Showing 99001 words to 102000 words out of 153964 words

Chapter 34 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3797

kuma ta iya kallon fuskarsa sosai, wani irin fresh ne da fatar jikinta mai d'aukan hakali, gashi yayi shaving sajen sa tas! Babu ko tuntub'en gashi, sannan gashin kansa... Wannan gashin nasa a kwance cikin alamun danshi dake shaida cewa bai dad'e da fitowa daga wanka ba.

"Me yasa baki gaya musu baki da lafiya ba?"

Ya tambaya a hankali yana juya shi kowanne b'angare, hakan ya dad'a sa Fadeelah taji hannun ya zama kamar ba'a jikinta yake ba, saboda haka ta janye shi da sauri, ya d'an tsaya kamar baiji dad'in hakan ba sai ya mik'e a hankali ya tsaya akanta.

Bayan tabon, idonsa k'unshin hannunta kawai ya gane masa, k'unshin daya fara fita saura d'an zirin zanensa kawai waje-waje, bai san me yake tunani ba har sanda muryata ta bashi amsar da yake jira.

"Lafiyata k'alau, kuma idan ma bani da lafiyar banga abinda ya had'a ka da hakan ba." Ta d'ago da kanta tana kallonsa sanda ta fad'i hakan.

Ya ilahi. Bata san ya yake jin kaifin wannan kallon nata ba, bai ce komai ba sai da ya lumshe nasa idanun tukunna.

"Idan baki da lafiya zai shafi aikina, don za'a k'arawa? shari'ar nan kwanaki ne muyi ta zama cikin abu d'aya."

Ta had'iye sauran wani burbushi abu a makogwaronta kafin ta iya bashi amsa.

"Ni lafiyata k'alau, wannan cizon sauro ne kawai."

Yana daga tsayen yace.

"Amma kina ciwon kai?"

Kamar ba zata amsa ba sai kuma tace.

"Eh."

"Kin ci abinci yau?"

A lokaci d'aya taji wani iri, don bata gane inda ya dosa ba, ita tayi zaton zuwa yayi mata wata tambaya ko ya gaya mata wani abu game da shari'ar da suke ciki, amma meye amfanin wad'annan tambayoyin? Saboda su ya guntule mata d'an lokacin data samu tare dasu Mami?

"Kinga..." Ya fad'i hakan sanda ya nemi wata kujera a gefe ya zauna."

"Ina tambayarki duk wannan abun ne saboda yanzu aka fara shari'ar, kuma kowa ya ganki zai san cewar kin canja mutuk'a daga yadda kika zo wajen nan tun ba'ayi zama na biyu ba, ni lauyan ki ne dole ne in damu ..."

Kamar wani ya katse shi ya tsaya bai k'arasa ba, saida ya saita kalamansa dake shirin zamewa sannan ya cigaba.

"Wannan cizon da sauro ya miki ko baki yi zazzab'i yanzu ba zaki iya gobe ko jibi, ba zan iya kawo likita nan ba amma zan iya samo miki magani ko hanyar da zaki ji saukin abubuwa, na gaya miki in kika fara rashin lafiya zai shafi dukkaninmu."

Ba wai ta yarda da zancen bane yasa tayi niyyar bashi amsa, kawai ta k'agara ya tafi ne don bata son abinda take ji a yau game dashi, maganganunsa wani a hankali kamar sai sunyi tracing kan fatar ta ne kafin su shiga kwakwalwarta, sannan ga inda ya rik'e hannunta har yanzu tana ji kamar k'ankara aka d'ora a wajen.... Saboda hakan ta bud'e baki ta gaya masa duk wasu abubuwan da take fama dasu a wajen, abubuwan da bata taba gayawa waninsa ba, sai hirar tasu ta zama kamar ta tsakanin likita da mara lafiyarsa kwata-kwata bai sako mata zancen da ya shafi shari'ar ba itama bata tambayi komai har kuwa ya tafi, don zuciyarta na cike da d'acin yadda har yanzu baya nuna wata alama ta ya san hallitarta a America.

Ba'afi awa d'aya da tafiyarsa ba, Musa mai tsaronta ya kawo mata wata madaidaiciyar leda mai d'auke da tarkacen magaunguna da kuma da kuma kayan ci ma irin na leda, sannan harda wani lotion da in mutum ya shafa sauro baya iya hawa jikinsa, bayansu sai manyan robobi na ruwa. Allah kad'ai ya san irin hanyar da yabi kafin a bar kayan nan ya iso gareta, don su Mami ba irin kokarin da basu yi ba amma aka hana su shigo mata da ko ruwa.

