Showing 27001 words to 30000 words out of 153964 words

Chapter 10 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3771

mata magana da tsananin affection da kulawa irinsa, toh amma kasancewar babu da wata alak'a tsakaninsu da zata iya d'orarwa, sai taji kamar zata sulale ne k'asa ta narke.

Abu d'aya ne ya ceceta daga jiran amsarta da yake wadda bata santa ba, sautin k'ararrawar doorbell daya karad'e kaftanin falon.

"Mun dad'e ko Deelah?" Mami ta fad'a sanda suke shigowa cikin falon bayan ta bud'e musu k'ofa.

"Gaskiya baku dad'e sosai ba."

"Aah tunda Al'ameen sarkin surutu yazo ai ba zaki ga dad'ewarmu ba dama."

Cewar Mamin tana kallon Al'ameen daya fito daga kitchen d'in bayan ya biyo bayanta, ya rarumi Iman ya d'aga? ta can sama a hannunsa, ta shiga callara ihun murna tana k'ank'ame shi.

"Baby girl, muga kwak'idon gashin naki da aka gyara, yayi kyau?"

Zahra ta turo baki jin haka kafin tayi hanyar d'aki bata ko kalle shi ba.

"Allah ya kawo ranar da zaki fahimci tsakonarki nake yi."

Mami tayi dariya kawai tana k'ok'arin? fito da wasu 'yan kayayyaki da suka siyo, Sai yanzu Fadeelah ta fahimci ashe basa shiri shi yasa bata tab'a jin zancen Al'ameen a bakin Zahra ba, duk kuwa da had'uwarsa na irin mazan da take bi a social media.

Yana k'ara cilla Iman a hannunsa ya nufi d'akin Farouk inda sautin k'arar TV ya ragu jin dawowar Mami.

"Mami wasu kayan kuka siyo?"

Fadeelah ta tambaya tana kallon ledar gabanta guda biyu.

"Kaya dai na siyo, amma kinga an kawo wasu ne yau?"

"Al'ameen ya shigo da wasu d'azu suna kitchen, nayi zaton ma ke kika aike shi."

Rana ta farko da bakinta ya fara furta sunan 'Amintacce!'

Murmushin dake fuskar Mami ya k'aru kafin tace.

"Allah ya kawo mu kenan ya dawo, in dai Al'ameen ne Deelah yanzu kika fara ganin wannan d'awainiyar tasa."

A take Fadeelah taji zuciyarta ta nutse can wani k'arshe mai nisa, tana son mutum mai kyautatawa a rayuwarta.

Har ya tafi a ranar, basu k'ara magana ba don sai da Magriba ya baro d'akin su Farouk suka je masallaci gabad'aya, bayan sun dawo kuma hira sosai ta kama tsakaninsa da Mami don ta fahimci suna shiri sosai, haka kurum ta samu kanta da yawan kallon fuskarsa mai fara'a lokacin da suke hirar da Mami har sai da Iman dake gefenta ta lura.

A wannan daren lokacin da tazo kwanciya, sai wayarta tayi k'arar alamun shigowar sak'o, ta d'auko ta a hankali daga bedside drawer ta kalla.

Bak'uwar number ce a jere mai kyau, sai dai sak'on jiki ne yasa zuciyarta ta matse ta kuma kwance a take.

Hey memory loss girl!

Good night!

Murmushi mai fad'i ya sauka akan d'an k'aramin lebbenta, har ya tale zuwa tsawon da bata tab'a tunanin ya tab'a kaiwa ba.

Allah ya sani a wannan ranar kaf! ta manta cewar Al'ameen jinin Aunty Miryaamah ne.

***

"Bari in duba in gani, idan baya nan sai mu tafi."

Fadeelah ta fad'a bayan sun gama classes d'insu na ranar suna shirin tafiya gida, Romilda taja tsaki kafin tace.

"Dole ne sai kin duba? kawai ki taho mu tafi, meye amfanin zuwanki kullum yana b'ata miki lokaci?"

"Ina ga yafi da ace banje ba gabad'aya, zan miki text in zan tsaya d'in."

Lokacin da ta murd'a k'ofar Library d'in ta shiga, yana zaune daga wani sabon tebur, dogo mai fad'i, akansa tarin wasu ledoji ne kamar na siyayya. Shima ya d'ago da kansa jin an bud'e k'ofa, yana sanye cikin wata doguwar jacket light brown da gashinsa cikin wani style kamar an barbaza shi wajen goshinsa, k'arya zata yiwa kanta in har tace bai yi kyau ba.

Ya k'ifta idonsa a hankali kafin yace.

