikin kowacce jijiya dake amfani da harkar sauti a jikinta.

"Hello, memory loss girl!"

Wannan husky muryar ce mai cike da tarin kwarjini.

A hankali ta juya gefe, cikin kallo d'aya idanunta suka gano mata wani irin tsantsaren kyau da kamala fiye da wanda ta sani a baya!

Fararen idanu tas! d'an siririn hanci a tsaye masu k'ananan k'ofofi na shak'ar iska kawai, gira mai kauri, dogwayen gashin idon da har inuwarsu ake gani akan fatarsa, d'an siririn leb'e dake tsakiyar wani kwantaccen saje... ta biya hakan ta kuma tuno da tsohuwar haddar da ta yiwa kammanin Al'ameen!

?%O??%

Waye ya hango k'addarar data fara a shafin nan?=??



BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

13

(&_&)

"Jiya Daddy yake gaya min naji haushin maganar sosai Miryam, ace muna zaune a gari amma har Al'ameen zai zo ya bi wasu abokanan aikinsa su sauka a hotel? ko bamu da guri ne ai sai haka."

Mami ta fad'a a safiyar washegarin da Al'ameen ya kwana a gidan, suna cikin kitchen ita da Fadeelah a lokacin suna had'a abincin karin safe, yayin da sauran 'yan gidan ke can kowa na fafutukar shiryawarsa.

Ta cikin wayar muryar Aunty Miryama tace.

"Ai ba wani abu bane Saffiya da baku d'orawa kanku d'awainiya ba wallahi, watak'ila shi sai yafi sakewa ma acan."

Daga yanayin fuskar Mami bata ji dad'in maganar ba, amma sai ta daure tayi murmushi kad'an kafin tace.

"Da nan d'in da can duk d'aya ne ai babu takura Miryaam, shima kuma na san zai so..."

Fadeela ta d'auke hankalinta daga kan saurarenta ta juya wainar kwai ta k'arshe da take soyawa sannan ta kwashe ta a cikin plate. Daga daren jiya zuwa yau bata san me take ji a ranta ba, watakila abu biyun da suka damu zuciyarta ne suka had'u suka zuk'e duk wani emotion d'in da take dashi, kuma ta karb'i hakan hannu biyu don ita kanta a yanzu bata da tabbacin abinda take ji.

Har yanzu akwai wani nauyi a gefen zuciyarta tun daga ranar data rasa wannan magazine d'in mai irin gashin Adam, nauyin daya zama kamar wani abu daya k'ara ingiza tunaninsa a ranta, har ya kai ta binciko takardun lesson d'insu don kawai kullum ta kalli rubutunsa, wannan tsantsareren rubutun da kamar buga shi akayi tsabar tsaruwarsa daki-daki, ta dad'e da fahimtar cewa komai nasa a tsare yake cikin nutsuwa, kamar wannan muryar tasa da in yana magana dole ne ko waye ma ya saurare shi.

Yanzu kuma ga zuwan Al'ameen, wani mutum da tayi kokarin yakicewa daga zuciyarta a baya, ta daurewa kanta ta hana shi yin tasiri a rayuwarta har zuwa lokacin da take ganin sun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login