Showing 57001 words to 60000 words out of 153964 words

Chapter 20 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3792

su gaishe da ita kafin su koma.

Da shawarar Fatima, ta hutar da Mami a ranar ta shiga kitchen ta had'a musu abinci mai dadi, harda kalar na turawa da ta iyo a can. Kuma ba'yan gidan kad'ai ba, ita da kanta kanta tana juya al'amarinta a kwakwalwarta, wai Al'ameen d'in da k'iri-kiri ta yiwa kanta katanga dashi a baya shi zuciyarta kuma ke janta yanzu akansa, tana gaya mata cewa komai ba zai zama matsala ba tsakaninsu.

Sai dai wannan abun shine kusan
jigon daya fara dawo da hankalin Al'ameen kanta, don a washegari da taje yiwa Mami sallama zata tafi makaranta da kansa yace bari ya d'auko muk'ullin motar ya kaita.

"So shekara d'aya? Me kika cimma a rayuwarki so far?"

Ya tambaya sanda go-slow ya tsaresu akan hanya.

Tayi shiru kafin ta d'aga kafad'unta kad'an, idonta na kan motar dake gabansu tace.

"Abubuwa da dama kamar... na shiga university, ciwona yayi sauk'i, na saba da dangin su Mami sannan na iya hausa sosai."

Yayi guntun murmush a gefen lebb'ensa kafin yace.

"Nice! kin samu abubuwa da yawa, na?miki murna."

Ta gyad'a kanta,? "Nagode."

"You're welcome."

Shiru ya biyo baya, kafin ya bud'e kofar motar ya fita, yayi d'age kad'an don hango adadin motocin dake gabansu kafin yaja tsaki ya dawo.

Kamar kar tayi magana sai kuma ta kalle shi tace.

"Sai hak'uri Nigerian mu kenan."

Ya sake wani guntun murmushin da kyallinsa ya haska cikin idanunsa ya kuma sa ta jin wani iri,? Ya Allah! ba wannan ne karon farko data kalle shi ba, amma tun bayan zuwansa,? wannan ne karon farko da ta kalli cikin idonsa kusa da kusa haka, wai meke damunta ne?

"Waya gaya miki bana son Nigeria,? zan iya dawowa nan ma baki d'aya, ina son duk k'asar da kokarin ka zai yi determining waye kai."

Sai ta kawar da kanta gefe.

"Baka san Nigeria ba, Mami tace a anan matsayinka da kuma matsayin wanda ka sani shine kawaia zai fanshi duk kokarin ka."

"Wannan kusan koina ne Fadeelah..."

Sai zuciyarta tayi tsalle ta dira gefe d'aya jin yadda harshensa ya nad'o harafan sunan nata.

"... Kawai dai na wani wajen yafi na wani yawa ne."

Bata k'ara cewa komai ba ta cigaba da kallon rayuwar mutanen waje dake faruwa a bayan windon motar, so take ta tambaye shi bayan gemunsa daya k'ara kyau me kuma ya faru dashi a shekara guda, amma harshenta yayi nauyi ya cika bakinta.

Tun daga wannan ranar sai hira ta fara shiga tsakaninsu, hira mai ma'ana ba irin wadda suke yi a shekarar baya ba, babu wasu kalamai masu taushi, sai magana kawai mai muhimmanci data danganci ra'ayin kowannensu da kuma abubuwan da suke burin cimma.

Ranar daya fara samun numberta kuma Mami ce ta kira shi cewar ya taimaka ya d'auko ta daga makaranta, su dukkaninsu basa nan don shirin bikin Aseeyah ya kankamaa lokacin.

Dole ya karbi numberta ya kira ya shaida mata cewa zai zo d'aukanta,? kuma bayan ya d'auko tan maimakon ya kaita gidan Hajiya Amarya kamar yadda Mami tace, sai da suka tsaya a wani k'aton library tukunna, ya nuna mata wani abu da suka yi musu akansa game da rebe-raben k'asashen duniya.

Sanda ya sauke ta a harabar gidam Hajiya Amarya, Fatima ta d'ago mata hannu daga barandar saman benen alamun fara samun nasararsu fiye da koyaushe.

"Bafa wani abu Faty, har yanzu gaisawa muke sai kuma 'yar hira kawai."

Fatiman tayi dariya a lokacin sannan ta sauke muryarta k'asa don kar su Mami dake gefe suji tace.

"Zauna nan, ke kin san tunaninsa ne? Duk sanda kuke tare kin san me yake ji?"

