Showing 105001 words to 108000 words out of 153964 words

Chapter 36 - BAYAN NA MUTU Book Original By Aisha Shafii.doc

30 Aug 2025

3792

akan kumatunsa, ta d'ago da screen d'in wayarta ta kalli fuskarta, wata koriyar kala ce ta shafi a gefen kumatunta, sai ta juya da sauri ta zaro tissue a jakarta ta shiga gogewa...

Tana tare dasu Fateemah, Rahma da wasu tarin k'awayensu a cikin d'akin Aseeyah ranar da aka kaita, Rahma ta bud'e labulen tagar d'akin ta hango can wajen gate, To Asee da fatan kin shirya ga Ango nan tafe, Aseeyah ta d'ago da fuskarta tace, Ya k'araso mana, shiri na yaushe kuma? Suka kyalkyale da dariya bakid'ayansu...

Tana zaune a gaban Daddy, yana yi mata nasihar dake shaida cewa ya bada aurenta ga Al'ameen, kuka take yi, na farin ciki da kuma bak'in cikin cewa rayuwarta zata d'ore ba tare da sanin Danginta ba...

Tana zaune ranar bikinta da Al'ameen, lokacin da Mc ke kiran su Zahra filin rawa, lokacin da Sadiya ta tunkud'o Mairo tsakiyar rumfar da take zaune... Lokacin da rayuwarta juya, ta gangara sannan ta tankad'a gab'ar ramin da a yanzu take tunkararsa.

Ta lumshe idanunta a hankali sannan ta bud'e su tar! Akan gefen zanin matar dake fuskantarta... in har duk wad'annan abubuwan sun faru da ita a rayuwarta ta baya, me ya rage zai tsorata ta kuma a yanzu? Ta san cewa tabbas wannan wani sharrin ne daga su Kawu Danjuma tunda har bata ga Habiba tare dasu ba, amma tun lokacin da ta farka a asibiti ta yiwa kanta alkawarin dake zuciyarta ga dukkan wani k'alubale daga gare su, ta rantse zata fuskance su a matsayin wannan DANGIN nata da tun usuli basa k'aunar wanzuwarta a duniya.

Ta rufe idanunta gaba daya sanda motar taja ta tsaya sannan rugugin bud'e gate d'in KURKUKUN daga can waje ya cika kunnuwansu.

Barka da zuwa Fadeelah.

Ta yiwa kanta gaisuwar da babu mai yi mata.

****

"Muna da dokoki anan..."

Muryar wata k'atuwar mata ta karad'e d'akin da aka tsayar dasu bayan shigarsu cikin kurkukun.

"... Kuma dole ne kowaccenku ta kiyaye su walau dad'ewa zaku yi a wajen nan ko kuma akasin hakan, bayan dokoki akwai ayyuka da muke rabawa kala-kala kuma dole ne kowannenku yabi su don mu zamu gaya muku yadda zaku yi komai anan,??sanda zaku tashi, sanda zaku yi aiki, sanda zaku ci abinci sannan sanda zaku kwanta. Ba'a tashin hankali a wajen nan, duk wadda tayi mana taurin kai zata fuskanci hukunci mai tsananin da zata gwammace kashe ta akayi a maimakonsa."

Yadda take magana idanunta a tsaitsaye da kuma sautin muryarta ya tsorata wasu da yawa daga cikin matan amma banda Fadeelah, ta riga ta saba had'uwa da mutane masu irin wannan siffar na baiyana tsana k'arara daga kowanne b'angare na rayuwarta.

Wasu matron biyu ne suka tafi dasu cikin wani gini daga nan, aka kaisu wajen da aka d'auki jinin kowaccensu don tantance lafiyarsu, bayan nan kuma dukkansu aka auna fitsarinsu don ganin inda akwai mai ciki.

Daga nan a mik'e hanyar wasu band'akuna a jere aka kaisu.