Akwai 'yar jotter a cikin ledar daya rubuta mata yadda zata sha magungunan, idonta ya tsirawa rubutun ido... Ta kara yarda cewa tabbas wannan Adam d'in data sani a America ne don ga rubutunsa nan kamar yadda ta haddace sh a lokacin tutorial d'insu, mamaki ya sake d'aure tunaninta game dashi, ta kasa gane dalilin da yasa yake b'oye mata kansa, kamar yadda ta kasa gane yadda akayi yazo Nigeria har cikin 'yanuwanta.

***

"Haba Hajiya, nan fa ba gidan dubiya bane, d'azu wasu suka zo suka matsa sai da suka ganta yanzu kuma kinzo? Ba fa a ma barin ziyara da yawa a kotun nan amma ku tun yaushe muke d'aga muku k'afa? Daga wannan yazo sai wani yazo, ko an gaya muku ku kad'ai ne masu 'yar uwa a koton ne?"

Wani mutumi dake zaune a teburinsa ya fad'a cikin masifa sanda Mairo da Kawu Ibrahim ke tsaye a gabansa suna rok'on abinda Mairo ke ganin a yanzu rayuwarta ta ta'allak'a akai.

Ashe har wasu sun rigata ganin Mairo a yau? Saboda su kuma ake shirin hana ta ganinsu yanzu... A cikin zuciyarta ta tsinewa lokacin data b'ata a wajen su Kawu D'anjuma da bai amfane ta da komai a yau ba, Kawu Ibrahim daya samu labarin zuwanta ne da kuma abinda ya faru a jiyan ya had'a taro na gaggawa bisa alfarmar daya nema a wajen Kawu D'anjuma.

Taron ya had'a harda wad'anda ba'a kira ba sai suka zo don jin abinda za'a tattauna, inda ba komai akayi ba sai rok'o da Kawu ibrahim d'in yayi tayi akan a taimaka a yafe mata laifin da tayi tunda har tayi hankalin dawowa cikinsu a yanzu, amma sai da aka kai ruwa rana sannan Kawu d'anjuma yasa baki a gajarce cewa shikenan taje sun yafe mata, bayan kuma ta gaya musu cewa tana da miji har da 'ya'ya biyu, sai komai ya nemi dawowa sabo...

Da yawansu suka saka baki kan cewar laifinta na raini ne da son zuciya, tunda har ta iya haihuwa biyu kafin ta neme su, su kace kar ta sake ko da wasa ta kawo 'ya'yan cikinsu balle kuma shi mijin data fifita akansu, ba irin kuka da magiyar da ba tayi musu ba cewa itama bada son ranta tayi hakan ba, amma haka aka tashi Kawu Ibrahim baici nasarar tara sun da yayi ba.

Daga nan ya kaita b'angarensa, inda matarsa Aunty Hassana ta karb'eta da mutunci, ta bata ruwa tayi wanka, sannan ta d'auko sababbin kaya a cikin nata ta bata ta sanya, ta fita daga cikin suturar data danganci Sadiq da dukiyarsa. Bayan taci abinci kuma tasa aka samo mata magani saboda zazzab'in yayen Muhammad daya fara kamata, amma duk wannan abun da ake yi zuciyarta hanqoro kawai take na son ganin 'yaruwarta.

Yayin da duk wannan abinda ake yi kuma, Sadiq na daga can gefen layin cikin motarsa yana samun bayanin abinda ke faruwa daga wajensu Saminu, don da gaske Maryam take ta yanke alak'arsa da ita, bata k'ara nemansa ba kuma bata k'ara bari ya ganta ba, gashi ba ko waya a hannunta tunda daga asibiti ta taso, ga magungunanta ma suna zube a motarsa bata ko sake waiwayarsu ba.

A safiyar ranar ne k'annwn mahaifiyarsa biyu, su Umar suka zo kamar yadda tayi alkawarin turo su, kuma bayan bayaninsa mai cike da kwana-kwana ya lallab'a su suka koma ba tare da sunga 'yanuwan Mairo ba kamar yadda ya turo su da k'udirin hakan.