Me yake ji? Fadeelah tayi tambayar a cikin kanta, don itafa har a lokacin in banda kyawun Al'ameen da kirkinsa da take gani bata san me take ji game dashi ba.

Amma shi kuma fa? Me yake ji game ita?

***

Ji yake zuciyarsa na bugawa da wani irin salo duk sanda yake tare da ita sannan ji yake kamar ita kad'ai ce abinda ke sashi annashuwa a rayuwarsa, sabon da suka yi a yanzu babu abinda yake haifar masa sai k'ara tunatar dashi cewa zuciyarsa ta k'aunace ta a baya kuma bayan wata yarinya daya tab'a kulawa a makaranta, ita kad'ai ce wadda ya taba ji cewa yana son kasancewa da ita har k'arshen rayuwarsa.

Baya gajiya ko kad'an da sauraren hirarta sannan baya taba fasa d'okin wayewar gari a kullum don ya ganta, murmushi kad'ai in tayi sai yaji zuciyarsa ta k'ara dulmiya cikin tunaninta. Ya san cewa ya rufe wannan babin a da, amma yanzu da kowacce dakika in suna tare, k'ara burge shi take, tana k'ara shiga cikin zuciyarsa sannan kuma tana raba tunaninsa gida-gida.

Kuma a cikin kowanne rabe-raben,? abu d'aya ya sani shine har yanzu yana k'aunar Fadeelah kuma ba abinda zai canja hakan, sai dai zai cigaba da mafarkin zaune ne muddin cewa bai motsa ba, bai sake gwada sa'arsa a karo na biyu ba, sannan bai d'ago da kwantaccen hargitsin daya san zai faru daga b'angaren Maminsa ba.

Ya nisa a hankali ya fitar da iska ta siraran k'ofofin hancinsa, yana tsaye ne a gaban motarsa daga harabar wajen bikin, a gabansa mutane ne ke ta wucewa suna shiga ciki, har kuwa da jerin 'yanmata kala-kala kowacce cikin kwalliya, sai dai a idanunsa shi duk mata a irin wannan shekarun na 'yammatanci d'aya yake ganinsu, ba turawan da yake cikinsu ba, ba kuma wad'annan jinsin hausa-fulanin da yake gani a yanzu ba, kowaccensu kallo d'aya kawai yake musu,? na Mace kawai!

Amma Fadeelah, tun daga ranar daya fara ganinta a cikin kitchen d'in nan,? yaga kamar ansa wata filtila ne ta samanta an haska ta, hasken da ya shiga har cikin idanu da zuciyarsa ya haska su, yasa ya yarda cewa ita d'in daban ce da kowa, tun daga wancan lokacin har zuwa yanzu kuwa. Shi yasa yake ganin lokaci yayi da zai fuskanci k'addarar dake biye dashi tsawon wannan lokacin.

A sanda Fadeelan ta ratso daga cikin wajen ta nufo wajen adana motocin da yake, zuciyarsa ta matse fiye da koyaushe ganin yadda kwalliyar fuskarta ta sake fito da tsantsareren kyawunta da bai taba gani ba, kamar yadda bai taba ganinta cikin kwalliyar ba.

Kwarai lokaci yayi da zai sake gwada sa'arsa kan Fadeelah a karo na biyu, karon da yake jin cewa ba zancen Hamida ba, a yanzu ko Maminsa bata isa tasa ya guntule farin cikinsa ba.

Abu d'aya kawai shine bai san cewa in a yanzu zata karb'e shi ba, ko kuma tarihi zai sake maimata kansa!

***

"Wai ba nan aka rubuta a jikin venue d'in ba da gaske?"

Wata 'yar kyakkyawar Matashiyar mata ta fad'a sanda take gyara hular kan yaron da take rik'e dashi a hannunta, kamar ita, yaron fari ne sosai sai dai har yaso ya zarta ta ma a kyau in akayi duba ga ya had'o da kammanin Mahaifinsa ne wanda ke zaune a gefensu yana shirin kunna had'addiyar motar da suke ciki.

"Sunan da address d'in duk iri d'aya,? amma sunce wai wannan sunan Amaryar Aseeyah ba Amina ba."

"Bibty mu koma gida kawai dan Allah,? kayi musu Allah ya sanya alkhairi in ka koma office, don ina jin ma Afra zazzabi ne ke shirin kamata."

Ta fad'a tana juyawa ta kalli wata 'yar yarinyar dake zaune a baya motar cikin shigar wasu pink kaya masu kyau, babu ko d'ankwali akanta sai yala-yalan gashinta da aka tufke cikin k'ananan kalba da ribbons.