"Akwai sabulu a ciki kowacce ta wanke jikinta sannan karku maida kayan dake jikinku, akwai zannuwa a gefe daga ciki."

D'aya daga cikin matron d'in ta fad'a sanda mutum bakwai suka shiga cikin kowanne toilet d'aya. Daga inda suke tsaye Fadeelah na hango k'afafun kowacce daga cikin matan kasancewar k'ofar bata kai har k'asa ba, hakan yasa ake iya ganin fasashshen simintin dake cikin kowanne band'aki, yayi ramuka wanda kowanne bak'in ruwa ya taru cikinsa.

Zuciyarta ta tashi a lokaci guda taji tana shirin yin amai, sannan wani abu ya shiga zarya a tafin k'afarta saboda tsananin kyankyami, anya zata iya zama anan kuwa? Me yasa bata tambayi mutumin nan ko za'a iya samun number Adam ba?

"Ina da magana dan Allah..."

Muryar wata mata a bayan Fadeelah tayi magana.

"...inaga ni ba sai nayi wankan.."

Bata k'arasa ba d'aya daga cikin Matron d'in nan ta buga mata wani bak'in sanda dake hannunta a fuska, matar ta dafe gefen fuskarta yayin da jini ya fara fitowa daga hancinta.

Matron d'in ta lailayo wani zagi ta rafka mata sannan tace.

"Mu ke da iko daku yanzu ba ra'ayin kanku ba saboda haka kar ki kuskura ki sake magana idan ba'a tambayeki abu ba, gargad'i ne ga kuma dukkanku."

Tana rufe baki idonta ya kai kan Fadeelah, ta nuna ta da sandan hannunta tace.

"In kika kuskura kika yi mana amai anan sai naci uw*rki."

"Ku fito! Lokaci yayi!" Daya Matron d'in ta kwalla wa na ciki kira. Ba b'ata lokaci kowannensu ya fito rufe da wani yamusashshen zani, Fadeelah ta had'iye yawun cikin bakinta sannan tabi layin matan dake shiga band'akin.

Bayan kowannensu ya fito suka shiga wata k'ofa daga nan wajen inda k'aton d'aki ne mai cike da buhunhuna na kaya, wata k'atuwar mace ce a wajen kamar Matron d'in farko da suka fara gani, ta kintaci yanayin kowaccensu sannan ta shiga mik'o musu uniform na kurkukun mai kalar ruwan toka, kowacce kala biyu, sannan pant, da brassier, slippers, da kuma man shafawa roba d'aya.

Bayan sun shirya aka raba su gida biyu, anan Fadeelah ta fahimci a cikin su goma sha takwas, su biyar ne kawai ba'a yanke musu hukunci ba amma duk sauran da adadin watanni ko shekarun da zasu yi akansu.

Su da ba'a yanke musu hukunci ba d'aki daban aka kaisu inda wani mutumi ya d'auki hoton passport d'insu ya lik'a a jikin forms d'insu da aka kawo daga can kotun.

_Shikenan! Ta kafa tarihin da har abada ba zai goge a rayuwarta ba!_

A cikin su biyar d'innan Fadeelah taga harda wannan 'yar k'aramar yarinyar data gani a mota, ta daina kukan da take d'azu, da alama tayi ne har zuciyarta ta k'ek'ashe don idonta a tsaye yake kyam! Tanabin fuk umarnin da aka bata?kamar inji.

A lokacin da aka gama komai aka sake had'e su da sauran, sai aka raba su gurin wasu matron shida, kowacce Matron aka bata mutum uku.

"Daga gobe za'a raba ku b'angare-b'angare na kalar ayyukan da zaku yi, yanzu za'a raba muku cell kuma nan zai zama wajen kwananku daga yau."

A sannan ne Fadeelah ta had'a ido da wannan yarinyar, sanda matron d'in da aka basu taja su zuwa wata hanya daban da inda su suke, Fadeelah bata san me yasa ba, amma ta hango wani zurfi a idon yarinyar makamancin nata, ta had'iye yawu a hankali sannan ta juya tabi tasu Matron d'in, bata sani ba ko zata sake ganinta.