"Kin kyauta yau da baki makara ba."

Ya salam! taji kamar ya rad'a mata maganar a cikin kunnenta ne saboda yadda muryar ta fito cike da laziness.

"Bani da lokacin b'atawa yau, idan har ka san zaka sake cewa sai gobe ne, ka fad'a min tun yanzu in juya."

Kamar bai jita ba sai ya turo leda d'aya gaban teburin.

"Kizo ki duba, ina ga kamar na siyo komai daidai, in kuma akwai abinda baiyi ba gobe sai a sake siyowa."

Ba yadda ta iya, haka ta k'araso ciki zuciyarta cike da mamakin me ya siyo, Ledar farko data fara bud'ewa kayan painting ne na kaloli da kuma brushes d'in shafawarsu, ta biyu kuma tarin tarkace ne fal da suka tabbatar mata da abinda kwakwalwarta ke tunani... abubuwan da take so ne gabad'aya a cikin ledar! ma'ana duk abubuwan da suka shafi hobbies d'inta wanda ta rubuta masa jiya.

Ta shiga fiddo su d'aya bayan d'aya zuciyarta na juyawa cike da mamaki, har zuwa kan wata hadaddiyar MP3 dake d'auke da complete karatun alqur'ani... ta tuna cewar ta rubuta harda sauraren alk'ur'ani don hakan ma ya dad'a k'ona ransa, sai gashi da hannunsa yaje ya siyo ya kawo mata.

Ta kasa daure mamakin don haka sai ta d'ago ta kalle shi, ya sake lumshe idonsa kad'an sannan ya gyad'a mata kai.

"Yau zamu fara Maths, ta hanyar da kwakwalwarki zata karb'e shi."

Ya lura bakinta ya k'ulle gabad'aya, ta rasa me zata ce ko kuma abinda ya kamata tace d'in. A daidai wannan lokacin ne kuma wayarsa tayi k'ara, ganin number dake kira yasa ya mik'e da sauri ya nufi can d'aya b'arin library d'in, wajen da dogwayen durowuyin littattafai ke jere.

"Barka da aiki yallab'ai." Ya fad'a muryarsa cike da girmamawa.

Daga d'aya b'angaren wayar aka amsa.

"Barka dai Adam, komai lafiya?"

"Lafiya k'alau, komai yana tafiya daidai."

"Babu wani suspect?"

"Babu ranka ya dad'e daga malaman har d'aliban babu mai zargin wani abu har yanzu."

Da alamun gamsuwa a muryarsa ya sake tambaya.

"Ka kusa gamawa?"

"Duk da ya amince dani a yanzu, wasu abubuwan baya sakin jiki akansu sosai, amma dai a yanzu ma akwai evidence da yawa."

"That's good, kuma babu wata matsala data k'aru?"

Wannan maganar tasa ya juya a hankali ya kalli Fadeelah dake tsaye tana ta juya kayayyakin nan?har yanzu, bayanta kawai yake iya gani daga nan, amma zuciyarsa na iya karanto labarin kan fuskarta, musamman daga cikin wad'annan idanun nata...

Sai ya girgiza kansa kawai, ita d'in kamar nauyinsa ce a yanzu ba zai tab'a sanyata cikin lissafinsu ba.

A hankali muryarsa mai taushi tace.

"Babu wata matasala ranka ya dad'e, kuma ina k'okarin kare duk wata hanya da zata fito da cewar ni LAWYER ne!"

*?%O??%*


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

09

(&_&)

"Mu fara?"

Muryarsa ta tambaya bayan ya dawo daga wayar daya amsa. Ta juyo da idonta t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a kalle shi, me yasa ne wai yau yayi kyau a idanunta?

Har yanzu bakinta ya k'ulle ta rasa me zata ce, don haka sai ta d'aga kanta kawai sanda yaja kujerarsa ya zauna, tana shirin zama a ta gabanta ya tsaida ita ta hanyar d'ago mata zara-zaran yatsun hannunsa.

"Wane irin lenses kike amfani da shi a glass d'inki?"

"Aspheric."

Ya gyad'a kansa a hankali.

"Yana nuna rubutu a juye ne?"

"Kamar yaya?"

"Ina nufin idan nayi rubutu anan, zaki ganshi a daidai daga nan?"

Ta gane me yake nufi amma bata da niyyar magana saboda haka ya nuna mata kujerar dake gefe da d'an allinsa, wadda dama kamar ya tanade ta ne saboda ita. Bayan d'an gajeren tunani taga cewa bata da zab'i saboda haka ta saki kujerar ta zagayo a hankali ta zauna a gefensa.