"Hakan za'ayi kawai, nima na fara gajiya, don munsha yawo yau."

Mijin ya amince kai tsaye sannan ya shiga kokarin yin reverse a harabar wajen. Sai dai me? A daidai lokacin daya juya kan motar cikin saurin dake nuna lafiyar injinta, idanun matar nan suka sauka akan wata budurwa daga can nesansu, tana sanye cikin pink kaya na alamun ankon bikin sannan tana kokarin nufar wani saurayi dake jingine a gaban wata mota.

Da dare, da tazara tsakaninsu da kuma girma daya sauka akan fuskar budurwar, amma duk wad'annan ba komai bane, koda ragowar numfashi? guda d'aya ne ya rage mata a rayuwarta... Ba zata tab'a kasa shaida kammannin k'anwarta jal a duniya ba.

BINTUN IKARA!

?%O??%


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

19

(&_&)

A lokaci guda komai ya haska tar! Cikin idanun matar, a wannan duhun safiyar data tsallake shimfid'ar 'yar k'anwar tata ta nufi k'ofa, da sanda har ta zura kafarta waje ta juyo ta sake kallonta duk'unk'une cikin zanin rufarta kasancewar lokaci ne irin na sanyi a sannan, da kuma sanda ta ciro wani zoben hannunta da Bintun ke yawan k'alatarsa ta dawo ta ajiye mata a gefen fuskarta sannan tabi duhun safiyar da idanun jama'a suka yi k'aranci cikinsa, ta tafi ga abinda take jin gwara mutuwarta da ta rasa shi a rayuwarta.

Wannan wani abu ne da ta dad'e da mantashi, baya ma cikin lissafinta kwata-kwata, don tun bayan da hakan ta faru, bata tab'a waiwayarsa ba ko a cikin kanta, amma a yanzu da tunaninsa yazo mata, sai take jin kamar a jiya ne akayi komai.

"Menene? Me ya faru?"

Mijin nata ya tambaya yana kokarin kallon inda ta juya, sai ta katse shi ta hanyar juyowa ta kalleshi da fararen idanunta k'al! wanda maik'on kwallar data fara taruwa a ciki tayi musu wani ado.

"Bibty wata na hango acan kamar..."

Maganarta ta katse, saboda a daidai wannan lokacin igiyar jikin wani mutum-mutumi da aka had'a da tarin layoyi ta sake daurewa tamau! Sannan d'igon jini guda ya d'iga a jikin k'asar kabarin da aka binne shi.

Ta d'an tsaya cak! Kamar wadda ake gogewa wani abu kafin kuma ta girgiza kanta a hankali sannan tace.

"Wata na gani kawai kamar na santa, mu tafi daga nan wajen dan Allah."

Ya gyada kansa sau d'aya sannan ya karasa juya kan motar suka nufi hanyar gate, Tarihi ya sake maimata kansa!

Sanda yazo mik'awa mai gadin wajen pass d'in hannunsa ne ya kalleta ta gefen ido, ta sunkuyar da kanta kad'an sannan da zaren hular kan d'ansu Muhammad ta d'auke 'yar k'aramar kwallar data fara taruwa a idonta.

Bai san me ta gani ba amma a take yaji zuciyarsa ta matse cikin k'irjinsa, wata irin matsewa mai rad'ad'i, irin yadda yake ji a duk lokacin daya tuno abinda yayi da kuma sanadin kasancewarta matarsa. Wani gefe a cikin tunaninsa ya shiga shaida masa abinda ya shafe tsawon lokaci yana nusar dashi, cewa lokaci yayi da zai daina bautar da ita ta hanyar dole!

Watak'ila a yanzu zata zauna dashi ko don albarkacin 'ya'yansu.

***

"Nayi zaton ka shigo ciki."

Fadeelah ta fad'a sanda takunta ya k'arasar da ita gabansa.

Sai da Al'ameen ya had'iye wani abu a mak'ogwaronsa jin siririyar muryarta sannan ya mike tsaye daga jiginar da yake. Tsawonsa akanta ya baiyana tazarar incinan dake tsakaninsu sosai duk da cewa ya lura takalmin k'afarta na da d'an tudu.

"Naji ance kamar biki biyu ne a wajen, shi yasa ban san ina zan shiga ba."

"A'a..." Ta girgiza kanta.

"Fatima tace bikin wata Aminah ne suka yi mistake suka saka date din yau alhali sai gobe ne nasu, shi yasa mutane ke ta zuwa suna tambaya."

"Okay, na gane."