Babu kowa a harabar wajen har suka shiga wani dogon gini mai d'auke da tambarin *'Block G'* wata irin hayaniya ta shiga kunnensu a lokacin da Matron d'in ta bud'e k'ofar wajen, Fadeelah ta juya kowanne b'angare na hall d'in ta kalli d'imbin fuskokin dake lek'owa daga kowanne cell, dukkaninsu mata ne sanye da uniform irin na jikinta da kuma sauran mata biyun da aka shigo dasu tare, bayan hayaniyar wani abu kamar tsami ko wari ya ziyarci hancinsu, Fadeelah taji cikinta ya juya aman d'azu na shirin dawo mata, anya bata yi kuskuren k'in kiran su Mami ba ko Kawu Sulaiman? Ta yaya zata fara zama anan?

Taji kamar a cikin ruwa take tafiya lokacin da suke wuce tarin cells da maganganun matan dake lek'owa daga cikinsu, kwakwalwarta ta riga ta rufe a lokacin don haka bata iya fahimtar komai ba sai fito kawai dake fitowa daga kusan kowanne cell.

Matron d'in ta bud'e wani cell daga b'arin hagu.

"Shiga." Tace da Fadeelah da kuma d'aya daga matan.

Gabanta ya fad'i sanda matar ta shiga, ta d'an tsaya kad'an kafin tabi bayanta, garam! K'ofar ta rufe, Matron d'in tayi gaba tare da d'ayar matar.

Kunnen Fadeelah ya amsa sautin k'arara rufewar k'ofar kamar wani abu dake gaya mata cewa sake fitarta zuwa duniyar waje abu ne mai wuya.

Fuskoki hud'u da suka juyo suka zuba musu ido yasa ta fahimci kowanne cell mutum shida ne, duk kuwa da cewar bashi da girma, wasu siraran gadajen k'arfe guda uku k'anana sai toilet na tsugunne daga can gefe inda aka kare rabinsa da katako, akwai kan famfo a samansa, amma babu alamun ruwa don warin daya gauraye iskar d'akin ta tabbata daga shi ne, Ya ilahi! Watak'ila dai mafarki take yi! Bai dace ta tsinci kanta a irin wannan wajrn ba.

"'Yanmata biyu a rana d'aya."

Muryar wata mace ta shaida mata cewa a tsakiyar zahiri take! Babbar mace ce a jiki da kuma shekaru tana zaune daga kan gadonta tana kallo su, hak'oran cikin bakinta data washe sune kad'ai abu mai haskawa a fuskarta, a saman gadon kuma wata 'yar siririyar ce da fuskarta ke nuna alamun k'abila don ga bille nan rad'au? fuskarta.

Sauran matan biyun suna zaune a k'asan sauran gadajen suna kallonsu, ko kuma tace mace d'aya kawai, wadda ta zame hannun rigarta d'aya tana shan iska, amma ta bayanta babu marabar kammaninta dana maza, jikinta mai tsawo ne da girma sannan babu wani alamun tsari irin na jikin mace, komai nata ihun fad'i yake yi.

Ta katse nazarinta ta hanyar washe bakinta sannan tace.

"Barkanku da zuwa, bak'inmu."

Fadeelah ta lumshe idanunta cike da rud'ani.

Ashe da mai yi mata Barka da zuwa.

***


BAYAN NA MUTU!

?AYSHA SHAFI'EE

34

(&_&)

Watak'ila tafi minti biyu a tsaye tana kallon 'yan kananan kwarukan dake layi suna bin gefen yamusashshiyar katifar da aka nuna mata a matsayin gadonta, sama ne amma bashi da maraba da k'asa don tsalle d'aya kawai mutum zai yi ya haye.

"Mun gama gaisawa da 'yaruwarki, ke yaya sunanki?"