Sassanyan k'amshin turerensa kuwa ya nemi k'ofofin hancinta yayi masauki, sai ta runtse idonta kad'an jin k'amshin da kwakwalwarta ta yiwa tambari da NASA.

Ya jawo ledar farko mai d'auke da kalolin zane, ya b'are su daga cikin ledojinsu sannan ya d'auko wata farar cardboard paper a gefe.

"Abu na farko da kika fara rubutawa jiya shine kina son zane (painting), don haka dashi zamu fara."

Yanzu da take kusa dashi, sai taji kamar ya lalubi kunnenta ne yana rad'a mata maganar, saboda haka sai ta karkatar da kanta kad'an.

Ya bud'e robobin kaloli guda goma sha biyu.

"Daga 0 zuwa 9, kowacce number zan zana ta da kala daban, sai ki rik'e kalolinsu yadda idan muka fara amsa tambayoyin, kwakwalwarki zata karbi kowacce number da irin kalarta, za'a samu saukin hargitsewarta wajen gane nambobin."

Bata ce komai ba ya cigaba.

"0 - green, 1- blue, 2 - orange, 3- yellow, 4- red, 5-...."

"Kayi d'aga muryarka bana ji sosai."

Ta katse shi. Ya juyo a hankali ya kalleta.

"I'm sorry haka muryana yake, ina damunki ne?"

Kamar yaya yana damunta? yana tunanin muryarsa tana da wani tasiri akanta ne?

Ta girgiza kanta da sauri.

"Ta yaya zaka dame ni, ka cigaba kawai ina jinka."

Bayan ya juya tasa yatsanta d'aya ta k'asan glass d'inta, ta duba kwarmin idonta da tunanin ko kwantsa ya gani a ciki, don ta lura duk sanda zai kalle ta cikin idonta sosai yake kalla kamar mai son lalubo wani abu nasa da ya tab'a rasawa.

Da wata tambaya guda d'aya a topic na farko 'Pythagoras' suka fara, kamar wasa ko wani abu ma majigi, sai gashi? a hankali Fadeelah ta fara gane abinda yake yi, saboda yadda yake bin kowanne step na lissafin daki-daki cikin rubutunsa mai tsananin kyau da kuma yadda raunanniyar muryarsa ma ke mata bayanin kamar ana zirara ruwa cikin roba a hankali.

Sannan dad'in dad'awa da taimakon yadda kowacce number ke fitowa cikin nau'in kalarta daban, sanda suka gama tambaya ta farko sai yayi kama da draft d'in zane, ta dinga gani a idanunta yadda zata ja kowacce kala zuwa 'yaruwarta har su had'u su fitar da wani hoton. Lissafin da ake yinsa a aji tana ganinsa kamar wani tashin duniya sai ya zama kamar d'an uwan zanenta a yanzu har taji ta k'agu a tafi wata tambayar don ta samu a sake fitar da wani abun.

Wasa-wasa, a cikin awa guda kawai sai ta suka amsa tambayoyi hud'u, wanda babu wanda bata fahimta ba a cikinsu, Allah ya sani kwarai ta jinjina masa yadda ya iya mata bayanin cikin nutsuwa, sai yanzu ta fahimci zancensa da yace zasu iya gama gabad'aya topics d'in cikin lokaci.

A wannan daren bayan ta gama dukkan harkokinta na ranar, tayi sallah sannan tayi wanka, ta saka wata 'yar k'aramar riga armless iya gwiwa, sannan ta d'ago cardboard paper da ta amsa question guda d'aya da yace in ta koma gida tayi, rana ta farko a rayuwarta data amsa lissafin Maths kuma tayi daidai, don ya rubuta mata final answer a bayan paper yace in har tayi daidai amsar da zata samu kenan, kuma bayan ta dawo gidan ta kasa ko cin abinci sai da ta zauna tayi, haka tayi ta zagaye gidan da murna? rik'e da paper su Mami ma na taya ta.

Ta rufe idonta a hankali, sanda fuskarsa ta ranar ta haska a cikin su, tana son kalar brown sosai watakila shi yasa shigarsa ta yau tayi mata kyan da har ta kasa manta ta.

Ta hango yadda gashin idonsa ke kwantawa akan na k'asansa duk sanda yake rubutu, sai kaga kamar ya rufe idon ne gabad'aya. Me ya same ta ne wai? ya kamata tayi wa kanta fad'a, Adam d'in data tsana kamar me shine tun ba'a je koina ba take b'ata lokacinta wajen tunaninsa? don kawai ya koya mata maths ta gane? wannan ma ai shirme ne.