"Baku taho tare dasu Ya Abdullahi ba?"

"A'a, su suna ciki ai ina jin, ni kai tsaye daga gida nake."

Sai ta gyad'a kanta a hankali, kwakwalwarta na gaya mata duk mutanen ita kad'ai ce ta san hanyar shigar dashi kenan, a sannan shi kuma ya tsaida idonsa akan fuskarta da kuma surarta mai shagaltar dashi na 'yan wasu sakanni kafin yace.

"Kinyi kyau 'yanmatan Mami."

Sai ta kautar da kanta gefe kadan cikin jin kunya, wanda hakan ba komai ya haifar ba sai kara tsima shi da tayi sakamakon wata mota data shawo kwana ta haske fitilarta dal akan fuskarta.

"Kaima kayi kyau, Mr. Balaraben Bature kuma Bahaushe a yau."

Ta fad'i hakan ne, tana kallon kayan jikinsa, wani yadi ne mai d'an banzan kyau da yasha fitted d'inki mara aiki irin wanda samari ke yayi a yanzu, kuma tun zuwansa k'asar, yauce rana ta farko daya fara sanya dogayen kaya, don telan Ya Abdullahi da suka fara shiri dashi a 'yar tazarar dake tsakanin gama aikinsa da yanzu ne ya bawa kwangilar yin kayan don kar ya fita daban a taron bikin.

Yasa hannu ya shafa lallausar sumar k'eyarsa sannan yace.

"Yana iya? Tunda hausawan sun rik'e ni ai dole ne in ajiye komai a gefe in shiga cikinsu."

"Kar ka damu, bikin dai daga yau sai gobe, Mami ta kusa sakinka."

Amma ke fa? Zaki taba sakin zuciyata ne Fadeelah?

"Mu shiga ciki?"

Ta tambaya jin baice komai ba, sai ya gyad'a kansa kawai tare da nuna mata hanyar. Da kowanne taku da yake bin bayanta, ji yake kamar ya fisgo hannunta ya tsaida ita, ya gaya mata dukkanin abinda zuciyarsa ke ji game da ita, cewa komai ya dawo sabo... Yana sonta kamar zaiyi hauka!

Amma ina! irin wannan kasassab'ar ita yayi a farko, ya gaya mata yana sonta ba tare da wani tsari ko shiri ba, ba tare da ya shagaltar da zuciyarta ta manta da duk wani k'alubalen da zai iya faruwa tsakaninsu ba.

Mace kamar kwai ce...

Kamaal ya tab'a gaya masa a wani lokaci.

... iya kokarinka wajen lallab'a kwan nan da kula dashi, shi zai sa har ka kai ga cinsa. Amma da zarar kace zaka rik'e shine ta duk yadda kaga dama, to a lokaci guda zai fad'i har dandaryar k'asa ya fashe.

Sanda suka k'arasa cikin hall d'in kusan kowa na cin abinci anata aikin bawa ciki ba babba ba yaro, don haka wata cool music ke tashi a wajen babu hayaniya sosai. Ance wai idan mutum na cikin damuwa a lokacin yake fahimtar me ake fad'a wak'a musamman idan wak'ar ta shafi shigen halin da kake ciki ne, don dalla-dalla Al'ameen ke jin kowacce kalma da wak'ar dake tashi take fadi a lokacin.

I wish I could go back to the very first day I saw you
Should've made my move when you looked in my eyes
'Cause by now I know that you'd feel the way that I do
And I'd whisper these words as you'd lie here by my side

I love you! please say
You love me too, these three words...
They could change our lives forever...

Duk tarin d'imbin jama'ar hall din nan suka zuk'e a idanunsa, Fadeela dake take tafiya a gabansa kawai yake gani da kuma wak'ar da yake jin kamar daga bakinsa take fitowa, da kyar ya sawa k'afarsa birki bai had'e da ita ba sanda ta tsaya daga tsakiyar hanyar tana waige-waige.

"Anan wajen fa na barta dasu Aunty iyami, ina kuma suka tafi?"

To whisper in your ear
Words that are old as time
Words only you would hear
If only you were mine...

Baitin wak'ar yayi daidai da yadda ya tsaya dab da ita kamar zai rad'a mata wani abun, a lokacin itama ta juyo ta kalle shi bakinta a bud'e kamar zata yi masa magana, sai kuma ta maida shi ta rufe sakamakon wani irin maganid'isun abu data hango daga kyawawan idanunsa.

Hasken flasher ne ya katse ya kuma janyo su daga tunanin da kowannensu ke shirin fad'awa a lokacin.