Wannan mai siffar mazan ta fad'a sanda ta tsaya a gefen gadon. Kallo d'aya kawai Fadeelah tayi mata sannan ta fad'i sunan dake rubuce jikin form d'inta.

"Bintu."

Ba zata tab'a bari wajen nan ya amsa sunan Fadeelah ba, Fadeelah mai wankakkiyar zuciyar ce da ko k'uda bai tab'a mata sharri ba, zata kare martabar wannan sunan daga samun gurbi a k'azamin waje irin wannan, duk kuwa da cewar sunan ya fara sulalewa daga gareta, Bintu ta riga ta dawo tayi kane-kane da komai na rayuwarta... Banda su Mami da kuma Adam da ta sani a America watakila da ita kanta ma ta fara manta cewa ta tab'a zama Fadeelan.

"Sunana Kenken..." Matar ta cigaba sannan ta juya ta nuna d'ayar nan mai cirarriyar hannun riga.

"Waccan sunanta Gheto..." Sai ta nuna wannan Babbar da har yanzu ke kallon Fadeelah tana washe baki.

"Wannan itace shugabarmu a d'akin nan, sunanta Lalita, sannan Zazu..." Ta nuna mai kama da k'abilar nan ta saman gado.

Yanayin fuskar Fadeelah ya shaidawa Kenken cewa sunayen basu bada ma'ana a kwakwalwarta ba, saboda haka tayi wani karkataccen murmushi wanda daga gani ta saba yinsa sannan tace.

"Ba sunayenmu na gaskiya bane, inkiya ce muke kiran kanmu da ita don mu manta da rayuwarmu ta waje,?duk wanda kika gani a wajen nan yana da sabon suna don haka kema kwanan nan zaki samu naki, "

Bata ce komai ba Kenken ta cigaba da cewa.

"Karki damu kowa anan ya shiga irin halin da kike ji zaki ware nan da lokaci kad'an, kin riga kin shigo cikinmu yanzu, zamu zama 'yanuwa kuma abokai mu taimaka miki ki fara sabuwar rayuwa, ki manta da komai ki kuma samu duk irin dad'in da kika baro a waje."

Ta k'arashe da murmushi tana k'ok'arin dafa kafad'unta, amma sai ta matsa baya da sauri sannan ta juyar da kanta, haka kurum zuciyarta bata amince da kenken ba ko d'aya daga cikin sauran 'yanuwanta.

Hakan da tayi kuma bai b'ata ran matar mai kama da maza ba, sai ma murmushi da ta sake yi sannan ta d'auke hannunta daga iska.

"Kar ki damu Binbi, muna da isashshen lokaci ai."

Taji sunan da ta kira ta, amma bata so ma ta yardarwa kanta cewa ta jin, saboda haka ba tare da ta k'ara kallon kowaccensu ba ta janyo katifar kan gadon ta karkad'e ta. Zan zauna zuwa wani lokaci,ta ayyana a ranta. Zata daurewa zama da mutanen nan kafin lokacin da za'a sanar dasu Kawu Ibrahim yazo yasa a bata cell ita kad'ai, Kafin kuma dawowar Adam yazo ya fitar da ita gabad'aya.

A lokacin wata iska ta kad'o ta tsakanin k'arafan k'ofar cell d'in, wani tsami ya taho ya kuma kwaso warin toilet d'in cikin cell d'in ya baza shi a iska, Fadeelah ta saka duka hannayenta biyu ta rufe hancinta da bakinta, don ta raba kanta da warin don kuma ta hana kanta ihun dake shirin fasowa daga k'irjinta.

"Wai baki da lafiya ne?" Muryar wadda Kenken ta kira da Zazu ta tambaya daga saman gadonta.

Bata bata amsa ba, haka bata juya ba har saida ta tabbatar ta kwantar da kukan dake neman 'yancinsa sannan ta maida katifar ta hau gadon, ta d'ora kanta akan kayan da aka bata sannan ta duk'ule duka jikinta.