Kuma da yake har yanzu Nairar jikinsa na sawa ya fad'a aji sai suka yarda ya sama musu jirgin yawon da ya tashi k'arfe d'aya na rana? suka koma harda Zakkiya da Muhamnad. A yanzu yana jiran kiran mahaifiyarsa ne da kuma duk wani hukunci da zai fito daga Maryam.

"Yallab'ai don girman Allah, wannan 'yaruwarta ce shekara da shekaru basu had'u ba, bama ni saina shiga ba ka taimaka ta ganta ko na minti goma ne."

Cewar Kawu Ibrahim, mutumin ya girgiza kai baya ko kallinsu.

"Naga gobe zaku shiga kotu, meya na saurin? Ta ganta a can kawai."

Kafin Kawu Ibrahim ya sake cewa wani abun k'ofar ofishin ta bud'e, wani mai tsaro ya shigo.

"Ranka ya dad'e kira ne daga waje."

"Ahh haba dai! To gani nan."

Ya rufe file d'in gabansa da sauri kawai sannan ya fita daga office d'in ya barsu."

"Kawu dan Allah mu zauna ya dawo, mu k'ara rokonsa ko zai yarda." Cewar Mairo bayan fitar tasa.

Sanin irin yadda ta damu ne yasa Kawu Ibrahim ya amsa mata suka cigaba da zaman jira a office d'in amma ya riga ya fahimci cewa bashi da niyya.

Kusan minti biyar sai gashi ya dawo.

"Yawwa nace ku ai baku yi bayanin cewa 'yanuwa ne na kusa ba, ni tunanin da nake irin daga nesa kuke ne shi yasa, amma ba komai zaku iya shiga ku ganta yanzu, sai dai ku hanzarta don naga yamma tayi, kuje za'a fito muku da ita."

Ba Kawu Ibrahim ba, hatta Mairo dake cikin zumud'i sai da tabi mutumin nan da kallon mamakin yadda ya canja a lokaci d'aya. Sai dai ita bata yi tunanin komai ba saboda hankalinta ya tafi gabad'aya ga son ganin Bintun, amma a tunanin kawu Ibrahim zato yayi Adam ne ya bada umarnin a barsu su ganta.

Sadiq na tsaye daga cikin office d'in wani Babban ma'aikaci a wajen ya sauke ajiyar zuciya a hankali lokacin da ya hange su sun nufi d'akin da ake ganawa da d'aurarrun.

***

Da ace akwai inda murna zata iya yin masauki a zuciyarta, da babu abinda zai hana Fadeelah jin hakan lokacin da aka shaida mata cewa ta sake samun mai zuwa ganinta har sau biyu a rana guda.

Watakila ba'afi awanni biyu da shan maganin da Adam ya kawo mata ba, amma har taji sauk'in yanayin jikinta da kuma taimakon kayan cimar ledar nan sannan ta d'add'aki ruwan ma kamar ba gobe, don ji tayi kamar ta shekara rabonta da ruwa mai tsafta irinsa.

K'afarta bi da bi take bin bayan mai tsaron nan Musa, har zuwa wajen da a yanzu shi kad'ai ne silar samun sassaucinta, tunda a nan ne kad'ai inda zata had'u da mutanen da basa ganinta da wannan laifin.

Kawu Ibrahim idonta ya fara gane mata, sannan kuma ta tsaya cak sakamakon fuskar Mairo data ci karo da ita a gefe, Mairo dai da ta gani a Abuja, Mairo 'yaruwarta tsaye tana kallon hanyar k'ofar data shigo ta ciki idanunta a zare kamar zasu zazzago daga mazauninsu su fadi k'asa.

A lokaci d'aya taji iskar da bata san wace iri bace ta zarce cikin makogwaronta sannan d'an mitsitsin sauk'in data samu game da kulawar Adam ya murmushe yabi iska, ta sake kallon Kawu Ibrahim sosai, sannan Mairon da bata jira komai ba ta fara kokarin tahowa gare ta da sauri, sai kawai ta juya da sauri itama ta fita daga wajen, ta koma hanyar da suka biyo.

Kawu Ibrahim ya sani, ta gaya masa cewa bata son ganin Mairo bata buk'atar sake ganinta a rayuwarta, amma shine ya kawo ta har nan... Tiryan-tiryan tabi hanyar data haddace ta har cikin cell d'in da yake nata a yanzu, ba tare da wani mai tsaro ba ta shiga da kanta kuma ta janyo k'ofar ta had'e ta, yadda take ji a cikin ranta duhun wannan cell d'in ya fiye mata ganin Mairo da dukkan kasancewarta a duniya.