"Yawwa Hajiya, ku d'an juyo nan haka kuma muga, d'ari biyu ne kowanne kati ba tsada."

Wani mai hoto daya saita camerar sa akansu ya fad'a yana k'ara durk'usawa. Ita ta fara janye idonta ta juyo ta kalli mai hoton sannan ta girgiza kanta da sauri tace.

"Yi hakuri Malam ba hoto zamu yi ba."

"Ayya hajiya wallahi baki ga yadda d'ayan yayi kyau ba, ko biyu ne mana ku tsaya a d'an kara yi, ku ajiye na tarihi."

Ta sake girgiza kanta.

"Ka goge shi kawai mun gode..." Ta juyo ta kalli Al'ameen d'in dake tsaye baice komai ba tace.

"Ga wajensu Ya Abdullahi can, ko zaka je kafin in nemo Mamin."

Bata jira amsarsa ba ta juya zata tafi, sai dai me? Caraf ya riko hannunta guda d'aya, ya zagaye yatsunta cikin nasa yayi musu rumfa, gabanta ya fad'i sannan zuciyarta ta buga a lokacin d'aya kafin ta juyo ta kalle shi, idanunta na nuna tsananin mamaki.

"Ki tsaya ayi mana hoton ko guda d'aya ne."

Jin haka yasa mai hoton dashe baki sannan ya sake d'aukar saiti don kyallara musu.

"Please."

Ya fad'a da muryarsa a hankali yana kallonta, ya had'a ta da Allah, ba yadda ta iya, bama zata k'i iyawar ba. Sai ta gyad'a kanta sau d'aya sannan ta juya kawai ta kalli mai camerar da ya gama shirinsa yana jiran nasu, ta gefen idonta taga sanda shima ya juyo ya kalli mai hoton da guntun murmushi a fuskarsa.

"Masha Allahu, wallahi Alhaji kunyi kyau, ko amarya da angon nan sai haka."

Murmushin nasa bai goge ba yace.

"Ka wanke kowanne biyar, iya kyan da suka yi, iya yawan kudinka."

Da sauri ta zare yatsunta daga cikin nasa sannan a gajarce tace.

"Ina zuwa."

Da haka ta juya ta barshi da mai hoton suna cinikin rabon da Allah ya kawo masa. Bata yi nisa ba taci karo da Fatima wadda ke ta faman zarya daga nan zuwa nan saboda ita kanta adadin mutanen gaiyarta daban ne.

"Faty Mami nake tambaya kinga inda suka yi?"

"Gasu can wajen amarya suna d'aukar hoto, me za'ayi?"

"Al'ameen ne zai bata sak'o kafin ya wuce gida, wai ba dad'ewa zaiyi ba."

Da murmushinta tace.

"Yarinyar nan zaki biyani fa wallahi plan d'ina yayi aiki, kice har bibiyarki yake ko'ina."

"Bafa saboda ni yazo ba, na gaya miki Mami tace ya bari sai anyi bikin sannan ya tafi."

Kafin ta amsa mata, Aunty iyami daga can wajen ta shiga d'ago musu hannu, don duk 'yan gida masu irin ankonsu suna ta zuwa ana d'aukar hoto da Amarya da ango wanda sai fara'a suke dukkaninsu cikin shigar brown kaya da suka dace da kwalliyarsu.

"Mami, Al'ameen ne yake nemanki, yazo yanzun nan."

Fadeelah ta fad'a cikin hasken flasher sanda suka jeru gabad'aya ana d'aukar hoton, ta san a wannan lokacin ne kad'ai Mamin zata saurareta, ganin ana d'aukar hoton ma wasu daga can na d'ago mata hannu. Ai kuwa da kyar ta samu ta had'ata da Al'ameen d'in da ya dad'e a tsaye yana jiranta bayan dawowarsa daga wajensu Ya Abdullahi.

"Mami kayan da kika ce in taho dasu ne daga gida, suna nan a cikin booth, kuma ni yanzu zan juya."

Cikin alamu na rud'ewar biki Mami Safiyya tace.

"Yawwa to ai ga ma Fadeelah a kusa, kuje ki karbi muk'ullin motar hannun Farouk, a kwashe kayan a saka a cikin booth d'insa, plates ne da za'ayi amfani dasu gobe da safe na manta ba'a tafi dasu ba."

Da haka bata k'ara cewa komai ba ta juya ta koma wajensu Aunty iyami.

"Kin san inda Farouq d'in yake?" Al'ameen ya tambaya.

Ta girgiza kanta tace.

"Ai Farouq ma baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login