Ta daurewa abubuwa da yawa a baya, don haka wannan ma zata daure masa.

Zata daure.

Zata daure.

***

Bayan kwana biyu.

Ba mafarki bane, tunani ne kawai cikin bacci, don babu abu d'aya da ya canja na wancan lokacin.

A wannan d'akin ne....

Cikin kotun da suka baro, inda d'aurarru ke ganawa da baki, Lokacin da Adam ke bacci a gabanta....

Wani irin tausayinsa ne ya dirar mata a sannan, don bayan sajen da taga ya tara, wannan baccin shine abu na biyu daya tabbatar mata cewa baya samun isashshen hutu a kwanakin nan... Duk saboda shari'arta.

Ta lumshe idanunta a hankali tana cigaba da kallonsa.

Shine wanda ta tsana a wancan lokacin da zuciyarta bata fahimce shi ba.

Shine wanda bata ko son inuwarsa da tata su kasance waje d'aya.

Sannan shine wanda a baya take ganin kamar yana rik'e da makamin tarwatsa rayuwarta.

Sai dai wannan bayan ta riga ta wuce, ta dad'e da shud'ewa tun farkon lokacin da k'addarar koyon karatu ta had'a su, wani b'ari na zuciyarta ya bud'e har ta fahimci b'oyayyun halayen da yake binnewa a bayan fuskarsa... Wannan fuskar dake gigita d'aukacin matan makarantarsu tana saka musu yardar cewa shine k'ololuwar duk wani fatansu.

Ta sake lumshe idonta tana kallon yadda yake baccinsa tsakani da Allah, zuciyarta cike take da hasashen wace irin k'addara ce ta cillo shi Nigeria kuma kan hanyarta.

Ta cije gefen lebb'enta kad'an tana hasko ma'anar K'addara a cikin kanta... Hukuncin Allah ne da babu tunanin wani d'an adam d'in da ya isa ya kai gejinsa, ta yarda da wannan har cikin ranta don in a yanzu in ba hukuncin Allah ba ta yaya shi d'in data baro a can wata nahiyar duniya zai tsallake koina yazo ya same ta har cikin 'yanuwanta anan? Kuma sab'anin a baya, yanzu ya zama mai fafutukar ceto rayuwarta?

Duk da baccin da yake yi, mai kallonsa zai iya tsinto zallar halayen da kowanne cikakken Namiji ya kamata ya tara, dogaro da kai, juriya, jajircewa, sanin ya kamata da kuma zurfin tunanin da zai zarta na tarin mutane.... Kyawunsa mai sanyi ne ba kamar Al'ameen ba mai manyan kyau.

Al'ameen.

Tuna sunansa da tayi ya dawo mata da zagayen rayuwarta da tasa, ta tuna cewa har ta fara taka matakin zama Amarya.

Amaryar shi d'in da a yanzu bata san wane hali yake ciki ba, Mami ta gaya mata komai ya tsaya saboda rasuwar mahaifinsa amma ta san ta fadi hakan ne don ta lullub'e ta daga ainihin gaskiyar... Gaskiyar itace komai ya cakud'e saboda abinda ya faru da ita da kuma rasuwar mahaifin nasa.

Zuciyarta na tausayinsa kuma tana kewarsa, kewar cewa da tuni suna tare yanzu, da ta dad'e da zama mallakinsa a can k'asar da zuciyarta bata marari, k'asar da komai kud'inka babu wani sakewa a matsayinka na musulmi kuma mai banbanci da kalar fatarsu, sannan k'asar da zata nesanta ta da duk wasu danginta sai nasa kawai, nasan dake d'auke da mahaifiyarsa wadda ta kwana da sanin cewa bata k'aunarta... Amma banda wad'annan abubuwan zuciyarta ta san cewa zamanta da Al'ameen zaiyi dad'i, don Allah ya sani ko a yanzu da komai na rayuwarta ta baya ya dawo mata ba zata iya kwatanta kowa dashi a kyautatawar mu'amala ba.