Ta ja tsaki a hankali sannan ta ninke paper ta ta ajiye akan bedside drawer, daidai sanda wayarta dake gefe tayi haske alamun shigowar message.

Memory loss girl kin kwanta?

Ta karanta sak'on da muryar Al'ameen kamar yadda number ta nuna shi ya aiko, a cikin kwana biyu ta fara sabawa da Al'ameen sosai ta hanyar chatting d'in da ta koya ta dalilinsa, don kullum zai aiko mata da text lokacin da zata kwanta wani lokacin ma har da safe kafin tafiyarta makaranta, sai dai bai k'ara zuwa ba don kullum yana gaya mata abubuwan sun masa yawa, don harkar settling d'insu a garin da komai yana hannunsa.

Da murmushi a fuskarta hannayenta suka rubuta.

A'a

Beeem!

Wani sak'on ya shigo a take.

Thank god ban tashe ki ba, kin yini lpya?

Lafiya k'alau. And you?

Dama baki tambaya ba, don nasha wahala sosai yau, in na fara gaya miki zaki tausaya min.

Ta sake wani murmushi sannan ta rubuta.

Me kayi?

Intrested? ya tambaya.

Yes.

Ta tura sak'on da ya haddasa doguwar hira a tsakaninsu, doguwar hirar data shafe ta kuma wanke tunanin Adam a kanta!

***

Adam ya rufe idonsa a hankali yana hasko nata daga ciki, idanun dake hana masa sukuni a kowacce bullowar rana zuwa fad'uwarta, musamman a kowanne dare lokacin da zai zo kwanciya. Ya lullub'e jikinsa da bargo baki d'aya kamar hakan ne zai hana shi tunanin idanun nata kafin bacci ya d'auke shi.

A baya inda zai karanta cewa wani abu zai zo ya dami kwakwalwarsa bayan burin da yake dashi, zai k'aryata koma meye ne kuma yayi sanadin dakatar dashi.

Sai dai sanin gaibu baya hannun d'an adam, a yanzu ya tabbata koda wani zai kawo masa hanyar da zai cire tunaninta daga kansa ba zai tab'a karb'a ba, don watak'ila ya saba koma yana jin dad'in hakan.

A hankali tunaninsa ya gangara can baya zuwa wani lokaci baya kad'an...

*WANI LOKACI BAYA KAD'AN.*

K'arfe takwas da rabi na safiyar ranar talata, had'addiyar motarsa tayi parking cikin jerin gwanon motocin dake harabar ma'aikatar kotun.

Ya d'auki ragowar lemonsa dake gefe yana d'iga saboda rab'ar sanyi ya k'arasa shanye shi sannan ya zare bak'in gilashin dake fuskarsa, kwayar idonsa mai kyau ta haska a cikin d'an karamin mudubin dake gaban motar, gashin kansa a kwance yake cikin style mai kyau yana kyalli sannan yana da saje amma ba mai yawa ba, mai laushi wanda yabi ya kwanta kan fatarsa mai kama da launin chocolate mai haske.

Ba wai fuskar tasa yake kallo ba, a'a tunani ne fal a cikin kansa wanda zuciyarsa ke d'ebewa da tarawa a hankali. A jiya ya gama case d'in da yake aiki akai kuma yayi nasara, yana fatan hakan ya bashi ikon samun hutun watanni ukun da yake nema wanda zai saita rayuwarsa dasu, ya san abu ne mai wuya a yanzu da ba lokacin leave d'insa ba ya samu hakan shi yasa ya dage iya k'okarinsa ba dare ba rana ya had'a evidence d'in da suka bashi damar cinye shari'ar da fatan a dubi nasararsa a bashi wannan damar.

Ya jawo 'yar k'aramar briefcase d'insa dake kan kujerar mai zaman banza sannan ya fita daga motar, ta tsakanin d'inbin motocin dake tsaye a wajen yayi ta kurd'awa har zuwa cikin tamfatsesiyar kotun.

"D'an k'araminsu babbansu kenan!"

Muryar wani abokin aikinsa ta fad'a sanda ya nufi hanyar elevator d'in da zai kaishi ofishinsa.

"Ka san jiya ban zauna ba, ashe an gama case d'in nan kuma kayi nasara, gaskiya Man na taya ka murna kayi k'ok'ari sosai, weldone Steve! "

Ya kirashi da surname d'in da suke kiransa a kotun.

"Thank you Ryan, Nagode sosai."