Ta san cewa tunaninta yafi karkata ga cewar ita Fadeelah ce a yanzu, amma tunda har tunaninta na farko a matsayin Bintu yana tare da ita, zata karbi kowanne hannu biyu ta bashi hakkinsa...

"...duk sanda Mairo ta dawo gareku kuce na yafe mata Malam, wallahi na yafe mata.

Muryar Innarta a ranar da zata mutu ta haska cikin kanta sanda ta nemi can k'arshen cell d'inta zauna, Inna Saratu ce taje ta tashe ta a safiyar ranar akan cewa tazo Inna Aminar na nemanta, kuma bayan tabi bayanta har zuwa d'akin da take ciki, ta tsinci k'arashen wannan zancen nata tana gayawa Baba dake zaune a gefe rik'e da hannunta.

A lokacin k'afafunta rik'ewa suka yi ta kasa karasawa cikin d'akin, bata kai yanzu wayo ba amma tun a sannan tayi zaton cewa irin bak'in ciki da wahalar da Mairo ta jaza musu ba wanda zai iya ko d'aga ido ya kalleta duk ranar da ta waiwaye su balle har ayi zancen 'yafiya'.

Taso a yanzu zata iya haskawa Mairo wannan lokacin da Innarsu ke kan gab'ar mutuwa amma tana fad'in cewa ta yafe mata duk da cewa kuwa itace silar ciwon nata, taso zata iya nuno mata taga irin soyayyar da ta gujewa ta tafi neman wadda bata k'unshi komai ba sai sha'awar duniya, taso zata iya nuna mata irin bak'in ciki da kuma azabar da dukkaninsa suka jure a dalilin son zuciyarta... Taso zata iya nuna mata yadda ta rasa uwa, Baba ya rasa mata, inna Saratu ta rasa 'yaruwa duk a gaban idonsu saboda ita kad'ai kawai.

Ta rufe idonta a hankali sanda ta jingina da bangon, ta dad'e da d'aukarwa ranta alkawarin cewa ba zata tab'a yafewa Mairo ba koda kuwa duniya zata nad'e da ita a cikin k'asa.

Jinginen ba dadi saboda haka ta lalubi? dandaryar simintin nan ta d'ora fuskarta? sanda tunaninta ya dawo mata lokacin da Baba ke biya kalmar shahada cikin kunnen Innar da kowacce gab'a ta jikinta ke girgizawa mintuna kad'an bayan shigarta d'akin.

A lokacin hawayen dake fita daga idanunta sun k'afe, tana rik'e da hannunta mai d'umi da ita Innar da kanta ta miko mata ta kama, Baba ya cigaba da furta kalmomin shahadar cikin kunnenta kafin ta iya karb'a da wata irin murya mai k'arfi data cika d'akin.

"Lailah ha ilallah, muhmad rasu..."

Shiru ne ya biyo baya bata k'arasa ba, sannan a lokaci d'aya kuma hannun da ke cikin nata yayi sanyi kalau, idanunta suka bi sama da kallo sannan numfashinta ya yanke, ya yanke tare da duk wani ragowar tunaninta a lokacin.

Tana iya tuna yadda shirun d'akin ya fallasa k'arfin kukan Inna Saratu yayin da Baba yayi k'ame kawai rike da hannun gawar kamar yadda itama take.

A duniyar nan kaf! Gwaggo lami da ta shigo d'akin daga baya, itace ta fara furta rasuwar Inna Amina.

****

Gwaggo lami ita ta fara zuwa a matsayin shaidar Kutama ranar da akayi zama na biyu, tazo ta fad'i duk wasu k'arairayin da babu ko d'igon gaskiya a ciki, amma ta rantse ta kuma kalli Alkali ta tabbatar da gaskiyar ta fad'a.

Fadeelah ta san Adam bai so yi mata? tambayoyi ba amma irin maganganun data fad'a yasa shi ya mik'e, amma da yake ita d'in tsohuwar makira ce ta bashi dukkan amsoshin da suka tafi daidai da k'aryar data fad'a. Bayan ita Kutama ya kira 'yan sandan da suka je neman Bintu har garin Kano a lokacin da akace motarsu tayi hatsari, ya kira? likitocin da suka tabbatar da irin gubar da aka sanya a kokon, ya kira wad'anda suka tantance shaidar hannun Bintu da ya fito a jug d'in data kai mata kokon, hatta mai markaden geron da akayi sai da ya kira kuma Alkali ya gamsu bayanansa da yawa ta yadda a cikin wata guda kawai ko makaho zai shaida inda shari'ar ta dosa.