A sannan ne k'ofar wajen ta bud'e, mai tsaron nan Musa, da Adam ya umarci ya basu waje ya lek'o da kansa alamun iya lokacin da aka d'iba musu yayi.

Da sauri ta janye idonta daga fuskar Adam ta kalle shi.

"Yallab'ai inaga kamar lokacin da aka d'iba ya k'arato." Ya fad'a yana kallon bayan Adam d'in, kasancewar ita take fuskantarsa.

"Yi hakuri Malam Musa..." Zancen ya fito cikin hardaddiyar hausar Adam.

"...yanzu muke shirin kammalawa."

Da tsananin mamaki tayi saurin juyowa daga kan Malam Musa ta kalle shi, dama ba bacci yake ba? dama idonsa biyu yayi shiru ya barta tana ta kallonsa?

Malam Musa ya gyad'a kansa sannan ya koma ya maida k'ofar ya rufe, Sai tayi sai ta d'auke kanta sannan ta mik'e tsaye tana sake cukwuikwuye ledar hannunta.

"Kin gama? Zan iya tafiya?" Taji muryarsa ta fito kamar had'e da murmushi.

Ya ubangiji ya Allah! Ta gama me? Kallon nasa? Ko me? Dame zata kare kanta tace ba haka bane, watakila kawai idan k'asa ta tsage ta shige komai zai fi sauk'i, amma simintin dake k'asa yak'i bud'ewar.

Ya taso rik'e da waya da kuma tarkacen su jotter ya tsaya a gabanta, taji girmansa kamar na wata katuwar bishiya a kusa da ita, cikinta ya yamutse sannan yawu ya shiga zaryar shigewa mak'ogwaranta, ta gagara ko motsa kafafunta.

A hankali taji yace.

"Zan yi tafiya jibi..."

Ta dago da sauri ta kalle shi.

"... Na gaya miki a zama na gaba mu zamu fara gabatar da shaidu, to zanje wani bincike ne akan abinda nake tarawa saboda haka ba lallai ki k'ara gani na ba a cikon kwanakin nan, may be sai ranar da za'a zauna."

K'arar kiran wayarsa a wancan lokacin yayi daidai da k'arar k'ararrawar da ta karad'e d'akin.... K'ararrawar data tashe ta daga tunanin rabuwarta da Adam na k'arshe.

Ta kalli yanayin lokacin, wajen k'arfe uku ne na rana, wanda ya kama lokacin da kowa zai tafi yin aikinsa kamar yadda yake tsare a jadawalin tsarin wajen da ta riga ta haddace.

5:00 A.M? Za'a kad'a k'ararrawar tashi.
5:15 A.M wanka da alwala
5:30 A.M Za'a fito sallar Asuba.
5:40 A.M Za'a koma cikin cell.
6:00 A.M Za'a fito kowa ya tafi gurin aikinsa.
10:00 A.M Za'a tafi wajen cin abinci.
10:30 A.M Za'a tafi wajen motsa jiki.
11:00 A.M Za'a koma gurin aiki.
02:00 P.M Za'a tafi yin sallar Azahar.
02:30 P.M Za'a koma cell.
03:00 P.M Za'a koma wajen aiki.
04:00 P.M Sallar la'asar.
04:30 P.M? Za'a tafi wajen koyon sana'o'i.
06:00 P.M Sallar Magriba.
06:30 P.M Za'a tafi cin abincin dare.
07:00 P.M Za'a koma cell.
08:00 P.M Sallar Isha'i.
08:50 P.M K'ararrawar shirin kwanciya.
09:00 Za'a kashe fitila kowa ya kwanta.

Ranar yau, ita ke shaida cewa kwananta biyu a wajen, kwana biyu cikin wata sabuwar uk'uba ta rayuwa ba tare da zuwan 'yanuwanta ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login