Ya amsa da muryarsa mai zurfi sanda ya bud'e elavator suka shiga bakid'aya, sai dai kafin k'ofar ta kai ga rufewa wani lawyer mai suna John ya shigo rik'e da files d'insa, bai ko? kalle su ba ya nemi waje ya tsaya, lift d'in ya shiga d'agawa.

"Ka san me, zan zo in karb'i clues a wajenka, don ina assisting wani case lowcoast court shigen naka, wa ya sani mu ma muyi nasara in mun bi irin hanyoyin da kayi amfani dasu saboda..."

Ryan ya cigaba da magana lokacin da gravity na lift d'in ke d'aga su sama, sai da hankalin Adam kwata-kwata baya kansa, yana ga mutumin nan dake gabansa hannayensa rik'e da files, haka kurum jikinsa ya bashi wani abu, don mutumin yana d'aya daga cikin 'yan team d'in da suke adawa dashi tun farkon fara aikinsa a wajen wanda yanzu shekara guda kenan.

Zarginsa ya k'ara tabbatuwa lokacin da John d'in ya tsaya a hawan da office d'in shugabansu yake, saboda haka ya sawa zuciyarsa ta yarda cewa dole akwai wani abu da aka shirya masa yau wanda ke shirin faruwa, don ya fahimci cewa an daidaici lokacin zuwansa ne ma aka saka John yazo rik'e da wad'annan files d'in don a nuna masa daga ina koma meye ake shirin k'ulla masan ya fito.

Da kyar ya samu ya tserewa surutun Ryan ya k'arasa cikin office d'in nasa. Kasancewar jiya ya gama case d'insa sai ya zama ba abinda zaiyi yau illa rubuta wasu dokoki da zai turawa wani d'an kasuwa kan sha'anin da ya shafi kasuwanci.

Wajen k'arfe goma ya jawo wayarsa ya danna kiran da kusan kullum yake saman call log na wayarsa, kiran kuma da ya san ba zai tab'a amfanarsa da komai ba.

"Hello, barkan ka dai, kana magana _ne da gidan kula da tsofaffi da masu rauni na garin Leicester a k'asar England."

Ya lumshe idonsa kad'an jin wata sabuwar murya ba ta matar daya saba ji in ya kira ba. A hankali ya amsa.

"Barkanki da aiki, ina neman wata mata ne mai suna Magareth, ance min tana tare daku."

"Haka ne kwarai Magareth tana tare damu, waye kai a wajenta? d'anuwa ne?"

"A'a..." ya amsa abinda yake fad'a kullum, sannan ya cigaba da k'arashen.

"Ina son inyi mata wasu tambayoyi ne game da IYAYENA!"

"Na fahimta amma sai dai kayi hakuri, magareth ta tsufa da yawa kuma tana da lalurar kunne bata iya amfani da yawa, sai da kazo da kanka in har kana son amsar tambayoyinka, zata ji dad'in zuwanka!"

D'ib! ya kashe wayarsa sannan ya koma da baya ya kwanta a jikin kujerar, a kowacce safiya dake fitowa magareth k'ara tsufa take, don haka dole ne yayi k'ok'arin samun lokacin da zai isa gareta kafin ta mutu, damar da yake da ita guda d'aya ta tankwab'e.

Da kyar ya samu ya saita tunaninsa, sannan ya koma kan aikinsa ya cigaba. Da misalin k'arfe sha biyu na wannan ranar kuma ya samu kiran da ya sawa zuciyarsa tsammaninsa, ya samu kiran da ya canja akalar rayuwarsa kamar yadda igiyar ruwa ke tambali da k'aramin jirgi a tsakiyar teku.

"Na taya ka murnar samun nasara akan case d'inka."

Muryar shugaban nasu ta ambata lokacin da yake zaune a kujerar tsallaken teburin bayan ya amsa kiransa.

"Nagode sir." Adam ya fad'a a hankali kamar koyaushe.

"... sannan naga proposal d'inka cewa ka nemi hutu na wata uku ko?"

"Haka ne sir, ina da wani abu mai muhimmanci ne da nake son yi a yanzu."

Sai ya tab'e bakinsa kad'an.

"Amma ka san baka dad'e da karb'ar hutu ba ko?"

"Na sani, shi yasa na nemi hakan a matsayin alfarma."

Shiru ya biyo baya kafin ya sake magana.

"Mu ajiye zancen hutunka a gefe Steve, akwai aikin da shigo yanzu kuma ba wanda ya dace dashi sai kai... saboda haka wannan ba case ne da zaka yi din ra'ayinka ba, case ne da ya zama umarni bama daga ni ba, daga can shugabanmu gabad'aya kuma babu wanda ya isa ya canja shi."

Adam bai ko yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login