'Yan Babban gida suka sami abinda suke so, farin ciki ya rufar musu ganin cewa suke da nasara a kowanne zama da akayi, hankalin Kawu Ibrahim ya tashi ya zama kusan kullum yana zarya tsakanin Ikara da Zaria wajen Adam, Mami ma ta k'ara rud'ewa gani take a kowanne lokaci za'a iya yankewa Fadeelah hukunci akan shari'ar nan, ita kanta Fadeelah duk sanda aka shiga zaman kotun ta kalli fuskar 'yan Babban gida taga yadda kowannensu ke murmushin jin dad'i sai zuciyarta ta sare, don hatta Habiba yanzu ta fara goge tashin hankalin kan fuskarta ganin yadda shari'ar tafi karkata gare ta a kullum.

Sai itama ta fara tunanin cewa sa'a na hannun kowa, rayuwarta tare dasu Mami zai iya kasancewa shine lokacin hutunta kawai a duniya, komai zai iya k'arewa a wannan gab'ar a yanke mata hukuncin da zai kawo k'arshen rayuwar tata.

Akwai zaman da akayi wanda Kutama ya dinga kawo hujjoji harda hotunan gawar Hajiyan ga Alkalin, hankalin mutane ya nutsu aka dinga ganin kamar a ranar za'a kawo karshen shari'ar saboda yadda komai ke fitowa fili... Amma Alkalin ya juya zaton kowa da sake d'aga k'arar zuwa wani lokacin, da alama yayi amfani da rok'on Adam na tun farko cewar kar kotu ta yanke hukunci cikin gaggawa.

Sai dai duk wannan abin da akeyi, hankalin Adam a kwance yake tsaf don shi kad'ai ke iya k'arfafawa Kawu Ibrahim gwiwar cewar ya kwantar da hankalinsa shima, Kutama yana barazana ne kawai da abinda bai sani ba.

Aunty Hadiza, Fatima dama kuma Abdullahi duk sun koma a lokacin, don haka Daddy da a dole ya nemi hutu a asibitinsa shi kad'ai ke kwantar da hankalin Mami data kafa ta tsare cewar ba zata koma Abuja ba sai an gama shari'ar nan, tana zaune a garin har lokacin kuwa da aka d'age shari'ar da hutun sati biyu, su Zahra ma sunzo amma har suka tafi basu samu ganin Fadeelah ba don an dad'a saka tsaro sosai akan ganin nata.

Abinda ya dad'a d'aid'ata rayuwar Mairo kenan wadda har a lokacin take wajen Kawu Ibrahim, kullum tana gidan bata taba fita sai ranar da za'ayi zaman kotu, ta toshe kunnenta kuma ta hakura da duk wani zagi da maganganun da ake fad'a mata a Babban gida, ta karb'i rayuwar a yadda tazo mata hannu biyu ta manta da Sadiq da wasu 'yanuwansa, 'ya'yanta ne kawai kan fad'o ranta lokaci zuwa lokaci tana jin kewarsu, amma duk da haka a ranar da Sadiq ya shafawa idonsa toka ya d'ebo 'yanuwansa har cikin Babban gida da sunan biko, bata ko kalli 'ya'yan ba balle shi.

Kawu Ibrahim kawai suka samu ya saurare su a duk fad'in gidan, kuma shima bai basu wani fata ba don yace sai abinda ita ta yankewa kanta tukunna, saboda laifin Sadiq ya riga ya fito k'arara su kansu 'yanuwan nasa a yanzu sun san ya aure ta ne bisa rashin sanin iyayenta, amma da yake da kud'insa a k'ugu sai hakan ya zama kamar ba laifi ba kowannensu ya rik'a sunkuyar da kai wajen nemar masa bikon.

Tawagar biko na biyu daya kawo ta mata ce, wadda hakan ya had'a har da yayar mahaifiyarsa, suka zo da dad'in bakinsu, don har magiya sun had'ata da ita suna gaya mata halin da 'ya'yanta ke ciki amma daga k'arshe tashi tayi kawai ta k'ulle kanta a band'aki har suka gaji suka tafi. Ta riga ta yiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login